Share this page
6 / 7
sai da ta tambaye ni ko lafiya ?” “Lafiya lau,ina nan ina ta fafutukar iya addinin Maman don ta bar min ke” Bobby ya faɗa. Anita ta ce “Ka na nufin larabci ka ke koyo ko kuwa karatun?” “Duka biyun” Ta ƙura masa ido,bakin na ɗan rawa ta ce “dama har haka ka ke sona?” Ya bata amsa da “Fiye da haka” Anita ba ta san lokacin da ta yi saurin kwanto shi ba,ta na mai kai bakinta kan lips ɗinsa.Mai son kuka an jefe shi da kashin awaki! Bobby kamar mai jira ya yi mata kyakkyawan masauki akan ƙirjinsa.... Wacce ta shirya payement za ta turo 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte Moov ta 200f [24/07 à 15:40] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 17_18* Yadda yake sarrafa ta a haukace ya saka tsoro yi wa Anita dirar mikiya a ƙawon zuciya.Ƙoƙarin cire gangar jikinta take,amma sam ta kasa saboda kamun sandar makauniya da Bobby ya yi mata.Mugun sonta sai ƙara bijiro da tsohuwar sha'awarsa yake,duk yadda yake ƙoƙarin controling kansa ya kasa .“Bo..b...byyy please ka bari har bayan aure” Anita ta faɗa cikin fizgar numfashi bayan ta ci nasarar zare bakinta daga na shi. Ido tab hawaye Bobby yake dubenta,sam ya kasa yin magana .Rabon da ya tsinci kansa cikin irin wannan yanayin tun ranar da ya kawar da budurcin Anita. Hannunta ya yi saurin kamawa ya ɗora saitin zuciyarsa da take faman bugawa,ta sani sarai a wannan lokacin babu abin da Bobby ke da buƙata illa ta basa haɗin kai bori ya hau.Waiwayen baya da kwanyarta ke yi mata na uwar azabar da ya gana mata shi ke daɗa tsoronsa a zuciyarta. Ta ya haɗiye yawu haɗi da jan ajiyar zuciya ta ce,“zan taimaka ma ka samu nutsuwa amma please kar ka kusance ni” “Don mi?” ya tambaye ta hawaye na zubowa zirrr kan kumatunsa . “Doli Maman za ta gane in na koma gida.Bobby tun bayan rabuwata da kai babu namijin da ya taɓa kusantata,hasali ma ban yi wani saurayi ba ka ga kuwa muddin mu ka yi sex zan sha wuya ne” Da sauri Bobby ya girgiza mata kai ya ce “ba zan yi miki da ƙarfi ba, please Anita ki fahimce ni zan iya mutuwa fa” ya na faɗar haka ne tare da kuma kai hannu jikinta ya na sarrafata. Ta rumtse ido gam,Bobby ya cirata cak ya ɗora kan bed.Sai da ya sha daga sosai kafin ya raba Anita da kayan jikinta.A halin da ta gansa kawai ya sa ta fashe da kuka,bai saurareta ba ya toshe bakinta ta hanyar saka nasa ciki bisanin ya fara kusantar ta. Kamar wata amarya haka take kuka da faman fizge-fizge,an ɗauki ɗan lokaci kafin ya koma gefe.Cike da jin haushi Anita ta miƙe ta shiga toilet, Bobby ya take mata baya . Cikin bawon wanka suka shiga,suka yi wankansu bisanin su fito su ci abinci da ke kan table. Kayan jikinta ta maida sannan ta yi masa sallama ta fita. Bobby kuwa wani tsadadden murmushi kawai yake saki,wata irin nutsuwa yake ji da salamar ruhi.Group ya shiga suka fara yin message shi da Fadeel don Kameel tun komawarsa Senegal ba kullum yake hawa online ba. ANITA ta na cikin mota ta na tunanin scène ɗin su da Bobby .Ta ci wuya ba laifi amma a wannan karon ta ƙudiri aniyar ba za ta barsa ba za ta dinga jure wa buƙatarsa. Ta na isa gida ta tarar da Maman a falo ta na karatun Alkur'ani. “Oh! Allah ” ta furta cike da gajiya bisanin ta zauna ta na cire takalmin ta . “Ina shopping ɗin da ki ka ce za ki yi?” Maman ta tambayeta ta na mai ƙare mata kallo. Gaban Anita ya faɗi,sam ta manta da ƙarya da ta yi wa Maman kan za ta be shopping ne alhalin don ta je gun Bobby ne. “Am .. Eh...Su na can cikin mota Maman,amma mi yasa ki ka tambaye ni?” da i'ina ta yi maganar. “Ina matsayin mahaifiyar ki bai dace na san inda ki ka je ba?” “A'a ban ce ba! Kawai dai na yi mamaki ne yadda aka yi ki ka tambaye alhalin lokacin baya ba ki yin haka” Anita ta faɗi haka ta na mai kwashe takalminta ta nufi hanyar bedroom don gudun wata tambayar. “Ya shi Mohamed Bobby ɗin ya na lafiya ko?” Da mugun sauri Anita ta juyo ta kalli mahaifiyarta sai kuma ta shige ɗakinta ba tare da ta amsa mata ba. Ta na nan zaune bakin bed Maman ta shigo. “Anita ke yarinya ce! Ki na tunanin za ki iya yi min wayo? Dubi yanayin ki haka ki ka fita? Ina kwalliyar da ki ka yi ? Haka nan kawai ta goge?” Maman ta jero mata tambayoyin. Anita ta ɗan rikice duk alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta. Murya na ɗan rawa ta ce “Maman na sani ! Na je gun Bobby amman babu abin da ya shiga tsakanina da shi.Ko kin manta na faɗa miki shi ma musulmi ne? ” “Ki yi hankali shi ne kawai abin da zan faɗa miki.Samun ciki a shekarun ki ba tare da aure ba shi nake guje miki.” Mama na gama faɗar haka ta fice.Anita ta ja wani dogon numfashi ta na mai faɗa wa kan bed ɗin ta yi kwance ta na kallon sama. ★SENEGAL Kamar jaririn da aka haifa yau haka suka zagaye wayar su na dubawa.Habiba zuciyarta fal farin ciki yau dai ta fara riƙe abun da su Twins ba su taɓa samu ba a rayuwarsu. “Na yi mamaki sosai da ki ka ce yau ne ku ka haɗu kuma har ya iya saya miki waya” Zahra ta faɗa. “Ya na sona ne shi yasa ke ma da zarar kin samu mai son ki zai saya miki ” Habiba ta bata amsa. Bintu ta ce “tun Abba na da rai kullum sai ya yi mana faɗa akan kar mu kula samari haka ma kar mu amshi abun hannun su to mi zai sa ta karɓa?” “Hhhh! Hassada ta dai ku ke yi in na gane,to na gaba ya yi gaba iyeee! Ƴan baƙin ciki” ta na gama faɗa ta miƙe ta fita daga ɗakinsu dama ta shigo ne ta nuna masu wayar. Twins suka kalli juna cike da mamaki, Bintu ta taɓe baki ta ce “Kin ga Zahra ki tashi ki ɗauki duk abin da ki ke so , Lilu ya ce zai kai mu asibiti gun Mama” “Can za mu kwana?” “Eh mana! Ko kin manta gobe weekend ?” “Amman ai za mu je islamiyya ” “Mtsw! Kullum ba mu na zuwa ba? Gobe ne kawai za mu yi fashi fa” “Ok to” Zahra ta faɗa ta na mai tashi ta saka kayansu kala biyu cikin wata jaka. Halilu da kansa ya zo ya yi masu magana suka fito ya sa su a mota ya kai su haɗaddiyar asibitin. Ko ina tsaf yake babu ƙazanta,a asibitin ba su buƙatar ƴan jinya likitocin ne ke kula da duk patients.In kuma ka na son ganin wani sai weekend. Da murna suka je suka rungume mahaifiyarsu wacce tsabar yadda ake kula da ita ya saka ta yi kyau. “Mama don Allah ki koma gida ” cewar Bintu. “Zan koma ƙarshen watan nan lokacin na iya tafiya da ƙafata ” “Mun yi kewar ki sosai” Zahra ta faɗa kamar za ta yi kuka. “Ni ma haka.Ya ya ƴan gidan? Fatan ba a takura maku?” Bintu ta ce “Hum! Kawu zai barin mu haka nan ba tare da tsangwama ba? ” “A'a bai da matsala ke ce ki ke takura kan ki” cewar Zahra. Bintu ta ce “Mama wannan da ki ke gani ba ta san ciwon kanta ba.Ko kin san da Kawu ya tursasa ni sai da na cire masa code ɗin system ɗin Abba ?” Mama ta yi murmushi ta ce “ki barsa shi da Allah ne! Haƙin zumunci kawai ya isa ya tambaye shi.Wai ban ma tambaya ba wa ya kawo ku?” “Lilu ne!” Bintu ta bata amsa. “Wane ne kuma haka?” “Wai Halilu kin san yanzu soyayya suke” Zahra ta faɗa ta na tuntsira dariya. “Kun ci abinci ne? ” “A'a sauri muke kar Kawu ya dawo ya hana a kawo mu” “Ok ku buɗe frigine akwai kaza da madara da kuma ayaba sai ku ci” Da murna suka je suka ɗauko,su na ci su na yin hira har suka gama suka shiga toilet suka wanke hannu. Hira sosai suke,bayan sun yi sallah isha'i ne wata nurse ta shigo ta kawo masu wasu ƙananan matala lakai-lakai guda biyu. Bisanta suka kwanta da dare ya yi. Bintu na cikin bacci ta fara jin sanyi na ratsa ta bisanin kuma wata zazzafar shafa mai shiga ɓargo.Ba ta san mine ne feeling ba sai a mafarki,tuni jikinta ya fara ɗaukar caji ta na jin daɗin yadda ake taɓa sassan jikinta.Lokacin da ya fara kusantarta tamkar ta yi ihu haka take ji don daɗi,a haka har ya gama ya sauka kanta.Daidai nan ta farka,da wani mugun sauri ta tashi zaune ta na mai dafe zuciyarta. Toilet ta shiga ,sai ta lura duk ta ɓata jikinta.Duk da ba ta da wani dogon ilimi amma a makarantar islamiyya an yi masu bayani kan babin wanka janaba da na jinin haila da kuma abubuwan da ke sharhanɗa wanka. A hankali ta kunna pampon ta yadda ƙarar ruwan ba zai tayar da su Zahra ba ta gabatar da wankan.Bayan ta gama ta yi alwala ta fito,a zaune ta tarar da Mama da sauri ta sunne kanta da ke ɗigar da ruwa. “Je ki kwanta Bintu kin wani zo kin yi tsaye” shi ne abin da Mama ta faɗa.A hankali ta ja wata ɓoyayyar zuciya,ta yi tunanin Mama za ta tambaye ta wankan mine ne ta yi. Kan katifa ta je ta kwanta,sai dai ta kasa yin bacci tunanin mafarkin nan kawai take yi wanda ba ta san dalilin yinsa ba . Sai wuraren asubahi ta samu bacci,wanda a ƙarshe Zahra ta tashe ta don yin sallah.Ta na gama wa ta ɓingire bacci. A zaune ta ganta cikin wani jeji mai furanni tsanwa sharrr.A gabanta kuwa wani kyakkyawan saurayi ne ya na sakar mata murmushi. Kyawunsa ne ya ja ta izuwa gun shi,kalaman soyayya ya fara faɗa mata ya na yi ya na shafar jikinta. Kan cinyarsa ta hau,ta ɗora bakinta kan lips ɗinta daga nan suka fara sarrafa juna,ya na gaf da ya kusanceta ta ji muryar Zahra ta daki dodon kunnenta. Kanta ya yi wani bala'in sarawa,cikin fushi ta tashi ta ce “mi aka yi ne?” “Ki tashi ki yi wanka sai mu ci abinci ” cewar Zahra,a harzuƙe ta ce “ban ci ” sai kuma ta yi luuuu ta koma ta kwanta. Idonta har wani dishi-dishi suke,cikin son ta koma baccin ya fara hura mata iska a fuska.Cikin sauri ya fara kusantar ta kamar abun yaƙi,ya na gamawa Bintu ta farka. Wannan karon haka kawai ta ji hawaye na yi mata zuba ba tare da ta san dalili ba.Can ta tsinkayi Zahra a zaune kusa da Mama su na cin abinci,dakyar ta miƙe ta shiga toilet.Baƙin cikin ganin yanzu ma jikinta ya ɓace ya saka ta fashewa da kuka,bisanin ta sakarwa kanta shower. Rigar da ta cire ta ɗaure kanta tamau don kar Mama ta ga gashinta a jiƙe.Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki ta fito,can gefe ta zauna ta shafa mai da turare sannan ta saka kaya. Duk abin da take Mama na ankare da ita kawai dai ba ta ce mata komai ba ne. Dakyar Bintu ta ci abinci, sam ta kasa sakewa saboda ƙuncin da take ji. A can gida kuwa Kawu Mansur sai da ya yi kamar zai daki Halilu da ya samu labarin ya kai su Twins can asibiti.Inna ce ta yi ta faman basa haƙuri,ita kuwa Habiba ta na can maƙale da waya ita da sabon saurayinta wanda tuni ya saye mata zuciya. Tsaf ta shirya cikin wasu riga da zane na atamfa,kamar yadda suka yi da saurayinta Haidar shi ya zo daidai inda ta kwatanta masa. Su na tafe a mota sai yaba kyawunta yake,ita kuma banda juya ido da murmushin jin daɗi babu abin da take a haka har suka isa gidansu Mardeeya. “Sai yaushe za ki koma gida?” Haidar ya tambaye ta . “Ina ga sai bayan sallar magrib,don yanzu aiki ne za mu yi sai kusan ƙarfe biyar baƙon nata zai zo” Habiba ta basa amsa. “Ok in kin gama sai ki kira ni,ki kula min da kan ki” Ta washe baki ta ce “to in sha Allah!” sannan ta fito. Mardeeya ta kira bisanin masu gadi su barta ta shiga,da ihu suka tarbi juna kafin Habiba ta aje jaka ta canza kaya sannan suka shiga kitchen. Yau kam mai aiki gefe ta koma ta na kallonsu, lokaci zuwa lokaci ta na ɗan taimakawa da abun da ba a rasa ba. Mardeeya kuwa sai murna take don tuni ta faɗa ma baƙonta da kanta za ta yi masa girki. Sai bayan sallah azahar suka gama,Habiba na fitowa daga kitchen ta yi kiciɓis da Kameel ya shigo shi da wata farar Baby sun nufi can saman bene. Wani takaici ne ya rufe ta ,a nan ta yi tsaye ta na kallon su har suka ɓace ma ganinta. “Oh! Nan ki ka tsaya? Bari na je na yi sauri na yi wanka” cewar Mardeeya ta na mai rugawa ta nufi ɗakinta. Sama da minti biyar Habiba na nan tsaye bisanin ,wata zuciya ta raya mata bin bayan su Kameel . Can sama ta hau,sai dai ta rasa wane ne ɗakinsa don ɗaki uku ne a gun.Har ta juyo za ta tafi wani sauti ya ja hankalinta.Da saurinta ta kai kunnenta jikin ƙofar,ta wani waro ido saboda kalaman da suke fitowa daga bakunan masoyan.Bugun zuciyarta ne ya tsananta bugawa da ƙarfi,yayin da kuma ta fara jin tamkar da ita ne Kameel ke tarayya.Hannunta har rawa yake wajen tura ƙofar ciki,ba tare da wani tunani ba ta kutsa kai ciki..... Masu buƙata shiga group 200 ne kacal kuɗin karatu,ki tura ta wannan account ɗin 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte airtel ko Moov ta 200f MRS SADAUKI 💫✍️ [25/07 à 11:46] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 19_20* Habiba ta kutsa kai cikin ɗakin,cak ta tsaya ta na faman zaro ido ta na kallon Kameel da budurwarsa da ke ta sha'aninsu kan kujera.Sam ba su ma san ta shigo ba,suratai da kuma kalaman soyayya kawai suke amayarwa. Ido na zubar da hawaye Habiba ta fito daga ɗakin.A sanyaye take saukowa daga step ɗin,direct ɗakin Mardeeya ta shiga ta samu bakin bed ta zauna.Tun da take ba ta taɓa ganin wannan lamari ba,ko a TV iya kiss ne kawai ta saba gani yau kam da idonta ba a mafarki ba sai ga shi ta yi kallon yadda ake tarayya. Ta wani zabura ta na mai rumtse ido da sauri,bisanin ta buɗe ta kalli Mardeeya wace ba ta tsaya da yarfa mata ruwan yatsunta ba. “Tunanin mene ne ki ke haka? ” “Babu komai” ta bata amsa ta na mai tashi ta shiga wankan ita ma . Bayan ta fito Mardeeya ta yi mata simple make-up ta zaɓo mata abaya irin na Makka . “Waooo! Amma dai ba aro ki ka ban ba ko?” “Kin ji ki da wani zance,to kyauta na baki” cewar Mardeeya. Cike da murna Habiba ta saka rigar,ta kuwa karɓeta tsaf ta yi mata kyau.Mardeeya kuwa cikin wani mahaukacin Sahari ta shirya kai kace ba'indiya don ma dai fatarta na baƙa. Falo suka fita,tuni mai aiki ta gyara ɓangaren da za a sauke baƙon.Selfie kawai suke da wayar Mardeeya,su na nan zaune har sai da ya zo. A tare suka fita suka tarbo shi,suka yi masa iso ciki.Tamkar ƙaramar yarinya haka Mardeeya ke zuba masa shagwaɓa shi kuma ya na biye mata. Bayan ta gabatar masa da Habiba ne sannan suka fara taɓa kalolin abincin da suka yi. Nader sai santi yake ya na yaba abinci, Mardeeya duk da ba wata uwar ta tsinana wajen girkin ba amma ta ji daɗi sosai. “Bari na tashi na baku wuri don ku zanta da kyau” cewar Habiba ta na mai miƙewa. Mardeeya ta ce “fara yi ma hoto ni da Habiby kafin ki tafi” Ta karɓi wayar ta fara yi masu hotuna bisanin ta je can ɗakin Mardeeya.Wayarta ta ɗauka ta kira Haidar ,kamar yadda ta ɗauki darasin shagwaɓa haka ita ma ta fara yi masa ai kuwa ta samu karɓuwa duk ta rikita Haidar. “In ki na yin shagwaɓa sai ki sa na zauce” Haidar ya faɗa. Habiba ta ɗan yi wani far da ido ta maƙale murya ta ce “ai na fi son haka Babyna,ko kai ba ka so ne?” “Ina so mana sosai ,ji nake kamar ace ki na kusa da ni” “Ko zuwa za ka yi ne?” “Kin gama komai ne?” “A'a sai zuwa an jima” “To ki bari har ki gama my dear ” Hira soyayya suka ci gaba da yi,ba su yanke kiran ba sai da Mardeeya ta zo nemanta. Har bakin motarsa suka yi masa rakiya,mai gadi ya shigar da tsarabar da ya kawo mata bayan kuɗi da ya basu dukan su biyun. Habiba har tuntuɓe take wajen shiga falon don duba kayan.Cike da mamaki take buɗe duk ledodin ta na mai tambayar Mardeeya “na ce halan kuɗi gare shi irin sosai ɗin nan? Dubi kayan nan fa sun fi 500k/mill kamar dai za a haɗa lefe” Mardeeya ta saki wani murmushi ta ce “Yanzu dai ki duba wanda suka yi miki sai ki zaɓi ko kala goma.Kaina na yi min ciwo zan shiga daga ciki” “Ki turo min hotunan da mu ka yi kafin ki kwanta” “Na gaji sosai ki duba a status duk na saka su” “Har da na Balaraben?” ba ta bata amsa ba ta shige cike. Habiba ta shiga zaɓar wanda za ta ɗauka,kamar daga sama ta ji tsuki.Ta na ɗago kai ta yi arba da Kameel da budurwarsa da dukkan alamu kuma ita macen ce ta ja tsukin. Kamar gumki haka ta tsaya ta na kallonsu,har suka fice.Hawayen takaici ta goge,ƙunci da ke naƙarƙasasar ruhinta bai hanata zaɓar kayan ba.Sauran kuma masu aiki suka shigar da su can ɗakin Mardeeya wacce tuni bacci ya ɗauke ta. Habiba ta kira Haidar ya zo ya ɗauke ta ,su na tafe su na hira har suka kawo ƙofar gidansu.Haidar ya kama hannunta ya ce “yanzu Baby sai yaushe?” “Gobe mana,ko ba za ka zo makarantar ba?” “Zan zo mana,amma kafin nan ai za mu yi waya ” “Ba ka gajiya da waya” “Son ki ne silar haka” “Hum!” “Allah kuwa Baby ji nake kamar kar mu rabu” Yadda ya yi furucin ya saka Habiba saurin kallon shi. Haidar ya nitsa idonsa da kyau cikin nasa ya fara aika mata da wani mugun kallo mai kashe jiki.Hannunta da ke cikin nasa ya fara ɗan matsawa,Habiba ta wani jan ajiyar zuciya ta na haɗiye yawu muƙut! Sai kuma ta kawar da kanta. “Ko na ture iyayena su nema min auren ki?” Haidar ya furta kamar mai shirin kuka.Da mugun sauri ta juyo ta ce “Aure kuma? Duka yaushe ne mu ka haɗu da kai shi ne ka ke min maganar aure?” “Habiba shi muradin zuci babu ruwansa da jimawar masoya,kin san irin yadda son ki da sha'awar ki suke azabtar da ruhina?” Ta maimaitata kalmar ‘sha'awa’ a zuciya. Ba ta san lokacin da bakinta ya furta “mi ka ke nufi da sha'awa?” “Buƙatuwa mana,ina son kasancewa da ke na ji ki rungume cikin ƙirjina ina kissing ɗin ki” Zuciyar Habiba ce ta fara bugawa da mugun gudu,yayin da madubin idonta kuma yake hasko mata video Kameel da budurwarsa.Nan take jikinta ya ɗau rawa,da sauri ta fizge hannunta da ke cikin nasa ta tura ƙofa da niyyar fita Haidar ya tsayar da ita ta hanyar ƙara riƙota. “Gida zan shiga ban cikin nutsuwata,in an jima za mu yi waya” ta furta cikin rawar murya,ba tare da ya sake cewa komai ba ya barta ta fita.Sam ta manta da ledarta wacce ta zubo kaya,shi ma haka. Ta na shiga gida ta tarar da su Twins su ma sun dawo.Zahra na karatu yayin da Bintu ke yin hira ita da Halilu .Kamar zararra haka ta nufi ɗakinta wanda ita kaɗai ce mallakinsa,direct toilet ta shiga ta tsabtace jikinta. Kan bed ta kwanta ta na tunanin abubuwan da suka shuɗe a yau, murmushi kawai take saki a haka har bacci ya ɗauke ta . Bayan sallar magrib Haidar ya yi mata text akan ya na ƙofar gida ta fito ta karɓi ledarta.Kallabi kawai ta ɗora kan kanta ta fita,can nesa da gidan su ta tsinkayi motarsa inda ke da ƙarancin haske. Tun fitowar ta ya ƙureta da ido ya na kallon shap ɗin ta mai tafiya da hankali duk wani lafiyayen namiji,har ta ƙaraso.Daidai ɓangaren da yake zaune ta tsaya haɗi da bubuga glass ɗin.Haidar ya buɗe tare da ziro ƙafa ɗaya.“Ƴan mata adon gari” ya furta ya na mai kallonta,Habiba ta ce “ina ledar take ban so Baba ya zo bai gan ni ba” hannu yasa ya jawo ledar ya miƙa mata ta ce “sai da safe ko?” “ɗan duƙo ki ji” cewar Haidar Habiba sokuwa ta ɗan rage tsawo kawai sai jin bakinsa ta yi kan lips ɗinta. Kai ta girgiza ta bar gun da sauri shi kuma ya yi ta dariya. Ta na ƙoƙarin shiga ɗaki muryar Kawu ta daki kunnenta “uban waye wancan mai motar?” Gabanta ya bada ras! Ko kafin ta kai ga furta wata kalma Kawu ya zo gabanta ya sharara mata mari sannan ya nuna ta da yatsa ya ce “daga yau sai yau kar na sake ganin kin kawo min ƙato a gida.Ban shirya yi miki aure ba karatu za ki yi ki je can na baki aikin offishi,in kuma na sake ganinsa a ƙofar gidana za ki sha mamaki” Da gudu Habiba ta ƙarasa cikin ɗakinta ta na kuka,ba ta yi jinkirin sanar da Haidar furucin mahaifinta ba.Shawarar farko da ya bata shi ne ita sai ta rinƙa zuwa wajensa su na yin hira,abun ka da zuciyar da ta kamu da so sam ita ba ta ga illar yin haka ba. ƘAUYEN JOAL Mohan ne hakimce kan kujerarsa ta alfarma,bayan ya gama ganin mutanen da ke zuwa wurinsa da sunan ya yi masu aiki shi ne ya zauna ya na hutawa.Ƙatuwar wayarsa ce riƙe a hannunsa,saƙon mataimakin shi mai kula da duk wani fice dashigar kuɗi ya fara dubawa bisanin na sauran mutane.Har zai ajiye wayar sai kuma ya nufi ɓangaren status,na Mardeeya ya shiga.Murmushi ɗauke da fuskar shi yake kallon ƴar tasa wacce ke zaune ita da mijinta na gobe ,hotunan ya ci gaba da dubawa har ya faɗa kan na Habiba.Zoom ɗin hoton ya yi ya na ƙare wa duk wani lungu da saƙo na jikinta kallo,a ƙasan hoton an rubuta my Bestie. Mohan ya fiddo halshe ya wani lashi leɓensa na ƙasa kamar tsohon maye.Kusan shekaru biyar kenan da mutuwar matarsa,tun daga nan bai sake yin aure ba amma ganin Habiba ya saka jin kamar ya samu matar aure. Screenshot ya yi na hoton,bisanin ya fita daga WhatsApp ya kira Mardeeya. A shagwaɓe ta ɗauki kiran ta na mai cewa “Dad ka manta da ni ” “A'a ku na raina,in sha Allah zan shigo gobe.Na ga ashe Nader ya zo yau” “Wa ya faɗa ma? Cewa ya yi ko kai bai sanar ba ” “A status ɗin ki na gani.Har da hoton Bestie” Murmushi mai sauti ta yi sannan ta ce “Bestie Habiba ,ajinmu ɗaya a makaranta.Dad ka ga ƴar ƙauye ce ko ba ta dace na yi ƙawance da ita ba?” “A'a ko ɗaya,ai kun yi daidai kamar Twins.Wane ne mahaifinta?” “Dad na faɗa ma ƴar ƙauye ce ba su wani jima da dawowa birni ba.” “Ok ! Ina Kameel ?” “Ban ji ɗuriyarsa ba duk yau ƙila ya na can wajen dadiron shi” “Mardeeyyya!” ya kirata da wata irin murya . Kamar za ta yi kuka ta ce “saboda Allah Dad abin da Ya Kameel yake yi daidai ne? Gidanmu kamar wata club haka ƴan mata ke shige da fice,da zarar na

Chapter 6 of 7