na rama mai idon damusa kawai." Tana fada ta tattara yawo ta watsa masa daidai fuskarsa kafin ta arce a dari ta shige ciki.
Rikicewa Saheer ya yi take kansa ya fara wani gigitaccen ciwo,idanunsa suka kada suka yi ja.
Cikin sauri ya shiga toilet ya fara wanke fuskarsa yana wanken bakinsa.
Karshe sai da ya kara brush ya kara yin wanka yasa kaya.
Da sauri ya bar dakin domin gabadaya a tsarge yake da dakinma.
Ciki ya shiga domin gaida iyayen nasa, ya shiga dakin Momy ya gaidata har zai fita ta ce, "Saheer."
Ya juyo ya kalleta yana amsawa.
Ta ce, "sai dai ka yi hakuri kuma ka sa aranka cewa babu Ɗan da zaiyiwa iyayensa biyayya ya taɓe biyayya bata taba zama a banza ka da kasa komai aranka ka ji cewa kawai duk abun da Ubangiji ya tabbatar shine daidai a garemu duka."
Da mamaki ya kalli Momy domin sam bai gane inda ta nufa ba,don shi ya ma mance da wani batun auren shi da Salma.
Ya ce, "Momy ban gane ba,me ya ke faru wa?"
Momy ta ce, "magana nake akan aurenka da za a hada dana yar uwarka Salma."
Momy na fada Saheer ya kara ji kanshi ya yi wani irin sarawa.
Da sauri ya dafe kan.
"ka karbi hakan a matsayin kaddara da biyayya kuma In sha Allah nan gaba zaka alfanun hakan." Momy ta fada.
Kau da kanshi ya yi kawai bai ce komai ba ya fice.
Momy ta kara fadin, "Dadynka na falo kaje ku gaisa kafin ka fita."
Falon ya shiga kuwa ya tarar da shi zaune da Inna da Salma.
Salma na ganin shi ta fara murguda mishi baki tana harara.
"Inna kin ga wallahi duka na ya dunga yi da wani abu kamar wayar injin mugun ne."
Gaishe da ita Saheer ya fara,
"Inna an tashi lafiya?".
Da harara ta bishi kafin ta ce, "Gidanku na ce ka ci gidanku da ban tashi lafiya ba zaka ganni hakane? Kodayake ai daman kai da Uwartaka fatan mutuwa kuke mun to ahir dinku na fiku tijjara da tashanci ni fa na gama fahimtar take taken yaron nan wato saboda kazo fyeɗeta baka samu galaba ba shine ka daura mata karan tsana da duka? Na ce to karbi nan gidanku gobe goben nan za a daura maku aure sai kaje can ya karata da maitarka." Ta kalli Dady kafin ta ce, "Illu ka ga abun da nake gudu ko? Wannan Ɗan naku tuzurun tuzure indai ba a gaggauta anyi abun nan ba akwai lukutar matsala kana ganin idanun sa ma ai ka ga mai bidar aure , gabadaya ya ga yarinya yar dumurmur ya birkice to ahir ayi abun da ya dace amman ban da duka."
Dady ya ce, "In sha Allahu Inna."
Saheer ya gaida Dady ya fice cikin sauri a dakin domin ya fara kasa gane kan shi.
Bai nufi School ba,a kan hanya ya yi parking motarshi gefe ya kunna sigari yana sha.
Aranshi yake fadin, "wai da gaske wannan bagidajiyar kazamiyar yarinyar za a aura mun? Aure ni kuma da wannan yarinyar? Mu zauna gida daya? Inuwa daya? Kai Never." Ya fada da karfi.
Inna ta kalli Dady ta ce, "Yawwa Illu maza ka tashi ka je a tanadi goro da mintinan kan lokaci kuma kar a manta a kawo mun nawa yawwa, ke kuma Salame tashi mu shiga daki in baki wasu sirruka domin nan da gobe kin zama matar aure, kar waccer figaggiyar matar mai kirjin faranti ta ji ta karu maza mu shige ciki."
[6/28, 12:39 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*
PAGE-5
Tashi Inna da Salma suka yi suka shiga cikin daki.
Dukaninsu suka ɗare kan gado.
Inna ta kalli Salma kafin ta ce, "Salame, ki jini da kyau ki saurareni yau zan baki sirrin da ya sa na mallake zuciyar Kakanki Malam Auduwana, kai Allah sarki Malam Auduwa na shatou mun diga soyayya fa kamar ba za a mutu ba mu fa tsabar soyayya har zuciyoyinmu magana suke da juna,haka inuwarmu in muna tafiya basa taba rabewa zaki gansu manne da juna, ina fada miki ka da ki kuskura ki bar mijinki shi kadai duk inda yake kina bibiyarsa sannan kina daukan wanka kina kashe kala wannan jagirar da kike ta kauye karki fasa."
Salma ta ce, "Tom Inna ai nan ban da kayan kwalliyan fa."
Inna ta ce, "Shi mijin naki ne ai zai siyo yoo ai shi zakiyi yiwa kwalliyar nidai ina fada miki, kuma ki dunga yi masa fari da idon nan."
Inna ta karasa maganar tana wani irin juya ido.
Kwaikwayonta Salma ta fara suka kyalkyale da dariya Inna ta ce, "Yawwa hakan kina ganinsa ki fara kina tande baki kina tsukewa wannan lamari ba karamin kara ɗankon soyayya yake ba,ko ya fita ke kawai zaina gani cikin idanunsa kamar ni da malam amadu shi fa ko kasuwa yaje in ba na bi bayansa ba ko ya dawo gida ya ganni mun hada ido nayi masa farin nan hankalinsa sam bai kwanciya."
Salma ta gyara zama ta ce, "ai tare ma zamuna fita da shi duk inda zaije dinnan."
Inna ta ce, "Yawware yar albarka haka nake son ji, in kuma baya nan ya dawo,yana dawowa ki rungumeshi irin rungumar da kike gani a talabijin din mudi mai balangu na yan indian nan."
"Eee ee na gane inna har hada bakinsu suke fa suna wani abu wai shi kuss (kiss)" Salma ta fada tana tafi da hannunta tana dariya.
Inna ta ce, "Tabbas kuss tsuke bakin ake sosai asa a ciki,yanzu ma kin ga kije kiyi wanka kisa kaya zanje in karbo miki kayan kwalliya gun waccer matar kafin ya dawo da dare ya ganki kin dau wanka."
Hakan aka yi kuwa Inna taje ta titsiye Momy ta karbo kwalli da hoda salma na wanka ta mulka wata irin gira daga gishi har ido ta cika bakinta da baki tana juya ido.
"Aradun Allah Inna na san inya kalleni suman dadi zaiyi domin na san na yi kyau na fitar hayyaci wooo ni Salame ."
Inna tayi wani guntun murmushi ta ce, "ai Indai ina raye sai sahaaaru ya zame miki mijin kan ta ce ma."
Mai Salma zata yi ban da dariya har cikin ranta wani dadi da shauki take ji.
★★Salman kuwa da ya fitan ma bai samu nutsuwa ba har sai da ya sha sigarinsa kamar yadda ya saba kafin ya shiga school.
MARIA MEMORIAL PRIVATE SCHOOL.
School ce mai kyan gani da kuma sanya son kasancewa a ciki ga dukkanin wasu yara masu tasowa domin cike take fal abubuwan wasaani da karatu.
Saheer shine Headmaster a school din kuma yana koyarda Mathematics ga yan primary 4 da 5.
Yana samun girmama matuka agun teacher din da students domin duk miskilancinsa yana da saukin kai da tausayi.
★★★Koda dare ya yi Saheer ya dawo bai shiga cikin gidan ba,domin aransa ji yake baya son ganin salma sam in ko ya ganta zai iya kasheta a yadda zuciyarsa take.
Inna da ita nata faman jiran shigarsa sunji shiru.
Inna ta ce, "maza ke tashi muje ki dauki mayafin ki muje kuyi zance ba zan iya da wannan lamarin naku ba dake shi din munafukine yana so yana kaiwa kasuwa Kodayake ai da kunya yaga asirinsa ya tonu na gano shi."
Suka fita sunata bambami.
Daidai kofar part dinsa suka je suka tsaya suna bugawa kamar zasu buga kofar.
Inna na fadin, "kai sahaaru ka bude mune nan ."
Tsaki ya yi ya bude kofar ba don ya so ba.
Suna hada ido da Salma ta fara kada masa ido tana fari tana cuno masa baki kamar zatai mai kiss.
Inna ta ce, "hira na kawota kuyi, ee hira zance zakuyi na masoya kafin gobe a daura maku aure."
Saheer ya ce, "Inna kaina ciwo yake Don Allah ku barni in huta."
Yana fada Inna tasa hannu aka ta kurma ihu tana, "na shiga uku na lalace Sahaaru har ni zan ce ma kayi abu ka ce baza ka yi ba? Har ni."
Su Dady na fitowa ta kara daga murya tana kuka tana share hawayen da mayafinta.
Shi kam Saheer ma ya rasa abun cewa binta da kallo kawai yake cike da mamaki ita kuma Salma na rarrashinta.
Dady ya ce, "lafiya Inna?"
Inna ta nuna saheer ta ce, "Yoo ina lafiya ilu ,na ce ina lafiya? Ummmm wai har nice zan sa sahaaru abu yaki? Wai daga na ce suyi zance da Salma tunda gobe za a daura masu aure wai shi aa kar mu dame shi,dole inyi kuka dole inyi kuka." Ta karasa maganar tana kara kakulo kukan .
Dady ya ce, "ki yi haquri ki daina kukan Inna Don Allah." Ya kalli Saheer kafin ya ce, "kai kuma ka fito ku zauna kuyi zancen ai ko ba komai yar uwarka ce."
Inna ta ce, "sosai ma kuma matarsa ba."
Haka Inna ta tasa su a gaba suka zauna a falo .
Salma ce kadai ke sambatunta Saheer kam takaici ya hanashi fadin komai.
Karshe sai wayo ya musu yace zaije ya dawo ya yi ficewarsa.
Washegari
Dady na dawowa daga sallar asuba ya shedawa Inna an daura auren Saheer da Salma kamar yadda ta bukata.
Inna ta ce, "Ma sha Allah Illu Allah yyi ma albarka ince dai wani gidan zasu tare ba nan ba ko? Suje can su ci amarcinsu ni zan zauna anan sai ta haihu sai inje can in mata wanka."
Dady ya ce, "In sha Allah yanzu ma zan kira Saheer din muyi magana."
Zuciyar Inna fara sol domin ta samu abunda take so.
★★Jiki a sanyaye Saheer yake durkushe gaban iyayen na shi.
Dady ya ce, "na san cewa an wuce zamanin auren dole, don haka ina so kasa aranka cewa kai ba auren dole aka yi ma ba, auren biyayya da kuma sadaukar ne, sannan ina so ka mai da Salma makaranta ku dinga tafiya tare domin tamkar ceto rayuwarta zaka yi ,a cire ta daga duhun jahilci da kuma abubuwan da take wanda sam basu kamata ba dole sai ka yi hakuri amman ka sani akwai ranar yin murmushi da farinciki mara misaltawa da ikon Allah don haka zan baka keyn wancen gidan zaku tare acen an gyara anyi komai yau da dare In sha Allah acen zaku kwana."
Saheer bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron iyayen nasa har suka gama yi masa nasiha ya yi godiya sannan ya tashi.
Tun yamma Inna ta daurewa Salma tsimmokaranta a tsimma suka zauna suna jiran Saheer yazo ya dauketa.
Harda kular dafaffen abinci.
Ba yadda ya iya kuwa hakan aka yi ta shiga mota.
Sai tabe tabe take tana yi masa sambatu shi kuwa aransa ji yake kamar ya jefar da ita ta windown.
Suna shiga gidan ya shige daki ya barta a falo ta baje kular abincinta ta fara naƙa sai da ta ci ta koshi bayan nan kuma ta bige da kallo.
Da taga ta fara jin barci ta bishi ciki.
Tana shiga ta tarar shi kam Saheer ya jima a duniyar barci daga shi sai singlet da gajeren wando.
Itama afkawa kan gadon tayi ta baje tana barci.
Tana daga kafarta sai cikin bakin shi.
Ga wani gwarti da take gabadaya ya mamaye dakin.
Baki a bude duk ta wage jikinta kan gadon.
Jin abun da ya yi a bakinsa yasa shi saurin bude ido......
08103080717
[6/29, 11:12 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*
PAGE-6
Cikin bacin rai Saheer ya hular da kafarta gefe ya tashi ya daka mata duka abaya.
A zabure ta farka tana, "wayyo wayyo Allah na."
Ya daka mata tsawa, "ke dalla yi mun shiru, ke wai baki da hankali ne? Haka ake kwanciya? Wai ma waya baki damar kwanciya mun akan gado ne?"
Sai da ta gama kare mishi kallo kafin ta Wage baki tana hamma tukun ta ce, "Mtsww aradun Allah ni na zata ma wani abun ne yake hwaruwa, gado kuma ai na mijina ne ko ance ma mata da miji na rabuwa ne? Inna ta ce a tare zamuna kwana kuma manne da juna ma kuwa muna shakar numfashi saboda yana kara dankon soyayya."
Ta fada tana komawa ta kwanta daf da shi.
Cikin zafin rai ya tureta gefe sai da ta fadi akan gadon.
Ta tashi tana, "Kambala'i ashe za ayi ruwan bala'i da masifa cikin daren nan tureni ka yi fa har na fadi? To da na gurde fa? hmm ka ci sa'a barci nake ji amman ka sani bashi ka ci kuma sai na rama babu fashi."
Ganin da gaske dai bazata bar gadon bane yasa Saheer daukan filo ya fita falo dake gidan karamine bed room dayane kadai.
Ita ma filon ta dauka ta bi bayan shi.
Yana kwanciya akan 3sita kawai ya ganta tsaye akanshi tana, "matsa mun to nima."
Kallonta ya yi ya kara kallon inda yake kwancen
A zuciyarsa ya ce, "ina ga dai wannan yarinya ta tabu." Ya rufe idonsa zai koma barci.
Jinta ya yi kawai ta kwanta akan shi kamar an jibga kayan wanki.
Ya hankadata ta fadi kasa ya tashi ya sake mata wani gigitaccen mari biyu ta kowanni bangare.
Ihu ta fara tana birgima.
Saheer ya ce, "ke wai wacce irin mayyace? To wallahi kika kara bina ko kika kara kuskura kika zo inda nake bare har ki taba jikina sai na baki mamaki."
Rike hannunta tayi afuskarta tana, "na shiga uku wayyo ni wayyo Allah na,kuma wallahi sai na fadawa Inna ka ce kai baza kana kwana dani akan gado ba wallahi sai na fada."
Saheer bai kara kulata ba har ta gama kukanta da sambatunta barci ya yi awun gaba da ita a falon.
Asuba na yi ya tashi zaije ya yi sallah ya ganta yashe baki a wangale ga gwarti ga yawon barci ga kafofi duk a wangale.
Tsaki ya yi ya wuce ta gefe yaje masallaci ya dawo .
Ruwan sanyi yaje ya dibo ya watsa mata domin bai son ko hannunshi ya tabata.
Aiko a firgice ta tashi.
Ya ce, "maza ki tashi kije kiyi sallah kiyi wanka ki shirya zamu fita tare muje School."
Da magagi take tana kokarin komawa amman tunda ta ji ya ce za su fita tare da sauri ta tashi tana washe baki tana , "To Miji... miji...mijinaaaa."
Tana cewa mijin nan wani takaici ne ya kara tokaran saheer a kirji.
Tsaki ya yi kawai ya nufi kitchen.
Indomie ya dafa masu da kanshi ya zuba mata sannan shi ma ya zuba na shi.
Ajiye mata ya yi,bayan tayi wanka tana sallah idonta na kan indomie tana yi mi shi gyaran murya.
Ko kallon inda take bai ba bare ya kulata aiko da sauri ta dungura sallar nan ta tashi ta fara nakar indomie.
Tana ci tana, "cab miji ashe ka iya girki, amman ko ni naji dadi ashe Inna ta iya zabe,ita tasan me ta hango tace sai munyi aure ji taliyar yaran nan kamar karta kare caii dadi iya dadi, aure dadi miji dadi."
Ta na magana Saheer ji yake kamar ya tura ta cikin rami ya boye.
Ta cinye tas sauran romon kuwa daga filet din ta yi tasa a baki ta shanye tas.
Ko wanke hannu bata yi ba taje ta zumbula wata katotuwar rigarta duk da cewar tana da jiki amman yawo take a cikin kayan.
Ya dauki hoda ta mulla ta kara kwaba farar hodar da ruwa tasa a bakinta.
Gaban Saheer ta tsaya tana, "miji kalleni na yi kyau?"
Daga kan da zaiyi sai da ya zabura domin ta koma kamar wata fatalwa.
Rai baci cikin daga murya ya ce, "common jeki goge wannan shirme da haukan naki baza ki bini da wannan haukar ba."
Da gudu taje ta wanke tana"cab yanzu haka kishi yake yi na yi kyau kar a kalle mai ni ,yoo da yaki fita dani ai gwanda inje in goge ,ysn kishi yake ya ga kyakkyawar mata."
Saboda ta riga ya gama caba fuskar raguwa dai hodar tayi amman da sauran fari farin.
Ta koma tana washe baki, "Mijin na goge."
Bai ce komai ba ya tashi.
Ita ma ta bi bayan shi.
Suna shiga motan sai ga kiran Dady ya na cemai su biyo ta gida kafin su wuce zai bashi sako.
Suna zuwa gidan Salma ta shige a guje ta rugume Inna.
Inna ta ce, "ke wai har kin gama amarcin ne ya haka?"
Sallamar Saheer ce ta katse su
Da yake duka Momy har Dadyn ma suna falon.
Dady ya ce, "e zasu je makaranta ne zata fara zuwa Inna kinga ba dadi abarta a gidan ita kadai."
Inna ta ce , "Ah eeh kuma kam hakane ya yi kyau."
Bayan duk sun gama gaisawa Dady ya bawa Saheer Files din da yace ma shi yazo ya karba.
Zai tashi kenan Salma ta ce, "Yawwa Inna ba kin ce gado daya zamuna kwana ba?"
Inna ta ce, "kwarai kuwa yo mene ne auren in ba kwana gado daya ba?"
Salma ta ce , "aradun Allah cewa ya yi wai shi bazai kwana dani ba har da tureni a kasa kuma wai ko jikinshi kar in kara tabawa."
Kuka Inna ta fashe da shi, "Oh Allah oh duniya yanzu Sahaaru abun da za ka mun kenan? Ka ce baza ku kwana gado daya ba? Sahaaru in baka kwana da matar ka ba dawa zaka kwana?bakin ciki kake mun da ganin yaran salame kafin in bar duniya? Sahaaru anya kana so ka ga Annabi kuwa? Wato da so kake ka ci bulus ka ci bati siddin anki an rufa ma asiri shine bari mu ka tona mana" Ta kara fashewa da kuka.
Dafe kai Dady ya yi,ya kalli Saheer ya ce, "Ka bawa Inna hakuri kuma daga yau kar ka kara cewa ba za kwana da matarka ba kar in kara jin abu makamancin wannan."
Saheer ya ce, "kiyi hakuri Inna in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba."
Share hawayen ta yi ta ce, "to too Allah yasa, ku tashi ku tafi."
★★Suna zuwa school din ta fara washe baki tana, "mijin nan ne makarantar da zaka sani?"
Wani gigitaccen kallo ya bita da shi da yasata yin shirun dole.
Office dinsa ya wuce da ita kai tsaye sannan ya kira wata teacher ya ce mata ta je ta mata interview kafin a bata class.
Rike mata hannu tayi suka fita suka shiga wani office din.
Ta mika mata takarda da biro ta ce, "Oya write ur name."
Kallonta salma ta yi da mamaki tana, "namai? Namai kuma?"
Teacher din ta yi murmushi ta ce, "Sorry rubuta mun sunanki."
S din ta fara rubutawa tana kallon gabas kafin ta rubuta a na kallon yamma l din kuwa tun daga kasa har sama aka rubuta anan ta tsaya.
Ta washe baki tana, "gashi nan malama."
Teacher Hafsat ta ce, "mene ne sunan naki?"
Salma ta kara washe baki kafin ta ce, "Salamatu amman Inna na ce mun salame amman yan garin nan gidan yan uwanmu ce mun suke salma."
Teacher Hafsat ta jinjina kai kafin ta ce, "to zaki iya rubuta mun Abcd yanzu?"
Salma ta girgiza kai, "cab aradun Allah ban iyawa duka na dai iya rerawa da waka duk."
Bayan Teacher ta gama yi mata tare suka koma office din Saheer ta ce, "Sir gaskiya akwai matsala bata iya abubuwa ba da dama infact ma zan iya cewa tana bukatar sabin darusa ne indai ana son karatunta ya tashi da sauri."
Saheer ya ce , "ok Teacher Hafsat amman me kike ganin ya dace a mata a yanzu?"
Teacher Hafsat ta ce, "ehto ina ganin akaita primary four amman kuma a bawa iyayenta shawarar ana mata lesson a gida domin zamanta a primary 1 to 3 zai iya durkusar da ita maimakon so da ake ta tashi tunda duk yarana kananu sosai, in akace sa'a kuma ta maida hankali ina ganin za a iya samun abun da ake so."
Saheer ya ce, "Ok to ki kaita class din yanzu sai kije ki duba ko za asamu uniform daidai nata da duk wasu materials ki hada ki kawo mun nan."
"Ok sir." Ta amsa kafin su suka fice.
Salma na shiga class kallon kallo take da yan ajin kusa da wani namiji da girman jikinsu ya kusan zuwa daya ta zauna.
Ya daga mata hannu.
Ta washe masa baki tana, "sunana salame kai fa."
Ya ce , "Habib."
Dariya ta yi ta ce, "Habibu."
Kwanciya tayi akan desk ta fara barci har sai da lokacin break ya yi Habib ya tabata.
Tana fita ta yi office din Saheer.
Cike yake da mutane ya yi baƙi ko a jikinta ta bankada ta shige tana, "Mijin an fita tara,ka bani kudin tara......
Free pages na daf da karewa In sha Allah
Saura two pages
500 ne kacal
8103080717
Aisha Abdullahi Sani
Opay
Or
1453215759
Aisha Abdullahi Sani
Access Bank
Evidence of payment to
08103080717
Luvs u all
[6/30, 10:38 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *°°°MATAR HEDIMASTA°°°*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
©️ *XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH*
PAGE-7
Saheer ya kau da kai kamar bai ji me take fada ba.
Ya ci gaba da yi musu bayani.
Karasawa gabansa ta yi ta ce, "Mijin na ce ma an fito tara ka bani kudi inje in siya abu nima in ci."
Ganin hankalin kowa agun ya koma kanta yasa shi yin gyaran murya ya ce, "Sorry guys she's our new student and she comes from villege,so she may not be familiar with our way of behavior."
Yana karasa maganar ya duba aljihunsa daga 500 sai 1000 , 500 din ya mika mata domin damuwarshi kawai ta fice daga office din ne a halin yanzu.
Aiko yana mika mata ta fisge da sauri ,ta juya zata tafi Coke din ta gani gaban bakin ta koma ta kallesu sai da suka hada ido kafin ta dauka ta zura aguje.
Sai da taje bakin kofar zata fita kafin ta juyo ta kallesu ta yi gwalo kafin ta ce, "in kana da karfi kazo ka kwata."
Ta arce a dari.
Dariya suka fara ban da Saheer da ya kulla.
Ya yi gyaran murya ya ci gaba da maganarsa.
Ita kuwa tana fita school shop din ta nufa inda ta ga yara na siyan abubuwa.
Tana zuwa ta mika kudin tana abani, "fanke."
Tsayawa kallon ta matar tayi domin ita bata fahimci me take fadi ba.
Da salma ta ga haka ta ja robar fanken ta ce, "ki bani wannan fanken guda uku."
Sai a lokacin ta gane ta zuba mata uku a leda sannan ta bata canjin dari biyu dake dari dari ne.
Salma na karba ta baje school compound .
Gabadaya ta wage jiki kamar an aje kayan dauda.
Ta sa bakinta ta bude coke din, ta fara cin fanken tana hadawa da coke din hankalinta kwance tana waƙa.
Sauran student din sai binta da kallo suke tamkar tv.
Wata ta zo wucewa tana kallonta.
Bakinta cike fal ta fara galla mata harara tana, "ke dilla ya da kallo? Na ci tuwon gidankune ban wanke kwano ba? To mijina ne ya bani kudin tara na siya ehee kwadayayya kawai." Ta kara galla mata harara.
Tsayawa yarinyar tayi tana mata kallon tara saura kwata ta ce, "villege girl."
Salma bata fahimta ba ta ci gaba da zakan coke da fankenta.
Sauran kawayen yarinyar ne suka hadu su biyar suna kallonta suna dariya suna fadin villege girl.
Daya a cikinsu ta ce, "She's not getting it, she only speaks hausa, so let's switch langauges."
Suka fara fadin, " 'Yar Kauye kawai , katuwar banza ji beta ta wani baje tana shan coke."
Salma na jin jawabansu ta tashi ta ajiye coke din da sauran fanken gefe ta cire karamin dankwalin dake kanta ta daura a ƙugunta ta ce, "ni kuke cewa yar kauye? Ni kuke cewa wawiya?"
Nunata da hannu suka yi suna dariya, "e din wawiya yar kauye ka....
Kafin su karasa rufe baki Salma tayi kansu gabadaya dukansu take ta ko ina ba ji ba gani gasu su biyar ita daya amman ta gagare su.
Da gudu sauran yaran dake gefe suka kira displine master din school din.
Aiko dakyar ya kwacesu a hannun salma.
Daga mai fasasshen baki sai masu kumburarren goshi duk ya yi ƙulu rudu rudu domin dukansu take ta ko ina harda wacce ta ciza kumatu.
Sai numfarfashi take tana fadin, "ba ku kun iya raini ba? Iye ku kun iya raini? Ance muku ni sa'ar kuce? Mijine dani e mijine dani."
Sai da displine master din ya zabga mata bulala kafin ta yi shiru tana cuno baki tana sosa baya.
Kamar bakin ya mutu sai kuma ta ci gaba da sambatu, "gaba kwa kuma waya ce muku ni ana kawo mun wargi wallahi zan balballa yarane gida saba in ba tara, ni ba sa'ar wasanku bace ko a kauye ma ni ba saar yara bace bare nan."
Kallonta displine master din ya yi ya ce, "After all this nonsense you've done, you should be ashamed to speak further. You ought to be more reflective,Oyaa get on your knees."
Kura masa ido ta yi tana kallonsa, kafin ta ce , "ni kuma? ni na yi me?