kin san hali na tun da kika ji na faɗi haka ki yadda da ni”. Dariya Umma tai kafin Ta ce“Ban da abin Ayrah da na yadda da kar na yadda mene amfanin sa tun da ba ni da ikon da zan iya taimaka masa wanda ya wuce addu'a”. Jinjina kai Ayrah ta yi kafin Ta ce“Umma ke kina da ikon yi masa addu'a ina fata kuma Allah ya amsa, amma ni ina da ikon taimakon sa”. Mamaki ne ya kama Umma jin abin da Ayrah ta faɗa, to ta ina ma take da wata hanyar taimaka masa ita ba ɗiyar kowa ba kuma ba wata ba, kar fa ta janyo musu bala'i. Da tashin hankali Umma tana zaro ido Ta ce“Ke Ayrah ki rufa wa kan ki da mu baki ɗaya ki tausayi maraici da ƙuruciyarki da kuma halin da muke ciki kar ki jefa kan ki a musubar da za ta dawo kanmu”. Miƙa wa tsaye Ayrah ta yi kana tai taku ɗaya zuwa biyu kafin ta tsaya tana kallon Umma wadda ita ɗin ma ita take kallo Ta ce“Umma ba kin ce ni ba yar kowa ba ce kuma ba mai mulki,izza,ko sarauta ba? To bari ki ji abi sa taimakon da yai min da kuma ceto na da yai da kuma ƙaunar da ta kullu tsakani na da shi zan yi amfani da dama ta wadda Ubangiji subhanahu wata'ala ya ba ni domin kuɓutar da shi!”. Jikin Umma ya mace murus tsoronta ɗaya kar Ayrah ta ka musu bala'i wanda zai zo ya danne wanda shi yaron ke ciki, cikin sanyin jiki Umma Ta ce“Amma Ayrah ba mu da gata sannan idan kin faɗa musiba nice a ciki saboda ni mahaifiya ce?”. Ayrah ta durƙusa gaban Umma tare da kamo hannunta ta damƙe cikin nata sannan Ta ce“Umma a da kin san Ayrahnki matsoraciya ce kuma mai gudun abin faɗa da magana mai kamun kai da tsoron Allah mai gojewa haram zuwa halak ɗin ta, Umma Ayrahnki ba ta shiga sabgar mutane wanda ko da kuwa tata sabgar ka shiga. Amma kin san wani abu Umma a wannan rana kuma a dai dai wannan lokaci Ayrah ta aje duka waɗan nan abubuwan a gefe zata yi amfani da dama da kuma baiwarta, fatan nasara da albarka nake nema a gare ki Umma tare da addu'a domin cin nasara akan abin da na sa gaba domin rama alkairi da alkairi!”. “Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Ya Rasulullah!”. Shi ne abin da Umma ta iya furtawa domin gaba ɗaya ilahirin jikinta ya gama mace wa, ba ta san cewa Ayrahnta haka take ba; ba ta san cewa mutum zai iya sauyawa ba sai yau; waɗan nan kalaman da ƙwarin gwiwar da ce mata akai Ayrahnta ce ta faɗa ba za ta yadda ba amma sai ga shi da idanunta da kunnuwanta tana ji kuma tana sauraro. Ayrah Ta ce“Alƙawari ɗaya zaki min Umma sannan ki min alfarma daya darajar yadda da ki kai har kika ɗau cikina kika raina kika haifa har na zo duniya kika kula dani zuwa girmana”. Cikin sanyi Umma Ta ce“Wane alƙawari ne wannan sannan wace alfarma ce?”. “Alfarmar itace ina so ki samin ido a duk abin da zaki ga ya faru sannan kar ki min gyara akan kuskure na, alƙawarin kuwa shi ne ki riƙe min sirrina bana so ko da Ya Taufiq ya san ainahin gaskiya daga cikin sirrina dan Allah Umma!”. Ayrah tai maganar wasu hawaye na zubo wa daga idanunta, ita kanta ta san cewa abin da za ta tunkara ba ƙaramin abu ba ne sannan dala ce zata ɗauka ba tare da gammo ba, amma koma dai mene ne ta shiryawa yaƙin. Umma ta janyo Ayrah zuwa jikinta ta rungume tare da ɗan bubbuga bayanta, Ta ce“In sha Allah Ayrah zan ƙoƙarin wajan cika alƙawarin sannan na amince miki Allah ya ba ki nasara domin ina da tabbacin bakya rashin nasara a al'amarin ki”. Da sauri Umma ta sa hannu ta goge hawayen da suka ta so ma ta suke shirin zuba sakamakon tuna wa da tai da wani ɓoyayyan sirri a game da Ayrah wanda daga ita sai mijinta wanda ya rasu sai Allahn da ya halicce su suka sani amma sai dai ba ta da Hujjar bayyana shi.
************“Wallahi na ji wannan mutuwa nace mutum ba a bakin komai yake ba”. Senator Sammani Kaita ne yai wannan maganar yana matsar hawaye. Alhaji Habu Mai Lafiya Ya ce“Hmmm! Kai dai bari kam Senator ai ni babu abin da ya zu min lokacin da na ga mutuwar irin mahawararka da shi wani zama da akai”. Ai Senator Sammani Kaita na jin wannan ba tun yai saurin ɗaga kai yana kallon Alhaji Habu Mai Lafiya Ya ce“Kai! Kai!! Kai!!! Ka ga Alhaji Habu mu bar wannan magana, ai ni kowa ya san ni da Alhaji Auwal aminai ne wannan ma akasi aka samu”. Alhaji Sani Musa ne Ya ce“Ni wallahi abin da yake damuna ma shi ne yaron nan Ashman da aka kama ake zargi”. “Yo da bai aikata ba hukuma zata kama shi ne? Da hujja fa aka same shi ɓaro ɓaro!”. Wani mutum yai maganar mai suna Salisu Sallau. Haka dai suka cigaba da tattaunawa ana jajanta abun.
Wannan kenan
*#WhatsApp Chat:- 08143907733*
*BA NI DA HUJJA 3*
By Zainab M Indian Girl
08143907733
Free page 3
_______________________Abubuwa sun cigaba da tafiya, Barrister Muhammad Umar Mai Kano ya dawo wajan Ashman har sau uku amma babu wani abu da ya samu daga gare shi illa kalma ɗaya kawai wadda itace *BA NI DA HUJJA* duk iya ƙoƙarin da Barrister zai yi na ganin an samu ko da Hujja ɗaya wadda za su yi amfani da ita a kotu wajan wanke Ashman amma bai samu ba har ranar zaman kotu ta zo. Yau ya kama litinin 10/02/2023 wanda a yau ne kuma za a fara sauraran shari'ar Ashman, ƙarfe 7:00Am na safe wanda kafin sannan kotu ta cika maƙil da jama'a kowa yana son jin yadda shari'a za ta kasance. Sai ƙarfe 11:00am alƙali ya iso cikin kotun, bayan ya zauna ne ya bukaci da a gabatar da mai lefi. Nan kuwa aka shigo da Ashman wanda duk wanda ya san shi a kwanaki biyu zuwa uku ya gan shi yanzu ya san tabbas ya sha wuya ba kaɗan ba. Tun da aka shigo cikin kotun ya din ga bin mutane da kallo bai ga abokansa ba ko ɗaya a ciki ya san me suke gudu kar a zo a jefa su ciki, amma me sai idanunsa ya sauka akan abin da ya sa zuciyarsa tai wani irin bugu ya zuba mata ido ba ƙaƙƙautawa yayin da ita kuma wani kyakykyawan murmushi take sakar masa, bai san me yasa ba shima sai tsintsar kan sa yai da mayar mata da kalar na shi wanda a ciki da hango abubuwa da yawa masu wuyar fassaruwa. Har suka isa a ka saka shi a cikin in da ake tsayawa bai ɗauke idanunta a kanta ba wanda ita ɗin ma hakan ce ta kasance. Bayan tsayuwarsa Alƙali yai sallama tare da ɓuƙatar lauyoyi su gabatar da kan su, Barrister Sulaiman Cinnaka shi ya fara miƙe wa tare da gabatar da kansa Ya ce“Sunana Barrister Sulaiman Cinnaka kuma ni ne lauyan gwamnati wato lauyan marigayi Alhaji Auwal Ashrab Soda tare da matarsa Hajiya Fatima,A tare da ni akwai mataimaka na Barrister Saudat da kuma Barrister Hafsah. Ya mai girma mai shari'a!”. Ya faɗa tare da komawa ya zauna Barrister Saudat da Barrister Hafsah suka gabatar da kan su. A nutse Barrister Muhammad Umar Mai Kano ya miƙe da murmushi wanda ya yi ne domin samun wani abu da shi ka ɗai ya sani. Ya ce“Sunana Barrister Muhammad Umar Mai Kano ni lauya ne mai zaman kan sa kuma ni ne wanda ke kare wanda ake tuhuma a tare da ni akwai mataimakiyata Barrister Salma Muhammad Umar Mai Kano”. Yana faɗar haka Barrister Salma Muhammad Umar Mai Kano ta miƙe ta gabatar da kanta sannan ta zauna. Maga ya miƙe tare da karanta ƙara kamar hara “A yau wannan kotu mai albarka zata saurari ƙarar da tafi kowace ƙara rikitarwa, wannan ƙara kuwa itace kisan da akai wa Alhaji Auwal Ashrab Soda da matarsa wanda a satin da ya ci zaɓe aka kashe shi, kuma ba kowa ake tuhuma da wannan laifin kisa ba sai ɗan sa Muhammad Auwal Ashrab Soda”. Yana gama karantowa ya miƙawa alƙali ƙunshin takardu sannan ya zauna. Alƙali Abdul Rahman Hakim ya dudduba kafin ya ɗago idanunsa ya sauke akan Ashman dake tsaye idanunsa a runtse sannan ya mayar da kallonsa ga yan kotu kafin Ya ce“Ko lauyan gwamnati yana da wasu tambayoyi da zai yi wa wanda ake tuhuma?”. Da sauri Barrister Sulaiman Cinnaka ya miƙe da Ce wa“Ya mai girma mai shari'a, akwai tarin tambayoyi wanda ina roƙon wannan kotu mai albarka da ta ba ki izinin gabatar da su ga wanda ake tuhuma”. Mai shari'a Ya ce“Kotu ta baka”. Cikin takun isa Barrister Sulaiman Cinnaka ya isa gaban Ashman ya tsaya tare da zuba masa ido na 'yan wasu daƙiƙu kafin Ya ce“Kamar yadda aka gabatar wa da kotu kunshi tuhumar da ake maka, ina son zan maka tambayoyi kuma ina fatan zaka ba ni amsa”. Sai yanzu Ashman ya buɗe idanu ya sauke akan Barrister Sulaiman Cinnaka amma bai ce komai ba. Barrister Sulaiman Cinnaka ya gyara tsaiwa sannan Ya ce“Malam Muhammad, oh ko nace Ashman domin na tabbatar jama'a sun fi gane ka da wannan sunan. Tambayar da zan maka itace me yasa ka kashe iyayenka ko da yake a wannan gaɓa ba za a baka wannan matsayin ba, me yasa ka kashe Alhaji Auwal Ashrab Soda da matarsa Hajiya Fatima?”. Ashman ya ɗan runtse idanu sannan ya buɗe, ya yi alƙawarin har a gama zaman kotu ba zai ce uffan ba dan haka ba abin da zai furta domin shi dai ya san cewa ba shi da wata hujja da zata kawo ƙarshen wannan shari'a da ya wuce shi ma a kashe shi. Shirun da yai na wani lokaci ya sa Barrister Sulaiman Cinnaka ya juya ga Alƙali kafin Ya ce“Ya mai girma mai shari'a sakamakon Ashman ya aikata laifin da ake tuhumar sa da shi hakan ya sa ba ya da wata amsa da zai iya bawa wannan kotu mai albarka”. Barrister Muhammad yai saurin miƙewa yana Ce wa“Ya mai girma mai shari'a ina riƙon da aka gargaɗi lauyan gwamnati akan ɗora alhakin kisan kan da yake akan wanda ake tuhuma”. Mai shari'a Ya ce“Kotu ba ta karɓi ƙorafi ba, lauyan gwamnati yana kan dai dai ya cigaba da tambayoyi”. Barrister Muhammad ya zauna rai babu daɗi yayin da Barrister Sulaiman Cinnaka yai wani shu'umin murmushi Ya ce“Na gode ya Mai Shari'a”. Sannan ya mai da hankalinsa ga Ashman kafin ya sake Ce wa“Ashman ina so kai wa wannan kotu mai albarka cikakken bayani akan dalilin da ya sa ka aikata wannan ɗan yan hukuncin”. Nan ma Ashman yai shiru bai magana ba, tambayoyi wajan biyar Barrister Sulaiman Cinnaka yai masa amma bai iya ya amsa masa ko ɗaya ba hakan yasa ya dubi kotu da Alƙali Ya ce“Ya mai shari'a ina roƙon wannan kotu mai albarka da ta yanke wa wanda ake tuhuma hukunci dai dai da laifin da ya aikata domin duk wani hujja da ake nema wadda za ta tabbatar da shi ya aikata wannan kisan ta tabbata domin shirunsa ka ɗai ma amsa ce”. Ashman suka haɗa ido da Barrister Muhammad, Barrister yai masa kallon ka tausaya kan ka ka ba ni bayanai, amma sai Ashman yai saurin ɗauke kai. Barrister Sulaiman ya koma ya zauna. Mai shari'a Ya ce“A bisa ga rashin kwararan hujjoji wannan kotu mai albarka ta ɗaga wannan shari'a zuwa 20/02/2023, kotu!”. Ya ƙara sa yana buga guduma, nan kowa ya fara fita a yayin da jami'an tsaron da suka zo da Ashman suka aza ƙeyarsa domin komawa, ƙara sowa in da suke Barrister Muhammad yai kafin ya dubi Ashman zai magana amma sai Ashman yai saurin tarar numfashinsa da Ce wa“Dan Allah Barrister bana buƙatar taimako ina buƙatar mutuwa ne a wannan hali”. Yana faɗar haka suka ja ji zuwa wajan mota, wani abu ya faru a cikin daƙiƙa ɗaya zuwa biyu wanda ba wanda ya sani daga Ashman sai wanda ya yi abun, haka aka shigar da shi mota a yunƙurin 'yan jarida na son jin ta bakin wanda ake tuhuma amma ba su samu dama ba anan na hango gidan rediyon Garanty da Freedom har da vision da sauran gida jen rediyo amma babu wanda ya samu jin ta bakin wanda ake tuhuma. “Barrister Mai Kano!”. Barrister Sulaiman Cinnaka ya kira sunan Barrister Muhammad wanda ke ƙoƙarin shiga mota domin tuni ita Barrister Salma ta shiga mahaifin na ta take jira ya shiga su wuce. Tsayawa yai har Barrister Sulaiman ya iso ya miƙa mai hannu suka gaisa kafin Ya ce“Barrister ina so nai maka wani tuni ne wanda ina da tabbacin ka san shi, abin da nake so da kai Barrister ka janye kan ka daga cikin wannan case ɗin domin zai kai ka ga nadama, amma ko da yake ai na ji labari baka faɗuwa ko rashin nasara a shari'a. Amma ka sani a wannan karon faɗuwa za kai ba za kai nasara ba”. Kalamansa sun taɓa zuciyar Barrister Salma cikin fushi ta fito a mota kafin mahaifinta yace wani abu ta dubi Barrister Sulaiman Ta ce“Me yasa duk da sani da kai na cewar mahaifina ba ya faɗuwa ko rashin nasara a shari'a amma ka zo domin yin gargaɗi? Ko da yake tunasarwa ce kai wa kan ka!”. Ta faɗa tana ɗan guntun murmushi. Barrister Sulaiman yai wani shashashan murmushi da Ce wa“Yaro man kaza, idan har kina son mahaifinki da kuma ke kan ki tu ki bawa kan ku shawara”. “Me zaka iya wanda Ubangiji bai iya shi ba? Ko kana tunanin barazana tana illata kyakykyawar zuciya? To bari ka ji babu gudu ba ja baya kuma nasara ta mu ce”. Isowar 'yan jarida wajan yasa Barrister Muhammad shige wa mota ya zauna domin ba ya son yin wata magana da su a yanzu, amma sai Barrister Salma ta buƙaci da su matso za tai magana ai kuwa suka saita camera a kanta kafin ta fara magana. Ta ce“Ɗan halin da ka raina wata rana shi ne zai tsone maka ido! In ji masu iya magana kenan. Abin da nake so nace shi ne shari'a za ta zo ƙarshe a zaman kotu na gaba kuma wanda ake tuhuma zai kuɓuta yayin da munafukai sai dai su ji kunya”. Tana gama faɗar haka ta shige mota ta ja suka bar wajan. “Barrister ko akwai abin da zaka iya cewa game da wannan shari'a?”. Wata farar 'yar jarida ta faɗa tana sai ta camera akan Barrister Sulaiman Cinnaka, a sannan ne shi kuma ya dawo hayyacin sa domin gaba ɗaya yarinyar can ta kwance shi da yawa, amma su zuba su gani.
*#08143907733#*
*BA NI DA HUJJA 4 08143907733*
__________________Wani guntun murmushi ya yi kafin cikin ƙwarin gwiwa irin ta sa Ya ce“Ta yaro kyau take ba ta ƙarko, gonar zomo kuma ta girmi shigar ɓera, in ji 'yan iya magana sun ce gani ya kori ji dan haka ku saurare mu a shari'a ta gaba domin jin yadda za ta kasance wajen tabbatar da cewa an hukunta mai laifi dai dai da abin da ya aikata”. Bai kuma sauraren maganganun da 'yan jaridar suke yi ba ya shige motarsa ya tayar ya bar wajan. Suma 'yan jarida suka naɗi iya abin da suka samu sannan suka watse. Wannan karon ba police station aka kai shi ba kai tsaye prison aka wuce da shi tare da kai shi ɗaki na musamman shi ka ɗai. Ya jingina da bangon ɗakin tare da sauke wani numfashi yana mai duba aljihun wandon sa wanda yana da yaƙini anan ne ya ga ta sanya masa wani abu wanda ba ya da masaniyar sanin ko mene ne, wata farar takarda ce aka yi mata na ɗin laya aka nannaɗe da zare. A hankali ya warware zaran dake jiki kafin ya shiga buɗe takardar wadda akai wa rubutu kamar haka. *Na san ka san ni sanin da ba a ɗauki maƙonni masu yawa ba balle aje ga watan ni ko shekaru, a tunanina kana sona domin hakan na so fahimta a cikin idanunka. Ka taimake ni kuma ka tserar da ni daga gudun mutuwa da kunyatar duniya a domin haka ne nima na sha alwashi wajan ganin na rama alkairi da alkairi, zan yi amfani da wannan abu wanda ta silarsa ka taimaken kuma ka tserar da ruyuwata ga barin kunyatar duniya. Ina da makaman da zan iya ceton rayuwarka dan haka ina fatan ka zauna cikin shiri kuma ka kasance cikin farin ciki* “A a ba na so hakan ta kasance dake zan juri iziyar wahala ko mutuwa amma zan juri takaici da baƙin cikin faruwar haka ta sila ta ba amma *BA NI DA HUJJA* ko damar da zan iya dakatar dake!”. Ya furta hakan yana buga kansa da bango tare da fashewa da wani marayan kuka.
*************“Da kyau mutumina ka san ni na fi son zafafan nan!” . Yai dariya da Ce wa“Kai dan ba ka gan ta ba ne she is beautiful”. Suka sake sa dariya tare da tafa wa. Tun bayan rasuwar Alhaji Auwal duniya ta zame wa 'yan jam'iyya abin daɗi suke cin karansu babu babbaka domin dama ba sa son sa da hawa mulki. “Jeka shigo min da yarinyar na ganta”. Senator Sammani Kaita ya faɗa yayin da azuciyarsa yake tuna wani abu wanda sirrinsa ne kuma shi ka ɗai ya sani. Ahmad Shasha ya amsa sannan ya fice, bai fi mintuna ba suka shigo da wata yarinya wadda da gani ka san 'yar duniya ce. Ahmad Shasha yana murmushi Ya ce“Ga ta nan ranka ya daɗe me girma shugaban ƙasa”. Wani murmushi shi ma Senator ya sakarwa Ahmad Shasha kafin Ahmad ɗin ya fice. Yarinyar ta ƙara sa cike da rausaya da jan hankali ta isa gare shi tare da fara aika masa saƙonni daga cikin abin da ya kawo ta gare shi, ya fara biye mata suna aikata wannan lamari sai kuma ya dakata sakamakon tuna wa da yai da wani sirri wanda shi ne silar da ya sa a nemo masa 'yan mata domin ya gani ko zai nasarar samun wadda yake nema. Maganganun boka ya tuno lokacin da yake ce masa cikin kakkausar murya “Dole ne ka kwanta da yarinyar kafin kwanaki goma masu zuwa domin idan har kai sake baka samu yarinyar ba ba kai ba mulki kowane iri ne har abada”. Jikinsa na rawa a lokacin cikin rawar baki Ya ce“To…To…To Boka…a ina zan samu wannan yarinya?”. Boka ya turɓune fuska kafin Ya ce“Ba ma da masaniya sanin haka, kuma ƙarfinmu bai isa ya san ina take ba domin ita ɗin ba wai kawai mutum ce kamar mu ba ita sirri ce mai wuyar fassaruwa!”. Jikin Senator yai san yi da jin hakan Ya ce“To amma ta ya zan fahimci cewa yarinyar da ka sa ni nema itace idan na same ta?”. Boka yai wasu abubuwa na su na shirka kafin Ya ce“Zaka gane ta ne ta kalaman da za ta zo da su domin abu ƙalilan za ta buƙata a gare ka wanda ya zamar maka dole ka nema mata shi ko ta halin ya ya ne domin ba kuɗi ba ne ko mulki”. Ajiyar zuciya Senator ya sauke bayan tunawa da yai da wannan bayani na boka kafin kuma ya biyo wa yarinyar suka aikata abin da Allah ya haramta yai hani da aikata shi wato zina. Bayan sun kammala sun kimtsa yarinya za ta tafi Senator ya tambaye ta me take ɓukata amma sai yarinyar Ta ce“Ni akwai wani abu da zan buƙata da ya wuce kuɗi”. Zuciyar Senator ta cika da takaici haka ya sallame ta. Kamar hauka haka Senator ya dinga neman yara matan 'yan mata amma shiru babu labari yayin da kwanki ke ta raguwa.
***********
Ta shigo hannunta ɗauke da ɗan ƙaramin tre wanda ke ɗauke da madaidaicin flask na shayi da kofuna akai da ganyen shayi mafi armashi da daɗi, ta aje akan tebur ɗin dake gabansa tare da zama a kujera tana fuskantar sa Ta ce“Amma Daddy nake ga ba tunani ya kamata ka dinga shiga ba, ya kamata ne mu tashi haiƙan domin nemo gaskiya ko dan mu kunyatar da azzalumin Barrister ɗin nan!”. Ajiyar zuciya Barrister Muhammad Umar Mai Kano ya sauke yana mai zuba wa 'yar ta sa idanu kafin Ya ce“My Daughter ta yaya kuma ta ina za mu fara bincike? Kin san dai cewa ba mu da Hujja wadda za ta tabbatar da cewa ga gaskiya”. Ɗan murmushi Barrister Salma tai wanda na kwantar da hankali ne Ta ce“Daddy na san da cewa su ba bincike suke ba kaifi da ƙarfinsu shi ne zai samar musu da hujja ko da kuwa ta ƙarya ce, amma ya kamata mu yi bincike domin neman gaskiya”. Zuba mata idanu Barrister Muhammad yai har ta ida magana sannan Ya ce“Kina sane da cewa kwanaki huɗu 4 suka rage a koma kotu? Ta ina za mu fara da zamu samo hujja a kwana huɗu 4?”. Barrister Salma ta janyo tre ɗin da ta shigo da shi ta haɗa tea a kofi sannan ta miƙa wa Barrister Muhammad ya karɓa sannan itama ta ɗauka ta ɗan kurɓa ta aje kafin Ta ce“Haba Daddyna kar ka sa na sare nima mana, kai ne ma gwarzo kuma jarumin lauya wanda baya gazawa ko sarewa kuma mai cimma nasara a ko da yaushe yasa abu a gabansa, a ko da yau she Daddy kai ne abin kwaikwayona a cikin aiki dan haka ina son ƙwarin gwiwar ka domin ƙarfafa tawa ƙwarin gwiwar”. Kalaman 'yar tasa sun shige shi sosai yai murmushi da Ce wa“Ba zan taɓa sarewa ba domin ina da jajirtacciyar ɗiya wadda ba ta tsoro ko gazawa”. Barrister Salma tai dariya Ta ce“Yawwa Daddy na, yanzu ta ina za mu fara?”. Barrister Muhammad Ya ce“Dole dai prison za mu sake komawa wajan Ashman ko Allah zai sa mu samu wani bayani daga gare shi”. Barrister Salma Ta ce“Daddy ka je gidan marigayi Alhaji Auwal domin yin naka binciken ni kuma ka bar ni da Ashman”. Barrister Muhammad Ya ce“Bana jinki ta wannan ɓangare, Allah ya ba mu nasara”. Barrister Salma ta amsa da “Ameen”. Ƙarfe 12:00pm na rana Barrister Salma tai wa gidan prison ɗin da Ashman yake ƙawayan yayin da mahaifinta Barrister Muhammad shi kuma ya ziyarci gidan Alhaji Auwal Ashrab Soda a dai dai wannan lokaci✍️
*#08143907733#*
*BA NI DA HUJJA 5 08143907733*
_________________Bayan shigarta ta samu ganawa da Ashman, ta shiga cikin ɗakin da yake wanda ƙazanta duk ya cika shi. Ganin ta da Ashman yai bai sa ya ji wani iri ba domin ya san dama za su sake bibiyarsa don son jin wata hujja daga gare shi. Gefe guda ta samu ta sanya takalmin ta ta zauna kafin Ta ce“Sannu fa”. Bai kula ta ba, tai murmushi da Ce wa“Na san zaka iya shaidar fuskata amma bari na sake sanar da kai, sunana Barrister Salma Muhammad Umar Mai Kano mahaifina ya so jin wasu hujja daga gare ka amma baka ba shi wannan damar ba ko me ya sa?”. Wani kallo yai mata kafin Ya ce“Saboda *BA NI DA HUJJA* Kuma ko da ina da hujja bana buƙatar taimako na fi buƙatar mutuwa a yanzu”. Barrister Salma Ta ce“Subhnallahi! Ko ka san da cewa Ubangiji ba ya kashe rai ba tare da lokacin da ya yi ba, Ashman yanzu haka Ubangiji ya tsara maka rayuwa ta shekaru masu yawa. Kana tunanin waɗan nan shekaru ka ƙare su a prison saboda wani dalili naka mara tushe?”. Ashman ya ɗan cigi lips ɗin sa na ƙasa kafin Ya ce“Mene amfanin faɗar wata hujja bayan duniyarmu mutane sun cikata da son zuciya, rayuwar al'umma ta koma ba komai ba a wajan shugaban ni, makirci yaudara da cin amana sun zama ruwan dare a wannan duniya