gabansu , kawai Nabila ta fashe da kuka ta rungume Jafar
ita ma baba anje duk tausayin Umar ya rufe ta da ganin ciwon dake tare dashi
"Dan Allah yaya Umar ka je ka huta a halin yanzu kaji abin da doctor ya ce ."
Jafar ya yi maganar Nabila kwance a kirjinsa yana rike da hannun Umar.
Umar ya janye hannunshi tare da fara cewa ," Ni bana jin komai Jafar , yanzu kawai Kalisa ce damuwar , domin karku mance akwai bukatar yi mata aiki tun kafin wannan accident din."
Wasu zafafan hawaye suka zubo masa sannan ya ci gaba da cewa ,"Na ga karfe ya huda gwiwar Kalisa, na ji zafi a zuciyata kuma na bayar ta rasu , yanzu kawai lafiya zamu nema mata. "
Baba anje cikin tashin hankali ta ce "Gaskiya ne , innalillahi wa inna'ilaihir raji'un."
Dactor ya ce "Tom gaskiya ciwonta ni bazan iya dubata ba , ku jira kwana biyu likita yana zuwa." Yana gama maganar ya wuce
Ba zato sukaji Umar ya shako sa ,"Kai wanne mara hankali ne , har gobe zamu jira tana cikin wannan yanayin, ina imaninka da tausayinka ka je fa su."?
Likita da ya ji shakar sa ta yi yawa cikin wahala ya fisge ya hankade Umar "Kai mahaukacin ina ne , bari na kira security su fitar da kai." Dactor din ya karasa maganar ya nufi wajen masu gadi
Umar ya ce , "Mu dauki Kalisa mu koma babban asubitin dactor Aisha hakan zai fi."
Nabila ta yi ajiyar zuciya tana kiran sunan Allah .
Mahmud ne ya fito waje yana duban yanayin anguwar yadda tsarinta kullum yake sake burgeshi , duba ga manyan gidaje da sanyin anguwar
hakan ya sa har yau ya kasa komawa gida, har Aminu ya koma , amma shi ba shi da niyya , amma babban dalilin 'kin komawarsa a kan Zainab ne .
Sake bude idanunshi ya yi yana sake kallon abin da ya hango daga gefe ,
kofar gidan wani mutum malam na lado , wanda har almajirai yana dasu
Mahmud ido ya sake zubawa yana kallon ikon Allah
"Mene Harun yake yi anan".
Mahmud ya tambayi kanshi .
Daga bisani lokacin da Harun ya kula da Mahmud ya yi murmushi ya nufo wajensa.
" Malam Mahmud me ake kuma anan." Harun ya tambaya lokacin da ya karaso gaban shi
Mahmud zuciyarshi wata irin tafasa take masa kamar ya kai masa duka, amma ya daure ya kalle shi yana cewa "Mene ka zo yi a wannan anguwar."?
Harun ya sheke da dariya har da tafawa , sannan ya ce ," Mahmud ni wallahi ma dariya kake bani , to mene ya dameka dani, sannan kuma kar ka yi zaton na bar Zainab, Wallahi ban bar ta ba , kai ne kamin shamaki da ita , amma wallahi kasa a ranka da zarar na zama soja wallahi sai na kawar da kai dan na samu Zainab, ka rubuta ka aji ye ni Harun ni ne ajalinka. "
Ajiyar zuciya Mahmud ya yi yana cewa, " Mu yi mu gani , kar kai tunanin dan ka 'bata Asma'u na ya zamo ina jin tsoron ka......."
Mahmud bai karasa maganar ba Harun ya dakatar dashi da cewa ,"Zan yi wulakanci idan nasa kaki , wallahi Mahmud sai na wulakantaka, zaka gani."
Ya wuce ya yi tafiyarsa
Ran Mahmud ya matukar baci sosai , gida ya shiga cikin bacin rai , ya shiga cikin lambu ya kasa tsaye ya kasa zaune , kawai maganar Harun ce take masa yawo , cikin ranshi yake sake nanata zancen
"Tabbas Harun azzalumi ne , zai aikata duk abin da yake so, yanzu mene mafita."?
Mahmud ya dafa kanshi da ya farai masa ciwo " To ko dai na shigar dashi kara. "?
Ya tambayi kanshi , tare da bada amsa kuma
" Gaskiya 'a'a wannan ba shawara ba ce ."
Ya tsuguna kamar mai shirin yin kuka , sannan ya tashi tsaye yana kallon sararin sama yana ajiyar zuciya.
Da sauri ya dawo da kanshi kasa tare da rudewa da farin cikin shawarar da ta zo masa,
da sauri ya shiga cikin gidan ya wuce d'akinshi ya dauko wayarshi dake caji ya zauna a bakin gado .
Sannan ya fara danna wayar yana cewa, "Hhh kwananka ya kare Harun." A daidai lokacin yana kiran numbar Hauwa 'yar gidan lu'utanal
Kamar jira take karaf ta dauki kiran "Ya Mahmud manyan gari kwana biyu." Ta yi maganar cikin yaren turanci
Murmushi Mahmud ya farayi sannan ya ce "Ke dai bari Hauwa ai kasar ta ku ce , wallahi ina cikin tashin hankali."
"Subhanallahi yayana meke damunka." Hauwa tai maganar cikin tsantsar kulawa
Nan take Mahmud ya fara zuba kai tsaye "Wallahi Hauwa Harun ba shi da imani mazunaci ne yadda kika san ba dan halak ba , azzalumi ne , mata yake lalatawa ke har HIV yana d ita ."
Jin ya yi shiru ne ya sa ta kwashe da dariya 😂
"Au dariya zaki mini." Ya yi maganar cikin haushi
Hauwa cikin dariya ta ce ,"Yi hakuri, nasan daga ji haushin sa kake ji , domin nasan da yana kusa da kai sai Allah. To amma ni mene nawa a ciki."
Mahmud ya sanar mata da komai tun daga waye Harun , har zuwa yau din nan , tare da neman alfarma ta sanar d mahaifin ta Lu'utanan
nan Hauwa ita ma ranta ya baci ta kashe waya ta fita falo
Mahaifiyarta Hajjiya Bilkisu na zaune ta fad'a jikinta ta kamata .
"To mene kuma ko sirikin nawa ne." Hajjiyan ta fad'a
Hauwa ta tashi ta bata rai tana cewa "Momy wani ne ..."
Lu"utanan Sadik ya shigo ya tari numfashinta yana cewa "Ya taba ki ko me? fad'a min mamana."
"Dady a cikin sojojin da zaku diba akwai Haruna Sani mu'a zu , irin wannan d'auri ne ya dace dasu." Ta karasa maganar cikin kwalla
Hakan ya sa Lu'utanal hankalinsa ya tashi "Manana waye ne shi mene ya miki."
Nan ta fad'a masa waye Harun kuma da kalar barnar da yake da kuma wacce zai idan ya samu aikin soja .
Nan ita ma Hajjiya Bilkisu tai Allah wadai dashi
yayin da Lu'utanal Sadiq Muhammad ya tabbatar wa Hauwa za ai bincike a kan shi .
"Yawwa dady ina so zanje gidansu Surayya, domin tun da ta dawo daga America bamu had'u ba."
"Okay gidan ambassador koh."? Lu'utanal ya tambaya.
" Eh can dady."
"To ki bari idan na samu lokaci sai mu je tare."
Hauwa ta ce ,"Okay dady."
.A halin yanzu Kalisa ta dawo hayyacinta , doctor Aisha tana iya yinta domin samawa Kalisa lafiya , sai dai ta tabbatar musu fitar da ita ne kawai mafita .
Jafar har gida ya je neman Sahid sai dai tun jiya mahaifinsa ya tabbatar ba ya nan , sannan dukkan SMS din sa basa tafiya .
Ran malam Aminu ya yi matukar baci sosai dana mahaifiyarsa, musamman jin halin da Kalisa ke ciki ma ya tabbatar musu gobe zai zo garin ya ga jikin nata , kuma zai nemo Sahid din in sha Allah, Jafar jikinsa duk ba dadi ya koma asubitin.
Shugaban makaranta ne da Uncle Yahaya da bayis tare da wasu malamai biyu zaune a falonsu Laila.
Gefe guda kuma ga Laila da mahaifiyarta zaune ,ga kuma barrister Adam ran shi bace .
"Dan Allah barrister Adam ka duba wannan lamarin, mun yi kuskure sosai wanda a tarihin DR.DD ba a taba irin sa ba , amma a matsayin mu na masu ilmi mu yi sulhu dan Allah barrister." Shugaban makarantar ya aje maganar cikin tausayin kanshi .
Amma barrister Adam kamar sun sake fama masa ciwo haka ya fara magana.
"A she kuna da ilmin kuka aikata hakan , ni fa na gama magana kawai ku je ku nemi lauyan da zai tsaya muku , dan haka ku fitar mini a gida kawai."
Idanun shugaban makarantar ya ciko da ruwa ya kalli barrister yana cewa, "Wannan makaranta ita ce cigabana rufin asirina wallahi sunan ta zai baci barrister ka taimake ni."
Barrister tsaye ya tashi yana cewa "Ciwon zuciya ne ya sameta yanzu a kan ku , ta ya zan share wannan lamarin kamar ba kaunar ta nake ba ko ina jin tsoron ku."
Uncle Yahaya ya yi kasa da kai cikin jin haushin kansa.
Laila kuwa ganin yadda shugaban nasu Doctor Dauda ya shiga wani yanayi ya sa taji duk tausayinshi ya kamata, cikin sanyin murya Laila ta ce ,"Dady."!
Barrister Adam ya kalleta yayin da duk kowa ya maida hankali gare ta .
"Ni ce aka yi wa komai dady amma abin kai ne ya shafa , bani da wani farin ciki sama da kai, hakan ya sa wannan ciwon dole ya barni tun da ina tare da kai."
Tai ajiyar zuciya tana sake cewa "Ina matukar girmama shugaba kuma wannan tarbiyar ku ce
Duk abin da ya faru da kai wanda ba za ka taba mancewa dashi ba kuma idan ka tuna kanajin ciwonsa to wannan shi ne Gubar Rayuwarka."
Ta aje maganar tana kallon uncle Yahaya ,yayin da ya yi kasa da kanshi .
Mahaifinta ta kalla barrister Adam tana cewa "Dady dacter ba shi da laifi dan Allah ka janye karar."
Kowa ya kalleta cikin mamaki tare da sa'ke-sa'ke kala-kala da kowa ya ke yi a ransa.
Cikin wani Murmushin ta kaici barrister Adam ya ce "Babu ruwanki Laila wannan maganar kar na sake jinta a bakin ki , dole ne na dauki mataki, shin ko baki san wanne kalar jiwo suka jawo miki ba ne , ke ce kawai Allah ya bani kuma duk wanda ya yi kuskure irin wannan dole hankali na ya tashi idan ban dauki mataki ba Laila."
Cikin hawaye Laila ta tashi tsaye tana kallon barrister da dukkan girmamawa ta fara magana.
"Dady ni kaina nasan kana kaunata ,
amma wannan shi ne Gubar Rayuwata domin ba zan taba mancewa ba amma dan Allah dady ka janye karar."
Ta karasa maganar yayin da wasu hawaye suka zubo mata.
Hakan ya sa barrister Adam ya kalli Uncle Yahaya yana cewa .
Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><>
Page 23 & 24
"Laila ina kaunar ta." Ya fad'awa Yahaya
sannan ya kalli doctor ya ce "Na janye karar tare da sharadin matukar Laila ta mutu sanadin wannan ciwon to akwai babban tashin hankali."
"Babu abin da zai samu Laila in sha Allah barrister, sannan na yi alkawarin duk in da magani yake zan ke nema mata har ta sami lafiya."
Shugaban ya yi maganar cikin tashin hankali da rawar murya
"Lafiya ta Allah ce kuma ni zan cigaba da nema mata magani , dan haka zaku iya tafiya nasan kun bar d'alubai a makaranta."
Barrister Adam yana gama maganar ya shige ciki .
Sannan suka yi sallama da Hajjiya da Laila suka fito
DR Dauda cikin fusata ya fito ranshi matukar bace suka dauki hanyar makaranta, babu wanda ya ce da kowa komai har suka isa makarantar
Suna shiga shugaba ya sa a fito assembly hakan ya sa wasu malaman mamaki da tunani
Bayan kowa ya fito suma malaman suka hallara
Kowa yana iya ganin 'bacin rai da damuwa a fuskar dactor,
Bai jira wani gabatar da abin da aka saba ba ya fara magana
"Wato duk kun debi zancen Laila kun yada a gari ta fadi ta kamu da ciwo , shi ke nan
ina jan kunnenku da duk yarinyar da wani malami ya ce yana sonta suka fara soyayya zamu dauki mummunan mataki wallahi a kan su."
Ya kalli Uncle Yahaya sannan ya ce " Daga yau mun sallami Yahaya a wannan makaranta, babu wanda zaike kawo mana farmaki ba mu dakatar dashi ba , idan kunne yaji ."
'Dalubai suka karasa masa maganar cikin murya mai karfi
Wani abu ne ya tirnike zuciyar uncle Yahaya da abin da shugaba ya yi masa .
Hakan ya sa bayan ya koma office ya je ya same shi
"Shugaba sallama ta fa kayi gaban d'alubai." Uncle Yahaya ya yi maganar cikin maraici
haka shi ma shugaba ya fara magana "Hukuncin da zan maka ke nan domin haka ne ya dace da kai , kuma kaji ka sani ko albashi ba zan biyaka ba , zan yi amfani dashi na gyara 'barnar da kamin cikin makaranta, fitar mini a office."
Uncle Yahaya ya fita cikin damuwa ya nufi gida .
koda yaje gidan ya ga ya masa duhu kakarshi ta bar masa duniya , babu wani hanyar samun kud'i da yake dashi yanzu, bare ya nemi matan da ya saba , duk yaji duniya ta masa zafi sosai .
Yana cikin wannan yanayin ne sai ga kiran Fa'iza ya shigo masa , ba tare da ya boye yanayin da yake ciki ba ya fara magana da ita .
Da baba anje da Nabila ne zaune a d'akin Kalisa dake asubiti,
a wannan lokacin ne baba ta kàlli Kalisa tana cewa "Yau dai Kalisa na ga jikin naki da sauki Allah ya dorar dashi."
Kalisa cikin zuciyar ta ta ayyana cewa "Kawai dauriya nake baba , amma Allah ne yasan abin da nake ji."
Nabila ce ta ce "Amma aunty Kalisa cikin ba ya ciwo ko."?
Kalisa tai murmushi kawai
Umar da Jafar ne suka shigo a lokacin tare da sallama
" Ina kuka shiga ne haka tun safe."?
Baba anje ta fad'a bayan ta amsa sallamar
Umar ne ya fara magana yana kallon Kalisa cikin kauns
"Tun da har yau babu labarin Sahid a kan me zamu zauna to baba , mun fita neman kud'in da za a mata aiki , kuma a halin yanzu mun sami dubu dari biyar ."
Nabila ce ta ce "To yaya Jafar me zai hana mu siyar da gidan da muke ciki."
Jafar yayi ajiyar zuciya tare da cewa "Nabila komai fa yana hannun wannan azzalumin babu takardun gidan ."
Umar ya yi ajiyar zuciya
Kalisa ce cikin wata muryar tsananin wahala ta ce "Akwai takardun wani gidan momy da dady ya bata , nasan zamu sami kudaden da zasu isa idan aka siyar."
"Alhamdulillah Allah mun gode maka." Baba ta yi maganar
Jafar ya ce aiko ba wasa za a yi ba yau za a siyar dashi in sha Allah komai zai tafi daidai."
Umar ya ce "In sha Allah kuwa."
Kalisa ta kira Umar kusa da ita cikin kasa da murya ta ce "Ina matukar kaunar ka."
Koda yaji hakan sai ya ja da baya cikin tausayi da wasu hawaye a cikin idanunsa
Sannan ya dago ya kalleta ya ce "Ni ma ina kaunar ki Kalisa zaki samu lafiya in sha Allah."
Baba anje ta ce "Allah kai ne abin godiya, ka bawa Kalisa lafiya."
Nabila ta amsa da "Amenn." tare da sake cewa "A gaskiya ya kamata a sanar da baba Garba duk ba su san abin dake faruwa ba."
Baba anje ta ce "Gaskiya ne za a sanar dasu."
Sallama da aka yi ne ya sa duk hankulansu ya koma kan kofar
Mahaifan Sahid ne suka shigo
nan aka basu wajen zama zamansu ke nan Kalisa ta fara shure- shure
hakan ya tayar da hankalin kowa saida aka kira dactor Aisha
bayan ta zo ta mata abin da ya dace har ta samu bacci .
Cikin tashin hankali malam Aminu yake tambayar dactor "Yarinya meke damunta haka."
"Baba tana dauke da mummunan ciwo a cikinta, kuma kullum tsanani yake karawa , sannan da fari kasar waje za a kaita , amma a halin yanzu an sami asubitin da za mata aikin , kud'in ne ba su samu ba , kuma ni gaskiya babu abin da zan iya mata kawai aiki take bukata , sannan a gwajin da mukai dalilin accident din nan karfen da ya tsagata ta sami cancer., Amma in sha Allah da zarar an mata aiki komai mai wucewa ne ."
Bayan ta gama ta musu sallama ta fita
Malam Aminu ya ce "In sha Allah."
Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa da Jafar "Mu je a nemi dillalai wannan ba abin zama ba ne Jafar."
Jafar ya ce "To yaya Umar."
Ya tashi cikin kasala da matukar damuwar da yake ciki .
Kafin su kai ga hanyar fita wani saurayi ya shigo cikin d'akin tare da sallama, nan take malam Aminu ya shaida shi ya caf ki sunan shi
"Sani."
Saurayin ya amsa tare da gashshe shi , sannan ya kalli Jafar yana cewa "Don Allah ka yi hakuri tun shekaran jiya MD Sahid ya bani sako a company amma ban kawo ba na mance ."
Ya Ka rasa maganar yana ciro wata takarda da aka sata a gidan sirri ya ba shi .
Ya musu sallama ya fita, kowa mamaki ne ya rufe shi har Kalisa da ba komai take iya ganewa ba.
Bayan ya bud'e takardar ya karanta a zuciyar shi , bayan ya gama ya yi shiru , yayin da ya barsu cikin tashin hankali dalili kuwa sun ga tashin hankali a tare dashi .
Mahaifiyar Sahid ce ta bude baki tana cewa dashi "Yaro mene a ciki me ya aiko haka."
Jafar ya kalli Kalisa cikin tsananin tashin hankali
Yadda Umar abin ya yi masa ciwo kawai ya karbi takardar ya fara karantawa shima a zuciyar sa
Bayan ya gama irin yanayin da ya shiga har yafi na Jafar
"Haba dan Allah wai mene wannan yaron ya rubuto kun yi mana shiru." Cewar mahaifiyar Sahid
Baba anje ta karbi takardar ta bawa Nabila.
"Nabila dan Allah karanta mana sun bar mu a duhu." Baba ta yi maganar cikin damuwa
Idanunta fal da hawaye ta karbi takardar cikin rawar jiki
muryarta na rawa ta fara da cewa "Assalamu alaikum.
Kalisa ku yi hakuri amma a halin yanzu babu wani kud'i da zaku samu duk da naku ne , ba zan baku komai ba balle ku fita kasar waje, a halin yanzu nayi biza ina birtàniya kuma ina da hakki cikin dukiyar Alaji Idris don haka na tafi na ci nawa .Sai wata rana."
Cikin mummunan yanayi Nabila ta aje karatun tare da tashin hankali
"Na yi asarar haihuwa , Sahid mutumin banza ne wallahi, Allah wadaran ka." Mahaifinsa ya yi maganar cikin kuka
lokaci guda kuma ya fad'i kasa
Hankalin matarshi ya tashi , hakan ya sa duk su Umar suka yo kanshi , da gudu Nabila ta fita kiran likita tana zuwa wajen doctor Aisha ta turo wasu nurse zuwa wajen shi .
Bayan sun kanshi daki cikin hanzari ita ma dactor ta shigo dakin domin taimakon gaggawa .
Zuuuu duk suka fita Nabila da Kalisa aka bari a dakin .
Lamarin yana dukansu , a can daga waje kuwa mahaifiyar Sahid kuka take tana cewa, "Wallahi shi ke nan malam mutuwa zai , zuciyar shi ta buga , yaron nan duk irin hidimar da Alaji Idris ya mana bai gani ba , Allah wadaranka Sahid, ka yi asara ka kashe mahaifin ka , wallahi ba zan yafe maka ba."
Baba anje ce ta fara bata hakuri cikin rarrashi "Ki yi hakuri , ba mutuwa zai ba , babu abin da zai same shi ."
Ta fusge jikinta a jikin baba anje tana cewa "Ni nasan halin malam wallahi, shi ke nan malam sai mun taho." Tana gigicewa da kuka
Ran Umar da Jafar duk ba dadi , Allah ne yasan ciwon dake ransu .
Dactor Aisha tana nuna kwarewa , yayin da tai saurin masa abin da yake bukata hakan ya tabbatar mata yana da rai .
Yayin da daya a cikin nurse din ke shiran sa masa ruwa ne , ya fara fisge fisge sai aman jini.
Nan doctor Aisha ta dawo kanshi .
Anan waje kuka kawai matarshi take , cikin kukan ta kira yayan Sahid take fad'a masa malam Aminu ya mutu, cikin tashin hankali ya fanno asubitin.
Zama ta yi dirshen tana ta kukanta , har baba ta gaji da rarrashi .
Sannan sai doctor Aisha ta fito tare da nurse din .
"Ba sai kin fad'a mini ba nasan ya mutu 😭 jeki abin ki." Matarshi ta yi maganar cikin kuka
"Likita ya ake ciki ya jikin nashi ."?
Jafar ya tambaya yayin dasu baba duk suke jiran amsa
likita Aisha ta fara magana" Ku yi hakuri Jafar , mun yi iya yin mu dan cetar ransa , amma Allah ya amshi abinsa."
Dauuuuu suka ji zuciyoyinsu na wani dukan dubu dubu na tsantsar tashin hankali.
Aisha suka wuce suka basu guri .
"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un.Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un"
Baba anje ta fada cikin tashin hankali, su Umar duk sun kasa cewa komai
Ba a dade ba danta Jibrin ya karaso asubitin, shi ma , aiko su Jafar cikin wannan tashin hankali suka bisu kauye har saida aka shiryashi aka sallace shi sannan da aka kaishi suka dawo wajen dare.
Allah ya sa mu dace
Share and comment..........................,..📚
Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano