Share this page
ke ƙumshe da ita. “Maa shi kenan ba zan ƙara jin taushin gangar jikinki ba?” ita ce tambayar da na yi mata madadin na sanar da ita matsalar da ta kawo ni. Ta ce “Naomi a zangon da nake na fita daga sawun duniyar bil'adama na koma cikin duniyar matattu,ki kira ni da ruhi kai tsaye” Kallonta na yi,tabbas ita ɗin ruhi ce kamar yadda ta faɗa ɗin.Na kai hannu na shafi kumatuna da nake jin wani damshi,wanda na yi imanin cewa ruwan hawaye ne .Murya na ɗan rawa na ce “mahaifiyar Deborah ta faɗa hannun mugaye shi ne nake son sanin ta ya zan ceto ta?” “Babu buƙatar yin haka,saboda ita ɗin ba kanwar lasa ba ce.Za ta iya fitar da kanta kar ki wani damu kanki” Maa ta faɗa . Na ce “amma kuma ita ce da kanta ta aiko da takarda domin sanar da mu” “Ta yi haka ne domin ku ci gaba da rubuta littafin bayanai ba wai don kawo mata agaji ba.Ki sanar da Deborah cewa lokaci ya yi da ita ma za ta ɗauki muƙaminta na rubuta tarihi kamar yadda mahaifinta ya karɓa gun mahaifinsa,ita kuma mahaifiyarta ta karɓa daga mahaifinta,yanzu kuma ƙaddarar littafin tarihi ta dawo hannunta” Maa na gama furta haka sai ta soma nitsewa cikin ruwa haskenta na tarwatse wa haɗi da disashewa.A gaban idona ta ɓata,na lumshe idona ina mai furta kalaman tsafi tare da buɗe su kuma a nan na tsinci kaina a ɗakina. Deborah na kwance amma ba bacci take yi na.Kallonta na yi kafin a takaice na sanar da ita abin da Maa ta shaida mini,da wani irin sauri ta miƙe ta zauna tana kallona can kuma ta soma furzo da wani irin furuci sai na ji tsafin da take yi ba irin nawa ba ne yana da banbanci kamar yadda Hausar wani gari ba ɗaya take da ta wani garin ba. Babu jimawa sai muka soma jiyo kukan jemage yana wani tsala shi kamar zai fasa gidan,a tare muka fita nan muka yi gamdakatar da wani baƙin jemage baƙi ƙirin da shi ga kuma wani irin girma na ban mamaki. Kan ƙafafunsa ya sauka bayan ya cillo wani tsohon littafi ya dira a tafukan hannun Deborah. Kallo ɗaya na yi masa na fahimci cewa shi ne wanda aka wakilta domin tsare littafin ya basa kariya.A hankali ya soma yin tsalle har ya isa gun Deborah,babban farcenta na ƙafar hagu ya kama ya fasa shi tare da soma shan jininta irin sosai ɗin nan don har sai da ta soma yin wani irin haske irin na rashin jini amma ko kaɗan ban yi yunƙurin tsayar da shi ba har sai da ya gama sha sannan ya tashi sama,sai dai bai yi wani nisa ba ya ɓace ɓat. Sai a lokacin na je na kama ta na ja ta zuwa ciki na zaunar da ita,magani na ɗauko na soma rufe mata yatsan da shi wanda har yanzu yake ɗigar da jini. “Ki kwanta ki huta na san kin gaji” na furta. “Ki soma karanta littafin kafin ni na karanta miki ” ta furta tare da miƙo mini,kamar ba zan karɓa ba sai kuma na kai hannu na karɓi littafin na ajiye a gefe.Ido ta lumshe ta soma yin bacci mai kama da mutuwa,wanda na yi imani cewa a cikinsa ne za a miƙa mata wasu asirai da kuma power kariyar kai da kuma ta abin da aka damƙa mata amanarsa. A cikin wannan daren ne na soma karanta littafin tarihi wanda ya ƙunshi rayuwar jarumai da kuma irin gwagwarmayar da suka yi fama a kai.Na samu sirrika dayawa,na yaƙi da kuma yadda ake sarrafa maita ta sigogi daban-daban. Wannan littafin ya ƙara saka mawa zuciyata cewa duk inda babu magic to lalle babu rayuwa mai inganci, Magic shi ne komai na duniya a cikinsa ne za ka samu ƴanci da kuma gata.Rufe shi na yi tare da raɓawa gefen Debora na kwanta,ina lumshe idona na soma jin wani irin motsi a cikin kunnena tamkar ƙwaro na tafiya.Ƙara nutsuwa na yi sai na soma jin tamkar ana yi mini magana ne,amma ta ina? Ban sani ba.Ji na yi ana danne ni ana saukar mini nauyi,na furzar da huci mai zafi jin wasu kalmomi daga wata murya da ban san mamallakinta ba. “ A duk inda kike a faɗin duniyar nan sai na nemo ki,ni ne nan zan kashe ki da hannuna ƙaramar matsafiya muguwa mai idanun maciji” muryar namiji ce amma ban san wane ne ba, sannan ban fahimci abin da yake nufi ba har ya ƙara yin wani furucin “ina ma ace annabi sulaiman bai yi wafati ba,da na roƙi alfarmarsa ya tura rundunar aljanu su gana miki azabar da ta fi ƙarfin tsafinki ” Saurin buɗe idona na yi,ina mai tambayar kaina “wane ne kuma Annabi Sulaiman?” sai dai banda amsar wannan tambayar,in akwai wanda zai faɗa mini ita to bai wuce Deborah ba wannan yasa na kasa haƙuri na kai hannu na shafi fuskarta.Ta buɗe idonta tarau a kaina,sai dai babu ɗigon baƙi a cikinsu da alamu har yanzu ba ta dawo daga balaguron ruhi ba. “Wane ne Annabi Sulaiman?” na tambaye ta,idanunta ne suka dawo normal nan take ta tashi zaune sannan ta bani amsa da cewa “ ya kasance ɗa ga Annabi Dawuda shi ma kuma annabin Ubangijin Ka'aba ne.Yana da matuƙar power don a tarihin annabawa shi ne kaɗai ya mulki mutane da kuma aljanai,sannan kuma yana iya yin magana da dabbobi da kuma jarirai waɗanda bakinsu bai buɗe ba.Ya yi mulki cikin hikima da adalci ga al'ummarsa” Zuciyata ce na ji tana wani irin bugawa na jin bayanin da Deborah ta yi mini.Kamar mai tsoron sake jin wata buwayar na ce “amma me Annabin ke nufi?” “Mutum mai isar da wahayi daga Ubangijin Ka'aba zuwa ga al'umma ” ta bani amsa kai tsaye.Ban ce mata komai ba sai tashi da na yi na fito waje ina kallon taurari ina kuma juya kalamanta. Ƙofar gidan na ji ana bugawa,na je na buɗe sai na ga gungun matsafan garin ne da alamu sun fito maitar dare ne suka biyo. “Ranki shi daɗe mun samu baƙuwar fuska a yankin nan,wani mutum ne maharbi mun tsince shi a wata gona yana bacci.Mun ɗaure shi da duk wata igiyar tsafi amma ta ƙi yin tasiri a kansa saboda girman tsafinsa wannan dalilin ne yasa muka zo zuwa gare ki” ɗaya daga cikinsu ya faɗa . Raina a mugun ɓace na ce “me yasa ba ku kashe shi ba?” Kallon juna suka yi kafin wani kuma daga cikinsu ya ce “ kamar dai yadda ya faɗa miki ɗin ne,tsafinsa nada matuƙar ƙarfi da dukkan alamu mutum ne na daban ko a duniyar ruhaniya” Ban ce komai ba na yi gaba a fusace yayin da su kuma suka take mini baya.Tun kafin na isa gonar nake jiyo numfashin baƙin tsafinsa,ina isa ya yi saurin tashi tsaye muna fuskantar juna.Ɗan saurayi ne da ba zai haura shekara ashirin da takwas ba,sanye yake cikin kayan maharba ya rine gefen fuskarsa da baƙin abu yayin da kuma ƙirjinsa aka zana wata baƙar kunama. Ban tsaya tambayar wane ne shi ba na kai masa farmaki,ya tare kafin kuma mu shiga masayar kalaman tsafi muna haɗawa kuma da yaƙin gangar jiki.Kamar yadda suka faɗa ɗin tabbas shi ɗin na daban ne,ban ida fahimtar haka ba sai da ya kai ni ƙasa ya saita kibiyar tsafinsa daidai idona. Yana jan wani numfashi ya furta “kafin a farmaki baƙo a fara tambayarsa da wace aniya ya zo,duk waɗannan matakan tsaron na ruhikan ruwa da kika saka ba su iya tare ni na shigo yankin nan ba sai ke ce kike tunanin za ki hana ni yin abin da na zo yi?” shi abin da ya furta,amma duk da haka ban saurare shi ba na fito da wuƙar mahaifina na daɓa masa ita a ƙirji daidai kunamarsa yayi wata irin kururuwa da ta saka dajin amsa wa kafin ƙyafta ido sai ganin kunamu muka yi suna zubowa kamar ana ruwa..... [13/04 09:49] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 05 Yadda baƙaƙen kunamun suka dabaibaye jikina shi ya fi komai ɗaga mini hankali,ga shi kuma masarafin tsafina ya ƙi aiki.Idona ƙurrr kan mutumin da na cakawa wuƙa yana tsaye ƙyam kan ƙafafunsa,yayin da kuma kunamun suka buɗe hannuwansu da alamu umarninsa suke jira su shiga harbata. Tafin hannunsa ya buɗe ya soma yin furuci cikin Yaren tsafi wanda ya sha banban da nawa,a hankali duk kunamun suka yi ɓata dabo sai a lokacin na yunƙura na tashi zaune ina kallonsa cike da mamakin me yasa bai kashe ni ba kamar yadda na yi yunƙuri. “Wane ne kai?” na tambaye shi.Bai bani amsa ba sai nuni da yayi mini da wuƙata wacce har zuwa yanzu tana nitse a cikin ƙirjinsa.A hankali na miƙe tare da zuwa na ciro wuƙar,abin mamaki sam babu ko da ɗigon jini da ya zuba illa kawai alamun an huda ƙirjin. “Banah!” ya bani amsa,na maimaita sunan a bayyane kafin na ce “me ya kawo ka YANKIN MUTUWA?” “Ke!” ya bani amsa kai tsaye,kallon ban gane ba na yi masa kafin na ce “ni kuma?” Kai ya jinjina mini kafin ya ciro wata sarƙa da ke a wuyansa mai tambarin gumki ya miƙo mini,na karɓa tare da juya ta sannan na ɗago na dube shi. “Ba ki ga komai ba?” ya tambaye ni. “Me kake son nuna mini?” “Duba da kyau dai” ya sake faɗa ,sai na nutsu da kyau nan ne na ga gumkin jikin sarƙar zanen mace ne da ƙusumbi a bayanta. Na shafi ƙusumbin da ɗan yatsana,nan take ya kawo wani haske kamar an kunna ƙwan lantarki.Banah ya matso kusa da ni shi ma ya ɗora nasa yatsan kan nawa sai hasken ya ƙaru a hankali kuma muka fara yin sama ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka lula can cikin iska. Mutanen gari ne suka fara fitowa,sai kuma suka shiga yin kiɗa da bushe-bushe yayin da wasu kuma suke rawa.Ban taɓa tunanin cewa wai hakan aure ne muka ƙulla ni da Banah ba sai da wasu ruhika suka bayyana a gare mu suka yi mana bushara da hakan tare kuma da ƙara mana power. Sarƙar nan mai hoton gumkin mace da ƙusumbi ita ce kabancin sadakina,ita Banah ya saka mini a wuya kafin mu sauko ƙasa. Gefe na koma ina kallonsa,ba mummuna ne ba amma kuma ba za a kira shi da mai kyau ba.A kallon farko za ka tabbatar da cewa shi jarumi ne a fagen tsafi,kumatuna da ya shafa shi ya katse mini ɗan guntun nazarin da nake yi a kansa. “Tunanin me kike yi?” ya tambaye ni,da sauri na juya masa baya ina mai basa amsa da cewa “ ban san wane ne kai ba,daga ina kake kuma amma kai tsaye ka zo ka aure ni ba tare da neman shawarata ba” “Naomi ba fa ni ne na tsara haka ba,allolin prophecy suka ga dacewar mu haɗu ni da ke domin mu cika alƙawarin da magabatanmu suka ɗauko” Da sauri na juyo ina kallonsa na ce “to ka riƙe ni matsayin abokiyar aiki kawai” ina gama faɗar haka na soma tafiya cikin rangaji saboda yanayin larurata.Ina jin yana take mini sawu har muka isa gida,Deborah na tarar a tsaye kamar mai jiran zuwana. Da ido ta tambaye ni shi kuma wancan na bayana? Na juya na dube shi da sauri ya ƙaraso ya gabatar da kansa ga Deborah sai na ga yanayin fuskarta sam babu annuri. “Zo ina son yin magana da ke” ta faɗa tare da kama hannuna muka shiga cikin ɗaki. “Ta ya aka yi ya zama mijinki alhalin tarihi bai nuna za ki yi aure ba a doron duniya?” Deborah ta tambaye ni tana wani tsure ni da ido. Ni ma ɗin kallonta na tsaya yi saboda gaskiyar da ta fito daga bakinta wacce na san ita kanta ba san ta faɗe ta ba. “ Ba zan yi aure ba?” na tambaye ta,sai a lokacin kuma na ga ta sha jinin jikinta tare da soma yin kame-kame . “ Tun yaushe kika gano haka?” na sake jefo mata wata tambayar. Ta yi ɗan ƙasa da murya tare da sauke idonta daga cikin nawa ta ce “tun ranar da Umma za ta bar garin nan zuwa neman tarihi a wasu guraren , ta shaida mini cewa ba za ki taɓa yin aure ba muddin alamomin prophecy sun bayyana a gare ki.Ita ce da kanta ta nuna mini tsanin nan da ke cikin ruwa,ni kuma na ja ki muka je” Sosai na ji ɗaci har ƙasan raina jin wai ba zan yi aure ba alhalin a duniyar nan babu abin da na fi so kamar na yi aure na haifi yara.A daidai wannan lokaci ne kuma na ji wani abu game da Banah,ko da a ce auren bogi ne to zan karɓe shi ko ba komai dai za a kira ni sawun ma'aurata kuma zan haifi ƴaƴa. “Ƙusumbin da ke gare ki ba zai taɓa barin maza su yi sha'awarki ba,in akwai waɗanda da za su so ki to ki sani mata ne ƴan uwanki ” Deborah ta faɗa tare da kamo hannuna alamun rarrashi. “Wannan furucin naki duk ƙarya ne,kin faɗi haka ne saboda kin jima kina sha'awarta wannan dalili ne ma yasa kika tunzura ta har kika kai ta karɓa muƙamin iko alhalin wa'adin karɓarsa bai yi ba.Kin san cewa muddin Maa nada rai ba za ki taɓa samun Naomi ba” Banah ya faɗa yana mai shigowa ɗakin. Kallon tsana Deborah ta soma binsa da shi kafin ta ce “muddin ina raye ba zan taɓa bari ka cutar da Nao ba” Ya yi wani murmushi kafin ya ce “na gode da tunatarwa ” sai kuma ya maido dubansa gare ni yana jefo mini kallon so da ƙauna ya ce “ ki sa a ranki Banah yana sonki kuma zai zauna da ke ko da kuwa dukkan jikinki ciwo ne” Wata ajiyar zuciya na sauke jin furicinsa ,kafin na dubi Deborah na ce “ba zan so ki tsani Banah ba saboda shi ɗin murfin rufin asirina ne.Deborah ki sani zuciyata ba za ta taɓa lamunta rashin miji ba” Kai ta girgiza mini tana mai cewa “Banah ba mijinki ba ne,in ma dai akwai shi to ba na ce a jinsinmu ba ne don kuwa tarihi bai nuna hakan ba” Da sauri Banah ya zo ya shiga tsakiyar mu yana mai ɗan ture Deborah ya ce “dama ba tun yau matsafan tarihi ke ƙirƙirar ƙarya ba domin cimma manufarsu” kallona ta yi,sai na kawar da kai ita kuwa da sauri ta fita. ★ “Ba zan taɓa lamunta ki auri ɗan maƙiyiyata ba,ki sani cewa ko bayan raina kika auri Naslam ban yafe miki ba“ Dadda ta faɗa tana yi wa A'ishah wani mugun kallo. “Ki haƙuri Dadda amma ina son yarima fiye da raina,ki sani cewa in kika hana ni aurensa to tamkar kin yi mini shamaki da duk farin cikin duniya” A'isha ta faɗa tana hawaye. Dadda ta yi mata mugun kallo kafin ta ce “da dukkan alamu har yanzu ba ki warke daga cutar haukan naki ba,ɗan matsafiya kike sha'awar aure ki haɗa zuri'a da shi?” Ta dubi mahaifiyar tata da jajayen idonta kafin ta ce “ Dadda babu wanda ya tabbatar cewa Ummi Naslam na yin tsafi,kawai ƙage aka yi mata wannan dalilin ne ma yasa ta bi dare ta bar masarautar nan” “Wato ƙage na yi mata? Don ubanki da idona na gani tana tsafi.Tashi ki ɓace mini ko na sabauta ki ” ta ƙarashe cikin tsawa,da wani irin sauri kuwa A'ishah ta fita daga ɗakin direct can baya ta nufa inda tantabarun yarima suke.Tana zuwa ta yi tsaye tana kallonsu yadda suke ciyar da junansu da kuma yadda suke yin wanka, murmushi ta soma yi tana jin sonsu ba don komai ba saboda yadda ta san muhimmancinsu a gun yarima.Daga bayanta ta ji muryar Barham yana mai cewa “har sai yaushe ne za ki bayyana asalin fuskarki? ” Ba tare da ta juyo ba ta ce “ ranar da ka bar ɓoyen taka!” “Amma ai kin san ni da ke ba ɗaya ne ba,magani nake bayarwa domin sanin wasu tsirrai dole sai na haɗa da Magic ” A'ishah ta juyo tana wani murmushi kafin ta ce “me yasa kake saka mini ido a lamurrana? Bayan ni ai ka san waɗansu masu ɗauke da kambun baka me yasa ba za ka takura musu ba ?” “Ki iya bakinki ko kuma...” ta yi saurin katse shi da cewa “ko kuma me? Ka je ka sanar da sarki? Hahaha! To bari ka ji abin da har zuwa yanzu tsafinka bai nuna maka ba,hatta yarima Naslam maye ne,yana ɗauke da kambun baka ” Cikin zafin rai Barham ya ce “ ki sani cutar kambun bakan yarima daga Ubangijin Ka'aba take ba wai ta tsafi ba ce,ke kuwa uwarki ce ta saka miki ita.A kullum cikin yin ƙoƙarina nake na ganin na magancewa Yarima cutar nan saboda na san hankalinsa zai tashi muddin ya farga” Shiru A'ishah ta yi tana nazarin kalamansa,wai ita Dadda ce ta saka mata maitar baka hakan na nufin kenan hatta Dadda matsafiya ce? Ba tare da ta ce masa komai ba ta yi saurin barin wurin ta koma can sashensu.Sai dai tana shiga ta tarar da Dadda cikin wani irin yanayi wanda da ace normal mutum ce ita da tabbas har taɓin hankali za ta iya samu. Dadda ce cikin siffar maciya tana a tsaye gaban madubi idonta a rufe tana furzo kalaman tsafi tana haɗawa da sunan mahaifiyar yarima Naslam. A'isha ta yi tsaye tana kallon cikin madubin wanda yake ta fitar da tiriri tamkar an ɗora shi kan wuta har wani hazo-hazo ke tashi. Ummi ce ta gani wato mahaifiyar yarima Naslam tana zaune kusa da ruwa da alamu so take yi ta wuce amma ta kasa shiga ruwan.A kallon farko da za ka yi mata za ka fahimci cewa kaf illahin jikinta dabaibaye yake da mugun baƙin tsafi. Dadda ta yi wata mahaukaciyar dariya tana mai fito da harshe waje tana yin wani tsafin A'isha sai gani ta yi Ummi ta faɗa ruwan,ba ta san lokacin da ta fasa ƙara ba ta ce “Ummiii?” hakan ya jawo hankalin Dadda matsafiya ta kuwa juyo da kanta ta kalli A'ishah tare da juya idonta suka fitar da wani haske ya je ya shiga A'ishah nan take ta faɗi ƙasa a sume. Dadda ta yi saurin komawa normal kafin ta je ta dubi ƴarta,hannuwanta ta kama ta soma janta ƙiii har ta kai ta kan shimfiɗa. Wata kwalba ta ɗauko ta gubar tsafi ta buɗe tare da dangwalo maganin ta shafawa A'ishah babu jima ta buɗe idonta tarau sai dai babu ɗigon baƙi. Dadda ta soma sarrafa tsafi babu jimawa kuwa duk maganar da A'ishah ta yi ita da Barham ta shiga tariyo kanta.Dadda ta naushi iska tana mai cewa “ wato dai mugun tsohon nan ba zai taɓa fita hanyata ba” sai kuma ta luluɓa bargo ta fice ta bar masarautar. A ɓangaren yarima Naslam kuwa a daren ranar haka ya kasa sukuni,yana kwance yana tunanin Naomi haɗi da yin surutunsa ba tare da ya san cewa ba zanen hotonta da ke ƙarƙashin pilow yana naɗar duk wata magana da zai yi ta yadda ita kuma za ta ji komai cikin ƙwaƙwalwarta. Sai wuraren ƙarfe biyun dare ya samu bacci mai nauyi ya ɗauke shi,mafarkin Naomi yayi.Wannan karon ba mu'amala suke yi ba,a'a takobi yasa zai sauke mata kai bayan an ce ta miƙa wuya ta karɓi shahada ta ƙiya.Yana datsa mata takobin ta yi kururuwa wacce kai ka ce a gaske ne sai ya ji abin har kunnensa.Daidai nan ya farka yana jan numfashi tare da soma yin magana shi ɗaya. ★NAOMI Duk da ban ji daɗin abin da ya faru ba tsakanin Banah da Deborah hakan bai sa na wani damu sosai ba saboda a ganina kowanne yana da hujjar da zai kalubalanci ɗan uwansa.Ita matsafiya ce mai rubutun tarihi,yayin da shi kuma matsafi ne mai ilimin jeji don maharbi ne. Washegari haka muka zaga gari ni da Banah a matsayinsa na mijina,kafin kuma yasa shela mutane suka taru a ƙofar gidanmu.Sabbin dokoki ya ƙara kafawa kafin kowa ya kama gabansa,haka muka zauna ni da shi ina basa labarina yayin da shi kuma ya yi mini alƙawari sai da dare sannan ya bani nasa labarin.Wannan yasa ko da daren yayi a ƙage na ce masa “ina saurarenka bani labarinka ” Maimakon yayi abin da na ce,a'a sai ma fatar dabbar da na suturce jikina da ita da ya yane ya soma yana shirin kai hannu kan jikina na zabura sakamakon kalaman nan irin na jiya da na soma ji suna ziyartar kwanyata ba tare da na san daga ina suke ba. “Ya Rabb! Ka taimaka ka kuɓutar da ni daga dukkan wani tarkon sheɗanu da mabiyansu.Ya Ubangijin al'arshi ka bani kariya a duk lokacin da na fuskanci uƙubar mushrikai kamar yadda ka bai wa Annabinka Ibrahim.Ya Hayyu ! Ya Ƙayyum ! Ya zul...” da wani mugun sauri na toshe kunnuwana ina mai yin wata ƙara don tamkar ana ɗiga mini dalma haka nake ji, wannan dalili ne ma yasa ban bari na ji ƙarashe ba.Jikina na yin ɓari na ɗauki suturata na mayar kafin na buɗe ƙyauren ɗakin,sauri-sauri haka nake tafiya har na isa ƙofar gidansu Deborah . A zaune na tarar da ita kan wani kututturen icce tana kallon sama,da alamu aikin nata ne take yi wato lissafin taurari.Gefenta na zauna ina mai cewa “ki yi haƙuri” “Ki yi tambayarki kai tsaye” ta faɗa ba tare da ta dube ni ba. “Wane ne Annabi Ibrahim ?” na tambaye ta a raunace don hatta faɗar sunan ma yana yi mini wani irin raɗaɗi. “Yana ɗaya daga cikin masu isar da wahayin da Ubangijin Ka'aba ya umarce su da shi.Kamar yadda tarihi ya zo Annabi Ibrahim ya fito daga cikin al'ummar da ke bautar gumaka amma duk da haka shi tun tashinsa bai taɓa bautar wani Ubangijin ba sai na Ka'aba.Al'ummarsa sun so hallakar da shi ta hanyar jefa shi a cikin wuta amma sai Ubangijinsa ya cece shi ya mayar da zafin wutar sanyi mai daɗi ba mai cutarwa ba” Shiru na yi ina nazarin bayanin da ta yi mini,ina shirin tambayarta wane ne shi Ubangijin Ka'abar sai ga Banah ya bayyana a gabanmu kamar walƙiya.Hannuna ya kama yana yi wa Deborah mugun kallo kafin ya ce “ina mai yi miki kashedi na ƙarshe ki fita idona na rufe” Debora ta miƙe tsaye tana cewa “abin da nake da niyyar faɗa maka kenan ka guji wasa da wuta” Tamkar wata sokuwa haka na tsaya ina kallonsu,sam hankalina ya ƙi tsayuwa wuri guda abin da nake son sani shi ne wane ne Ubangijin Ka'aba?????????? [13/04 09:49] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 06 Maimakon Banah ya kai mu gida a'a daga nan sai ya wuce da mu gaɓar ruwa. “Shawoli narat kohi jayi!” ya furta kalaman tsafi cikin wata irin murya,babu jimawa wata irin ƙara ta karaɗe wurin kafin ruwan ya soma darewa yana fitar mana da hanya.Haka Banah ya ja ni muka shiga muka fara tafiya,ko tsakiya ba mu kai ba aka soma yin ƙasa da mu har muka dangane da ƙasan ruwa.A nan ne na yi arba da tsoffin garinmu waɗanda suka mutu,wasu tun banda wayo a labari ne na ji mutuwarsu yayin da wasu kuma da hankalina suka yi mutuwar. Kamar yadda ake yi wa baƙo in ya zo a wuri haka suka karrama ni,a wannan lokaci ne na ida ganin ainihin ɓoyayyar fuskar Banah shi ɗin ba iya mutum ba ne a'a jinsi biyu ne. Wani abu aka shayar da ni wanda ya dagula mini lissafi ya juye mini hankali na ji tausayi,so,ƙauna da duk wani abu da ya shafi mutumci sun fita daga zuciyata.Sai dab da za mu fitowa ne sannan aka kawo Maa zuwa gare ni,tana tsaye cikin siffar nan ta matattu sai dai yanayin fuskarta ya nuna tana cikin damuwa kamar ba ta jin daɗin rayuwar wannan duniyar. “Maa” na kira ta ina mai shigewa jikinta,yadda na ratsa ruhin nata na fita shi ya sa ni saurin janye wa na koma kan ƙafafuna. “Naomi me yasa har zuwa yanzu ba ki yi wani aikin bajinta ba wanda zai sa ruhina ya mori aikinki? Dube ni yadda na rame har yanzu ruhikan ruwa ba su yi amanna da ni ba” ta faɗa cikin wani irin yanayi. “Maa sam ban gane abin da kike nufi ba” na faɗa . Ta ce “Ta hanyar kashe mutane ne kawai zan samu abinci Naomi ” ta bani amsa ,wato so take yi na fara

Chapter 7 of 10