Share this page
2 / 7
ce “zan yi komai akan Anita sai dai fa Daddy ban san gidansu ba?” “Kar ka damu,mu da muke da Father duk zai faɗa ma.Mu je ka ci abinci”Cewar Daddy ya na mai jan hannun Bobby suka sauko ƙasa. Umarni ya bada aje a gyara ɗakin Bobby ɗin,Mamy kuwa da mamaki ta ce “ya haka? Ka shiga da fushi ka sauko da murna?” Bobby ya shagwaɓe fuska ya ce “ a bani abinci yunwa nake ji” “Jansh? Janash ?” Mamy ta ƙwala kiran ƴar aikin nasu,da saurinta ta fito ta na mai amsawa “ki zo ki yi saving ɗin mu kafin ki ci gaba da aikin ki” duk suka samu wuri suka zauna,Janash ta zuba masu frite da niƙaƙen nama suka fara ci su na hira. Daddy ne ke shaiwa da Mamy yadda lamarin tsafar da Bobby ya kasance a ƙarshe ya ƙara da “Ruhinsa na da ƙarfi sosai wannan ya sa Father cewa a fara tun yanzu don akwai jan aiki a gabanmu,sam ban yi tunanin Bobby zai fito da rai ba yadda na dutsen Barclay ya ƙi karɓarsa ” “Kar ka ji komai,ai tun ranar da na haife shi na faɗa ma Ɗana waliyi ne ya na da wata baiwa ta musamman ”Mamy ta faɗa ta na murmushi. Bobby ya ce “oh! Na manta bari na je na ɗauko wayata ina son jin su Kameel” ya faɗa tare da tashi ya nufi ɗakinsa. Wayar ya ɗauko sannan ya fito zuwa filin training inda yake wasar mashi da ta doki.Cikin rumfa ya shiga sannan ya buɗe data, group ɗinsu na su uku ya shiga ya yi masu hi! Ai kuwa dama duk su na online su ka maido.Hira suka fara taɓa wa,hannun Bobby har rawa yake wajen rubuta masu abubuwan da suka faru.Tuni suka ruɗe wanda har ta kai su da bada wurin haɗuwa domin su tattauna. Da sauri Bobby ya koma ɗaki ya shirya tsaf,cikin motarsa ya tafi can gidan shakatawar.Har sun zo,hannu ya basu suka gaisa sannan ya samu kujera ya zauna “Mu fara cin abinci kafin ka bamu labarin al'mara ” cewar Kameel ya na dariya don shi sam bai yarda da maganar ba. “Ni kam na ci abinci kafin na fito zan sha da lemu” Bobby ya faɗa. Fadeel kuwa sam ya kasa cewa komai sai tunani yake in kuwa hakan gaske ne ya zama dolai shi ma ya je. Bayan an kawo masu abubuwan da suke buƙata Bobby ya ƙara jadadda masu komai kamar dai can farko. “Aboki ka ce ita mai gadin wurin mace ce,kuma wurin na da haɗari ? Kaiii ban yarda ba” cewar Kameel. “Amma mi yasa Daddyn ka ya kai irin wannan wurin mai haɗari? AOKIGAHARA fa duniyar fatale ce,duk wanda ya shiga dajin ba zai dawo da rai ba,in ma ka fita da ran to fa a mahaukaci ne kawai” Fadeel ya faɗa cike da nutsuwa. “To ni dai kam mun je,in kuma ba ku yarda ba sai ku shirya na kai ku ” “abin da ke raina kenan,amma yadda Kameel ke da tsoro ina ga ba zai iya zuwa ba” Fadeel ya faɗa ya na dariya. Kameel ya kai shawarma bakinsa ya ce,“in za ku je mi zai hana ni zuwa?” “Bobby tunda haka ne yaushe za ka kai mu?” Fadeel ya tambaya. “Duk lokacin da kuka shirya” Bobby ya basa amsa. “Awa ɗaya ce daga nan zuwa AOKIGAHARA ina ga mu na iya tafiya yanzu” cewar Fadeel cike da zaƙuwa. “Dare na iya yi mamu a hanyarmu ta dawo wa,ku dai bari har gobe” Bobby ya faɗa. “Hum! Dama nace ƙarya ce,ga gaskiya nan ta bayyana sai kwana-kwana ka ke” Kameel ya faɗa don shi sam bai yarda ba. “Ku tashi mu tafi” Bobby ya faɗa ya na miƙewa tsaye,“da motocin za mu je ko mu tafi da ɗaya kawai?” Fadeel ya tambaya. “Mu je da ta Bobby kawai ,in mun dawo sai mu biyo ta nan ka ɗauki taka” Kameel ya faɗa. Haka kuwa aka yi suka shiga mota ɗaya,Fadeel shi ne ke driving Bobby na gefensa yayin da Kameel ke zaune can gidan baya. Hanyar da za ta kai ka dajin sam dama babu wasu gidaje sai irin uwannan mutanen maras galiho da suke ɗan buga gidan roba.Tafiyar awa ɗaya da rabi suka bisanin su kawo ƴar siririyar hanyar da za sada su da can cikin ainahin dajin. “Mota ba ta shiga” cewar Fadeel ya na samun wuri ya yi parking duk suka fito. Bobby ke gaba su na binsa baya,ko tako goma ba su yi ba suka ji wata irin ƙara ƙiiiiii! Suka waiga a tare mi za su gani? Hanyar shigowa ta rufe ruf.... ★SENEGAL Wasu ƴan mata biyu ne zaune kan capet,su na cin kayan marmari.Kallo guda za ka yi masu ka san ƴan gata ne,duba da yadda baƙar fatar su take wuwulniya ta na sheƙi kamar ka lashe. A tare suka ɗago suka kalli ƙofar shigowar,“mtsss!” ɗaya daga cikin Twins ɗin ta yi tsaki,yayin da ɗayar kuma ta amsa sallama cikin sanyin murya ta na mai cewa “wa'aleykum salam! Kawun ina wuni? Ya hanya ya kuma iyali?” Wanda ta kira da Kawun,ya ƙarasa shigowa ya na amasa wa ya ce “lafiya lau Zahra ,ya wajen ku fatan na tarar da ku lafiya?” “Ba a sani ba! In ba tsabar iya yi ba ai ka gan mu ƙalau mine ne na tambaya? To Abba bai nan sai a tattare tsamokaran tsumman da aka kwaso ƙafa aka zo da su mtsw!” Kawu ya ce “Bintu ina matsayin Yayan ubanki ki ke ja min tsuki? Eh lalle! Amma ba laifin ki ba ne,laifin wannan munafukar uwar taki ce da take koya miki fitsara” Bai ida rufe bakinsa ba wata kyakkyawar mata ta fito ta na cewa “hayaniyar mi nake ji haka ne kamar ana yaƙin duniya?” su na haɗa ido da Kawu ta wani yamutsa fuska ta na haɗe rai ta ce “Yaya Mansur ne?” “A'a ba ni ne ba! Wato Hajara bayan kin mallake ƙanena shi ne kuma ki ke koyar da ƴaƴansa mugun hali ko? ” “Eh ta je ta...” uwar tsawar da aka daka mata ce ta sa ta yin shiru ta na turo baki haɗi da kallon Abban nata. “Ya Mansur ina wuni? Ya su Inna fatan duk su na lafiya?” Abba ya faɗa cike da kulawa. Mansur wanda suke yi wa laƙabi da Kawu ya haɗiye wasu yawun baƙin ciki ya na kallon gizner Ƙanen nasa wanda su biyu tal uwarsu ta haifa. “Alhamdullah! Dama zuwa ne na yi tunda kai an shanye ka ba ka da ta cewa ka auro alaƙaƙai.Yanzu Ayub shikenan ka tsinke igiyar zumuncinmu? Yaushe rabon ka da ƙauye ? ” “Don Allah Yaya ka zauna ,ko fa ruwa ba ka sha ba amma ka fara yin ƙorafi.Maman Twins haɗa wa Yaya abubuwan motsa baki” Abba ya faɗa ya na mai jawo hannun ɗan uwansa ya zaunar da shi kan salon. Bintu ta yi wani saurin tashi ta na toshe hanci,sarai Kawu ya ganta.Momy kuwa ba don ranta ya so ba ta shiga kitchen,ba a jima ba sai ga ƴar aikinsu ta shigo da tray ta ajiye a gabansa. Saboda mugun kari irin na Kawu ƙiri-ƙiri ya ƙi cin komai.Ji yake kamar ya shaƙe Abba ya mutu don ya gaji dukiyarsa. “Don Allah Yaya ka yi haƙuri in sha Allah sati mai zuwa zan je ” “Hum! Kullum haka ka ke faɗa,daga ƙarshe kuma ka ƙi zuwa” “Wannan karon in sha Allah zan je kar ka damu” “Zan koma,dama don na yi maka tuni ne akan haƙin da rataya kan wuyanka tunda an juye ma kwanya” cewar Kawu ya na miƙewa. Abba ya yi murmushi,ya san halin Yayansa sosai.“Haba Ya Mansu kar sheɗan ya hana ka yin aikin lada,duba fa da niyyar kwana ka zo tunda ga kayan ka nan ma ka zo da su.Yi haƙuri ,Zahra tashi ki gyara masa ɗakin baƙi” Da “to Abba ” ta amsa kafin ta miƙe,ta je ta ƙara gyara ɗakin sannan ta kwashi duk abincin da aka kawo wa Kawu ta kai masa can masaukinsa. Abba ya fita dama wajen aiki zai je, Kawu kuwa ya na shiga ɗaki ya fiddo tarkacen layun da bokansa ya basa kafin ya maida su ya na dariyar mugunta..... Share please [16/07 à 08:07] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 5_6* Bayan Kawu ya ci ya ƙoshi ya yi kwance sai faman murmushi yake.Dare na yi ya fara aiwatar da aikinsa duk ya bi gidan ya turbuɗe da layu. Washe gari Abba ya basa kuɗi masu yawa ya ce "ga wannan kafin na dawo" Kawu ya karɓa ba godi balle na gode ya saka aljihu . Falo ya fito ya zauna kan kujera ya na kallon TV,Bintu ta Zahra ne suka fito cikin shigar kaya kala ɗaya don komai nasu iri ɗaya ne wannan ya saka ba kowa ke iya banbance su ba,sai da halinsu don Bintu fitsararra ce ta ƙarshen aji,ita kuwa Zahra babu ruwanta asali ma tsoro ne da ita. "Ina kwana Kawu an tashi lafiya ?" "Lafiya lau tauraruwa alhamdullah ya fama da mai mugun hali?" Sai da Zahra ta ɗan yi murmushi ta kalli ƴar uwarta Bintu ta ce,"sai haƙuri Kawu" "Kin fi ƙarfin ko gaishe da magajin ubanki to ina kwana?" Kawu ya faɗa ya na hararen Bintu .Ita kuwa baki ta zumɓuro ta na gunguni,"kin yi wa ubanki Ayuba da uwar ki Hajara shigiya fitsararra wacce sheɗan ya yi ma fitsari akai" "Ni dai ba shegiya ba tunda da ubana kuma har aka kwaso jiki aka zo wajensa don cin banza..." Bintu ke faɗa cike da rashin kunya,Mama ta katse ta "Bintu mi na faɗa miki? Ban ce kar na kuma ganin kin yi wa babba rashin kunya ba?" "Mama shi ya fara ja na fa" ta faɗa a shagwaɓe. Jiki na ɗan rawa Mama ta ida sauko wa daga step ɗin ta na taɓa hannuwa "Yayan mahaifin naki ki ke faɗar shi ya fara jan ki?" Wani irin dundu ta kai mata a baya kafin ta balbaleta da masifa. Kawu Mansur ya yi wani murmushin mugunta,ƙasan zuciyarsa fal farin ciki. "Ya Mansur don Allah ka yi haƙuri ka san har yanzu ƙurciya ne da ita,duka 15years babu yawa" "Ko ma dai mine ne ai ke ki ka koya mata,kin ga ma tafiyata" ya na gama faɗa ya shiga ɗaki ya a haɗe kayansa ya koma can ƙauyensu *Djifer*.Ɗansa babba Halilu ya tarbe shi,"Baba ya ya komai ya tafi daidai ?" "Fiye da yadda ka ke tunani,kawai ka fara shirin zuwa kamun kifi gobe wanda za a yi masa girki" Halilu ya washe baki ya ce "Baba har na matsu garin Allah ya waye wayyo daɗi " "Ai wannan karon ba zai kubce mana ba,yadda na bi ƙa'idodin da boka ya ce tabbas zai zo.Wai ka ga yadda shegiyar matarsa ke min ladabi? Da zan tawo har da haƙuri ta yi ta bani hhhhh" Halilu ya ce "Haba dai? Kenan ita tuni asirin ya fara aiki a kanta? " "Eh sosai! Shi ma uban gayyar har wani rawar hannu yake da zai bani kuɗi inda can farko ne bai wuci ya bani dubu goma ba" "Baba ka san kuwa ina son Bintu?"cewar Halilu ya na wani karkace baki. "Mu bar wannan maganar ka ji! Bari na shiga daga ciki" Halilu ya bi bayansa da kallo kawai ya na jin ko sama da ƙasa za su game Babansa bai isa ya hana shi auren Bintu ba. A can kuwa ɓangaren Mama sosai take mugun shakkar Kawu Mansur ɗin.Sam zuciyarta ta ƙi sukuni,haka ta kira Daddy murya na ɗan rawa ta ce "Baban Twins Kawu fa ya yi fushi ya koma Djifer(ƙauyen su) ina ta basa haƙuri amma ya ƙi saurarena" yadda Abba ya ji hankalin matar shi a tashe ya ɗaga nasa hankalin babu shiri ya dawo gida. "Kawai ka je Djifer ka basa haƙuri" cewar Mama. Abba ya ce "ina da aiki sosai a office sai dai zuwa gobe,mine ne ya faru har ya yi fushin?" "Bintu ce ta masa fitsara,ka san ba mutumci ne da ita ba" "Ina take?" "Sun tafi makaranta" "To ki kwantar da hankali don Allah,zan je na basa haƙuri har gida" "To Allah sa ya haƙura ɗin,sam zuciyata babu daɗi baban Twins" Kumatunta ya ɗan bubuga tare da rarrashinta,dakyar ta barsa ya koma can wajen aikinsa. Makarantar islamiyya ce suka tafi,ba wani sosai suke maida hankali ba ga karatun amma babu laifi sun iya karatun sallah.Zahra duk hankalinta ta tattare wuri ɗaya ta miƙa wa malam wanda yake karatu kan Tauhidi. Bayan sun taso daga makaranta ,su na shigowa falo suka tarar da Mama ta rabka uban tagumi. "Mama ina ta yin sallama ba ki amsa ba" Zahra ta faɗa ta na mai durƙusawa ta cire mata tagumin. "Har kun taso?" "Eh Mama" su yi gamon baki suka amsa mata. "To ku je ku yi wanka ku ci abinci" "Mine ne ke damun ki Mama?" Zahra ta tambaya. "Babu komai kawai zuciyata ce nake jin ta yi min nauyi babu daɗi sai ƙunci" Mama ta faɗa kamar wata sakarya. "Zai wuce Mama ki yi ta addu'a " Ɗakinsu suka wuce ko wace ta yi wanka ta saka kayan shan iska.Su na cin abinci su na hira,Bintu ce ke bata labarin barkwanci da kuma na ban tsoro ita kuwa baiwar Allah Zahra har tsoratar take. Da Abba ya dawo sosai ya yi wa Bintu faɗa ,kafin ya haɗe su da Zahra ya yi masu nasiha.Mama na daga gefe ta bi ayari ta yi shiru kai kace sabuwar musulunta. Washegari Ƙauyen Djifer Abba ya yi sammako.Daidai ƙofar gida ya parker motarsa sannan ya fito ya shiga bakinsa na shirin yin sallama ya ji ƙafarsa ta yi wani girrr. Halilu da ke tsaye ya na wankin kifi ya ga komai sarai ya ce "ka shigo mana Baban Twins " Abba ya haɗiye wasu yawu dakyar sannan ya shigo,"babu kowa gidan?" "Baba da Inna sun tafi gona,Habiba kuma ta na ɗaki ta na yi wa Tsohuwa tausa" Halilu ya basa amsa. Abba ya sake matsawa ya yi sallamar da ya so yi tun a bakin ƙofa,aka amsa sannan ya shiga. Mahaifiyar tasa wacce suke kira da tsohuwa ya gaida bisanin ya yi zaune,Habiba ta gaishe shi ita ma ta na fitowa waje. "Ga ruwa nan a langa ki kai masa ya sha" "Halilu daga zuwansa ?" "Na ci uwarki ki ɗauka na ce" Habiba na zumɓurar baki ta ɗauki ruwan wanda ainahi boka ne ya bado su ta kaiwa Abba .Cike da ladabi ta ce "an kwaso hanya ga ruwa nan Abba " ta ajiye a gabansa ta fita. Abba ya ɗauki ruwan ya sha kaɗan ya ajiye.Ya na nan zaune sai ga Inna matar Kawu ta shigo,gaisawa suka yi ya na mai tambayarta "ina Yaya Mansur ɗin?" "Ya shiga banɗaki yanzu ya fito" Kawu Mansur kuwa ya na gun Halilu da ke faman gasa kifi sai barbaɗa magani suke su na hira ƙasa-ƙasa. Abba da ya gaji da jiran shigowarsa ya fito ya na mai kiran sunansa.Kawu Mansur ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba,sannan ya zo suka gaisa da ƙanen shi. "Ina dawowa gida aka ce min har ka tafi,shi ne na zo na ji in lafiya?" Abba ya faɗa . "Hum! Ta ga dama ta baka dama ka zo?" "Don Allah Yaya ka bar wannan maganar ai dai gani na zo ta ƙorafi ta ƙare" Kawu Mansur ya ɗan washe baki tare da rungume Abba ya ce "har na ji daɗi ƙanena,Habiba shimfiɗa min tabarma can gidin bishiya mu yi hira ni da ƙanena " Ganin murmushi kan fuskar Kawu Mansur sai Abba ya ji wata irin nutsuwa. Kan tabarma suka zauna su na hira ,kafin Halilu munafiki ya kawo hasashen kifi babba da ƙarami "Baban Twins wannan ne naka ,Baba kai kuma ka yi haƙuri ka ci wannan tunda kullum ka na ci" cike da munafurci yake faɗa tare da ƴar dariya . "Babu komai ka basa har da nawa ɗin,ka je ka ƙara kamo wasu sai ya tafi da shi can gida" cewar Kawu Mansur ya na kishingiɗa. Abba kuwa a duniya babu abin da ya fi so kamar kifi wannan ya saka babu jira ya fara ci,ya ce "a'a Yaya wannan ma ya ishe ni" jin haka ya saka Mansur ɗaukar nasa shi ma ya bi bayan Halilu suka koma can bayan gida su na ƙyalƙyata dariya. Tsohuwa ta fito waje,"tsabar mugunta a gasa kifi shi ne ba za a ban ba?" Ta faɗa ta na tako a hankali. Abba ya yi saurin raba wa biyu ya bata rabi, tsohuwa ta fara ci ta na saka masa albarka. Kawu Mansur ya na dawowa ya ga kifi a hannun tsohuwa da mugun sauri ya ƙaraso ya na cewa "Tsohuwa ba dai kifin ne ki ke ci ba?" Abba ya ce "Ni na bata ya na ga hankalin ka duk ya tashi?" Kawu ya haɗiye wasu yawu ya ce "a'a babu komai" Sai marice lis Abba ya koma can gida. ★JAPON “Kar ku ji tsoro ai dama haka ne ƙa'idar dajin da zarar ka shiga yake rufewa ” Bobby ya faɗa ya na saka masu murmushi bisanin su ci gaba da tafiya. Kameel ya yi ihu ya na mai dawowa tsakiyar su Fadeel. “Lafiyar ka?” “Wlh ji na yi kamar an taɓa kafaɗata” Kameel ya faɗa . “Ku Afirka wa Allah ya yi ku da shegen tsoro,mu uku ne kawai to wane ne ya taɓa ka ɗin?” cewar Fadeel cike da masifa. “Oho! Dai ina na nan tsakiyar ku ba zan gusa ba,dama ku da Aljannu banbacinku kaɗan ne”Kameel ya faɗa ya na wani riƙe rigar Bobby shi da ke gabansa. Duwarwatsu ne ta ko ina yayin da gayen ya yi kore tsanwa shar,dajin tsit ba ka jin komai sai kukan tsuntsaye da kuma sawun sawayensu. A haka har suka shigo tsakiyar dajin inda yake mai faɗin gaske."Ƙwaƙwaƙwa! Tsutsutsu! Tsitsitsi!" Kawai ke tashi kamar ana ruwa. Kameel ya ɗaga kansa sama,ido huɗu suka yi da wani tsuntsun mai manyan ido ya tattakura ya fasa ƙara ya na cewa “wayyo! Aljani! Aljani! Ku duba ” Su ka kece da dariya Bobby ya ce “mujiya ce fa! ” Fadeel kuwa ƴar bangar Kameel ya yi sannan ya ce,“haka ake aljani? Mtsw! ” “Ku biyo ni wannan ita ce hanyar shiga kusurwar dajin inda bishiyoyi ke magana” cewar Bobby ya na mai yin gaba suka take masa baya,Kameel sai waige-waige yake a haka har suka iso ƙofar shiga NOIRA wanda yake tamkar kogo. Yau babu mai gadi,Bobby ya fara shiga sannan Kameel a ƙarshe Fadeel . “Hiiyihiyi! Zhumm!” haka kogon ya fara ɗaukar wannan sauti bisanin ya fara juyawa kamar majaujawa. Mutane masu fararen shiga suka fara ketowa ta ko ina su na dariya,wacce sautinta kawai ake ji amma ba a ganin fuskokinsu sai ƙwarangwal. Abin da bai kashe Kameel ba, lokacinsa ne kawai da bai yi ba.Wani uban tsalle ya yi ya ɗale jikin Fadeel wanda shi ma a tsorace yake. Bobby ne ya fara magana “kar wanda ya cutar da su abokaina ne,kar ku matso kowa ya tsaya inda yake” ya na maganar ne idonsa na ɗaukar wani irin haske . Da sauri duk suka fara ja baya,domin hasken ba ƙaramin cutar da su yake ba. “Kar ku ji tsoro ina tare da ku” Bobby ya faɗa wa abokansa,“Bobby ka fitar da mu don Allah zuciyata za ta tsinke” Kameel ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Fadeel ya wani cire shi daga jikinsa ya ce “ƙaton banza matsoraci! Buɗe ido ka ga yadda fatalwa ke tsoron Bobby saboda miracle ɗin da ke fitowa a idonsa” Kameel ya buɗe ido ya sauke su kan Bobby wanda har zuwa yanzu idonsa ke fitar da haske kamar wanda aka saka masa ƙwan fitila a ciki. “Matsafi! Bobby kai matsafi ne?” Kameel ya faɗa cikin ɗaga murya ya na waro ido. Dirar mikiya NATA ta yi masu ta ɗauke Kameel da Fadeel ta yi sama da su, bisanin ta fara magana cikin fushi “ka aikata babban kuskure na zuwa da bare a cikin kogon NOIRA wanda babu mai shigarsa sai wanda aka yi wa wankan TSAFI.Wannan kusurwa ce ta musamman domin members kawai,don haka zan saka abokan ka gidan Yari in ka na son su to ka kawo sacrifice ka fanshe su” ta na gama faɗar haka ta jefa su Kameel cikin wata raga da ke can rataye ga icce. Bobby ya ɗaga kai ya kalli abokansa sai ihu suke su na neman agaji. Hasken idonsa sam basa iya yi wa NATA komai. Murya na ɗan rawa ya ce “Ki yi haƙuri daga yau ba zan sake ba” Nata ta sauko ƙasa ta na mai komawa ƴar matashiyar budurwa ta ce “a wannan duniyar ba a san kalmar haƙuri ba,jini ake bayarwa a maimakonta.In ka na so na sauko ma da su to ka kawo jinin ƴan yara biyu da ba su balaga ba kafin nan da faɗuwar rana” ta na gama faɗar haka ta wani hura masa iska a fuska,Bobby bai tsinci kansa a ko ina ba sai a waje kusa da inda suka ajiye mota...... [17/07 à 11:26] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 7_8* Bobby ya dafe kansa ,ya na mai sake duba yanayin garin da tuni duhun magrib ya fara ketowa.Tunaninsa ɗaya ina zai samu yara biyun da za ayi sacrifice ɗin? Ya na mugun son abokansa sai dai sam ya rasa tudun dafa wa. Keey ɗin motar ma ya na can ga Fadeel ,a hankali ya fara yin tafiya bisanin gundu. Ya gaji sosai,sai dai yin gudun shi ne mafita gare shi.Sama da minti ashirin kafin ya zo bakin hanya wacce take tsit tamkar an shareta. Bobby ya riƙe ƙugu ya na haƙi tare da waige-waige,bai da nisa da dajin AOKIGAHARA ɗin wannan ya saka yake iya ganin abin da ke faruwa. Wasu irin gizai-gizai ne baƙi ƙirin suka haɗu daidai dajin kawai sai walƙiya yake.Gaban Bobby ya faɗi,in ba zai manta ba ya na ɗaya daga cikin abin da Sarkin ruwa ya shaida masa.Da mugun sauri ya koma,ya fara gudu kamar ransa zai fita har zo hanyar da za ta sada ka da dajin. A buɗe take,kawai shiga ya yi har ya isa ciki. Kogon NOIRA ya shiga,ko tako biyu bai yi ba ya ji muryar Nata a bayansa “ina yaran biyu da aka ce ka kawo?” Bobby ya juyo suka haɗa ido da ita,muƙut! Ya haɗiye wasu yawu bisanin ya ce “ban san inda zan same su ba” Nata ta shiga ƙyalƙyata dariya har sai da ƙasa ta amsa bisanin ta ce “Sacrifice ya zama dolai,ko kum....” ba ta ida kai ƙarshen maganar ba ta ji murya Marlin bayanta. “Nata ki kawo mana su can gaɓar Teku ” Da mugun sauri Bobby ya juya ya na ganin mahaifinsa ne ya ji wani sanyi a ransa.Sai dai yadda fuskar Daddy take kicin-kicin ya saka Bobbyn shan jinin jikinsa. NATA ta ɗauko Kameel da Fadeel uwanda tuni sun fara fita hayyacinsu ta kai su gaɓar Teku .Daddy na fita Bobby ya take masa baya har suka isa can gaɓar ruwan. Tuni an cire ma su Kameel kaya an saka su cikin ruwa,Bobby ya yi tsaye kawai ya na kallon Mohan da Martan. “Ka matso kusa” Daddy ya umarci Bobby ,a sanyaye ya matsa tare da jerawa layi ɗaya da su ya rufe ido kamar yadda suka yi. Kogin na fara yin ruguuuu suka fara karanto ɗalasiman TSAFI.Bobby bai san ta yaya ba amma samun bakinsa ya yi da rera harafofin. An ɗauki sama da minti goma sannan kogin ya kwanta.Duk wata ajiyar zuciya suka sauke,Bobby ya kalle su a zuci ya ce ‘ko mi hakan ke nufi?’ Kameel da Fadeel suka fito cikin ruwa fatarsu na wani irin sheƙi ba kamar lokacin da suka shiga ba. Cike da murna Daddy ya rungume su ya na mai cewa “Barka da shigowa cikinmu yarana” ko wanensu murmushi kan fuskar shi ya amsa ma Daddy bisanin su je ga iyayensu. Kogon NOIRA suka dugunzuma,aka ci gaba da yi masu sauran tsibace-tsibace.Fadeel ya ɗauki baƙin tsafi,yayin da Kameel kuma jan tsafi.Bayan sun gama zaɓa aka basu wasu ruwa cikin wata tsohuwar ƙwarya.Ruwan baƙi ƙirin suke,su na shan ruwa duk illahirin gangar jikinsu ta ɗauki caji suka fara jin banbanci su

Chapter 2 of 7