Share this page
5 / 7
bai tafi ba yana nan tsaye,wani murmushi ya saki yana mai jawo hannuna ya fiddo ni waje.Cike da jin haushi na soma kai masa duka shi kuma banda dariya babu abin da yake yi mini,wato burinsa dama shi ne na tsorata shi yasa ya rufe ƙofar. Dukkan hannuwana ya kama ya riƙe gam,fuska shaɓe-shaɓe da hawaye nake kallonsa.Cikin taushin murya ya soma magana,“ban san me mahaukaciyar nan ta faɗa miki ba,amma ina so ki yarda da ni kar ki saki ki saurare ta ko kuma ki yarda da soki burutsun da za ta faɗa miki.Ita ɗin muguwa ce,ba mutumniyar kirki ba ce don haka ina so ki aje hankalinki wuri guda ki yarda ki gane ba ki da lafiya” yana gama faɗar haka sai ya sakar mini hannuwa ya tafi,na bi bayansa da kallo har ya fice. Ko da na ƙaraso falo sai na tarar da Ammy da Maryam a zaune suna karatu,amma sam ba na Alkur'ani ba ne wani littafi ne daban .Gefen Maryam na zauna ina mai baza idona kan rubutun abin mamaki sai na ji wai zan iya karanta shi,amma sam ba da baki a'a ta ido kawai.Wani irin sanyi ne na soma jin jikina na yi kamar wacce aka saka a ƙanƙanra,yayin da kunnuwana suke tariyo muni wata murya wacce rabon da na ji ta tun ina ƴar shekara uku.Wannan murya ba ta kowa ba ce sai ta aljana macijiya,matar da take fito mini a zahiri ba wai cikin mafarki ba.Tunanina da lissafina ba su yi wani jinkiri ba suka ɗingiza ni izuwa shekaru ashirin da suka shuɗe a baya. A tsaye nake gaban wutar da ake dafa tumu,Mama da Abba suna yin hira jefi-jefi yayin da kuma gefe guda Abba ke ƙara juyara zangarniyar gero wanda yake farkon fitowa wanda kuma shi ake kira da tumu.Daga cikin wutar nake hango wasu manyan idanuwa masu mugun haske suna kallona,sam ban ji tsoro ba kasancewar shekara ta uku kacal a duniya sai ma abin ya burge ni har ta kai da na sa hannu a cikin wutar na kamo su sai dai ba iya idanu ba ne har da wani dogon bindi wanda ya kasance na maciji.A jikin bindin gasashen tumu ne jere rasss,haka na sa hannu ina ɗebowa ina ci yayin da idanuwan nan masu mugun haske suke daɗa yi mini wani kallo . Ina tsaka da morewa Abba ya ce “Fateema ungo wannan ki ci” Mama ce ta ce masa “ai ba za ta karɓa ba sai ta cinye wanda ke hannunta” ta ƙarashe faɗa tana mai hasko mini fitila,sai na ga ta yi cilli da ita tana salati a nan take kuma abin da ke riƙe da hannuna ya sulɓe mini ya koma cikin wuta.Abba ya ce “lafiyarki?” muryar Mama na rawa ta ce “busashen maciji ne a hannun Fatee” sai dai da Abba ya haska fitila babu komai a hannuna,sai ya ce kawai don har zuwa lokacin Mama ba ta fidda zancen maciji a ranta ba.Haka dai muka ci tumun muka kwanta,sai dai nawa baccin sam bai yi wani nisa ba na farka saboda wata murya da ke kiran sunana.Haka na tashi na soma takawa har na isa inda sautin muryar ke fitowa,cikin ciyawa ne,sai na ja na tsaya.Fararen idanuwanta masu matuƙar haske su ne abu na farko da na fara gani kafin ta ida fiddo ainahin jikinta wanda shi ma yake walwali yana fitar da wani hasken wuta abin sai ya burge ni na duƙa na ɗauke ta.Sosai muka yi wasa da ita wanda a ƙarshe ta kai ni wata duniyar mai cike da macizai irinta tana nuna musu ni tana cewa ƴarta ce ni.···· Sanyin ruwan da na ji a jikina shi ya farfaɗo da ni daga duniyar wankin idon da ake yi mini na tuna rayuwata ta baya.Maryam na gani a tsaye riƙe da bokiti yayin da kuma Ammy ke faman busa wutar hayaƙi,a hankali nake ƙara ware idona ina kallonsu so nake na basu labarin abin da na gani amma tamkar an toshe mini maƙoshi haka na ji ba zan iya bada labari ba.Miƙewa na yi na fita harabar gidan ,wani irin canji na riskata wanda sam ban san farkon tono baƙin sirrina ne ba.Can cikin jardin na ja na tsaya tare da nutsuwa ina sauraren wani amon murya wacce ba ta ƴan adam ba,sai da na nutsu irin sosai ɗin nan sannan na fahimci cewa sautin na fitowa ne ta cikin ciyayi.Haka na zube kan gwiwana na soma buɗe korin shuke-shuken har Allah ya kai ni ga wata daula ta tsutsotsi...... Only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 08 Tamkar yadda mutane ke kafa daula su yi gidan sarauta haka idanuna suka gane mini masarautar tsutsotsi.Kamar wata zararriya haka nake kallonsu suna ta hidindimu,abin da ya fi ɗaga mini hankali shi ne yadda aka yi har nake jin maganar da suke yi. Jikina ne ya soma yin rawa jin topic ɗin da suke tattaunawa a kai ba na komai ba ne sai na yadda za su yi su kashe Mu'azzam.Ban gusa ba sai da na ji ta yadda suka tsara plan ɗin,na miƙe da sauri ina tafiya ƙafafuna na harɗewa na nufi can wajen direba . Kame-kame na fara kafin na ce “Mu'azzam ya ce ka kai ni can wurinsa” na faɗi haka ne sanin shi ne direbansa.Ba tare kuma da yin gardama ba kuwa ya buɗe mini mota,na shiga gidan baya na zauna muna tafe ina tunanin abin da na gani ɗin. A can ɓangaren Mu'azzam kuwa yana fita direct babbar asibitinsa ya wuce.Bai iya duba kowanne patient ba ya dai samu wuri ya zauna suna hira da babban abokinsa Jabeer inda yake faɗa masa matsalolinsa shi kuma yana basa shawara. “Wallahi abokina tun da yarinyar nan ta shigo rayuwata duk komai ya ida cakule mini,kana ga fa a yanzu ko minti ashirin ɗin ban yi haka nake zaryar shiga toilet.Abin da ma na lura kamar in na samu kusanci da ita matsalar ta fi saurin taso mini,ina ga saura ƙiris ni ma na dinga saka pad ɗin” Mu'azzam ya faɗa yana wani kama kai. Jabeer ya ce “duk dai komai ya kusa zuwa ƙarshe tun da an samo bakin zaren ka gano kalar macijin da Ummarta ɗin ta kashe” “Babu wani sauƙi don har zuwa yanzu ban samu na yi magana da ita Fateemar ba,kuma abin takaici abokina ta ƙi yarda ba ta da lafiya to ta ya za a yi mata magani? Kuma fa Nadiya ta soma yi mata fatalwa tana fito mata,kai abin dai sai godiyar Allah ” Mu'azzam ya faɗa yana tashi tsaye ya nufi toilet,jimmm kaɗan ya fito yana haɗe rai. Jabeer ya ja numfashi kafin ya ce “amma me yasa da ka kai ta asibiti ba ka jona mata hullar gaskiya ba wacce za ta saka ta yin bayani don dole?” Mu'azzam ya basa amsa da “ta ya za a saka mata hulla alhalin dodon jikinta har ya riga ya bayyana,ni babban tashin hankalina ma bai wuce kar ta ƙi sakin kurwar nurse ɗin” Jabeer shi ma ya miƙe tsaye sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi ya ce “ina ga kawai hanyar da ba ka son bi ɗin za mu ɗauka muddin muna son ceto kurwar nurse ɗin,ka ga masu amfani da maitar maciji abin da suka ƙi jura shi ne hayaƙi me zai hana ka ɗauko Fateemar a gwada yin haka ɗin ?” Mu'azzam ya ce “wannan solution ce mai haɗari,don ana iya wajen ceto kurwar ita Fateemar numfashinta ya tsinke tun da ainahi ba ita ce ke yin maitar ba,saka ta ne ake yi” sai kuma duk suka yi shiru suna nazari. Sosai direba ke sharara gudu har muka iso,shi ne ya yi mini jagora har zuwa ofishin Mu'azzam wanda a jikin ƙofar ma an rubuta sunansa.Ba tare da neman izini ko yin sallama ba na buɗe ƙofar da ƙarfi,a tare duk suka juyo suna kallona ni kuwa sam ban damu da irin kallon da suka yi mini ba na nufi Mu'azzam ina mai basa labarin abin da idona suka gane mini amma sai na ga suna kallon juna kamar ba su yarda ba. Cikin son sai na sa sun gaskata na ce “wallahi da gaske nake,in kuma ba ku yarda ba ku zo na nuna muku” .Harshe Jabeer ya canza sai kawai na ga Mu'azzam ya kama hannuna yayin da shi kuma ya take mana baya,cikin wata mota ce daban muka shiga inda Jabeer ya tuƙa mu.Duk da ban san gari ba amma na gane hanyar asibitin nan ce ta mahaukata,ina ji ina gani kuwa suka shiga da ni. Tamkar wata ƴar kaso haka Mu'azzam ya ɗaure ni jikin kujera,wanda kafin ya iya yin haka sai da ya sha fama da ni don har cizonsa na yi. “Jabeer kunna hayaƙin” Mu'azzam ya faɗa,shi kuwa tamkar jira yake ya buɗe wani akwati da ke cikin ɗakin sannan ya fiddo komai tare da haɗa komai. Ina ganin hayaƙi ya fara tashi na ƙara ƙaimin kuka ina mai ce masa “ina da cutar toshewar numfashi don Allah ku kash....” sauran maganar ce ta maƙale mini jin harshena ya soma zazzalowa yana ƙara tsayi har yana taɓo cinyata.Hayaƙi ya turniƙe mini hanci da maƙoshi,tamkar an zuba mini wuta haka gangar jikina ta ɗauki zafi.Ba a ɗauki lokaci ba kuma wannan abin da ke cikin jikina na ji ya soma yin magana,“in ma dai niyyarka ka kashe Fateema to ka makaro domin kuwa hatta cutar toshewar numfashin da take magana ni ce nan na haifar mata da shi,kuma ba zan baku abin da ku ke so ba yadda ka ƙulle hanyar da zan haɗiye kurwar nurse ɗin nan haka ni ma zan ƙulle maka ƙofar da za ka janye ta daga gare ni” Mu'azzam ya ce “Jabeer miƙo mini ruwan floris sannan ka ƙara zuba turaren a ciki” wata gora ya miƙo masa ya buɗe ta sannan ya soma watsa mini ruwan ,nan take kuwa na soma yin ihu ina son kubcewa ruhin da ya ɗauki mallakar tunanina kuwa sai kuma ƙara nanata wa yake yi ba zai bayar da kurwar ba. Tsawon lokaci da Lahaula Wala ƙuwata illa billahi sannan na ji wani abu ya gangaro maƙoshina ya fito da gudun bala'i.Tamkar dunƙulen gulusuwa haka yake,sai dai fari ƙal yake yana gama fitowa bakina ya fashe tare da yin sama cikin iska sai kuma a lokacin na dawo hayyacina. Cikin wata irin muguwar tsana nake kallon Mu'azzam don ni sam duk abin da ya faru a yanzu na manta shi shaf.Da kansa ya kwance mini igiyoyin da ya ɗaure ni da su,ya ɗauki wani ƙyalle ya fara goge mini hijabina da duk ya ɓace.Cikin jin haushi na ture shi tare da tashi tsaye,ban kuma yi jinkiri ba na ruga a guje na ɓalle ƙofa na fita. Yadda nake gudun da sauri yasa ban ɗauki lokaci ba na fito harabar asibitin sai kuwa na yi rashin sa'a a daidai wannan lokaci ne wani mahaukaci ya kubce.Cak na tsaya ina waro ido yadda ya nufo ni gadan-gadan,da wani bala'in gudu na yi baya zan koma inda na fito sai na ci karo da Mu'azzam.Banda wani zaɓi wannan yasa na nufe shi don tseratar da kaina sai dai ina tuni mahaukacin ya kwashe ƙafafuna sai da na yi sama kamar zan faɗi,amma wani irin haske ya fita idona ya daki ƙasa sai gani ina yawo cikin iska sam gangar jikina ta ƙi taɓa ƙasa. Da yake mahaukacin nada rabon wahala haka ya ja ƙafata ta baya,wanda ban san a ina na samu ƙarfin buge shi ba sai ga shi ya faɗi warwas. Daidai nan na yi tsaye kan ƙafafuna,yayin da kuma likitoci suka zo suka ɗauke shi.Ni kuwa sunne kai na yi ganin kallon da Mu'azzam ke aiko mini,kamar wata ƴarsa ya damƙi hannuna ya ƙara mayar da ni can ciki.Wani sashe na musamman muka shiga mai ɗauke da wasu zane-zane da ban san ma'anarsu ba. Hannuna ya saki tare da cewa “zauna can” ya nuna mini wata kujera mai hoton zaki,na maƙe kafaɗa na ce “ni gidan zan koma” rikitatun idonsa kawai ya zuba mini babu shiri na je na zauna. Wata hulla ya ɗora mini a kai sannan ya saka mini wani gilashi wanda ya kasar da duk hasken ganina.Tamkar makauniya haka na koma,abin mamaki kuma sai na ji na kasa yin motsi.Ina cikin sabon yanayin ne na ji tambayar Mu'azzam kamar daga sama. “Nana Fateema ina son ki bani labarin kanki,sannan wace ce ke ? Wasu irin laifuka ki ka aikata tun ƙurciya zuwa yanzu da kike zaune a gaban dodon Mayu?” yana gama dire kalamansa haka na ga rayuwata a cikin idona kamar wacce aka kunnuwa tv. “Kamar yadda ka sani sunana Nana Fateema a wannan duniyar,yayin da kuma a ɗayar duniyar ake kirana da Goddess/déesse.Rayuwata ta kasance ruwa biyu ,rabi ta normal mutum rabi kuma ta keɓaɓiyar duniya ta waɗanda ba su baccin dare sai na rana.Kamar yadda na gani a wani wankin idon waiwayen bayan rayuwata,a ranar da Abba yana gasa mana tumu a wannan ranar ce na yi gamdakatar da Jinniya wacce ta ɗauki matsayin uwa mahaifiyata sakamakon ɗanta da Momata Hindu ta kashe.Tun daga wannan lokaci sai ta soma zuwar mini a mafarki da kuma rayuwar zahiriya.Babban zunubin da na fara aikatawa shi ne na kashe matar Abbana wacce ya auro saboda jinkirin haihuwar da Mama ta samu .Tun daga ranar da ta shigo gidan Abba duk ya canza,ni kuma na kasa jura wata rana da dare na damƙe mata kurwar a cikin daren kuma ta mutu.Mutum na biyu kuma shi ne ƙanen mahaifina na kashe shi a lokacin da na cika shekara biyar a duniyar sakamakon zargina da ya soma yi ,duk wannan bai ishe shi ba ya soma bin didigina a garin nemo gaskiyar ni wacce ce na rikiɗa na zama macijiya na kashe shi har lahira” ina kawowa nan na yi shiru. Mu'azzam ya sake cewa “amma ta ya aka yi aka toshe miki hanyar ci gaba da yin mugunta?” “Mama mutum ce mai baiwa,tana ganin abubuwa a cikin mafarki wanda kuma ba kowa ke sanar da ita ba sai aljanunta.A cikin mafarki ta ga komai, amma da yake ta iya takun saƙarta sai ta yi shiru da bakinta ba ta sanar da kowa ba har Abbana.Ban san a ina ta samo maganin raba ni da ruhin dodon jikina ba kawai na samu kaina da rashin sinadarin.Sosai kuma na fahimci canjin da na samu, amma babu wanda zan iya yi wa magana sai dai abin yana damuna saboda kewar uwa Jinniya wacce ta ce ita ce mahaifiyata.Yawan tunaninta yasa na soma yin mummunan mafarkai na dinga zabura haɗi da yin suratai, wannan dalilin ne yasa Mama da Abba yanke shawarar kai ni wajen mai magani da ke can wani ƙauye mai nisa.Yayin wannan dogon balaguron mun haɗu da ƙalube da dama a bisa hanya,ciki kuwa har da lalacewar motarmu wacce Abba ya aro.Muna tsaka da tafiya ta tsaya cak, Abba ya fita yayi ƴan taɓe-taɓe kafin ya ce “ku fito ina ga sai na nemo mai gyara” Mama ta buɗe murfi muka fito tana mai cewa “a ina za a samu mai gyara cikin wannan dokar dajin?” “Zan dubo! Bari na fiddo muku tabarma ku zauna kafin na dawo” ya faɗa tare da buɗe Boot ya ciro mana tabarma.Mama na karɓa sai ya tafi,yayin da ta ja hannuna muka ƙetara can gaban wata inuwar bishiya.Tabarmar ta shimfiɗa tare da yin zaune ni kuwa tsaye na yi ina kallon wata mata mai fararen kaya hannunta na riƙe da ƙwaryar nono. “Fatee zo ki zauna” cewar Mama tana nuna mini gefenta. Na maƙe kafaɗa saboda hasken idon matar ba za su barina har na samu damar isa can ba,ban san dalili ba amma ƙila saboda ruhin dodon da ke kwance a jikina a dabaibaye. “Zo ki zauna” ta sake faɗa tare da miƙo mini hannunta,na girgiza kai na ce “ki cewa wannan macen da ke bayanki ta bar kallona” A tsorace Mama ta juya sai dai da dukkan alamu ita ba ta ganinta,jikinta na ɗan rawa ta miƙe tare da cewa “don Allah ki yi haƙuri kar ki cutar da mu motarmu ce ta lalace shi ne muka zo mu zauna kafin a gyara amma za mu gusa ” wani murmushi na ga matar ta yi kafin ta ce “haƙiƙa ko a bil'adama akwai masu kyakkyawar zuciya, waɗanda suke ɗaukar ƴaƴan kishiyoyinsu tamkar nasu.Allah ne kaɗai ya san dalilin da yasa motarku ta lalace a daidai kuma bakin ƙofar gidana,ƙila don na tura motar kyakkyawan burinki ta kai ga ci” da dukkan alamu hatta Mama ta ji wannan furicin don kuwa sai da ta mayar mata da amsa inda take cewa “na gode sosai da kika fahimce ni,kin ga ni ma daga yau na yarda cewa har a mutanen ɓoye akwai na kirki na bar ki lafiya” sai ta naɗe tabarmar,sai dai fa matar ba ta bari muka gusa ba sai da ta zo ta ratsa gangar jikin Mama ta shige tamkar yadda ruwa ke huda ƙasa su nitse haka na gani.Ina shirin yin magana Abba ya dawo shi da mai gyara,sai kawai muka tafi wurinsa.Ba a ɗauki ko da minti biyu ba motar ta tashi wanda na yi imani cewa ƴar bafulatanar nan ta jikin Mama ce ta warware sharrin da yasa motar ta tsaya.Ko da muka shiga ciki sai Mama ta jawo ni ta rungume a ƙirjinta,tamkar ana gasa ni haka nake ji sai dai na kasa kubcewa haka na daure har muka isa wajen wani mai bada magani. Duk da mun tarar da jira haka ya sa aka zo aka ja mu,da muka shiga ciki sai da ya dubi Mama na wani lokaci kafin ya ce “duk da na ga kun samu wacce za ta taimaka muku sai dai ku sani ruhin dodon Jinniya nada mugun ƙarfi saboda zaluntarta da aka yi,sannan kamar yadda na samu labarin zuwanku tun kafin ku zo to haka na ga mummunar ƙaddarar da za ta faru da ku nan gaba.Amma babu komai,zai zo da sauƙi ku tashi ku nemi wuri ku kwanta kun yi doguwar tafiyar zan sa a kai muku abinci ita kuma wannan ku bar ta nan” haka kuwa aka yi a bai wa su Abba masauki bayan sun ci sun sha ni kuwa kasa ci na yi,a wannan daren ne Mama ta samu cikin ƙanwata Maryam wacce zaɓi ce daga ƙaddarar rayuwata. Bayan tafiyar su Mama wankan magani ya yi mini sannan ya ɗaura mini wata laya a wuyana wacce shigarta kenan na ida jin komai da ya danganci ɓoyayyar duniya ya tsaya mini cak na dawo normal yarinya ƴar shekara biyar. Washegari kafin mu tafi mai bada magani ya shaidawa iyayena kar su bari layar nan ta bar wuyana.Daga nan muka ɗauki motarmu ta komawa can gida,a nan ne wani mummunan hatsari ya same mu.Cikin irin soyayya ta uwa Mama ta ƙanƙame ni gam,tare da buɗe motar muka fito daidai nan kuma mota ta soma ci da wuta alhalin Abba na ciki.Muna kuka muna kallo motar ta toye ƙurmus a dokar daji,faɗar tashin hankalin da muke ciki ya fi gaban misali.Haka Mama ta goya ni muka soma tafiyar ƙasa,wacce duk tako ɗaya da za ta yi ya fi taki ɗari da wannan muka isa gida a wannan dare.A washegari Mama ta sanar da rasuwar Abba aka yi masa zaman makoki mai cike da tsiyar gumi ana cewa ita mayya ce ta kashe kishiyarta yanzu kuma ta damƙe mijinta.Surutun mutane yasa ta sayar da ɗan abin da dangi Abba suka rage mana,ta haɗe kayanmu muka bar gidan muka koma can cikin ainahin birnin Kibri inda muka fara rayuwa mai cike da ƙalubale.Sana'ar ƙosai Mama ta fara haka da haka har cikin jikinta ya tsufa ta haifo Maryam ,wacce zuwanta duniya shi ya yaye ƙuncin rayuwarmu wanda kuma ba kowa ya kawo canjin nan ba sai ƴar bafulatanar nan ta jikin Mama.A ranar suna Mama ta samu kyaututtuka da dama wanda yasa bayan arba'in ta fara sana'a mai gwaɓi har ta saya mana gidan da muke zaune ciki .Haka rayuwa ta shuɗe na tsawon shekaru har na gama karatuna na soma fafutukar neman aiki,wanda a ƙarshe wata asibiti ta yarda na je na dinga yin aiki amma albashin ba wani ba.Mama ce da Maryam suka ƙarfafa mini gwiwa kan na je na soma yi wanda da ace sun san cewa asibitin nan ita ce mafarin tono baƙin sirrina na tabbata ba za su yarda ba. A ranar farkon zuwana wuraren ƙarfe shidda na yamma ne,komai na tafiya daidai ina duba patient har zuwa dare.Inda gizo ya fara saƙa shi ne wani ɗan yaro da ya mutu tsakiyar dare,wanda tun zuwana na ji mugun sonsa.Wannan soyayyar tasa ta haifar mini da ƙawa zuciya har na yi masa rakiya zuwa MUTUWARE,tamkar ni ce uwarsa haka na rungume gawarsa ina kuka daga bayana na ji an dafana da wani irin hannu wanda ba zan iya misalta yadda na ji ba,amma da na juyo sai na ga babu kowa.Wani tsoro na ji har zan fita sai kuma wani akwatin gawa ya buɗe.Kamar wacce ake tatsowa ruhi haka na ji ana fizgata a haka har na isa kusan akwatin .Gawar wani kyakkyawan saurayi ce a kwance,sai dai da dukkan alamu ba mutuwa ya yi ba saka shi aka yi a ciki. “Ki taimaka mini na fito” ya furta,na waro ido jikina na soma rawa.Ya ci gaba da cewa “kar ki ji tsoro kina iya taimakona,ban mutu ba sharrin maƙiya ne suka saka ni a nan.Sunana Dr Bilal shararren likitan nan na garin Kibri...” ina jin abin da ya ce sai na zuba da gudu a guje sai dai ina zuwa bakin ƙofa sai ta dantse...... [18/08 15:13] MRS SADAUKI: *TUKUNYAR MAYU*🏴‍☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Fateema Abdou dite Mrs Ƙarshen Ƙauna🇳🇪 *FCWA*☀️ ________________________ 09 Ko da na juya akwatin gawar na ga yana fitar da wani haske.Jikin ƙofar na jingina tare da rumtse idona ko zan ji sassauci,ashe ma ƙaimi na ƙara don kuwa tamkar fitar iska haka na samu ruhina ya fice daga gangar jikina ya isa can bakin akwatin gawar.Hannu na miƙa masa ina mai cewa “ka zo na cece ka amma da sharaɗin za ka yi mubaya'a kai da sauran doctor's na asibitin nan” na yi wannan furicin ba tare da ni kaina na san me hakan ke nufi ba. “Na amince” Dr Bilal ya furta,yayin da kuma na kai hannu na jawo shi na fitar da shi daga akwatin,kafin ruhina ya zo da wani bala'in gudu ya koma cikin gangar jikina.Wani irin shock na ji ya shige ni tamkar na kama da wutar lantarki daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti. Na tashi dakyar ina dafe kaina da ke yi mini azabar ciwo,sam kuma na kasa tuna abin da ya faru.Haka shugabanmu ya ce na tafi gida sai na huta,godiya na yi masa na dawo gida.Ina shigowa Maryam wacce a lokacin ba za ta wuce shekara sha huɗu ba ta zo ta rungume ni sai kuma ta yi baya tana ƙare mini kallo.Yanayinta na ga ya canza kafin ta ce “anty Fatee me ya faru ki ka dawo gida tun asubar farin? Ba sai ƙarfe goma za ki sauka ba?” “Ni ma ban sani ba Maryam,kin ga banda lafiya ne” na faɗa tare da raɓawa gefenta,sake da baki take kallona tana mai hana ni wucewar har za ta yi magana Mama ta leƙo daga kitchen tana mai cewa “ki barta ta huta mana,in ta tashi sai ku yi magana” “Amma Mama yanayin ƙamshin jikinta ya canza daga wanda na sani kuma ma ...” “Ya isa Maryam!” Mama ta katse ta tare da ce mini “je ki Fateena ki kwanta” kai na jinjina mata tare da wucewa da sauri na shige ɗaki. Ko kaya ban rage ba na haye gado na soma lumshe ido,a can cikin ɓargon zuciyata ina jin cewa da akwai wani abu da ya faru da ni amma na manta .Da na ga kamar ina son jawowa kaina matsanancin ciwo ne sai na ture tunanin na soma sauke ajiyar zuciya ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.Tsawon lokacin ina baccin kafin na farka,wanka na

Chapter 5 of 7