Share this page
10 / 10
rai yana cewa, "Ka ga ni dai bana san wani iyayi kawai ka bani magani." Murmushi Dactor ya yi yana cewa, "Gashi ma ko gaisawa bami ba , amma bari na kira nurse ummi taje ta raka ka a yi maka gwaji , shi kuma kunnen naka gaskiya sai ranar da dactor ya zo." Harun ya ce ,"Okay ." Likitan ya d'auki waya ya kira nurse sannan ya durkusa yana rubutu a cikin takarda lokaci guda kuma yana cewa, "Idan ka je a kai maka sai ka dawo mu yi hira kafin result din ya fito." Yana rufe baki Ummi tana turo kofa ta shigo Wani shegen kallo Harun ya zuba mata , sakamakon yadda ta shigo wani sindi-sindin da wani karamin hijabi Had'iye yawu ya yi yanayin shi duk ya canja Sa'id ya bata takardar yana cewa, "Ummi ki kai shi a dubashi bako na ne , idan result ya fito sai ki kawo min ." "Okay sir ." Shi ne abin data fad'a Tana fita Harun yabi bayanta , harda hard'ewa da tuntu'be yana tafiya , yadda ya ga ta ba shi baya tana tafiya yaji kamar ya yi abin da ya saba , domin ta matukar shiga ranshi a wannan yanayi Jitai an sa hannu ana shafa mata baya cikin wani salo , hakan ya sa taji wani yarrrr ta juyo cikin tsananin mamaki da tashin hankali Harun ta gani yana mata wani murmushi, hakan ya sake fusatata "Kutumar uba .Kai wanne irin d'an iska ne wawa shasha ." "Allah ya baki hakuri." Ya yi magana yana duban da hange karta tara masa mutane "Allah wadaran jahili irin ka , baza ka gama da duniya lafiya ba wallahi Allah ya isa. Wallahi ba da ban doctor Sa" id bane ya had'a ni da kai sai ka ga abin da zan maka ". Ta buga wani tsaki tare da harara ta cigaba da tafiya Ana yiwa Harun wannan gwaji ya koma wajen doctor kamar yadda ya ce " Sannu Harun ." In ji abokinshi "To ya kake ya kwanaki ai wallahi na yi zaton zaka dawo da kakin soji." Harun ya ce ,"Ina ta lafiyata ina wani maganar kakin sojoji , wallahi kunne na kamar , kaiii ina shan wahala dactor. " "To Allah ya sauwake yanzu ya ake ciki ne ."? Cewar dactor Sa'id Harun ya gyara zama yana cewa," Yawwa ni abin dake damuna ma wallahi Yahaya ne , domin na jima banajin shi , ga shi har na dawo an ce wai ya tafi legos. ". Ya karasa maganar cikin tsananin son jin Sa'id ya yi magna a kai Sa'id ya ce ," Allah sarki Yahaya , ai wallahi bamu da labarin shi tunda ya tafi legos, bamu san halin da yake ciki ba ." Cikin damuwa Harun ya ce ,"Gaskiya ya kamata mu san halin da yake ciki doctor. " Sa'id ya ce ,"Insha Allah zan sa a bincika mana legos din , domin akwai wani abokinshi Shu'ai bu." A lokacin Ummi ta shigo ta mikawa dactor result din Harun Yayin da ta zo fita ya sake 'kura mata idanu ta jefeshi da wata harara ta fita Bayan ya bude sakamakon ya tabbatar wa Harun yana d'auke da ciwon hanta Amma Harun bai damu ba , sai da doctor ya tabbatar masa ciwon hantarshi mai tsanani da muni ne , domin a kan mutuwa lokaci guda ko kuma hantar mutum ta dan'kare waje daya. Sannan ne hankalin Harun ya yi matukar tashin gaske , nan ya nemi matakan kula d kanshi da magunguna ,bayan ya koma gida ma dai jikin nashi ya sake matsawa sosai musamman ciwon kunnenshi da yake fitar da ruwa mai warin gaske , iyayenshi suna matukar iya yinsu domin samun lafiyarshi amma har yau Allah bai yadda ba . Haka anan cikin gidan yari Sahid rayuwa ta juya masa baya , ya matukar yin nadama yadda ya kula ba shi da wani gata , mahaifinshi babu , mahaifiyar shi bata tare dashi ga kuma wannan ciwon kafar da a halin yanzu zuwa anjuma za a yanketa , innalillahi wa innailaihir raji'un Baya jin dadin rayuwarshi ko kadan a halin yanzu. Allah ka yi mana da kyau A yanzu zainab da Mahmud ranar biki kawai ake jira , domin tuni an yi shiri tsaf dukkan family suna ta murna da wannan had'i . Haka farin ciki a gurin su baba anje , komai ya komai daidai ba su da wata damuwa , Umar yana tare dasu ga dukkan abin da ya taso musu , domin ya sadaukar da rayuwarshi ga Kalisa , sai dai muce Allah ya jikan wanda suka rasu , muma kuma Allah ya.... Matukar ciwo Harun yake ciki, yana tabbatar wa kanshi wannan yanayi da ya tsinta kanshi sa'bon Allah ne da ya ringa aikatawa, sai dai a halin yanzu Harun ya matukar shan jiki Wannan ciwon kunne , matukar wari, ruwa kuwa ba dare ba rana , sai ya tafi ya fara jin sauki sai komai ya sake lalacewa, ya ringa sunbatu ke nan har yake sanar da iyayensa irin abin da ya aikata a kano , ya ce musu alhaki ne ke bibiyarshi, su dena nemar masa magani . Sun matukar koka sosai dajin halin yaron nasu , sai dai dukkan inda aka ji mai magani ana nemawa Harun , amma har yau ba a dace ba , ko da ya tafi sai ciwon ya dawo , har da kanshi ya gane mutane gudunshi suke saboda wannan wari da yake cutar dasu. Babban abin da ya sake girgiza shi yadda doctor Sa'id ya tabbatar masa da mutuwar wulakancin da Uncle Yahaya ya yi abin ya sake d'aga masa hankali da jin tsoron duniya. Wata mata ce dumur mur da ita zaune a falo tana wasa da 'yarta wacce bata wuce shekara biyu ba Matar tana jin an kwankwaso kofar falon ta tashi ta bude Mijinta ne ya dawo daga wajen aiki , nan ta tarbeshi ya karaso ciki yana d'aukar 'yar tashi yana mata wasa Matar tashi ya kallah yana cewa, "Faiza wannan babyn tamu fa ta yi wayo , a gaskiya ya kamata a yi maka 'kani." Ohhhh ni ko na ce ashe faiza ce da mijinta , iko sai Allah Cikin wata kissa ta kalleshi tana amsar babyn ta aje ta gefe , kana ta rungumo mijin nata tana cewa, "Ai ni kai nake jira , duk sanda ka shirya." Yadda yaji yanayin ya masa dadi ya sa ya fara sunbatar Fa'iza , ita ko ta sake kankameshi tana....... Ooooooohh nan mata da miji ne , kowa ya basu guri , daman Fa'iza yaya a baya , bare yanzu me dalili . Ni ko na ce Alhamdulillah ala kulli halin , anan na kawo karshen wannan kaggagen labari mai suna GUBAR RAYUWATA⚡🎈 Abin da mukai daidai Allah ya amfana Abin da ya faru sakamakon karancin ilmi ina fatan Allah ya haskakan anan gaba Ni Fatima Abdallah kano (Autar marubuta) Ina mika godiya ga masoyana masu comments, like da kuma sharing Allah ya saka muku ya cika muradan ku. A kan haka nake muku albishir da sabon labari mai suna FATIMA DA ZARAH. Wanda ya samu tsarawa da shiryawa daga gareni . Anan zan barku tare da dukkan wani fatan alheri 🙏🙏🙏 07040805269 Autar marubuta An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10