ta wayar baban ku ita take sanar min da rasuwar” Duk sai suka yi shuru suna jin babu daɗi a ransu. “Amma ya kamata ki je gida tsawon shekaru fa ba ki je ba, izuwa wannan lokaci mun samu cigaba tun da mijin Noor yana iya ƙoƙarinsa a kanmu” Cewar Fiddoh tana ƙoƙarin shiga bayi jin ana kiran sallar magariba.
..........Abban Amrah yana faka mota Suhaima ta yi saurin fita dan ta san Daddy a cike yake da ita, aikuwa shi ma ya fita da sauri da zummar cin ƙaniyarta sai dai Aminin nasa ya dakatar da shi tare da lallashinsa kan ya ƙyaleta har yanzu giyar ƙuruciya ke ɗaiwaniya da ita Alhj Aminu bai ce komai ba har Abban Amrah ya yi masa sallama yana faɗin “Sai mun zo diner anjima dan kasan ban taɓa cin girkin Amariya ba, yau da ni da za a yi wannan bushashan” Suhaima kuwa tana shi falon ta fara ƙoƙarin shigewa ɗakin Amnoor miƙewa Hajiya Laraba ta yi tare da faɗin. “Ina kike shirin zuwa?” Tsayawa ta yi zuciyarta na bugawa dan ba ta tsammaci maganar mahaifiyarta ba. Ba ta aune ba taji ta sauke mata yatsu biyar bisa kuncinta hagu da dama. “Kina ƙoƙarin zubar mana da mutunci ke har kin yi wayon bin namiji gida? Oya muje in duba ki dan wallahi ban yarda da ke ba Suhaima” Cikin kiɗimewa Suhaima ta ce “Wallahi tallahi Momy ƙalau nake....” Saukar bulala ta ji da jikinta nan take ta saka ihu tare da ƙwalawa Amnoor kira. “Wayyo Allahna! Dan Allah Aunty Noor ki zo ki ceceni, wallahi tallahi Daddy ba zan sake ba Momy ki ba shi haƙuri, wayyo yaya Hisham..” A zuciya ya dinga sauke mata bulalan a jikinta. “Kar ka kashe min 'ya, wannan wane irin baƙin zuciya ne? Ka daina dukanta!” Nunata ya yi da ɗan yatsa yana faɗin “Ba ga irinta nan ba, to wallahi idan Suhaima ta ɗebo abin kunya sai dai ki tattara da ke da ita ku barmin gida shashasha mara lissafi, bari ki ji in gaya miki wannan ba soyayya bace! Ba tarbiyya bace! Wallahi kin ji na rantse miki kika sake min magana a kan hukuncin da nake yi wa Suhaima sai na saɓa miki.... Cikin ɓacin rai ta ce. “Sai me? Ka fito fili ka yi magana ka ce za ka sake ni ai tun da ka yi aure ka ɗauke hankalinka daga gare mu ƙarshe ba tura min 'ya ka yi wani wurin don a barka da matarka.... “Ya isa! Ya isa, kar ki yarda ki sake kirin gidan mahaifiyata da wani gun” Ya yi cikin muguwar tsawa, matsowa ta yi tana mishi kallon raini tare da kai hannu za ta janye Suhaima aikuwa cikin fushi ya zuba musu bulalan daga ita har Suhaiman. “Wallahi na faɗa maka ka daina duka min 'ya! Ka bar dukan Suhaima Aminu!” Bai saurara mata ba daga ita har Suhaiman. Sallame sallar na yi ba shiri jin irin kururuwan da Suhaima take yi tana k'wala min kira. Da sauri na fito wanda ku san a tare muka ƙaraso ni da Hisham, tare Suhaima na yi tare da faɗin. “Ka yi haƙuri Daddy...”
“Matsa a nan!” Cikin tsawa ya yi min maganar tare da min nuni da gefe. Girgiza mishi kai na yi tare da riƙe Suhaima wacce ta ƙanƙameni tana kuka. Hisham kuwa cak ya tsaya yana kallon Suhaima tare da Amariyar mahaifin nasa wacce tun da ya zo gidan bai ganta ba sai yau. Ƙuru ya yi mata da ido yana sake jin sautin muryanta inda take ba wa Daddy haƙuri. Lumshe ido ya yi yana jin zuciyarshi na wani iri da sauri kuma ya buɗe ido jin Suhaima ta saka ihu tana kiran sunan Amnoor. Da sauri Amnoor ta ja Suhaima zuwa ɗakinta Hajiya Laraba ta ce “Ki dawo mishi da ita ya kasheta! Ai wallahi Aminu ni da kai ne, ba dai ka haɗa ɗi da Suhaima ka daka ba?Shuru Amnoor ta yi tare da faɗin “Haba Hajiya! Ta yaya zai dinga mata irin wannan dukan? Ai sai ya ji mata rauni maimakon ki rarrashe shi ya ƙyaleta duk irin kururuwan da take yi na ɗauka ma kina ɗaki ne, a she duk kina kallonsu gaskiya irin wannan dukan bai dace ba, duk da ba ta kyauta ba, amma ai ta ba da haƙuri..” Nuna Amnoor ta yi da yatsa tare da faɗin “Kar ki sake min magana irin haka, ina magana a kan 'yata ne da mijina dan wallahi zan ɓata ranki, Aminun ne zan lallashe shi? Shi yarone? Ko shi jariri ne? Ki je ki ɗauko Suhaima ki dawo mishi da ita, ba duka ba, ƙarshen duka ya kasheta, kai kuma na dawo gare ka, da ke 'yar gwal matar so, ta fito ta yi magana dole ka dakata da dukan ko? To na rantse da Allah ka sake taɓa lafiyar Suhaima ko, abin da zan maka sai ya ba ka mamaki” Da wani irin mutuwar jiki Hisham ya fita a falon yana jin wani irin abu ya toƙare shi a ƙirji, domin Amnoor kawai yake kallo zuciyar shi kuwa na wani irin yanayin da ya kasa fahimta, wayar shi ya ɗauka tare da kiran Munir ko sun ƙara so dan ya je ya ɗauko su a filin jirgi, tun yau yake son sanin inda take ba zai iya jira mai tsayi ba.
Sake bulalan ya yi tare da zubewa kan kujera yana kallon Laraba, tsaki Hajiya Laraba ta yi tare da barin falon, ruwan sanyi Amnoor ta ɗauko tare da zama kusa da shi ta kai ruwan bakin shi. “Ka yi haƙuri Daddy” Ta faɗa tare da riƙe hannunshi tana murzawa cikin nata. Bayan kalmar haƙuri ba ta san abin da za ta ce mishi ba. Wayarshi da ya yi ƙara ne ya ɗauka yana magana ya ce mata “Ina abincin da na ce a yi wa baƙi na?” Ya fad'i haka tare da miƙewa tsaye. “Na kammala komai ai” Yana ƙoƙarin fita ya ce “Ki shirya komai ina dawowa”
“Allah Ya tsare hanya” Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta sunkuyar da kai na yi ƙasa ina murza 'yan yatsu na. Ji kawai na yi ya ɗago fuskata tare manna min kiss a goshi yana faɗin “Amin” Sannan ya fita a gidan. Ɗakina na nufa a falo na ci karo da Suhaima kallona ta yi tare da faɗin “Auntynmu irin wannan love haka? Naga Daddyna ai” Kame fuska na yi tare da faɗin “Allah Ya shiryar da ke Suhaima”
“To Amin, amma ai gaskiya na faɗa. Ni kam ki lallaɓa Daddy idan Dalil ya zo a yi maganar aure kawai, dan wallahi ina son shi da yawa, ba zan iya barin shi da wancan karuwar tana zuwa mishi ba” Juyowa na yi ina kallonta kafin na ce “Suhaima wani abu ya taɓa shiga tsakanin ku?” A tsorace ta zare ido tare da faɗin. “Wallahi tallahi a'a Aunty, babu abin da ya taɓa haɗa mu, ko kiss komai bai taɓa min ba” Ajiyan zuciya na yi tare da faɗin “Allah Ya tsare gaba. Tun da karsashi soyayya ya goge zafin duka oya sai muje a tayani shirya abincin baƙi ko?” Suhaima ta ce “Ok mu gama sai na yi miki makeup dan ban ga kina irin kwalliyar nan ba” Share batun na yi muka nufi kitchen, sai da muka jera komai a daining sannan na koma ɗaki. Wanka na yi tare da yin alola na gabatar da sallar magariba ina cikin yin azkhar Suhaima ta yi sallama ta shigo zama ta yi tana faɗin “To in kin gama sai in miki” Kallonta na yi sannan na ce “Wai ke da gaske kike? Ni fa ban damu da wannan fenti da ake yi wa fuska ba” Gyara zama Suhaima ta yi tana faɗin “Tabɗi! Manyan baƙi Daddy zai yi kuma ma ba ki ga kwalliyar da Momy ta yi ba, Auntynmu ki zo kawai in gwangwaje ki da kwalliya dan in wanke fushin da Daddy yake yi da ni Please” Ganin lallai da gasken gaske take yi ya sa na ce mata “Bari na yi sallar lsha'i to” Ina idar da sallah kuwa ta sani gaba da fente-fenten fuska kusan minti goma sha biyar muna abu ɗaya dirin motar shi ya sa ni faɗin “Wai har yanzu?” Cikin sauri Suhaima ta ce “Sorry yanzu zan ƙarasa miki..” Ai bata rufe baki ba sai ga kiran wayarshi “Kin gani ko? Kwalliyar ya isa haka Please ban so ya zo yana jirana gwara ni na jira shi” Suhaima ta ce “Ai na gama ma ɗaurin ɗankwali kawai za mu yi” Leshi wanda ake yi wa ɗinkin zamani riga da siket wanda ya ji adon stone na fito da shi na saka bayan na shafa turare masu sanyin ƙamshi “Gaskiya Auntynmu turaren ki suna min daɗi sosai” Ɗan murmushi na yi tare da faɗin “Bari mu gama hidimar baƙi sai na ware miki wasu” Cikin murna ta ce “Wow! Ina godiya sosai” Tana gama ɗaura min ɗankwalin ta ce “Haɗuwa! Tsakani da Allah kin fito cas! Kin yi acan-acan bari mu yi hoto yanzu na turawa Daddy” Ba laifi kam, dan ko ni ma na yaba da kwalliyar. Haka ta ɗauke mu hoto sannan ta yi min, nan take kuwa ta tura mishi.
Daidai lokacin da yake shirin sake kiran wayarta ya ga saƙon Suhaima buɗewa ya yi yana kallon hotunan ƙuri ya yi wa wayar sai yau ta fito fess a Amariya miƙewa ya yi tare da nufo ɗakin. “Assalmu Alaikum!” Kallon juna muka yi, aikuwa Suhaima me za ta yi bayan dariya. Amsa sallamar muka yi sannan Suhaima ta kama hanyar fita bayan ta yi mini raɗa a kunne, tana kallon Daddy da ya ɗauke kanshi daga kallonta domin har yanzu da saurin fushinta a ranshi bai huci ba. Harɗe hannuwa ya yi a ƙirji ya tsaya ƙare mata kallo “Alhamdu Lillah Ma Sha Allah! Very nice” Ya faɗa tare da haɗa 'yar manuniyar yatsarshi da babban yatsar alamar ta yi kyau sosai. Murmushi kawai na yi sannan na fara taku ɗaɗɗaya ina zuwa inda yake tsaye daidai kafaɗar shi na saka kaina tare da buɗe wayata na shiga Camera. Ji kake cat-cat na ɗauke mu hoto. Ina shirin barin jikinshi ya sake kamo ni tare da kai hannuwanshi ƙugunta yana zagayewa kanshi ya saka a wuyanta yana shinshinar ƙamshin jikinta kana ya dawo fuskarta, ɗan ƙaramin bakinta da ya sha man baki sai maiƙo yake nan ya dire ido tare da kai bakin nashi kan lips ɗinta yana wani irin sauke mata zazzafan numfashi runtsa ido ta yi tare da suke ajiyan zuciya daidai lokacin da ya fara tsotsar lips ɗinta.
_Shin ko burin Fiddoh zai cika na auren mahaifin Suhaima? Yaya batun furucin da Hajiya Laraba ta yi wa Alhaji Aminu? Suhaima za ta cika burinta na Auren Dalil? Shin Dalil ɗin zai amince da ita? Zai zo ya amsa kiran da Alhaji Aminu ya yi masa? Ina labarin Emanuel? Yaya Hisham zai yi idan ya binciko kuma ya gano yarinyar da ya ɓatawa rayuwa ce take matsayin matar mahaifinsa? Shin zai haƙura da soyayyar da yake mata? Koma dai mene ne ku biyoni don jin yadda labarin zai kasance._
_Na kammala free PAGE. Don samun cigaban akwai Number asusu da kuma inda za ku tura shedar biya._
#Ayshajb
#Amnoor
#Sexstory
#Lovestory
#Sister'slove
#Paidbook
₦500
2389596965 Aisha Jubreel Zenithbank.
A turawa wannan Number shedar biya 09079740079
[5/9, 11:46 PM] FARHATULƘALB💔🤗: *♡AMNOOR...!*
Romance Story.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 14