Duk da yanda mutane suka rufe shi, hakan besa hankalin shi ya bar kan ammien shi ba, agogo yake ta kalla yana jiran me gidan nashi yazo ya karɓe shi, dan lokacin tafiyar shi gida yayi.
Tsaki yake taja yana duba lokaci, gaba ɗaya sai da ranshi gama ɓaci sannan yazo.
"Kayi hakuri ashraff naɗan tsaya yin abu ne"
Bece masa komai ba ya fito, yayi gaba ko sallamar shi be karɓa ba.
Kanshi kawai ya girgiza idan da sabo ya riga ya saba da halin abokin aikin nashi.
Da sallama ya shiga gidan, ɗakin ta ya shiga.
"Ammie na gani na dawo, kiyi hakuri oga nane be dawo da wuri ba"
Matsawa kusa da ita yayi yaga ta ɓata wajen da take, ruwan zafi yaje dafa, babu kyankyami haka ya gyara wajen data ɓata da jikin ta, turaren tsinke ya kunna take kuwa ɗakin ya fara kamshi.
★★★★★
"Zaki faɗa min kukan me kike ko kuma sena mugun ɓata miki rai"
Cikin muryar kuka ta fara magana tana ɗaga murya tamkar tana magana da sa'ar ta ba mahaifiyar ta ba.
"Mom ashraff dad yace ze aura min shi, amman har yanzu shiru, yau a ƙalla shekara nawa dayi min wannan alƙawarin amman shiru, meyasa zemin alƙawarin daba ze cika min ba? Koni ma ƙaryar daya sabawa mutane zeyi min? Baze yuyu ba wallahi mom dole na auri ashraff"
Gaba ɗaya ta har gitse duk abinda yazo bakin ta furta shi take ba tare da ta tauna ba.
Ji take tamkar ta tashi ta rufe ta da duka, amman tasan dukan ta shine mafi munin kuskure da zata aikata, a gidan dan baban ta baze dubi cewar ita ta haife ta ba, tsaff zeyi mata hauka, dole tayi mata banza.
Ganin ba ƙara kula ta zatayi ba ne yasa ta wuce sama a guje tana kuka.
Murɗa handle ɗin tayi da karfin ta shige ciki.
Zama tayi tana kuka tana me ci gaba da cin alwashi akan sai ta auri ashraff koda kuwa meze faruwa......
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
BY
RABI'ATU KABIR ACHADU
(FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)
A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina❤️💫
SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY🤍
Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏
FULANI🤍
08082101373
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
PAGE 4
Gaba ɗaya jikin ta yayi sanyi, dan bata ƙaunar abinda ze sa akhien ta yayi fushi da ita.
Koda abhi ya dawo da sauri ta tarbe shi, tana ɗora kanta a kafadar shi, "abhi nayi kewan ka sosai"
"Nima nayi kewan ki auta na"
Ɗakin shi ya wuce yaje yayi wanka, sallah suka fita shida farooq, ganin ko kallon ta beba yasa jikin ta ƙara yin sanyi.
Alwala taje tayi, sallah tayi ta sakko ƙasa, ta riga kowa zama a dianing.
Koda suka dawo daga masallaci suma duk wajen suka yo suka zauna.
Miemie ce ta sakko tana ta baza ƙamshi, sosai tayi kyau cikin kwalliyar tata bazaka taɓa cewa itace ta haifi umar ba.
Murmushin ya sakar mata.
Itama mayar mishi tayi tana zama a kujerar datake fuskantar shi.
Ayraah ce ta tashi tayi saving kowa sannan ta koma ta zauna.
Gaba ɗaya ta kasa cin abincin sai jujjuya shi take yi.
"Meyafaru auta na, naga kin kasa cin abincin"
"Bakomai abhie kawai na ƙoshi ne"
Be matsa mata ba dan daman sun san abincin ba wani damun ta yayi ba.
Kan kujera ta koma ta zauna.
Game take a wayar ta, hankalin ta amman ba akan game ɗin yake ba yana kan akhien ta.
Koda yazo wuce ta yayi ba tare da yace mata komai.
Tashi tayi tabi bayan shi.
Duk da yaji takun ta be juyo ba yaci gaba da tafiyar shi.
"Akhie! Akhie!!"
Jin yanda muryar ta take rawa ne yasa shi juyo wa yana kallon ta.
Kunnen ta riƙe duka biyun idon ta taff hawaye tace "ayya akhie kayi hakuri in sha Allah bazan kuma"
Murmushi yayi yaja hancin ta.
" Ka haƙura akhie?"
"Daman ina fushi dake ne princess nima ramawa nayi ai"
Dariya tayi beauty point ɗin ta ya lotsa sosai dake ɓarin fuskar ta na hagu.
hannun ta yaja suka koma kan dianing ɗin, abinci ya zuba mata yana bata a baki da kanshi.
Iyayen nasu murmushi kawai suke suna kallon su.
Sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya raka ta ɗakin ta ya sakko.
Sallama yayi musu ya shige ɗakin shi ya kwanta.
Har ta kwanta ta ɗakko littafin ta da kayan zane.
Ganin kayan kawai farin ciki suke sata, zane burin tane, tun tanayi ana hana ta har ta kai ta kawo yanzu da kan su suke kawo mata kayan zanen.
Tana zanen tana sakin murmushi, bata ɗau dogon lokaci tana yi ba, ta gama kallon hoton take tana sakin murmushi.
Akhie ne a jiki da ita yana bata abinci a baki.
Wayar ta ta ɗakko tayi hoton zanen, a status ta ɗora da rubutu a ƙasa.
"My world best"
Addu'ar bacci tayi ta kwanta, bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta.
★★★★★
Sai da ya tabbatar ya bawa ammien shi abincin ta, sannan yaje yayi wanka da alwala ya kwanta, be daɗe ba bacci ya ɗauke shi.
Kiran sallar asubar farko ya tashi, ɗakin ammien shi ya shiga.
Itama idon ta biyu, ɗagota yayi ya gyara mata jikin ta tare da alwala.
Komar da ita yayi, ya fice masallaci.
Ana idar da sallar, ya taso ya nufo gidan, dan haka kawai yake jin gaban shi na faɗuwa tun da ya baro gidan.
Da gudu ya shiga jin yanda yake jin kakarin amai na tashi daga ɗakin da ammie take.
Ko kafin yaje har ta faɗo daga kan katifar datake.
Ɗagota yayi jikin shi yana kiran sunan ta, sai dai abinda ya gani ne ya ɗaga mishi hankali harya nemi fita hayyacin shi, gaba ɗaya jikin shi karkarwa yake.........
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
BY
RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)
A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina❤️💫
SADAUKAR WA GA ACHADU'S FAMILY🤍
Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏
FULANI🤍
08082101373
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
PAGE 5
Sosai jikin shi yake rawa ganin yanda take aman jini ta hanci ta baki.
Ya rasa abinda ya kamata yayi ɗagota yayi ya ɗora a jikin shi tana ci gaba da aman, gaba ɗaya ta ɓata shi amman ko kaɗan hakan be dame shi ba.
Cikin rawar murya ya fara kiran sunan ta
"Ammie karki tafi ki barni dan Allah ke kaɗai gare ni"
Sosai yake jijjigata yana kiran sunan ta.
Kaman wanda aka mintsina haka ya miƙe ya saɓeta a kafaɗar shi yayi waje cikin sassarfa.
Babu kowa unguwar tsitt, saboda ba'a daɗe da idar da sallar asuba ba, a haka ya nufi titi da ita ko takalmi babu a ƙafar shi.
Jefa ƙafar shi yake yana addu'a a ranshi Allah yasa ya samu abin hawa da wuri.
Be daɗe ba ya samu cikin sauri ya shigar da ita shima ya shiga ya zauna.
Ganin yanayin su ne yasa yaja napep ɗin.
"Bawan Allah wane asibiti zan kaiku?"
"Aminu Kano"
Daga haka be ƙara magana ba, gaba ɗaya hankalin shi, yana kan fuskar ammien nashi da zuwa yanzu ma kaman bata numfashi.
Har cikin asibitin ya shigar dasu, ze bashi kuɗi yace ya bar shi Allah ya bata lafiya.
Kai tsaye emergency ya nufa da ita a kafaɗar shi.
Da sauri nurses suka karɓe ta, suka shiga da ita.
Gaba ɗaya ya kasa tsaye ya kasa zaune zagaye kawai yake a wajen yana addu'a.
★★★★★
Tun da tayi sallar asuba bata koma bacci ba, kitchen ta sakko ta haɗa musu break fast, tana gama wa ta jere a dianing ta koma ɗakin ta.
Wanka tayi ta shirya cikin riga da wando ta ɗora doguwar riga a sama, batayi kwalliya ba, kwalli kawai ta saka idon ta sai white lipstick, glass ta ɗakko ta saka.
Saida taga fuskar tata tayi mata yanda take so, sannan ta nufo ƙasan mayafin ta da jakar ta a hannu.
Ganin babu wanda ya sakko a cikin su ne, yasa ta nufi ɗakin akhie.
Knocking tayi mishi ya bata izinin shiga sannan ta shiga da sallama.
Murmushi ya mata.
"Morning pretty"
"Morning akhie ka tashi lafiya?"
"Alhamdullah har kin shirya?"
"Muna da lecture 9"
Dariya yayi yana kallon ta ganin yanda tayi da fuskar ta.
Tashi yayi ya nufi wardrobe ɗin shi tana tsaye ya dawo ya miƙa mata kuɗi.
Tsalle tayi ta maƙalƙale shi tana masa godiya.
Zare ta yayi daga jikin shi yace a sauka lafiya.
Da sauri kam ta bar ɗakin tana jin daɗi a ranta.
Dianing ta nufa ta haɗa tea a tsaye ta sha.
Sama ta koma tayi knocking ɗakin miemie, izinin shiga aka bata ta shiga da sallama.
Har ƙasa ta tsugunna ta gaida iyayen nata.
"Kin shirya auta?"
"Eh abhie"
Kuɗi ya ɗebo me yawa ya miƙa mata, godiya tayi mishi tayi musu sallama ta fita.
Ɗakin ta ta koma ta gyara fuskar ta tayi rolling, sannan ta fito.
Cikin takun nutsuwar ta ta fito harabar gidan.
Driver yana hango ta ya taso da sauri.
Yana shirin gaishe ta ta tari numfashin shi.
"Barka da safiya baba katashi lafiya"
"Alhamdullah madam"
Ze buɗe mata ƙofa tace ya barshi, ita har ranta bata son hakan, a haife ya haife ta duk seya sa tana jin kunyar shi.
Har suka je makarantar ba wanda ya ƙara magana acikin su.
Yana parking tayi masa sallama ta faɗa masa lokacin da zezo ɗaukar ta.
A yanda take tafiya bazaka taɓa cewa tana magana bare tsokana, komai nata cikin nutsuwa take yin shi.
Waje ta samu ta zauna batare data kula kowa a wajen ba.
Duka bata fi sati biyu a makarantar ba, toh bata gama sanin kan makarantar ba, kuma ita shiga mutane ba damuwar ta yayi ba ita dai barta da akhien ta da miemie se abhie.
Malamin da zeyi musu lecture ne ya shigo, hakan yasa ta mayar da hankalin ta gaba ɗaya kan shi.
Suna cikin lecture ɗin ta shigo, fuskar ta sanye da facemask, malamin ta gaisar, ta shigo cikin ajin sosai, sit ɗin da take zaune tazo ta zauna.
Kallo ɗaya ayraah tayi mata ta ɗauke kanta, itama batace mata komai ta mayar da hankalin ta, kan malamin.
Koda malamin ya fita
babu wadda ta kula wata a cikin su.
Waje ta fito ta samu waje ta zauna, Akhie ta kira a waya tana ringing be ɗaga ba, sosai ta zumɓuro bakin ta gaba tamkar yana gaban ta.
Game ta shiga tana cikin yi ya kira ta.
Cike da shagwaɓa ta fara masa magana kaman zatayi kuka.
"Akhie yunwa zata halaka maka ni"
"Kije capteria kici abinci mana"
"Uhm uhm akhie ni cornflask nake so na sha"
Tsaki yaja ya kashe wayar shi.
Maida wayar tayi ta
ajiye.
Jin kaman ana kallon tane yasa ta ɗago kanta.
Yarinyar data zo ta zauna kusa da ita ne a kujerar da take facing ɗinta tana kallon ta.
Bakin ta ta tura gaba tana hararar gefe Allah ya gani ita bata son kallo, tana cikin mita a ranta taji wayar ta na ringing, dakkowa tayi ta duba me kiran, ganin akhie ne yasa ta ƙara ɓata rai ta ɗaga dan taji haushin kashe mata waya da yayi, ɗaga wa tayi ba tare da tayi magana ba.
"Kizo ki karɓa malama ko nayi tafiya ta"
Murmushin da bata shirya masa bane ya ƙwace mata, da sauri ta tashi ta nufi wajen depertment ɗin nasu, tun daga nesa ta hango shi a jikin mota a tsaye.
Tun daga nesa take sakar mishi murmushi, shikam harara kawai yake zabga mata.
"Sannu da zuwa Akhie"
Bai kulata ba ya buɗe bayan motar ya shiga, itama shiga tayi ta zauna, da kan shi ya haɗa mata cornflask ɗin ya bata, gaba ɗaya bakin ta yaƙi rufuwa, sosai tayi farin ciki da zuwan akhien nata.
Tana gama sha ta ɗora kanta a kafaɗar shi tana lumshe ido.
"Akhie bacci"
Buɗe ƙofar motar yayi ya nuna mata ƙofa alamun ta fita.
"Bye bye akhie nagode sosai Allah ya bar min kai"
Cikin makarantar ta koma tana mejin farin ciki a tare da ita, ba wata yunwar arziƙi take ji ba ta kira shi kawai dan neman magana sai gashi kuma ya kawo mata.
Cikin class ɗin su ta koma ta zauna, bata daɗe da zama ba yarinyar ɗazu tazo ta zauna a kusa da ita, babu wanda ya kula wani har suka gama lecture's ɗim su na ranar.
Tana fitowa taga driver na jiran ta, dan haka babu ɓata lokaci ta shige motar suka nufi gida.
★★★★★
Da ka ganshi dole ne ya baka tausayi, gaba ɗaya ya fita daga cikin hayyacin shi, tsawon awannin da doctor's ɗin suka ɗauka a cikin emergency be zauna ba, haka be saka wa cikin shi komai, idon shi yana kan ƙofar ɗakin.
Ganin an kashe hasken ɗakin yasa gaban shi tsanan ta faɗuwa, a hankali doctor's tare da nurses suke fito wa duk sun haɗa gumi a tare dasu.
Kaman wanda ƙwai ya fashewa a ciki haka yabi bayan doctor yana tambayar shi lafiyar ammien shi, kallo ɗaya doctor yayi masa yace ya biyo shi office ɗin shi.
Tun da doctor ya fara mishi bayani yayi ƙasa da kan shi, hannun shi dafe da ƙirjin shi, dan ji yake tamkar wuta ce take kamawa a cikin ƙirjin na shi.
Toh kaman dai yanda na maka bayani tun kafin ciwon nata ya tsananta, yanzu ma zan ƙara maimaita maka, mahaifiyar ka na cikin tsaka mai wuya, a halin yanzu tana tsakanin rayuwa da mutuwa, idan har kana buƙatar mahaifiyar ka dole ne ayi mata aiki nan da kwana uku, shima saboda aƙwai gwaje_gwaje da za'a sake mata.
Shiru doctor ɗin yayi yana nazartar shi ganin yanda ya jiƙe jarkaf da gumi tamkar babu ac a office ɗin.
Cikin shaƙaƙƙiyar murya ya tambayi doctor yanzu kuɗin aikin da komai da komai yakai nawa.
Cike da tausayi doctor ya bashi amsa da 1.5million.
1.5 million......
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
BY
RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)
A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina❤️💫
SADAUKAR WA GA ACHADU'S FAMILY🤍
Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏
FULANI🤍
08082101373
❣️💫 AYRAAH 💫 ❣️
PAGE 6
Kuɗin kawai yake maimaita wa a cikin ranshi, jargaf haka ya jiƙe da gumi kaman wanda aka watsa wa ruwa.
Shidai likitan kallon shi kawai yake.
Bece masa komai ba ya tashi ya fita daga office ɗin, be zarce ko ina ba se bakin titi a ƙafa yake tafiya, yana saƙe_saƙe a cikin ranshi, yayi tafiya me nisa kafin ya samu napep ya ƙarasa da shi hotoro, yana sauka ya ƙarasa layin da ƙafa, wani irin bugu yake tamkar ze ƙarya ƙofar.
A firgice me gadi ya buɗe ƙaramar ƙofar, ganin yanayin shi daya ganine yasa ya bashi hanya ya wuce.
Main ƙofa ta gidan ya tunkara cikin sassarfa, be tsaya yin knocking ba ya danna kanshi cikin ƙofar, matar gidan na zaune, kai tsaye ɓarin me gidan ya nufa.
Tashi tayi tana shirin dakatar da shi, wani ɗan iskan kallo daya watsa mata da jajayen idanuwan sa ne yasa ta ja da baya babu shiri.
Jin takun tafiya ne yasa gaba ɗayan su juyawa inda me tawowar yake, babban mutum ne ya sha manyan kaya, sai tashin kamshi yake, kai tsaye idan ka kalle shi ka kalli ashraff dole ne kasan cewa suna da alaƙa.
Kujera ya samu ya zauna, ya ɗauki jarida yana ƙoƙarin buɗeta.
Gaban shi yaje ya zube, ya haɗe hannayen shi guda biyu cikin alamun roƙo da magiya ya fara mishi magana Muryar shi cike da rauni.
" Dan Allah uncle ba danni ba badan halina ba kate make ni, ka biya kuɗin aikin da za'ayi a ceto min rayuwar mahaifiya ta"
Ƙafar shi ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana mishi kallon ƙasƙanci da wulaƙanci.
Be damu da abinda yayi mishi ba ya ci gaba dayi mishi magiya fuskar shi na zubar da hawaye.
Tamkar baze kula shi ya daure cike da gadara ya tambaye shi nawa ne kuɗin aikin.
"1.5million ne"
Makirin murmushi ya saki a ranshi yace faɗuwa tazo daidai da zama, dan jiyan nan babyn shi tagama ɗaga mishi hankali akan auren yaron.
Wani ɗan iskan kallo yaje fa mishi, yace "ka tuna yarjejeniyar mu?"
Kanshi ya gyaɗa mishi.
"Toh malam yanzu wane hukunci ka yanke?"
" Ko yanzu a shirye nake a ɗaura auren in har zaka biya kuɗin nan"
"Idan kuma bazan biya ba fa?"
Shiru yayi masa zuciyar na tarfafasa ta ciki.
"Dad kai wane irin mutum ne yace ze aure ni kuma kana maganar idan baka biya kuɗin ba fa?"
Muryar ta ta katse musu maganar tasu.
Gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallon ta, kayan bacci ne a jikin ta, rabin jikin ta duk a waje.
Da sauri ashraff ya ɗauke kan shi daga kanta.
Zama tayi a jikin dad ɗin nata tamkar yarinya ƙarama.
"Baby ai kinsan zan bashi kuɗin tunda har yace ze aure ki, kawai dai"
Da sauri ta ƙara katse mahaifin nata.
"Kaga dad ya isa haka kawai ka bashi kuɗin, idan na shirya lokacin auren zanyi maka magana sai ayi dan yanzu inada abinda nake son ƙarasawa kafin nayi aure"
"Yanda kike so haka za'ayi baby"
Kallon shi tayi tana shanye idon ta " babe nawa ne kuɗin?"
Be kalleta ba ya bata amsa "1.5million"
Tashi tayi ta nufi ɗakin mahaifin nata, locker da yake ajiye kuɗi ta saka security ta ɗebo kuɗin ta fito da su a hannun ta.
Miƙa masa kuɗin tayi, yana miƙi hannun shi ze karɓa ta mayar da su ta ajiye a cinyar ta iyayen nata ta kalla tace!
" kuɗan bamu waje zamuyi magana"
Dad ɗin tane ya fara tashi, ganin mom ɗin ta bata da niyar tashi ya jefa mata wani kallo ba shiri ta tashi tabi bayan shi.
Ganin babu kowa a wajen ne yasa ta kalle shi ta nuna masa kusa da ita alamun yazo ya zauna.
Kanshi kawai ya girgiza mata, alamun nan ma ya ishe shi.
"Babe Kasan nawa ne kuɗin nan?" ta jefa mishi tambayar tana juya su a hannun ta.
Shi dai kallon gefe yake ba tare daya kalle ta ba.
"2 million ne zan baka su, ayiwa tsohuwar ka aikin, amman ina da sharaɗi, dole zaka dinga zuwa zance waje na, kuma duk sanda naji ina buƙatar kazo muje outing zaka je, sannan kuma kayan da nake siya maka kana ƙin karɓa ya zamar maka dole ka karɓa, saboda yanzu a matsayin mijin zainab kake bawai ashraff ɗan gidan buzuwa ba".
Tsare shi tayi da idanun ta tana jiran jin amsar shi, ganin bashi da niyar kulata ne yasa ta kwashe kuɗin ta miƙe ta kalle shi tace "duk sanda ka shirya bin umarni na kazo ka karɓi kuɗin"
Daga haka ta nufi stairs............
FULANI
08082101373
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
BY
RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA)
A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina🤍
SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY🤍
Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏
FULANI🤍
9131319938
RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY
300
SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA👇
08082101373
❣️💫 AYRAAH 💫❣️
PAGE 7
"Na amince!!!" Ya bata amsa zuciyar shi na zafi.
Murmushi ta saki tana ayyana wa a ranta, daman tasan dolen shi ya amince idan har yana son ceton rayuwar mahaifiyar shi, domin su shaida ne akan ƙaunar dake tsakanin shi da ammien tashi.
Dawowa tayi ta bashi kuɗin, tana masa kallon ƙasan ido.
Karɓa yayi ba tare da yace mata komai ba, gaba ɗaya jikin shi yayi sanyi, da wannan yanayin da yake ciki, shi kansa yasan amince mata da yayi wani babban ƙalu bale ne ya kira wa kan shi.
Jiki babu laka ya nufi waje da kuɗin a hannun shi.
"Babe"
Chak ya tsaya ba tare da ya juyo ba.
Jaka ta miƙa masa ƙarama, karɓa yayi yasa kuɗin a ciki ya juya ya tafi.
Har ya koma asibitin tunani ka kala kala ne a cikin ranshi.
Kai tsaye office ɗin likitan ya nufa da kuɗin, wajen biyan kuɗin ya tura shi ya biya kuɗin komai da komai suka bashi raciept.
Sai da yaje yaga ammien shi, yaji dama dama a cikin ranshi, tana kwance da kayan asibiti a jikin ta, hancin ta an saka maka mata oxgyen domin taimakawa numfashin ta, hannun ta ya riƙe ya ɗora kanshi a kai, hawayen shi ne yake ɗiga a hannun na ta, na tausayin kanshi dana mahaifiyar ta shi, ya daɗe a wajen ta sannan ya tashi ya fita daga ɗakin, ya nufi gida domin canza kayan jikin shi da ɗebo musu kayan da zasu buƙata a asibitin.
★★★★★
Gefen titi take kalla itama bata san meyaja hankalin ta ga barin danna wayar ta ba ta zubawa titin ido, dum dum dum haka zuciyar ta take bugawa da matsanancin bugu, hannun ta tasa ta dafe saitin zuciyar ta, duk addu'ar da tazo bakin ta karanta ta take, jin yanda zuciyar tata ta ci gaba da bugawa ne yasa ta runtse idanuwan ta da ƙarfi hawaye nabin gefen fuskar ta.
Har suka zo gida bata sani ba, bugun zuciyar ta kawai take saurara a cikin kunnuwan ta, jin ƙarar tsayawar motar ne yasa ta buɗe idanun ta da sukayi jajir, a hankali take tafiya tamkar mara laka a jikin ta, babu kowa a parlown sama ta nufa tana haɗa hanya da ƙyar ta kai kanta ɗakin ta, zubewa tayi a kan gadon ta tana maida numfashi da sauri_sauri tamkar wadda tayi gudun tsiri.
Ta ɗau tsawon lokaci a hakan kafin ta miƙe ta nufi toilet, wanka ta samu tayi tare da alwala ta fito, ƙaramar doguwar riga ta saka da hijab tayi sallah, zuwa lokacin data idar da sallar zazzaɓi ne sosai a jikin ta.
Zame wa tayi ta kwanta akan daddumar hawaye nabin fuskar ta, tabbas tamanta rabon da ta tsinci kanta a cikin wannan yanayin tasan yanzu kuma dawowar ta daidai saita Allah kawai.
Miemie ce ta sakko