sai ga Dada da Al-hassan sun shigo gidan Baaba Hajo shajaran majaran, hankali tashe Dada na sharar kwalla, Al-hassan kuwa idanu jajur.
Lokacin ina madafi ina izawa Baaba Hajo wuta, jin muryar Dada yasa na dago a razane, Baaba Hajo ma da shiganta d'aki kenan ta fito da sauri har tana tuntu6e da dakalin kofar dakin.
Ganin Dada ta nufo in da nake kai tsaye yasa jikina ya fara 6ari na soma ja da baya, sai dai ga mamakina, tana isowa gabana cikin zubar hawaye take cewa "Balkisu ki dubi Allah da ma'aiki ki yafe mana."
Kaina ne ya kulle, na zaro ido a tsorace ina tunanin ko dai Dada ta zauce ne da take gayamin wannan maganar, ban dawo cikin nutsuwata ba naga tana neman zube gwiwowinta biyu a kasa a gabana, da sauri na dakatar da ita ta hanyar saka hannayena biyu na tarota ina girgiza kai tare da cewa "Kar ki duka a gabana Dada, wallahi na yafe miki har abada saboda Allah saboda darajar Yaya Hussain da soyayyarsa."
Cikin kuka ta shiga cewa "Balkisu zamu rasa Usaini ya na can kwance rai a hannun Allah, tun da kika juya kika fice daga gidan ba tare da waiwayarsa ba ya yanke jiki ya fadi, muka yayyafa mai ruwa, tun muna daukar lamarin da wasa, ashe ya fi gaban nan in takaice miki yanzu haka yana kwance a babban asibiti zuciyarsa ta kumbura,lokaci kawai yake jira, da taimakon iskar oxygen ya ke numfashi ko daga yatsarsa baya iyawa bare ya bude baki ya yi magana, kuma Dr ya tabbatar mana kece kadai wacce za ki iya taimakawa ya samu lafiya, don Allah Balkisu ki dubi, Allah ki taimakeni kar ki bari mu rasa Usaini kar ki bari na rasa dana mai tsananin biyayya a gareni zan yi harasa."
Irin tashin hankalin da na shiga da jin kalaman Dada bazai misaltu ba, hajijiyane ya shiga kwasata jiri na nema kayar da ni , tuni na naimi miyau a bakina na rasa, a haka na yi karfin hali kama tafiya na durfafi hanyar kofar fita daga gidan cikin tashin hankali da gushewar tunani.
Baaba Hajo ce ta karaso jiki a sanyaye ta rike ni ganin yadda jikina ya dauki na mazari, cikin rarrashi take cewa "Ki nutsu Balkisu ina za ki je haka, ki zo ki zauna kar jiri ya kayar da ke." Cikin kuka na ce "Baaba bazan iya zama ba, Yaya Hussain na cikin irin wannan halin asibitin zan tafi."
Dada cikin sharar kwalla ta ce "Yawwa Balkisu, na sani ke yar albarka ce baza ki ta6a juyawa Usaini ba ya ba, ga mota nan kizo muje Hasan ya kai mu asibitin.
Hijabi Baaba Hajo ta dauko min a daki ta ce " kuje Balkisu nima idan na karkare sanwar zan biyo ku."
Ko da muka isa ban samu ganin shi ba, domin inda yake ba a shiga sai da kwakkwaran dalili, ga shi likitan da yace in zo ya ta shi wani ya canji hannunshi.
Ranar asibitin na kwana, don yin duniya Baaba Hajo ta yi in zo mu tafi na ki, dole haka ta wuce ta barni, ban iya rintsawa kwana na yi ina sharar hawaye tare da rokawa Yaya Hussain lafiya.
In takaice muku sai da na yi kwana goma sha biyu cif a asibitin nan ba tare da na koma gida ba, saboda a yadda naga Yaya ban za ci zan kifta ido in bude in tarar da shi yana numfashi ba, sai dai cikin hukuncin ubangiji da taimakonsa da nawa dana Dr Yaya Hussain ya fara samun Lafiya har ana iya mikar da shi zaune, a ranar kuwa da ya fara magana, maganar data fara shiga tsakanina da shi ta farko, shine" Na mayar dake dakinki matata Balkis." A gaban Dada da sauran yan uwanshi ya yi maganar, sosai na tsorata, ganin yanayin da na shiga yasa ya kawo hannuna ya rike yana murzawa a hankali, fuskarsa dauke da murmushin fari n ciki ya sake cewa, "Kar ki damu a wannan karon da sahalewar Dada da kuma yan uwa na aureki." Jin haka yasa na dago kai na kallesu ba ki daya ganin yadda fuskokinsu ke murtuke kamar an aiki musu da sakon mutuwa musamman Dada da Tanimu ya tabbatar min da akwai lauje cikin nadi.......
[1/18, 12:39 PM] +234 803 069 9057: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 49*
Duk da haka na yi farin cikin jin cewa ya mai da ni dakina, domin Allah ya sani ina son Yaya Hussain, son da na ke jin zan iya rayuwa da shi cikin ko wanne irin yanayi matsawar da igiyar aurensa a kaina.
Kwana biyu ya k'ara a asibitin aka sallame shi, ya ji sauki sosai sai rashin kwarin jiki da sauran abinda ba za a rasa ba, wannan kuma dama sai a hankali.
Da fari haya ya ce zai kama mu zauna, kafin ya karasa ginin gidansa, sai dai fir Dada ta ki amincewa, wai bata so ya yi nisa da ita, ya zauna a cikin yan uwanshi tunda ba rasa dakuna aka yi a gidan ba, shi karan kan shi bai so ba, bare kuma ni, amma babu yadda muka iya haka muka yi hakuri ya gyara min d'akin da ke kusa da na matar Al-Hassan, ciki da falo ne, masu matsakaicin girma, ya siya min gado da katifa da sauran tarkacen kayan aiki masu muhaimmanci wadanda dole zan bukace su, na tare a d'akina bisa rakiyar Baaba Hajo, wacce ta zame mini dangi d'aya tamkar dubu, Allah ya saka mata da Alkhairi ya jaddada Rahma a gare ta.
Fatima da Aliyu har suna hada baki wajen cewa "Ta rasu ne?"
Girgiza kai kawai Ummi ta yi ta saki wani murmushi mai ciwo ta ci gaba da cewa;
Na zaci cewa tunda wannan karon da sahalewar Dada da yan uwan shi ya aureni, bazan sake fuskantar wata damuwa mai yawa ba, ganin cewa Dada har k'asa ta duka don neman yafiyata, ashe ban sani ba talala ta yi min mai kamar sake.
Ko sati guda ban rufa da fara amarci ba, na fahimci cewa Dada kwantan bauna ta yi mini, domin na zame mata kadangaren bakin tulu, ashe yafiyar data nema a gare ni ba har zuciya ba ne yaudara ne don kar ta rasa d'anta, ashe babu abin da ya rage a zuciyarta na daga kiyayyar da take min sai ma nunkuwa da ya yi.
Bazan iya ba ku labarin irin rayuwar da na yi a gidan Maman kura a matsayin matar Hussain ba, domin ba shi da dadin ji, zuciyoyin ku baza su iya daukar wannan hargitsin ba.
Rayuwa ce na shekara biyu rak! Mai cike da kunci da damuwa da tarin bakin ciki, tamkar mujiya a cikin taron mutane haka na yi rayuwa a gidan har ta kai ta kawo ko kofar d'akina bana iya lekawa saboda bala'i, ba daga uwar miji ba, ba daga yan uwan shi ba, kai hatta da facalolina ban samu rangwame daga garesu ba, uwa uba kuma Yaya Tanimu.
Sam babu imani da tsoran Allah ko miskala zarratin a zuciyar Tanimu, da auren kaninsa uwa d'aya uba d'aya a kaina amma hakan baisa ya daina bibiyata da neman keta haddina rashin samun galaba a kaina yasa ya kara tsanata , ya zame min tarnaki da tashin hankali, ya kara hura wutar kiyayya tsakanina da duk wanda ke rauyuwa a cikin gidan nan, duniya ta kara yi mini zafi, babu in da na ke rabewa na sanyi sai wajen mijina.
Sai dai wani abin mamaki da al'ajabi, aurena da Hussain ya zame masa tamkar wani taki, nan da nan arzikinsa ya fara hau hawa kamar farashi, kasuwancinsa ya bunkasa sosai kamar dama jira ake mu yi aure, ya zama busy man sosai ba shi da lokacin kansa sosai, baya zama yau yana Cotonou gobe yana Lagos saro kaya sabanin da, da iya kano kawai ya ke zuwa sari.
Ban ta6a sanin ana samun hassada a tsakanin yan uwa ba, sai akan Al-hussain da yan uwansa, sai dai na yi wa hakan fassara da irin uwar da suke da shi wacce ta kasance tukunya mai bori a tsakanin su.
Sam Yaya Tanimu ya kasa boye hasaadarsa akan dan uwan nashi a zuciyarsa, karara ya ke nuna nunawa agaban kowa yana adawa da samun nashi, duk da irin sha tara na arziki da yake musu kuwa.
Cikin shekara daya da watanni da aurenmu ya mallaki gidaje na alfarma har guda biyu, shagunan shi kuwa dankara-dankara uku a cikin kasuwar kure, ya zuba ma'aikata yana biyansu.
A lokacin ya so ya ta shi ya bar family hause ganin ya mallaki gidajen kan shi, still Dada ta hana ta ce sai dai ya zuba yan haya, ya kada ya raya ta ki amincewa, da ya dage sai ta fashe da kuka tana cewa wai don ya ga ya yi kudi shine ya ke son ya gujeta, dole ya sake hakura a karo na biyu, sai kawai ya rushe gidan ya mai da shi na zamani plat plat, sak yadda ya gyara mana sashe ya zuba mana komai na zamani, haka ya yi wa dukanin yan uwan shi, babu bambanci sai na launuka, yawancin dawainiyar gidan ya dauke musu, kama daga kudin wuta da ruwa, kudin makarantar yayansu da sauransu, ta ko ina bai rage su da komai ba daidai gwargwadon hali yana musu.
Sai dai duk da haka bai tsira ba, kullum kiran shi suke yi mara mutunci baya kyautata musu, ya yi kaza ya yi kaza, haka Tanimu zai saka Dada a dinga fada mata karya da gaskiya yana sukar kanin nashi sharri kala-kala ita kuma baza ta yi bincike ba zata saka shi a gaba tana mai fada wanda rabin shi duk zagi ne da debe albarka.
Duk da haka na shi nafila ne akan nawa domin gani suke yi ba ce nake hanawa ya yi musu abin da suke so wanda iya hange na banga abin da ya ragesu da shi na, wanda har suke ganin na hana ya yi musu.
Wata rana ya dawo daga tafiya kamar yadda ya saba, cike da kewa da soyayya na tare shi, ya shigo daki cikin wani irin yanayi, jikinsa a sanyaye sannan ranshi a bace.
A rude na shiga tambayarsa menene, saboda bai taba dawo min cikin irin wannan yanayin ba.
Bai amsani ba sai da ya nemi waje ya zauna ya umarceni da na bashi ruwan sha.
Bayan ya sha ruwan ya furzar da wani huci mai zafi, a hankali kamar mai ciwon ba ki ya ce "Sa6ani muka samu da Yaya Tanimu, har sa'insa ya shiga tsakaninmu Balkisu."
A tsorace na ce "Subhanallahi! Akan me?"
Ya dago ya kalleni, kamar zai yi magana, sai kuma ya yi shiru ya dafe kai, kusan minti ashirin muna a haka, sai kuma naga ya mike da sauri ya shiga d'aki, ina nan zaune kamar ruwa ya ci ni ya fito ya zauna kusa da ni ya koma hannuna ya saka mini wata takarda, ya ce "Balkisu wannan takardar wani karamin gida ne dana siya da sunan ki, babu wanda ya san da shi a cikin yan uwana, ga shi nan a hannunki na mallaka miki shi halak malak.
Na sake baki ina kallon shi, ya ci gaba da cewa " Gobe idan Allah ya kai mu zan koma Lagos, idan Allah yasa na dawo lafiya zan kai ki ki ga gidan idan kuma ban dawo ba, makullin gidan shine makullin dana ba ki ajiya kwanaki, gidan yana a unguwar Abayi."
Tuni hawaye suka wanke min fuska, na bude baki da niyyar yin magana ya dakatar da ni, " Shiiii! Bana son jin komai, kuma bana son kukan nan." Ya fada yana mai share mini hawaye. Sai kawai na fada jikin shi na rungume shi, ya zagayeni da hannensa shima, yana sauke numfashi ina iya jiyo yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri sauri. Wani irin yanayi muka tsinci kan mu a wannan lokacin mara misaltuwa, tsoro da fargaban wani abu wanda ba mu san ko menene ba ya cika zukatanmu.
Mun dade a haka kafin ya yi karfin halin raba ni da jikinsa.
Daren ranar ba mu yi barci ba, wata irin soyayya ya gwadamin wanda tun da muka yi aure bai ta6a gwadamin irin shi ba, bayan mun kimtsa, maimakon mu kwanta saboda dare ya tsala, sai ya janyo hannuna muka zauna bakin gado wai hira zai min, duk irin yadda barci ke idona haka na ba shi hadin kai na biye masa, yana ta bani labarai Kala kala, wasu na fahimta wasu kuma sai dai kawai na yi murmushi ba dan na gane mai ya ke nufi ba, na so kwarai ya ba ni labarin sa'insar da ya shiga tsakanin shi da Yaya Tanimu amma sam bai kuma tada zancen ba, kamar na tambaye shi sai wata zuciyar ta kwabeni.
Mummunar mafarkin da na yi ya tilasta min farkawa daga gajeren barcin daya kwashe ni ba tare da sani na ba, na ganni kwance a gado na yi matashi da cinyar shi idanunsa kurr! A kaina, sai dai bani din yake kallon ba, ya yi nisa ne cikin tunani, firgigit yayi lokacin da na motsa, ya riko hannuna da sauri yana sakin ajiyar zuciya. Cike da damuwa na ce "Yaya baka kwanta ba." Ya yi mini murmushi ya ce, "Balkisu kamar kar na koma tafiyar nan gobe, amma kuma ji na ke kamar ana jana zuwa garin ko kuma in ce kiranye." Na sauke ajiyar zuciya na ce "ka yi ta addu'a yaya nima zan taya ka, alkhairin da ke cikin tafiyar Allah ya tabbatar sharri da hatsarin da ke ciki Allah ya kare ka."
Karfe shidda na safe ya gama gimtsawa tsab cikin fararen kayan dana zabar masa masu kyau, har bakin kofar falo na rako shi, ina yi masa Addu'a, ya karbi jakarsa da ke hannuna ya rungume ni a jikinsa tsam,
🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*PAGE 50*
Ƙarfe shida na safe ya gama kintsawa tsab cikin fararen manyan kayan da na zabar masa, ya ɗaura tsadaddiyar baƙar hula, ya yi mini kyau sosai, fuskarsa ta yi fayau sai wani annuri ta ke fitarwa.
Har bakin ƙofar falo na rako shi, ina yi masa Addu'a, ya karɓi jakarsa da ke hannuna ya rungume ni a ƙirjinsa, shiru na yi ina sauraren bugun zuciyarsa yayinda nawa bugun zuciyar ke ƙara hauhawa a cikin kowanne daƙika.
Mun daɗe a haka kafin na yi ƙarfin halin janye jikina, muka haɗa ido ya sakar mini tattausar murmushinsa mai narkar mini da zuciya a ko da yaushe, ji na yi kuka na shirin kuɓuce mini, na yi ta maza na dake, tare da sakin murmushin da iyakarsa laɓɓana, don na san idan na kuskura na yi kuka a gabansa to zai iya fasa tafiyar, bayan kuma ya sanar mini da mahimmancin tafiyar a garesa, amma har ga Allah hankalina bai kwanta da tafiyar ba.
Jin saukar hannayensa a marana ya saka ni dawowa gayyacina, ya ɗage mini gira tare da cewa "Har ya yi kwari, watansa nawa yanzu?," kunya na ji ya lulluɓe ni, ya yi dariya mai sauti cike da nishaɗi ya ce "Hmmm! Kin ɓoye mini ko? kin za ci bazan gane ba ko? To ki sani komai kankantar canji a tattare da ke ina ganewa, na yi farin ciki sosai, na so na zuba miki ido na ga iya gudun ruwan ki, sai dai na kasa, sati ɗaya zan yi da, amma saboda shi zan yi ƙoƙari in dawo jibi mu gaisa da kyau." Da langwaɓe kai tare da cewa "Ni fa ba ni da komai Yaya."
Ringing ɗin wayarsa ya katse shi daga amsar da ya ke shirin ba ni, ya ɗaga, ya ce "Ok ga ni nan fitowa." Bayan ya ajiye wayar ya ce "Zan ta fi Balkisu, ki kula mini da yarana da kan ki da unborn ɗi na." Ya ƙarasa maganar tare da rage tsawo ya sumbaci marata.
Take kwallar da na ke ta ƙoƙarin riƙewa ya cika kwaurin idanuna, ganin haka ya sa ya fice da sauri ya na cewa "Take care luv , za mu yi waya kin ji."
Sulalewa na yi na zauna a wajen, gabana na wani irin dokawa, from no where na ji kuka ya suɓuce min, mafarkina na jiya na sa ke dawo min dalla dalla, na daga hannu na shiga kwararo ma shi addu'ar kariya da fatan isa lafiya.
Na daÉ—e a wajen ina kuka babu mai rarrashi, kafin na yi karfin halin mikewa na shiga ciki domin shirya Al-ameen ya tafi school ganin ya kusa makara.
Wunin ranar haka na yi shi a wahale, musamman da na yi ta traying lambar Yaya Hussain switch off, ga faɗuwar gaban da tsinkewar zuciyar da ke ta hauhawa a gareni, kafin magrib tuni na fara ficewa daga hayyacina, gani na ke kawai mafarkina ne ya tabbata, ba ni da wanda zan gayawa damuwata ya fahimci halin da na ke ciki a lokacin, Al- ameen da Fatima na saka a gaba ina sambatu kamar taɓaɓɓiya, har zuwa lokacin da dare ya raba.
Ko da wasa barci bai yi gigin kawo mini ziyara ba a wannan daren, haka na zauna ina kuka ina sake traying lambar wayarsa amma maganar É—aya ce a kashe, ganin wannan bazai fishsheni ba, yasa na mike na dauro alwala, na shiga jero nafilfiliq a'a, Ni kaina bazan ce ga iya adadin raka'o'in da na yi ba saboda É—imuwa, sai da na ji kafata na rawa na zauna na ci gaba da addu'a, ban san yadda aka yi barci ya kwashe ni ba, sai dai mummunar mafarkin da na sake yi ya saka Ni farkawa a hargitse, na fashe da kuka tare da lalubar wayata hannu na rawa na sake kiran lambar Yaya amma bata canza zane ba.
Kasa jurewa na yi, ban san yadda a ka yi na tsinci kafafuna a tsakar gida ba, duk da duhun dare ga rashin wuta hakan baisa na ji ko É—ar ba, gidan Baaba Hajo zuciyata ke ingiza ni, in je gareta in faÉ—a mata damuwata ko zan samu sassauci.
Haka na yi ta tafiya ina jin kafafuna kamar ba nawa ba, ko ganin gabana ba na yi, daga ni sai dogon hijabin da na yi sallah akan rigar barcin jikina kafata ko takalma babu, ina isowa zaure na dakata saboda hango mutum da na yi, ya juya baya yana magana a waya ƙasa ƙasa, kafin na gama tantance wanene kunnuwana, suka jiyo mini abin da ya sakani zaman dirshan a wajen, "Ƙusa ka tabbatar Hussain ya mutu?" Ya yi jim kafin ya saki wata irin shaiɗniyar dariya ya ci gaba da cewa "Wondeful wato harda direba, kai dole ma in ƙara maka 500'000, ok ka tsumayeni nan da kwana biyar."
Tashin hankali yasa na ƙasa kwakkwaran motsi a wajen, tuni na dena fahimtar mai ya ke cewa, ina kallonsa ya juya ya yi cikin gidan yana sakin wani irin shu'umar murmushi.
Tsananin tashin hankalin da nake ciki ya sa na rasa a sama na ke ko a kasa, cikin ƙudirar Allah na tsinci harshena da fara maimaita kalmar "Inna lillahi wa Inna alaihi raji'un." Ban san yadda a ka yi na iso dakina ba amma ina kyautata zaton da rarrafene.
Na zuɓe a bakin kofa bayan na rufe ƙofar, a wahalce na ke jan numfashi gefe guda kuma ga wani irin tamkewa da marata ta yi, ban san awa na yi a haka ba, kafin a hankali na fara jiyo kiran Assalatu daga masallacin kusa da gidan, gama kiran sallan ke da wuya, na samo jiyo kururuwar Daada da sauran mutunen gida yara da manya,
"Usaini ya yi hatsari a hanyar shi ta zuwa Lagos, sun mutu daga shi har direbansa har ba a iya tantance gawarwakinsu."
Iya abin da na iya ji kenan daga nan kuma ban sake sanin in da kaina ya ke ba sai farkawa na yi na ganni kwance a falona babu kowa a kusa da ni sai Amintacce yana riƙe da hannuna fuskarsa duk busasshen hawaye, kafin in gama tantance komai, Baaba Hajo ta yi sallama ta shigo, ta karaso da sauri ganin na farka ta na fadin "Sannu Balkisa, sannunmu da haƙuri, Allah ya jiƙan Usaina kaico kaico mun yi rashi mutuwa mai tonon silili." Jin waɗan nan kalaman daga bakinta ya sa na ji wani irin kuka ya taho mini daga can kasan zuciyata. Rungumeni Baaba Hajo ta yi ta na ci gaba da faɗin "Zubar da hawaye Balkisa, zubar da hawaye na taya ki, abin kukan ne ya same mu."
A wannan lokaci ji na yi ba ni da sauran amfani a duniya, ba ni da sauran farin ciki, ji na yi dama ace nima mutawan ta zo ta tafi da ni.
Dakyar Baaba Hajo ta yi jarumta ta shiga rarrashi duk da itama ba wai ta yi shirun bane, da kyar na tsagaita ganin haka yasa ta ce "ki tashi ki je ki yi ma shi sallama ku yi bankwana ki yi mi shi addu'a, an riga an shirya shi yanzu za a dauki gawar zuwa gidansa ma gaskiya."
Da taimakon Baaba Hajo na fito tsakar gidan, mata ne dam kam ta ko ina yan uwa da abokan arziki ana zazzaune cikin alhini da tashin hankali, kowa ya yi shiru muryar Daada kawai ke ta shi sai kuka take yi ta na cewa ta shiga uku ta lalace,.
Ina fitowa kallo ya dawo kaina, hango ni da Daada ta yi, ya sa ta mike daga in da take zaune ta nufo ni, ta na zuwa ta cakumi wuyan hijabina ta shiga girgiza ni da karfi ta na fa ɗin " Kin kashe shi hankalin ki ya kwanta Balkisu kin kashe mini ɗa, Allah ya isa tsakanina da ke ban yafe miki ba Balkisu abin da ki ka mini Allah ya haɗa ki da wacce za ta yi mi ki ninkin shi sau ɗari." Cikin ihu da karaji ta ke maganar don ba iya matan wajen ba har maza da ke cike da kofar gida suna jiyo muryarta." Ta ke ƙananan magana ya fara tashi ƙasa ƙasa kowa na faɗin Albarkacin bakinsa. Duk da ba na cikin cikakken haiyacina raina ya yi mummunar baci da abin da Daada ta yi, hakan yasa na buge hannunta da ke jikina, na raɓa ta zan wuce zuwa ɗakinta in da gawar ke ciki, ta sake jawoni tana faɗin "Ina za ki je, Algunguma, Wallahi ba za ki gan shi ba, ke da shi har abada." Baaba Hajo ce a zuciye ta ce "haba Daada wannan wane irin ra shin hankali ne, mutuwa Husaini ya yi fa ko gawarsa ba a ɗauke ba, wannan ai shashanci ne jahilci ne Wallahi kin ba ni mamaki,kuma ki sake ta, ta je ta yi sallama da mijinta idan ba haka Wallahi sai rayuka sun yi mummunar ba ci." Kafin Daada ta kai ga bata amsa aka fito da gawar, sai hankalinmu duk ya koma can, ganin yadda jini ya rina farin likkafanin da gawar Yaya Hussain ke ciki ta ke jiri ya shiga diba na, da sauri na dafe Daada ina maimaita kalmar "Inna lillahi wa Inna alaihi raji'un." Daada ta tunkuɗe ni, ta ke na yi wani irin mugun faɗuwa a wajen wanda ban farka ba sai bayan kwana uku da binne gawar Al-Hussain.
Kallo ɗaya na yi wa ɗakin na tabbatar asibiti ne, kafin in gama haɗa tunanina waje ɗaya, ta tsinci Muryar Baaba Hajo ta na mini sannu, kallo ɗaya na mata na fashe da kuka, ta dafa hannuna tana tsaye daga bakin gadon da nake kwance ta ce "Ki yi hakuri Balkisu, kuka ya isa haka, Addu'a za ki yi masa, Addu'ar ki ya fi buƙata a yanzu." Sai kawai na runtse ido na shiga kwararo ma shi Addu'a kamar da bakin kwarya, da larabci da Hausa duk
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 22