bata nemi komai ta rasa ba, Amina gudun maza take ba son kai kanta garesu ba. Amina na son aikinta fiyeda komai a rayuwarta. Ta sha gaya mata yana sanya mata nutsuwa, yana sa ta nishadi, yana sa ta farin – ciki yana rabata da damuwa.
Duk ta yarda da wannan, kawai dai burin ta a yanzu Amina tayi aure shine kwanciyar hankalinta, ba wai bata son ta da aikin ta bane. Kuma ta yarda yanzu Amina bata korar masu son ta sune suka dauke kafa.
Goggo Hauwa ta nisa ta dubi Amina, Zulai da Ilya masoyan su na gaskiya da duk suka zuba mata ido. Kowannensu ta bakinta yake son ji don a yanke maganar haka kowa ya huta.
“Amina, na yarda kije aikin ‘yar Gwamna amma a bisa alkawari guda daya”.
Amina ta dago da nutsuwa akan kyakkyawar fuskarta, “wane alkawari ne Goggo? Insha Allah zan cika miki shi muddin bai fi karfin na ba”.
Kije kiyi aikin na amince, amma idan kafin cikar wa’adin aikin ya cika Allah ya kawo miki mijin aure zaki bar aikin kiyi aurenki. In yaso idan mijin ya amince sai ki cigaba”.
Amina tayi murmushi har gefen kumatunta biyu suka lotsa.
“Ai a bisa wannan alkawarin muke Goggo har gobe. Wallahi ba ni nake korar su ba, su suke korar kansu. Amma na kara yi miki wannan alkawarin. Ko yau na fara aikin gobe mijin ya zo, zan bar aikin nayi aure ko wanene shi.”
Da sauri Ilya yace “A’ah Dr. Amina, daina cewa ko wanene, idan kuturu ko Gyartai ya zo ba ruwan Goggo fa, ke zaki zauna dashi”.
Goggo Hauwa bata san sanda tayi dariya ba, duk zukatansu sukayi dadi, don basa son ganinta cikin damuwa ko yaya, walwalarta itace tasu. Inna Zulai ta mike tayi musu sallama tana fadin
“kin bari sun kalallameki da dadin bakinsu. Ni nayi nan, tunda ko na sake cewa komai ma ba tasiri zaiyi ba”.
Ilya yace “haka ne Hajiya Inna, gara ki adana yawun bakinki zai yi miki amfani gobe. Sai Ji-kas! Wallahi sai Ji-kas!! Insha Allahu sai Ji-qas bamu fada a banza ba, bamu sha rana a banza ba!!! Gashi tun ba’a je ko’ina ba nida Amina mu zamu fara shan inuwar gwamnatin Ji-qas. Mune a cikin gidan gwamnati!”.
Washegari Amina da kwarin gwiwar ta ta doshi ofishin consultant dinta Dr. Usman Turaki. Saidai kash! Ofishin Turaki a kulle. Wani masinja ke gaya mata ai Dr. Turaki an bashi appointment na kwamishinan lafiya. Ya bar asibiti sai nan da shekaru hudu.
Allah ya so tanada lambar wayarsa a lokacin waya ta fara a cika duniya. Duk wani babban ma’aikaci yanada ita.
Ta kira shi ya kwatatanta mata sabon ofishinsa, sai yace ta jira a office dinta zai turo direba ya kaita yanzun nan.
A wata sassanyar mota da Amina bata taba shiga irinta ba, aka kaita (ministry of health) inda ofis din kwamishina Turaki yake.
Amina bata bi dogon layin da ake bi wajen ganin kwamishinan ba, kai tsaye aka sada da ita gareshi.
Amina ta shiga da nutsuwar ta kamar yadda take ciki kullum, irin wadda zuzzurfan ilmin boko ke gadarwa mai shi.
Ta gaisheshi, ta kuma yi masa murnar sabuwar kujerarsa. Yayi godiya, sannan ya tambayeta ta yi shawarar? Iyayenta sun amince?
Amina ta ce “Goggo ta amince. Amma a bisa sharadin in miji ya zo kafin lokacin kwangila ya cika zan bar aikin in yi aure”.
Dr. Turaki yayi murmushi mai kama da dariya. “That’s good”. Wani dan tunani ya darsu a zuciyar sa akan Ma’arouf da Amina. Amma daya tuna halin mutumin nasa sai yayi gaggawar goge tunanin daga zuciyarsa ya janyo na abinda ya tara su.
“kiyi parking yau. Duk da mai girma gwamna ya gayamin bakya bukatar zuwa da komai, amma mutum baya rasa abin amfanin sa. Kayan sanyawa ne bakya bukatarsu. Yau za’a maida takwararki gidan daga kauyen Ji-qas. Don Allah Amina ki kula da ita yadda ya kamata. As a doctor nasan bakya bukatar a tuna miki yadda zakiyi da patient dinki. But wannan patient din need extra-more saboda marainiya ce, sannan lafiyarta (matters a lot to her Dad). Zai nutsu ne kadai wajen aikin al’ummar sa in ya tabbatar Amina tana a kyakkyawan hannu kuma tana cikin koshin lafiya koda bata taka kasa.
Daga yau zan bar zama jakada a tsakaninku, kai tsaye zaki dinga magana da His Excellency in kuna bukatar wani abu ko sanar dashi wani abu na cigaba ko na ci baya da ya danganci lafiyar diyarsa. Be the best doctor and the best physiotherapist as we know. Kawo wayarki in sanya miki lambar tasa”.
Amina ta mika masa, ya sanya tayi saving. A ranta ta san ta karba ne kawai amma bazata taba iya kiran MA’AROUF JI-KAS ba! Wani kwayan mutum guda daya da ko sunansa bata taba kwatanta fada ko da a zuciyarta ba, duk da zasu kasance gida daya, shi din dai (Turakin), zata cigaba da baiwa jakadancin ko yana so ko baya so.
Su wanene wadannan gwarazan Ma’arouf da Amina? Daga ina suke? Menene asalinsu? Ga dai kaddarar rayuwa ta hadasu bayan kowannensu alamu sun nuna duniyar sa daban ce data dan uwansa??? Mu waiwaya baya.
****
ASALIN LABARIN
Goggo Hauwa na zaune a madafi tana kullin zobo da kunun Aya, wanda ya kasance sana’a a gare ta mai albarka. Ta kwala wa Amina kira daga nan inda ta ke zaune a kujera ‘yar tsugune cikin tsaftataccen madafinta.
“Me ki ke yi wa tantabarun nan ne haka Amina? Ki fito ki sa hannu mu yi mu gama kullin nan”.
Daga can dakin tantabarun Amina ta amsa,
“Dan bebina ne ba lafiya, ya kasa cin abinci shi ne nake dura masa dawar. Amma ga ni nan”.
Ta ajiye dan tattabarar a cikin tukunyarsa, ta fito ta tadda Goggo.
Wata kujerar ta jawo ta zauna tana fuskantar Goggon, suka ci gaba da aikin; in Goggo ta zuba sai ta bata ta kulla. Suna yi suna hira irin ta Da da mahaifi.
“Goggo in kin dauki adashen wannan watan ne zan koma makaranta ko?”
Amina ta fada cikin murya mai ban tausayi, wadda daga ji za ka fahimci rashin komawa makarantar yana damunta. Cikin muryar tausasawa Goggo Hauwa ta ce,
“Insha Allahu Aminatu, saura kwana biyar ma in dauki dashin. Insha Allahu in dai ina raye Allah zai nuna min cikar burinki. Ga ki can na hango ki cikin farar rigar likitoci kina tsira wa mutane allura…”
Nan da nan Amina ta washe baki, farin ciki mara misaltuwa ya bayyana a kyakkyawar fuskarta.
“Da yardar Allah kina raye Goggo, kuma da na fara daukar albashi kin bar sana’ar lemon Aya da Zobo, Cincin da meat pie. Ni zan saya miki duk abinda kike so, in kai ki Makkah, in saya miki mota, ki kwanta a gida ki huta.
Allah ya jikan Baba, da yana raye da karfinsa kafin ciwo ya kwantar da shi ina za ki rinka wannan wahalar? Dubi fa in kin tashi da asuba bakya kara komawa bacci, sannan in dare ya yi ba za ki kwanta a kan lokaci ba sai kin gama hada kayan aikin gobe.
Ina tausaya miki Goggo, har wani lokacin in ji bana son komawa makaranta saboda wahalar da nake barinki a ciki”.
Goggo Hauwa ta yi murmushi.
“Amina ke nan, ko Babanki yana raye ba na zama babu sana’a, ba don komai ba sai don in tallafa masa, kasancewarsa mai karamin karfi. Da kuma ciwo ya kwantar da shi dole na ci gaba da sana’a saboda kudaden magani.
Rayuwa ta canza yanzu kowa ya dogara da kansa shi ya fi, kada ki yi la’akari da abin da ki ka yi wa mutane ki ce za su rama miki. Dubi dai yadda kanne da yayyen mahaifinki suka yasar da mu saboda kasa ta rufe idanunsa. Don haka Amina na hore ki da sana’a komai kankantarta, ko da ta kiwon Tantabarun nan da ki ka kwallafa wa rai ne watarana za su yi miki amfani”.
Amina ta girgiza kai, “Abin yana ba ni mamaki Goggo, wai har Kawu Sule shi ma ya watsar da mu, duk irin taimakon da Baba ya yi masa, ya dauko shi daga kauye ya rike ya samar masa sana’a, dubi albarkar da ya samu a ciki, amma wai ko (school fees) ba zai iya biya min ba”.
Goggo ta ce, “Kada ki kullace shi, duk lalacewar shi ubanki ne. ba ki da wanda ya fi shi, kuma ba dolensa ba ne ya dauki nauyin karatunki don babu mahaifinki, kada ki dogara da kowa ki dogara ga Allah sai Ya iya miki”.
Amina ta girgiza kai, “To ke Goggo ba ki da dangi ne? tunda na taso na yi wayo ban taba ganin wani ya ziyarce ki da sunan dan uwanki na jini ba sai abokan arziki”.
Goggo ta yi murmushi, “Ba irin dangin da ba ni da su Amina. Ba zan je ko’ina ba ne sai ranar da Allah ya cika miki burinki, na aurar da ke a hannu na gari, sannan ne zan koma gare su Amina”.
Aminan ba ta kara magana ba, saboda sun gama aikin. Can kuma ta ce,
“Allah ya yarda Goggo”.
Ta mike ta jawo manyan kuloli tana shirya lemukan a ciki. Ta bude (freezer) dinsu ta soma ciro kankara tana zubawa a kai.
Daga can soro suka tsinkayi sallamar Ilya mai kura, wanda ke daukan kayan sana’ar yana kai wa makarantu da asibitoci, kura uku suka shigo da ita da samari biyu a bayansa bayan Goggo ta amsa sallamarsu, ta kuma yi musu izinin shigowa. Suka dauki manyan kulolin da bokitan da aka shirya meat pie da cake suka zuzzuba a kura suka yi waje kamar kullum.
Shi Ilyasu dan makotansu ne da yake kula da sana’ar Goggon cikin amana, tana biyansa duk wata. Katangarsu daya da gidan Goggon. Amma yanzu a dakin soron gidan yake zaune tun bayan tashin Sule kanin Baban Amina.
Amina ta cire hitar ruwan zafi daga bokiti da ta jona don ruwan wankanta ya yi zafi, ta dauka ta nufi bayan gida. Saboda dadi da tsaftar lemon Goggo Hauwa, da an fita da shi karfe takwas zuwa la’asar sai kudinta a hannu. Wasu kuwa gida suke zuwa saya, sana’ar Goggon sai masha’Allahu domin tana da nasibi a ciki.
Gidan marigayi Malam Mas’udu gini ne na talakawa masu rufin asiri. Dakali biyu sun sa kofar gidan a tsakiya, da ka sanya kai zaure (soro) za ka tadda, a cikin soron akwai daki falle daya wanda marigayin ya mayar dakin hutawarsa da karbar bakinsa masu zuwa daga kauyensu wyin kwanaki a wajensu. Daga baya da ya dauko kaninsa Sule a dakin ya zauna ya yi samartakarsa har ya yi masa aure.
A halin yanzu Ilya dan makotansu shi ke zaune a dakin wanda ya zama kamar Da ga Goggo, saboda maraya ne kamar Amina shi ma mahaifinsa ya rasu tun yana karami.
Da ka wuce zauren za ka tadda tsakar gida madaidaici. A tsakar gidan, dakuna ciki dai-dai ne guda uku, madafi a gabas, bayan gida a kudu. A tsakiyar filin tsakar gidan bishiyar umbrella ce wacce ta bude ganyayyakinta sosai ta ba da duhuwa mai sanyi.
Daki falle daya na maigidan ne Malam Mas’ud, kafin Allah ya dau ransa, daya na Goggo da Aminatu, tare suke kwana ba sa raba shimfida, yayin da daya dakin Tantabaru ne fal kala-kala maza da mata, sabuwar haihuwa da masu tashi, kowanne aure cikin tukunyarsa.
Sana’ar Baban Amina kenan, ya kiwata Tattabaru in sun girma ya kai kasuwa ya sayar. Wani zubin kananan ma ana saye. Da wannan sana’ar ya rike iyalinsa, suka rayu cikin rufin asirin Allah. Duk da matarsa Hauwa tana gwada sana’o’in hannu iri-iri.
Garin Bauchin Yakubu shi ne asalin garin Malam Mas’ud na haihuwa, sun fito daga kauyen Shira. A kauyensu tun yana yaro kiwon Tattabaru yake yi, wani ne ya ba shi shawarar ya dinga shigo da su maraya ana sayensu da daraja, da haka ya fara, ya yi keji babba ya zuba su a kasuwar Wunti, Allah kuma ya sanya masa albarka a ciki, ya koma gida Shira ya sayar da katuwar gonarsa ta gado ya dawo ya sayi gidan da suke ciki a yanzun.
Hauwa’u mahaifiyar Amina, asalinsu ‘yan kasar Sirrleone ne. Kasuwanci ne ya kawo iyayenta Bauchi har ta zame musu gida. Rannan ta shiga kasuwar Wunti wajen Babanta kai masa abinci kamar yadda ta saba kullum karfe biyu na rana, tana ‘yar shekara goma sha uku, ta ga Tantabaru guda biyu a hannun wani abokin cinikin Babanta. Cikin sha’awa ta soma tattaba su, ta ce, “Baba, don Allah ni ma ka sayo min in yi kiwonsu, ina son Tantabaru”.
Babanta Malam Hadi wanda shi kuma sana’ar saida kaji yake yi ba su da nisa da Mas’ud, wanda a lokacin saurayi ne mai tashen kuruciya, ya yi dariya ya ce, “Ba na son rigima Hauwa’u, ina za ki iya wani kiwon Tattabaru ke da ko kajin da nake bari a gida ba iya kula da su ki ke yi ba, ina za ki iya wani kiwon Tantabaru?”
“Wallahi Baba zan iya, don Allah ka saya mani”.
Hauwa ta dage, Malam Hadi yana matukar son Hauwa, don ita kadai Allah ya ba shi, tare da maidakinsa Aishatu.
Ya ce, “Tunda kin dage bari in sallami wannan mu je in saya miki wajen Masa’udu, amma lallai in kina barinsu da yunwa zan dawo masa da su”.
Hauwa ta amince da sharadin Babanta.
Masa’udu yana zaune ya zuba tagumi, yau tun safe bai yi cinikin ko Tattabara daya ba, Hauwa da Babanta suka yi masa sallama, ya dago da sauri idonsa bai fada a ko’ina ba sai cikin na Hauwa, ya kuwa zuba mata ido ya kasa daukewa. Yarinya kyakkyawa, doguwa kalar mutanen Sierleone, wani abu ya ji ya fizgi zuciyarsa a kanta, sai da Malam Hadi ya yi gyaran murya ya yi firgigit ya maida hankali kansa, tukunna ya fara gaishe shi, Malam Hadi ya dube shi cikin kulawa.
“Masa’udu tunanin me ka ke yi haka? Ko yau ba kasuwa ne?”
Masa’uudu ya yi dan murmushi, don a halittarsa ba shi da yawan magana. Malam Hadi ya ce.
“Kada ka damu, ai kasuwa ta gaji haka, wataran kaf mutum ya rasa ciniki, idan Allah ya koro cinikin kuma sai ka ganshi fiye da tunani, Allah ya ba mu kasuwa mai albarka”.
“Amin”. In ji Mas’ud.
Ya maida hankalinsa kan Hauwa, ya ce, “Kanwarka ke son Tattabaru aure daya, nawa suke?”
Masa’udu bai san sanda ya sanya hannu cikin kejin ya zaro wadanda suka fi sauran kyau ba ya mika wa Hauwa, ta karba kowacce a hannu daya tana ta murna.
“Nawa suke?” Malam Hadi ya sake tambaya.
“Naira Maitan, amma ita kyauta na ba ta”.
“A yi haka Mas’udu?” In ji Malam Hadi yana murmushi.
“Har fin haka za a yi, tunda kanwata ce kamar yadda ka ce”.
Malam Hadi zai ja da nisa Mas’udu ya katse shi, “Idan har da gaske ka ke kanwar tawa ce, to don Allah ka barshi haka”.
Malam Hadi ya ce, “Shi ke nan Masa’udu, Allah ya kawo kasuwa mai albarka”.
Masa’udu ya ce, “Amin”.
Hauwa ta rusuna ta ce, “Na gode”.
Kai ya daga mata, Babanta ya wuce gaba, ta bi shi a baya.
Masa’udu tun ganinsa da Hauwa ya kasa sukuni, kwana uku bayan nan ban da tunaninta ba abin da yake yi, daga baya ya gane kaunar Hauwa’u ce ta shige shi farat daya. Ya kuma yanke shawarar kai kukansa ga mahaifinta ko da ba zai ba shi ba a kalla ya samu sukuni cikin zuciyarsa.
Washegari ya tadda Malam Hadi a nasa kejin, ya sunkuyar da kai, Malam Hadi ya ce, “Ya aka yi ne Mas’udu? Mun gaisa ka yi shiru bayan da ganin bakin nan naka akwai motsi a cikinsa”.
Mas’ud ya muskuta ya daure ya ce.
“So nake ka ba ni izinin shiga cikin maneman Hauwa’u Malam, in har ba an yi mata miji ba”.
Malam Hadi ya yi murmushi, a ransa ya ce, “Na san za a yi haka”. A fili kuma ya ce, “Ka zo sau uku ku shirya, in ta amince ni da ma a shirye nake da in aurar da ita”.
Zuwan Mas’udu biyu wajen Hauwa suka shirya kansu. Ya tattara ya tafi Shira don turo danginsa. Iyayensa sun dade da rasuwa, sai kannen Babansa guda biyu Malam Bilya, da Malam Tasi’u. sai kaninsa Sulaiman wanda a lokacin yaro ne. Ko da ya kai maganar ga kawunsa Bilya sai cewa ya yi, “Ni nan ai na riga na yi maka mata, kanwarka Talle. Jira nake ka zo da ma in yi maka zancen”.
Masa’udu ya ce, “Ba zan iya auren zumunci ba Kawu, don Allah ka amshi zancen Hauwa’u, ita ma iyayenta mutanen kirki ne”.
Malam Bilya ya danne bacin ransa na kin amsar ‘yarsa da Masa’udu ya yi, ya ce zai zo marayar ya sauka gidan amininsa ya yi bincike a kan yarinyar da iyayenta, kafin ya yarda ya shige masa gaba kan aurenta. Ya je ya dawo bayan sati daya.
Masa’udu ya kasa barin satin ya cika, kwana shida ya yi ya dawo Shira wajen kawunsa, sai da ya gama sha masa kamshi sannan suka zauna.
“Na gama bincike na tare da aminina Malam Dahiru, abin ikon Allah ma makota suke da iyayen yarinyar da ka ke nema din. Bincike ya nuna iyayenta bakin haure ne daga can wata kasa da ban taba ji ba wai Saliyo. Don haka ni ba zan shige maka gaba kan auren wadda ban san asalinta ba. In ba za ka auri kanwarka ba, to ka nemo wata ‘yar asali amma ba na cikin auren bakin haure’.
Masa’udu bai hakura ba, sai ya koma kan daya kawun nasa Tasi’u, don shi kam mai ilimin addini ne, limami ne guda a shiyyarsu, shi kam ya karbi maganar da muhimmanci, da ya yi nasa binciken ya nuna ban da kasancewarsu baki iyayenta mutanen kirki ne da aka yi musu kyakkyawar shaida, yarinya kuma ta samu tarbiyya da ilmin addinin islama har alqur’ani ta sauke.
Don haka shi ya shige wa Mas’ud gaba ya auri Hauwa, ya sayar da gonarsa ya saya musu gida a nan inda suke zaune har yau. A lokacin duniya na kwance sayen gida ba tashin hankali ba ne. gidansu yana nan a unguwar Gwallaga, wanda suke raye har yau a ciki. Sana’o’i iri-iri Hauwa ta yi don ta taimaki kanta da mijinta. Sun dade Allah bai ba su haihuwa ba, sai da suka shekara goma da aure, sannan Allah ya ba su Amina.
Lokacin da Masa’udu ya yi karfi a kan sana’arsa sai ya dauko kaninsa Sule daga Shira ya nuna masa sana’ar Gwanjo, ya sai masa ‘dealer’, ya fasa yana sayarwa da dai-daya, cikin sa’a sana’ar ta karbe shi, har dai da ya yi wani ubangida da ke ba su (dealer) su fasa su sayar su kawo mishi uwar kudi su rike riba. Ya ba shi daki a nan zauren gidansa suke zaune tare, kasancewar iyayensu su biyu rak suka haifa, Kawu Bilya da Kawu Tasi’u duk uba suka hada, shi ya sa sau da yawa idan Hauwa na nuna damuwarta a kan rashin haihuwa ya kan ce, ni kam ba na damuwa, watakila rashin haihuwa a cikin jinina yake, don duk zuriyar su mahaifiyata daga mai Da daya sai mai biyu.
Da Sule ya yi karfi a sana’ar gwanjo ya yi gidan kansa, ya auri ‘yar ubangidansa Atika, sannan ne ya bar gidan Yayansa Mas’udu Baban Amina, domin zuwa lokacin ya fi Yayan nasa samun nasibi don Alhajinsu na ji da shi, har dai da ya auri Atika, shi ma ya sakar masa harkar sosai, har Turai yake zuwa ya shigo musu da kaya.
Amina, ta taso yarinya mai hazaka da son karatu, ga naci a kan abin da aka koya mata, har sai ta ga ya zauna a cikin kanta. Ga son iyaye da son kyautata musu. Tun tana shekara shida ba ta barin Goggonta da ayyukan gida, ko dai a bar mata tayi, ko ta sa hannu su yi tare. Albarka kullum shanta ta ke daga bakin uwa da ubanta tun tana kankanuwa, shi ya sa ta taso yarinya mai matukar nutsuwa da wadatar hankali. Amina ba ta da aboki sai littattafanta da alqur’ani. A zuwa makaranta Amina ba ta san latti ba, daga islamiyya har boko, kullum ita ke daukar tsintsiya ta share ajinsu na islamiyya dana boko saboda tana riga kowa zuwa.
Amina na da shekaru goma sha biyu mahaifinta Mas’udu ya gamu da lalurar shanyewar barin jiki, sun tashi lafiya sun wuni lafiya, da yamma ya dawo daga kasuwa suka taba hira a tsakar gida da iyalinsa. Ana gab da kiran sallar magriba ya mike.
“Yar albarka zuba min ruwa a buta ki gani in yi maza ko na samu jam’i”.
Amina ta ce, “Baba, ai tun dazu na zuba maka”.
Ya kai hannu ya daga butar, “Haka kuwa, Uwata Allah ya kara albarka”.
Murmushi Amina ta yi.
Yana shiga ita da Goggo suka mike don gabatar da tasu alwalar, sai ji suka yi timmm! Ya yanke jiki ya fadi cikin bandakin. Da gudu suka danna kai a bandakin daga uwar har ‘yar, ba tare da tunanin halin da za su riske shi a ciki ba.
Hauwa na kokarin taimaka masa ya mike, ta kasa don idanunsa sun kakkafe, bakinsa ya gicciye. Amina sai kuka, Goggo ta ce.
“Maza kirawo Ilya”.
Ta kwasa da gudu domin kiran Ilya a dakin soro.
Ilya ne ya samo taxi suka taitayi Malam Mas’udu, suka sanya shi suka nufi Specialist Hospital Bacas.
Duk wasu shige da ficen shi ya yi har likitoci suka karbe shi. Abin da suka gaya wa iyalinsa bayan sun dudduba shi, ya yi matukar daga musu hankali. Cewa Mas’udu ya gamu da lalurar shanyewar barin jiki, (sudden stroke) don haka sun ba su gado, za a ci gaba da ba shi kulawa da taimakon gaggawa.
Aka danka wa Ilya (bill) na allurai da magunguna da ake bukata, ya je gidan Kawu Sule ya kai masa, ba da son ransa ba ya kawo kudin ya bayar amma bai je asibitin ba yace da Ilya ya gaya musu tafiya ta kama shi Allah ya kara sauki. Ilya ya kawo ya biya komai harda na aljihunsa ya kara aka ci gaba da ba shi kulawa.
Satinsu uku a asibitin ya ji sauki, aka ba su sallama. Yana iya motsa hannunsa da kafarsa, amma ba ya iya yin komai da su. A gida jinyarsa ta koma hannun Goggo, domin Sule ko dubiya bai zo ba bai kuma kara tallafa musu da komai ba tun bayan wancan taimakon da yayi na sayen abinda ake bukata a asibiti lokacin da abin ya faru.
Sai ya zamana Amina tun tana shekaru goma sha biyu ita ke dafa abin da za su ci a gidan, ta tsaftace ko’ina ta kula da sana’ar Goggo ta kalanzir da sayar da itace da ta ke yi a lokacin. Har ya zamanto tana makara a zuwa makaranta, sannan ba ta da nutsuwa kwata-kwata, tana tunanin halin da za ta koma ta riski Babanta a ciki, malamanta kansu sun fahimci hazika Amina Mas’ud ta canza. Da ko an tashi makaranta Amina ba ta gaggawar tafiya gida sai ta kammala rubuce-rubucenta, in aikin gida ne (homework) sai ta kammala shi a lokacin sannan ta tafi gida. Amma yanzu ana kada kararrawa Amina ce farkon fita daga aji cikin sassarfa, wani lokacin ma da gudu ta ke fita.
Ranar wata lahadi a islamiyyarsu inda suke yin Tahfiz daga karfe takwas na safe zuwa azahar wani malaminsu Ustaz Abdulsalam wanda Allah ya daurawa kaunar Amina (ba kauna ta soyayya ba), bayan ta bada haddarta ya daga kai ya dube ta tana harhada takardunta don komawa gida ba tare da an yi addu’ar tashi ba.
Ya ce, “Amina Mas’ud, zauna ki jira ni in gama da ‘yan uwanki, akwai maganar da za mu yi”.
Ba da son ranta ba Amina ta koma bencinta ta zauna tana ta sake-sake cikin ranta, “Ban daura abincin rana ba, na san yanzu daga Goggo har Baba sun dawo daga asibiti ba su samu na dafa komai ba…” Sai hawaye sharr-sharr.
Ustaz na lura da Amina, kawai sai ya ji zuciyarsa ta karye, ya fahimci tsayar da ita din da ya yi ne ya sa ta kuka. Shi kuma so yake ya ji me ta ke yi wa sauri haka da har ya shafi hazakarta a kan karatu? Tana daga cikin daliban da ya sanya sunansu za su halarci gasar karatun alqur’ani mai tsarki ta duniya (International