Share this page
miƙa mata shi ta koma gefe cike da ƙwarewa ta damƙe kurwar yaron .Da ta fita wankin kayan da suka ɓace ta samu wuri ta haƙa rame ta binne ,duk da zuciyarta babu daɗi amma ji take ya zama doli ta cinye jikanta na farko ko yawunta sun koma. Daren nan dai ba su yi bacci ba jariri nata yin kuka hatta likitocin sai da suka shigo suka duba shi,sai asubahi ya rumtsa wuraren ƙarfe tara na safe aka basu takardar sallama bayan sun biya.Hajara ce ta je ta taro ɗan sahu,bayan ta saka kayansu Murjanatu ta shiga sannan ita ma ta shige tana kallon wurin da ta binne kurwar jariri can ƙasan zuciyarta ta furta ‘ zuwa dare zan zo na tone’ haka suka isa gida. Ta kuwa ci sa'a Daddy bai fita ba,Murjanatu ta gaishe shi ya amsa tare da yi mata barka kafin ya maida dubansa ga Hajara wacce sai raba ido take kana gani ka san ba ta da gaskiya. “ Hakan da kika yi daidai ne? Don dai ba ni ne na haifi Murjanatu ba shine kika koro Habibah daga asibiti? ” “Ka yi haƙuri ba koro ta na yi ba,na dai ce ta dawo gida tun da ba za a barin mai jego ita ɗaya ba a gida” “Mi yasa ba ki kira ni kin shaida min zancen haihuwar ba? Ban cancanta ba ne ko me?” “Ka yi haƙuri Daddyn yara,yanzu dai ka kira shi mijin nata ka shaida masa zancen haihuwar ” Bai amsa mata ba ya fice,sai a lokacin Habibah ta fito idonta kan jaririn wanda ke baccin wahala.Cike da tausayinsa ta ƙarasa ta ce “ barka Murjanatu Allah raya shi kan sunnah” “Amen na gode” ta amsa tare da miƙa mata jaririn,Habibah ta karɓe shi tana mai zaunawa kan kujera ta shafi sumar gashinsa tana kallonsa da kyau ta tabbata kurwarsa na gidan yari ba a cinye ba sai dai ba ta san a ina aka binne ta ba.Haka ta gaji da binciken ta miƙa shi ga uwarsa ta miƙe suna ƴar kallon-kallon ita da Hajara wacce idon nan nata suke wiƙi-wiƙi na maras gaskiya. A sanyayye Habibah ta koma ɗakin Safeenatu,“ ya dai Gwaggo Habibah lafiya na gan ki duk kin yi wani iri?” Feenat ta tambaya. “ Babu komai Safeena,bacci Baseerat take?” “Eh ba ta jima da rufe idon ba” “Mu gan ta” Habibah ta faɗa tare da yin zama, Safeenatu ta ɗora mata jaririyar kan cinya.Hannunta mai safa ta kamo ta cire sannan ta soma shafa shi ,zuciya cike da rauni ta soma yin magana “ ki tausaya ki ceto jaririn da bai san komai ba,ki sani shi ma tamkar Basheer yake mai rauni ne.In kuma har yanzu kuna cikin fushi ne shi yasa kuka hana ta ɗauki mataki ku yi haƙuri,amma dai a duba lamarin” tana gama faɗa Baseerat ta buɗe idonta taram cikin na Habibah,ita kuwa ta shiga kallon abubuwan da suka faru bayan ta bar asibitin a cikin ƙwayar idon jaririyar ta ga komai har inda Hajara ta binne kurwar.Tana gama gani Baseerat ta maida idonta ta rufe, Safeenatu dai na gefe a yanzu ma kallonsu take ba tare da ta ce komai ba. Habibah ta ja ajiyar zuciya ta sakar mata murmushi ita kuwa kai ta ɗauke,tana mai jawo wayarta ta kunna data so take ta yi bincike don gano shin abubuwan da suke faruwa zai iya kasancewa ko kuwa ƴarta ce kawai ke da shi. Tunanin ta watsar ta shiga WhatsApp ta fara duba saƙonnin mutane masu yi mata barka kafin kwatsam ta ganta cikin wani group.A hankali ta soma biyayar abubuwan da ke faruwa sai ta ga amsoshin tambayoyinta kan wani posting. ```“M” CIKIN TAFIN HANNU,MAUME HAND/PAUME DE MAIN Chiromancy wata daɗaɗiyar hanya ce ta hango makomar mutum da kuma fassarar halayyar mutum daga dalilin layukan hannu. Wani lokaci waɗannan layuka na iya samar da lambobi da haruffa. Ɗaya daga cikin waɗannan wasiƙun na iya zama wasiƙar M, ma'anar wacce mystics da dama suka yi nazari a kanta. Kamar yadda mutane da yawa suka yi imani, layukan da ke kan tafin hannunmu suna bayyana halinmu da ƙaddararmu. La lettre M est attribuée à des personnes vraiment spéciales(The letter M is assigned to truly special people). An ba su kyakkyawar fahimta kuma suna wakiltar abokan haɗin gwiwa akan dukkan wasu kasuwanci. Idan mutanen da kake so suna da wasiƙa ta musamman M a cikin tafin hannu ya kamata ka sani cewa ba za ka iya raina masa hankali ba kuma ta wata hanyar ba za ka iya yin ƙarya ko yaudarar wannan mutumin ba. Kasancewar shi mai dubara da hankali da tsantsar lura sosai, mutamin da ke da harafin M a tafin hannu cikin sauƙi zai fahimci cewa ana yi masa ƙarya ne ko yaudara. ``Matan da suke da harafin M a tafin hannunsu suna da zurfin tunani fiye da maza, har ma da waɗanda suke da wannan wasiƙar. Ana yi musu baiwa da ikon sarrafawa da shawo kan duk wani cikas a rayuwa, kuma sun san yadda ake amfani da albarkatu da damar da ake da su. Harafin "M" a kan tafin hannu ma na iya nufin: • Ƙwarewar shugabanci • Iko wato power/pouvoir``` Zuciyar Safeenatu banda bugawa babu abin da take yi har sai da ta ajiye wayar ta je ta ɗauki ruwa masu sanyi ta sha .Ta dawo ta zauna don ƙara duba saƙon sai dai hatta shi kansa group ɗin ya ɓata a wayarta babu shi sam .Kamar mahaukaciya haka ta miƙe ta je ta yi wani gurwanau a gaban net ɗin da aka saka Baseerat,ta zuge zip ɗin ta kalli ƙofar toilet inda motsin ruwa ke ta zuba da alamu Habibah wanka ta shiga ba tare da ita ta san yaushe ta shiga ba . Murya a ɗan kasalance ta ce “ Baseerat ni ce mahaifiyarki,ni na haife ki.Duk wani wanda bai son ganin kin cutu to tabbas sai dai ya biyo bayana,don haka kar ki ga kamar ban son ki a'a wallahi zuciyata raunk ne da ita.Magana nake son yi miki game da abin da na gani cikin wayata,shin kina da masaniya? In dai tabbas ke ƴar baiwa ce kamar yadda saƙon nan ya bayyana to ki buɗe idonki ki kalle ni” ko rufe baki ba ta yi ba kuwa Baseerat ta buɗe idon sai da Safeenatu ta dafe ƙirji saboda tsoro. “Mine ne wai?” daga bayanta Habibah ta tambaya ,zip ɗin net ɗin ta mayar tana mai cewa “ babu komai Gwaggo Habibah,na yarda na aminta da lamarin nan gaske ne ana samun ƴan baiwa to Allah bata ikon yin amfani da ita ta hanyar ƙwarai” ruwan sama ne suka fara sauka a daidai lokacin da Safeenatu ta rufe bakinta. Gwaggo Habibah ta yi wani ɗan ihun murna tare da rungume Safeenatu ta ce “ kin ga ko? Ƴarki ta musamman ce ancestor/ ancêtre suna tare da ita” A wannan daren cike da zullumi da tunani Safeenatu ta yi shi,da ta samu bacci ya ɗauke ta mafarkai ta yi barkatai akan goben Baseerat. Washegari tun da safe kukan jaririn Murjanatu ya cika gidan kamar wanda ake cirewa rai. “Jaririn can ba dai kuka ba” Safeenatu ta faɗa . Habibah ta ja baki ta yi shiru tana tuna jiya irin gumurzun da suka yi ita da Hajara akan kurwar yaron.Dakyar ta yi nasara ta tone ta tare da saka Hajara don doli ta mayar masa abarsa wacce tuni ita kanta kurwar ta yi rauni,kukan da yake yi kuma saboda ciwon jiki ne. ★A kwana a tashi babu wuya wurin Allah yau ne sunan Twins ɗin Safeenatu waɗanda dangin Bashir suka yi bajinta sosai wurin yankan manyan raguna uku biyu na BASHEER ɗaya kuma na BASEERAT .A wannan rana ta farin ciki Safeenatu ta rakuɓe wuri guda tana ta yin kuka,ga shi dai ta sha ƙunshi da kitso ga kuma gizner ta gani ta faɗa amma rashin masoyinta ya dawo mata daram musamman yadda ake ta faɗar an yi masa madadi da kuma addu'o'in da mutane ke yi. Da wannan damar Gwaggo Hajara ta shirya mugunta wacce take kambacin fansar da ta yi niyyar ɗauka akan Habibah da hana ta rawar gaban hantsi.Sai da ta bari duk hankalin mutane ya ɗauku,sannan jarirai duk an fitar da su can tsakar gida saboda zafin da ɗakin ya ɗauka sannan ta nufi ɗakin Safeenatu.Duk da akwai mutane hakan bai hana ta gwada sa'arta ba,“ ungo Safeena Gwaggonki Habibah ta ce ki ci abincin nan kafin ta zo ta yi miki ta ƙarfi tun da dai ke ba ki jin magana kina jego amma kin ƙi cin abinci ” Hajara ta faɗa tare da miƙa mata plate mai cike da nama ya sha jar miya,ta karɓa tana turo baki tare da soma ci don ita duk a tunaninta gaske dai Habibar ta bata.Cike da murna Hajara ta bar ɗakin ta je ta kasa kunne tana jiran sakamako. Da rana mutanen arziki sun cika gida, Safeenatu ta shiga Toilet ta yi wanka da canza kaya daga shadda zuwa less.Kamar wacce aka yi wa wankin ido haka take ganin ƴan biki tsirara tamkar babu kaya jikinsu,zuciyarta ta yi wani mugun bugawa ganin ta soma ganin hanjin cikin mutane yayin da kuma take jin wani abu a bakinta da ba ta san mine ne ba.A daidai nan free page ya ida mai son complete zai tura 800 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [13/04 09:49] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCRW☀️ ____________________________________________ 01 Cikin duhun dusar ƙanƙara wata mata mai ƙusumbi ke ta ɗangala sanda cikin sauri har ta isa wani ƙaton kogo mai cike da hayaƙi kamar an yi gobara.Tana shiga kogon ya fara rawa yana fitar da wani sauti,baƙin bargon da ta luluɓe kanta da shi ta sauke kan kafaɗunta hakan ya bayyanar da shafafar fuskarta wacce babu ido,babu tsinin hanci sai iya baki kawai.Bakinta ta buɗe tana yin wani gurnani mai fitar da magana cikin wani yare na ƙarnin baya “ uleja naho kajulu ramhakaya fyayal!” cak kogon ya tsaya da rawar da yake tare da ɗaukar wani irin shiru kamar mutuwa ta ratsa,babu jimawa kuwa wasu fararen halittu suka fara shawagi ko ta ina. Da sauri ta zube kan gwiwanta tana mai buga gundulalun tafukan hannunta a ƙasa tana mai daɗa furzo wasu kalaman. “Za ki iya gabatar da abin da ke tafe da ke” wata murya ta ratso iska ta bata umarni. “Naomi!” ta furta cikin rawar murya. “Alƙaluman doka sun riga da sun ƙafe babu wani canji da za mu iya yi miki” aka bata amsa. “Ita ɗin yarinya ce ƙarama ƙwaƙwalwarta ba za ta iya ɗaukar wannan hatsabibin tashin hankali ba” tana gama rufe bakinta wata tukunyar ƙasa ta faɗo a gabanta ,“ki bata waɗannan ruwan ta sha daga nan komai zai tafi kan tsari” Tukunyar ta ɗauka kafin ta gyara luluɓinta sai kuma ta fito,bai wuce tako uku da ta yi ba sai ta furta wani furuci wanda ya haifar da wata hatsabibiyar guguwa tashi ta zo ta zagaye ta tana fitar da wani iska,sannu a hankali guguwar ke daɗa yin sama da ita a haka ta ɓace ɓat kamar walƙiya ba ta bayyana ko ina ba sai a ƙofar gidanta. Ina zaune ina ƙulla garin magunguna na ji motsi,da sauri na ɗago kai sai na hangi Maa na daidaita rufin ƙyauren gidanmu.Murmushi ne ya wanzu a fuskata ba tare da na ce mata komai ba na ci gaba da kallonta har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana mai miƙo mini tukunyar hannunta.Na karɓa,sanyin haɗi da wani shock suka ratsa ni yayin da na ji kwaɗayin shan ruwan ciki.Baki na kafa na soma shan abin da ya kasance a ciki don sai bakina ne kawai ya iya tantance mini kallon kitse na yi wa rogo don kuwa ba zallar ruwa ne ba. Ina ajiye tukunyar sai na ji tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwaƙwalwa,wasu abubuwa da suka keɓancin mahaifiyata nake son sani. “Maa me yasa ake kiranki da mayya?” “Saboda ababen bauta sun mallaka mini baiwar da ta keɓanta da ta sauran mutane” “Kina nufin makantar ido?” “Eh! ” “Amma ai kina gani duk da babu gurbin ido a fuskarki ” “Naomi??” muryar ƙawata ta katse zaren tambayoyin da nake yi wa mahaifiyata wacce ta kasance jigona,bango abin jiginata. Miƙewa na yi da sauri ina ƙara gyara zaman fatar dabba wacce ta suturta tsaraicina ina mai duben Debora wacce ke sanye da wani tsohon bargo duk ta yane jikinta da shi.Murmushi ta sakar mini kafin ta yi mini alama da hannu,Maa na duba ina mai cewa “zan yi wa Debora rakiya ne” “To kar ki jima saboda lokacin zuwa farauta ya kusa” Maa ta bani amsa,ba tare da na ce komai ba na kama hannun Debora muka fito ƙofar gidanmu wanda ya kasance na kara. “Ya meke labari?” na tambaye ta . Kamar munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce “zo mu je na nuna miki wani abu” sai kuma ta fara ɗan gudu-gudu tana nufar bayan gari yayin da ni kuma nake take mata baya har muka isa bakin Teku .Da wani irin kallo na bi ta da shi ina mai cewa "me kuma za mu yi a nan?” Da hannu ta yi mini nuni da can tsakiyar ruwa,sai dai sam ban ga abin da take son nuna mini ɗin ba.Lura da hakan yasa ta ce “yi kamar za ki rufe idonki” hakan na yi na lumshe manyan idona kafin na ɗan buɗe su a hankali sai a lokacin na ga wani abin mamaki wanda tunani da hankali ba za su ɗauka ba.Dogon tsani ne a cikin ruwan tare da shata wata doguwar hanya da alamu za ta ɓulle a wani wurin.Umarnin zuciyata ƙafafuwana suka bi ba tare da na shirya hakan ba na ji sanyin ruwa ya ratsa ni.A hankali nake tafiya har na isa kan tsanin na fara taka matakalansa sai dai ban fi tako uku ba na ji kamar an tunkuɗo ni sai ganina na yi a wani wajen na daban ko kuma na ce wata duniyar wacce ta sha banban da wacce na taso na tsinci kaina a cikinta. Wasu halittu ne masu irin siffata sai dai yanayin launin fatarsu da kuma shigarsu ya sha banban da irin ta duniyarmu.A karon farko da na ji tsoro,don ban taɓa ganin irinsu ba .Ƙafata ta hagu na ɗan mayar a baya ina kallon yadda wani mutum ke musayar wuta shi da maƙarabansa,ina daf da na koma cikin ruwa muka yi ido huɗu da shi hakan ya haifar mini da matsanancin faɗuwar gaba tare kuma da rikicewar tunani.Mun shagala da kallon juna ,ƙarar wani abu da ban san me ake kiransa ba ya dawo da ni hayyacina.Sai da na yi dogon nazari sannan na fahimci cewa ta cikin ƙirjinsa ne aka halba masa abar kashe mutane.Faɗuwa yayi ƙasa,wanda hakan ya jawo hankalin tawagarsa kusan su duka na ji sun ce “yalaɓaiii?” kafin su yo kansa,ɗaya daga cikinsu ne ya zube ƙasa tare da ɗora kansa kan cinyarsa yana mai cewa “Naslam?” cikin tashin hankali yake kamar yadda fuskokin sauran suka bayyana. Abokan adawarsu ne suka fara yi musu sarƙa suna gargaɗarsu da su miƙa musu wannan mutumin kawai suke buƙata in kuma sun ƙi za su kashe su duka su tafi da shi. “Rayukanmu fansa ne akan shugabanmu babu gudu babu ja da baya don haka dakaru ku juya ku fuskance su” shi ne abin da ya faɗa yana mai shimfiɗe Naslam ɗin. A wannan gaɓar ce na ga wani al'amari mai shige da irin rayuwarmu ta can duniyar,yadda su mutanen da ke neman ran Naslam duk suka wani zazzalo harshe waje suna sarrafa shi,kafin ƙyaftawar ido sai gawarwaki nake gani suna faɗuwa. Idona na ji suna yi mini ƙaiƙayi ,babu jimawa suka furzo da wani hatsabibin haske wanda ya tarwatsa taron Mayun duk suka faɗi babu rai sai ɗaiɗaiku ne suka gudu. “Naomiiii?” na ji muryar Debora tana kirana daga ta can ɓangare,kamar kifi haka na faɗa ruwa na koma duniyarmu.Ko da na fito daga cikin ruwa jama'ar gari na tarar duk sun cika wurin suna jiran fitowata.Ko kaɗan babu wani damshi ruwa a jikina a bushe nake ƙamas,sai dai a akwai banbanci tsakanin lokacin da na shiga da kuma yanzu da na fito.Kaf illahirin jikina ya rine yayi baƙi yayin da kuma wani abu da nake tunanin ƙusumbi ne ya bayyana a bayana.Fuskokin wasu cike da mamaki yayin da wasu kuma na hango tsoro da hassada a tattare a ciki. “Naomi me kike yi ƙasan ruwa kusan kwana biyu ba ki fito ba?” ƙawata Debora ce ta zo gare ni tare da tambayata. “Kwana biyu ?” na maimaita yayin da kuma cike da mamaki,ɗaya daga cikin tsofin garin ta matso tana mai nuna ni da yatsa tana mai cewa “dama tun ranar da aka haife ki na hango ajalin mahaifiyarki a tattare da ke saboda kin tabbata butulu ki rasa wacce za ki kashe sai wacce ta kawo ki duniya” sai kuma ta juya ta fuskanci mutanen gari tana mai cewa “kuna ta tambayar wa ya kashe Maa to ƴarta ce” Normal mutane ne kawai suka tsorata da furucinta yayin da su kuma dangina masu ido uku suka rufo kaina suna mai cewa “ita ma a kashe ta” sai dai ko kusa da ni ban bari sun ƙaraso ba na yi wani furuci duk suka ƙame ƙyam a wuri guda kamar wasu bishiyoyi. Magana na soma yi sai dai abin mamaki ba muryata ba ce ke fita,ta mahaifiyata ce.Gargaɗi ne mai ban tsoro haɗi da bushara ga waɗanda suka yarda suka miƙa wuya a bisa sabuwar dokar da na shimfiɗa musu.Kamar yadda ake rusunawa sarki haka duk suka zube suna jinjina mini haɗi da gaishe ni,ƙawata Debora ce kawai a tsaye tana wani mayen murmushi mai fitar da tsantsar farin ciki. Hannunta na kama na ratsa ɗimbin jama'ar muka wuce,har muka isa gidanmu ni da ita babu wanda ya cewa wani kanzil.A ɗaki na tarar da gawar Maa a kwance tuni ta fara ruɓewa tsutsotsi na shige da fice ta bakinta.A lokacin ne na ji wata murya daga can cikin ruhina tana bani mafita da shawari,yayin da ni kuma na yi tako ɗaya na aiwatar da abin da na ji.Hannuna na ɗora a goshin Maa na soma yin wani furuci wanda ban koya ba,kawai zuwar mini yayi.Babu jimawa ta soma bajewa tana komawa hayaƙi a haka har ta baje gaba ɗaya sai sautin muryarta da ya soma yi mini bushara “ ina tare da ke a duk inda za ki kasance ƴata Naomi kar ki yi baƙin cikin rabuwarmu wannan shi ne matakin nasararki,hidimar da za ki yi kuma na san mahaifinki zai yi alfahari da ke.Zan tafi na koma asalina,a duk lokacin da kika yi kewata ki je magudanar ruwa ki cilla dutsen karlis zan jiyo sautin kiranki” tana gama faɗar haka aka kece da ruwa mai bala'in ƙarfi wanda rufin ɗakinmu bai iya tare shi ba.Na yi saurin lumshe idona ina jin sabuwar halittata na yi mini wani irin motsi haɗi da ƙara girma wanda silar haka na ji kafaɗata ta ƙara nauyi hakan ya haifar mini da ɗan rusunawa kamar dai yadda mai ƙusumbi ke yi. An ɗauki lokaci kafin ruwan ya tsaya cak ,sai a lokacin kuma na tsinci muryar Debora na cewa “haƙiƙa kin kasance mai babban rabo ƙawata,ina mai sanar da ke cewa nan ba da jimawa ba amon mulkinki zai ƙetare duniyarmu ta ruwa ya tsallaka duniyar turɓaya ” Sai da na haɗiye wasu yawu masu ɗaci kafin na ce “a yau na ga wata duniya ,wasu mutane na gani a siffar tawaga biyu,ɗayar tawagar ta kasance ta Mayu ce yayin da ɗayar kuma ban san ta mece ce ba abin da kawai na iya gani shi ne fuskokinsu na fitar da wani irin haske mai natsuwa haka ma hannuwansu.A goshin shugabansu na ga abin da ya kusan dakatar da numfashina,wani baƙin tabo ne wanda ya ƙawata goshin nasa ya kuma fitar da tsantsar hasken fuskar tasa” “A yadda kika siffanta su sak sun fito a al'ummar nan da ke bautar wani Ubangijin Ka'aba,sam ba su nuna tausayinsu ga matsafa da kuma waɗanda suka saɓa dokar Ubangijinsu” Zuciyata ce na ji tana wata irin tafasa hakan yasa na juyo a fusace ina kallon Debora wacce ita ɗin ta kasance ƴa ga babban malamin ilimin tarihin duniya.Tun da na ji ta ambaci haka tabbas kuma na san gaskiya ta faɗa ,“dama har akwai masu tsanar Magic a duniya? Shin ba su san tasirin tsafi ba ne ko kuwa sun jahilci lamarin ne?” “Ko ɗaya! Su ɗin sun yi imani a kaf duniya babu wanda ke tafarkin gaskiya sai wanda ya kasance ɗaya daga cikinsu.Wannan dalilin ne ma yasa suke shirya yaƙi duk shekara suna shiga ƙasashen matsafa.Kin ga mu bar maganar nan ma saboda ba ta shafe mu ba” “Ta ya za ki ce ba ta shafe mu ba alhalin kin san duniyarmu ba mu yarda da wani addini ba? In fa suka farmake mu?” ban san me yasa na ji tsoro da shakku dangane da mabiya addinin ba, musamman in na tuna fuskar mutumin nan Naslam. Debora ta riƙo hannuna tana mai cewa “masana tarihi sun tabbatar mana cewa yankinmu zagaye yake da ƙoramai ta yadda babu wata halitta da ta isa ta ƙetaro izuwa nan sai da izinin esprit ɗin ruwa,kina tunanin uwayen gijinmu za su lamunta a kawo mana hari ?” wani irin numfashi na sauke ko ba komai kalaman ƙawata sun ɗan rage mini fargaba amma duk da haka ban yi ƙasa da gwiwa ba na yi shela ina son ganin dukkanin matsafan garin domin zuwa kowacce kusurwar ruwa su kai saƙo zuwa ga aljanai da ruhikan ruwa....... [13/04 09:49] MRS SADAUKI: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐 """"""""""""""""""""""" LoVe aNd HoRrOr StOry☠️ ```MRS SADAUKI```💫✍️ FCWA☀️ ____________________________________________ 02 Ƙananun shekaruna ba su hana ni jagorantar tsoffi da kuma dattizai zuwa bakin kowacce kusurwar ruwa ba.A tsaye nake ƙiƙam ina kallon yadda ake masayar kalamai tsakanin aljanun ruwa da kuma matsafa,kamar yadda na faɗa musu tun farko ina son a bai wa garinmu kariya haka su ma suka faɗa sai dai aljanun sun ƙi lamincewa da ƙudirinmu kai tsaye sai da suka kawo nasu sharuɗan.Daga ciki akwai bayar da jinin baƙaƙen dabbobi duk ranar laraba, sannan a kowacce ƙarshen shekara ɗaya daga cikin mutanen yankin zai zama hadiya ta aljanai. Shiru wurin ya ɗauka suna kallona,suna jiran amsata a matsayina na shugaba.Ni ma shirun na yi ina nazari,wanda ban san ashe cewa tazarar lokacin da na ɗauka kafin na miƙa yardata ya fusata aljanun ruwan sun komawarsu. “Sun fusata ba za su sake yin magana ba sakamakon shirun da kika yi yayi yawa.A matsayinki na shugaba ya kamata a ce kina bada amsa ne a kai ba tare da nazari ba” ƙawata Debora ce ta yi wannan furucin idonta na kallon tsakiyar ruwa.Dukkan matsafan sun yi amanna da furucinta,ban ce komai ba sai taku da na fara yi ina ɗaga kafaɗata gefen da ke da ƙusumbi na shiga can tsakiyar ruwan.Tafin hannuna na hagu na kalla ina yin wani furuci nan take ya tsage jinina ya soma ɗiga a cikin ruwan.Duk ɗigo ɗaya ina iya jiyo wani nishi daga can ƙasan ruwa,na ɗauki kamar minti biyu a haka kafin na dakatar da zubar jinin sai kuma na soma yin magana cikin sauti ƙasa-ƙasa “joliho kuntahee namaruju kalmari hanaighar kashmuh balbilancaaaa!” babu shiri na lumshe ido jin yadda wata irin guguwar ruwa ta tashi tana tunkuɗo duk wani masarafin tsafi izuwa gare ni. “Ya ke ƴa ga Bazuka ki sani cewa kowanne tasiri da farashinsa,sannan mu halittun ruwa ba mu taɓa mance duk wata alaƙa da aka ƙulla da mu .Za mu bai wa garinki kariya kamar yadda kika buƙata sai dai ki sani a duk lokacin da kika take dokarmu za mu bayyana miki asalin me ake kira da masifa da annoba ” wata murya da ke kama da ta macijin ruwan ta yi mini jawabi. “Hakan ba zai taɓa faruwa ba,zan kiyaye dukkan sharuɗanku” wannan karon na bada amsa kai tsaye. “Mu ne za mu zaɓar hadiya da kanmu,a duk sa'ilin da lokaci ya yi za mu nuna miki mutumin da muke buƙatar jininsa ta mafarkinki ” “Na amince!” “Sannan kuma haramun ne shiga ruwa ranar Laraba ” “Na amince!” ina furta haka kawai sai yanayin garin ya canza ya ɗauki wani irin launin duhu amma ba sosai ba,sararin samaniya ya cika da baƙaƙen giza-gizai yayin da kuma kukan tsuntsaye da kaɗawar bishiyoyi ya tsaya cak. “Aroroke! Aroroke! Aroroke!” shi ne abin da sauran mutanen da muka zo suka fara faɗa cikin murna saboda dukkan

Chapter 5 of 10