Share this page
3 / 3
ƙasa tana duba lokaci, ya kamata ace ayraah ta dawo tuntuni amman har yanzun shiru babu ita babu alamar ta, ta kira wayar ta kuma ba'ayi picking ba gaba ɗaya bata jin kwanciyar hankali a tare da ita. Wayar Akhie ta kira. "Hello miemie na" "Akhie har yanzu ayraah bata dawo gida ba, ina ta kiran wayar ta kuma bata ɗaga wa" "Ki kwantar da hankalin ki miemie ukty tana lafiya, dan ɗazun da kaina na kai mata cornflask makaranta kuma banga alamun rashin lafiya a tare da ita ba, zan kira ta yanzu nima" Badan hankalin ta ya kwanta ba ta ajiye wayar ta zauna ta dafe kanta. Wayar ta yake ta kira bata ɗaga wa jin yanda shima hankalin shi ya tashi ne yasa shi nufo gidan, ko gama parking beba ya nufo cikin gidan. Ganin yanayin da ya shigo ne yasa miemie miƙewa tsaye babu shiri. "Akhie meyasa mi yarinya ta?" Kasa tsayawa bata amsa yayi ya nufi sama kaman ze tashi sama, da ƙarfin shi ya murɗa handle ɗin ɗakin nata, wata wawuyar ajiyar zuciya ce ta ƙwace masa ganin ta a kwance a ƙasa ta dunƙun ƙune cikin hijabi. "Uktyyyy" yaja sunan yana ɗago ta. Da ƙyar ta ɓude idon ta ta kalle shi sai kuma ta rufe....... FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr ❣️💫 AYRAAH 💫❣️ BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina🤍 SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY🤍 Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏 FULANI🤍 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 👇 08082101373 ❣️💫 AYRAAH 💫❣️ PAGE 8 "Uktyyyy baki da lafiya ne wai?" Jikin shi ta shige tana sakar masa kuka. Sai a lokacin yaji yanda jikin ta ya ɗau zafi. Jin shirun shi yayi yawa ne yasa miemie ta biyo shi saman, ganin ayraah jikin akhie ne yasa ta saki ajiyar zuciya duk da alamun su bai nuna mata lafiya suke ba. Ƙarasowa tayi jikin ta a sanyaye "meyasa meta akhie?" "Miemie zazzaɓi ne a jikin ta" Ɗaga ta yayi ya mayar da ita kan gadon ta, ɗakin shi yake ya ɗakko mata magani ya bata. Zama yayi ya riƙe hannun ta har tayi bacci, sai a lokacin yaji hankalin shi ya kwanta. Kafaɗar shi miemie ta dafa ɗagowa yayi ya kalle ta. "Kaje kayi wanka ka huta tunda ta samu bacci" "Toh miemie kece zaki zauna tare da ita?" "Akhie babu abinda ze same ta ai kaga ta samu bacci insha Allah kafin ta tashi zazzaɓin ya sauka a jikin ta" Tashi yayi ya nufi ƙofa ta bishi da kallo, tasan daman indai ɗaya bashi da lafiya tare suke jinyar. Har abhie ya dawo daga aiki gaba ɗaya gidan babu karsashi a cikin shi, daman tunda yaga auta bata ta tare shi ba yasan akwai matsala, be ƙara tabbatar wa ba seda aka zo cin abinci yaga duk ƙaunar akhie da abinci ya kasa ci sai a lokacin ya magantu. "Gaba ɗaya yau banga auta na ba tun da nadawo daga aiki" "Abhi bata da lafiya fa" Ajiye cokalin abincin yayi ya kalli akhie, "kaci abincin ka kaji akhie zata samu lafiya" Kallon abhin yayi kawai yayi ƙasa da kanshi, ukty itace duniyar shi a duk lokacin da wani abu ya same ta ji yake tamkar shi abin ya sama, baya san abinda ze taɓa masa lafiyar ta. Ƙarshe dai haka suka ci abincin babu walwala a tare dasu, gaba ɗayan su ɗakin ta suka nufa sai dai har lokacin bacci take kuma alhamdullah zazzaɓin jikin nata yayi sauƙi, haka suka je suka kwanta jiki babu ƙwari, musamman akhie. ★★★★★ Ji take a yau babu wanda ya kaita farin ciki, duk da tasan taurin kai irin na ashraff amman yanzu ya shigo hannun ta. Waya take kira tana taka rawa a hankali. "Hello baby" akace daga ɗayan bangaren. "Kirani matar ashraff kan ki tsaye babe" "Hmmm na gaji da jin wannan waƙar har na hadda ce ta" " A wannan lokacin ashraff ze zama mallaki na, duk abinda ya faru ta zayya newa ƙawar tata" "Gaskiya zee ban taɓa sanin shashasha bace ke se yanzu, kinyi gangancin bashi kuɗin nan, tunda kinfi kowa sanin halin gayen nan, yanzu idan ya canza ra'ayi bayan samun lafiyar mahaifiyar shi dame zaki masa taƙama?" Ɗifff tayi tamkar ruwa ya cinye ta, tana jin yanda gaban ta yake faɗuwa akan tunatar war da aminiyar tata tayi mata. Cikin sanyin murya take tambayar ta. "Toh yanzu menene mafita?????? FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr ❣️💫 AYRAAH 💫❣️ BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina🤍 SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY🤍 Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏 FULANI🤍 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 👇 08082101373 ❣️💫 AYRAAH 💫❣️ PAGE 9 "Taya zaki tsaya tambaya ta mafita bayan kin gama ɓata komai" "Ki gane babe banyi wannan tunanin ba, wataƙila ma shine abinda dad yaso fahimtar dani naƙi tsaya wa na saurare shi, nidai yanzu dan Allah ki faɗa min abinda ya kamata nayi" ta ƙarasa maganar kaman zatayi kuka. "A halin yanzu mafita ɗaya gare mu, kuma ita zamu aiwatar" Cike da zaƙuwa take tambayar ta menene ta faɗa mata. Bayani tayi mata, har ta gama tsaff tana sauraren ta, seda ta gama tayi mata magana. "Babe abin nan beyi tsauri ba kuwa?" "Nidai nabaki shawarar da zan iya baki zaɓi kuma ya rage naki" Ajiyar zuciya ta sauke tana me na'am da bayanin ƙawar tata, duk da tasan aƙwai ƙura a ƙasan aikata hakan. ★★★★★ Yana koma wa gida ya gyara inda ammie ta ɓata, sannan yayi wanka ya shirya ya fita, komai cikin hanzari yake yinshi dan burin shi ya koma asibitin, kayan da zasu yi amfani da shi ya ɗiba ya fito, har ze wuce ya fasa ya nufi shagon charging da yake jira, bayani yayi mishi akan ammien shi na asibiti dan haka baze samu zuwa ba sai yaga abinda hali yayi tukun nan, addu'a yayi mata da fatan samun lafiya, ya juya ya tafi. Har ya koma asibitin tananan a yarda ya barta, locker da take jikin gadon ta ya jera musu kayan su, ya ɗora yan kananun kwanuka a saman ta, sai da ya gama da komai, ya fita ya siyo musu ruwan sha da sabulu klin, sai bayan ya gama da komai ya fara jin yunwa, dan haka ya fita nema wa kanshi abinda ze iya ci a cikin asibitin. Cin abincin yake tamkar me cin magani, yana cine kawai dan yayi maganin yunwar cikin shi, bawai dan yana jin daɗin abincin ba, yana cikin ci yaji saƙo ya shigo wayar shi, har ze share sai kuma ya ɗakko ya duba. "A wane asibiti sirikata take ina son zuwa na duba ta ne" Iya kacin abinda saƙon ya ƙunsa kenan, ji yayi abincin bakin shi ya maƙale ya kasa wuce wa, dole ya ɗauki ruwa ya kora, shi yasan zuwan ta baze haifar da ɗa ido me ido ba amman bashi da zaɓi dole ya bata amsa. Aminu kano, Al Hassan ɗan tata ward. Daga haka ya ture abincin dan ya riga da ya fita daga ranshi kuma. Zama yayi cikin zulumi da tunanin da wacce zata zo masa kuma, Allah masani, ya kai awa ɗaya a zaune yakasa taɓuka komai yaji ringing na wayar shi, wayar ya ɗago yana kallon me kiran har ta katse be samu damar ɗaga wayar ba, wani kiran ne ya ƙara shigo wa sai da ta kusa yankewa ya ɗaga. " Ina bakin ward ɗin kazo ka shigar dani" daga haka ta katse kiran. Juyawa yayi ya zuba wa ammie ido daba tasan wanene a kanta ba, ya ɗau a ƙalla 10 minutes yana kallon ta sannan ya tashi ya fita. Tana tsaye tana danna waya, riga da wando ne a jikin ta, sai ƙaramin mayafi da tayi rolling da shi, baƙin glass ne a fuskar ta daya kusa rabin fuskar tata, baka ganin koda ƙwayar idon tane. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kanshi yana jan tsakin dabe san yayi shi ba. Ƙarar tsakin ne yasa ta ɗagowa daga danna wayar ta ta tana kallon shi. Cike da izza ta kalle shi, ta fara magana. "Ka barni a wajen ina zaman jiran ka bayan kasan na tsani jira, sannan yanzu kazo kana jamin tsaki?" Be bata amsa ba sai juyawa da yayi ya nufi ɗakin. Sakin baki tayi tana kallon shi, tamkar bashi ne ɗazun abin tausayi ba, amman yanzu kalli har halin nashi ya dawo jikin shi, kar dai maganar babe ta zama gaskiya, bayan shi tabi cikin takun ta na isa, tana kiran sunan shi. Ko juya wa ya kalle ta beba har ya ƙarasa gadon ammien ya zauna. Glass ɗin idonta ta cire tana masa kallon takaici, ga yanda ya wulaƙanta ta cikin jama'a, tana ganin yanda mutanen ɗakin suka bisu da kallo. "Ashraff dame kake ta ƙama ne da har zaka min wannan abin cikin mutane, kar ka manta kai ɗin tamkar bawa kake a waje na" Bala'i ta ci gaba da zazzaga masa amman yayi biriss da ita tamkar ba da shi take ba. Ganin yanda ya mayar da ita mahaukaciya ne yasa tayi kan ammie dake kwance. Ta ƙasan ido yake kallon ta yaga me zata aika ta. Oxgyen din hancin ta ta zare tana wuci. Ai besan sanda ya miƙe yazo gaban taba, kyakkyawan mari ya sakar mata akan fuskar ta, karɓar abin yayi ya mayar mata da shi. Shock ne ya hata magana da farko tare da tsananin mamaki, jin yanda ya finciki hannun tane yasa ta ɗago idon ta dake zubar da hawaye ta bishi da kallo, sai da suka matsa daga wajen mutane sosai ya saki hannun ta, juyawa yayi ze tafi sai a lokacin tayi magana, cikin muryar kuka. "Akan wannan sauran gawar ka mare ni?" Chak ya tsaya, juyo wa yayi ya zuba mata idon shi da yayi jajir saboda ɓacin rai. "Mahaifiyar tawa ce sauran gawa?" "Eh itace uwa ta ce kuma insha Allah bazata tashi daga wannan rashin lafiyar ba mutuwa zatayi, sannan..." Bema barta ta ƙarasa ba ya ƙara ɗauke ta da marin dayafi na farko. Fuskar ta ta dafe jin yanda abu me ɗumi yake bin gefen hancin ta ne yasa ta kai hannun ta, sosai ta zare idon ta ganin jini a hannun nata. Sosai zuciyar sa take masa zafi, ya rasa me zece mata tsabar ɓacin rai, ammien tashi da duk duniya bashi da kamar ta wannan yarinyar take faɗa wa haka. "Wallahil azim sai kayi danasanin wannan marin da kayi min, zaka san kaɗebo ruwan dafa kan ka, zamu gani ta yanda za'ayi wa uwar ka aikin ai bare ta samu lafiya, kuma wallahi ka rubuta ka ajiye aure tsakani na da kai babu fashi, amman hakan baze hana ka girbi abinda ka shuka ba" FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr ❣️💫 AYRAAH 💫❣️ BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI) YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION (YOTA) A har kullum ina jinjina a gare ki garkuwar fulani mahaifiya ta abar alfaharina🤍 SADAUKARWA GA ACHADU'S FAMILY🤍 Yanda na fara lafiya Allah ya bani ikon kammala shi lafiya🙏 FULANI🤍 9131319938 RABI'ATU ABDULLAHI KABIRU OPAY 300 SAI A TURA SHAIDAR BIYA TA 👇 08082101373 ❣️💫 AYRAAH 💫❣️ PAGE 10 LAST FREE PAGE Fuuuu ta juya ta tafi tana kuka me cin rai, babu wani mahaluƙi dayake mata abinda ashraff yake mata, amman a wannan karon taci alwashin sai yayi danasanin abinda ya aikata mata. Kujera ya samu ya zauna ya dafe kanshi da yake mahaukin sara mishi. ★★★★ Ba ita ta shi daga bacci ba sai wajen 11:pm na dare, a hankali ta miƙe ta nufi toilet, wanka tayi da ruwan ɗumi sosai tare da alwala, sallolin da ake binta tayi, hannayen ta ta ɗaga da niyyar addu'a, hawaye ne sosai yake bin fuskar ta, haɗe hannayen nata tayi ta rufe fuskar ta kuka take sosai wanda da ace wani yana kusa da ita zeji yanda kukan nata yake fita tun daga ƙasan zuciyar ta. Ta ɗau tsawon lokaci a haka kafin ta miƙe ta koma ta kwanta, bacci ya ƙaurace wa idanun ta, duk yanda taso tursasa kanta yin bacci abu ya gagara. Tashi tayi zaune ta cire ribbon ɗin dake kanta, dogon gashin tane ya baje a jikin ta sosai, baka ganin koda fuskar tane. Kaman wadda aka mintsina, ta miƙe ta nufi wardrobe ɗin ta kayan ta take watso wa, bata ga abinda take nema ba, gaba ɗaya ta hargitsa ɗakin wajen neman abin da take son ganin. Zubewa tayi akan gwiwar ta tana fashe wa da kuka. Tunani take sosai akan ina taje fa abin, kaman ance ta ɗaga idon ta sama ta hango wata trolley baby pink me kyau, da sauri ta tashi ta hau kan abu ta janyo ta, buɗe ta tayi, ajiyar zuciya ta sauke ganin abinda take nema suna ci. Card board paper ne a ciki masu yawa wadda take saman ta fara ɗakkowa. Kyakkyawan zane ne na gefen fuskar namiji, sosai sajen shi da sumar kanshi suka fito tamkar a zahiri, kallon hoton take hawaye na zuba a kai. Gaba ɗaya hotunan ta fito da shi, gaba ɗaya babu wanda cikakkiyar fuskar shi ta fito ajiki, duk rabin fuska ne sosai hotunan suka zanu, tabbacin wanda yayi zanen ya ƙware sosai. Rungume hoton tayi tana kuka sosai. Wata card board paper ɗin ta ɗakko da kayan zane ta farayi, sosai zanen ya fita. Rubutun dake ƙasa take kalla hawaye nabin fuskar ta. *Adaidai lokacin da gangar jiki take buƙatar hutu, ƙwaƙwalwa take buƙatar nutsuwa, adaidai lokacin ne zuciya ta take rasa nutsuwar ta tare da farin cikin ta, zuwa wane lokaci zan ci gaba da zama cikin wannan raɗaɗin? Se yaushe ne zuciya ta zata huta? Tsawon wane lokaci zan ɗauka ina jiran ka? Sai yaushe hawaye na zai daina zuba akan ka?* *Wanene kai? Yaushe zaka bayyana a gare ni?* Tambayoyin take wa kanta tana kuka, tana zaune a wajen har a kayi kiran Sallah, Alwala tayi ta gabatar da sallah, ci gaba da zama tayi akan daddumar, tuna cewar za'a iya shigowa a same ta haka ne yasa ta tattare hotunan ta tura su ƙasan gadon ta. Hijabin jikin ta ta cire, tayi zaman ta a haka. Jin an taɓa handle ɗin ɗakin ne yasa ta juyo ta zubawa ƙofar ido. Akhie ne ya shigo da sallama, turuss ya tsaya ya zubawa fuskar ta ido, ganin yanda idanun ta suka kumbura sukayi sumtum, ga fuskar ta ma ta ɗaga sosai gaba ɗaya tayi ja. Cikin sauri ya ƙarasa ɗakin, fuskar ta ya riƙe a hannun sa yana kallon idanun ta da suke ƙyallin hawaye. "Meyafaru ayraah?" Kanta ta girgiza masa hawaye nabin fuskar ta. "Dan Allah ki faɗa min damuwar ki a wannan lokacin na roƙe ki ukty" Hannun shi ta riƙe ta ɗora akan saitin zuciyar ta, jin yanda zuciyar tata take bugawa sosai ya tsorata. "Akhie zuciya ta zata fashe tun jiya take wannan bugun, kaina kaman ze rabe gida biyu akhieeee" Jin yanda numfashin ta yake riƙe wa ne yasa shi janyo ta ya rungume ta a jikin shi. Numfashi take sauke wa sosai a jikin shi, can kuma yaji numfashin nata ya tsaya, jikin ta ya saki a jikin shi. Da bala'in ƙarfi ya zaro ta daga ƙirjin shi yana kallon ta, ganin yanda idanun ta suka kakkafe ne yasa shi fasa ihu kaman ƙaramin yaro. "Miemieeeee!! Abhieeeee!!!" "Ayraah ki tashi, uktyyyy" Kaman ze zare haka yake jijjigata. Kusan rige rigen shigowa ɗakin ake tsakanin miemie da abhie. Ganin autan nasu a haka ne yasa jiri ya ɗibi miemie ta faɗi a wajen itama numfashin ta na ƙoƙarin ɗaukewa, da sauri abhie ya riƙe ta yana kiran sunan ta. Shikam akhie zuwa lokacin ya fara fita daga hayyacin shi. Ganin yarinyar daya raina da hannun shi kwance bata numfashi a gaban shi. ★★★★★ Tabbas sai yanzu yaga wautar da yayi na marin yarinyar da yayi amman hakan be dame shi ba, yana jin ze iya aikata komai ga kowa akan ammien shi koda kuwa hakan na nufin ya rasa rayuwar shi. Gashi doctor yace masa gobe idan Allah ya kaimu za'ayi wa ammie aiki, saboda jikin ta ƙara rikicewa yake. Gaba ɗaya ranar be runtsu ba, sallah yake kawai tare da addu'a akan Allah yasa a wannan karon ayi cikin Sa'a. Tun yana jiran sakamakon abinda ya aikata wa zainab a daren har ya haƙura ya cire fargabar a cikin ranshi. Sai dai yana da tabbacin shirun su ba Alkhairi bane. Ƙarfe 11 na safe za'a shiga da ammie ɗakin tiyata, goma da rabi aka shirya ta cikin kayan aikin, nurses suka zo tafiya da ita yabi bayan su. Ana shirin shiga da ita yaji cikin kaushin murya ance! "Ku dakata" Gaba ɗaya juyawa sukayi suna kallon me maganar banda shi da yaji yanda zuciyar shi take bugawa tamkar zata faso ƙirjin shi ta fito. "Ku kama min shi" Yan sanda ne cikin farin kaya suka zagaye shi. "You are under arrest" Innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un kawai yake maimaita wa acikin zuciyar shi. Sai a lokacin ya juyo yana kallon uncle ɗin nashi, da yar gwal ɗin yar shi da fuskar ta take kumbure saboda marin data sha a hannun shi. Tashin hankali ne rubuce akan fuskar shi. Wani irin kallo yake wa uncle ɗin nashi me wuyar fassara. Babbar rigar shi ya saɓa ya matso gaban shi. "Kai har kanajin wanene kai da zaka marar min yar?" Koni ban taɓa ɗora hannun na a kanta ba bare kai, talakan banza talakan wofi" "Yanzu yanzu ina son kadawo min da kuɗin da tabaka jiya, wallahi sai dai wannan uwar taka mara amfani ta mutu" Gaba ɗaya jijiyoyin jikin shi sun miƙe samɓal, tsabar ɓacin rai da tashin hankali. "Zaka dake nine? Ina kuɗi na?" Cikin shaƙaƙƙiyar murya yace! "Nariga na biya kuɗin aikin" "Da ayi mata aiki da kuɗi na gwara ace nabar wa asibitin kuɗin" kai kuma Kasan duk yanda zakayi da ita uwar taka" Sosai nurses ɗin suke bashi haƙuri, da nuna mishi irin tsananin wahalar da majinyaciyar take ciki, amman ya rantse akan baza'a mata aikin nan ba sedai ta mutu. Har ƙasa ashraff ya tsugunna da niyar bashi haƙuri, sai dai kafin yayi magana ya ɗauke shi da mari cike da ɓacin rai. "Ku ɗauke shi ku tafi da shi... Itama uwar tashi ku biyo ni da ita.... Topha ana wata ga wata ga ƙoshi ga kwanan yunwa. ku biyo alƙalamin yar gidan baba Achadu dan jin yanda zata kasance. FULANI 08082101373 https://chat.whatsapp.com/Kqi1tusHnZa6SHgbTgFqlr An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3