dinta a ‘Physiotherapy’, wanda ta kwashe shekaru biyar tana yi, Goggo Hauwa ta soma shiga damuwa a kan rashin kwakkwaran manemi ga Aminar, a lokacin ta cika shekaru ashirin da daya a duniya. Abin ya soma damunta sosai.
An tura su Amina ‘internship’ na shekara daya a asibitin koyarwa (Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital), bayan kammala ‘B.Sc’ dinta, jininsu ya hadu da (consultant) dinsu Dr. Usman Turaki saboda kokarinta. Dr. Turaki na yabawa Amina sosai, yana kiranta ‘Young Doctor’, don duk cikin ‘team’ dinsu da ke karkashin Dr. Turaki ita ce karama.
Amina na girmama Dr. Usman Turaki don ta lura mutumin kirki ne mai tsanteni da mutuncinsa, ba shi da wasa ko kadan ga rikon addini. Duk sanda yake koyar da su da zarar an kira sallah, to fa zai katse ya yi umarni ga musulman cikinsu su je su yi sallah, sannan bai taba yi mata maganar banza ba, don haka tasu ta zo daya suke ganin mutuncin juna, duk abin da ya shige mata duhu shi ta ke samu, shi ya shige mata gaba ta ke samun (scholarship) daga gwamnatin jiha, ko da ba ta gaya masa komai da ya danganci (personal life) zahirin rayuwarta ba, ya lura iyayenta masu karamin karfi ne, an kuma taba gaya masa Babanta ya rasu, wannan ‘scholarship’ da ta ke samu duk shekara ba karamin taimakawa yake yi ba.
*** *** ***
Goggo Hauwa da aminiyarta Zulai Babar Ilya, a dakin Goggon suke tattaunawa a kan damuwar Goggon.
“Na rasa daga ina matsalar ta ke? Aminatu sam ba ta da niyyar aure a rayuwarta Zulai, boko dai, boko dai? Ina ki ka fito? Asibiti, ina za ki? Asibiti! Babu mashinshini ko daya, lamarin nan yana tayar min da hankali, mu shekarunmu goma sha hudu aka yi mana aure, yau Amina in watan nan ya mutu shekarunta ashirin da uku. Yaushe ne ta ke tunanin ajiye iyali na kanta? In na tambaya babu manemi ta ce babu, ga Hafizu da ta kora yanzu yaransa biyu, jiya suka zo shi da maidakinsa da yaransa ba ki gani ba abin sha’awa, ta san ta yi ta yin nan-nan da yaran wasu, amma ko miskala zarratin ba ta damu da itama ta yi ba, sai hidima da na mutane”.
Goggo Zulai ta gyara zama, “Kina nema wa yarinyar nan taimako kuwa? Yanzu ba wuya aljanu sun auri bil’adama su cire musu son aure a ransu, ga jifa irin na marasa imani dole ki mike tsaye”.
Goggo ta girgiza kai, “In dai irin wannan mikewa tsayen ne ba zan taba mikewa ba, kullum na kai goshina gaban Ubangiji dare da rana, yini da safiya sai na roki Ya baiwa Amina miji na gari, addu’ar iyaye kuma karbabbiya ce a kan ‘ya’yansu, abin daga Aminar ne, na tabbatar korar maneman ta ke tun kamin su iso gida. Na yi fadan, na yi nasihar duka a banza”.
Zulai ta ce, “In haka ne sai ki daina damuwa ki jira lokacin da ijaba za ta zo, amma duk da haka ki sa a dinga rubuce mata alqur’ani tana shanyewa saboda shi maganin komai ne. zan yi wa masu rubutu magana a fara yi mata”.
Goggo ta amince da shawarar Zulai. Ta sa aka yi rubutun jarka guda tana takura wa Amina tana sha a gabanta.
*** *** ***
Amina zaune a gefen gado, Goggo a kasa, kitso Amina ke yi wa Goggo suna hira jefi-jefi. Amina ta ce, “Wai ni Goggo shekararki nawa ne? furfurarki ba ta da yawa”.
“Shekaru na hamsin”.
Goggo ta ba ta amsa.
“To Goggo me ya sa ba za ki yi aure ba, na ga dattijai ma da suka fi ki suna yin aure”.
Goggo ta sha kunu, sau tari Amina ‘treating’ din Goggo ta ke kamar kakarta.
“Sai ki kai ni bola ki yar in gajiya ki ka yi da ganina”.
“Wuh!” In ji Amina tana dafe baki cikin dariya.
“Goggo na my life, my soul”.
Goggo ta ce, “Idan ba za ki yi maza ki lallabe min kan nan ba ki kyale ni”.
Amina ta maida hankali ga kitso, amma bakinta ya kasa shiru,
“Goggo yaushe za mu je Sirrleone?”
Goggo ta yi mata shiru, sai ba ta ja ba, don ta san shirun Goggo na nufin ba za ta yi abun a lokacin da aka ba ta umarni ba.
Ilya ya shigo yana kakabin nan irin na ‘yan siyasa, “Sai Ji-qas, wallahi sai Ji-kas…!”
Ya yi tsalle ya dire ya shigo dakin Goggo yana ci gaba da fadin, “Sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas!”
“Mene ne Ji-kas?”
Goggo da Amina suka hada baki suna tambayarsa.
“Goggo ina rediyonki? Hira ake da Engineer Ma’aruf Habibu Ji-kas, dan takarar gwamnan Bauchi daga jam’iyyar NPC (Northern People Congress)”. Ya fadi yana ta kokarin murdo rediyon har ya samu radio Bauchi.
“Yaushe ka zama dan siyasa Ilya?” Goggo ta tambaya cikin mamaki.
“Ban zama ba Goggo, amma a kan Ji-kas zan zama. Daya tamkar da goma, mai son ci gaban matasan Bauchi, gagara-gasar masu gasa, bujimi uban matasa. Giwa an buga an barki, Ji-kas ikon Allah ke nan”.
Muryoyi suka soma fitowa tar-tar daga rediyon, na dan jarida da wanda ake yi wa tambayoyin yana ba da amsa cikin nutsuwa da wadatar ilmi, the programme is live (wato a lokacin ake yi).
Ba su ji farkon hirar ba, sai tsakiyarta.
“Mene ne babban burinku idan kun samu nasarar hayewa wannan kujera a garin Bauchi da kananan hukumominta guda ashirin?”
Ya dan ja lokaci kafin ya amsa, a hankali kuma ya soma bayani cikin Hausa mai tsafta wadda babu kalaman turanci a ciki.
“Babban kudirinmu shi ne gina matasa, saboda su ne shuwagabannin gobe. Za mu fadada samuwar aikin yi ga wadanda suka yi karatu, wadanda Allah bai ba su dama ba za mu samar da shirin koyar da sana’o’i, inda za a koyar da su duk sana’ar da suke so mu ba su jari wanda zai ishe su gina wannan sana’a, domin in ka lura akasarin matasan da ke samun kansu a shaye-shaye, daba da sauran laifuffuka rashin aikin yi da hanyar abinci shi ne sila, duk masu yin karatu a fannin kiwon lafiya (medicine), gwamnatinmu za ta dauki nauyin karatunsu. Wannan alkawari ne muka yi ga al’ummarmu da muke rokon Allah ya ba mu ikon cika shi.
A sauran bangarorin ma ba za mu bar ko daya ba, tun daga kan ilmi, ruwa da wutar lantarki, tsaro, cin hanci da rashawa, tituna da hanyoyin sadarwa, karawa malaman makaranta albashi, hakkin ‘yan pansho, tsaftar muhalli da sauransu, muna kira ga matasa da su fito wannan karon su zabi wadanda suke so su zama shuwagabanninsu ta hanyar aiki da hankali, kada su zabi wadanda za su zo suna da na sani…”
Dan jarida ya gamsu da amsar da ya samu, ya ce, “A karshe masu sauraro za su so su ji mene ne ‘Ji-kas’ da ya bi ya dabaibaye Engineer, har sunansa ya bace sai Ji-kas din?”
Murmushi ya yi mai sauti, kana iya jiyo sautin murmushin nasa ta rediyon.
“Ji-kas, kauye ne da ke karkashin jihar Jigawa, a karamar hukumar Gwaram, na san mutane da yawa za su ce ya ya dan Jigawa zai nemi kujerar Bauchi? To Ji-kas kauyen da mahaifiyata ta rayu a can ne saboda yanayin rayuwa, amma uslin iyaye da kakannina ‘yan kasar Bauchi ne, kuma a nan aka haife ni, sai dai na budi ido na gan ni a garin Ji-kas, da na isa shiga makaranta sai na baro Ji-kas na dawo Bauchi na ci gaba da zama da mahaifina”.
Dan jaridar ya ce, “Masu saurare da fatan kun gamsu? Bari mu kyale ka haka Hon. Ma’aruf Habibu Ji-kas. Ga sakonni suna ta shigowa na goyon bayan al’umma a gare ka, amma lokaci ba zai bari mu bi su daya bayan daya ba. A takaice wane sako ne gare ka ga dumbin masoyanka?”
Babu nuna kosawa cikin muryarsa, “Sako na ga jama’ata shi ne, ranar zabe kowa ya fito ya kada kuri’arsa don kwatar ‘yancinsa na dan kasa, kada a zauna a gida a ce su je su zabo mana alheri, a’ah, hakkin kowane dan kasa ne ya yi zabe don kar a yo masa zaben tumun dare. Sannan su ci gaba da addu’a Allah ya ba su shuwagabanni na gari, ba wanda suke so kadai ba”.
A nan hirar ta kare. Ilya ya yi zambarwa yana fadin, “Sai Ji-kas!”
Amina ta ce, “Hala cin hanci ya ba ka, wannan irin soyayya haka?”
Ilya ya ce, “Wallahi ko sisi. Kawai ina son mutumin. Ku ne ba ku sanshi ba, amma kaf garin nan waye bai san Engr. Ma’aruf Jikas ba? Takarar ma talakawa ne suka angiza shi saboda irin taimakonsa gare su, amma a da dan kwangila ne kawai bai da alaka da siyasa ko kadan”.
Zancen duk ya gundiri Amina, ta karasa wa Goggo kitsonta, ta mike ta yi waje don sake wanka ta tafi asibiti, tana da laccar karfe hudu na yamma.
A yanzu haka Amina na shirin gama ‘internship’ bayan kwashe shekaru biyar a jami’a, tana cikin shekaru ashirin da hudu, gabadaya shekarun gwamnati ce ta ci gaba da biya mata scholarship abin da Goggo ke kashewa ba yawa, don haka asusunsu cike yake taf da kudi da su kansu ba su san adadinsu ba.
An yi bikin yaye su Amina ranar wata asabar a matsayin cikakkun (physiotherapy proffessionals). Gabadaya danginta na kauye sun zo mata ban da kawu Sule, Hafiz da iyalinsa ma ba a barsu a baya ba. Goggo ta hada gagarumar walima a nan gidansu, an ci an sha daga abinci mai kyau da ababen sha masu kyau. (Ina ruwan mai abu da abunsa?) An yi taro lafiya an watse lafiya, Amina ta ci gaba da hutawa a gida kafin inda za a tuttura su hidimar kasa ya fito.
*** *** ***
Amina da Goggo suna hira a yau, Goggo ta dubi Amina cikin damuwa, “Har yanzu lokaci bai yi ba da za ki kawo min miji Aminatu? Sai na fadi na mutu ban ga ‘ya’yanki ba Amina? Me ki ke nema a rayuwa haka? Na bi ki, na bi ki da duk abin da ki ke so da burikanki, sai yaushe ni za ki faranta min, ki cika min nawa burin a kanki?”
Hankalin Amina in ya yi dubu to ya tashi, ganin Goggo tana share hawaye. Ba ta san sanda ita ma idanunta suka yi rau-rau ba, ta gurfana tana bai wa Goggo hakuri,
“Na yi miki alkawari Goggo, duk wanda ya fara zuwa yanzu zan ba shi dama ya fito ba zan kara korar kowa ba”.
Sai a sannan ne Goggo ta sauko, ta daga hannu sama ta ce,
“Ya Allah ka kawo wa Aminatu miji na gari alfarmar Alqur’ani”.
Wani ikon Allah kuma sai dif! Maneman suka dauke kafa, babu su babu alamarsu, har Amina ta tafi hidimar kasa jihar Gombe..
To duk wanda ya zo, in ya ji cewa Amina cikakkiyar likita ce, sai ya ga ta fi karfinsa ya cika bujensa da iska.
*** *** ***
Bayan Amina ta kammala hidimar kasa, an rarraba su asibitoci da dama, da taimakon Dr. Turaki aka bar Amina a ATBU Teaching Hospital, Dr. Amina Mas’ud Shira ta fara aiki a ‘physiotherapy department’ cikin kawarewa da sanin makamar aikinta.
****
Maballan ‘suit’ din da ta sanya masa ta ke ballewa, a tausashe kuma tana yi masa hira, ta dauko ‘necktie’ mai ruwan makuba ta zarga masa ta ja ta matse tana fadin,
“Ba ka ga yadda ash (ruwan toka) ke karbarka ba Baban Amina, ya kamata mu shiga gasar (handsomes) ta duniya, saboda har tafiyarsu ka iya, matsalarka daya rashin fara’a, kullum handsome fuskar nan a cikin seriousness, zan yi rantsuwa ban yi kaffara ba, idan nace ban da Amina ba wanda ke ganin dariyarka, ko ni albarka…...”
Bai san sanda ya yi dariyar ba, Aisha will never cease to amuse him (Aisha ba za ta bar sa shi dariya ba kullum), mace ce ta gari da kowanne namiji ke burin samu, idan har samun mace ta gari shi ne cikar rabin addini yana da yakinin cikar nasa rabin addinin. Ya kama karan hancinta ya ja kadan,
“Kin ga malama yi sauri ba na son shirme, flight dina to Abuja karfe sha daya na safe zai tashi, don ba ni da yadda zan yi da ke ne zan barki da Ameena ku taho a mota. Ni rasa me ye abin tsoro a jirgi, matsoraciya kawai”.
Aisha ba ta yi magana ba, ta dauko masa (briefcase) dinsa. Ita dai tunda Ubangiji ya halicce ta ta ke tsoron hawa jirgi, ga ta dai ba haihuwar kauye ba, ko wani abu makamancin haka, it happens by nature.
Akwai lokacin da maigidan ya takura mata don ya zama dole, umrah za su je bayan aurensu, zuwa dakin Allah ya kori komai ga kowanne musulmi, don haka Aisha ta yi shahada ta hau jirgi, suka nabba’a a mazauninsu, bayan sun sanya ‘belt’. Da jirgin ya yi kururuwa ya karci kasa ya luluka sama, Aisha ta rungume mijinta ta runtse idonta, sai jini ya kece kamar an yanka rago, cikin watanni uku ya fice.
Tun daga lokacin bai kara takurawa Aisha wajen hawa jirgi ba. Shi zai bi jirgin, ita ta bi mota su hade a inda za su je. Fita kasar waje kuwa ba ya daga cikin al’adun rayuwarsa, ba ya zuwa kowacce kasa duk da arzikin da Allah ya yi masa ban da Saudi-Arebia. A cewarsa bai ga me zai je ya yo ba ban da asarar dukiya, duk abin da muke nema na jin dadin rayuwa muna da shi a kasarmu mai dumbin albarka.
Mutum ne mai girmama kasarsa da son yankinsa (Arewa) kwarai da gaske. Bai yi kowanne irin karatunsa a kasar waje ba. Bayan kammala sakandirensa a (Science College D/Tofa) ya wuce jami’ar Ahmadu Bello, inda ya nazarci ‘Civil Engineering’.
Ya fita da digiri mai daraja ta farko, bayan kammala hidimar kasa bai bata lokaci ba ya koma jami’ar ya hado digiri na biyu..
Bai fito daga gidan masu hannu da shuni ba, ko gidan wasu masu fada-a-ji, dan talakawa ne likis, mahaifinsa Malamin makaranta ne, inda mahaifiyarsa ta kasance mai sana’ar kiwon dabbobi. A haka ya rayu cikin wahalar karatu. Da ta abin amfani har Allah ya sa ya kammala.
A wancan lokacin, karatun boko bai zama yadda ya zama yanzu ba, gwamnati neman masu zuciyar yin karatun ta ke kawai ta tallafa musu. Don haka zai iya cewa matsalolin da ya ci karo da su a zamanin karatunsa ba masu yawa ba ne, ban da nisan gari da gari da yake a tsakani. Amma har alawus na abinci iyaye ba su faya wahala a kai ba, gwamnati na yi musu.
Yana dan shekaru uku mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, a dalilin ya auro wata, don haka ba ta barshi a hannun matar Babansa ba ta dauke shi ta tafi da shi wani kauye a Jihar Jigawa, inda kanwar mahaifiyarta ke aure. A can ya yi firamare ya gama, da ya isa shiga sakandire ta samu miji a can ta yi aure, shi kuma ta maido shi hannun mahaifinsa, ya dauke shi ya kai shi makarantar sakandire ta kimiyya da ke Dawakin Tofa, daga wancan lokacin ya ci gaba da zama hannun mahaifinsa har ya shiga jami’a.
Matar da yake aure din mai suna Luba, ta dauki tsangwamar duniya ta dora masa saboda ita Allah bai ba ta haihuwa ba, tana kishin kaunar da mahaifinsa ke yi masa, komai ya samo a kansa yake karewa.
To zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ga muzuru, ana ga shaho sai ya yi. Bayan kammala digirinsa na biyu ya ci gaba da zama da mahaifinsa, har ya samar masa aikin koyarwa a sakandiren da yake aiki.
Watarana da yamma yana karanta jaridar (Daily Trust) ya ga wani kamfani na cigiyar (Civil Engineers) masu matakin digiri na biyu. Kamfani ne da ke karbar kwangilar ginin tituna, gidaje, asibitoci, gadoji, Dam, titin jirgin kasa da sauransu. Ya dauki adireshinsu na (Fax) da (post office) wadanda da su ne ake amfani wajen sadarwa a wancan lokacin. Ya rubuta (application) ya hada da photocopy na takardunsa ya aika musu. Ya ci gaba da harkar koyarwarsa bai kara tunawa da zancen ba.
Kusa da gidansu da ke unguwar Yelwa gidan Alh. Mansur Maifata ne, mutumin yana da rufin asiri sosai, don duk unguwar babu mai sukuninsa, duk ‘ya’yansa mata ne ta ukun ita ce Aisha, ya sha ganinta tana wucewa in yana kofar gida yana karatun jaridar da ya zame masa taba, in bai karanta ‘Daily Trust’ kullum ba, ya ji halin da kasarsa ke ciki ba, jinsa yake kamar mara lafiya.
Kullum yarinyar ta wuce sai ya bi ta da kallo, shi ba ma’abocin kula mata ba ne duk da dalibai mata yake koyarwa, amma bai san me ya sa duk ranar da bai ga wucewar Aisha ta gabansa ba, sai ya ji wata irin kewa. Ya kura wa kofar gidansu ido ya yi ta Allah-Allah ya ga giftawarta.
Aisha Mansur, ba wata kyakkyawa ba ce fiye da ‘yan uwanta ba, amma duk ta fi su nutsuwa da kwarjini. Bai taba ganin ta tsaya da wani namiji a kofar gidansu ba kamar sauran ‘yan uwanta, abin da bai sani ba shi ne, ko an aika ba ta fitowa sai dai saurayi ya gaji da tsayuwarsa ya tafi.
Baban su Aisha na matukar kokari a kan tarbiyyarsu. Shi dai bai taba yi mata magana ba, haka ita ma. Amma ya lura in ta dawo daga islamiyya ta wuce shi, ya bi ta da kallon da ya saba binta da shi, in ta kai kofar gidansu sai ta juyo cikin dabara ta kalle shi, sannan ta wuce. Sai ya yi murmushi ya maida kai ga jaridarsa.
Ranar da ta lura ya kamata tana kallon inda yake, da gudu ta shige gidansu.
Murmushi ya yi, ya ci gaba da karatun jaridarsa, ya rasa me ya sa yake jin yarinyar a ransa. Ko sunanta bai sani ba.
Ranar wata juma’a suna zaune a kan tabarma a kofar gida shi da Babansa, suna cin tuwon dare a kwano daya, daya daga cikin ma’aikatan gidan Alh. Mansur ya zo ya gaida Baban, ya kuma sanar da shi Alh. Mansur ne ya aiko shi ya sanar da shi zai zo ganinsa karfe tara na dare.
Baban ya ce, “Allah ya kawo shi lafiya”.
Bayan sun gama cin abinci sun wanke hannu da ruwan butar alwala, Baban yake janshi da hira, don ya san in ta dan nasa ne, to a zauna a haka awa uku baki a rufe, ko kowa ya dauki jarida ya karanta.
“Ni wai cewa nake wata mai zuwa za ka cika shekaru ashirin da bakwai ne?”
Ya yi dan lissafi, ya ce, “Eh, Fabrairu insha Allahu”.
“Kuma ba ka da niyyar aure ko? A da in an yi magana ka ce karatu, hidimar kasa, aiki, yanzu wanne ne ya saura?”
Ya yi dan murmushi bai ce komai ba.
“Daidai gwargwado Allah ya rufa mana asiri, ba za mu kasa rike mata ba. Albashinka ya isa ka ciyar da iyali, ga gidan nan babba ne na ja maka katanga na ware maka muhalli, me kuma ya rage?”
Ya yi ‘yan mutsu-mutsu na rashin abin cewa, domin ba shi da hujjar da zai bayar, kuma ba zai iya fada wa Babansa abin da ke ransa ba, ganin abin ba mai yiwuwa ba ne.
Inda Allah ya kwace shi daga titsiyen Baba shi ne, isowar Alhaji Mansur Maifata. Turarensa mai dadin kamshi ya baibaye su, shaddarsa har walkiya ta ke. Ga damanga ya kafa, wadda a da babu masu sanya ta sai masu hannu da shuni. Ya ba su hannu dukkaninsu, Baba ya ba shi wurin zama, shi kuma ya yi musu sallama ya tashi ya ba su waje.
Bayan gaisuwa da tambayar iyali, Alhaji Mansur ya gyara murya,
“Wato Malam Habibu, abin da ya kawo ni neman alfarma ne, na neman iri. A zaman shekaru ashirin da muka yi tare na yaba da halayenka, da tarbiyyar da ka ba wa yaron wajenka. Ga ilimi mai kyau da ka tsaya tsayin daka ya samu, ban taba jin an ce yau ga abokin fadansa ko ga wani hali na banza da aka same shi da shi ba. Wannan ne ya kawadaitar da ni in neme ka mu hada iri, in har ka amince.
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya hore mu da mu nema wa ‘ya’yanmu mazan aure na gari a aurensu na fari. Duka yarana na ba su dama su zabi mazan aure da kansu su uku manyan, Aisha ce kadai ban bai wa wannan damar ba, a dalilin ita marainiya ce, mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta, ta sha wahala a hannun matana, ina so ta samu kwanciyar hankali da sukunin zuciya a gidan aurenta.
Ba wanda zuciyata ke kawo min kullum, sai hoton MA’AROUF dan wajenka, shi ne na yo tattaki in nemi wannan iri mai albarka. Ba na bukatar komai sai sadaq (sadaki) da Allah Ubangiji ya yi umarni. Amma idan Ma’arouf bai amince ba, don Allah kada hakan ya yi sanadiyyar da gaisuwar makwabtakar da muke yi da juna za ta tawaya, kuma kada a takura masa. Abu ne dai da nake da yakini a kai ba zai samu matsalar komai da Aisha ba, saboda ko cikin ‘yan uwanta ta fita daban wajen hankali da kyakkyawar tarbiyya”.
Malam Habib ya ja numfashi ya sauke, ya dubi Alhaji Mansur cikin murmushi.
“Wato dauki ne Allah ya kawo mini ina zaune a kan tabarma ta. Wallahi Alhaji tashin nan da ka ga ya yi zancen da nake yi masa ke nan, a da in na yi ya ce karatu, hidimar kasa, project, masters. Amma a yanzu babu ko daya, bai dai kai ga ba ni amsa ba ka zo, amma na san ba zai ki abin da na yi masa umarni ba. Sai dai kamar yadda ka ce, ba zan tursasa shi ba, zan ba shi zabi ba umarni ba.
Duk da haka wani hanzari ba gudu ba, ‘yar wajenka Aishatu ka ce sunanta ko? Za ta iya zama a wannan muhalli da Allah ya hore mana? Domin dai yatsun ba daya ba ne, kuma babu karya ko yaudara a tsakaninmu”.
Alhaji Mansur ya yi murmushi, “Ko a bukka ne cikin jeji na yi wa Aisha aure za ta zauna. Ina tabbatar maka da wannan. Tana da gida nata na kanta da ta gada daga mahaifiyarta, amma a gidan mijinta za ta zauna ko ya ya yake. Don haka kada ka kara wannan tunanin”.
Suka yi musabaha suka yi sallama, cike da aminci ga juna, Alhaji Mansur ya tafi.
Saboda farin ciki Malam Habibu da kyar ya bari garin Allah ya waye suka tafi masallaci sallar asubahi, da suka fito tun a hanya yake gaya masa yadda suka yi daren jiya da Alhaji Mansur.
Shiru ya yi kamar mai tunani, jinsa yake kamar a kan gajimare, yana shawagi don farin ciki. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, bai tabbatar cewa ita ba ce. Su hudu ne kuma bai san sunan kowacce ba. Baba ma bai sani ba, balle ya tambaye shi, yadda Baba yake murnar nan ba zai iya tula masa kasa a ido ba, kawai sai ya yi kundumbala ya ce, “Idan ita yarinyar ta amince ni ma na amince”.
Baba ya kama hannayensa ya rike cikin nasa, yana ta sanya masa albarka.
Baba da kansa ba aike ba, ya je ya sanar da Alhaji Mansur amincewar Ma’arouf wa auren Aisha. Gadan-gadan suka shiga shirye-shiryen auren shi da Alhaji Mansur. Ta fannin Baba, ya sa an yi fenti na farar kasa a sassan da ya ware wa dan tilon dan nasa, aka yi shafe na sumunti, daki ne ciki da falo matsakaita sai wani falle daya a gefe. Falle dayan Ma’arouf ke zaune ciki matsayin nasa, ciki da falo aka bar wa amaryar, sai makewayi guda biyu, na wanka daban, na bayan gida daban, sai ‘yar rumfar kwano da aka bari matsayin madafi. Tsakar gidan ya sha sumunti fes gwanin sha’awa. Gidan sai kamshin sabon fenti yake yi mai dadi.
‘Yan uwanta uku Khalisa, Halima da Zainab sai rawar kai suke wajen hidimdimun biki, ita kam a sanyaye ta ke, ko can ba shiga sha’aninsu ta ke ba saboda ba ta da wannan kuzarin (power). Ban da iya shege ba abin da suke mata, wai Baba ya ba da sadakarta wa malamin makaranta. Ko lefe ba a yi mata ba. A zuciyarta cewa ta