Share this page
4 / 4
fa kar a bar ku a ba ya fa🙄** https://chat.whatsapp.com/BeEdSOYVSSr2bstxdbuft6 *BA NI DA HUJJA 8 08143907733* *Marubuciya Zainab Muhammad Indian Girl* _Saura 2 pages mu gama free page littafin fa haɗaɗɗene ba sai na faɗa ba, Ga masu son fara payment za su iya tura wa ta wannan account ɗin Naira ₦300 ne kacal_ *5053077402* *Zainab Abubakar Umar* *Moniepoint* *Sai a turo shaidar biya ta number dake sama* _______________Yarinyar tana zaune akan kujera sanye da dogon hijab har ƙasa yayin da fuskarta ke lulluɓe cikin niƙab fararan idanuwanta masu matuƙar kyau da ɗaukan hankali masu ɗauke da kyakkyawar kwayar ido mai shanning sai zararan gashin ido wanda ya ƙara wa idanun kyau, duk da ba fuskarta Senator ya ga ni ba amma jikinsa ya ji ya mutu lokacin da idanunsa suka sauka a kanta, jiki ba ƙwari ya ƙara sa cikin falon tare da zama yana mai zuba mata idanu, bai san mene ya sa yake jin wani irin yana yi ba a game da ita. Amma ganin ba amfanin wani tunani a halin yanzu ya sa ya mai da kallonsa ga Ahmad Shasha kafin Ya ce“Shasha itace wannan?”. Ahmad Shasha yai dariya irin ta riƙaƙƙun 'yan bariki kafin Ya ce“Eh ranka ya daɗe, ga tanan tamkar tuffa ko ɗawisu!”. Senator Sammani Ya ce“To ai ba ta buɗe fuskarta ba gashi ma kuma ta saka ƙaton jikab”. Ahmad Shasha Ya ce“Ai ranka ya daɗe tace ita haka tsarin ta yake ba wanda yake ganinta sai wanda za su ƙalla harƙalla tare dan haka nima nan da ka ganni ko kamnninta ban sani ba”. Duk da sauyin yana yin da Senator yake ji a jikinsa hakan bai hana shi Ce wa“To amma Ahmad ina ka samo ta?”. “Ba samota nai ba itace nan ta samo ni, sauran zan ce gaka ga tanan na bar ku lafiya”. Ahmad Shasha ya faɗa yana bin hanya ya fice. Ajiyar zuciya Senator ya sauke kafin Ya ce“To yarinya hanzarta mu yi abin da ya kawo mu domin ina da uzuri”. Wani irin murmushi ta yi da Ce wa“Baka da wani uzuri idan har kana tare da ni domin ni zan saka kuma zan hana ka”. Mamaki ya kama Senator kafin Ya ce“Amma yarinya saboda me kika ce haka?”. Tai dariya tare da ta so wa ta nufo in da yake ta tsaya gabansa still fuskarta a rufe Ta ce“Saboda ni nake da mulkin ka a hannu, bin umarni na da yin biyayya a garan shi ne cikar burinka”. A zabure Senator ya miƙe yana nuna ta da mamaki kafin ya iya Ce wa“Amma ke ɗin wace ce kuma mene hujjarki wadda zan tabbatar da cewa kece wadda nake nema?”. Ta zauna hannun kujerar da yake zaune tare da zuba masa idanu wanda shi ma kallonta yake amma cike da tsoro da mamaki. Ta ce“Hujjar da zaka yadda cewar nice wadda kake nema ta na cikin abin da zan saka a yanzu”. Gaban Senator ya buga tun kafin ma ya ji mene abin da za ta faɗa ya fara yadda a zuciyarsa cewa wannan itace yarinyar, cikin zaƙuwa da son jin me zata ce, Ya ce“Mene buƙatar ki? Faɗi ko mene zan biya miki ita domin biyan tawar buƙatar”. Yarinyar ta miƙe tare da yin taku ɗaya zuwa biyu kafin ta tsaya ba tare da ta kalle shi ba Ta ce“Ina so ka kuɓutar da Ashman daga wannan prison ɗin sannan a ranar da za a shiga kotu ka tabbatar da cewa an yi yadda za ai domin wanke shi daga wannan lefin, wannan ka ɗai shi ne zai baka damar cikar naka burin”. Tun da ta fara magana gumi ke keto masa, cikin ƙarfin hali Ya ce“Ta ina zan iya hakan bayan ba ni na aikata kisan kan ba kuma ba na da masani akan wanda ya kashe? Sannan wace hanya zan bi dan faruwar hakan?”. Ta yi wata shashashar dariya wadda ta ƙara sanyaya jikin Senator Ta ce“Ta yadda zaka iya komai domin ganin ka samu mulkin ka, ba zan baka haɗin kai ba har sai na ji wani labari daga nan zuwa gobe sannan zan zo maka domin ka cika naka burin”. Tana faɗar haka ta juya zata fice. Sa sauri Senator ya bi bayanta yana Ce wa“Amma ta ya zan sake ganinki idan kika tafi?”. “Ta yadda nai na zo ba tare da ka sani ba hakan zan yi da zarar ka aikata abin da na ɓukata”. Ta faɗa kafin ta fice da sauri, bai fi mintuna biyu da fitar ta ba Senator ya bita a guje amma sama ko ƙasa ya nemi ko da sahunta ya rasa wanda hakan ya ƙara sanyaya jikinsa yake tunanin ko dai aljanna ce, “mma ai malam yace ba aljanna ba ce tana dai da wani ɓoyayyan sirri”. Ya yi maganar a fili, jiki ba ƙwari ya koma ciki. Tunani kala kala ne suka cika masa kwanya, yanzu ta ina kenan zai fara dan ganin ya kuɓutar da Ashman?. Wani abu ya tuna sai kawai ya saki murmushi tare da ɗaukan wayarsa ya yi kiran wata number, ring ɗaya tai aka ɗaga daga can ɓangaren aka ce. “Sai me gida, idan kaga kira ta samu!”. “Busha kana ina ne yanzu?”. Senator ya faɗa cikin zaƙuwa. Busha Ya ce“Wa? Ai mu me gida bama gida ɗaya”. Senator Ya ce“Shikenan du ba wannan ba, ina son ganinka a yau!”. Busha Ya ce“Huh! Me gida a yau, eh to ba za a ƙi taka ba zan shigo ɗin”. Senator Ya ce“Yawwa Busha, sai na jika in da muke haɗu”. “Sai mai gida”. Busha ya faɗa tare da kashe wayar. Senator ya sauke ajiyar zuciya sannan Ya ce“Next, an gama da wannan”. Wata number ya kira bugu ɗaya biyu aka ɗaga. Daga can ɓangaren shugaban jam'iyya Alhaji Idris Uba Dogo Ya ce“Shigaban ƙasa namu, yau ina ka shige ne?”. Senator yai ajiyar zuciya Ya ce“Yau ina cikin wata masifa ne?”. Da mamaki Shugaban jam'iyya Idris Uba Dogo ya tambayi Senator da Ce wa“Ban gane kana cikin matsala ba, dama Senator akwai matsalar da take iya damunka?”. Senator Ya ce“Ba zaka gane ba ne shugaban jam'iyya akwai matsala a ciki”. “Faɗa min mene?”. Shugaban jam'iyya ya tambaya. Senator Ya ce“Ka san dai burinmu bai wuce muga an mai do da mulkin nan kanmu ba ko? A lokacin da akai zaɓe daga Alhaji Auwal a waɗan da suka fi yawan ƙuri'u sai nice dan haka muke sa ran dawowar mulki a hannunmu. Dai dai wani hanzari ba gudu ba”. Shugaban jam'iyya Ya ce“Tabbas wannan ne fatan domin duk yadda aka shirya plan ya tafi dai dai abu ɗaya ne saɓa ni a ciki shi ne kisan da akai wanda ba mu da masaniya akai, amma mece matsalar?”. Senator Ya ce“Matsalarmu shi ne Ashman!”. “Ashman kuma? Ta ya Ashman zai zama matsalarmu ba yan yana kulle kuma sa ran da ake ma za a yanke masa hukuncin kisa!”. Shugaban jam'iyya yai maganar da matuƙar mamaki. Senator Ya ce“Tabbas hakan shi ne fatanmu a da, amma a yanzu reshe ya juye da mujiya domin kuwa dole mu fitar da yaron nan”. Kan shugaban jam'iyya ya fara kullewa a game da wannan zan tukan na Senator, dan haka Ya ce“Ban fahimta ba, fahimtar da ni!”. Senator yai masa gwari gwari tare da nusar da shi cewar Ashman ta sanadinsa za su iya rasa muƙami baki ɗaya, kuɓutar da shi kuma zai janyo musu alkairi amma bai sanar da shi cewar bokansa ne ya ba shi wannan aiki ba. Jinjina kai shugaban jam'iyya ya shiga yi bayan gama sauraran Senator da yai, ya fahimce shi. Dan haka Ya ce“To ta ina kake gani za mu ɓullo wa al'amarin wajan ƙuɓutarsa domin ni ta wajena zan ƙoƙari wajan ganin an rufe case ɗin na har abada bayan an gama komai”. Senator ya sanar da shugaban jam'iyyar tsarinsa. Dariya suka saka cike da jin daɗi da basirar da kowanne ya kawo wadda ta yi dai dai. ****** Zama tai akan tabarma tana aje hijab ɗin ta a gefe Ta ce“Umma sannu da gida”. Umma dake wanke wanke ta amsa da “Yawwa Ayrah sannu kin ji, kin dawo lafiya?”. Ayrah ta amsa da Ce wa“Lafiya ƙalau Umma, amma dai Yaya bai shigo ba ko?”. Umma Ta ce“Eh bai shigo ba kin san tun da ya samu aikin nan yanzu sai dare yake dawo wa”. Ayrah Ta ce“Haka ne, Allah dai ya taimaka”. Umma ta amsa da “Ameen! Ya naki aikin an dace?”. Ajiyar zuciya Ayrah ta sauke Ta ce“In sha Allah Umma ina sa ran nasara domin tun da na tunkari neman aikin nan jikina ya ban da nasara”. Umma tai murmushi Ta ce“A kullum ina miki fatan ta, Allah ya taimakeki akan kyakykyawan nufin ki”. Ayrah Ta ce“Ameen Umma”. Miƙewa Umma tai tana Ce wa“Bari na kawo miki abinci”. Tana faɗar haka ta shige ɗakin girki. Ayrah ta lumshe idanu tana tuna wasu abubuwa da suka faru a in da ta je neman aiki, a lokacin ta samu wani ɓaƙon yana yi a jikinta a lokacin da ta haɗa idanu da wanda take neman aikin a wajansa. ******* Har dare yayi Barrister Salma ta kasa bacci bincike kawai take yayin da ƙwaƙwalwarta ta shiga charge tare da son samu wasu hujjoji a game da binciken da take amma har yanzu wayam ba abin da ta samu. Kamar za tai kuka ta kai wa iska duka a lokacin da laptop ɗin ta ke gabanta a saman tebur yayin da ita kuma take zaune a kujera, kamar za tai kuka Ta ce“Oh My God! Allah ka kawon ɗauki a cikin wannan al'amari!”. Da sauri ta kalli ƙofa jin an turo an shigo kafin kuma ta sauke idanunta ƙasa Ta ce“Mama kece?”. Mama ta ƙara so ta zauna kusa da Barrister Salma tare da dafa ƙafaɗar ta Ta ce“Salma ba ki yi bacci ba har yanzu ƙarfe 12 na dare? Haba ki samu natsuwa mana tun safe kike abu ɗaya amma yanzu ba zaki samu ki huta ba?”. Barrister Salma Ta ce“Mama na kasa kwanci kuma gashi har yanzu ban samu komai ba akai”. Mama cikin taushin murya Ta ce“Salma aikinku yana buƙatar hutu da nazari amma gaba ɗaya daga ke har mahaifinki kon takura kan ku bakwa bawa jikinku da ƙwaƙwalwar ku hakkinta ta ina aikin ku zai tafi yadda kuke so?”. Kamar zata fashe da kuka Barrister Salma Ta ce“Mama me yasa idan na yi ƙoƙarin samu wata hujja sai kuma hanya ta toshe? Mama jikina na ban akwai mai bibiyarmu ni da Daddy”. Mama ta ɗan yi shiru, a ranta tsausayin 'yar tata da mijin ta ne fal domin da ta ita me ba za su karɓi wannan case ɗin ba, amma saboda ta san taurin kai irin na Barrister Muhammad ya sa tai shiru wanda idan ya fara shari'a ba ya tsoro sai da in kashe shi za ai a kashe shi. *A yi payment jama'a😂😂😂🙄🙄* *BA NI DA HUJJA 9 08143907733* *Marubuciya Zainab Muhammad Indian Girl* https://chat.whatsapp.com/BeEdSOYVSSr2bstxdbuft6 _Saura 1 pages mu gama free page littafin fa haɗaɗɗene ba sai na faɗa ba, Ga masu son fara payment za su iya tura wa ta wannan account ɗin Naira ₦500 ne kacal_ *5053077402* *Zainab Abubakar Umar* *Moniepoint* *Sai a turo shaidar biya ta number dake sama* _______________Mama Ta ce“Dama ai dole za a bibiye ku domin case ɗin ba ƙara mi ba ne”. Barrister Salma Ta ce“Mama a cigaba da mana addu'a in sha Allah muna tare da nasara!”. Mama Ta ce“In sha Allah, yanzu ki samu ki kwanta ki rage baccin gobe idan Allah ya kai mu kya ɗora daga in da kika tsaya”. Barrister Ta ce“To Mama”. Mama ta miƙe tare da yi mata sai da safe ta fice tare da janyo mata ƙofa da sanar da ita ta kulle ɗakin. Jiki a sanyaye Barrister ta miƙe bayan fitar Mama ta rufe ɗakin tare da hayewa gado ta kwanta ba tare da ka kashe laptop ɗin ba. ***** “An gama me gida mu da waɗan da za su iya siyar da ransu ba tare da wata matsala ba”. Busha yai maganar yana duba Senator. Senator Sammani Ya ce“Shikenan zan tura maka mazajan kuɗa ɗe a yadda aka saba, ina so daga nan zuwa gobe a gama komai”. Busha ya haɗe hannuwa yana Ce wa“Sai mai gida”. Abubuwa haka suka cigaba da faruwa masu daɗi da marasa daɗi a cikin daren zuwa wayewar garin daren. Ciki kuwa har da faruwar shirinsu Senator domin komai ya tafi yadda aka tsara. A gidan prison kuwa wani abun mamaki ne ya faru wanda ya girmama kowa wato tashi da akai aka ga gawar Ashman yashe a ɗakin wanda da alama ma ya jima da mutuwa. Nan jami'ai aka fara shige da fice wajan ganin ya za ai kar a kalle su da lefin mutuwar tasa, an gama komai an je an bunne gawar ba tare da kowa ya ga fuskarsa ba. **** “A yau Lahadi 19 ga watan 2 na shekarar 2023 aka tashi da mutuwar matashin nan mai suna Ashman wanda ake zargin sa da kashe iyayensa, wanda a gobe Litinin 20/02/2023 ake sa ran zaman kotu domin cigaba da saura ran ƙara. A sakamakon hakan kotu ta dakatar da shari'ar tare da wanke prison ɗin da ake ajiyarsa a ciki, a yanzu haka ma ya rigamu isa ɗakinsa na gaskiya. Bayan wannan kuma za ku ji cewa…”. Da sauri Umma dake ɗaki tana sauraran rediyo ta fito tana kwalla kiran sunan Ayrah. Da sauri Ayrah ta fito daga ɗaki da fargaba tana tambayar Umma lafiya?. Umma Ta ce“Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Ayrah shikenan ya mutu!”. “Waye ya mutu?” Ayrah ta tambaya a tsora ce. Umma Ta ce“Yaron nan mana Ashman, yanzu ake faɗa a gidan rediyo”. Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Sulalewa ƙasa Ayrah tai ta zauna jabar wasu hawaye na zubo mata, nan Umma ta shiga ba ta baki. ***** “What! Ina ba zai yiwu ba”. Barrister Salma ta furta hakan sakamakon ganin labarin rasuwar Ashman da tai wanda zuwa yanzu ba in da ba a ɗora labarin ba. Da sauri Barrister Salma ta zura takalma ta nufi ɗakin Daddynta tana zuwa ta ga shima ya shiga ruɗu wanda hakan ya ba ta tabbacin ya san abin da ya faru. Ta samu waje gefan carfet ta zauna domin shi yana zaune akan kujera ne. Kafin ta kai ga magana Barrister Muhammad Ya ce“Tabbas akwai lauje cikin naɗi a wannan al'amari!”. *Tofa masu karatu ya ne? Ƙaƙa ƙara ƙaƙa🫪🫪😲* A yi payment daga 10 pages an gama free *BA NI DA HUJJA 10 08143907733* *Marubuciya Zainab Muhammad Indian Girl* https://chat.whatsapp.com/BeEdSOYVSSr2bstxdbuft6 _Saura last pages mun gama free page littafin fa haɗaɗɗene ba sai na faɗa ba, Ga masu son fara payment za su iya tura wa ta wannan account ɗin Naira ₦500 ne kacal_ *5053077402* *Zainab Abubakar Umar* *Moniepoint* *Sai a turo shaidar biya ta number dake sama* _______________“Daddy mene mafita?”. Barrister Muhammad Ya ce“A halain yanzu Salma ba mu da wata mafita amma mu zuba idanu mu ga abin da zai faru tukun”. Barrister Salma Ta ce“Shikenan Daddy, amma ni gani nake kamar kashe shi su kai dan kar ya ba da wata hujja a kotu”. Barrister Muhammad Ya ce“Mu dai ɗan ba da lokacin kafin mu ɗora bincike”. Barrister Salma ta miƙe jiki ba ƙwari ta koma ɗakin tare da nufar laptop ɗin ta, anan ta ga ashe ma ba ta kashe ba. Ƙoƙarin kashewa take wani saƙo ya shigo mata. Duk da ba ta san mene a cikin saƙon ba amma sai da ta ji ƙirjinta yace ras,ta buɗe saƙon ta fara karantawa. *"Ina so mu haɗu domin na sanar dake wani abu da baki sani ba wanda zai baki ƙwarin gwiwar sake cigaba da bincike"* saƙon babu lamba kuma babu suna sannan babu wani abu da zai ba ta damar bibiya, wani saƙon ne ya shigo wanda ke ɗauke da location time da kuma gargaɗi akan kar ta sake ta je da wani domin komai na ta a tafin hannu yake a ƙarshe ta ga wannan alamar ta kalmomi. Ta furzar da iska tare da jama jabar akan kujera tana dafe kanta da dukkan hannuwanta biyu. ******* “Amma Nasiru wane ya baka wannan wasiƙa?”. Ayrah ta faɗa tana sake jujjuya takardar dake naɗe. Nasiru ya taɓe baki da Ce wa“Gaskiya ban sani ba domin a mashin yake kuma yana miƙon cewa yai ka ba Ayrah ya ja mashin ɗin sa ya tafi”. Ayrah ta sake Ce wa“Fuskarsa fa ka gani?”. Nan ma Nasiru ya girgiza kai. Ayrah Ta ce“Ok, jeka shikenan”. Nasiru ya fice maƙocin su Ayrah ne. Ayrah ta shige ɗaki tare da zama akan katifarta ta shiga warware wasiƙar tare da fara karantawa kafin tai wata irin zabura tana zazzare ido tana girgiza kai *(Kuna son sanin me ta karanta? To ku yi payment mu haɗu a book 2)*. ****** Tun kafin lokacin ya yi Barrister Salma ta kimtsa ta fice domin samun ɗan sahu dan ba ta son zuwa da mota domin ba ta san mene zai faru ba. Bayan isarta ta sauka ta biya mai ɗan sahu kuɗinsa ta nufi wani ɗan dakali ta zauna tana kalle kalle dan ganin ta ina wannan mutumin zai ɓullo mace ce ko namiji Allah masani. ****** Hankalin Senator fa ya kai ƙololuwa wajan tashi domin babu yarinya babu labarinta gashi ya cika mata alƙawarin ta amma ita ta ina zata cika masa nasa, ya ɗauki waya ya kira Ahmad Shasha tare da sanar da shi yana nemansa. Bayan zuwan Ahmad Shasha Senator Sammani ya shiga jeho masa tambayoyi a game da yarinyar sannan ya ɗora da Ce wa“Tabbas dole ne a nemo ta a duk in da take domin cikar burina”. Ahmad ya sauke ajiyar zuciya Ya ce“Na faɗa maka ban san ta ba babu abin da na sani game da ita domin itace ta kawo kan ta da kanta”. Senator Ya ce“Kenan kana nufin tsintarciyar mage ka kawo? To ai dama ba ta mage gashi ta yauda re…” . Bai ƙara sa ba suka jiyo murya daga bayansu tana Ce wa“………………”. *Tofa masu karatu nan muka zo ƙarshen book 1 wanda ya kasance free ne, amma fa book 2 shi ne rikicin domin shi ne tsagwaran labari yake*. *Shin da gaske Ashman ya mutu?* *Shin shi ne ya kashe iyayensa ko kuma ba shi ba ne?*. *Wane sirri ne Barrister Salma take son sani?*. *Me Barrister Salma ta gani a cikin akwati lokacin da ta kai wa Ashman ziyara?*. *Me alamar (B.L.K.C.B.A) take nufi?* *Da sauran tarin tambayoyi duk sai a littafi na biyu wanda payment babu tsada ₦300 ne kacal*. A tura a wannan account ɗin 5053077402 Zainab Abubakar Umar Moniepoint Shaidar biya ta wannan number 08143907733. Ina godiya da bibiya da kuke🥰🥰🥰🥰 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4