yi magana kuma ka ga laifina.”
“Ko ma dai mine ne ɗan uwan ki ,in ba ki rufa masa asiri ba wane ne zai rufa masa?”
Ta turo baki kamar ya na ganinta ta ce “in ni aka yi ma abin da yake yi wa ƴaƴan mutane har kashe mutum zai iya! ”
Dad ya murmusa ya ce “shi ɗin garkuwar ki ce! Ya ne kin ci abinci?”
“Eh na ci sosai yau Habiba ce ta yi mana girki mai shegen daɗi ka san ƴan ƙauye sun fi kowa iya abinci gargajiya”
“Ah haba? To gaskiya ni ma gobe a kira Bestie ta yi min girkin na ci na ji in ya yi daɗi sai na bayar da tukuici”
Mardeeya ta shiga ƙyalƙyata dariya bisanin ta ce “Dad ai kuwa zan faɗa mata kawai ka shirya gift ɗin da za ka bayar,don Bestie maƙura ce wurin girki”
Ido ya lumshe ya na jin sotayyar Habiba na daɗa hauhawa a birnin zuciyarsa.
Washegari
Kamar kullum direba ne ya kai su makaranta,su Twins ya fara ajiye wa sannan ya wuce da Habiba .
A bakin ƙofar shiga makaranta ta ci karo da Haidar.Ta waro ido ta na kallonsa,“tun ɗazu ke nake jira,so nake na ga kyakkyawar fuskar ki kafin na je aiki” ya furta cikin taushin lafazi.
Wani mayen daɗi ne ya rufe zuciyar Habiba,ta ce “na gode sosai masoyi”
Ya ce “ki shiga kawai ni zan tafi ki kula da kan ki,ina son ki” bai bata damar da za ta mayar masa da martani ba ya yi saurin tafiyarsa ya shige motarsa.
Habiba ta bi motar da kallo har sai da ta ɓace ma ganinta.Ta ja ajiyar zuciya bisanin ta shiga daga ciki.Saman bayan mota ta tsinkayi Mardeeya,da ƴar sassarfa ta ƙarasa.
“Bestie albishirin ki? Jiya na baiwa Dad labarin girkin ki ya yaba sosai ya ce na gayyato ki yau ki yi masa shi ma ya na son ci” Mardeeya ta faɗa cike da zumuɗi .
“Ki ce yau zan ga Dad?”
“Eh! Mu na sauka daga makaranta sai mu wuce gidanmu ”
“Da wane lokaci zai zo?”
“Bai sanar da ni ba,amma dai ya ce girkin kawai yake son ci”
Habiba ta saki murmushin jin daɗi,bisanin su shiga aji.
Bayan sun sauka kamar yadda suka tsara haka suka wuce gidan su Mardeeya.
Haɗaɗen girki Habiba ta shirya kala biyu,tuwon shinkafa da ɗanyar kuɓewa sai kuma tuwon macaroni da miyar ganye.Ɓangaren lemu kuwa mai aiki ce ta yi ,Habibar na kallonta don har yanzu ba ta ƙware ta wannan fannin ba.
Mohan kuwa tun da wuri ya shigo cikin gari, office ya fara zuwa ya rage ayyuka sannan ya zo gida .
Mardeeya ya tarar a daidai wurin da yake cin abinci kullum ta na gyara table ɗin.Da murna ta tarbe shi ta na mai cewa “yawwa Dad gwara da ka zo yanzu,Habiba na can na saka uniforme wai gida za ta kar ayi mata faɗa”
“Ok zan shiga wanka,in ta fito ki ce ta tsaya sai mu gaisa ” ya na gama faɗa ya yi sama.
Mardeeya ta shiga ɗaki,ta kalli Habiba wacce ta mayar da uniforme ta tuntsire da dariya ta ce “wai duk tsoron kar a dake ki ne ya saka duk ki ka yi wani iri?”
“Mu je ki kai ni don Allah ban son surutu?”
“Dad fa ya zo”
Gaban Habiba ya faɗi ɗaram! Haka kawai ta ji zuciyarta ta shiga wani yanayi.
Mardeeya ta ci gaba da cewa “mu je in ku ka gaisa sai na kai ki gida”
Jiki a sanyaye ta fito,kan kujera suka zauna su na jiran saukowarsa.
Kamar minti goma haka,Dad ya fara saukowa har ƙarar sautin takunsa ake ji.
Habiba ta ɗaga kai ta sauke su kan dattijon da tuni farin gashi ya fara yi masa sallama.Su na haɗa ido gudun zuciyarta ya kusan tsayawa,a haka ta daure.
“Barka da fitowa Bestie ” Dad ya furta ya na yi mata wani kallon ƙasa-ƙasa mai cike da kwaɗayi,Habiba ta buɗe baki za ta yi magana kenan Kameel ya shigo......
*Masu karatu yanzu ne ƙaddarar Habiba za ta soma,na san kun fahimci labarin na tafiya ne daki-daki a sannu a hankali ko wacce Star ta littafin zan zayyano irin ƙalubalen da ta fuskanta.Mun fara da Bintu mai namijin dare,sannan Habiba wacce a halin yanzu ta faɗa son Kameel yayin da kuma shi Mohan ke sonta shin ya za ta kaya?* Sai ku biyo NI cikin book 2 wanda a cikinsa ne duk lamurran za su faru,ita ZAHRA babbar Star ɗin ko ɓangaren ta ban ɗauko ba🤩
Masu buƙatar shiga PAID GROUP za su biya 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte airtel ko Moov ta 200f
*NB:* daga lokacin da na kammala book ya zama complete 500 ne farashinsa.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels