ke, ‘Ai gara zama da malamin makarantar da zama a gidan da ko dariya ban isa in yi ba, gara zama da malamin makaranta da zaman gidan da ban taba farin ciki a cikinsa ba, tunda aka haife ni. Gara zama da malamin makaranta da zaman gidan da ba ni da ‘yanci. Ya Allah ka sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ni”.
Duk abinda Alhaji Mansur ya yi wa sauran ‘yan uwanta shi ya yi mata a dakunanta, amma dole aka koma da wasu kayan saboda babu wajen sanyawa.
Aka daura aure lafiya da mafi kankantar sadaki, kafin nan ya je sau biyu domin su fahimci juna a bisa umarnin iyayen, sam ta ki yarda ya ga fuskarta, cikin hijabin islamiyyarta ta ke daga sama har kasa. Ta dai gaishe shi da ‘yar siririyar muryarta, shi kuma ya rasa me zai ce mata. Sai suka zauna shiru. Da shirun ya ishe shi ya bude jarida wadda ke tule a kan wani tebir na falon kala-kala, hakan ya sa ya gane falon Babansu ne. Da ya ga dare ya yi, sai ya yi mata sallama ya tafi. A ransa ya kudurce ko kuturwa ce zai zauna da ita a haka, in har hakan zai sa Babansa farin ciki. Wanda ba abinda bai yi masa ba a rayuwa.
An yi biki lafiya aka kai amare dakunansu.
*** *** ***
Wani irin zama ake yi tsakanin Ma’arouf da mai dakinsa Aisha, kowa na dakinsa, ko da ta fito yin wata sabgar ta ji motsinsa zai shigo, ko zai fito daga dakinsa komawa daki ta ke sai ya fita, ko ya shigo ya shige nasa dakin. Ga shi an kawo ta da gara don haka ba ta bukatar komai daga gare shi, shi kuma kullum zai tafi aikin koyarwarsa sai ya ajiye mata kudin cefane a kasan kofar dakinta yadda tana budewa za ta gani.
Baba ne ya samar mata almajiri kullum yake zuwa ya yo mata cefane, da aike in ta yi girki ta zuba masa. Amma ko sharar tsakar gida ba ya yi mata, ita ta ke tsabtace abinta ciki da bai dinsa.
Aisha ta samu kanta cikin wani irin kwanciyar hankali wanda ba ta taba samu a gidansu ba, sai tsangwamar matan uba da ‘yan uba, kawai don Babanta ba ya iya boye kaunar da yake mata. Tuni ta murmure, kyanta ya soma fitowa. Ta yi kiba, ta yi (fresh) da ita cikin watanni uku. Da kuwa kamar sillen kara aka kawo ta, ga cima mai kyau da tafi ta gidansu. Sammata abinci ake a gidansu kamar an zuba wa karamin yaro, a nan kuwa ita ta ke dafa abin da ta ke so ya ji kifi ko nama, saboda kudin da Ma’arouf ke ajiye mata kullum ya fi karfin cefanen rana daya, haka ta ke ta tara ragowar a ranta ta ce, banki zan saya in yi ta tara masa abinsa.
Wani sabon salo, sai Inna Luba matar Baba ta soma zagayowa wajen Aisha in sun fita aiki. Ita Aisha ba ta san halin Inna Luba ba, da zuciyarta daya ta ke girmamata, in ta yi girki kullum sai ta zuba ta ba wa almajirinta ya kai mata, tunda mijinta bai ba ta iznin ta dinga fita ba.
Ta zauna ta sa Aisha a gaba ta yi ta surutun banza da wofi tana bata Ma’arouf a idonta, tana fadin ba abin da ba ta yi masa a rayuwa ba tun yana jariri, amma ko gaisuwa ba ta isa ya yi mata ba. Musamman da ta lura ba abin da ya taba shiga tsakaninsu. Tana tsoratar da ita akul ta shiga turakarsa ko ta bari ya shigo dakinta ba mutumin kirki ba ne. Da ya samu abin da yake so wulakantata zai yi, ita ma haka ta ke hakuri da ubansa.
In za ta fita kuma ta ce ta auna mata sukuri ko shinkafa nata ya kare bayan tana aika mata abinci sau uku a rana. Wataran ta ce, “Kina gani ko garar nan da aka kawo ki da ita ba a ware min nawa ba, saboda ba a dauke ni a bakin komai ba. Kullum sai ta tuhume ta ko Ma’arouf ya zo inda ta ke ta ce, “A’ah”.
Aisha ta zauna tana tunani a karan kanta, me ye matsalar matar nan ne da irin zaman da nake yi da mijina? In ba mutumin kirki ba ne Baba ba zai aura min shi ba. Ba ta taba fadar alheri ba a kansu shi da mahaifinsa alhalin tana matsayin matarsa. Tana tunanin ba ni da nawa tunanin ne ko ba ni da hankali ne?
Ranar da Allah ya tashi kama Inna Luba wata litinin ce.
Ma’arouf ya yi sammakon tafiya wajen aiki. Har ya je makaranta ya tuna bai barwa Aisha kudin cefane ba. Haka ya juyo ya dawo duk da akwai ‘yar tazara daga makarantar da yake koyarwa zuwa gidansu.
Ya sako kai ke nan ita kuma tana kokarin fitowa daga sassan rungume da kwarya cike da shinkafa, ledar maggi, galan din mankuli da sukari leda guda, suka gabza karo kayan hannunta da wanda ta dora aka suka watse a kasa. Ta kasa tattarawa ta shiga ‘yan mutsu-mutsu na rashin gaskiya, gabadaya ta daburce don ya kalle ta ne da wannan fuskar tashi ta (seriousness) wadda ba alamun wasa ko sanayya a ciki.
Jiki na rawa ta ke so ya ba ta hanya ta yi ta kanta, shi kuma ya ki, sai da ya tabbatar ya gama ladabtar da ita da idanunsa masu sheki (oily eyes) sannan ya ba ta hanyar. A fusace ya danna kai dakin amaryar tasa.
Aisha ta sha wankan safenta, ta ci ado da atamfarta mai barewa, kan nan ya sha kitso yiri-yiri, ta yi daurinta (simple) da dankwalin atamfar, jelunan kitso sun zubo a dokin wuyanta da rediyo a hannunta tana ta murdo tashoshi ta ga mutum tsaye a kanta.
Da sauri ta dago, sai idonta cikin nasa. Nasa cikin nata. Wannan saurayin ne mai karatun jarida, wanda ya dade yana farautar zuciyarta kwana da kwanaki, wata da watanni…!
Da ma an ce kowa ya bi iyaye zai ga da kyau a rayuwa. Haka Babanta yake gaya mata kullum.
“Ki bi ni, da zabin da na yi miki, ba za ki yi da na sani ba”.
Ta tuna kalaman Babanta na karshe lokacin da za a taho da ita gidan miji.
A nasa bangaren kujera ya laluba ya zauna, don kafafunsa sun gaza daukarsa.
“Baba na fi-sauran babanni ne, what an amazing father Allah blessed me with!!! Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya yi mana umarni da mu yi wa iyayenmu biyayya.
Ya ga idan bai yi magana ba, zai zama ba namiji ba, su taru su zama matan shi da ita. Hannun damansa ya mika mata yana gayyatarta musabaha.
“Sunana Ma’arouf… ina nufin Ma’arouf Habibu Ji-qas, cikakken sunan ke nan, ko ya sunan Malamar?”
Shi kansa ya yi mamakin sautin da ya yi amfani da shi wajen yin wadannan kalaman. Shi ne mafi kankanta da sirantar sauti da Allah ya halicce shi da shi.
Kanta ta sanya a tsakanin cinyoyinta tana wani irin murmushi, ta kasa ba shi hannun, har ya gaji ya maida abinsa aljihun farar shaddar da ke jikinsa.
“To da alama abotar tamu ba za ta yiwu ba, tunda malamar rowar muryarta ta ke min. Bari in koma makaranta, da ma kudin cefane ne na mance ban ajiye ba. Ga su”.
Ya ciro daga aljihunsa ya mika mata. Har yanzu ta kasa dagowa ta karba.
Ya karasa gabanta ya ajiye mata, “Tattara kayan da ta zubar a tsakar gida ki kai mata, sai dai ina rokonki ba umarni ba, wannan ya zamo mu’amala ta karshe da za ta kara shiga tsakaninku”.
Cikin nutsuwa ya juya ya fita, ya koma wajen aikinsa.
Hatta dalibansa sun lura yau Malam Ma’arouf yana cikin farin ciki. Wata koyarwa yake yi musu cike da nishadi wanda ba su taba gani a tare da shi ba.
Ana tashi ba inda ya tsaya sai gida, ya tarar ta gyara tsakar gidan tas ta shige uwardaka ta kure karatun alkur’ani mai tsarki a rediyo. Ta turare gidan da turaren wuta mai dadin kamshi. Wanka ya fara yo wa ya yi alwala ya nufi masallaci. Da ya dawo ya tarar ta shirya masa abinci, amma yau ba ta ajiye a kofar daki ba ta shigar masa da shi ciki. Ya yi murmushi, a ransa ya ce, “An samu ci gaba ke nan”.
Ya ci abincinsa ya yi kat! Ta iya girki sosai. Yau ba fita kofar gida karatun jarida. Kananan kaya ya sanya, ya fito a gogaggen dan bokonsa. Kansa ba hula, babu tarin suma, kuma bai dade da yin saisaye ba. A very smart guy.
Ga turare ya fesa mai dadin kamshi, ya nufi dakin matarsa.
Zaune kawai ta ke tana sauraron karatun da ta kunna, da alama bi ta ke a zuciyarta. Jin zuciyarta ta ke kamar an yi mata rahma ga dukkan zunubanta. In ba ta gode wa Allah ba me za ta yi? Ba ta ankara da shigowarsa ba, sai da ya kai hannu ya kashe rediyon. Wani irin shiruu! Ya ziyarci dakin, idonta yana lumshe ne don haka ta bude su don a tunaninta kaset din ya kare ne, suka sake yin arba da juna a karo na biyu.
Zama ya yi a kusa da ita har kafadunsu na gugar na juna. Aisha ta samu kanta cikin wani sabon yanayi, ga ba wurin gudu. Sauran abinda ya biyo baya ba zai taba gogewa a tarihin rayuwarsa ba. Kullum yana tunawa, tunanin na kara masa sonta da kaunarta. The first life-partner ever, yet the best! The very best!!!
*** *** ***
Sun kulle sun dunkule sun zama abu daya, abokan sirrin juna, masoyan juna, kuma ‘yan uwan juna, kasancewar dukkaninsu ba su da wanda za su kira dan uwansu na jini, sai junansu.
Aisha na shara a tsakar gida wani yaro ya shigo, “Wai ana neman maigidan”.
Ba tare da ta juyo ba ta ce, “Ya tafi wajen aiki, sai karfe daya da rabi zai dawo”.
Yaro ya fita, can kuma ya dawo da ambulan mai fadi a hannunsa,
“Wai ga shi a ajiye masa, sako ne daga ‘post-office’. Aisha ta ce, “Toh”.
Ta karba ta kai daki ta ajiye a kan talabijin dinta ta fito ta ci gaba da ayyukanta.
Da ya dawo ba ta ba shi takardar ba, sai da ya gama komai na al’adar rayuwarsa, ta dade da kashe fita kofar gida karatun jarida don a cewarta da haka zai kallo wata tunda kallon masu wucewa yake ba karatun jarida ba. Ya kan ce,
“Ki yi abin da ki ke so dole a bi, ko ana so ko ba a so”.
Tare suke hirarsu na abubuwan da suka shafe su, ko al’ummah. Inna Luba ta dade da shafa mata lafiya.
“Au! Ka gani na manta, dazu aka kawo maka wai daga (post-office)”.
Ya karba yana juya ambulan din mai dauke da tambarin kamfanin ‘Lange&Grant’, ya ciro ya bude yana karantawa.
Bai san sanda ya mike tsaye ba,
“Aisha, alheri zai same mu, kirana ake yi intabiyu. Na dade da neman aikin wajen shekara guda ke nan. Sai dai ga bikin zuwa babu zanin daurawa”.
Ta ce, “Kamar ya ya?”
“Eh, toh!. Sai na je Lagos. Ga shi babu kudin mota. Wata ya zo karshe, kuma gobe-gobe ake so in shiga Lagos jibi in shiga intabiyu din”.
Aisha ta mike ta shiga dakinta, ta jawo abu daga kasan gadonta. Sai ganinta ya yi ta fito da bankin kasa, ta tika shi da kasa, sai ga kudi fululu.
Da mamaki yake kallonta, “Wannan fa?”
“Naka ne”.
“Kamar ya ya nawa?”
“To an ce da kai haka ake ba wa iyali kudin cefane kamar ma’aikata? Ko an ce maka maigida ba zai dinga adana komai ba a kudin cefane yake karewa? Ko kuwa mu hudu ka ajiye da ka ke ba ni tsabar kudin da ka ke ba ni kullum? Karbi ka shirya ka tafi”.
Shi dai ya kasa magana, sai binta yake da kallon kauna.
“Ba zan karba ba sai kin yarda rance za ki ba ni”.
Da ta ga zai bata mata lokaci wajen ja-in-ja, ta ce, “Na yarda”.
Sannan ne ya soma kirga kudin. Za su kai shi har karshen Nigeria su dawo da shi Bauchi lafiya.
A daren ta hada masa kayan da zai bukata, sun shirya da asuba zai fita. Ya yi sallama da Baba tun a daren ranar ya ce suna fitowa daga masallaci zai nufi tasha. Baba ya yi masa addu’a sosai.
Ya gamu da wahalhalu irin na matafiyi, har Allah ya kai shi garin Ikko lafiya.
Ofishin Lange&Grant na nan a 53 Akanbi Onitiri, Eric Moore Road a Surulere cikin jihar Lagos. Bai sha wuya ba ya riski kamfanin kasancewar yana da adireshin a rubuce.
Su suka ba shi masauki, washegari suka yi masa intabiyu da (screening) din takardunsa. A take suka dauke shi cikin manyan ma’aikatansu, saboda kyawun takardunsa.
Sun ba shi sati daya ya koma gida ya shirya ya dawo ya shiga office.
LANGE AND GRANT kamfani ne mai zaman kansa da ke karbar kwangilar gine-gine (construction company) na abubuwa da dama, sannan suna daukar nauyin ma’aikatansu da tura su kwasa-kwasai kasashen da suka ci gaba, babban ofishinsu yana nan a jihar Lagos. Samuwar aikin nan ga Ma’arouf ba karamar sa’a ba ce a gare shi, da duk wani mai kaunarsa.
Ya dawo gida cike da farin ciki, ya sunkuci Aisharsa yana juyi da ita a tsakar daki.
“You are a blessing Aisha. Tunda na aure ki nake cin karo da farin ciki iri-iri, da ci gaba ta kowane fanni. I really love you. Pack our belongies (harhada mana kayayyakinmu). Mun zama ‘yan Lange&Grant”.
Murmushi kawai Aisha ta ke yi. Ita ba za ta iya gaya masa adadin kaunar da ta ke masa ba, kuma ba za ta gaya masa kullum ta yi sallah addu’ar ci gaban rayuwa da gamawa da duniya lafiya ta ke masa ba.
Baba ma ya yi farin ciki. Ya sa Aisha ta shirya ta je ta yi wa mahaifinta sallama. Har matan baban ta gaisar ta yi musu sallama, ta gaya musu za su koma jihar Lagos da zama. Ba wadda ta damu da me ta ke ciki, don haka suka bi ta da ‘a dawo lafiya’.
Tare da Baba suka tafi Lagos ya je ya gano muhallinsu. Madaidaicin gida mai dakuna uku da falo. Komai na bukatar rayuwa akwai shi a gidan daidai bukatar kowanne dan Adam.
*** *** ***
Shi kansa shugaban ‘Lange & Grant’, Mr. Timothy Emmanuel na mamakin (talent) irin na Ma’arouf, kullum cikin kawo musu sababbin ‘discoveries’ da ‘ideas’ yake. Tunda ya zo bangarensa na ginin titunan mota da jiragen kasa kara inganta yake, sai samun abokan ciniki suke. Ma’arouf ne ya sa suka yi kokarin da suka soma karbar kwangila daga (Federal Government), hakan ba abu ne mai sauki a gare su ba a da (before), amma da zuwan Ma’arouf sai ya maida shi mai saukin. Suka soma samun kwangila daga gwamnatin tarayya.
Cikin shekaru biyu da shigowar Ma’arouf kamfanin, ya samu ci gaba a dukkan bangarorinsa, don haka shi ma ogansu Mr. Timothy ya kara masa promotion, da daraktansu ya yi (retire) ya dora ma’arouf a kujerarsa. Ya zamo daya daga cikin (board of directors) na kamfanin, da tafiya ta yi gaba ya zama mataimakin Mr. Timothy.
Abin da ke bai wa Mr. Timothy mamaki da Ma’arouf ya ki zuwa kowanne (course) da suke tura shi Amurka, bai yi shiru ba, kuma ya yi masa bayani, ra’ayinsa ne, tsarin rayuwar da ya yi wa kansa ne ba shi ba fita waje. Shi ma sai ya kyale shi, sai dai ya ga abokan aikinsa na fita, su kuma hakan na musu dadi. Saboda suna kishin daukakar da ogan ke masa a kansu, shi da ya zo a bayan-bayansu, amma har ya isa kololuwa.
Zuwa wannan lokacin duk wani rufin asirin rayuwa da dan Adam mai ilimi ke nema, Ma’arouf Habibu Ji-qas ya same shi. Falla-fallan motocin hawa har guda biyu, ya gina (smart mansion) dinsa a Fati Mu’azu Links cikin Bauchi, ya bige gidansu ya yi wa Baba ginin da ya ja hankali a unguwarsu, ya doke na Baban Aisha.
A kauyen Ji-qas ya yi wa mahaifiyarsa da mijinta gida na gani a fada, wanda duk kauyen babu kamarsa. Haka yake dauko ta ya kawo ta Lagos ta yi kwanaki ta huta tare da Aisha. Suna son juna ita da Aisha suna girmama juna, suna kiyaye mutuncin juna.
A cikin wadannan shekaru Aisha ta goge, ta waye, ta zama cikin wayayyun matan Arewa a Lagos. A Lekki suke da zama. Ta shiga (Unilag) ta yi digirinta a kan (Accountancy) ta yi hidimar kasa a nan Lag ta adana takardunta a karkashin gado don Ma’arouf bai yarda da aiki ba, ko da ya barta ita ba ta da ra’ayi, burinta kullum ta kula da Ma’arouf ta janye idanunsa daga sauran mata masu auren maza don abin hannunsu.
Sai kuma ta yi sa’a shi Ma’arouf din akan karan-kansa ba mai ra’ayin aure-aure ba ne. Sannan iyayensa a tsaye suke a kansa wajen yi masa addu’a da ba shi (azkar) iri-iri yana yi duk inda zai shiga.
To da ma Ubangiji ba ya barinka haka ba tare da ya jarrabe ka ta wani bangaren ba. Hakan ce ta faru da Ma’arouf da Aisha, ko batan wata Aisha ba ta kara yi ba, tun wannan barin data yi a cikin jirgi, haihuwa sun neme ta sama ko kasa Allah bai ba su ba. Shekara biyar ke nan da aure.
Tebirin likitoci iri-iri a Lagos da Abuja babu inda ba su tsugunna ba. Duk amsar daya ce, dukkaninku lafiyarku kalau, Allah ne bai nufa ba. In suna da damuwa a rayuwarsu, to wannan ce. Har taimakon magungunan Hausa Hajiyan Ji-qas ke kawo wa Aisha, amma shiru, kamar an aiki bawa garinsu.
Mr. Timothy wanda da zuciya daya yake kaunar Ma’arouf ya zauna yake tunani, shi ga shi shekaru sun tura, ya san kuma yadda dukkan ma’aikatansa ke kishi da Ma’arouf, idan ya yi (retire) ko ya mutu yanzu Ma’arouf zai ga ba daidai ba a ‘Lange & Grant’ ga yaron ya taimaka masa ya tara dukiyar da shi kansa bai san iyakarta ba cikin shekaru biyar kacal, kuma an ce dadewa a bauta ‘yanci ne, ya kamata ya taimaka masa ya tsaya da kafafunsa.
Don haka ya wari wani kaso na dukiyarsa ya tura ‘account’ din Ma’arouf, abin da ya firgita Ma’arouf ya zo ganinsa har gida afujajan.
Sun kulle kansu a dakin ganawa da bakinsa na musamman, a nan Mr. Timothy ke yi masa bayanin kudurinsa a kansa. Cewa daga yau ya bar ‘Lange & Grant’ ya zama (contractor) mai zaman kansa, zai buda masa hanyoyin karbar kwangilar gine-gine daga kwastomominsa. Wannan godiya ce a gare shi na wahalta masa da ya yi da zuciya daya har kamfaninsa ya kai matsayin da ya ke da shi a yanzu.
Ba shi da abin cewa sai godiya, don ya san halin ogan nasa, ba ya niyyar yin abu ya fasa, amma da ya ce masa zamansa karkashinsa ya fiye masa dadi, kuma (remuneration) din da yake samu a karkashinsa ya ishe shi. He is contented with his life as such... Amma an ce ba a maida hannun kyauta baya. Kuma a yadda ya san abin da Ogan nasa ya mallaka, wannan ba wani ‘big deal’ ba ne a wajensa (babban abu).
Don haka ya dauko Baba da Hajiyan Ji-qas da Alhaji Mansur (surukinsa) suka zo har Lagos suka je suka yi wa Mr. Timothy godiya. Sai ya hau Ma’arouf da fada, (how dare…) ya kwaso dattijai haka ya ba su wahala. Ba zai kira shi a waya su yi maganar ba (a lokacin waya ta shigo, amma rike ta sai wane da wane).
Shi ma ya sayar da duk kadarorinsa, filaye da gonaki biyu da ya saya a Bauchi, ya hada da ‘capital’ din da ubangidansa ya ba shi, ya gina kamfanin kwangilar gine-gine mai zaman kansa, kuma da yake ya san kan harkar, idonsa ya riga ya bude da ita. This is the beginning…
Da wannan ‘JI-QAS CONSTRUCTION COMPANY LTD’ ya kafu, mai hedikwata a Abuja da Lagos. Ya dauki karantattun ma’aikata ya zuba, suka soma karbar kwangilar gina wani (oil-refinery) a jihar Ondo, daga gwamnatin tarayya, da abin ya yi gaba ya dawo gida Bauchi yana karba daga gwamnatin jiha, makarantun firamare ne, gadoji ne, tituna ne, gyaran Dams, hydro-electric power, da sauransu. Allah kuma ya sanya albarka a ciki.
Ma’arouf in ya zauna yana tunani a kan kansa, yana kididdiga arzikin da ya samu cikin dan lokaci kalilan, sai ya ga ya kamata ya soma wani tallafi ga matasan jihar Bauchi, wadanda ke zaman banza, da wadanda ke da zuciyar neman ilimi babu damar yi, wadanda suka yi karatu babu aikin yi, da ilimin yara kanana a jiharsa Bauchi ganin yadda gwamnati ta yi wasarere da su saboda abin ya yi mata yawa ita kanta gwamnatin, hakkin masu hannu da shuni ne su sanya hannu a gudu tare don ci gaban al’umma, amma fa masu zuciyar taimakon kadai.
Ya fiddo da wani tsari na gina matasa mai suna (Ma’arouf Foundation), ya sa aka rika cigiyar matasa a kafofin yada sadarwa masu matsalolin can da ya ambata a baya.
Matasan Bauchi da iyayen yara talakawa suka amsa kiransa da gaggawa, ya dora ma’aikata masu amana, aka soma yi wa matasan maganin matsalolinsu daga cibiyar MA’AROUF FOUNDATION. Ya gina katuwar makarantar firamare ta kyauta, wadda gwamnati ta san da zamanta.
Allah kadai ya san adadin matasan da suka samu kwalin digiri daga aljihun Ma’arouf a jihar Bauchi. Su gama ya yi musu hanyar samun aiki daga gwamnati ko (private sectors), ilmin firamare mai kyau (free) ga kananan yara, masu zaman banza an sanya su (6-week orientation) sun koyi sana’o’i ana ba su wadataccen jari. Sai a hankali sunan Ji-qas ya fita a Bauchi har ake masa kallon wani babban dan siyasa ne. Har zuwa yanzu (foundation) din na ci gaba da gudana.
Wannan ne ya janyo ra’ayin matasan Bauchi na son ya tsaya musu takarar gwamna na kara yaduwa. Sun yi gangami sun bayyana masa ra’ayinsu na son ya shiga siyasar ya taimaka wa jiharsa, su kuma za su tsaya wajen yi masa kamfen babu ko sisinsa. A lokutta da dama hakan ta faru babu wanda ya samu gamsasshiyar amsa daga bakinsa.
Daga baya jama’ar suka bi ta kan surukinsa wanda an san ba ya ketare shawarwarinsa a gare shi. Sun zauna ya yi masa nasiha, cewa ya rungumi alherin da mutane suke so da shi, ya tsaya takarar ya barsu da kokarin komai na Allah ne. Mahaifinsa kuwa addu’ar da ba ya fasa yi masa kullum ita ya yi masa, yana fadin, “Allah ya yi jagora, Allah ya zaba mafi alkhairi”.
Hajiyan Ji-kas, kusan ra’ayinsu daya da Baba, cewa ta yi idan siyasar alkhairi ce Allah ya yi riko da hannunka”.
Aisha ce kadai ba ta son zancen siyasar nan. A cewarta yanzu haka sai in dau lokaci ban sa ka a idanuna ba, kana nan kana can, ina kuma ga ka shiga siyasa? Ina kuma ga ka zama gwamna?”
Ita ma ba ya ba ta amsa, murmushi kawai yake yi.
Yau da gobe ba ta bar komai ba, kwadaita masa siyasar da kowa ke yi da goyon bayan da ya samu daga sama da kasa ya sa ya amince, ya shiga siyasa karkashin jam’iyyar (NPC) wato ‘Northern People Congress’. Bai tsaya takarar gwamna ba, ta dan majalisa ya tsaya mai wakiltar Bauchi ta Kudu don ya kara bude ido da yadda al’amuran siyasa ke tafiya.
Ai kuwa da gudu ya haye, suka koma Abuja shi da iyalinsa. Su Baba kan je, Hajiyan Ji-kas kan je ta yi hutu duk sanda ta so, su ma kuma suna zuwa ganinsu akai-akai.
Ashe da kafar dama suka fada siyasar, domin a shekarar ne ciki ya billo a jikin Aisha. Murna da godiyar Allah gurin ma’auratan da iyayensu da duk wani mai kaunarsu abin ba a cewa komai. Sai shukrah ga Lillahi.
*** *** ***
Aisha ta sauka lafiya a ‘National Hospital’ ta samu ‘yarta mace, santaleliya mai kama da ubanta a komai. Ranar suna Baba ya sanya mata suna Amina. A cewarsa babu sunan da ya kai wannan albarka (Aminatu