An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
SANADIN KENAN!
1
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
Babbangoro2015@yahoo.com
takorikabara@gmail.com
SADAUKARWA
Littafin AMINA sadaukarwa ne ga duk makaranta littattafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda bansani ba. Ina son ku, ina alfahari daku. Allah ya kara zumunci.
GARGADI
Ba’a yarda a karanta ko a rubuta littafin nan a kowacce kafar sadarwa ba, gidan radio da sauransu ba tareda izinin marubuciyar sa ba. Yin hakan zai jawo gurfana a karkashin shari’a insha Allahu.
TUNASARWA
Ba labarin wani ko wata nawa bane, kirkirarren labari ne don fadakarwa da nishadantar da mai karatu. A guji zargin cewa anyi ne don wani ko wata. AMINA kirkirarren labari ne.
SHIMFIDAR LABARIN
Yayi missing flight dinsa ne mai zuwa Abuja ba da son ransa ba.
Ashe da rabon zai ga bacin ran da bai taba shiga kwatankwacin sa ba.
Ta danna madannin kararrawar dake jikin bango ta kiran ma’aikatan gidan, nan da nan mutum biyu suka zo, samari ne guda biyu masu share-share da goge-gogen gidan, ba wanda bai wuce shekaru ashirin a cikinsu ba.
“Ku dauketa ku kaita ‘toilet’ kuyi mata wanka, ku cire mata ‘pampers’ dinnan tun dakin bai soma wari ba”.
Matasan biyu suka dubi juna kamar masu yin shawara, ta galla musu harara “ko bazaku yi bane?” Da sauri suka ciccibo yarinyar, daya ya riko kai daya ya riko kafafunta sukayi bandaki da ita, suka tube ta suka cire ‘pampers’ zasu soma wanke ta.
Kamar wanda aka jefo ya shigo babu zato babu tsammani. Yana so ya gaya mata jirgin ya tashi ya barshi sakamakon wasu muhimman baki da yayi suka tsaida shi. Saidai ya jira na yamma insha Allah.
Idonsa bai sauka akan komai ba sai kartin maza kabilu rike da Amina sun tube ta, idanunsa suka kada sukayi jawur, zuciyarsa ta rika wani irin tafarfasa, hakan bai sa yayi magana cikin fada ko bacin rai ba, a sanyaye ya zuba mata ido na ‘yan dakiku kafin ya soma magana.
“Maza balagaggu kika sa suka tsiraita ‘ya ta haka? ‘Yar tawa kwalli daya Lailah?? Ban yi zaton ko auren kiyayya kika yi dani ba Lailah bazaki iya taimakawa mara lafiya marainiya ba!
Kina nufin su sanya hannu a (private part) din diya ta? Ban taba dukan mace ba, bana fata in fara a kanki, kije duniya ce, kuma in gaya miki wannan yarinyar ta fi mun duk abinda na mallaka da rayuwar baki dayanta. Kisa a ranki kema mace ce, kuma zaki haifa, baki san yaya kaddara zatayi da abinda kika haifa ba kina raye ko bakya raye”.
Kallo daya ya yiwa ma’aikatan suka saki ‘pampers’ din da suke cirewa suka yi waje. Cike da addu’a a zukatansu, kada Allah yasa wannan ya zamo sanadin hanyar abincinsu. Suma sun ji umarnin da aikin da aka sanya sun ‘odd’ to amma meye laifinsu? Salin-Alin suka fice.
Da sauri ya wanke Amina da kansa yayi mata wanka da soso da sabulu mai kamshi, ya nado ta cikin shawul ya fito da ita. Ya shafe ta da vaseline ya sanya mata sabuwar ‘pampers’ da sababbin riga da siket masu kyau. Sannan yayi waya kicin a kawo masa ‘tea’ da ‘pancake’.
Da kansa ya rinka baiwa Amina a baki wani na shiga wani na dawowa yana goge mata har ta koshi ta ture. Jiki ba kwari Laila ta wuce don ganin yadda yayi kamar babu ita a dakin. Bata taba tsammanin zai dawo a yau ba sai bayan kwana uku kamar yadda ya ce. Ta kulla a zuciyar ta ko ‘cangal’ bazata yiwa yarinyar ba har ya dawo.
Maganganun da ya gaya mata ba su ta zata ba, tafi zaton dan banzan duka daga gareshi yadda ta lura yana son yarinyar tasa. Kafafunta ba kwari ta nufi dakinta.
Ya sumbaci Amina a goshinta ya mayar da ita ya kwantar ya gyara mata pillow, ya fito falo ya jibgu a kujera mai tsananin taushi. Ya kai hannun damansa ya dafe kzźansa dake tsananin sarawa. Ji yake dan son da ya fara yiwa Lailar na ‘decreasing gradually........(raguwa a hankali). Zufa ta shiga karyo masa, da ya tuna kalami na karshe na uwar Amina.....
“Ka kara kula da Amina, ba don na raina kulawarka gareta ba, she will need extra more...”.
Yess! Tana bukatar karin kulawa, kuma zata samu insha Allah in har ina raye kuma kudi suna da amfani zata samu kulawa. Da gaske kula da ‘ya mace sai mace. Na lura matar nan son kashe min Amina tayi ko abinci bata bata ba har karfe biyu na rana. Kuma tasa maza su tozarta ta ba don Allah ya dawo dani ba.
Ya san muddin ya gayawa Hajiyarsa wannan abun cewa zatayi zata dawo ta kula da jikarta. Bayan yanzu ta fara samun nutsuwa a gidan mijinta da nata koshin lafiyan, hankalinta ya tsaya waje guda. Zaiyi ‘finding solution (nemo mafita) da kansa.
Babu wanda ya fado masa a rai sai tsohon abokinsa Dr. Usman Turaki. Consultant a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa teaching hospital.
Tare sukayi sakandire, sun shaqu sosai a wancan lokacin, yanayin karatu a gaba ya raba su, kowa da jami’ar da ya wuce da fannin da ya zaba.
A take ya zakulo lambar Dr. Turaki, ta jima tana kara kafin matarsa ta daga. Abinda tace shine “Doctor is on call. A gida ya bar wayarsa” “ok. Please da ya dawo kice ya kira ni da wannan no.din. Ma’arouf Ji-qas ne”. “Insha Allah zan gaya masa”
“nagode agaida yara”
“zasu ji. Allah ya tashi kafadun Amina”.
Ji yayi kamar ta yi masa addu’ar Allah ya sanya shi a aljannah. Wato komai na dan siyasa baya buya. Kamar kasawa ake a faranti ana terere da shi. Kowa yasan yana da ‘ya mara lafiya.
Dr. Turaki na komawa gida matarsa Zainab ta isar masa da sakon abokin nasa, ko abinci ta kasa bari ya ci. Balle ta barshi yayi wanka, amma tayi kokari ainun wajen boye azarbabinta da murnarta na yau ta yi magana da Ji-qas. Tauraron taurari a wurin al’ummar Bauchin Yakubu.
“Zan kirashi gobe dana shiga ‘office’
“Haba kai kuwa Baban Aadil, ka kirashi yanzu mana muji menene? Ka sani ko kujerar Makkah ce?” Dr. Turaki ya tuntsire da dariya,
“Zainab mai idon cin naira, ki bari Allah ya bashi kujerar Bauchin, Makkah kinje kin dawo insha Allahu”.
Ita dai Zainab ba haka ta so ba, ta so ya kirashi tana zaune taji kwaf! Ko samu ne.
Kamar yadda ya cewa matarsa, yana shiga ofis washegari ya bude tagogi Ji-qas din ya fara kira.
A lokacin yana baiwa Amina ‘golden morn’ ya dakatar ya daga kiran Turakin.
“Sai yanzu kaga damar kira na?” “Afuwan Yaa Maulaaya, lokutan likita a kididdige suke” yayi murmushi, ba raha ya kira shi suyi ba kamar da, da ya bashi amsa don haka kai tsaye ya zarce da gaya masa makasudin kiran.
“Akan ‘yar ka Amina ne. Mun bar gadon asibiti don dukkannin mu ba zamu iya ba ni da Hajiya, saboda wasu muhimman uzurirrika musamman ni da yanayin rayuwata ba na tsuguno bane a wuri guda. Sai na tsaya nayi tunani akan abinda yafi kawai inyi ‘hiring professional’.
Ina son hayar (physiotherapist) da zata cigaba da baiwa Amina (treatment) a gida da kula da komai nata bilhaqqi, zata bar aikinta na asibiti ta zauna da Amina a gida ta cigaba da kula da ita tsahon shekara daya mu ga abinda Allah zai yi.
Zan ninka mata albashin data ke karba a asibiti sau hudu a kowanne karshen wata.
Saidai Turaki ba kowacce ba, shi yasa ma na biyo ta kan ka ban bi ta kan likitocin Amina ba. Ina son wadda akwai sanayya ta sosai a tsakaninku, ka yarda da ita, ka yarda da tarbiyya da amanar ta. Mata tsoro suke bani Turaki. In kana da kudin da zaka basu babu mai zama da kai tsakani da Allah. Yau na firgita na tsorata da al’amarin mata yadda baka zato. Sun karya min zuciya sun kara sa ni kewar Mahaifiyar Amina. Mata irin ta tsiraru ne a cikin al’umma.”
Dr. Usman ya ja numfashi, babu wadda ta zo masa a rai sai likitar da ya raina da hannunsa, ya kwashe shekaru bakwai zuwa takwas tare da ita, ya lakanci dukkan halayen ta; Dr. Amina Mas’ud Shira!
Dukkan suffofin da Ma’arouf ke so (proffessional) din ta kasance dasu Amina ce ta mallake su. A dai likitocin wannan bangaren nasu (physiotherapy) da ya sani a duniya.
“AMINA MAS’UD SHIRA!”
Ya furta da sauti mai dan kauri (husky) kuma a hankali, kamar a zuciyarsa ya fada, Ma’arouf din ma bai ji sosai ba.
“wacece haka?”
Suna ne na likiciyar data dace da komai daka ambata ne. Dalibata ce, ni na raine ta, physiotherapist ce”.
“Ka yarda ta hada duk abubuwan dana lissafa a sama?” “har ma ta zarta. Proffessional ce data san kan aikinta at a very young age.
Bayan lakantar aikinta harda baiwa cikin al’amarin ta. Ta karbi ‘award’ shekarar baya na ‘Best Physiotherapist in Africa’. Sannan ‘yar babban gida ce, by saying this, ba ina nufin gida na masu kudi ba a’ah, gidan tarbiyya da mutunci. Ka fahimce ni? ”.
“Na fahimta. Ka yi mata magana toh. Cewa zan dauketa kwangila na tsawon shekara daya in bata da aure. Ta kula min da mai sunanta paralysed diya ta. Zan ninka mata albashin ta sau hudu in ta amince. Duk karshen mako sai ta tafi gida, nikuma zan maida kwana biyun lokutan zamana da Amina in cigaba da kula da ita har ta dawo....” “.......excuse me please....” Turaki ya katse shi da wani irin tune mai kama da tun zura a muryar sa, “meye amfanin matarka idan har bazata iya kula da abinda ka haifa ba ko da na kwana biyu a sati?”
Murmushi yayi, zuciyar sa ta hasko masa yadda karti biyu suka tube Amina a bandaki a bisa umarnin Laila, tana gefe toshe da hanci, idanunsa suka wani irin rine sukayi jajawur da kyar ya bashi amsa.
“Ban aureta don in sa ta jinya ba. Yaushe zaka yi magana da likitar?
“lallai” Inji Dr. Turaki. Ya san zurfin cikin Ma’arouf din bazai barshi ya zurfafa zancen ba, haka Allah ya halicce shi, amma jikinsa ya bashi akwai wata a kasa. Ya kyale zancen shima ya bashi amsa.
“insha Allahu gobe. Yau tana off. Sannan sai ka dan tsahirta ta rubuta (leave without pay) that’s in har ta amince kenan. Zanyi kokari a bata (leave) din don ba kowa ake baiwa ba. In kuma bata amince ba sai mu nemi wata....” “no please. Ita kadai na aminta da. Idan bata amince ba I will find another solution”. “Jikina yana bani zata amince saboda tana ganin girma na kuma bata yi auren fari ba”.
Da wannan suka kawo karshen tattaunawar tasu.
****
Dr. Amina Mas’ud tana (ward round ) ranar Litinin da safe aka aiko wata nos ta gaya mata Dr. Turaki na kiranta in ta gama abinda take yi. Ta amsa da “toh” a zuciyarta tana fadin ‘this is not his habit (wannan ba dabi’ar sa bace) kebewa da mata, ko kiran likita yana tsakiyar aiki. It must be important. Kwana biyu basu zo aiki ba saboda ‘election’ (zabe), bayan zabe kuma taje kauye gaida Baffanninta ta kwana biyu, don haka yau tanada aiki da yawa zai shiga lokacinta gaskiya.
Ta cigaba da zagaya marassa lafiyarta daya bayan daya tana rubutu a files dinsu bayan ta yi musu tambayoyi har ta gama. Sannan ta nufi ofishin consultant din nasu.
Da sallama ta bude kofar ya amsa sannan ta shiga,
“have a seat please Dr. Amina”.
Ta zauna, sannan ta gaisheshi. Ya amsa cikin sakin fuska sannan ya dora bayani.
“Nasan kinsan Engnr. Ma’arouf Ji-qas ko? Ba sai na gabatar dashi a gareki ba?”
“Na fara sanin shi a bakin Yayana Ilya, na sanshi a kafafen yada labarai tun yana dan majalisa, na kara sanin shi shekaranjiya waccan as the elected governor (matsayin wanda ya lashe kujerar Gwamna). Ka ga kuwa na san shi da yawa. Har kuri’a saida Ilya ya tattagemu muka je muka sa masa nida Goggona.
An shaideshi da cewa mutumin kirki ne. That’s all I know about him. Bayan wannan bansan komai da ya dangance shi ba”.
“Da kyau. Kin taba sanin yana da (paralysed daughter) mai shekaru biyar?”
“gaskiya bansani ba. I know nothing concerning his personal life (bansan komai na kebantacciyar rayuwarsa ba. Maybe Ilya ya sani, sabida shige-shigensa da bin kwakkwafinsa a kansa”,
Usman Turaki yayi murmushi.
“To shine yake neman wani taimako daga gareki.... kodayake ta wani fannin baza’a kirashi taimako ba tunda aikinki ne ya gaji hakan, kuma abu ne da ba kyauta zaki yi shi ba. You are on your proffession. Yana so ki koma gidansa da zama ki cigaba da bawa yarinyar sa (treatment) da asibiti ke bata zuwa shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Kinsan dai yadda (paralysis) yake ba abu ne da za’a ce ga ranar tashi ba tunda bashi da kayyadadden lokaci. Yayi alkawarin ninka miki albashin da kike karba daga gwamnati sau hudu a kowanne wata. Duk (weekend) zaki tafi gida ki dawo Monday.
Na yarda da kwarewar ki akan aikinki da sadaukarwa. Shiyasa na zabo ki cikin dubu. A ganina wannan wata hanyar samun alkhairi ce mai dimbin yawa gareki da iyayen ki. Amma zamu baki gajeren lokaci kiyi tunani ki kuma nemi amincewar iyayenki daga yau zuwa gobe saboda hakan ya bukata, yaya kika gani?”
Amina ta nisa. Tunda ya fara magana bata katse shi ba. Ba rayuwa a ‘government house’ ne abinda ya dadata da kasa ba a’ah, kudin nan da za’a ninninka a bata wadanda in a asibiti ne sai tayi shekaru tana Tarawa, ba kuma amfanin kanta zatayi dasu ba, burin data dade dashi akan Goggonta zata cika dasu ta huta tarin data soma tun fara aikinta mai bata lokaci da cin rai, har yau kuma bata tara kwatan abinda take son tarawa ba tunda ba wani dadewa tayi da fara aikin ba, gaskiya ilmi mai zurfi yayi a rayuwa don har abada bazaka daina cin moriyarsa ba. Allah yasa Goggon ta amince.
******
Amina da Goggonta, tareda Inna Zulai Babar Ilya kuma aminiyar Goggon, da Goggo ta kirawo don ta taya ta jin wannan almara ko kuwa rashin kan-gado da Amina tazo mata da shi.
“In banda rashin kan-gado irin naki Amina, ina hankali na zai kwanta kina kwance wani muhalli daban da nawa, alhalin nasan ban yi miki aure ba?” Goggo ta fada cike da damuwa, muryarta a sanyaye.
Inna Zulai ta ce
“Dama ace aurenki zai yi ne don ki kula da diyar da ya fi armashin ji”.
Amina ta jefawa Inna Zulai harara ta gefen ido, ganin tana tufksa tana kara warware mata. Amina ta gyara zama.
Goggo akan aikina nake. Mune proffessionals din da ake ‘hiring’ har gida mu kula da mai lalurar shanyewar barin jiki ‘if a person can afford (idan mutum zai iya biya). Sannan ban bar aikina na gwamnati ba za’a bada aro na na shekara daya ne in daina karbar albashin gwamnati in karbi na wadanda suka haye ni. Ki kwantar da hankalinki Goggo duk karshen sati zan taho gida in koma Lahadi da yamma. Sannan fa akwai matar aure a gidan. Kuma Goggo gidan gwamnati ya wuce duk yadda kike tsammani. Girmansa da fadinsa in ba kai ka nemi mutum ba ba abinda zai hada ku. Albashina za’a ninka sau hudu Goggo bada jimawa ba Allah zai cika min burin dana ke dashi akan ki. Ki barni nayi aikina Goggo in har kin yarda akan-kanki cewa kin bani tarbiyyya yadda ya kamata. Duk inda na shiga zan iya kula da kaina Goggo, zan nuna tarbiyyar da kika yi min da yardar Ubangiji bazan baki kunya ba. Hakan bazai yiwu ba ba tareda na samu goyon baya, kwarin gwiwa da albarkar ki ba Goggo.
Shekaru bakwai ina karatu a Jami’a wbaki taba samun wani abin Allah wadai daga gareni ba, sai don zan je aiki na shekara daya duk karshen mako ina tare da ke? Da zanyi hidimar kasa Gombe na tafi, duk baki nuna damuwa ba goggo sai wannan da muke cikin gari daya?”
Goggo ta nisa, “Amina mutane da halayen su canzawa suke kamar wahainiya in suka samu daular duniya, ina tsoron ki da shiga daular nan Amina kada halayen ki da tarbiyyar ki su canza...”.
Kafin Amina tace komai Ilya yayi sallama ya shigo. Amina ta gode Allah a zuciyar ta don ta tabbata mai taya ta wannan ‘battle (yakin) da wadannan dattijai masu tsoron duniya da abinda ke cikinta ya zo. Itama tana yarda da abinda suke hangowa kawai tana kare kanta ne don tana son yin aikin ko burin data ke dashi akan Goggo ya cika. Ba tana son yin aikin bane don taje taji dadin rayuwa ko makamancin hakan, zata cika alkawarin data taba yiwa Goggo ne tun tana kankanuwa.
Goggon da bata yi karatun zamani ba, amma ta tsaya (against all odds) ta samar dashi gareta, ta cika mata burin ta, har gashi yau al’umma na amfana da ita, ya zame mata hanyar samun abinci na har abada, ya zama silar samun hanyar dogaro da kai a gareta.
Kullum ta dauki albashi cikin asusun ta sai ta tuna babanta,
“Ina ma kana raye Baba? In rashin kudi ne yasa ka sha wahalhalun da ka sha a rayuwarka, yau ga kudin na samar maka bani da abinda zanyi dasu. Don haka zanyi komai da gumi na don Goggo taji dadi a karashen rayuwarta.
Ilya ya shigo ya zauna gefe “Wai me kuke tattaunawa ne ana gani na aka yi wani gumm?”
Goggo bata tanka ba, don ta san shi sarai, muddin ya ji akan aikin wa ake wannan takaddamar Amina tayi nasara ta gama. Don kaifin bakinsa sai yafi na kowa. Inna Zulai da batasan hakan ba ta soma harhada masa dan abinda ta fahimta.
“wai Gwamna Ji-qas, ke son daukar Amina aiki ta kula da diyar sa mai shanyeyyen jiki, amma dole sai ta koma gidansa don ya rabo yarinyar daga gadon asibiti, zai dinga ninka mata albashin ta na asibiti sau hudu duk wata. Goggo ta kasa amin......” Ilya ya kasa tsayawa yaji karshen zancen nan yayi tsalle ya dire yace “kan uban nan! To shine kuka sa Dr. Amina a tsakiya kuna son yi mana sagegeduwa? To ke Amina yanzu wai me kike ce musu sun ki yarda? Goggo in wannan damar ta wuce Amina anya kin yiwa kanki adalci ganin irin wahalar da kika ci da jikinki, lafiyarki da aljihun ki kamin Amina ta zama likita? In tambaye ku, ina ruwan Ji-kas da Amina don ya dauketa aiki cikin gidansa, ance muku bashi da mata ne ko manemin mata ne? To in silar hakan ne Allah zai baiwa Amina miji sai ku sa kafa ku shure alherin Allah? Kai ban taba jin Goggo kin bani takaici irin na yau ba, kin biyewa Inna Zulai kifin rijiya kuna ta bata yawun bakinku akan alherin da yazo har gida ya same ku.
Shin wai ance muku Amina itace kadai likitar kashi a jihar Bauchi? Don kun samu Allah ya zabo ta cikin dubu ya bata shine zaku tsaya kuna kasa ta akan faranti tana lallashin ku tana muku bayani kuna dojewa? Dr. Amina, adana yawun bakinki zai yi miki amfani a gaba, barni dasu. Ku gayamin duk abinda kuke gujewa na shigar Dr. Amina gidan gwamnati. .....”.
Amina banda dariya ba abinda takeyi, Goggo da Inna sun kirne fuska sai jifansa suke da harara. Shi kuwa ya kai hannuwa ya harde a kirji ya mike kafafu a dole jira yake su bashi amsa. Goggo tace.
“ Sannu uban mu. Matse baku nan mu sai mu gaya maka abinda muke gujewa din na zuwan mace babu aure wani waje ta kwana”. Ilya ya gyara zama ya gyara murya.
“A inda babu Uba, komai kankantar namiji Uba ne. Don haka ni Ilya uban Amina, na amince diya ta Dr. Amina taje aiki gidan Engnr. Ji-kas.
Da take kwana a asibiti binta kuke? Kai ni ba don kar ace nayi rashin kunya ga Iyaye ba da sai ince ban taba ganin gidadawan mutane irinku ba. Ana kiranku gidan Gwamnati kuna cewa ba zakuje ba....”.
Goggo ta dauki kwanon silva a gefenta ta jefe shi da shi, Inna Zulai data fi kusa dashi ludayi ta kaiwa bakinsa ya kauce. Amina tace “haba Yaya Ilya, maimakon ka gyara ka tayani lallashin su duk ka kara damalmala al’amarin. Goggo kuyi hakuri, nidai na gaya muku akan aikina zan je gidan Gwamna don wani kebantaccen uzri dana ke dashi akan ki Goggo. Amma in baki amince ba na hakura Goggo, zan je na samu Dr. Turaki gobe in fada masa ban samu amincewar ki ba”.
Jikin Goggo yayi sanyi. Ta san Aminan ta har ga Allah batada kwadayi,