ɓata yasa Maryam ba ta tsaya yin tata kwalliyar ba ta saka kayanta ta fice.
Jiƙaƙen gashina da ta ɗaura a tsakiya na baje ina turo baki tare da cewa “salon ya yi mini wari ta wani ɗaure mini gashi” mayafin rigar na ɗora a sama sannan na saka takalmi masu tsinin sai na fita ni ma .Tsit falon yake babu kowa amma ina jin ɗan sautin music daga can waje,hakan yasa na yi saurin fita ina tafe ina ɗan riƙe rigar kamar mai koyon tafiya haka nake takawa gudun kar na faɗi sam ban yi tunanin salon tafiyar zai jawo hankulan mutane a kaina ba.
Idona banda ɗan ƙyaƙyafta su babu abin da nake yi,wani irin iska ne ke kaɗawa wanda ya yi sanadin faɗuwar mayafina daga saman kai zuwa kafaɗa nan take gashina ya soma tashi sama har yana rufe mini fuska.Baza ido nake yi ina son hango Maryam sai dai ban ganta ba,ina juyawa na hangi Jabeer da sauri na nufi can.Sam ban yi lura da tawowar Mu'azzam ba wanda shi ma hankalinsa yake kan waya sai ji na yi na kai masa karo.Na yi baya zan faɗi amma kuma sai na yi saurin cabko hannunsa hakan yasa na dawo gaba sai dai fa tsayuwa kan ƙafafuna ta gagara.Ga mahaukacin ƙamshin da yake zubawa ya fi na kullum,ga kayan jikinsa waɗanda faɗar tsadarsu ɓarnar baki ne ga kuma rikitatun idonsa da ya tsoma cikin nawa.Duk suka taru suka ruɗa ni,hasken cameraru ne ya dawo da ni daga kogin kallonsa da nake yi ,shi ma da dukkan alamu ya shagala da kallona.
Wasu daga cikin waɗanda aka gayyato ne suka soma yi masa congratulations da samun kyakkyawar mata irina.Maimakon ya ce musu ba matarsa ba ce a'a sai ma dai idonsa da yake ci gaba da kallona da su,daga bayana na ji muryar Maryam da sauri na tafi na bar shi har ina shirin faɗuwa.
“Shi ne kika wani tawo kika bar ni can ɗaki” na faɗa ina mitsike mata kumatu,ta yi murmushi kafin ta ce “ki yi haƙuri anty Fatee zo mu je ki zauna” haka ta ja ni muka zauna kan kujerun da aka tanada don zama.Maimakon ta zauna ita ma sai ta tafi ta bar ni,duk sai na soma jina a takure ina jin kaɗaici na mamaye ni.Kamar walƙiya haka na soma ganin wani abu mai ƙyalƙyali na wasa da hankalina,a hankali na miƙe tare soma dosar can cikin shuke-shuken .Sam ban farga da na bar cikin gidan ba sai da na soma jin ƙarar ruwa,da na duba da kyau sai na ga ashe ƙasurgumin dajin nan ne na ɗazu.Ina shirin takawa baya don komawa kawai sai ji na yi na rumza ƙafata ta maƙale a cikin wani rame.Daidai nan wurin ya ɗauki matsanancin duhu,sai kuma wata murya da ta cika wurin baki ɗaya.
“Ke ce wacce aka zaɓa domin kammala mission mai muhimmanci. Dukkannin ƙarfin iko na power da suke ɓoye a jikinki su ne makulin da za ki ceto duniyarmu wacce aka rushe.Amma kafin nan dole ki zauna ki koyi yarenmu na ƙarnin baya,sannan ki san muhimmancin TUKUNYAR MAYU da kuma abin da take nufi” muryar na gama faɗar haka sai na ji ƙafata ta fito yayin da kuma wata ƴar mitsitsiyar tukunya kamar wacce Bugaje ke yin shayi ta bayyana a hannuna na haggu.
Daidai bakin tukunyar shayin wani hayaƙi ya soma fitowa mai yawa,ina taɓa shi wani irin shock ya damƙe ni kamar na lantarki dukkan idanuwana suka firfito yayin da kuma wani girgije ya bayyana a gare ni wanda ya hasko mini dukkan rayuwata ta baya da kuma ta wacce da zan yi a gaba.Lokacin da shock ɗin ya sake ni,sai na ji tamkar na ƙurmar ihu jin wai ba Mama ce mahaifiyata ba,sannan Mu'azzam yana ɗaya daga cikin ƙaddarar rayuwata wanda aka umarce ni da na kare daga sharrin abin harinsa.
Ido na lumshe tare da motsa laɓana,iska ne ya fige ni ya kawo ni can gidan Mu'azzam a kuma ɗakinmu.Zaune na yi dirshen a tsakiyar ɗaki ina kallon ƴar butar shayin wacce a zahiri ita ce TUKUNYAR MAYU da duk ƙasar Kamaru da kewayenta ke cece-kuce a kai.A zuci na ce ‘ kenan duk mutanen da ke ikirarin akwai tukunyar mayu a asibitocinsu ƙarya ne?’ wani ɓangare na zuciyata ne ya bani amsar ’eh duk ƙarya ce, wannan ta hannunki ita ce ta gaske kuma mallakinki ce,ke ce Goddess kuma ke kike da alhakin kula da ita’
Wani murmushi na yi na samun wata rayuwa a wata duniya ta daban kafin na yi wani furici kamar ƙyaftawar ido kuwa na tsinci kaina a cikin ƴar ƙaramar tukunyar,ta ƴar hudar nan na fito sai dai ba a siffar mutum a macijiya.Direct wajen taron ƴan diner na fantsama ina gudu haɗi da ziro harshe .
Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group za ta biya 509 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822.Don Allah ga detail nan in kina so ki tura kai tsaye ki bani shaidar biya,wacce ta san kuma ba ta shirya ba ki yi wa girman Allah kar ki yi mini Magana
*NB:* yanzu nake typing 18.08.25 in kuma na kammala shi 1k ne kuɗinsa.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels