ta mu, ba na tunanin samun kuɓuta daga cikin wannan halin da nake ciki dan haka ina roƙon ki da ki kyale a yanke hukunci!”. Jikin Barrister Salma ya yi sanyi sosai, tabbas maganar da Ashman ya faɗa gaskiya ce domin shugaban ninmu suna amfani da damar su wajan aiwatar da mummunan ƙudirinsu akan al'umma, amma duk da haka ai ba duka ne aka haɗu aka taru aka zama ɗaya ba, akwai masu tsoron Allah da gudun duniya a ciki. Ta sauke numfashi da Ce wa“Adalci yana wanzu ne daga adalin shuga, Ashman shugabanni ba duka ne suka taru suka zama ɗaya wajan cin amanar ƙasa da al'ummar cikin ta ba, dan Allah a karo na biyu ina so in sake roƙar ka da ka daure ka faɗan iya abin da ka sani a game da wannan kisa, hakan shi ne zai baka damar fita daga cikin zargi”. Ashman ya ji shigar zan tukan Barrister Salma har cikin zuciyarsa dan haka zai iya sanar da ita wani abu da ya sani a ciki, cikin raunin murya Ya ce“Abu ɗaya ne zuwa biyu zan sanar dake shi ne mahaifiyata ba ta mutu ba domin babu gawarta iya gawar mahaifina aka samu domin duk yadda akai mai kisan ya ɓoyeta ne, sai abu na biyu shi ne ina so ki je da kan ki kiyi bincike a game da mahaifina ba sai na faɗa miki komai ba, sai ƙarin wani abun shi ne a yau zan faɗa miki cewa ba ni na kashe mahaifina sannan kuma ba ni da hujjar da zata ba da tabbacin hakan!”. Mamaki sosai Barrister Salma ta shiga yi da jin kalaman Ashman, amma sai tai wani murmushi domin tana ganin ya amsa laifin ne domin su ƙyale shi. Dan haka sai Ta ce“Kana nufin akwai wani ɓoyayyan sirri game da mahaifinka? Sannan kuma ba ni hujjar da za ta tabbatar da cewa kai kai kisan!”. Ashman ya ɗago hannayensa duka biyu yana kallonsu kafin ya nuna mata su da Ce wa“Kin ga waɗan nan hannun sune tabbacin cewa ni nai kisan domin da su ne na kashe mahaifina sannan kuma wuƙar da na aikata hakan da ita tana hannun jam'i'ai kin ga kuwa hujjar ni nai kisan ta tabbata”. Dariya Barrister Salma ta yi domin ta fahimci Ashman kawai raina mata hankali yake, amma a hakan ma tana samun wasu bayanan. Ashman kuwa ganin dariyar da ya ga Barrister Salma ta yi yasa ya fahimci cewa kallon sa take a mashiririnci, da haka yai guntun murmushi da Ce wa“Ko da an kashe ni ki yi bincike”. Ba ta kai ga faɗar wani abu ba wani jam'i ya zo yace mata time ɗin da aka ba su ya cika, ta miƙe tana gyara zaman jakarta a kafaɗa Ta ce“Ina da tabbacin ba zaka mutu yanzu ba, sannan ko da ba mu sake haɗuwa yanzu ba akwai lokaci!”. Tana faɗar haka ta fice shi kuma jam'in ya rufe wajan ya tafi. A can kuwa gidan Alhaji Auwal Ashrab Soda Barrister Muhammad Umar Mai Kano ya lula cikin binciken da wannan bai samu wata ƙwaƙwƙwar hujja ba amma ya samu wani abu da ya ɗan rikita shi, sannan kuma ya ci karo da wata wasiƙa wadda ke barazana da rayuwarsa ga abin da wasiƙar ta ƙunsa ***"Barrister Mai Kano! Ka sani daga kai har 'yarka babu wata hujja ko tabbaci da zaku samu wanda zai iya kuɓutar da wanda kuke kare wa, sai dai ka sani ba a shiga gonata a fita haka ba tare da tsaraba ba. Idan har kana buƙatar wannan tsarabar to ka cigaba da shiga gona ta zaka samu gwagwgwaɓar tsaraba da zaka kai wa iyalanka, kuma ka sani wannan shari'a rikitacciya ce a wannan gaɓa ƙarshen ta ya zo sai dai ka sani za ta kuma tashi domin tamkar rai ne da ita. (B.L.K.C.B.A)"***** Wata irin zufa ce ta karyowa Barrister Muhammad ba wai dan ya jin tsoron barazanar ba kuma ya san dama zai yi wuya ace ba a bibiyarsu amma abin da ya ba shi mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne wannan haruffan na ƙarshe da ya gani a jikin wasiƙar *B.L.K.C.B.A* me hakan ke nufi?. Da haka dai ya baro gidan jiki a sanyaye. Ɓangaren Barrister Salma kuwa bayan fitowar daga wajan Ashman motar ta kai tsaye ta shiga amma me wani abu da ya ɗaure mata kai ya kuma ba ta mamaki shi ne wata 'yar akwati da ta samu a cikin motar a gefen zaman driver, ta tabbatar da cewa motar ta a kulle take da key sannan glass ɗin motar shima yana rufe babu ta in da za a iya saka wannan akwati. “To ta ya ya akai haka? Hakan yana nuni da cewar ana biye da ni kenan?”. Barrister Salma ta faɗi haka a fili da mamaki a muryarta. A hankali ta sa hannu ta ɗauki akwatin wadda akai wa decoration mai kyau ta shiga buɗe wa, amma buɗewar da za tai tai wurgi da ita gefe cike da tsoro da mamaki tana zazzare idanu sakamakon abin da ta ci karo da shi a cikin akwatin…✍️
*#08143907733#*
*BA NI DA HUJJA 6 08143907733*
_______________“Ina ba zai yiwu ba, ta ya hakan za ta kasance?”. Barrister Salma tai maganar tana mai sake ɗaukar akwatin tare da ganin abin dake ciki a karo na biyu, ta sauke wani gwauron numfashi kafin idanunta ya sauka akan wata takarda dake nannaɗe. Ta sa hannu ta ɗauka tare da buɗe wa ta fara karantawa *"Ke ɗin kin kasance kyakykyawa ce amma gashi kina ƙoƙarin shiga gona ta tare da bankaɗo wani sirri wanda zai girgiza al'umma, kar ki sake ki yi wa wannan kyau naki illa ta hanyar jefa kan ki cikin rami mai zurfin da baya da iyaka. A shawarce ki dakata da wannan bincke idan ba haka ba akwai tukwici, fatan saƙon da idanunki suka gani bai girgiza ki ba?"* Ta ƙare karanta saƙon da hurar da iskar bakinta tana mai furta “Waye shi wane wannan shaɗanin?”. Ba ta da amsar tambayoyinta dan haka jiki ba ƙwari ta ja motar ta ta bar gidan yarin.
Wannan kenan.
Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi ya rikice gaba ɗaya ko ta ina mafita yake nema 'yan mata kuwa bai san yawan waɗan da ya farke ba sakamakon neman yarinyar da har yanzu taƙi bayyana a gare shi, ya kai wa glass ɗin tebur wanda ke ɗauko da tarkacen lemoku akai, take glass ɗin ya fashe hannunsa ya shiga zubda jini sakamakon sokarsa da kulba tai. Ya ɗan runtse ido tare da sakin 'yar ƙara. Hajiya Karima ce ta shigo falon da sauri ta ƙara sa ganin abin da yake faruwa da mijinta, ta riƙo hannun tana Ce wa“Subhanallahi Senator mene haka?”. Kallon gefe yai kawai kafin Ya ce“Ki taimaka min kawai”. Ta saki hannun tare da juyawa ta koma ciki dan ɗauko akwatin agaji domin ita ɗin malamar asibiti ce. Bayan ta dawo ta shiga treatment ɗin ciwon da ya ji, bayan ta kammala ta kira 'yar aiki domin gyara wajan. Ta samu waje kusa da shi ta zauna cikin taushin murya Ta ce“Senator mene yake damunka da har zaka iya illata kan ka?”. Senator Sammani ya juyo ya kalli Hajiya Karima da Ce wa“Ina daf da rasa duk wani farin cikina a wannan kwanakin Hajiya, Yau saura kwana biyu a koma kotu kuma idan an koma ba na tunanin wannan shari'a za ta kuma ɗaga wa ba tare da an yanke hukunci ba”. Hajiya Karima da mamaki Ta ce“To Senator kai mene damuwarka da hakan, ko da ace yaron nan bai aikata laifin ba ba ya da wata hujja da za ta kuɓutar da shi, addu'a ya kamata kawai kai masa”. Wani kallo Senator ya watsa mata kafin Ya ce“Ni ba damuwata yaron nan ba koma mene za ai masa bai shafe ni ba, siyasa ta ita nake dubawa kawai!”. Cikin mamaki Hajiya Karima Ta ce“Kenan baka damu da abin da ya samu amininka da ɗan sa ba?”. “Kin ga! Kin ga da halla kar ki ɓata min rai mana, amini! Amini!! Alhaji Auwal ai ba aminin arziƙi ba ne da zan wani damu da matsalarsa da aminin gaskiya ne ai da tun tuni zai sallama min mulki shi ma da yanzu haka yana duniya!”. Jinjina kai Hajiya Karima tai cikin mamakin mijin na ta Ta ce“Amma wallahi ka ba ni mamaki Alhaji a ce mutum ba ya da zuciyar imani ko ka ɗan! Na san da a ce…!”. Tsawar da Senator Sammani ya daka mata ce yasa ta yin shiru ba shiri, cikin masifa da ɓacin rai Ya ce“Tashi ki fice min a falo bana son na sake ganinki daga nan har a rantsar da ni, tun da ke ba kya so na da arziƙi”. Za tai magana ya sake dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. Haka ta miƙe ta nufi hanyar fita jiki ba ƙwari domin ta fara gajiya da halin mijin na ta, a hanyar fitowarta ta haɗu da Najma wadda ke shirin shiga. Najma sanye cikin riga da wando 3 quarter ta zubo gashinta babu ɗankwali. “Yawwa Mammy Daddy fa?”. Galla mata harara tai kafin Ta ce“Ban sani ba, shashasha me halin uba”. Tana faɗar haka ta wuce. Najma ta taɓe baki da Ce wa“Ita kuma Mammy ko me akai mata oho, me halin uba”. Ta kwaikwayi maganar Mammyn kafin kuma Ta ce“Ko wane hali ne da Daddyn nawa da zata dinga cewa wani me halin uba duk san da nai wani abu? Oho ma dai ita ta jiyo”. Ta ƙara sa maganar da shigewa ciki. Shi kuwa Senator sababi ya shiga yi bayan fitar Hajiya Karima. Najma ta ƙara in da yake tare da faɗa wa jikinsa Ta ce“Daddy lafiya na ji kana ta faɗa? Hala kai dai Mammy ne ko?”. Senator ya sassauta fuskar sa zuwa dariya domin duk ɓacin ran da yake ciki da zarar ya ga 'yar ta sa sai ya ji ya gushe saboda bala'in sonta da yake dan itace ta ɗauko komai na daga halinsa shi yasa yake ji da ita. Ya ce“Rayuwata ai kema kin san dama Mammyn ki ce”. Taɓe baki Najma tai da Ce wa“Ka ga Daddy ƙyale wannan Mammyn ka ji, ita komai faɗa ko wa'azi”. Senator yai dariya da Ce wa“Sai kace ta fi kowa sanin Allah da tsoronsa, yanzu My Life me kike so ne?”. Najma ta ɗan kwaɓe fuska Ta ce“Daddy za mu yi wata haɗaɗɗiyar dinner ne kuma nice star a wajan dinner”. Senator Ya ce“To yanzu me kike so a yi?”. Najma Ta ce“Daddy 10 millions nake so ka ban zan malegi saboda na san yanzu ba kuɗi ne da kai ba”. Senator Ya ce“Tabbas kuwa My Life, amma yanzu ban da kuɗi sosai a hannu gashi kuma kin ga ana hidimar siyasa dan haka zan baki 5.m”. “Kai, Daddy Allah kuwa ba za ta isa ko rigar da zan sa ta siya min ba”. Najma tai maganar a shagwaɓe kamar za tai kuka. Senator cikin rarrashi Ya ce“Sorry! Sorry My Life zan tura miki 10.m ko da kuwa za a ranto ne dan kin san ban son ɓacin ran ki”. Najma tai dariya Ta ce“Yawwa My Lovely Dad”. Ta sakar masa kiss a goshi shi ma ya mayar mata. Sannan Ya ce“Yanzu ki je zan tura miki ta account ɗin ki”. Ta amsa sannan ta juya ta fice tana tsalle tsallen murna. Senator ya bi ta da kallo cike da so da ƙauna.
*****
Zaune take akan tabarma gabanta kuma kwanon abinci ne tuwan shinkafa miyar kuka ya ji man shanu da yajin daddawa, hannunta na ciki tana ci. Ta ɗebo loma za ta kai baki Umma ta katse ta da Ce wa“Amma Ayrah mene shirin da kike akan wannan al'amari?”. Ayrah ta mayar da lomar da ta ɗebo cikin kwanon sannan tai murmushi Ta ce“Ai Umma wannan ɗin sirri ne ke dai kawai ki zuba ido”. Umma ta jinjina kai Ta ce“Abin da ya sa nai miki wannan tambaya shi ne na ga saura kwana biyu ya rage a koma zaman kotu?”. Dariya Ayrah tai mai ɗan sauti kafin Ta ce“Kuma in sha Allah a gobe al'amari zai sauya kafin ranar kotu komai ya zama labari!”. Umma da mamaki Ta ce“Ta ina komai zai zama labari kullum kina zaune a gida ban ga kina wani yunƙuri ba”. Ayrah maganar Umma ta ba ta dariya, sai da tai dariyar sannan Ta ce“Ina shiri mana kuma ga dukkan alamu shirina yana tafiya yadda nake so kuma ina ganin alamun nasara, ni kuma daga yau nawa zai fara!”. Umma cikin sanyi Ta ce“To Allah dai ya tsare ya kuma shige mana gaba”. Ayrah ta amsa da “Ameen”.
https://chat.whatsapp.com/BeEdSOYVSSr2bstxdbuft6
*BA NI DA HUJJA 7 08143907733*
_Saura 4 pages mu gama free page littafin fa haɗaɗɗene ba sai na faɗa ba, Ga masu son fara payment za su iya tura wa ta wannan account ɗin Naira ₦500 ne kacal_
*9039220854*
*Zainab Abubakar Umar*
*Opay*
*Ko*
*5053077402*
*Zainab Abubakar Umar*
*Moniepoint*
*Sai a turo shaidar biya ta number dake sama*
_______________“Ina ba zai yiwu ba, ta ya hakan za ta kasance?”. Barrister Salma tai maganar tana mai sake ɗaukar akwatin tare da ganin abin dake ciki a karo na biyu, ta sauke wani gwauron numfashi kafin idanunta ya sauka akan wata takarda dake nannaɗe. Ta sa hannu ta ɗauka tare da buɗe wa ta fara karantawa *"Ke ɗin kin kasance kyakykyawa ce amma gashi kina ƙoƙarin shiga gona ta tare da bankaɗo wani sirri wanda zai girgiza al'umma, kar ki sake ki yi wa wannan kyau naki illa ta hanyar jefa kan ki cikin rami mai zurfin da baya da iyaka. A shawarce ki dakata da wannan bincke idan ba haka ba akwai tukwici, fatan saƙon da idanunki suka gani bai girgiza ki ba?"* Ta ƙare karanta saƙon da hurar da iskar bakinta tana mai furta “Waye shi wane wannan shaɗanin?”. Ba ta da amsar tambayoyinta dan haka jiki ba ƙwari ta ja motar ta ta bar gidan yarin.
Wannan kenan.
Gaba ɗaya hankalinsa ya tashi ya rikice gaba ɗaya ko ta ina mafita yake nema 'yan mata kuwa bai san yawan waɗan da ya farke ba sakamakon neman yarinyar da har yanzu taƙi bayyana a gare shi, ya kai wa glass ɗin tebur wanda ke ɗauko da tarkacen lemoku akai, take glass ɗin ya fashe hannunsa ya shiga zubda jini sakamakon sokarsa da kulba tai. Ya ɗan runtse ido tare da sakin 'yar ƙara. Hajiya Karima ce ta shigo falon da sauri ta ƙara sa ganin abin da yake faruwa da mijinta, ta riƙo hannun tana Ce wa“Subhanallahi Senator mene haka?”. Kallon gefe yai kawai kafin Ya ce“Ki taimaka min kawai”. Ta saki hannun tare da juyawa ta koma ciki dan ɗauko akwatin agaji domin ita ɗin malamar asibiti ce. Bayan ta dawo ta shiga treatment ɗin ciwon da ya ji, bayan ta kammala ta kira 'yar aiki domin gyara wajan. Ta samu waje kusa da shi ta zauna cikin taushin murya Ta ce“Senator mene yake damunka da har zaka iya illata kan ka?”. Senator Sammani ya juyo ya kalli Hajiya Karima da Ce wa“Ina daf da rasa duk wani farin cikina a wannan kwanakin Hajiya, Yau saura kwana biyu a koma kotu kuma idan an koma ba na tunanin wannan shari'a za ta kuma ɗaga wa ba tare da an yanke hukunci ba”. Hajiya Karima da mamaki Ta ce“To Senator kai mene damuwarka da hakan, ko da ace yaron nan bai aikata laifin ba ba ya da wata hujja da za ta kuɓutar da shi, addu'a ya kamata kawai kai masa”. Wani kallo Senator ya watsa mata kafin Ya ce“Ni ba damuwata yaron nan ba koma mene za ai masa bai shafe ni ba, siyasa ta ita nake dubawa kawai!”. Cikin mamaki Hajiya Karima Ta ce“Kenan baka damu da abin da ya samu amininka da ɗan sa ba?”. “Kin ga! Kin ga da halla kar ki ɓata min rai mana, amini! Amini!! Alhaji Auwal ai ba aminin arziƙi ba ne da zan wani damu da matsalarsa da aminin gaskiya ne ai da tun tuni zai sallama min mulki shi ma da yanzu haka yana duniya!”. Jinjina kai Hajiya Karima tai cikin mamakin mijin na ta Ta ce“Amma wallahi ka ba ni mamaki Alhaji a ce mutum ba ya da zuciyar imani ko ka ɗan! Na san da a ce…!”. Tsawar da Senator Sammani ya daka mata ce yasa ta yin shiru ba shiri, cikin masifa da ɓacin rai Ya ce“Tashi ki fice min a falo bana son na sake ganinki daga nan har a rantsar da ni, tun da ke ba kya so na da arziƙi”. Za tai magana ya sake dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. Haka ta miƙe ta nufi hanyar fita jiki ba ƙwari domin ta fara gajiya da halin mijin na ta, a hanyar fitowarta ta haɗu da Najma wadda ke shirin shiga. Najma sanye cikin riga da wando 3 quarter ta zubo gashinta babu ɗankwali. “Yawwa Mammy Daddy fa?”. Galla mata harara tai kafin Ta ce“Ban sani ba, shashasha me halin uba”. Tana faɗar haka ta wuce. Najma ta taɓe baki da Ce wa“Ita kuma Mammy ko me akai mata oho, me halin uba”. Ta kwaikwayi maganar Mammyn kafin kuma Ta ce“Ko wane hali ne da Daddyn nawa da zata dinga cewa wani me halin uba duk san da nai wani abu? Oho ma dai ita ta jiyo”. Ta ƙara sa maganar da shigewa ciki. Shi kuwa Senator sababi ya shiga yi bayan fitar Hajiya Karima. Najma ta ƙara in da yake tare da faɗa wa jikinsa Ta ce“Daddy lafiya na ji kana ta faɗa? Hala kai dai Mammy ne ko?”. Senator ya sassauta fuskar sa zuwa dariya domin duk ɓacin ran da yake ciki da zarar ya ga 'yar ta sa sai ya ji ya gushe saboda bala'in sonta da yake dan itace ta ɗauko komai na daga halinsa shi yasa yake ji da ita. Ya ce“Rayuwata ai kema kin san dama Mammyn ki ce”. Taɓe baki Najma tai da Ce wa“Ka ga Daddy ƙyale wannan Mammyn ka ji, ita komai faɗa ko wa'azi”. Senator yai dariya da Ce wa“Sai kace ta fi kowa sanin Allah da tsoronsa, yanzu My Life me kike so ne?”. Najma ta ɗan kwaɓe fuska Ta ce“Daddy za mu yi wata haɗaɗɗiyar dinner ne kuma nice star a wajan dinner”. Senator Ya ce“To yanzu me kike so a yi?”. Najma Ta ce“Daddy 10 millions nake so ka ban zan malegi saboda na san yanzu ba kuɗi ne da kai ba”. Senator Ya ce“Tabbas kuwa My Life, amma yanzu ban da kuɗi sosai a hannu gashi kuma kin ga ana hidimar siyasa dan haka zan baki 5.m”. “Kai, Daddy Allah kuwa ba za ta isa ko rigar da zan sa ta siya min ba”. Najma tai maganar a shagwaɓe kamar za tai kuka. Senator cikin rarrashi Ya ce“Sorry! Sorry My Life zan tura miki 10.m ko da kuwa za a ranto ne dan kin san ban son ɓacin ran ki”. Najma tai dariya Ta ce“Yawwa My Lovely Dad”. Ta sakar masa kiss a goshi shi ma ya mayar mata. Sannan Ya ce“Yanzu ki je zan tura miki ta account ɗin ki”. Ta amsa sannan ta juya ta fice tana tsalle tsallen murna. Senator ya bi ta da kallo cike da so da ƙauna.
*****
Zaune take akan tabarma gabanta kuma kwanon abinci ne tuwan shinkafa miyar kuka ya ji man shanu da yajin daddawa, hannunta na ciki tana ci. Ta ɗebo loma za ta kai baki Umma ta katse ta da Ce wa“Amma Ayrah mene shirin da kike akan wannan al'amari?”. Ayrah ta mayar da lomar da ta ɗebo cikin kwanon sannan tai murmushi Ta ce“Ai Umma wannan ɗin sirri ne ke dai kawai ki zuba ido”. Umma ta jinjina kai Ta ce“Abin da ya sa nai miki wannan tambaya shi ne na ga saura kwana biyu ya rage a koma zaman kotu?”. Dariya Ayrah tai mai ɗan sauti kafin Ta ce“Kuma in sha Allah a gobe al'amari zai sauya kafin ranar kotu komai ya zama labari!”. Umma da mamaki Ta ce“Ta ina komai zai zama labari kullum kina zaune a gida ban ga kina wani yunƙuri ba”. Ayrah maganar Umma ta ba ta dariya, sai da tai dariyar sannan Ta ce“Ina shiri mana kuma ga dukkan alamu shirina yana tafiya yadda nake so kuma ina ganin alamun nasara, ni kuma daga yau nawa zai fara!”. Umma cikin sanyi Ta ce“To Allah dai ya tsare ya kuma shige mana gaba”. Ayrah ta amsa da “Ameen”. Sannan ta cigaba da cin tuwanta.
****
“Daddy akwai matsala fa babba!”. Barrister Salma tai maganar tana kallon mahaifinta Barrister Muhammad wanda ke zaune akan kujerar sa a office. Ya ce“Wace kalar matsala ce?”. Barrister Salma ta samu kujera ta zauna kafin Ta ce“A yanzu ba wai neman hanyar kuɓutar da Ashman ba ce mafitar mu akwai wani babban sirri”. Jikin Barrister Muhammad yai luɓus, Ya ce“Wane kalar sirri ne wannan”. Bai bari ta san cewa shima ya fara fahimtar wani a bu daban ba. Barrister Salma nan ta faɗa masa komai da komai amma ban da abin da ta gani cikin akwati wanda wannan ta bar wa kanta a matsayin sirri kuma za tai gwagwarmaya akan sa. Ajiyar zuciya Barrister Muhammad ya yi mai ƙarfi kafin Ya ce“Kice akwai gagarumar matsala a gaba, yanzu mene mafita?”. “Zuba idon tsammani, domin ganin abin da zai faru daga nan zuwa gobe”. Barrister Salma ta faɗa. Barrister Muhammad zai magana ƙarar shigowar saƙo wayarsa ya katse shi daga maganar tare da ɗaukar wayar yana duba wa, wani irin shock ya ji tare da miƙe wa a firgice yana zazzare idanu wanda ya sa itama Barrister Salma shiga kalar yana yin da mahaifin na ta ya shiga domin ba ta san mene ya san ya shi wannan yana yin ba.
*********
Sauri yake har ya na tuntuɓe ya isa motarsa ya shiga yana mai ɗaga murya yana bawa Najma amsa akan abin da take ce masa. Ya ce“My Life ki bari zan tura miki yanzu ina wani uzuri ne”. Bai jira cewar ta ba yai wa motar key ya fice ba tare da neman rakiyar wani daga cikin bodyguards ɗin sa ba. Najma ta zumɓuri baki kamar za tai kuka tai cikin gida. Hajiya Karima dake saukowa daga steps ɗin bene da idanu kawai ta bi Najma tare da taɓe baki, har Najma ta ɗan gota za ta wuce kome ta tuna sai ta dawo ta bi bayan Hajiya Karima har falo ta zauna ita kuma ta jingina jikin kujerar da ta zauna ɗin tare da ɗora kanta bisa ƙafafunta. Jin hakan da Najma tai yasa Hajiya Karima fahimtar akwai abin da take so dan ba ta zuwa in da take haka sakitan sai da buƙata. Cikin langwaɓewa da muryar tausayi Ta ce“Dan Allah Mammy alfarma nake nema”. Hajiya Karima Ta ce“To ɗiyar Daddynta wace kalar alfarma kuma nake da ita da zan miki?”. Najma Ta ce“Dan Allah Mammy ki ara kin 10.m kafin Daddy ya tura min za mu yi dinner ne kuma siyya za mu ni ka ɗai ake…”. Tsawar da Hajiya Karima ta daka mata ce ta sa jikinta ɗaukar rawa ta matsa gefe tana kallonta idanu a tsora ce. Hajiya Karima cikin faɗa Ta ce“Ina Najma!”. Cikin rawar murya Najma Ta ce“Ga…ga…gani Mammy”. Hajiya Karima ta runtse ido kafin Ta ce“Kafin na irga uku na buɗe idona ki ɓacen a gani”. Ai Hajiya Karima ba ta san tana fara rufe ido Najma ta wafce ɗaki a guje saboda ta tsorota da yana yin Mammyn tata. Hajiya Karima Ta ce“Shashashar yarinya kawai,
wallahi daga ke har mahaifin naki za ku da na sani ne wanda bai da amfani”.
*****
“Haba! Haba Ahmad kar ka damu gani nan na kusa ƙara sowa”. Daga can ɓangaren Ahmad Ya ce“To yallaɓai yarinyar ce take ta damuna”. “Ta jira! Ta jira!! Ga ni nan na ma iso gidan gonar”. Yana faɗar haka yai parking tare da kashe motar ya cire key ya fito ya nufi ciki. Tun da ya shiga gabansa ya yanke ya faɗi zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da saurin numfashinsa ya shiga barazanar rabuwa da jikinsa…
*Mu haɗu next amma ku yi payment