Share this page
littafin Mrs Sadauki na MAITAR IDO a nan duk za ki samu cikakken labarin.Ki sani cewa matsafa don su kama ruhinka ma abu ne mai sauƙi,abin da suke buƙata shi ne kawai keɓaɓen abu na gaskiya ta atomatik da ke fitowa daga mutumin da ake son cutarwar,kamar gashinsa,sunansa,date ɗin ranar haihuwarsa,zufar jikinsa wato tufafin da ya saka ba a wanke ba,ko kuma jinin jikinsa.Daga lokacin da matsafi ya riƙe ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan zai iya buɗe katinka na samaniya kuma ya karɓe ƙarfin ikonka wato power daga nan sai yayi abin da yake so” A sanyayye Safeenatu ta ce “ duk Baseerat za ta iya yin wannan? Gaskiya ni dai ban so in kin san hanyar da za a toshe wannan baiwar tata ni dai ki taimaka min don ina ji a jikina muddin aka bar ta da ita a gaba za ta zame mana masifa” Gwaggo Habibah ta yi mata wani irin kallo irin na ba ki da hankali kafin ta je ta ɗauki safar hannun ta saka ma jaririyar wacce ta buɗe ido sai kalle-kalle take kamar mai wayo,kafin kuma ta kafe idonta ga madubi Gwaggo Habibah ta yi kasaƙe tana kallon Baseerat a sannu a hankali ta ga idon yarinyar na sauya kala har suka zama farare tasss babu ɗigon baƙi,wani abu kuma ya soma fita daga bakinta yana bin direction ɗin madubi.Habibah ta ja wani dogon numfashi don kuwa ta fahimci Baseerat za ta yi tafiya ne ko kuma yawon buɗa ido wanda dayawan mutane na yinsa ba tare da sun san mine ne ba.Sai ka ji tamkar jikinka ya zama gawa kana son tashi daga bacci amma ka kasa tamkar an danne ka da dutse,har kwatanta buɗe ido ake amma baka iyawa saboda ruhinka da yayi balaguro ya bar gangar jikinka a kwance. #SAKEENATU Gefen da Nafisa ke ta sharar bacci ta duba kafin ta ɗaga kanta sama tana kallon yadda rufin ɗakinta ke wani lomaƙawa tsabar yadda ake tafiya a guje.Kukan jaki da na kare ga kuma na mage duk a lokaci guda,gefe guda kuma wata siririyar murya take ji tana kiran sunanta.Idonta ya ciko da hawaye,fitsari take ji amma tsoro ya hana ta tashi.Nafisa ta soma tayar wa,ita kuwa dakyar ta buɗe ido ta ce “ mine ne ?” “Fitsari nake ji” ta bata amsa kamar wata ƙaramar yarinya,cikin magagin bacci Nafisa ta ce “ ki je ki yi mana” sai ta koma baccinta.A hankali Sakeenatu ta zuro ƙafafunta ƙasa a tsorace ta shiga toilet ko Bismillah ba ta yi ba ballantana karanto addu'a,a tsorace ta je ta haye WC ɗin ta soma fitsari sai kuma jikin ya soma kyarma ganin ruwa na ta ɓulɓulowa ta ƙasan tile suna cika toilet ɗin ko kafin ta ƙyafta ido sun kawo mata a wuya ta yunƙura za ta tashi amma sai ta ji tamkar an saka super glue an manna ta a jikin WC ɗin ta ƙurma wani uban ihu wanda dama su mugayen shine suke jira ai kuwa suka tsaga rufin ɗakin ji kake ƙiiiiii kamar suna yaga zane.Idon Sakeenatu duk a waje take kallon yadda bindi mage,na kare da kuma idon wata baƙar mujiya a daidai wurin da suka tsaka.Cike da mugunta suka diro toilet ɗin wanda yayi daidai da tsinkewar numfashin Sakeenatu..... [31/03 06:14] MRS SADAUKI: MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 11 Duk da Sakeenatu ta suma hakan bai sa mugayen nan sun ƙyale ta ba,haka suka ajiye mata cutar a jikinta kafin su bar ta nan yashe a toilet.Cike da murna suka koma asibiti suka dinga bai wa Mamuh labarin abin da ya faru,cike da mugunta ta ce “ gobe da safe da hannunta za ta dafo wake ta kawo min ,daga nan kuma zan datse alaƙar farin cikinsu ita da Abbas zan maye mata gurbinsa ” duk suka sa dariya suna ƙara tsara mata wani salon muguntar. Washegari Kiran sallar asuba ya tashe da Nafisa,ta sauka daga bed ta shiga toilet nan ta ci karo da Sakeenatu a yashe babu numfashi.Hankalinta a tashe ta cika bokiti da ruwa ta zuba mata,ta ja ajiyar zuciya kafin kuma ta soma kuka cikin firgici.Nafisa ta kamo ta tare da fiddo ta haɗi da tambayar ta,duk a tsorace take wannan yasa ta kasa yi wa ƙanwarta bayani.Ganin haka yasa ita kuma ta je ta yo alwala ta yi sallah,bayan haka ne ta matsa wa Sakeenatu ta je ita ma ta yi sallar.Ko wanka ba su yi ba ta ce “ Nafisa tashi mu je gida wallahi tsoro nake ji” haka suka runguɗa suka je can gidan Mama wacce ke ta ƙoƙarin hura wuta domin ta ɗora ɗumame,tana ganinsu ta san ba ƙalau ba.Kamar wata ƴar yarinya haka ta je ta rungume mahaifiyarta tana wani sabon kukan,“ Subahanallahi! Nafisa mike faruwa?” “Wallahi Mama ban sani ba ni ma na yi ta tambayar ta amma ta ƙi faɗa min,alamu dai sun nuna tsorata ta ake yi a can gidan nata” Nafisa ta bata amsa. Mama ta ce “ to Allah ya sawwaƙa,ku wuce ciki bari na kira malam na shaida masa ” Can cikin mitsitsin ɗakinsu suka shiga,Ma'idah na kwance sai bacci take ba ta farka ba.Sakeenatu ta ɗauki abarta ta rungume ƙam kamar an ce za a raba su,mugun mafarkin da ta yi kan Ma'idar ya dawo mata a kai.Ta lumshe ido ruwan hawaye na kwaranya a kumatunta,ta yi tunanin kakarta ta yanke saƙa,ba ta taɓa tunanin za ta sake yin ƙunci a rayuwa bayan wanda ta yi a baya ba tun lokacin da Abbas ya shigo rayuwarta komai ya dawo mata normal ashe da sauran kallo a sama.Tsohuwar shuɗaɗiyar rayuwarta ce kwanyarta ta soma yi mata tariya,cikakken sunanta shi ne Sakeenatu Abubakar,ƴar gwagwarmayar rayuwa mai zuciya cike da burin zama wata aba a duniya.Karatun boko shi ne abokin da ta riƙa sannan kuma tubali don gina rayuwa mai inganci,sai dai ƴan magana na cewa rashin sanin ya fi dare duhu.Sakeenatu ba ta taɓa sanin cewa ba sanadin boko ne za ta zubar da mutuncinta ba,zuwanta jami'a shi ya ƙara buɗe mata ido sosai ta waye ta zama ƴar gayu,ƙwazonta a wurin karatu shi yasa ta ciri tuta a wurin malaman makaranta kusan duk maganarta suke suna yabon baiwar da Allah yayi mata banda malam Agali wanda tun ranar da ya ɗora idonsa kanta yake jin mugun sha'awarta saboda ta haɗu ta kowanne fanni.A wata rana Laraba ce wacce ta kasance ranar farko da ya fara ɗana mata tarko da kuɗi,“ki hau taxi” ya faɗa cikin taushin murya a gaban ɗalibai ba tare da ya ɓoye ba kuma ya sakar mata murmushin nan nasa wanda yake haukata ƴan matan makaranta da na wajensu .Ba za ta cewa tana sonsa ba,amma ita ma tana cikin waɗanda yake burge su saboda yadda yake da kyau kamar Balarabe ga baƙar sumar kansa ko wata macen ya fi sannan ɗan gayu ne kullum cikin shiri mai kyau yake.Ƴan matan ajin suka hau yin shewa suna taɓi tare da cewa yau dai an samu wacce ta sace zuciyar Dr Agali,da ido ta bisa kawai lokacin da yake fita daga ajin yayin da ɗalibai duk suka dawo kusa da ita kowacce na tofa albarkacin bakinta.Sakeenatu ta ji wani irin girman kai ya zo mata tare da alfaharin ita ce ta ciri tuta,cours ɗin da aka yi musu na gaba sam ba ta fahimci komai ba saboda tunanin malam Dr Agali.Ba ta buɗe ƴar enveloppe ɗin kuɗin ba sai da ta je gida, kuɗi ne ƴan jika-jika sabbi da su har guda goma.Ta kai su kusan hancinta ta shaƙi ƙamshin turarensa,tuni jikinta ya mutu murus ta na shirin saka kuɗin a jaka ne ta lura ɗaya daga cikin takardun kuɗin an rubuta lamba a jiki.Kamar wacce ake tsikara ta ɗauki wayarta ta loda lambar sannan cike da waswasi ta tura masa saƙo babu jimawa ya kira ta,kamar wani mutumin ƙwarai har da yi mata sallama ta amsa tare da ce masa “ fatan ka je gida lafiya?” Cikin muryar nan tasa ta buzaye waɗanda ba su ida iya Hausa ba ya amsa mata da “ a'a ina wata asibiti an kira ni in tiyata” Ta saki murmushi mai sauti ta ce “ ina son ganin ranar da za a ce Sakeenatu na yin tiyata” “Lokacin zai zo ke dai ki ci gaba da dagewa wurin yin karatu,na ji malamai sai yabon ki suke ashe ba a cours ɗina ne ba kawai kika ƙware” nan ma murmushi mai sautin ta yi kafin ta ce “ burina shine zama babbar likita wacce duk duniya za ta yi alfahari da ita,ana dinga nuno ni a TV” “Kina iya barin Nijar Keenat?” Dr Agali ya tambaye ta,kai tsaye ta basa amsa da “ eh sosai sai in gwamnati bai ɗauki nauyin karatun nawa ba” “To ki fara shiri in sha Allah ni nan zan sa burinki ya cika” “Keee Sakeenatu keee!” Mama ta faɗa tana mai kamata dundu wanda shi ya katse mata tunanin shuɗaɗiyar rayuwarta,da sauri ta dawo hayyacinta tana mai kallon Mama wacce ta janye Ma'idah da sauri tana mai ci gaba da cewa “ kawai ki kama yarinya ki riƙe gam tana kuka da ranta amma kin ƙi sakin ta” Sam ita ba ta san riƙon da ta yi wa Ma'idar ya cutar da ita ba,cike da takaici da zugin da zuciyarta take yi ta tashi ta fita ta cika bokiti da ruwan ta shiga banɗaki.Wanka take son yi amma tunanin Dr Agali sai ƙara kawowa kwanyarta farmaki yake,abin da ya faɗo mata a rai a yanzu kuma shi ne ranar da ya kira ta ya shaida mata Visa ɗinta ta fito ta zo ta karɓa bai jin daɗin jikinsa.Ba tare da wani tunani ba ta je gidan nasa kamar yadda yayi mata kwatance,duk a tunaninta yana da mata amma sai da suka shiga ciki ne ta ga shi ya bata ruwa sannan ya kawo mata lemu wanda ya zubar da shi a jikinta da gayya har tufafinta suka ɓace.Ta wani rumtse ido don takaicin ganin video yadda Dr Agali ya ɓalle maɓallan rigarta ya cire ta ya bar ta daga ita sai bra ya je wanke mata ita duk ta yi tunanin ƙauna ce ta kawo haka sai bayan ya dawo ne ya soma yi mata wasu zafafan romance.“ Ni fa dama ba zan yi miki komai ba, wannan ɗin ma ban san ya aka yi ya faru ba ki yi haƙuri ba zan sake ba sai bayan aure” Dr Agali ya faɗa lokacin da ta sakar masa kuka. “Anty Sakeena don Allah ki aje tunanin nan gefe ki yi wanka ki fito ga malam nan ya zo” Nafisa ta faɗa daga bakin ƙofa.Sai a lokacin Sakeenatu ta fara wankan ,bayan ta fito ta je ta gaishe da malam wanda ya kasance ƙanen Mama ne.Cikin garwashin wuta ya zuba ƴaƴan habbatu sauda hayaƙi ya turniƙe ɗakin,idon Sakeenatu duk suka fito waje ta soma tari kamar ranta zai fita shi kuwa karatu ya soma nan lamarin ya ƙara yin gaba don tuni ta soma yin kuka .Tsawon lokaci kafin ya bar ta haka nan,magani ya bada wanda za ta dinga shafawa da hayaƙe jikinta da kuma gidan.Bayan tafiyarsa ne ta samu ta ci abinci,wunin ranar dai Mama haka ta ƙare shi wurin yi mata nasiha dab da magrib Nafisa ta yi mata rakiya zuwa gidanta.A tare suka yi gyaran gidan da girki kafin ta yi wanka ta shafa man da malam ya bata ta kuma yi turare. A can asibiti kuwa tun safe da Abbas ya bar su bai koma ba,kuɗi kawai ya bar musu hakan bai yi wa Mamuh daɗi ba.Ana yin sallar magrib ba tare da likita ya sallame ta ba Gwaggo Rahamu ta haɗa tarkacensu suka fito a ɓoye.A bakin hanya suka samu adaidaita wacce za ta kawo su gida ,suna tafe suna hira “ ai tun da kika ga bai dawo ba to tabbas babu makawa da ya koma gida karuwanci ta yi masa kin san halin namiji kan mace sakarai yake zama” Gwaggo Rahamu ta faɗa . Mamuh ta tsuke bakin nan nata ta kasa cewa komai saboda baƙin cikin da ke addabar baƙin ruhinta,gani take yi ma tamkar adaidaitar ba ta gudu. Suna isa gida tun a bakin ƙofa suka canza kalar idonsu daga na mutum zuwa na mugunta,sai aka yi rashin sa'a Nafisa na tsakiyar falo tana hayaƙa hantiti da tazargade .A tare suka shigo,a tare kuma suka saki ihun azaba suna masu faɗuwa ƙasa suna yin wani irin huci a gaban idon Nafisa suka rikiɗe suka zama jibga-jibgan macizai kowa yace shi ba ma matsoraci ne ba to bai ga abin tsoron ba .Da wani mugun sauri Nafisa ta mangal ɗin hannunta mai cike da garwashi,da azama ta nufi hanyar ɗakin Sakeenatu sai dai kafin ta isa Gwaggo Rahamu ta yi wani uban tsalle ta naɗe handle ɗin ƙofar da bindinta tana mai buɗe ƙaton bakin,Nafisa na shirin komawa baya ta ji ana bin ƙafafunta wanda kuma tunaninta da ruhinta tuni sun shaida macijiya Mamuh ce...... [31/03 06:17] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* 12 Ido ta lumshe jikinta na ci gaba da kyarma,tuni Mamuh macijiya kuma ta ɓullo kanta tsakanin ƙirjin Nafisa ta fiddo halshe ta lashi fuskarta,yawunta masu mugun ɗohi suka daki hancin Nafisa.Ba tare da ta buɗe ido ba ta buɗe bakinta murya na rawa can ƙasan maƙoshi kamar mai yin raɗa ta soma karanto wasu ayoyin Alkur'ani da ke cikin suratul Yusuf daga aya ta 79 har zuwa 82 .Jikin Mamuh macijiya ne ya soma yin sanyi tsabar yadda ayayoyin ke dagargaza ruhinta musamman da ya zamana Nafisa ta soma ɗan ɗaga murya.Sululuuuu Mamuh macijiya ta faɗo daga jikin Nafisa ,a mugun tsiyace Gwaggo Rahamu ta bi ta ƙarƙashin ƙofa ta shiga ɗakin Mamuh don kuwa ƴan magana na cewa in ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta to kai ka shafa wa naka ruwa. Nafisa na jin saukar macijin ta buɗe idonta a hankali tare da sauke su ƙasa inda Mamuh ke kwance har yanzu cikin siffar maciji sai wani irin numfashi take fatar cikinta na lotsawa kana gani ka san ta wahala. Nafisa ba bakinta bai gushe da ci gaba da yin duk addu'ar da ta zo bakinta ba,a yadda take tsayen suka ƙure juna ita da Mamuh wacce duk wanda ya san ta to tabbas in ya ga macijin zai shaida wannan idon na Mamuh ne.Nafisa ta saki wani murmushin nasara lokacin da ta ga hawaye sun fara fita daga idon macijiyar,ta sani sarai har da kunya da gajiya suka hana Mamuh ƙoƙarin guduwa don babu abin da Mayu suka fi tsana kamar asirinsu ya tonu wannan yasa Nafisa ta nufi ɗakin Sakeenatu.Tana shiga daidai ita kuma ta fito daga Toilet ta yi wanka ƙugunta ɗaure da towel,“wani wankan kika sake yi?” Nafisar ta tambaye ta ba tare da ta nuna mata alamar wata damuwar ba. “Eh wallahi,maganin nan da na yi hayaƙi da shi sam babu daɗi shi yasa na yi wanka” Sakeenatu ta bata amsa tana mai kallon Nafisa,“Me? Wannan kallon fa?” “Fuskarki ce nake ganin kamar tana min wani iri” “Wani iri kamar ya fa?” Nafisar ta tambaya tana mai shafar fuskarta a daidai wurin da Mamuh ta lasa. “Babu komai! Bari na shirya na san yanzu Abbas zai shigo” “Ni zan yi sallah” cewar Nafisa tare da shiga Toilet,har ta gama alwala tana tunanin abin da ya faru da ta zo ta yi sallah sosai ta yi addu'ar neman tsari. Sakeenatu ma ta yi sallah tare da fara bitar karatun jiya da aka koya mata,in ta yi kuskure sai Nafisa ta gyara mata suna nan zaune har aka kira isha'i suka miƙe suka gabatar sai bayan sun ida ne suka fita falo. Nafisa ta dubi daidai wurin da ta bar Mamuh a ɗazu,tuni capet ɗin yayi alamun datti. “Anty Sakeena ni kam ina mai aikinki?” “Wa Fa'iza ? Wallahi kin ga shaf na manta da zancen ta.Ga shi kuma ba waya ce da ita ba ballantana na kira ta amma gobe in ba ta zo ba zan je gidan nasu na gani tun da babu nisa nan baya ne gidan Fulanin nan” “Oh! Can take ashe,tun da babu nisa bari na je na dubo” Kafin Sakeenatu ta bata amsa Abbas yayi sallama tare da shigowa,duk fushinsa ne ya ɓata nan take ganin uban adon da matarsa ta yi. “Ina wuni Ya Abbas ?” Nafisa ta gaishe shi tana mai yin murmushi don tana mugun sha'awar soyayyar antynta da mijinta,ba ƙaramin so yake yi mata. “ Lafiya lau Nafi ya gida?” ya amsa. “Alhamdullah” ta faɗa tana mai fita,ita kuwa Sakeenatu kamar wata yarinya haka ta wani rugo da gudu ta faɗa a jikinsa tana kuka.Abbas ya lumshe ido ya na mai cewa “ mene ne kuma na yin kuka uhum?” ba ta basa amsa ba ta dai lafe a jikinsa,tsawon lokaci suna a haka kafin ta hauƙura ta ja shi zuwa cikin bedrom ɗinsu.Da taimakonta yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya sannan suka fito suka ci abinci,cikin hira ne take faɗa masa ba ta da lafiya har sai da ta je gida. Ya ja dogon numfashi kafin ya ce “ni kina Keenat ban san abin da ke damuna ba yau gani nan dai” “Allah kawo mana sauƙi” “Amen!” FA'IZA Tun da lamarin nan ya faru da ita duk jikinta ya zama wani iri,tun da take ba taɓa jin makamancin abin da ta ji ba a ranar nan.Tana da saurayi don har manya sun shiga zancen amma duk tsawon lokacin da suka ɗauka ita tun can ba ta taɓa jin sha'awarsa ba don a tunaninta ma ba ta da lafiya ne tun da ta ji ana faɗar akwai matan da basu jin feeling.Sai ga shi babban al'amari ya faru da ita mai kamar mafarki kamar zahiri an yi wasa da sassan jikinta,a ranar da ta isa gida kasa cin abinci ta yi.A washegari kuma ta tashi da zazzaɓi dalilin da yasa ba ta je aiki ba,yanzu ma tana kwance kan tabarma ta shafe jikinta da wani maganin zazzaɓi sai ga sallamar Nafisa.Duk da gidansu bai da ƙwan lantarki zamani amma suna kunna uban sanjo wannan yasa ta gane Nafisa duk da ƙarancin haskensa.Ta tashi da sauri tana mai cewa “sannu da zuwa” Ita kuwa Nafisa gaisa wa take da Mamar Fa'iza wacce ba ma sosai take jin Hausa ba,ta zauna kan tabarmar tana mai cewa “fatan dai lafiya? Anty na ta jira shiru ba ki zo aiki ba” “Zazzaɓi ne ya rufe ni amma da sauƙi gobe zan je in sha Allah ” Fa'iza ta bata amsa. “Allah ƙara lafiya,ni zan koma” cewar Nafisa tare da miƙewa,har ƙofa Fa'iza ta rako ta sai a lokacin kuma ta yi mata tambayar “ni kam Fa'iza abin da ya faru da ke gidan anty Sakeenatu dama kina yin haka?” “A'a wallahi ban taɓa yi ba” “To ki dage da addu'a kin ji ko,saboda yanzu duniyar sai a hankali” “To na gode” da wannan suka rabu maimakon Nafisa ta koma gidan Sakeenatu sai ta yi tsinke gidansu tun da dai ga mijinta nan ya zo. #GIDANSU SAFEENATU Wuni guda currr jaririya Baseerat ta ɗauka tana bacci wanda gangar jikinta ta koma kamar gawa ko motsi ba ta yi. Idon Safeenatu taf da hawaye ta ce “ Gwaggo Habibah jaririyar nan fa ba ta motsi,ina ga ta mutu ne” “Da ranta Safeena,don Allah ki fitar lamarin yarinyar nan tun da dai ba ki da ƙarfin zuciya.Tun farko na faɗa miki Baseerat ba normal ba ce,kenan sai ki shirya ganin abubuwan ban mamaki.Wannan kwancin da kika gani ruhinta yayi tafiyar dogon zango ne amma da ranta,ƙila sai goshin magarib su maido ta” Hawayen da take ƙoƙarin mayar wa ne suka yi nasarar sauko wa akan kumatunta,ta girgiza kafin ta ce “ ni kam ba zan iya rainon ta ba,don muddin na ce zan zauna da ita zuciyata na iya bugawa.Su wane ne za su maido ta? Yarinya kamar ɗiyar jinnu ace tun safe tana bacci ko nono ba ta sha ba alhalin ɗan uwanta ya sha fiye da goma.Haba kuma ace ba zan yi magana ba?” Safeenatu ta faɗa zuciyarta na yi mata ciwo kafin ta miƙe ta fita, frigine ta buɗe ta ɗauko ruwa masu mugun sanyi ta juyo a roba sannan ta koma ɗakinta.Babu wani tunani ta ɗauki Baseerat ta tsoma cikin ruwan ƙanƙarar nan ,ko daƙiƙa biyu ba yi ba ta buɗe idonta farare tasss babu ɗigo baƙi kafin su rine su koma ja kamar nunnanen tumatur.Safeenatu ta yi baya da sauri cike da tsoro,tana jin wani azababen sanyi na game duk illahirin jikinta tamkar wacce aka jefa a frigini.Haƙoranta ne suka fara dantsewa suna fitar da wani ƙasƙas,sai a wannan lokacin Gwaggo Habibah ta miƙe ta cire Babyn tare da lumshe ido tana mai bata haƙuri “ku yi haƙuri uwa-uwza ce ta yi kuskure ba za ta sake ba” tana maganar ne tana jimƙe da hannun hagun Baseerat wanda ke fitar da haske,Gwaggo Habibah ba ta buɗe idonta ba sai da ta ji Sakeenatu na sauke numfashin wahala ta yi mata wani kallo ta ce “yanzu kin fahimci abin da nake son yi miki nuni?” kai ta gyaɗa,Baseerat ta soma yin kuka. “Zo ki bata ta sha” Safeenatu ta maƙe kafaɗata ta ce “wallahi tsoronta nake” “Sun tafi yanzu ita kaɗai ce ,zo ki bata yunwa take ji” tana ji tana gani haka ta shayar da jaririyar. Ana kiran sallar magrib Murjanatu ta dira a gidan da ɗirkeken cikinta,cike da murna suka rungume juna ita da Gwaggo Hajara.“Na yi kewarki sosai Mama ” cewar Murjanatu tana matsar ƙwalla,shiru Gwaggo Hajara ta yi jin ƙaton cikin ƴarta na tokare ta yayin da kuma yawunta suka soma tsinkewa tsabar maita...... [31/03 06:21] MRS SADAUKI: _____________________ MRS SADAUKI *MAITAR DARE* *Last free page 13-14* Wani irin mugun ƙishi ne ya wanzu a maƙoshin Gwaggo Hajara saboda Maitar shan jini ta motsa.Dakyar ta iya sakin Murjanatu ta koma gefe tana kallon ta,sai kuma ta kasa haƙuri sai da ta shafi ƙaton cikin da mugun sauri Murjanatu ta kai hannunta ita ma kan cikin saboda mugun juyawa da yayi. “Washhh! ” ta furta a wahalce kafin kuma ta dafe ƙugu jin kamar ta soma naƙuda ne,“ sannu Murjanatu ki zauna mana” Gwaggo Hajara ta faɗa tana haɗiyar yawu don tsaf take kallon jaririn wanda sai juyi yake a ciki. Kan gwiwanta ta zube tana mai ci gaba da yin gumurzu,tuni ita Hajara ta san da yau in ba wani iko na Allah ba sai ƴarta ta haihu.Da sauri ta shiga cikin ɗaki ta fito kafin ta ce “tashi mu je asibiti” a wahalce ta ɗago ta dubi mahaifiyarta ta ce “ wallahi Mama ban iya tashi” “To haka za ki zauna? Sai nake ganin kamar haihuwar ce” Ba ta rufe bakinta ba Murjanatu ta fasa wani uban ihu wanda ya jawo hankalin Gwaggo Habibah da saurinta kuwa ta fito tana tambayar lafiya sai kuma ta yi tozali da Murjanatu a cikin mawuyacin hali.Da taimakonta suka samu suka Murjanatu ta miƙe tsaye,Munir ne ya je ya nemo musu mai ɗan sahu.Kayan robar Safeenatu aka yi aro aka kai ta asibiti,sai uban ihu take tana kururuwa tana faɗin za ta mutu. Daga nan waje kuma inda mutane ke zauna wa,ran Gwoggo Habibah ya ɓace sosai tun tana ɓoyen abin har ta kasa ta ce “ yanzu ke hatta ƴarki ba ki bari ba? Wannan mugun hali naki bai yi ba.Wato babu babban makunyaci a duniya irin maye,tun da har jininsa bai bari ba” Gwaggo Hajara ta ƙanƙance idonta da suka kaɗa suka yi ja kafin ta ce “ ina ruwanki da ni ? Ke kika haifa min Murjanatun? Ƙanwar uwa ko ta uba?” Gwaggo Habibah ta miƙe ta ce “ kina fa da gaskiya,amma ki yi haƙuri farar zuciyata ta taimakon jama'a tasa na zo na tsoma hannnuna inda ba a gayyace ni ba.Tabbas Murjanatu ƴarki ce in kina so ki haɗa har da ita duk ki cinye” tana gama faɗa ta yi tafiyarta ta bar Hajara a zaune babu jimawa kuwa Murjanatu ta haifo ɗanta namiji. Ɗakin hutu aka kai ta,murya na ɗan rawa Gwaggo Hajara ta ce “ yo ina jaririn?” “Nurse na duba shi ne don tabbatar da lafiyarsa” ta bata amsa. Tsawon lokaci kafin a kawo shi jikinta har rawa yake ta karɓe shi,nurse ta ce “ a basa abincinsa ya sha da alamu yunwa yake ji” “Toh! Toh” cewar Hajara tana wani kafe yaron da idon mugunta,ya soma kuka Murjanatu ta tashi zaune babu kunya ta ce “ Mama kawo shi” ba don ta so ba ta

Chapter 4 of 10