Share this page
4 / 9
watse sai tsirarun ƙawayen Inna da suke shirin ganin ƙwal uwar daka. BAYAN SALLAR ISHA'I Kawu Sani, Inna, Malam Hasan da Rakiya ne zaune a ɗakin Inna. Kusan kowannansu fuskarsa a haɗe take babu walwala, Kawu Sani ya dubi Malam Hasan ya ce. "Idan na fahimce ka Hasan, tun da har zaman can ya gagara za ka dawo nan gidanka wanda ka gada daga wurin mahaifinka?" Malam Hasan ya gyaɗa kai ya ce, "Kawu a can ɗin ne ba a samun cinikin faskaren sosai, dakon da nake haɗawa da shi yanzu sai a hankali, shi ya sa ma na yanke wannan shawarar ta mu dawo nan gida." Kawu Sani ya dubi Inna da ta cika fam ya ce, "Kulu kin ji abin da Hasan ya ce ko? Da ma kuma wannan gidan kin san gidansa ne da ya gada a wurin mahaifinsa. Don haka zai dawo tare da iyalinsa, idan na sake na ji wata magana marar daɗi daga gare ki wallahi ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Sai da Inna ta furzar da iska mai zafi sannan ta ɗago ta ce, "Na ji duk abin da ka faɗa Yaya, amma kuma ni ma ina da sharaɗi." Dam! Ƙirjin Rakiya da na Malam Hasan ya buga kusan lokaci ɗaya, Kawu Sani ya dube ta yana karantar yanayinta ya ce. "Muna jin ki." "Ka yi haƙuri Yaya ba rashin kunya zan yi maka ba, amma dai Hasan ɗana ne. Kuma ni da kai ba ma samun kowacce irin matsala sai a sanadiyyar matarsa. Amma ƙiri-ƙiri an shanye..." "Kulu ba na san ƙananan maganganunki marasa lissafi." Kawu Sani ya katse ta a ɗan tsawace, wani abu ne ya sake tokare Inna. Ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta ce. "Sharaɗina mai sauƙi ne Yaya, don gaskiya ba zan zuba ido rayuwar Hasan ta ƙare babu 'ya'ya ba. Duk cikin 'yan'uwansa shi kaɗai ne bai samu wani cigaban ku zo mu gani ba, ga Gali nan tare suka yi aure 'yarsa Suwaiba mai shekara goma har samari sun fara tsayar da ita. Don haka na yanke shawarar a wannan karon sai ya auri Zuwaira." Da wani irin firgici Rakiya da Malam Hasan suka ɗago suna kallonta cike da zallar tashin hankali. GIDANSU FAUWAZ Jim Abba ya yi yana nazari, cike da gamsuwa da shawararta ya ɗago ya ce. "Maganarki a kan hanya take Tani, domin a makarantar allo ne kaɗai zai samu tarbiyyar da muke buƙata tun da ya riga da ya raina mu. Amma ban da lalacewa ta yaya yaro kamar Fauwaz da bai wuce shekara goma zuwa sha biyu ba har ya fara bin dare yana yi mana ɗauke-ɗauke." Tani ta saki ajiyar zuciyar farinciki, amma sai ta ɓoye jin daɗinta ta aro fuskar damuwa ta lulluɓawa fuskarta ta ce. "Shi ne tashin hankalin, amma idan aka kai shi makarantar allo zai koyi neman na kansa har ya iya tsayawa da ƙafarsa. Ka ga a can bai ɗauki na wani ba ballantana ya janyo mana magana, amma matuƙar muka cigaba da zama da shi a haka har 'yar uwarsa sai ya koyawa." Abba ya yi zaraf ya ce, "Wannan gaskiya ne Tani, wallahi shi ya sa nake ƙaunarki. Saboda kina da hangen nesa da sanin ya kamata." Tani ta saki murmushin jin daɗi, sannan ta cigaba da ɗora shi a kan shawarwarin da zuciyarta take saƙa mata wacce take gani ita ce hanya mai ɓille mata. Hawaye bibbiyu ne suka shiga sintiri a saman fuskar Fauwaz, a hankali ya ja ƙafa ya shiga wurin Abida da har lokacin take cikin mawuyacin hali. Ba shi da wata mafita, domin bai san kuma abin da zai yi mata ba. Don haka ya rungume ta ya fashe da kuka yana jin kewar mahaifiyarsa. Jikinta zafi ya ji shi zau kamar wuta, bakinta yana rawa cikin sanyin murya ya ce. "Yaya... mutuwa... zan yi." Girgiza kansa ya yi cikin kuka ya ce, "Ba za ki mutu ba Abida, da safe zan sai miki magani da kudun da na samo." Idanunta a lumshe suke don ko iya buɗe su ba ta yi, ta ɗago hannu tana laluben fuskarsa. Da sauri ya riƙo hannun ya ce, "Me kike so Abida?" "Ya... ya... ba na son na mutu na bar ka a wurin Aunty, yanzu Abba ya daina sonmu." Fauwaz ya kwantar da kansa a fuskarta ya ce, "Ba za ki mutu ba kin ji Abida, Abba kuma ba daina son mu ya yi ba Aunty ce take faɗa masa laifinmu. Shi kuma duk abin da ta faɗa sai ya yarda da shi. "Zan sha ruwa." Ta furta masa a galabaice, sai da ya kwantar da ita sannan ya miƙe da sauri ya ɗebo mata ruwa. Ta sha ruwan sosai, ragowar kuma ta ce ya shafa mata a jikinta don ta ji daɗi. Cikin hukuncin Ubangiji ya ji zafin jikin ya ragu da ya zuba mata ruwan, don haka yana zaune yana gyangyaɗi shi da ita bacci ya ɗauke su, ba shi ya farka ba sai da aka fara kiran sallar asuba. Lokacin da ya tashi idon Abida biyu, a wannan karon jikinta babu zafi sosai. Sai dai numfashinta da take fitarwa sama-sama, sai da ya yi mata sannu ta amsa a hankali sannan ya miƙe domin ya ɗauro alwala don ya tafi masallaci. Har ya je bakin ƙofa ta ɗaga masa hannu, don yadda numfashinta yake fita ya sa ta gagara furta sunansa da ƙarfi. "Yayy... yaya." Ta furta a sarƙe ganin har zai fita bai ganta ba, da sauri ya koma ya ce. "Ga ni Abida me kike so?" "Na yi mafarki... da Umma, ta ce... ka kusa daina wahala... da ni." Ta furta a wahalce, sai ta cigaba da cewa. "Ta... kuma ce na gaishe ka." Murmushi mai sauti Fauwaz ya saki cikin jin daɗi ya ce, "Allah da gaske Abida? Na ji daɗi sosai, ni kuma tun da Umma ta rasu sau biyu na taɓa mafarki da ita." Murmushi ta sakar masa, sai ya sake miƙewa zai tafi masallaci ta sake riƙo hannunsa. "Yaya ina son... na yi kuɗi... don mu koma wani gidan... Aunty ta daina ganinmu." "In Shaa Allahu idan na girma na samu kuɗi zan gina mana gida mu koma can." Ya furta mata kalaman har cikin zuciyarsa, sai a lokacin ya fita daga ɗakin ya je ya ɗaura alwala. Yana gama alwala ya ga mahaifinsa ya fito shi ma, babu wanda ya yi wa wani magana har suka fita. Suna hanyar masallaci Abba ya ce. "Ya jikin Abidan?" Kamar Fauwaz ba zai amsa ba, sai ya danne zuciyarsa ya ce. "Da sauƙi." Daga haka suka ƙarasa masallaci, sai da aka idar da sallah Fauwaz ya jima yana yi wa Abida addu'ar Allah Ya ba ta lafiya sannan ya fita. Kai tsaye wani ƙaramin asibiti ya nufa da ke Unguwa Uku da ƙafarsa, har lokacin da ragowar duhu a gari don haka yawancin babban titin Na'ibawa babu ƙananan motoci sosai sai manya. Kasancewar da ƙafa yake tafiya lokacin da ya ƙarasa Unguwa uku gari ya yi tangaran har rana ta fito, ƙaramin asibitin na kuɗi mai suna Farha Clinic ya shiga. A reception ya samu wata mata wacce da alama ba bahaushiya ba ce, sai da ya gaishe ta sannan ya miƙa mata kuɗin hannunsa gabaɗaya sannan ya ce. "Don Allah magani za ki ba wa ƙanwata, tana zazzaɓi sosai. Sannan mamana kafin ta mutu ta taɓa kai ta asibiti aka ce ƙodarta na ciwo ban sani ba ko ciwon ne ya tashi." Yadda yake maganar za ka fahimci kalaman daga zuciyarsa suke fitowa, sai dai da yake ba ta jin hausa sosai ya sa ta kira wani abokin aikinta wanda ya kasance bahaushe. Matashi ne siriri, fuskarsa a zagaye da baƙin gashi. Fari ne fat sai dai yana da ɗan ƙaton kai, sai da ya gama sauraronsa ya ce. "Ina mamanku ko babanku?" Muryarsa tana rawa ya ce, "Mamanmu ta rasu." "Babanku fa?" Ya sake jefa masa tambaya, ya lura da sauyin fuskarsa, sai ya kawar da tambayar da ya yi masa ya ce. "Likita don Allah ku ba ta magani tana jin jiki sosai, ko kuɗin ba su kai ba wallahi zan yi gwangwan na cika sauran." Tausayin Fauwaz ya kama shi, sai ya dafa kafaɗarsa ya ce. "Abokina nan asibiti ne, asibiti kuma ba sa bayar da magani kai tsaye har sai sun binciki marar lafiya, an yi masa gwaje-gwajen da ya dace sannan likita ya rubuta masa magani. Ka je gida ka samu wani babba ku kawo ta asibiti, idan likita ya duba ta sai ya ba ta maganin da ya dace ka ji." Tun bai dire kalamansa ba idanun Fauwaz suka ciko da ƙwalla, cikin damuwa ya gyaɗa kai don idan ya ce zai amsa masa kuka zai iya ƙwace masa. Ya karɓi kuɗin da ya ba su sannan ya juya ya tafi zuciyarsa cike da ƙuna, yana kuma fargabar halin da zai sake samun ta a ciki. A ƙasa ya ƙara komawa har Na'ibawa, har zai wuya 'yan lemo ya hango kemis ɗin Maman Junior tana ƙoƙarin rufewa don ya lura da alama abu ta ɗauka domin ba ta buɗewa da safe. "Maman Junior a ba ni magani." Ya furta yana miƙa mata kuɗin hannunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce. "Wone yiri magani?" "Ƙanwata ce take zazzaɓi, kuma kwanaki an ce ƙodarta tana ciwo." Zazzaɓin da ya ambata ta fi riƙewa, saboda yau da gobe da ake yawan sayen maganin zazzaɓi da sauran gama-garin cutuka a wurinta. Kemis ɗin ta buɗ ta shiga, sai ta haɗo masa maganin zazzaɓin maleria ta miƙa masa ragowar canjinsa. Gudu-gudu sauri-sauri a haka ya ƙarasa layinsu, tun daga farkon layin ya hango tsirarin yara a ƙofar gidansu. "Ikon Allah Ya wuce gaban komai, shekaran jiya fa Abida suna tare da Sumayya da ta gaishe ni ta ce min aikenta aka yi. Wai ita ce yau ta amsa kiran mahalicci, koico rayuwa tsakaninta da mahaifiyarta shekara guda kenan." Kalam maƙociyarsu da take shirin shiga gidansu suka daki kunnuwansa, waɗanda suka yi daidai da bugun zuciyarsa wacce take barazanar tarwatsewa. Share Pls Ummou Aslam Bint Adam 🌚 07062062624 [13/05, 18:20] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ba tare da izinina ba. Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne. https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t SHAFI NA BIYAR A hargitse ya wurgar da ledar hannunsa jikinsa yana rawa ya ƙarasa ya riƙe hannun matar ya ce. "Umman Sumayya wace ce ta mutu?" Sototo ta yi tana kallonsa da mamaki, ganin haka ya sa shi girgiza hannunta yana ƙara tambayarta. Don haka ta ce. "Fauwaz wai kana nufin ba ka san Abida ta rasu ba? Ina ka je ne?" Bai jira ta dire kalamanta ba ya faɗa cikin gidan a guje, ita da ragowar matan da ke tsaye suka bi shi da kallon tausayi. Kai tsaye ɗakinsu ya shiga, sai dai yana shiga ya hango katifarsu da kayan da ya fita ya bar Abida da su a jikinta. Da wani irin sanyin jiki ya shiga, don har lokacin zuciyarsa wasu-wasin abin da kunnuwansa suka ji take yi. 'Abida ba ta mutu ba, ɗazu fa na fita na bar ta a wurin nan.' Zuciyarsa ta raya masa, amma sai ɗaya tsagin zuciyar tasa ya ankarar da shi. 'Idan ba ta mutu ba tana ina? Shin Umman Sumayya za ta yi maka ƙarya ne?' Cikin sauri ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Tani ya shiga. Daga can jikin bango ya hango Goggo Jamila ƙanwar mahaifinsu tana kuka, sai Tani da ke lungu tana sharɓar kuka waɗansu kitika-kitikan ƙawayenta suna rarrashinta, waɗanda sune suke sake ɗora Tani a duk turbar da take kai. "Kaico mutuwa! Yanzu shi kenan Abida ta tafi, yanzu ko kallon Fauwaz na yi dole hankalina ya dinga tashi. Yaran nan kullum suna tare, ta ina zai fara jure rashinta." Tani ta furta cikin kururuwa, ilahirin mutanen da ke ɗakin suka bi Fauwaz da kallon tausayi. Wani abu ne ya tokare masa maƙoshi, sai kuma ya ji wani irin sanyi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya fita daga ɗakin duk da ya ji Goggo Jamila tana ƙwala masa kira. Yana fita ƙofar gida ya ga Sumayya ƙawar Abida tana kuka, tana ganinsa kukanta ya ƙaru ta ce. "Yaya Fauwaz wai shi kenan ba zan sake ganin Abida ba? Shi kenan mun daina wasa da su 'yar gala-gala?" Motsa bakinsa ya shiga yi sai dai ya gagara furta koda kalma ɗaya, da sauri ya wuce ta ya nufi maƙabartar cikin sauri da yake a cikin unguwarsu take, yana fatan ya ga koda gawar Abida ce. Sai dai yana shiga ciki ya hango mutane suna fitowa, bai fasa tafiya ba har suka haɗu a hanya. Mahaifin Sumayya ne ya ce, "Fauwaz ina ka shiga tun ɗazu ana ta nemanka?" "Hmmm zai wuce ya tafi yawon banza, tun da shi ya saka a gaba. Me ka zo yi maƙabartar? Ai da ka yi zamanka a can ba sai ka zo ba." Abba ya furta yana yin gaba, ba tare da ya jira cewar Fauwaz ba. Yawancin mutane wuce shi suka yi, sai tsiraru da suke yi masa ta'aziya. Zannur abokinsa ne ya dafa shi ya ce, "Ka yi haƙuri Fauwaz, mu ƙarasa ka yi mata addu'a ba." "Me ya sa ne Zannur? Me ya sa rayuwa ta juya mini? Me ya sa duniyar ta yi mini zafi? Na rasa Umma a daidai gaɓar da ban zata ba, ga shi yanzu mutuwar Abida ta shammace ni. Me ya sa Abba ba zai fahimci halin da nake ciki..." Kuka mai tsuma zuciya ya ƙwace masa. "Saboda kowanne bawa akwai launin ƙaddarar da ke bibiyarsa, taka a haka ta zo maka. Ina fatan za ka yi addu'ar Allah sa haka ne mafi alheri. Yanzu mu je ka yi mata addu'a." Zannur ya furta yana jan hannunsa, cikin kuka Fauwaz ya ce. "Ina jin kamar ba zan iya zuwa na ga kabarin Abida ba." "Za ka iya, domin addu'arka tana da muhimmanci a gare ta." Da tausasawar Zannur Fauwaz ya ƙarasa gaban kabarin Abida, sai da ya ci kuka mai isarsa sannan ya kwarara mata addu'a. Tsakanin kabarin mahaifiyarsu da na Abida babu tazara sosai don haka ya ƙarasa ya yi wa mahaifiyarsu addu'a suka fito daga maƙabartar. Koda suka ƙarasa gida zaune ya yi a ƙofar gida, komai da kowa ya fita daga rayuwarsa. Domin ji ya yi rayuwar ta ishe shi, har fata yake yi ina ma ajalinsa ya riske shi domin ko kaɗan gani yake ba zai iya jure rashin Abida ba. Yana daga nesa yana hango mahaifinsa yana ta karɓar gaisuwar mutane. Yadda yake haba-haba wurin karɓar ta'aziyya ya sa shi tuna mahaifinsu na baya da ke bakin ƙoƙari wurin ganin ya kula da damuwarsu. Don a yanzu gani yake kamar an canza musu shi, haka aka cigaba da zaman makoki dangin mahaifinsa suna lallashinsa da ba shi baki. A cikin waɗannan kwanakin rayuwar ta yi masa sauƙi a fanin kyara, hantara da ƙalubalen da yake fuskanta a ɓangaren Tani da mahaifinsa. Sai dai ji yake da za a dawo masa da Abida da ya gwammaci ya cigaba da zama a cikin ƙuncin rayuwar da yake ciki. Wani babban abin da ya ɗaure masa kai da Tani yadda take haba-haba da shi, har idan aka gama girki take aikawa a kira shi, ta sa a ba shi nasa daban wai ya ci ya ƙoshi kada ya zauna da yunwa. Sai dai hakan ba ƙaramin sake hura wutar ƙiyayyarta ya yi a zuciyarsa ba, don haka a kodayaushe ta yi masa maganar abinci kalma ɗaya yake furta mata ya ƙoshi. Su kuwa dangin Abba ban da farinciki babu abin da suke yi, don Goggo Jamila cewa ta yi tabbas Fauwaz ba zai yi maraici ba. Ranar sadakar bakwai da safe, Abba yana zaune bayan da aka gama addu'ar bakwai kira ya shigo wayarsa. Saboda haniyar mutane sai da ya fita daga cikinsu ya koma bakin masallacin da ke kallo su, sannan ya ɗauka cikin sallama. Ba a iya amsa masa ba, sai jawaban tashin hankalin da aka rattabo masa. Tun bai gama wayar ba, ya zame hular kansa yana faɗin. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Shiru ya yi ya cigaba da sauraro har aka gama jawabin aka yanke kiran, daɓar ya zauna a kan dandamalin da ke gaban masallacin cikin firgici da tashin hankali ya ce. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Allahumma ajir ni fi musibati, wa aklifni khairan minha." Yana gama faɗar haka ya yanke jiki ya faɗi. KAWU SANI Murmushin takaici Kawu Sani ya saki, Inna ta sake tsuke fuska don a wannan karon ta ci alwashin dole Malam Hasan ya bi umarninta. "Ina ce wannan tsohuwar magana ce Kulu? Ba tun kafin Zuwaira ta yi auren farko aka yi maganar ba yaron nan ya ce ba ya yi mata son aure sai na 'yan'uwantaka?" Kawu Sani ya wurga mata tambaya, Inna ta cure baki wuri ɗaya ta ce. "Haka ne." Kawu ya ce, "To a yanzu ma babu ita..." "Don Allah ka yi.haƙuro Kawu, Baban Fatihu zai aure ta a wannan karon." Rakiya ta yi ƙarfin halin furta haka, wani irin kallo Malam Hasan ya wurga mata cikin wata irin murya ya ce, "Ni na furta miki haka Rakiya?" Rakiya ta girgiza kai sannan ta ce, "A wannan karon matuƙar ba ka auri Zuwaira ba ni ma na gama zaman aure da kai." A wannan karon shiru ɗakin ya yi, Kawu Sani ya numfasa ya ce. "Ka ji abin da matarka ta ce?" Gyaɗa kai Malam Hasan ya yi sannan ya ce, "Na amince zan aure ta." Rakiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci tana jin kishin mijinta, domin idan ta ce ba ta ji kishin kalamansa ba ta yaudari kanta. Amma ta san hakan shi ne kwanciyar hankalinsu gabaɗaya, don ba za ta taɓa manta tarzomar da suka sha a shekarun baya ba. "AlhamduLillah! Ma Shaa Allah, Allah Ya yi maka albarka Hasan. Ubangiji Ya haɗa kan iyalinka." Kawu Sani ya furta sannan ya mayar fa kallonsa wurin Inna ya ce. "Kada na ji ko na ga wata fitina ta ɓullo daga wurin Zuwaira, domin ke da ita duka bakinku ɗaya." Inna ta amsa masa zuciyarta fes don ta san ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba. Zuwaira tun da ta ji maganar aurenta da Malam Hasan ta shiga firirta da feleƙe, sai dai duk abin da take yi ko kaɗan Rakiya ba ta nuna mata alamar ta fahimce ta na. A cikin kwana biyun da suka yi tsangwamar da Inna take yi mata ta yi sauƙi, sai dai duk wanda ya zo gaisuwa sai ta ji wata mummunar magana daga gare shi wacce za ta sosa mata rai. Ana cikin haka har Malam Hasan ya koma ya kwaso musu kayansu, wanda ya tabbatar mata da Kawu Sani ne ya ba shi kuɗin ɗawainiyarsu. Ɗakunan da ke cikin gidan ciki da falo-falo ne guda biyu, sai falle-falle guda biyu. Ciki da falon ɗaya su Rakiya suka ɗauka, sai Inna ta haɗe kayanta a ciki da falo ɗaya ta ce idan an ɗaura aure Zuwaira ta ɗauki falle-falle guda biyu. Satinsu ɗaya da komawa Malam Hasan ya kama awakinsa da Inna take yi masa kiwo guda biyu ya sayar, sai suka rage saura tinkiya ɗaya da rago ɗaya. Da wani kaso daga cikin kuɗin ya biya sadakin Zuwaira, ragowar kuɗin kuma ya kafa jarin turare irin wanda ake yawo da shi a kwando ana sayarwa da kayan yari na cikin glass. Yadda Zuwaira take rawar kai abin ba ƙaramin ba wa Rakiya mamaki ya yi ba, saboda wasu kalaman da abin da take yi sam ba su dace a gaban Inna ba. Amma sai ta ga ita Inna ko a jikinta, a daren ranar Malam Hasan bai shiga gidan ba sai bayan sallar isha'i. Hannunsa ɗauke da kwandon turarensa, ɗakin Rakiya ya shiga ya same ta zukuɗum tana tunani. "Rakiya ba za ki daina tunanin nan ba? Ko kina son ki dinga ɗaga mini hankali idan na fita." Malam Hasan ya furta cikin damuwa, ganin haka ya sa ta saki murmushin yaƙe ta ce. "Tunaninka nake yi fa ba na Fatihu ba." Ya ɗan haɗe fuska cikin wasa ya ce, "Kina tunanin ɗanki dai." Ta saki murmushin yaƙe ta ce, "Har abada ba zan daina tunanin Fatihu ba." "Yanzu dai ba wannan ba, ga kayan da zan fara saidawa. Ki saka mini albarka da bakinki mai albarka." Ya furta yana miƙa mata kwandon turaren da glass ɗin yari, fara'arta ce ta faɗaɗa. Cikin jin daɗi ta shiga kwarara masa addu'a, sai da ya gama amsawa sannan ya ce. "Zuba mini abinci." Hararar wasa ta yi masa ta ce, "Kai da amarya take jiranka, ko ka manta ne?" Guntun tsaki ya saki, yana jin wani tsantsanin Zuwaira. "Ni fa na gaji da kara tun da ba ku san zuru ba, na ga alamar idan na yi shiru sai ta gama da kai tukunna." Suka ji an furta a tsakiyar kansu, a tare suka waiga suka ga Zuwaira riƙe da labule fuska a murtuke. "Mene ne haka Zuwaira?" Malam Hasan ya furta, kamar jira take yi ya dire ta ce. "Kwanana na biyo, tun da na ga ana ƙoƙarin cin amana ta. Don ma dai a banza abin yake wai an tsikari kakkausa, tun da ba iya ƙyanƙyashe ƙwan take ba..." Tass! Malam Hasan ya ɗauke fuskarta da mari, sannan ya nuna ta da yatsa rai a ɓace ya ce. "Idan ganganci ya sake biyo dake ta cikin ɗakin nan sai na tattaka ki." Da sauri Rakiya ta sha gabansa ta ce. "Haba Abban Fatihu, me kake yi haka?" Yana shirin ba ta amsa Zuwaira ta fita da sauri tana sakin kuka tamkar wacca aka ba wa saƙon mutuwa. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ka ga za ka janyo mini ko? Rakiya ta furta, Malam Hasan ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Kada ki damu don Allah, na sanki sarkin tsoro ce." "Hasan! Hasan! Za ka fito ne ko kuwa sai an ba ka izinin fitowar?" Inna ta furta cikin ɗaga murya, kusan lokaci ɗaya Rakiya da Malam Hasan suka dubi juna. Suna nan zaune suka ji an ɗaga labulen ɗakinsu. "To sake shi baƙar munafika, tun da ba kwananki ba ne sai ki ba shi dama ya yi gaba." Inna ta faɗa tana wurga wa Rakiya harara. "Ga ni zan fito yanzu." Malam Hasan ya furta, tun bai gama rufe baki ba Inna ta nuna masa hanya ta ce. "Fita mu je na ce maka, shashasha bawan mace." Babu yadda ya iya, haka ya bi bayan Inna jiki a saluɓe, don ba ya son ya sake wata maganar ya ja wa Rakiya wani sabon zagin ko baƙar magana. Tamkar raƙumi da akala haka ya bi bayan Inna har suka fita tsakar gida, ɗakin Rakiya ta nuna masa ta ce, "Maza ka shiga wurin amaryarka, idan ka ga dama kada ka taɓuka abin arziki. Sakarai kullum kana can wurin da babu ƙaruwa ballantana mamora." Jiki a sanyaye ya nufi ɗakin Rakiya bakinsa ɗauke da sallama ciki-ciki, yana shiga Rakiya ta yi farat ya tare shi cike da kissa da kisisina. Tsaye Malam Hasan ya yi yana kallon ikon Allah, don rashin kunyarta ba ƙaramin mamaki take ba shi ba. Ya san dama ba za a taɓa haɗa kunyar budurwa da ta bazawara ba, amma kuma ko kaɗan bai fuskanci haka daga wurin mahaifiyar Fatihu ba, domin ita ma a bazawara ya aure ta. "Barka da zuwa angona." Zuwaira ta furta tana dafa ƙirjinsa, mamaki ne ya sake mamaye shi da ya ga ta ware kamar ba

Chapter 4 of 9