Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *BA NI DA HUJJA* By Zainab M Indian Girl Free page 1 “Wayyo Ashhh!”. Wata irin ƙara ya saki a lokacin da azaba ta ziyarci faratan ƙafarsa a yayin da ake azabtar da shi ta kowane nauyi na azaba, amma a ko da yaushe amsa ɗaya yake furtawa itace *BA NI DA HUJJA* wannan kalmar kuwa ita take baƙanta zuciyarsu da tunzurasu wajan cigaba da yi masa kowacce azaba a domin ya faɗi abin da suke son ji. “Yallaɓai ina jin fa sai mun aiwatar da punishment na gaba zai faɗa mana gaskiya”. Wani daga cikin 'yan sandan yai magana a yayin da gumi ke zubo masa saboda su kan su suma sun gaji da wannan abu. Ɗa yan Ya ce“Tabbas ina jin sai mun ke mataki na ƙarshe wanda idan har bai sanar da mu gaskiya ba to hukuncinsa kisa ne”. Wani irin sarawa kan sa ya yi, zuciyarsa ta buga jin abin da wannan ɗan sanda ya faɗa. “Miƙomin kayan aiki Kofur Sule”. Dan sandan da alamu ya nuna shi ne babba a cikinsu yai maganar yana watsa masa wani mugun kallo wanda yake nu ni zaka faɗi gaskiya ne. Cikin hanzari Kufur Sule ya nufi wajan kayan aiki domin cika umarnin. Innalillahi wa inna ilaihir raju'un. Azaba ce irin wadda tun da nake ban taɓa ganin irinta ba, izayar da ko a aikinsu bata bayar da izinin a yi wa mai lefi ita ba. Ɗaga kansa sama yai yana kallon silin rufin ɗan ƙaramin akurkin cell ɗin da yake ciki, idan yana kallon rayuwarsa ta baya da ta yanzu da yake ciki dai ya dinga ganin abin tamkar mafarki ne yake ba gaskiya ba, da ace ɗan adam yana iya sauya ƙaddararsa da tuni yayi ƙoƙarin sauyawa, da ace yana da dama gyara rayuwarsa ta baya da ya yi ƙoƙarin yin haka tare da cire wannan babbar musibar da yake ciki. Ina gatansa? Ina kuɗinsa? Ina taƙamarsa? Ina izzarsa? Ina mulkinsa? Ina jiji da kansa? Duk babu mafitar da zai kuɓuta daga azabar nan kawai yake nema. “Yallaɓai IG ya iso fa!”. Wani ya shigo da sauri ya faɗa masu. Wannan ne ya dawo da hankalina gare su domin ashe da na lula duniyar tunani ne. Asp saurin dakatar da yaransa daga abin da suke shirin aikatawa tare da kashewa daga wajan suka mayar suka aje. “Kai kuma za mu gamu next yanzu Allah ya kwace ka, ku kuma ku tashi muje”. Asp ya faɗa yana fice wa yaransa ma suka mara masa baya suna harararsa domin sun so a ce sun samu damar jiyar da shi roman wannan azaba da suka shirya. Wata kalar sassanyar ajiyar zuciya ya sauke yana mai furta “Alhamdulillah?” A can ƙasan laɓɓansa, ya lumshe ido yana tuna wani abu daga cikin rayuwarsa. **** *PLASH BACK* **** “Haba My Lovely Son ka tashi ka ji please Mommanka ce”. Hajiya Fatima kenan wadda ta kasance mata a wajan Alhaji Auwal Ashrab Soda shahararre kuma mai ji da duniya da kuɗi da mulki. Alhaji Auwal Ashrab Soda ya taka muƙamai na siyasa daban daban in da a halin yanzu yake tsaya a neman takarar zama shugaban ƙasar Nigeria baki ɗaya. A hankali ya muskuta daga makeken gadon da yake kwance yana kallon mahaifiyar ta sa ido a ƙanne yana ɗan cuno ɗan ƙaramin bakinsa. Hajiya Fatima tai 'yar dariya da Ce wa“Sorry ka ji My Lovely Son ka san bana son kana zama da yunwa shi yasa”. Cikin shagwaɓa kamar zai kuka Ya ce“Momma ba fa rana ce tai ba du dudu fa 12pm ne”. Ya ƙara she maganar yana kallon agogo. Hajiya Fatima Ta ce“Kai kuwa My Ashman rana ta yi mana, please oya tashi ka ji. Ai na ma ƙyale ka yau ban tashe ka da wuri ba”. Yana zumɓuro baki kamar ƙaramin yaro haka ya sauko daga bed ɗin. Hajiya Fatima ta miƙe tare da riƙo hannunsa Ta ce“Ka san irin son da nake maka kuwa My Ashman? Ƙaunar da nake maka Ubangiji na ne kawai ya san yawanta, hankalina ba zai kwanta ba idan ban ga ka yi breakfast ba”. Ya ɗan kwaɓe fuska irin na sangarta Ya ce“Momma to muje ki ɗan taimaka ki min alwala”. Murmushi Hajiya Fatima ta yi tare da amsawa da “To mu je”. Haka suka nufi toilet ɗin, a gabanta ya kama ruwa domin sam shi ba ya jin wata kunyar Momman na sa dan bai san ma wani abu wai shi kunya ba. Bayan ya kama ruwan ta zuba masa ruwa ya wanke, sannan tai masa brush da alwala suka fito. Ta shimfiɗa masa abin sallah ya yi ya idar sannan ta tashi suka nufi falo. Bayan sun isa wajan dinning tai sarving ɗin sa sannan ta shiga feeding ɗin sa yana wani tutture cokalin a haka har ya ɗan ci da yawa. Ajiyar zuciya Hajiya Fatima ta sauke tana yi masa murmushi Ta ce“Ma sha Allah”. “Momma ina Daddy ne?”. Murmushi Hajiya Fatima ta yi mai yalwa saboda jin an tambayi rabin ranta wato mijinta, Ta ce“Daddynka tun 7:00am ya fita saboda akwai wani zaman meeting da za su yi, ka san siyasa ta gabato shi yasa”. Ɗan taɓe baki Ashman ya yi da Ce wa“Ok”. Ya miƙe. Momma itama ta miƙe tana Ce wa“Sai ina kuma My Lovely Son?”. Ashman Ya ce“Momma zan ɗaki zan koma na shirya sannan na fita”. Addu'a tai masa sannan ya wuce itama ta koma ciki. Ko da ya koma ɗaki shiryawa yai cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na jeans masu kyau da tsada sannan ya ɗauko wasu sarƙoƙi ma gold masu tsada ya sanya a wuyansa tare da sauya barimar dake kunnasa ya yi matuƙar kyau abin ka da kyakykyawan. Ashman kyakykyawa ne na ƙarshen kwatance ko ta ina ya haɗu matuƙa ba ƙarya. Bayan ya gama shiryawa wata akwati ya buɗe ya ɗauki key ɗin mota da tarkacen wayoyinsa uku da ATM'S sannan ya fice. Da tafi sosai kafin a isa wajen aje motoci da cikin gidan hakan yasa idan zai fita yake sawa driver ya matso masa da mota zuwa saitin ɓangarensa ta yadda yana fitowa shiga zai yi. Bayan ya iso wajan matarsa ya shiga ya kunna ya nufi babban get, tun kan ya ƙara sa aka buɗe masa yana zuwa ya fice. ******** “No ban yi kyau ba”. Ta furta hakan a yayin da take tsaye gaban mirror tana kallon kanta, wata duguwar riga ce a jikinta me yankakken hannu an sa mata ado ta yi kyau amma ta ɗan bayyana sura. A hankali ta zame rigar ta nufi wardrobe ɗin ta shiga firfito da kaya, duk yawan kayanta wanda sun fi kala 200 amma da ƙyar ta iya samun wasu riga da sket milk and black, sun yi kyau sai dai da su da babu duk ɗaya ne. Ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta bayan kammala saka kayan kafin a hankali ta furta “Wow so cute dress”. Ta kammala shirinta ta nufi hanyar fita suka ci karo da Hajiya Saddiqa, Ta ce“Yawwa dama yanzu wajan ki zan zo na duba ki dan na ga yau ko ƙofa baki buɗe ba balle ki fito”. Cikin ƙosawa da shagwaɓa Ta ce“To Mommy yanzu ba ga shi na fito ba?”. Hajiya Saddiqa Ta ce“Amma Yusra sai ina yanzu?”. “Mommy! Haba na fa girma yanzu I'm 25 years, kin ga kuwa ai bai kamata ana tuhuma ta idan zan fita ba, kuma ba ai Daddyna yace ki dena yawan takura min”. A ƙagauce Yusra ke wannan maganar tana faɗa ta wuce za ta tafi. Hajiya Saddiqa ta sauke numfashi ba za tai mamaki ba domin halin 'yar tata dai addu'a gashi ta samu ɗaurin gindin mahaifi. Kafin ta samu damar magana Yusra har ta isa babban falo ta fice. “Allah ya kyauta” shi ne kawai abin da Hajiya Saddiqa ta iya faɗa ta wuce zuwa ɗakinta. ********Zaune yake cikin mota yana 'yan danne danne a waya time by time yana ɗaga kai yana kallon gidan dake gabansa. Ya ja wani dogon tsaki yana Ce wa“Sahail zai ɓata min time oh”. Rufe bakinsa ke da wuya sai ga Suhail ya filo daga gidansu yana ɗan waigawa da alama magana yake kafin ya nufo motar yana murmushi, yana zuwa ya buɗe ya shiga yana Ce wa“Sai da kai Dollars”. (Wannan suna ne da abokai ke kiransa da shi saboda ɓarin kuɗin da yake yi duk da a cikin abokan nasa babu 'ya'yan talakawa. “Mtsssss!” Ashman ya ja tsaki yana yi wa Suhail wani kallo. Dariya Suhail ya yi da Ce wa“Sorry! Sorry ka ji Dollars, ma fito zan tawo bayan ka kira ni ka iso shi ne Momcy ta tsai da ni”. Ashman bai ce komai ba ya ta da motar ya ja suka bar wajan. Naturally Good Life Club shi ne club ɗin da Ashman da sauran abokansa suka fi zuwa domin yanzu ma can suka nufa, parking yai bayan isowarsu, suka fito tare da nufar ciki. ********** Buga babban teburin Senator Sammani Kaita yayi ransa a matuƙar ɓace wanda bugun da yai wa tebur ɗin sai da tarkacen lemoku da ruwan da ke kai suka motsa. Cikin masifa da zafin zuciya yake magana da Ce wa“Ina wallahi ba zai yiwu ba, kenan ni na zauna na zama soko a cikin siyasa bayan da ni aka kafa jam'iyyar”. Wani dake kusa da shi ya taɓo shi da Ce wa“Nutsu mana Senator, kasan wannan tattaunawa ce kuma anan kowa zai san matsayarsa”. Senator Sammani Kaita ya kalle shi da Ce wa“Ai Honorable Isa idan har mutum ya san ya ido a wannan jami'a na ga ƙafa za ai masa”. Ajiyar zuciya wani kyakykyawan farin mutum mai cikar haiba da kwarjini ya sauke fuskarsa ɗauke da murmushi Ya ce“Haba mana Senator ka nutsu tukun a tattauna a san matsaya”. Hannu Senator ya ɗaga masa Ya ce“Ka ga dan Allah Alhaji Auwal Soda daka haka nan, so kake ni na zauna na zuba ido ina kallon siyasa na damawa babu ni, to bari ka ji a wannan gaɓa ba gudu ba ja baya a kujerar shugaban ƙasa nake so a tsayar da ni wannan karon sai dai kai haƙuri ka bar min!”. A fusace wani mutum dake zaune kusa da Alhaji Auwal Ashrab Soda ya miƙe yana watsawa Senator Sammani Kaita mugun kallo da Ce wa“Kana nufin kenan ta nan ka ɓullo? To bari ka ji kowa ya san takarar shugaban ƙasa a hannun Soda take dan haka ka cire buri a kanta!”. Nan fa teburin tattaunawar ya rikice da ƙananun maganganu kowa yana faɗar albarkacin bakinsa yayin da wasu ke goyan baya ga Alhaji Auwal Ashrab Soda wasu kuwa suna bayan Senator. Buga tebur ɗin da sugaban jam'iyya ya yi ne yasa kowa ya nutsu ya koma mazauninsa ya ya zauna. Shugaban jam'iyya Alhaji Idris Uba Dogo yai gyaran murya kafin ya fara magana “Alhaji Auwal Ashrab Soda shi ne wanda jam'iyya ta fitar ta ga cancanta da dacewar tsayawarsa a kujerar shugaban ƙasa, kai kuma Senator ai ba haka zaka zauna babu mulki ba kai ma za a sama maka wata kujerar ka tsaya takara da ita in ya so idan Allah ya nufa Alhaji Auwal ya kammala teluwar sa kai kuma sai a tsayar da kai”. “Ina! Ba zai yiwu ba wallahi shugaban jam'iyya, tun da na ta so a gidanmu babu wanda yake wuce ni sai dai ni na wuce anan ma ba zai yiwu na zama koma baya ba, tabbas wannan karan ni zan nasara dan haka daga yau na fita daga jam'iyyar (Z.L.M.F) Zaman Lafiya Muke Fata kowa ya gwada sa'ar sa mu gani”. Yana gama faɗar haka ya shiga tattara tarkacensa yana Ce wa“Wanda yake tare da ni ya biyo ni”. Yai gaba abin sa. Jikin Alhaji Auwal Ashrab Soda yai sanyi ganin abin da Senator ya aikata a duk domin sa, cikin ɗaga murya yake Ce wa“Senator Sammani Kaita dan Allah ka dawo a sasanta”. Ko juyowa bai yi ba balle ya tanka. Wasu daga ciki sun bi Senator amma ba du da yawa. Shugaban jam'iyya yai wani guntun murmushi kafin Ya ce“Na san hakan sai ta faru domin Senator so yake mu damƙa ragamar kula da ƙasar mu a hannunsa ya mayar da mu turɓaya”. Alhaji Auwal Ashrab Soda cikin san yin murya Ya ce“Yallaɓai a wannan karon zai yadda na koma baya a ɗora Senator akan wannan kujerar takara ni na haƙura”. Da mamaki jama'ar wajan suke kallonsa duk da sun san a cikin halinsa da ɗabi'unsa wannan ka ɗan ne, sam shi baya ƙaunar tashin hankali balle rigima kuma mulkinsa babu cuta babu zalunci shi yasa talakawa da al'umma baki ɗaya ke son sa da son kasancewar sa jagoran ƙasa. “Shugaban Jam'iyya…”. Ɗaga masa hannun da shugaban jam'iyya Alhaji Idris Uba Dogo yai ne ya sa yai shiru daga furta abin da ke bakinsa, Shugaban jam'iyya Ya ce“Matsayarmu ɗaya wato kai, dan haka babu gudu ba ka baya kai muka tsayar. Kowa ya cigaba da aikinsa domin in sha Allah nasara tamu ce”. Duk suka amsa da in sha Allah. Jikin ba ƙwari Alhaji Auwal Ashrab Soda ya miƙe ya nufi wajan motarsa domin ko da Alhaji Talle Sadau yake masa magana ce wa yai su yi waya kawai, yana isa wajan motar jami'an tsaron sa suka buɗe masa mota ya shiga sannan suka shiga na su sukar bar wajan. Wannan kenan. “Hhhhhhhh! Matsala ta da kai kenan ai”. Daga can ɓangaren Ya ce“Ba haka ba ne shugaba zuciyata ce ta kasa haƙuri shi yasa na fito masa a mutum”. Shugaban jam'iyya Ya ce“Shikenan dai ka cigaba da shiri ai idan ya san wata bai san wata ba”. Alhaji Sammani Kaita yai murmushi da Ce wa“Allah kuwa mutumina?”. “Allah kuwa kai dai ka zama a cikin shiri domin ba za a ce muna muƙami ba za mu mori shi ba, na tsani Alhaji Auwal saboda shegen tsoron Allahn sa da yai yawa amma ka ga idan kai ne ka ci shikenan sai fantamawa”. Shugaban jam'iyya ya faɗa muryarsa na nuni da tabbas yana cike da tsanar Alhaji Auwal kamar yadda ya faɗa. ************** *CIGABAN LABARI* ************** Har aka buɗe ƙofar cell ɗin da yake ciki bai san a buɗe ba sakamakon tunanin da zuciyarsa ta lula, sai da ya ji an ɗan bubbugi ƙafaɗarsa sannan ya dawo cikin hankalinsa a ɗan zabure yana kallon mutane da suka shigo cikin cell ɗin. 'Yan sandan wajan ne guda biyu sai wani mutum da bai san shi ba sanye da manyan kaya shadda ɗinkin riga da wando masu matuƙar kyau, da alama shekarunsa ba za su wuce 55 ba sakamakon yadda yana yinsa ya nuna. “Ina so ku ɗan ba ni waje daga ni sai shi”. Mutumin ya faɗa yana kallon 'yan sandan dake tare da shi. Ɗaya a ciki Ya ce“Barrister ba a barinsa da wani su ka ɗai sakamakon babban laifin da ya aikata”. Mutumin yai murmushi Ya ce“Ina son na keɓe daga ni sai shi ne saboda akwai tambayoyin da nake son yi masa kuma aikina ya ban wannan ikon”. Ɗayan Ya ce“Shikenan Barrister mun baka 10 - 15 minutes ka hanzarta”. Ɗaga musu kai kawai ya yi sannan suka fice. Mutumin ya gyara shugunan da yai yana mai zuba masa ido tare da yi masa kallon tsanake. Ya ce“Muhammad Auwal Ashrab wanda aka fi sani da Ashman ɗa ɗaya a wajan Alhaji Auwal Ashrab Soda wanda ya kasance matsayin shugaban ƙasa kuma marigayi a halin yanzu!”. Jikin Ashman ya sake mutuwa zuciyarsa ta karye hawaye suka ƙafe balle su zubo ya ji san yi a zuciyarsa. Barrister ya cigaba da Ce wa“Kamar yadda ka sani kuma nima na gani a shari'ar ka, ana zarginka ne da kashe mahaifinka Alhaji Auwal Ashrab Soda wanda sanadiyyar kashe shi da kai da ganin abin da ya faru ya sanya mahaifiyarka Hajiya Fatima shiga ruɗu tare da firgici wanda ta dinga kallonka a yayin da wuƙar da ka kashe mahaifinka take hannunka tana mai furta sai ta sanar da 'yan sanda, wannan ya sa itama ka kasheta ka bunne domin gudun samun hujja!”. Runtsewar da Ashman yai wa idanunta sai ka yi tunanin fashewar ƙwayar idanunsa a wannan hali, wannan kalamai suna bugun zuciyarsa numfashinsa na yi masa wasa a jikinsa ba tare da ya ɗauke ba ya buƙaci kusanci mutuwa a gare shi ba sai dai me *BA NI DA HUJJA* wanda za ta kawon ɗauki a rayuwa ta. *#WhatsApp Chat:-08143807733#* *BA NI DA HUJJA* By Zainab M Indian Girl Free page 2 ________________Shirun da yai hakan ya ba wa Barrister damar cigaba da magana, Ya ce“Ni sunana Barrister Muhammad Umar Mai Kano ni lauya ne me zaman kansa ba tare da taimakon kowa ba, ina so idan zaka amince kuma ka bani haɗin kai in taimake ka daga wannan halin da kake ciki”. Tun da yake magana zuba masa idanu kawai Ashman yai har ya kai aya bai ce uffan ba. Barrister Muhammad Umar Mai Kano Ya ce“Ina sauran ka me yasa ka kashe mahaifinka shugaban ƙasa Alhaji Auwal Ashrab Soda?”. Hawaye ne suka kawo masa agajin gaggawa a dai dai wannan lokaci wanda ba ɓata lokaci ya ba su damar sauka akan dakalin fuskarsa. Barrister Muhammad ya gama shiryawa domin ɗaukan bayani Ashman kawai yake jira ya ji me zai ce amma sai ya ji shiru har yanzu bai ce uffan ba. Barrister Muhammad Ya ce“Shurunka ba zai amfani ba sannan ba zai kawo mafita ba, amma idan ka yi ƙoƙarin ba ni wasu bayanai hakan zai ba ni ikon yin bincike yadda ya kamata”. Cikin karyayyar zuciya da murya mara ƙwarin gwiwa a cikinta tare da wasu ma'anoni masu wuyar fassaruwa Ashman Ya ce“Barrister a yanke min hukunci kawai dai dai da lefin da ake zargi na akai da gaske ni ne na kashe mahaifina Alhaji Auwal Ashrab Soda saboda ina so na maye gurbin kujerarsa a nawa tunanin amma sai dai kash an yi rashin sa a domin hasashe na bai zama dai dai ba!”. Wani guntun murmushi Barrister Muhammad Umar Mai Kano ya yi irin na ƙwararru kuma gogaggu a fagen sanin makamar aiki, Ya ce“Muhammad Ashman, kalamanka ya damar min da wata amsa wadda ina da yaƙinin cewa ba kai ne ka aikata wannan laifi ba”. “Me ce hujjar ka da zai baka tabbacin hakan, idan baka yadda cewar ni nai kisan ba wace hujja gare ka?”. Ɗan rubutu Barrister Muhammad Umar Mai Kano ya yi a cikin ɗan ƙaramin memo ɗin sa sannan ya ɗaga kai ya kalli Ashman kafin Ya ce“ *BA NI DA HUJJA* wadda zan kawo maka domin tabbatuwar hakan amma kai ne tsanin samun wannan hujja”. Ashman ya kyaɓe baki da Ce wa“Ni ɗin ma *BA NI DA HUJJA* tabbaci na baka shi cewar ni nai kisan”. Wata dariya Barrister yai wadda shi ne ka ɗai yake me dariyar take nufi. Shigowar ɗaya daga cikin 'yan sandan ɗazu yana Ce wa“Barrister lokacin da aka baka yayi har ya wuce”. Barrister Muhammad Umar Mai Kano Ya ce“Ohk, yanzu zan fito”. Dan sandan ya fice shi kuma Barrister ya haɗa kayansa a 'yar jakarsa ta aiki ya miƙe yana kallon Ashman Ya ce“Vary soon zan dawo”. Yana faɗar haka ya fice. Ɗan sandan ya rufe wajan ya juya. Ashman abu ɗaya ne yake cinsa a zuciya ba wai halin da yake ciki ba ne a a wannan yafi halin da yake ciki azaba a zuciyarsa. ************Tsaye take jikin kyauren ɗakin ta zuba mata ido tana kallonta wanda ita ba ta san ma wainar da ake toyawa ba domin ta lulu wata duniyar idanunta ne kawai ke zubda hawaye, a hankali ta ƙara sa cikin ɗakin tare da zama kusa da ita gefan tabarma tana mai riƙo hannunta. “Wallahi ba shi yai kisan ba sharri akai masa!”. Mamaki ya bayyana akan fuskarta jin abin da ta faɗa kamar ba ta cikin hayyacinta, cikin sanyi da taushin murya Ta ce“Ayrah waye ba shi yai kisan ba sharri akai masa? Ko mafarki kike?”. A wannan lokacin ne Ayrah ta dawo cikin hankalinta ya zuba wa mahaifiyarta idanu wanda suke cike da hawaye Ta ce“Umma ina da tabbacin ba zai iya kashe ko da ƙwaro ba ma balle rai, ran kuma wai na iyayensa ina ba zai yiwu ba!”. Ajiyar zuciya Umma ta sauke jin in da zan cen 'yar ta ta ya dosa, a hankali Ta ce“Ban da abin ki Ayrah har yau she ki ka san shi da zaki iya masa wannan shedar, kin san fa 'ya'yan masu kuɗin nan kuɗin iyayen kawai suke so ba iyayen na su ba; balle ma a ce ɗa a wajan shugaban ƙasa wanda ko rantsar da shi ba ai ba”. Girgiza kai Ayrah tai har yanzu ba ta fasa hawayen ba, Ta ce“Umma na san cewar sanin da nai wa Ashman ba zai yiwu ace na san hali da ɗabi'unsa ba, amma Umma farkon haɗuwata da shi da silar abin da ya haɗa ni da shi da kuma abin da ya maye gurbina da shi hakan ya sa na samu ƙwarin gwiwa na tabbacin ba zai iya aikatawa ba”. Umma Ta ce“Amma duk da haka Ayrah ba a shedar ɗan adam domin mutum mugun icce ne, ba da ban asirinsa ya tono ba da ba wanda zai yadda cewa ɗa zai iya kashe iyayensa”. Wani shashashan murmushi Ayrah ta yi tana duban Umma Ta ce“Wallahi Umma zan yi rantsuwar da babu kaffara a cikinta ba shi yai kisan nan ba, sannan Umma kin san ni

Chapter 1 of 4