Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ÿþ[21/02, 12:51] Mum Sayyeed&Noord'þ: *RUMBUN QAYA*       Free Page 1 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA BIYAR 2023=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý ***Tafiya me tsawon gaske ta iso da su Kano daga Yolar Adamawa, tun tana dauki da mararin zuwa har ta soma sarewa ganin tafiyar ba ta kare bace. Kallon tagar motar tayi lokacin sun iso garin na Kano ana gaf da kiran sallar magriba, karo na biyu kenan da tazo Kano tun bayan barin su, wanchan zuwan din ma ba zata iya dorar da komai akai ba dan bata da cikakken wayo. Motsa kafarta tayi da tayi mata matukar tsami ta tuno gwagwarmayar da aka sha da Dada kafin ta amince ta bar ta, ta taho bautar kasa Kano, sai da aka tabbatar mata da idan bata bar ta taje Kanon ba toh fa kudu za'a tura ta tunda bata da aure kanon ma sai da Lamido ya shiga ya fita sannan aka samar mata. Ala dole babu yadda ta iya ta hakura. Tunda suka dauko hanya take shan kira daga wajen yayyen nata, da Hamma Hydar ya kira sai Bobbo Sadeeq shima haka Lamido kuma duk Dada ce take sakasu kiran taji ya tafiyar tasu. Yanzu ma motar su na tsayawa a tasha kiran Lamido yana shigowa,dagawa tayi tana murmushi tace "Yanzu muka iso gamu a tasha." "Toh Masha Allah, ki kira Addan ki fada mata kun iso." "In sha Allah, ina isa zan kira Dada nah, Hamma kace mata ta kwantar da hankalin ta." Murmushi yayi ya katse kiran ta duk'a kad'an ta dauki jakar hannun ta sannan ta shiga jan akwatin ta zuwa hanyar fita daga tashar. Duk da kasancewar duhun dare ya soma yi amma garin tarwai yake da hasken fitilun dake haska kan titin. Tsayawa tayi daga nesa da Titin ta ciro wayar ta kira Addan. Napep tace mata ta hau ya kawota hotoro idan sunzo sai ta kirata. Maida wayar tayi cikin handbag dinta ta tsaida napep din ta fada masa in da zai kai ta, kasancewar unguwar ba boyayyiya bace yasa bata wani sha wahala ba suka iso, ta sauka ta bashi kudin sa ta sake kira. Tana tsaye a wajen yaron Addan Muhammad yazo ya tafi da ita dan daga titin gidan su layi daya ne ba nisa   Da murna Adda maimuna ta tarbe ta, hakan yasa ta sakewa sosai dan dama ita tun asalin ta bata da duhun kai, kuma tana da masifar son mutane, sam bata san wani abu wai shi bacin rai ko kunci ba dan ita din yar lele ce a gidan su, duk abinda take so shi ake mata. Abinci taci tayi la'asar da magriba da suka risketa a hanya ta dan zauna kad'an ta jira isha sannan tayi suka cigaba da yar hirar su da Asmau ita ma yar gidan Addan tasu ce kuma zatayi kusan sa'ar ta a shekaru amma ita yanzu take 200 level a university. Kasancewar ita dukkan stage din karatun ta da wuri tayi shi shiyasa ta gama da wuri gashi har zatayi service. Sai dare chan suka kwanta dan hirar suke tamkar ba zasuyi bacci ba.   Da safe ta tashi da dan ciwon kai kad'an saboda gajiya da rashin bacci amma zuwa gabannin azahar ta ware ta sake jera kayanta sosai da zata bukata a camp dan gobe iwar haka tasan tana Perm Orientation Camp dake Kusala Dam Karaye. Wajen la'asar suka fita tare da Amina ta rakata karshen layin suka karbo dinki sannan suka biya gidan wata kawar Aminan Hadiza anan suka kai har wajen magriba suna tutorial sannn suka dawo gida. Sallar magriba tayi ta zauna waya da Dada tana kara jaddada mata kama kanta da mutunci a duk in da ta samu kanta, maganar dai itace tunda aka soma maganar zuwa camp din dan har ga Allah Dada bata so dan karatun dai yazo da haka ne. Bayan ta gama wayar ta kwanta lamo tunanin Abbinta ta ya shiga zuwar mata, kasancewar ta a Kano babbar dama ce da zata je ta ganshi ita kadai ta gaishe shi, wannan shekaran ce shekarar da ake saka ran fitowar shi, duk karshen watan duniya Hamman ta suna zuwa su ganshi su kawo mishi abubuwan da zai bukata amma sam basa zuwa da ita sai dai idan sun je su kira waya a bashi su gaisa da ita, tana son mahaifin ta duk kuwa da ba zata dorar da rayuwar su tare ba dan ba wani wayo ne da ita sosai sanda abin ya faru ba, babban abinda ya jawo musu barin gari suka koma sabuwar rayuwa me cike da wahala. Hamman ta sun sha fama matuka wajen ganin sun gina rayuwar su ita da Dada sannan suma suka gina tasu har suka zama abinda suka zama a yanzu, basu taba barin ta, tayi kukan rashin uba ba, basu taba bari ta nemi abu ta rasa ba, zasu iya yin komai akan ta ga duk wanda yace zai sakata zubar da hawaye. Ita kanta bata san wani abu wai kunci ba, rayuwa take me cike da farin ciki har zuwa tahowar ta Kano wanda take ganin yana daya daga cikin cikar burin ta. Ko ba komai zata ga Abbinta yaga yadda Raihanan sa ta girma sosai ba a waya ba. Murmushi ne ya subce mata da ta tuna kalar farin cikin da suke ciki na fitowar Abbin, dan shine kadai damuwar su a yanzu, akwai abubuwa masu yawan gaske game da fitowar tasa, wanda ake ganin zai iya kawo karshen wasu mutane masu yawan gaske, sai dai zasu barshi ya sake jefa rayuwar sa a irin hatsarin da ya saka kansa a baya? Ko zai sake tsayawa gaskiya kamar wanchan lokacin? Manyan kasar basa san gaskiya ba kuma sa barin duk wani wanda zai fada musu ita. Cikin tunanin bacci ya dauke ta, dan bata farka ba sai kusan sha biyun dare, ko abincin dare bata ci ba haka ta tashi tayi sallar isha ta sake komawa dan baccin ne akanta sosai.     Tunda suka tashi da asubah ta hau shiryawa, a sanyaye take komai sai take jin kamar ta fasa wani irin feeling, she's nervous dan bata kuma san rayuwar da zatayi ba, haka ta daure ta karasa shiryawa dan ma Amina zata karata tare da Muhammad din, mota aka samo musu dama tun jiya drop da zata kaisu Lamido ne yayi duk wannan suna karyawa driver yazo suka fita, suka dauki hanyar Karaye suna dan taba hira har suka isa, sai da suka jirata ta shiga ciki bayan an gama duk arrangements din da akeyi a wajen gate sannan suka juyo suka barta da kewa. Rayuwar ta a sati ukun nan ta koyi darasin rayuwa sosai, sannan ta hadu da mutane kala-kala mabanbanta, kasancewar tazo da enough kudi yasa rayuwar bata yi mata wahala sosai ba dan har wasu suna mata kallon yar masu kudi saboda yanayin ta. Cikin nasara da kamewa ta gama sati ukun nan. Hamma Haydar ne yazo mata surprisingly tare da wannan driver motar da Muhammad wannan karon ba Amina dan tana da lecture, farin cikin ta ya gaza boyewa dan bata zaci zasu zo ba. Tare suka karasa komai suka dawo gidan Adda Maimuna daga nan ya koma dan dama zuwan nata ne hade da ganin Abbi dan Lamido baya nan sun yi wata tafiya a wajen aikin su, shi kuma Haydar ya zauna da Dada. Taso ta bishi amma dole ta hakura dan kwana uku aka basu zuwa ranar da zasu karbi posting letter din su.        Ranar da zata karba da kanta ta shirya a cikin NYSC khaki dinta ta fito ta samu napep tace ya kaita Gwarzo Road, tana zuwa bata wani bata lokaci sosai ba ta karbi posting letter din ta hade da ATM card dinta sannan ta fito. Wani me napep din ta sake samu ta tsayar tace ya kaita KURMAWA PRISON, sai da ya dan kalle ta sannan yace ta shigo, ta shiga ta zauna cike da zumudin ganin Abbin ta, ta bud'e posting letter din ta, taga an tura ta wata makaranta a Kumbutso local government, yanayin address din ya tabbatar mata kauye ne sosai, ji tayi duk babu dadi haka ta maida ta saka a jaka ta cigaba da kallon titi har suka iso, daga nesa da wajen yayi parking sannan ya nuna mata wajen da hannu, sauka tayi ta bashi kudin sa idanun ta akan wajen sun ciciko da kwalla. Kokarin tsallaka titin take kasancewar babu ababen hawa sosai, kai tsaye ta shiga tsallakawa bayan ta dan duba kad'an. Kamar daga sama taji an ture ta da abu me karfi, kafin ta gano menene ta kai k'asa baki daya jakarta ta watse ita kuma tayi nata wajen. Parking yayi a gefe ta balle murfin motar da sauri ta fito. "Raihana.." Ta riko ta da sauri tana kokarin daga ta daga faduwa da tayi, gefen hannun ta har ya soma jini saboda gurjewar da tayi.     "Subhanallah, Me ya faru Hajiya?" Wani mutum da yazo wucewa ya fada "Wallahi sam driver be lura da ita ba, shine ya dan taba ta, bari akwai clinic nan kusa tashi mu kaiki su duba ki." "Allah ya takaita ma, Allah ya kiyaye gaba." Yace yana wucewa Kanta da ya dan yi dum ta rik'e kafin ta mike da k'yar dan har guiwar ta sai da ta dirje, ta taimaka mata ta saka ta cikin motar shi kuma driver ya kwashe kayan ya maida mata cikin jakar sannan suka bar wajen    Wani hadadden clinic ta kai ta, aka duba ta aka gyara mata hannun da guiwarta, aka bata pain killer sannan suka fito. "Sannu kinji? Ina ne gidan ku mu ajiye ki?" "Hotoro." "Ok, amma in da muka ganki din inane? Ko chan zamu maida ke?" "Eh babana zan kaiwa ziyara a prison." Dan kallon ta tayi kad'an kafin tace "Ai yau ba lokacin ziyara bane ba, kuma kinga yanzu ma be kamata ya ganki da ciwo ba, ki bari idan kika samu sauki sai kije ki ganshi kinji? Ni zan shige miki gaba ki ganshi." "Ok tam, dama yau akayi posting dina ne shine zan je na ganshi na nuna masa." "Bautar k'asa kike yi?" "Eh..." "Ina aka tura ki?" "Kauyan Kumbutso." "Wai... Gaskiya yayi nisa, kina so ki chanja?" "Eh..." Ta gid'a kanta "Shikenan zan baki address dina, Monday kizo gida ki karbi sabuwar posting letter kinji?" Fuskar ta dauke da farin ciki tace "Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi." "Ba komai, muje na ajiye ki a gida kar mamanki taji shiru." "Ok tam." Tace cikin jin dadi, ba dan abinda ya faru din ba me dadi bane ba, da sai tace ita gwara ma hakan da ta faru dan da bata san yadda zatayi ta san matar ba, matar da kana ganin ta kaga babbar mace me aji da kudi, gata sam bata da girman kai idan wasu ne tafiyar su zasuyi su barta.   Har kofar gida aka kaita sannan ta dauko kudi me yawa ta tura mata a jakar ta, tayi godiya sosai sannan ta fito rike da complimentary card din matar dake dauke da number wayar ta wadda zata kirata idan taje gidan. Har ta soma takawa zuwa gate din gidan suna tsaye basu tafi ba, wani tunani ne ya fado mata, ta juyo ta dawo wajen motar sannan ta dan duka a hankali tace "Dan Allah kin san sunana dama?" "Ni a ah, ya akayi?" "Sanda na fadi naga kin fadi sunana, sannan a clinic din ma..." "Oh wannan? I'd card dinki ne da ya fado anan naga sunan ki." "Oh okh, nagode sosai." "Karki damu kinji? If you need anything just call me, kinga dama bani da 'ya mace, shikenan na samu 'ya." Murmushi tayi wadda yake bayyanar da zahirin kamar ta da mahaifiyar ta "Sunana Hajiya Zeenat, shiga gida zamu tafi, karki manta ki kirana Monday." "In sha Allah." Ta sake godiya kafin ta juya ta shige, murmushi Hajiya Zeenat tayi ta girgiza kanta tace; _"What a small world! bayan duk tsawon shekarun nan, yau ga yarka a tafin hannu na Nasir, let see how it will end."_ "Muje." Tace tana relaxing sosai, a cikin zuciyar ta, ta shiga sak'a yadda abubuwan zasu kasance _"Sai nayi wasa da rayuwar ka Aryan, sai na nuna maka na fika sanin rayuwa. Muje zuwa."_. Ta yi dariya tana tuna zamanin baya, tun daga lokacin har zuwa yanxu dai itace a sama, zatayi komai, domin ganin ta cigaba da rike mutuncin ta. *_ZAFAFA BIYAR 2023_*=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý _*Sabuwar shekara sabon salo sabon taku,*_ _*Makaranta littafan hausa kuma masoya marubutan zafafa kuzo ga sabuwar tafiya zazzafa tazo karku bari ayi babuku *_ _*Zafafan alkaluman haziqan maruban zafafa biyar kowa yasan na daban ne,wannan karon ma sunzo da sababbin salo me kama zuciya.*_ _*ZAFAFAN MARUBUTAN SUNZO DA SABABBIN LITATTAFANSU NA 2023 Kamar haka,*_ 1 _*IDON NERA*_ Mamuhgee 2 _*DAUDAR GORA*_ ciki ka shata Billyn Abdul 3 _*RUMBUN QAYA*_ Hafsat Rano 4 _*KI KULANI*_ mallakin zuciyata Hafsat Miss Xoxo 5 _*A RUBUCE TAKE*_ qaddarata Safiya Huguma _DUKA GUDA BIYAR DIN ZAKA SAMESU A FARASHIN 1200_ Guda 5 1200 Guda 4 1000 Guda 3 800 Guda 2 600 Guda 1 400 _*zaku saka kudin a wannan account din=ØGÜ*_ _*0022419171 Access Bank Maryam sani*_ Saiku tura shedar ta=ØGÜ _*09033181070*_ Idan kuma katin Waya ne zaku tura katin MTN ta wannan layin=ØGÜ 09166221261 TEAM ZAFAFA BIYAR=Ø%Ý=Ø%Ý MUNGODE=ØOÞ=ØOÞd'þ [21/02, 12:51] Mum Sayyeed&Noord'þ: *RUMBUN QAYA*              Free Page 2 ©® *_Hafsat Rano_* ZAFAFA 2023=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý ***A tsaye yake ya rike karfen jikin stairs din yana amsa waya, wayar da yake me matukar muhimmaci ce daga yadda yake magana. Idanun sa ya daga sanda yaji an bud'e kofa. Adam ne, dauke kallon sa yayi zuwa wani shashen na daban yana kokarin katse wayar "Zan kiraka back." Yace ya katse yana juyawa da nufin hayewa saman. "Aryan..." Ya kira sunan sa yana tahowa, tsayawa yayi da hawan ya juyo yana masa kallon neman karin bayani "Ashe kana ciki baka fita ba." "Ya akayi?" Yace a gajarce cikin yanayin rashin son maganar tasu tayi tsayi "Nothing much, kawai dai maganar Daddy zan tuna maka, dan naga kamar ka manta ne ko kuma kana kokarin shashantar da maganar, ina jiran ka ajiye aikin ka bani wajen, dan da alama babu abinda zaka iya da irin wannan zuciyar taka." Kallon rainin wayo yayi masa, yaja tsaki kawai ya juya da sassarfa ya haye saman, murmushi Adam yayi yana janye hannun sa ya hade su waje daya. "Karamin dan air." Sai ya juya yana bouncing shima ya bar wajen.    A harabar gidan suka hadu, daidai lokacin ta fito daga motar fuskar ta dauke da annuri, tsayawa yayi ta karaso ya karbi handbag dinta yana murmushi "Mom sai yanzu? Har ina shirin fita." "Bari kawai, yau nayi babban kamu, duk da dama da wannan plan din na fita, and it was a success gaskiya, muje ciki." "Sai Mommy ta, mu je toh." Tayi gaba ya bita a baya yana mata hirar maganar da yayi ma Aryan yanzu, da kin amsa ma san da yayi "For now ka bar wannan maganar, mu bi komai a sannu dan na samo bakin zaren." "Wai kina nufin na bar masa matsayin MD din?" "Kwarai, ka cigaba da bin sa a hakan, saura kiris ya rage." "Oh shit! Mom yaron nan fa yana kokarin kai ni karshe ne, ni dai ayi duk yadda za'a yi na gaji da bin sa kamar wani uba na." "Kai dai ka zuba ido, ka kyale min komai." "Shikenan Mom, I trust you ai." "Yawwa My boy, yanzu kaje in da zaka idan ka dawo sai muyi maganar, ka biya office din Daddyn naku kaga ko yana da bukatar wani abu." "Shikenan, sai na dawo." Ya ajiye mata jakar a gefen bedside ya fita. Zama tayi ta ciro wayar ta, ta shiga number Hajiya Maryam wadda itace Co-ordinator ta NYSC Kano, maganar minti uku sukayi ta fada mata bukatar ta, take tace ta tura mata NYSC number din yarinyar cikin kankanin lokaci akayi komai, ta sauya mata zuwa company su. Tashi tayi bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta sauya shigar ta zuwa wata shigar ta alfarma sannan ta fito babban falon tana kwala kiran Harira.     ***Wanka tayi bayan sun gama jimamin abinda ya faru da ita da su Adda Maimuna da Amina, magungunan ta, tasha sannan ta haye gado ta kwanta, cikin kankanin lokaci kuwa tayi bacci har da mafarkin matar da suka hadu wadda tayi masifar shiga ranta farat daya, ta burge ta matuka yadda ta jata a jiki cike da kulawa. Wajen la'asar ta tashi shima sai da Amina ta tashe ta dan yin sallah. Kasala ce ta rufe ta bayan ta tashi, tayi sallar da k'yar ta dan ci abinci sai kuma tunanin gida ya dawo mata, tayi kewar su dukka sosai, kamar ta fasa bautar kasar ta koma wajen Dadan ta tayi zaman ta haka take ji, dan ma gidan Adda Maimunan akwai dadin zama musamman aka zauna bayan magriba ayi ta hira wani lokacin sai akai sha biyu ana hira ana ciye -ciye, shiyasa take dan jin dama-dama. Dada ta kira bayan magriba sai dai bata fada mata bige ta da motar tayi ba dan tada hankalin ta zatayi tace dole dole sai ta taho shiyasa sai tayi kum suka gama wayar cike da kewar juna.    Kwana biyu da haduwar su da Hajiya Zeenat sai ga kiranta, tayi mamakin yadda ta samu number ta dan bata karba ba ranar amma sai bata kawo komai ba, ta duba ta sannan ta sake jaddada mata ta shigo goben ta karbi posting letter din tata kasancewar gobe sukayi dama Monday. Godiya ta sake yi mata cike da jin dadi sukayi sallama.  Washegari ta shirya cikin doguwar bakar abaya ta yafa medium veil tayi kyau sosai haka itama Amina ta shirya dan ita zata rakata suka fito titi suka samu napep suka masa kwatance kamar yadda yake a rubuce,kai tsaye yace "Ko dai gidan Alhaji Mukaddas?" Kallon juna sukayi ita da Amina kafin tace "Eh sunan dai matar da zamu gani Hajiya Zeenatu Mukaddas, gashi a jikin katin." "Ai sanannan gida ne wannan." "Alhaji Mukaddas wai me kudin nan da ake fadan sa?" Amina tace bayan sun shiga sun zauna "Eh shi fa." Me napep yace. Jinjina kai sukayi dukka suka ja bakin su sukayi shiru. Har gaban tangamemen gate din gidan ya kai su, kansa tsaye kuwa dan ba wannan ne karon farko da ya taba zuwa ba, duk azumi ana rabon kayan abinci kuma ya sha samu shi ma, dan ba wani nisa ne dasu sosai ba. Sakowa sukayi dukkan su idonsu akan gidan da ya cika da kyau da tsari, girman gate din ma kadai abun kallo ne. "Kin tabbata nan ne Raihana?" "Eh bari na kirata, amma dai ina kyautata zaton nan ne." "Toh kirata muji." Tace tana cigaba da kallon gidan. Kiran wayar tayi no answer, ta sake gwadawa a karo na biyu kafin ta daga tace mata suna waje, ok tace mata sannan ta katse wayar ta kira gate din tace a shigo da ita, suna tsaye aka bud'e karamar kofar shiga gidan, wani buzu ya leko kansa a rufe yace su shigo, a sanyaye suka shiga duk jikin su ya mutu saboda mamaki, har balcony din ya rakasu sannan yace su shiga, suna dosar kofar ta bud'e da kanta suka shiga da sallama wani masifaffan sanyi me hade da wani irin feshin raba ya bige su, wani irin tsam sukayi suna wurgurga ido a tsakiyar tamfatsetsen falon dake cike da manyan kujeru na alfarma "Raihana.." ta sake kiran sunan ta, tana sakkowa daga stairs din dake tsakiyar falon, murmushi ne a fuskar ta har ta karasa saukowa. Da sauri suka gaishe ta, ta amsa musu a sake tana nuna musu wajen zama. "Ya jikin naki?" Ta tambaye ta bayan sun gaisa tana cigaba da kallon su fuskar ta a sake sosai "Na samu sauki." "Alhamdulillah, sai zuwa ganin Baba kenan." Dariya suka sa dukka ta jawo wata drawer a jikin centre table din ta ciro envelop ta mika mata "Ga posting letter din ki as I promised!" Dadi ne ya kamata ta karba tana godiya sosai, ta bud'e sannan ta mikawa Amina ta karba itama ta gani, a sannan ne aka kawo musu snacks da juice da ruwa tace su ci tana zuwa. Zagewa sukayi suka ci Amina har ta daukar wani buns ta saka a tissue ta tura a jaka suka saka dariya "Mom!" Ya turo kofar yana kiran ta. Riga da wando ne a jikin sa, sai takalmi sau ciki, kansa rufe da pcap ya jona airpod a kunnen sa fari. Tsayawa yayi chak yana kallon su, kafin ya karaso ciki sosai still idanun sa na kansu yazo ya zauna a daya daga cikin kujerun falon. "Ina wuni?" Suka hada baki wajen gaishe shi "Lafiya Lou, wajen Mom kuka zo." "Eh suka amsa." "Adam ka dawo?" Tace tana fitowa daga hanyar dakin ta na kasa "Eh shigowa ta kenan, naga kin yi baki beauties dasu." "Raihana ce da sister din ta, ni ban ma tambayi sunan ki ba Yan mata." "Amina." "Yawwa Aminatu ce ashe tsohuwa." "Raihana... What a name! itace kuka bige ranar da driver?" "Eh itace." "Wow!" Yace yana taba gemun sa yana wani irin kallo k'asa k'asa, yana ayyana wani abu a ransa. *RUMBUN QAYA=Ø%Ý *DAUDAR GORA*=Ø%Ý *IDON NERA*=Ø%Ý *A RUBUCE TAKE*=Ø%Ý *KI KULANI*=Ø%Ý *_uhmmmm_*=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ=Ø Þ *Nasan zakuce ya da murmushi haka?* *Wanda bai shigo ba bazai gane ba* *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*:&þ:&þ *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU* *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?* *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?* Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200 *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý=Ø%Ý 0022419171 Maryam sani Access bank *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN* 09166221261 <ØóÝ<ØêÝ<ØóÝ<ØêÝ<ØóÝ<ØêÝ<ØóÝ<ØêÝ<ØóÝ<ØêÝ<ØóÝ<ØêÝ<ØóÝ<ØêÝ *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL

Chapter 1 of 4