Share this page
2 / 5
ni ta yi yana niyyar fita daga hall d'in ba ki d'aya. Da sauri ita ma ta bi bayansa,bayan ya isa in da ya ajiye motarsa yana k'ok'arin shiga, ta sha gabansa tana fad'in "haba yaya Abeed ba ka ce komai ba, ba ka ga yanda yarinyar take mutuwar sonka ba". Ai kuwa sai dai ta mutu in dai ni ne, I hate her, ya fad'a tare da shigewa mota ya ja da k'arfi da niyyar ficewa daga wurin, dai_dai lokacin Fadeela ta fito.......................... Www.hauwajabo.blogspot.com Www.jabohauwa.WordPress.com M Twins 😍 & Auntie M.Jabo ✍🏾🍃 [4/11, 2:54 PM] Wacce Zamuyi Book: 💫AN YI WALK'IYA 10&11 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA Bayan kwana uku Mufeeda da Fadeela suka yi shirin zuwa gidansu Abeed don gaishe da Mumy, sun taki sa a kuwa don sun tarar da Arfat da afrat suna gida, su na yin sallama, Arfat ta taso da sauri ta rungume Mufeeda tana fad'in "oyoyo! Mufeeda yau a gidanmu" ? Kafin ta yi magana, Mumy ta fito, nan da nan ita da Fadeela suka zube su na gaisheta, cikin fara'a Mummy ta amsa musu, sannan ta ce "Mufeeda shiru kwana biyu kin daina lek'o mu". Mufeeda ta ce "eh wallhy Mummy school ne ya 6oyeni", mummy ta ce " ayya!, nima nasan Mufeeda akwai zumunci, to Allah ya ba da sa a", suka ce ameen ". Sai kuma ta kalli Fadeela ta ce da Mufeeda" Wannan k'awarki ce "? Murmushi Mufeeda ta yi tana kallon Fadeela ta ce" eh, Mummy k'awa ta ce " Allah sarki ya sunanta"? Tace" Fadeela ", sannu Fadeela Mummy ta fad'a tare da mik'ewa ta na cewa" Arfat haka za ku bar bak'in naku ba d'an abun ta6awa "? Afrat ta ce" Mummy dama yanzu na ke son tashi", ya dai kamata Mummy ta fad'a tare da shigewa kitchen. Sun sha hira sosai, sannan daga bisani Mufeeda take ce da Arfat ya Abeed na nan kuwa?? Arfat ta ce "a'a, ina za ki ga ya Abeed yanzu, ai sai wurin k'arfe biyar yake dawowa daga office". Mufeeda ta ce "ok, Arfat ta ce" ko ta samu ne "ta fad'a tana murmushi, ita ma Mufeeda murmushin ta yi, sannan ta ce "sosai kuwa, Fadeela ce ke masifar son ya Abeed," Arfat ta ce "wow! ai kuwa ina ganin Fadeela na ji ta kwanta mun a rai, Allah ya sa ya Abeed ya amince, gaskiya da ya yi mata". Sai kuma ta mik'e da sauri ta na fad'in bari na je na sanarda Mummy ta zo ga sirikarta", Fadeela ta hanzarinta ta rik'o hannun Arfat tana Murmushi ta ce "don Allah kar ki gaya mata yanzu bari sai mun tafi Allah kunya nake ji, ita kanta Mufy ta san ba halina ba ne cewa ina son wani kawai na d'auki son yayanki a wani 6angare na k'addarata, amma kwata_kwata mace ta ce tana son namiji baya burgeni", ta k'arashe maganarta da d'an guntun hawaye. Dukan su jikinsu ya yi sanyi Arfat ta ce "in dai mummy ce ba ta da matsala Allah ki daina ma Jin kunya don ta saba ganin 'yan mata kala_kala masu zuwa neman ya Abeed". Har wurin k'arfe shida Abeed bai dawo ba, don haka suka yi shirin komawa gida, mummy ta had'a musu sha tara ta arziki, sannan ta saka driver ya kai su gida. Sai wurin k'arfe bakwai ya shigo gidan , bayan ya yi wanka ya ci abinci, mummy ta same shi tace ta na son yin magana da shi. Murmushin gefen kumatu ya yi sannan ya ce "ina Jin ki Mum". Mummy ta fara magana "Abeed dama akan maganar aurenka ne, gaskiya ya kamata ka nutsu kasan mai kake yi zuwa yanzu, ka ajiye duk wani shirme da ke ranka, ka za6i matar aure ka yi aurenka ya fiye maka, kuma mu ma zamu fi samun kwanciyar hankali, don na gaji da zaryar da 'yan mata ke mana a cikin gidan nan". Juyo da dubansa ya yi sosai gareta, sannan ya ce "Mum yau ma wata ta zo kenan"? Mummy ta ce "eh yarinya mai hankali da kunya da za ka bi maganata da ka nemeta, don daga gani ' yar gidan mutunci ce". Yace "Mum ba ki gane ba ne ni fa duk 'yan matan da ke zuwa gidan nan ba ni na ke cewa su zo ba,in fact wasu ban ma ta6a ganinsu ba, kuma har yanzu ban samu wadda na ke so ba, please Mum adaina takura ni akan wad'ancan ' yan matan wahala ce bata ishe su ba that's all". Da haka ya mik'e yana shirin tafiya Mummy ta ce "yanzu Abeed za ka so ' yan uwanka su Arfat su fad'a irin Wannan halin a fad'i irin abinda ka fad'a a kansu, don nasan yadda ka ke son su". Ya ce "no Mummy nasan ba za su yi irin wannan halin ba, Mummy ta ce" shi kenan dai, idan Daddynku ya dawo za mu tattauna akan maganar, je ka kawai".............. Mum Twins 😍 & Auntie M Jabo 🍃 M Twins😍& Auntie M. Jabo ✍🏾🍃 💫AN YI WALK'IYA 8💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA K'arasawa ta yi in da Mufeeda ke tsaye kamar an dasata ta ce "mufy ya na ganki a tsaye, bayan ya tafi dama nasan ba lallai ya amince da buk'ata na ba". Cikin yak'e Mufeeda ta ce "kar ma ki yi wannan tunanin Fadeela, zai so ki da yardar Allah, yanzu ma don bai ganki ba ne na tabbatar idan ya yi ido hud'u dake ba abinda zai hana ya so ki". A jiyar zuciya Fadeela ta yi, sannan ta ce "ta yaya zan kuma had'uwa da shi bare har ya ganni?? Kar ki manta, ko sunansa ban sa ni ba, bare in da ya ke". Murmushi Mufeeda ta yi, ta ce " idan akan wannan ne ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa, idan kullum kike son ganin Abeed za ki gan shi da yardar Allah." Cikin mamaki Fadeela ta ce "wow! nice name, sunansa kenan"? Mufeeda ta gyad'a kai alamar eh, Fadeela ta cigaba da fad'in "amma mufy ta yaya zan gan shi duk lokacin da na ke so ya gaya miki sunan unguwarsu ne, ko wurin aikinsa ?" Dariya Mufeeda ta yi sosai sannan ta ce" wannan kuma sai kin ba da wani abu sannan zan gaya miki, "6ata rai Fadeela ta yi cikin sigar wasa ta ce" dad'ina da ke kenan, yanzu za ki fara ja mun rai tunda kin ga ina son ji ". Tafiya Mufeeda ta fara tana cewa" shi kenan tunda ba kya son ji, da tuni kin mik'o wani abu, "gabanta Fadeela ta tara tare da cewa" haba friendy ko haka ki ka bar ni ai kin ja mun rai, don Allah ki gaya mun", ta k'arashe maganar kamar za ta yi kuka. Mufeeda ta ce "don't cry k'awata, he's my cousin", waro ido Fadeela ta yi tare da daka tsalle ta rungume Mufeeda tana cewa "don Allah da gaske kike yi mufy"? Mufeeda ta ce" yes da gaske ne ko gobe ki ke so zan kaiki gidansu ya Abeed, "Fadeela ta kuma k'ank'ameta tare da cewa amma na ji dad'i Allah ya sa hakan ya zama silar cikar burina." Mufeeda ta ce "ameen, sannan ta duba agogon wayarta ta ce" gaskiya Fadeela dare yayi fa, gashi lunching d'in an fara a makare bari na kira driver ya zo, sai ya fara kai ki gida, sannan sai mu wuce ". Fadeela ta ce" gaskiya kam don kar ayi mana fad'a kinsan hajiya idan ta fara," suka saka dariya. Www.hauwajabo.blogspot.com Www.jabohauwa.WordPress.com [4/11, 2:54 PM] : 💫AN YI WALK'IYA 12&13 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Ana kiraye_kirayen sallar isha'i Daddy ya dawo, kaitsaye masallacin manne da gidan ya nufa domin sauke farali, bayan an idar da sallah tare suka fito da Abeed zuwa cikin gidan, suna tafe suna hirarsu irin ta d'a da uba, Mummy suka tarar a parlor ta na jiran k'arasowar mai gidan nata, cikin fara'a da girmamawa ta yi masa sannu da zuwa, tana fad'in "dama na ce yanzu haka masallaci ka wuce", Daddy ya ce "eh na shigo ana shirin ta da sallah na ce bari na yi sallar in yaso kawai na shigo gaba d'aya" ya fad'a yana murmushi Mummy ta ce "gaskiya kam, yanzu dai ga abinci nan an kammala kai kawai mu ke jira", ok, bari na je na watsa ruwa takun, Daddy ya fad'a ya na shirin barin wurin. Sai wurin 8:30 suka zauna cin abincin, bayan sun kammala ne kowa ya yi hani'an, don su Abeed har sun bar wurin, Mummy ke sanar da Daddy maganar Abeed, ta k'arashe maganar da cewa "gaskiya Alhaji ya kamata a d'auki mataki akan maganar Abeed, don yanzu kusan sa'anninsa duk sun yi aure, wasu har sun fara tara yara, amma shi shiru ko zancen auren ba ya yi, ni abinda ma ya fi damuna shine k'udirin da ya d'auka ya saka a zuciyarsa na lallai shi sai 'yar gidan hamshak'in mai kud'i zai aura, bayan da talaka da mai kud'i duk na Allah ne". Gyd'a kai Daddy ya yi, ya ce "haka ne, amma kin san abinda za a yi"? Mummy ta ce " a'a, ya ce "dama Alhaji Usman tun kwanakin baya yake maganar mu had'a Abeed aure da 'yar wajensa Hafat, na ce da shi sai na yi shawara da ke, da kuma shi Abeed d'in, don bana son na takura shi akan abinda baya so, shi yasa na ba shi dama duk tsawon wannan shekarun, amma tunda abun na shi haka ya zama, lallai_lallai ki gaya masa ya je ya ga yarinyar su daidaita kansu, tunda ai yasan gidan, don Alhaji Usman ba 6oyayyene ba a wurinsa." Mummy ta ce "Allah dai ya sa ya amince, don lamarin na Abeed sai addu'a", Daddy ya ce "da kakkausar murya za ki gaya masa ni na ce ya je, idan dai ban da k'uruciya yaran gidan Alhaji Usman mai za a nuna musu, suna da tarbiya ga hankali ga ilimi, amma shi ya tsaya neman k'yale_k'yalen duniya da ba zai anfaneshi da komai ba sai wahala". Mummy ta ce " wallahi kam, ai yaran yanzu ba sa gane abinda ake hango musu, sai abinda zuciyarsu ta raya musu shi suke yi, bayan bahaushe yace " son zuciya 6acinta". Daddy ya ce "sosai Allah dai yasa mu ga ne", mummy ta bi shi da ameen". ********* Tun da safe Abeed ya yi shirin zuwa office kamar yadda ya saba, duk safiya kafin ya wuce office sai ya je ya yiwa mummy sallama ita da Daddy in dai ya na gari ko bai yi sammakon fita ba. Bayan ya shiga mummy ke sanar da shi yanda suka yi da Ddynsa akan maganar neman auren 'yar gidan Alhaji Usman, zaro ido waje ya yi yana fad'in "Mum wai wani Alhaji Usman"? Mummy ta ce" akwai wani Alhaji Usman bayan aminin Daddyn ku"? Mere baki gefe ya yi, sannan ya ce "Mum mun San fa komai gameda Alhaji Usman kawai dai muna shiru ne." Fito da ido waje ta yi, ta ce" mai ka sa ni game da shi? yana da wani mugun Hali ne"? Abeed ya ce "no ba abinda na ke nufi ba kenan, kawai dai a takaice yaron Daddy ne, don dai Daddy ya taimaka masa ya ba shi companyn sa da ke bompai ne ya na kula da shi, shi ne kawai ake ganinsa wani mai arzik'i, kin ga kuwa Mum kamar ni haka, ta yaya zan auri 'yar yaron babana!!! Ai na ci baya sosai, gaskiya mum bazan ma iya ba." Mummy da tunda ya fara magana take tafa hannu tana sallati tace "yanzu Abeed tanan ka 6ullo kuma"? Ya ce " Mummy don dai kin san Daddy da rik'on abokanai ne na tun k'uruciya amma ba don haka ba, ina laifin ko a cikin manya_manya attajiran garin nan ya nema mun 'yar wani perhaps da na amince na yi manage da ita." Mummy kam tuni ta dask'are a gurin don mamaki, tace "au maneji ma za ka yi da ita"? To bari Alhaji ya dawo na gaya masa, gaskiya ya nemo mai ruk'iyya ya duba ka don ina ga ba zaka rasa jinnu ba". Dariya sosai Abeed ya yi sannan ya ce "Mum wallahi ras na ke, kawai dai na gaya miki abinda ke zuciya ta ne," sai kuma ya kalle agogon dake daure a hannunsa ya Ce "Mum gaskiya na makara bari na tafi sai na dawo," Mummy tace "Allah ya kiyaye hanya", yace "ameen tare da ficewa daga d'akin...................... Mum Twins 😍 & Auntie M Jabo 🍃 [4/11💫AN YI WALK'IYA 9💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Cikin 6acin rai Abeed ya koma gida, parking kawai ya yi ko kulle motar bai yi ba, ya wuce part d'in sa, ransa a dagule yake gaba d'aya, yana tunanin wai yaushe ne burinsa zai ciki, ya samu yarinyar da ta dace da shi, wacce ya ke mafarkin samu, domin shi kansa yanzu ya hak'ik'an ce da ya na buk'atar aure, amma matsalar duk 'yan matan da ke sonsa yanzu ya raina arzikin iyayensu, duk da cikin su babu wadda za a d'auka ace babanta matsiyaci ne, don dai shi ya d'auki k'atoton buri ya sakawa zuciyarsa, dole sai 'yar mai hannu da shuni, lokaci d'aya ya tuna da wacce akace tanasonsa, wai babanta yayi rik'on logal government, dai rainin wayo, wani dogon tsaki yaja, yadan juya kwanciyar sa, ya kalli a gogon d'akin yana lumshe ido. ********* Goggo wacce nake tunanin y'ar uwar Dadyn su Abeed ce, zaune take tareda Mumy suna hira, Abeed ne ya shigo ya gaishesu cikin sakin fuska sannan ya wuce d'akin sa, nan suka fara hirar yau da kullum, har Goggo ta gangaro akan abinda ya dad'e yana damun ta, "hajiya yaran yanzu sai a hankali, sam basa tunani basa naziri, yanzu za ku ga wasu yaran masu kud'i idan za su yi aure sai su rik'a hangen wadda mahaifin ta ya dame nasu ya shanye da naira, don zilama, maimakon su nemi dai_dai su, tunda Malam bahaushe ma ya ce "dai_dai ruwa dai_dai tsaki, kuma kowace k'warya da abokin burminta" sannan ma ina laifin su yi k'asa_k'asa su nemi 'yar talaka bawan Allah suma su samu su lasa, kinga ai an taimaki juna an rufawa juna asiri ta wannan hanyar, amma ba a yi saboda buri ya cikawa masu irin wannan halin zuciya, kowa sai dai-dai shi," Mumy tace "Wallhy zancen ki dutse Goggon yara, nima abin yana damuna, musamman idan naga halin yaronnan banajin dad'i sam, amma kinsan kosu talakawan akwai nasu sabida sai su k'wallafa dogon buri wa yaran su, su mayar da yayan nasu kamar jari, domin wasu sai ka ga sun zaune jiran mai d'an maik'o_maik'o har yarinya ta tsofe a gida, ba iyayenba ba ' ya'yan ba, kije gida ki rasa gane uwa da yaran gida, akwai wani gida da mukaje ta'aziya, a gidan naga mata 'yar kyakyawa, wacce nake tunanin zata haifi yara biyu ko uku, nake tambayar matar gidan, an mata amarya ne, dan tare na gansu, sai take cemin ai 'yar kice wance, wallhy saida na kai zaunedDan mamaki, na tuna yarinyar sa'ar Muhammad ce fa! Amma har yanzu tana gida," Goggo ta saka dariya, " kin bani dariya, wai an miki amarya ne" itama Mumy dariyar tayi suka ci gaba da hira" wannan zamanin kowa kwad'ayi ya yi masa yawa, bayan sun mata Allah ke yin komai, domin kowa an riga an rubuta k'addararsa tun kafin ya zo duniyannan, we just trace, sai ka ga budurwa ta zauna jiran Mr right har ta tsofe tun tana samun masu zuwa har lokacin ta ya wuce ya zamana bata samu, ta tashi a tutar babu, k'arshe sai ta auri wanda bataso, sabida da yawa masu wannan burin, wallhy basa auren mazan da zuciyar su takeso, saidai dan kud'i, su tashi ba wan ba k'ani, ta yi haihuwar guzuma 'ya kwance uwa kwance, ba mai d'an maik'o_maik'o ba mijin kwatakwata" nan ma saida suka dara, Goggo tace, " nifa kina magana kina saka engilishi, kuma kinsan ba ganewa nakeyiba," sukayi dariya gaba dayan su, Goggo tace, " Allah ya sa masu wannan halin su gano su bari dan ba alkhairi acikinsa" ameen Mumy ta amsa dashi, Na kalli M Twins nace "nifa al'amarin Abeed yana bani mamaki domin ya d'ebo da zafi, kace sai 'yar wane ko wane," M. Twins tace " ?kedai bari Aunty Jabo, Allah na d'auka irin wannan abin matane kawai keda wannan hali, ashe har maza ma sunayi, abin kunya, amma hausawa sun ce "kowa ya d'ebo da zafi bakinsa"..........." Www.hauwajabo.blogspot.com Www.jabohauwa.WordPress.com M Twins 😍 & Auntie M. Jabo ✍🏾🍃 [4/11, 2:54 PM]💫AN YI WALK'IYA 14&15 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA Daddy na dawowa Mummy ta kwashe yanda suka yi da Abeed ta fad'a masa, ai kuwa ya yi ta fad'a, nan take ya d'auki waya yace "da Abeed duk abinda ya ke yi ya ajiye ya zo yana kiransa", Abeed ya ce "to Daddy ga ni nan zuwa" don dama ya san sai an yi haka, cikin abinda bai fi 10 minutes ba ya shigo gidan, kaitsaye parlourn Daddy ya nufa, bayan ya gaishe su, Daddy ya fara magana "Abeed ka saurare ni ka ji abinda zan gaya Maka, domin maryam ta gaya mun duk yanda ku ka yi da ita, to bari ka ji bazan d'auki wannan shashancin ba, dole ka bi maganata idan ba haka ba, ka sanni sarai". Rausayar da kai Abeed ya yi ya ce "Daddy dama abinda ya............" dakatar da shi Daddy ya yi ta hanyar d'aga masa hannu, yace "ba na son jin wata magana yanzu kawai tashi ka je ka yi abinda na saka ka". Jiki a sanyaye Abeed ya tashi yana fad'in "to". Daga nan dakinsa ya wuce, amma zuciyarsa a cunkushe take yana tunanin meye mafita, don dai shi ya hak'ik'ancewa zuciyarsa ba zai ta6a auren 'yar gidan Alhaji usman ba, ya san kwata_kwata ba ajinsa ba ce, da wannan sak'e_sak'en har barci ya yi awon gaba da shi. Ko da ya tashi da safe fuskar nan tasa ba annuri, su Arfat ma da suka ga yanayinsa tuni suka kama kan su, tare da gimtse dariyar da ke cin su, domin mummy ta gaya musu duk abinda ake ciki, bayan ya fita ne Arfat ta kalli Afrat ta ce "ni wallahi gwanda da Daddy ya yi wa ya Abeed haka ko ya maida hankali ya yi auren, mu ma mu fara ganin babies a gidanmu". Afrat ta ce "ni kuma gani na yi da Daddy ya kyale shi ya za6a da kan sa, idan ya ga bai samu wadda ya ke so ba ai dole ya yi hak'uri ya auri wata,kuma ni yaran gidan Alhaji Usman ba su yi mun ba, sai gwalli da iyayi amma ba su da wani kyau". Murmushi Arfat ta yi sannan ta ce "Ai k'arshen mai ruwan ido ke nan". Bayan ya dawo daga aiki mummy ta takurashi akan ya je su gana da Hafsat, dole ba yanda ya iya ya yi shirin zuwa gidan Alhaji Usman. Duk da ya saba shiga har cikin gidan a duk lokacin da ya je, amma wannan zuwan da ya yi tsayawa ya yi a inda ya yi parking motarsa, sai da mai gadin gidan ya ga ba shi da niyyar shiga ciki don ya ga ya dade a tsaye sannan ya je ya ce da shi, "yalla6ai Alhajin ya na ciki ka k'arasa mana", juyawa ya yi ya kalleshi ya ce "ai ba wurinsa na zo ba, ka je ka ce ana kiran Hafsat" Mai gadi ya ce "to bari na je na gaya mata" bai fi minti biyu da tafiya ba, ya dawo ya ce "ta ce tana zuwa". Hafsat kuwa tunda mai gadi ya sanarda ita ana sallama da ita, ta tambaye shi waye ya ce da ita Abeed ne, ta shiga tsallen murna, dama ba ta dad'e da fitowa daga wanka ba, nan da nan ta hau kwalliya a fenta can a manna can har ta gama, ta fito cas da ita. Dama mai gadi ya gaya mata yana bakin gate so direct can ta nufa, ana tafe ana yauk'i, kamar ba za a taka ba, sai kuma jikinta ya yi sanyi lokacin da ta fara hangoshi, don yanayinsa ya fi kama da wanda aka aikowa sak'on mutuwa, sai ta fara tunanin ko wani mugun sako ya kawo mata ne! Daurewa ta yi ta k'arasa inda ya ke ta masa sallama tare da fad'in "sannu da zuwa", sallamar kawai ya amsa ya yi shiru, sun yi kusan 4 minutes ba wanda ya k'ara cewa komai, sai can Hafsat ta ce "ai da ka zo mun k'arasa ciki ko"? A'a kawai ya ce da ita, ta ce" ai tsayuwar ce ba dad'i, ko za ka zo mu koma daga can wurin ta yi nuni da wani wuri d'an nesa da su kad'an da aka sawa rumfa tare da resting chairs, ya ce "ba zama zan yi ba, don yanzu haka bai fi 5 minutes na tafi ba", Hafsat a ranta ta ce anya kuwa Abeed ya na sonta? wata zuciyar ta ba ta amsa da cewa ai da yana sonki da tunda kika zo kin gani a fuskarsa, kawai dai........... Abeed ne ya katse mata tunani ta hanyar yin magana, yace "ba sai na miki dogon bayani, don na San a gida an miki bayanin komai, duk da dai ke ban san tunaninki akaina ba, amma ni zan gaya miki gaskiyar abinda ke zuciya ta, ni ban yarda da wannan auren had'in ba, kuma ba zan iya bijirewa maganarsu ba, kuma ke kin san duk burin mace bai wuce ta samu miji mai sonta da kaunarta ba sannan yake kuma tausayinta ba, don shi ne a kowane irin hali zai kasance tare da ita, idan dai ki na buk'atar hakan to kada ki kuskura ki amince da aurena, shawara ce na ke ba ki idan ki d'auka kin taimaki kan ki, idan kuma ba haka ba a shirye na ke da d'aukan duk wani k'alubale sannan zan aureki, smma zaki rasa duk wayanchan abubuwan idan kin shirya bismillah!!". Bai jira abinda za ta ce ba, ya fad'a mota ya yi mata key ya fice daga gidan. Hafsat kuwa ta fi k'arfin 10 minutes a tsaye a wurin tana maimaita kalamansa, sai da ta ga hakan ba mafita ba ne ta shuri k'afafuwanta ta shige ciki............. Mum Twins 😍 & Auntie M Jabo 🍃 [4/11, 2:54 PM] 💫AN YI WALK'IYA 6&7 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Tun da safiyar ranar mubarak yake ma Abeed waya akan kada ya manta please, yamai SMS ba adadi, k'arshe ya yarda zai tafi, dan har ya shirya dojewa. Sai wurin k'arfe tara da minti ashirin da biyar Abeed da tawagarsa suka shiga hall d'in, cikin takun isa da k'asaita yake tafiya, ya rufe idonsa da wani shade bak'i kaitsaye gurin da aka tanada domin zaman su suka nufa. Wohoho! Ku zo ku ga 'yan mata yanda suka zuba masa na mujiya suna kallo, kai basu kad'ai ba har mazan dake gurin kallonsa suke yi tamkar sun ga wata sabuwar halitta, shi kuwa gogan naku ko kallo ba su ishe shi ba, tafiyarsa kawai yake cikin isa da izza har ya isa wurin zaman su. Tun shigowarsa wata yarinya mai amsa sunan Fadeela, muka ga duk ta rud'e ta rikice, sai wani dube_dube take kamar mai neman wani abu. Sai can kuma muka ga ta nufi wani side na musamman, domin an yi decorating gurin sosai fiye da inda take zaune, Da sauri ta k'arasa wurin har tana tuntu6e, tare da rik'o hannun wata budurwa wadda ba zata wuce sa'arta ba, sannnan ta ce "Mufy ta so don Allah ki gan shi shine wanda na ke yawan yi miki maganarsa" ido Mufeeda ta zuba mata na d'an lokaci sannnan ta ce" wai ki na nufin guy d'in da ba ki da aiki sai na maganarsa shine ya zo nan gurin,"? Fadeela ta ce "eh tare da langa6ar da kanta gefe," Mufeeda ta yi farr da ido,sannnan ta ce "gaskiya fady kin ban kunya, duk yanda kika h'adun nan, kuma kike gwara kan samari son ranki amma ki 6ige da baran soyayya akan saurayin da ko sunansa ba ki sa ni ba". Dafa kafad'arta Fadeela ta yi tare da cewa "friendy ba ki ga guy d'in ba ne that's why kike wannan maganar, kin san first class guy, full options to shi ne, ni tsoro ma nake kar ki gan shi ki kasa controlling kan ki ki je ki shigar da kan ki ba ni ba" ta k'arashe maganar tare da sakin dariya! Duka Mufeeda ta kai mata, ta goce sannnan ta ce "an gaya miki akwai wanda ya isa ya ture gwamnatin k'albina ne," Mufeeda ta cigaba da fad'in "ni dai zo ki nuna mun in da ya ke, ga ganshi, na cigaba da abinda na ke yi". Fadeela ta ce "na ga dai sun nufi wurin da aka tanada don manya_manya abokan ango" ta fad'a tana d'an kalle-kalle OK, "to ta yaya zan yi na gane shi??" Cewar Mufeeda, nari mu je na nuna miki shi ko daga nesa ne, d'an nesa da su Fadeela ta tsaya take nunawa Mufeeda shi, ba tare da ko na kusa da su sun gane abinda suke yi ba. Tun da Mufeeda ta hangoshi take wasiwasin wani abu a zuciyarta, sai da ta zo daf da shi sannan ta tabbatar da abinda take zato. Sallama ta yi sannan ta ce "sannu yaya Abeed" Jin an kira shi da yaya, ya tilasta masa d'agowa da kan sa domin ganin mai magana. Fuskarsa ya d'an saki sannan ya ce " yawwa sannunki", ta cigaba da fad'in ashe kai ma ka zo bikin k'awarmu"?? Jin bai ce komai, ta ce "angon ne abokinka ke nan"?? kai ya gyad'a mata kawai, ta ce" ai ni amaryar ce close friend d'ina". Jin ya kuma shiru ta ce "yaya ba ka son zuwa gidanmu su Arfat ne kawai ke zuwa". Hmm! kawai ya ce, nan ma shiru ne ya kuma ratsawa, sai da ta ga shirun yayi yawa ta ce "dama akwai maganar da ta kawoni wurinka idan ba za ka damu ba ka ba ni 5 minute's please", kamar ba zai yi magana ba, sai can ya mik'e ya yi mata nuni da su fita daga gurin. Gefe suka koma, sannan ta fara masa bayanin abinda ya kawota, ta k'arashe maganarta da cewa don Allah yaya ka taimakawa k'awata ba ka ga yadda ta ke sonka ba." Bud'ar bakinsa sai ya ce "waye mahaifinta"? Cikin rashin fahimtar maganarsa Mufeeda da ta ce" Babanta dai d'an siyasa ne", ya ce "muk'amin meye da shi"? eh, to ni dai abinda na sa ni ya ta6a rik'on k'warya a local government". "What!" ya fad'a da k'arfi, yana had'e fuska, daga haka bai k'ara cewa da ita komai ba, sai ga ni ta yi yana niyyar fita daga hall d'in ba ki d'aya. Da sauri ita ma ta bi bayansa,bayan ya isa in da ya ajiye motarsa yana k'ok'arin shiga, ta sha gabansa tana fad'in "haba yaya Abeed ba ka ce komai ba, ba ka ga yanda yarinyar take mutuwar sonka ba". Ai kuwa sai dai ta mutu in dai ni ne, I hate her, ya fad'a tare da shigewa

Chapter 2 of 5