Share this page
5 / 7
hanyar gin ubanki" Ta gitgiza kai kamar tana gabanta, wlh bazan iya rabuwa dashiba zuciyata takamu da son yaya Abdul'aziz, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, tai sauri sherewa. ta daidaita muryar ta, yaya please dan ALLAH kayi hak'uri kaje kaga hakkinsune tunda suna gidan !! Banza yay mata, bata gajiba tak'ara maimai tawa, cikin raunin murya. "Zumbur ya mik'e yay matuk'ar k'ara d'are fuska, ya nunata 👉🏻👸🏻 kinsan ALLAH kika k'ara yimini magana saina kashe fuskarki da mari,ya koma yakwanta abinsa ya lumshe idanu. Ta dad'e zaune tana kallonsa, daga k'arshe itama ta kwanta can k'arshen gado kamar yanda takeyi. #""#""#""#""#""#""# Su ikileema kam tunda dady yay musu abunnan, sai sukai zuciya, suka nufi b'angaren husna. " husna tace kenifa bazan juri wulak'anciba, umma xan kira na fad'a mata, "Ikilima ta warce wayar, ALLAH husna baki da hankali, ke har yanzu baki shiga karatun tanatsuba, kinsan dai halin wannan jarababbar tsohuwar sarai, wallahi saidai ta sake b'ata komai ingaya miki, kinsandai taurin kai irin na mijinmu da miskilancin tsiya, idan kuma sokikeyi igiyar aurenki ta tsinke to, nidai wallahi inan, samun miji irin dady sai an tona, haka kawai bazanyi saki na dafeba, duk abinda zaiyi zan jure, to ashema idan muka tafi mun nuna ma waccan shegiyar faratun ta ci galaba akanmu, ta mik'a mata wayar, karb'a kikira ta nidai karkice dani, tafad'a tana ficewa ad'akin. Husna tabita da kallo, kumafa hakane 'yar uwa nagode dakika tunatar dani, dan nasan wallahi nafiki son dady......... 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam} [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 43 «*****» da asuba ya tashi yay alwala, ya tafi masallaci, baitada Munneerah ba tunda yasan tana fashin sallah. Ko da yadawo b'an garansa yanufa yay kwanciyarsa. " Munneerah tatashi, itama sannan gari ya waye, tai wanka sannana ta nufi kichin ta had'a break,harda su ikileema. Takoma d'aki tagyara ko ina taturare da k'amshi, tasake shiga wanka. "Dady ya tashi yay wanka, ya shirya cikin purple d'in shadda, d'ikin rigar daka d'an ya wuce d'uwawunsa, akagyara suma fas, azuciyata nace kai gay d'innan yanaji da sumarnan kamar ta kayan kud'i, bayan ya gama yakwashi wayoyinsa, da jakar aikinsa, ya nufi b'angaren Munneerah. Bata palo dan haka ya ajiye kayan hannunsa yanufi bedroom d'inta, tana zaune kan kujera ta baje kayan 'yan kunnanata akan tebir d'in gaban kujerar, tana neman d'an kunnan dazata saka. "Ya shigo d'akin da sallama, ta d'ago tana amsawa, tazame k'asa tana gaishesa. Ya amsa fuskarsa ba yabo babu fallasa, "Lafiyar ki kika baje kaya haka??? "Tad'an turo baki gaba irinna shagwa6a6u,d'an kunne nake nema kuma nak'i ganinsa, tafad'a ido nacika da hawaye" Shi dariyama tabashi, k'uruciya tatashi kenan ya fad'a azuciyarsa, yay d'an murmushi, sannan ya gintse fuska to kuma gashi ance dole sai shi zaki saka yau???? "Ta kuma turo baki gaba, nishi nakeson sawa wlh, "To yikuka yafad'a yana dariya ciki ciki, dole dai dariyar ta fito" Ta kallesa hawaye na shatata afuska, ya k'araso ya zauna kusa da ita, to 'yar shagwab'a bar kuka, ya sa hannu yana share mata hawaye, bari nataya ki dubawa ko, ya fad'a yana fara duba 'yan kunnan, wana iri kike nema, ta mik'a masa d'ayan data gani........ 🌺billy🌺 🌹{ Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 44 «******» cikin minti biyu yagano d'ankunnan, ya d'ago yana murmushi to gashi zona saka miki, ta mik'a masa kunne yasaka mata, tajuyo d'ayan yasaka mata. "Iye kaga 'yan matan baffa kinyi kyau fa sosai, amma da za'ayimini shagwa6a, tasa hannu tarufe fuska tana dariya 🙈. "Ya mik'e tashi muje kibani break na wuce nakusa makara wajan duba d'an kunne. Tace kai yaya duka minti nawa kayi kana dubawa?? "Oh hakama zaki ce" "Da sauri tace a'a yi hakuri" Suka iso wajana cin abincin, ta zuba masa komai, ta mik'e. Yace sai ina ? Zan kira au anty ikilimane muyi break d'in. Nan take ya gimtse fuska, Itama kanta saida ta tsorata taga yana k'ok'arin tashi. Da sauri tace dan ALLAH yaya yi hak'uri na fasa. Ya harareta kinsan ALLAH idan kika k'ara yimini zancensu saina 6ata miki rai. Ta dur kusa agabansa kayi hak'uri bazan sakeba. "Ki kiyaye" Yau baimaci abincin kirkiba ya tashi ya fice, haka ta daure taraka shi, tana masa addu'a kamar yanda tasa ba. Aciki ya amsa, yaja mota ya tafi. Munneerah ta dafe kai, yaya matsala kamar bashine ya gama dariya ba yanzun. Ta koma cikin gida ta had'a break d'in su ikileema a k'aton tire tanufi 6an garen husna tunda shine kusa da ita, ta tura kofar falon ta shiga ba kowa dan haka taje ta ajiye kan tebir ta fita. "Su asannan ma sunacan suna kwasar barci abinsu........ 🌺billy🌺 🌹{ Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 09093044460 Na billkisa ibrahim 📝📝 45 «*****» yana zuwa office ya fara duba marasa lafiya, kamar yanda yasaba. "Bayan yatashi yanufi gidansu Ya tura k'ofar palon, yashiga da sallamarsa bakowa palon, sai TV daketa 6a6atu, yanufi d'akin mom, nanma batana sai kawai ya haye saman dad, danyana tunanin tanacan. "Ilaikuwa suna tare da dad, dad ya washe baki oyoyo babana kaine agidan yau. Yazauna yana fad'in dad nine wlh, ya tsugunna ya gaida su. "Mom tace babammu daga ina haka?? Mom daga asibiti nake nace bara na gaidaku. To sannu ya aikin?? "Alhamdulillah mom" Ya rage fara'a Dad yace dadyna ya akayi ne?? Sunsan tun yana yaro idan yanason abu saboda miskilanci bazaiyi magana ba saidai fuskarsa ta nuna, dan haka sukan gano damuwarsa da wuri ta wannan hanyar. Yaja ajiyar zuciya dad yarannan ne suka dawo jiya" Dad yace su husna? "Ya gyad'a kai batare da yayi maganaba" To ai.shikenan babana saika had'asu ka rik'e da adalci kaji, kar kuma nasake naji wata fitina ta taso, kazama namiji a gidanka, miye kazama namiji, karka yarda wata ta cutar dawata acikinsu, su duka 'yan uwankane, bana son tasanadin aurennan zumincinmu yay rawa ko kad'an. Dady yace amma dad kasan fitinar yarannan, muna zaune abummu lafiya, yanxu sun dawo zasu 6atama mutane zama. Kayi hak'uri nida kaina zan tsawatar musu kasami lokaci koda daddarene ka d'akkosu kuzo kajiko. "To dad zanyi k'ok'ari" Mom.ina 'yan biyu?? "Suna makaranta dady, yanzu zaka gansu nan tunda sunce darasi d'aya garesu yau. To ALLAH yadawo dasu lafiya. "Amin" "Ya mik'e to bari nawuce gida" To babana kagaishe da iyalinnaka. "To zasuji, insu 'yan biyu sun dawo ina gaidasu, tunda sunk'i zuwa, Munneerah tanata so suzo. "Mom tace makaranta ke hanasu sakewa wallahi. Tayi hak'uri zasuzo" "To sai suzo. Bayan tafiyarsa dad ya kalli mom, bilkisu kinga babana saiwani kyawu yakeyi, gawani tashen k'iba dayakeyi. Mom tai dariya, dad'in mace tagari kenan alhaji, da yana ta wani shi bayaso, Dad yay dariya aikinga yanzu kinjishi shiru ko. ALLAH ya k'ara basu zaman lafiya dai. To amin........ 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 46 «******» husna tatashi abarci tafito falo tana mik'ar tashi da hammar yunwa, karaf idonta akan tiren abincin da Munneerah ta ajiye, ta k'arasa da sauri wajan tana bubbud'e kwanikan abinci wani k'amshi mai dad'i yadaki hanacinta, tace "wow" waya ajiye abincinnan?? Tanana tsaye ikileema ta shigo, ta k'araso da sauri husna a'ina kika samu abinci?? "Kedai bari wallahi nima yanzu nake jajen wanda ya ajiye" Munnerah ta shigo da sallama, suduka suka bita da kallo a wulak'ance, tace ina kwanan ku?? Ba wadda ta amsa mata saima tsaki da ikileema taja, husna tace to 'yar shishahigi miya kawoki b'angarena?? "Munneerah ta raunana murya kiyi jakuri anty husna dama cazan muku ga abincinan" "Gabad'ayansu sai jikinsu yay sanyi, amma dan karta ganosu sai husna tace to munji ga hanya nan, tafad'a tana nuna hanyar fita👉🏻🏡. Munnerah tafito tana murmushi, nace baiwar ALLAH kenan. Muta nan naku kuwa sai suka zauna suna kwasar gara suna santi dayaba girki ko dad'in abincinne yasasu mance wacece ta dafa. Darana takuma dafa wani lafiyayan abincin akakaiwa dady office, bata yi zuciyaba ta kaimaau ikileema suma. ~~~~~~~~~~ Dady yay hon maigadi ya bud'e masa k'aton get d'in ya shigo saida suka gaisa da mai gadi sannan ya ida shigowa. 6an garensa yanufa, yarage kayan jikinsa, kamar yanda tasaba yauma ta had'a masa ruwan wanka daketa tashin k'amshi, yashiga yay wanka yana maijin dad'in ruwa, yaudai koda ya shirya sai yanufi masallaci dan yaji anakiran sallah. Saida akai isha'i yadawo gida, 6angaren Munneerah ya wuce, su husna dake zaune suna jirnsa afalon Munneerah, bayan sun gama zaginta da cimata mutunci, tanata kuka amma tanaji sallamar dady cikin dabara ta goge hawayen, lokaci d'aya suka mik'e, ita tana masa sannu dazuwa, sukuma suna aikin kallonsa............ 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 47 «*****» Ya kuma tamke fuska kamar bai ta6a dariya ba, ya nufi bedroom d'in Munneerah, batare daya tanka suba, husna takalli ikileema. 'Yar uwa mubishi, suma suka nufi bedroom d'in, "Yana kwance akan gadon k'afafunsa nak'asa idanuwansa alumshe,suka zauna agefensa, sun sakashi tsakkiya kenan. Har asannan bai bud'e idanun saba, ikileema ta shafa sajensa my love!! ko motsi baiyiba' ikileema tace dan ALLAH dan ANNABI kayi hak'uri, kayafe mana. "Ya bud'e ido yana kallonta aini bakuyi mini komaiba. A'a my sweet. Wlh mun maka laifi tunda kak'i saurarenmu, amma dan ALLAH kayafe mana, munmaka alk'awari bazamu sakeba. In kuma kun sake nai muku mi? "Duk abinda kai niya" Ikileema tace in sha ALLAHU bazamu sakeba" Munneerah tashigo tace musu ga abinci fa, saidai zuciyarta tayi zafi daganin su ikileema sunsa mata miji tsakkiya, duk suka mik'e, suka nufi falon. Munneerah tazubama dady, sukuma suka zuba da kansu, tazuba kad'an tanaci, dady yakalleta wannan shine abincin?? Ta d'aga kai, alamar eh. "Shiyasa gakinan kamar tsinke" "Batace komaiba, sai murmushi........... 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN KL'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 09093044460 Na billkisa ibrahim 📝📝 48. «******» yau tsawon wata uku da dawo war su ikileema, gidan dady, dady yana k'ok'arin yin adalci atsakanin matan nasa, duk abinda suke buk'ata yana k'ok'arin yimusu. Duk da su ikileema basu bar halinsu ba, kuma suna ta6a fad'ansu dasuka saba, dukda suna nuna yanzu sun had'e kai. Suna takurama Munneerah, da zagi habaici kullum, amma bata ta6a gayama dady ba, koda ya ganta cikin damuwa ya tanbayeta, takance masa kanta yana ciwone, kodai tafad'i abinda zaiyarda da ita. Har yau babu abinda yashiga tsakaninshi da ita, sai girmamawa, dukkan abinda yasata tana masa. Tana yin abinci duk ranar girkinta, sukuma ranar nasu, su saka masu aiki, dady baya cin abincin, danshi yanada k'yank'yami, du ranar girkinsu saidai yaje waje yaci abinci. Munneerah tanason tarink'a dafa masa tana tsoron masifarsu, dan haka tasa ido. Yauma kamar kullum tagama had'a abincin dare, dayake dady yau a 6angarenta yake, tai wankanta fes, tana cikin canja kaya saitaji mararta ta murd'a tarik'e ciki kam tana ambaton sunan ALLAH, anan ta durk'ushe tana murk'ususu, batare data gama saka rigarba. Dady yadawo daga masallaci ya wuce 6angarensa, har yazauna yakunna TV zai kalli labairai, saikuma ya mik'e, yanufi 6angaren Munneerah, ya shiga falon batanan dan haka ya wuce bedroom, da sauri ya k'arasa yana fad'in Munneerah!!!. "Yad'agota dasauri yana tanbayarta mike damunta?? "Cikin kuka ta nuna masa mararta" Shima cikin mamaki yace mara kuma? dama ciwonnan bai tafiba? "Ya ajiyeta akan gado yanufi 6angarensa, allura yad'akko yay mata, kamar ranar cikin minti biyar barci ya d'auketa. Yaja ajiyar zuciya, shiyanzu miya kamata yayi akan ciwon nan na Munneerah ne?? ZUCIYARSA tace kaiko kake da abinda zakai mata tarabu da wannan ciwon, ya girgiza kai, kai bayanzuba sai nan gaba yanzu tayi k'ank'anta" "ZUCIYARSA takuma cewa ashe baka so ta warke kenan. Ya shafa kanta ina son ki warke abar k'aunata, nayarda da zuciyata Munneerah, nakamu da sonki, sokuma mai tsanani wanda ban ta6a yima wata d'iya mace ba, tausayinkine yakesani kasa neman wani abu awajanki........ 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 49 «*****» ya tsura mata fararen idanunsa masu yalwar gashi, sai asannan ya lura ma ba riga a jikinta, jiyay yana neman zaucewa, dama haka Munneerah take, ya rintse ido ya bud'e, lallai d'an hakkin da ka raina shike tsonema ido, dan shikam yau Munneerah ta tsone masa nasa idon. "Yamik'e kamar wanda kwai ya fashema aciki, gaba d'aya jikinsa yayi masa nauyi, k'irar Munneerah ta birkita masa kwanya, yaje wajen dirowarta ya d'akko mata riga, yazo yasaka mata. "Palo ya fito yaci abinci, ya kwashe kayan zuwa kichin, 6angarensa ya koma ya kashe komai ya kulle wajan yadawo, wajen Munneerah cikin shigar kayan barci, yazauna yana binciken nasa nafama, duk da yau bayama fahimtar karatun nasa, dan sai Munneerah kemasa gizo a ido. Ya dai rufe duk book's d'in, ya tashi ya hau gadon, kusa da ita yakwanta, yay musu addu'a, jikinsa ya jawota ya rungume, yaja nunfashi da k'arfi tare da fad'in ya salam. "Yauce rana ta farko daya fara rungume Munneerah, yakan dai zauna kusa da ita, ya kuma matseta kam ajikinsa har saida tad'an motsa, ya sassauta mata, yace kaji wani lafiyayyan jiki, lallai mata suna suka tara, hakadai yay ta tunane tunanen sa, harsai gabannin asuba barci ya kwasheshi, hakanne yaja masa makara da asuba, sai agida yay sallah. Ya dawo kan gadon ya kwanta, wajan k'arfe 7:24 am, Munneerah ta farka, jintatai ajikin mutum, tai saurin bud'e idanu, ta saukesu akan dady dake barci fuskarsa tamkar yana murmushi, ta dad'e tana kallonsa, har saida ya motsa ta runtse idonta da sauri, saida taji bai bud'e idoba sannan ta bud'e nata, tai k'ok'arin zame jikinta, ya bud'e ido yana kallonta, tasa hannu ta rufe fuska🙈, wai ita kunya, dady yay Murmushi. "Ai idan kin bar jikina dole na tashi, ya fad'a yana zame hannunta daga kan fuskarta, ta rintse ido kam, yay dariya yau kuma kunyar yaya akeji?? " tad'aga kai tana murmushi" "Ya mik'e zaune yana kallon agohon d'akin, to ai nima lokacin tashina yayi, bari naje na shirya zuwa office, ya kamo hannunta ya summba ta, da sauri tacusa kanta k'ark'ashin pilo. Ya fita yana dariya. "Yay turus danganin ikileema da husna tsaye kowacce rik'e da k'ugu👯......... 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 09093044460 Na billkisa ibrahim 📝📝 50 «******» ku kuma lafiya?? "Husna tace lafiyarce takawo haka, tafad'a tana murgud'a baki😘, "Yaratse ta gefensu zai wuce ikileema tai saurin shan gabansa, ya tsaya yana kallonta,itama kallonsa takeyi cikin tsakkiyar ido, ya sake canja hanya husna ta tareshi ta can, kai wai lafiya kuwa?? "Ikileema tace kace haka kuwa, amma cakai kowacce acikin mu ta rink'a zuwa d'akinka ko??? "Eh hakana ce, yanzu miyya faru??? Husna tace abinda yafaru shine munga kafito daga nan 6angaren, da alama ma nan ka kwana?? "Can na kwana sai mi,kuma yafaru? Kace haka kuwa, mudai inhar aka cigaba da cin amanarmu ALLAH ya isa wallahi. Suka bar gurin da sauri, dady yabisu da idanu, yana mamkin rashin tarbiyya irin na yarannan, amma zai gyara musu zama kwanannan. Ya wuce yay shirin zuwa office, sanda yadawo 6angaren Munneerah harta gama had'a break , ta shiga wanka, ya zauna yay break d'insa, yana cikin cin abincin Munneerah ta fito cikin bak'ar soguwar riga da ratsin blue, ta d'aura blue d'in d'an kwali. "Ta zaro ido 😳waje, yaya dakanka? mai makon kajirani nazo na zuba maka?? "Yay murmushi, saikace wani aiki? Wallahi aikine yaya kamarka kana zuba abinci da kanka, aiba girmanka bane. "Ya jawota jikinsa ya zaunar da ita kan cinyarsa, to minene girmana my beauty!!! ??? Ta sinne kanta cikin k'irjinsa tana shak'ar k'amshin turarensa mai dad'i, yay kissing d'in kunnanata, kibar jin kunyata my beauty, nifa mijinkine, kuma ai mata batajin kunyar mijinta. Takuma cusa kanta a k'irjinsa tana dariya, kinga tashi kici abinci, kisha maganinki, dukda nasan mak'iyinkine magani. Ta tashi zaune ta yinkura zata tashi, yarik'eta da sauri ina zaki kuma?? "Ai ni zan baki da kaina 'yan mata" Yaya please zanci da kaina, ALLAH kunyarka nakeji. aiko ki ajiye wannan kunyar yau da hannuna zan baki abinci, dole ta hak'ura yabata da kansa tana zaune asaman cinyarsa, da kyar ya barta, amma da yadage saita cinye filet guda na abinci, yabata maganin tasha tana yatsina baki, saida yayta lallashinta sannan tasha. Tarakashi har mota kamar yanda tasaba, suka rabu cikin tsantsar farinciki, da kewar juna. "Ta juyo tanata murmushi, ganin su husna ak'ofar 6angarenta sai jikinta yay sanyi dan tasan ba alkairine ya kaisuba. Aiko,tanazuwa suka hau zaginta, Ikileema tace shegiya karuwa dangin tsiya, yanda uwarki ta mallake ubanki, taraba shi da kishiyarta, haka kikeso ki mallake mana miji, kirabamu dashi. Husna ta cafe haba ALLAH yakiyaye muzauna wanan 'yar yariyar ta mallake mana miji wallahi. Husna takawo mata duka, aida Munneerah da gudu ta fad'a palonta tarufe k'ofa tunkan su shigo, tana fad'in bazan zauna ku dakeni abanzaba wlh....... 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 51 «******» dadyne kwance akan doguwar kujerar dake palon sa, idanuwansa suna kallon sama da alama yayi nisa aduniyar tunanni, yakuma gyara kwanciyarsa sosai ya lumshe idanu, toshi yanzu minene fafita, dan shi gaskiya bayason takurama Munneerah saboda shi aganinsa tayi k'ank'anta. Kuma alissafinsa yaune takeyin wankan tsarki. Jin anturo k'ofa yasashi bud'e idanu, su husna ne kowacce tana huci, baice musu komaiba, sai dai idanunsa suna kansu, ikileema tace katashi wlh kayimata kashedi inhar tak'ara zagar mini uwa wallahi zamuyita badad'i nida ita. Husna tace oh ni dakika gaya min bak'ar magana ban kawo k'ararkiba saikece zaki kawo k'arata, ankawo d'in da uwarki, suka fara dambe, yana kwance yana kallonsu baice musu k'alaba. "Suna cikin danben Munneerah tashigo da sallama, hannunta f'auke da tiren abinci dady, ta ratse gefensu taje ta ajiye kan tebir d'in dake gefensa. Yatashi zaune yana mutmushi, saidai ita fuskar tata babu walwala, yaya dan ALLAH karabasu yazasuzo gabanka suna fad'a bazaka rabasuba? Yajawo file yana zuba abinci to ai bani nahad'asuba ko, bare kice, kema ai 'yar uwarsuce jeki rabasu. Yaja abincinsa ya hauci. Sukam su husna basugama shigowar Munneerah ba, sai cin uban juna sukeyi, can aka buga kan ikileema da bango jikake bumm, ta kwalla k'ara ta silale ta suma, Munneerah ta zaro ido, tana fad'in yaya ta kasheta, ta k'arasa wajanta da sauri, itakam husna tayi tsaye jikinta sai rawa yakeyi. Ko kallon inda suke baiyiba yanata saka lauma abinsa. Munneerah tace yaya please tana zubar da jini, sai asannan yad'ago yakalleta, yakuma maida kai kan filet d'in abincin sa, saikuma ya mik'e yanufi bedroom d'insa suka bishi da kallo, Munneerah tace dan ALLAH anty husna kawo ruwa ayayyafa mata, jiki narawa husna takawo ruwa, tayayya fa mata,ikileema ta kawo numfashi da k'arfi, dady yafito d'akinsa rik'e da jakkar aikinsa, yagyara mata wajan yabata magunguna, yace kowa tatafi b'angarenta bayason hayaniya, Munneerah tatai makawa ikileema zuwa b'angarenta. Sannan tadawo wajana dady dan gyara inda yaci abinci. Dagudu tak'araso ta kwace biron ✒hannunsa da takardu guda biyu, yaya mikakeson yine?? yakalleta da idanunsa dasukai ja, na b'acin rai, halin yarannan ya isheni haka gwara na sallamesu kowa takama gabanta. Kayi hakuri yaya bakyau saurin saki, kacigaba da yimusu addu'a watarana zasu bari insha ALLAH. Ya girgiza kai bakisan halin subane nikad'ai nasan wahalar danasha abaya tasu saida kikazo nasan mi'ake nufi da aure, amma da bansansaba, yafad'a wata 'yar kwalla na tararmasa agefen idanu. Munneerah tazauna gefensa tana share masa hawaye kayi hakuri yayana ALLAH yana tare damasu hak'uri. Yajawota jikinsa yarungume tsam, ki "soni" my beauty koda rabin son dane mikine ya zira harshensa cikin bakinta yana aikama ta da kyakykyawar sumba, itako jikinta sai rawa yakeyi, saida taji zai wuce gona da iri tafara kuka, yad'agota yarunge sorry my beauty, kaunarkice taimini yawa shiyyasa nakasa jurewa. Tadad'e a jikinsa alafe daga baya yad'agota yana share mata hawaye yakama hannunta suka nufi b'an garenta.......... 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 [1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳 🌷ko BIYAYYA🌷 Na billkisa ibrahim 📝📝 52 «*****» suna shiga yace taje tayi alwallah, jiki asan yaye ta nufi bedroom d'inta yabita da kallo yana wani d'an murmushi, Yabita abaya, tana fitowa shima yashiga yayo alwallan, sunyi salla raka'a biyu, yadafa kanta yay addu'a, yacigaba da kwararo musu addu' oi. Yatashi yafita yana cemata yana zuwa. Yana fita tasama bedroom d'inta key, dan ita kam yau lamarin nasa yabata tsoro. Tai shirin barci ta kwanta. Dady yadawo yarufe ko ina yakashe komai, yatab'a kofar gimbiyar tasa yaji gam, murmushi yayi yazaro wani key a aljihun wandon kayan barcinsa ya bud'e, tuni hantar cikin Munneerah ta kad'a, ya ajiye ledar hannunsa yana fad'in my beauty badai harkinyi barciba?? "Tai shiru kamar tayi barci, ya hawo gadon ya kwanta, ainasan yanda ake tada mai barci, yafara yimata wasu abubuwa, dasuka girmi tunaninta, tadai daure tak'i motsi, ai tanaji yana shirin cire mata riga, tai saurin tashi zaune, shima ya tashi yana dariya, my beauty kin tashi? "Tai k'asa da kai tana d'an murmushi yakuma jawota jikinsa, nidai danaga yau dady dagaske yakeyi, saiya mada beauty d'in tasa mace sosai, aituni na arto palo da guduna na bara🏃🏻🏃🏻🏃🏻🏃🏻. Amma daga falo inajiyo kukan Munneerah da kiran baffa harasu yaya sadiq, nace lallai yaufa antab'o sarakan raki su Munneerah. Saida komai yalafa nad'an lek'a, sainaga dady yana sharema Munneerah hawaye, dasaka mata albarka, yana kwararomata addu'oi. 🙊NARIK'E BAKI, INAFAD'IN YANZUNANFA DUK WADDA TA BADA DARAJARTA AWAJE BAZATASHA WANNAN ALBARKAR BA KO, DA KYAKYKYAWAR ADDU 'A, WAJEN MIJINTA BAFA KO, YAN UWANA MATA MUJI TSORON ALLAH, BAWAYEWA BACE "ZINA", BABBAR ASARAH CE GADIKKAN MACEN DATA ZUBAR DA MUTINCINTA AWAJE, BUDURCI WANI DARAJANE MAI ZAMAN KANSA, INKIN ZUBAR KINYI ASARA, ADUNIYARKI DA LAHIRARKI, AWAJEN MIJINKI DAN HAR TSUFANKU YANA KALLONKI DA WANNAN MUMMUNAN HALIN, ZAI RINKA ZARGINKI KUMA, A KODA YAUSHE, TO ZANCEN DAI BAYA KAREWA ALLAH DAI YA SHIRYAMU YASA MUGANE AMIN🙏🙏🙏. Ya lallab'ata yabata fresh milk, tasha kad'an tace tak'oshi, baita kurataba dan yasan ta wahalu, dukda yake likita baimata ta sauk'iba, yabata magani tasha da kyar, tana masa kukan shagwab'a, haka yayta lallashinta har barci ya kwasheta, yaja ajiyar zuciya yanama ALLAH godiya daya saka masa da mace tagari, Nima dai gida nadawo da safe nakoma d'akko muku rahoto kunji 'yan uwa,ALLAH yasa karna makara........... 09093044460 🌺billy🌺 🌹{Mrs Abdus'salam}🌹 🌳AUREN K'ADDARA🌳

Chapter 5 of 7