Share this page
4 / 5
dauki wani dogon lokaci kafin a yi auren. Bayan sun gama tattaunawarsu a cikin gidan, suka fito Alhaji Sulaiman ya na cewa "Alhaji Bashir hakuri za ka yi, kasan komai nufin Allah ne, Allah bai kaddari matarsa ba ce, kasan yaran yanzu ba a musu dole, wata k'ila matarsa tana can wani wuri inda ba a zata ba". Gyada kai Daddy kawai ya yi, amma a k'asan zuciyarsa yana tunanin, taurin kai irin na Abeed, da haka suka yi sallama da Alhaji sulaiman, Daddy yana shiga gida ya rufe Abeed da fad'a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, daga karshe ya kuma tabbatar masa da aurensa yana nan ba fashi kamar yadda ya fad'a sai dai duk abinda zai yi ya je ya yi............. Maman Twins 😍 & Auntie M Jabo 🍃 [4/11, 2:55 PM] 💫AN YI WALK'IYA 29_30💫 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA Abeed ne ya fara rarrashinta, yana cewa ki yi hak'uri Afrat , komai muk'addari ne duk abinda kika ga ya faru da bawa to haka Allah ya tsara masa." Da haka ya yi ta tausar Afrat da kalamai masu sanyaya zuciya har suka iso gida. Washe gari ta kama ranar laraba, a ranar aka sallame su arfat daga asibiti, don ta warke sumul sai dan abinda ba'a rasa ba. Tunda suka dawo gida Arfat ba ta wata doguwar magana bare hira daga eh sai a'a, hakan da take yi ba k'aramin tadawa mutanen gidan hankali yayi ba, musamman mummy da Afrat. Mummy ce ta shiga d'akin su Arfat don yin magana da ita, kamar dai yadda ta koma tun faruwar al'amarin haka ma yanzu mummy ta tarar da ita a zaune ta na aikin tunanin da ta saba. Zama mummy ta yi akan gadon da Arfat ke zaune, sannan ta janyo ta jikinta, cikin sigar rarrashi ta fara magana "haba Arfat yanzu rayuwa ta yiyu a haka??? Duk Kin bi kin chanza, kin daina walwala,, ba kya son cin abinci, kullum ba ki da aikin da ya wuce zama a d'aki kina tunani, haba Arfan mummy why "?? Ta k'arashe maganar tare da shafa kanta. Hawayen da take ta mak'alewa ne suka samu damar gangarowa a kumatunta ta ce "Mummy kun k'i ku gaya mana asalin mu, kullum idan na yi magana sai ku ce za ku fad'a, amma har yau shiru ga shi kwanaki sai dad'a ja suke yi ". Ajiyar zuciya mummy ta sauke, sannan ta ce " abinda ya sa ba a gaya muku ba Arfat, ba ma so ne ki kuma shiga halin da kika shiga a baya, shi ne kawai ". Still hawayen ta ke yi ta ce "mum hakan da kuka yi, shi ya ke barazanar jefani wani hali, domin mummy yanzu buri na bai wuce nasan ni wacece ba, daga wani tsatso muka fito ni da k'anwata, ba ni da wani muradi da ya wuce hakan, domin Jin ainihin labarin mu shi zai kwantar mun da hankalina". Mummy ta ce "Arfat kin yi alk'awari, idan aka gaya miki za ki kwanta da hankalinki?? Za kuma ki dawo da walwalarki, ki dawo dai Arfat da na sa ni da bata yanzu ba, kuma ki kar6i labarin hannu bibiyu a duk yanda ya zo miki, kin yi alk'awari??? Arfat ta ce "yes mum, i promise you" Dad'a rungumeta mummy ta yi, ta ce "yawwa my lady, haka na ke son ji". Sannan mummy ta cigaba da fad'in "to ki kwantar da hankalinki idan Allah ya yarda Alhaji na dawowa za'a sanarda ku komai". Murmushi Arfat ta yi, for the first time, tun faruwar lamarin, ta ce "to mummy na gode". Murmushin mummy ta maida mata tare da mik'ewa tsaye ta mik'a wa Arafat hannu alamar ta mik'o na ta hannun su fito tare a dole Arfat ta mik'e suka fito daga d'akin, mummy na rik'e da hannunta har suka fito parlour. Arfat suka tarar a zaune tana kallo, duk da dai ita ma idonta ne kawai akan TV amma zuciyarta ta tafi bulayi, shigowarshi ne ya dawo da ita duniyar da ta shiga, da murnar ta mik'e tana fad'in "ah! Sisto yau an fito kenan??? Mummy ta ce "hmmm! Ga ta nan na 6a66akota dak'yar " Mummy ta k'arashe maganar da yin Murmushi. Afrat ta ce " Mummy aikam kin kyauta, don yawan zaman d'akin ita kadai yana k'ara mata damuwa." Mummy ta ce "sosai kuwa, bari na je na k'arasa girkin can, don yamma sai dad'a gabatowa take yi, tun da dai ku kun yi wa kitchen yaji kwana biyu". Murmushi suka yi dukan su, tare da cewa "Mummy za mu dawo ne very soon". Mummy ta ce "Allah yasa tare da shigewa kitchen. Auntie M Jabo 🍃 & Mum Twins 😍 [4/11, 2:55 PM] 💫AN YI WALK'IYA 26-28 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Daga nan Abeed bai zarce da Arfat ko'ina ba sai asibitin Dr. Usmam wato family doctor d'in su. Asibitin mai amsa sunan Apex Clinic da ke nan cikin nasarawa G.R.A, tun kafin ya k'arasa asibitin ya kira Dr. Usman ya sanar da shi halin da ake ciki. Don haka suna isa doctors suka rufu akan ta, cikin taimakon Allah ba'a d'auki wani dogon lokaci ba ta farfad'o. Mummy kuwa bayan fitar Abeed d'auke da Arfat , side d'in ta ta nufa da niyyar d'auko mayafi don ta bisu, sai da bayan ta fito waje sai ta ga wayam,ba Abeed ba motarsa, hakan ya tabbatar mata da sun tafi asibiti ne. Juyawa ta yi gurin da Afrat dake tsaye ta yi wani zuru-zuru da ita, cikin rashin k'arfin jiki tace "Afrat yi sauri d'auko mun key d'in motata mu tafi". Afrat tace, "To" Tare da komawa cikin gida. A k'ofar shiga parlour suka had'u da Daddy shima yana shirin fitowa don zuwa asibitin. Yace "Ya dai Afrat, ba ku tafi ba ne"?? Afrat ta ce "Eh Daddy, yanzu za mu tafi, na shiga ciki ne, key d'in motar Mummy zan d'auko". Daddy ya ce "Waye zai yi driving d'in?? Afrat ta ce "Mummy ce" Daddy ya ce "Bar key d'in mu je a tawa motar kawai". Waje suka fito in da Mummy ke tsaye, Daddy ya ce "Maryam ta yaya za ki yi driving a irin wannan halin?? Sanin kan ki ne ban fiye son kina driving ba, bare ki na cikin wannan yanayin, abinda za a yi ku zo mu je manu driver ya kai mu gaba d'aya hakan zai fi". Mummy ta ce "Shi kenan dama na k'agara na ga halin da take ciki ne shi yasa". Murmushi Daddy ya yi, ya ce "Mummyn yara kenan yanzu za ki ganta Insha'Allah". Bayan sun isa asibitin a reception su ka tarar da Abeed, da sauri Mummy ta k'arasa in da Abeed ke zaune ta ce "Abeed ya jikin nata, Allah dai ya sa ta farfad'o "??? Abeed ya ce "Mum ki kwantar da hankalinki, Arfat ta farfad'o tun dazu, don dai an mata allurar barci ne, da ido biyu za ku tarar da ita". Gaba d'ayan su suka yi murmushi tare da fad'in "Alhamdulillah" Dai_dai lokacin Dr usman ya k'araso wurin yana fad'in, "ah! Alhaji har kun k'araso ke nan"?? Daddy ya ce "Eh Dr. ya aiki "?? Dr usman ya ce " Alhamdulillah!" Anan dai duk suka gaisa cikin girmamawa, sannan ya ce "Ai za ku iya shiga ku dubata" Daddy ya ce "ok." Dr. na gaba suna biye har d'akin da aka kwantar da Arfat, Mummy da hanzarinta ta k'arasa wurin gadon da Arfat ke kwance, ta ce " sannu Arfat " Abeed shima K'arasawa ya yi wurin, ya ce "Mum ke nan, barci fa ta ke yi, ki ke ta faman yi mata sannu". Murmushi kawai Mummy ta yi, ta cigaba da kallon Arfat, fuskarta ta yi fayau, har ta d'an fad'a, ta kuma k'ara haske, sai gashin kan ta da barbazu ko'ina har ya kusan rufe kyakyawar fuskarta. Hannu mummy ta saka ta na tattaro gashin har ta hade shi gaba d'aya ya yi baya, sai dai ba ribbon d'in d'aurewa. Kamar Afrat ta San tunanin da Mummy ta ke yi, ta ce "Mummy bari na ciro ribbon d'in kaina sai ki d'aure mata da shi". Mummy ta ce "Yauwa Afrat da kin kyauta kuwa". Daddy ne ya kalli Mummy ta gefen ido ya yi murmushi domin har ga Allah ya na k'aunar matarsa, ko don kyawawan halayenta, domin mace ce d'aya tak, amma tamkar da d'ubu. Likitan ne ya yi magana ya ce. "Ai matsalar ta ta, ba wata babba ba ce, dan stroke ne ta samu sakamakon razana da ta yi, sai dai don Allah hajiya a rik'a kiyaye abinda zai saka ta damuwa don gudun kuma faruwar haka". Mummy ta ce "Insha'Allah Dr. Yanzu zuwa yaushe za a sallame ta"?? Dr ya ce "ko gobe ma za a iya sallamar ta" Mummy ta ce "Allah ya kai mu" Suka amsa da ameen. Daddy ya ce "Yanzu ya za a yi, za ku koma gida ne ku shirya ko kuwa?? Don na ga ba ku d'auko ko mai ba". Mummy ta ce "Gaskiya ni Alhaji ina nan, sai dai ko ku je da afrat, ta dawo tare da jummai ko da abinda za ta yi mana anan". Kwa6e fuska Afrat ta yi, kamar za ta yi kuka ta ce ta ce "Mummy nima gaskiya ina tare da ku" Murmushi Daddy ya yi, ya ce "Mummyn yara ke nan to kin ji abinda 'yar ta ki ta ce ita ma,saboda haka duk ku taso mu tafi gaba d'aya kwa dawo daga baya, tunda kun ji Likita ya ce sai zuwa 8pm ko zata tashi, kun ga kuma kwa shirya a tsanake, tun da akwai nurses masu kula da patients". Mummy ba a son ranta ba ta tashi sai don kar ta yiwa Daddy musu. Gaba d'ayan su suka fito da niyyar komawa gida, har Abeed don dai shima a gajiye ya ke lik'is don tun farkon faruwar al'amarin baya samun cikakken barci, don gudun abinda zai je ya dawo. Abeed ne ya fara shiga motarsa shi da afrat suka tafi, sannan Daddy suka shiga ta su, shi da Mummy manu driver ya ja suka tafi. Bayan sun fara tafiya ne, Afrat ta juyo da dubanta zuwa ga Abeed ta ce "Ni kam bros abinda ya faru yana ba ni mamaki ba kadan ba, wai ta yaya mummy za su ce ba su, suka haifemu ba, bayan dai dai da minti d'aya ban ta6a ganin sun nuna wani abu da zai nuna ba su suka haifemu ba." Abeed ya ce "Ba ke kadai ke mamaki ba Afrat, ni kai na abin ya yi masifar d'aure mun kai, a ce dukan ku, ku biyu ba su suka haife ku ba, duk da cewa, duk wanda ya kalleku ya san ciki d'aya kuka fito don tsananin kamar ku." Afrat ta ce " wallahi bros babban burina yanzu bai wuce na san su waye suka haife mu ba, kuma na san ta yadda mu ka zo hannun su mummy.... " Sai kuma wasu hawaye suka fara saraftu a fuskarta....... Auntie M Jabo 🍃 & Mum Twin💫AN YI WALK'IYA 31_32💫 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA K'arfe takwas na dare, gaba d'ayan su sun hallara parlourn Daddy, kamar yadda aka saba Daddy ne ya fara magana kamar haka "mummyn ku ta sanar da ni duk abinda ku ke ciki musamman ma Arfat akan maganar da aka fara kwanakin baya ba a k'arasheta ba, sakamakon wasu dalilai, amma bayanin da ta zo mun da shi yanzu ya nuna bayyana muku ainihin maganar shi zai samar muku da kwanciyar hankali a zuciyarku don haka muka yanke shawarar sanar da ku ainihin labarin iyayenku." A iya sanin mu iyayenku mutanen kirki ne, domin duk tsawon shekarun da muka shafe tare ba mu ga wani mummunan hali a tare da su ba, asalima ba 'yan nan k'asar ba ne,yan k'asar nijar ne,Allah ne ya hada mu da su kusan shekaru ashirin da biyu da suka wuce. A wancan lokacin ba a wannan unguwar muke ba, muna wata unguwa da ake kira tarauni, anan dai cikin birnin kano, wata rana muna zaune ni da mummyn ku da dare bayan sallar magrib, wani yaro ya shigo ya ce "wai Ana sallama da ni a waje". Na ce "da shi ya ce ganin zuwa, bai dade da fita kuwa nima na fita. Sai dai wad'anda na tarar a tsaye a wajen, abin ya matuk'ar ba ni mamaki, don ban San fuskokinsu ba, a haka dai na tsaya muka gaisa, namijin ne ya fara magana cikin hausar sa wadda ba ta fita sosai, don kana ganin su ka san buzaye ne, "Alhaji alfarma muka zo nema a gurinka" Na ce "Allah yasa zan iya" Ya ce "suna so ne idan da hali su zauna tare da mu, shi zai riqa yi mana gadi, matarsa kuma zata rik'a taya hajiya aiki" Na d'an yi Jim! Na d'an lokaci, sannan na ce "gaskiya ni ba ni da sha'awar mai gadi, domin a wancan lokacin arzik'i na bai kai haka ba, ina da kudi daidai gwargwado, don kusan layin da muke ba wanda ya kama k'afar arzik'i na. Anan dai suka hau yi mun magiya, har matar da suke tare ta matso wurin da nake tsaye, ta durk'usa ta ce "don Allah Alhaji ka taimaka mana, don idan muka bar nan ba musan in da zamu dosa ba, duk inda muka je gudun mu ake yi, wani wuri har jifan mu aka yi, aka mana korar kare", ta k'arashe maganar da sakin kuka mai ban tausayi. Har cikin raina na tausaya musu, sai dai tunanin yadda duniya ta lalace, nake yi ka yi wa mutum alkhairi ya saka Maka da sharri, tun a wancan lokacin ma, bare yanzu da komai ya k'ara ta6ar6arewa. Duk da wasu ke 6ata wasu, ba duka aka taru aka zama d'aya ba. Saboda haka na ce da su "yanzu ka ga ni ban San ku ba, ban san abinda ya fito da ku daga gida, ka ga kuwa haka kuram bana d'auke ku na kai gidana ba". Ya ce "Alhaji wallahi mu ba mugaye ba ne, k'addara ce kawai ta fito da mu daga gida , sakamakon wani iftila'i da ya faru... Mu 'yan kasar nijar ne, nijar d'in ma wani k'ungurimin daji, a nan cikin dajin k'auyen mu yake, mai suna Salmau , mutanen k'auyen gaba d'aya ba mu wuce 200 ba, kuma kusan dukanin mu dangin juna ne, muka taru muka tada k'auye guda, don ko aure a tsakanin mu ake hadawa. Wata rana da daddare muna kwance wata iska mai k'arfi ta taso, kanka ce me, ta fara tuge mana 'yan bukokin mu,anan fa hankalin mu ya tashi, nan da nan aka tsuge da wani irin ruwa mai tsananin k'arfi, a hankali ruwan ya fara tafiya da mutane, kan wani lokaci kusan rabin duk ruwa ya tafi da su, wasu kuma ruwan na Jan su,, suna ihu, ba muda abinda za mu iya musu, haka muka hak'ura muka kyalesu, don muma Allah ne ya yi da shan ruwan mu a gaba. Ko da gari ya waye, wadanda suka tsira ba mu da yawa, kusan duk an mutu, wasu ma ba a ga gawawwakinsu ba, ciki kuwa, har da iyayen mu da sauran 'yan uwan mu na jiki. To tun daga faruwar al'amarin muka yanke shawarar barin garin, ni da mai d'akina, amma mun sha bak'ar wahala kafin mu zo nan Alhaji. Daddy ya juya ya kalli Arfat da Arfat da tunda aka fara ba su labarin idon su ke zubar da hawaye ya ce "a gaskiya a yanda mahaifinku ya sanarda ni, ba k'aramar wahala suka sha kafin su k'araso k'asan nan ba, don ya ce tun daga k'auyen su har zuwa garin marad'i a k'afa zuka je, kasancewar a wancan lokacin ba hanyar abin hawa da zata kai mutum cikin gari, sai keken shanu, shi kuma duk masu irin aikin haddasu iftila'in ya shafa. Sai da suka shafe kusan wata uku da kwanaki suna tafiya kafin su isa, ga shi ba su da wani wadataccen guzuri, suka yi ta fama da matsananciyar yunwa, wani lokacin har da k'ishi...... Auntie M Jabo 🍃 & Mum Twins 😍 [ 💫AN YI WALK'IYA 23-25💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Mummy na tashi daga nan straight 6angaren Daddy ta nufa, a zaune ta same shi, ita ma neman kujera ta yi ta zauna jikin ta duk a mace, sannan ta ce "Alhaji yaran can fa suna can duk sun d'aga hankalinsu akan maganar da suka ji, ya kamata a musu bayani ko hankalinsu zai kwanta." Daddy ya ce "haka ne, dama ai dole a yi musu bayani, 6acin da raina yayi ne na taho ba tare da na musu bayanin komai ba." Mummy ta ce "hakuri za ka yi Alhaji ka san sha'anin yaro", Daddy ya ce "Ai shi ke nan, ya wuce, yanzu kin ga lokacin sallah ya gabato, bari na je masallaci, kafin na dawo kuma kun yi sallah, sai mu kuma wani zaman". Mummy ta ce "hakan za a yi, bari nima na tashi". Bayan an idar da sallah, Daddy da Abeed tare suka dawo daga masallaci, da ganin fuskar Abeed kasan yana cikin rud'u, Mummy kuwa ita da su Arfat tuni suma sun idar da ta su sallar, zaman jiran dawowar Daddy Kawai su ke yi, sai da suka nemi waje suka zauna, sannan Daddy ya fara magana. "D'azu na gaya muku mun yanke shawarar had'a auren kai Muhammad tare da 'yar uwarka Arfat! Ba don komai muka yi hakan ba, sai don sanin akwai aure tsakaninku, tsaftatacce ma kuwa, wanda Allah (S W A) ya halatta muku". Tuni fuskar Abeed ta sark'e da ta Arfat, suna kallon junansu, dukaninsu mun hango tsabagen mamaki a idanuwansu, Daddy ne ya katse musu tunani ta hanyar cigaba da magana "domin kuwa a cikin ku akwai wanda ba mu muka haifa ba...!!! Gabansu ne ya tsananta fad'uwa, har afrat dake gefe tana matsar k'walla, da sauri Arfat ta fad'a jikin Mummy tana kuka take fad'in Mum don Allah mu dai kar ku ce ba ku kuka haifemu ba, don duk duniyar nan ba mu San kowa ba sai ku Mummy," k'arashe maganar tare da sakin wani irin kuka, rungumeta Mummy ta yi tsam, kamar za'a k'awata ta ce "Arfat dama kaf duniyar nan mune iyayenku kowa yasan haka, kada ma ki yi shakkar haka, wannan maganar an taso da ita ne kawai don a warware wata matsalar". Sai kuma ta juya wurin Daddy tana fad'in "Alhaji don Allah abar maganan haka, tunda dai an gaya musu akwai aure a tsakaninsu, kuma sanin kan su ne ba za mu had'a haramtaccen Abu ba don son zuciyar mu, shi yasa tun fil'azal ban so aka bayyana wannan sirrin ba, don ni a tunani na barin zai fi mana kwanciyar hankali". Murmushi Daddy ya yi, ya ce "Maryam ke nan gwanda da kika ce a tunaninki, amma maganar gaskiya barin wannan maganar ba shi ne mafita ba, domin yin hakan shi zai haddasa tashin tashina a tsakanin su yaran". Abeed da tun dazu bai ce komai ba, idan ban da wulla ido da yakeyi, dak'yar ya kalato wani yawu ya had'iye a bushashshen mak'ogwaronsa, sannan ya ce "Mummy gaskiyar Daddy, don mu kanmu idan aka fayyace komai sai mun fi samun kwanciyar hankali". Jinjina kai mummy ta yi, tare da d'ago da kan Arfat dake kwance a cinyarta ta ce "Arfat kin ji abinda d'an uwanki ya fad'a kin amince a bayyana komai"??? Da k'yar Arfat ta iya d'aga kanta ta nuna alamar eh, don ita kadai ta san halin da take ciki. Daddy ne ya cigaba da fad'in " Gaskiyar magana Arfat da ke da afrat ba mu, muka haife ku ba.!!!" Dam! dam!! K'irjin Arfat ya dinga bugawa, sai kuma ta ji parlourn gaba d'aya yana juya mata, cikin k'araji ta ce "Mum kin ji abinda Daddy ke fad'a ko"?? Wai ba ku ka haife........ Sai kuma ta yi dif sakamakon duhun da taga ya mamaye mata idanuwa,, nan da nan ta yi baya da niyyar faduwa. Da sauri Abeed ya rik'ota ta fad'a jikinsa, sai dai gaba d'aya babu alamar numfashi tare da ita. Afrat da gudu ta yi kanta tana fad'in "sis Arfat don Allah kar ki mutu ki bar ni! Mummy don Allah ku gaya mata ku ne kuka haife mu, ta tashi". Sai kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, ita kanta mummy kuka take yi sosai, cikin kukan ta ce "Alhaji ka ga abinda na guda ko?? Domin nasan halin Arfat da saka abu a rai, yanzu wannan maganar zata iya janyo mata wani ciwon". Daddy ya ce "yanzu ba lokacin tsayawa yin wannan maganar, a yi kokarin ceto rayuwar ta tukun". Sai ya kalli Abeed ya ce "Muhammad dubo numbern Dr. Usman, ka kira ka ce ya zo yanzu ina neman sa". Abeed ya ce "Dad ai da d'aukan ta a ka yi kawai aka wuce da ita asibiti kaitsaye da zai fi, ko da asibitin Dr. Usman d'in ne, tunda kusa ne, ba nisa sosai." Daddy ya ce shike nan hakan za a yi, nan da nan Abeed ya suri Arfat, bai ajiye ta ko'ina ba sai bayan motarsa, bai jira fitowar su Mummy ba, ya ja sai asibiti....... Www.hauwajabo.blogspot.com Www.jabohauwa.WordPress.com Auntie M Jabo 🍃 & Mum Twins 😍 [4/11, 8:36 PM] Eve Jabo: 💫AN YI WALK'IYA 💫 33 & 34 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA Haka suka yi ta fad'i tashi har suka iso garin Kano. To bayan ya gama ba ni labarin nima na shigo na sanarda Mummyn ku, da yake akwai ta da tausayi nan da nan ta amince, mu ka yanke shawarar mahaifinku zai rik'a yi mana gadi, ita kuma ummanku idan Allah ya sauke ta lafiya za ta rik'a taya Mummyn ku aika_aikacen gida, da yake ko da suka zo tana d'auke da tsohon cikin ki, ya nuna Arfat da hannu. Ba su dade da zuwa ba kuwa, aka haifeki, yarinya mai kyau da ke, ga farin jini, kusan ko da yaushe a wurin Mummyn ku kike wuni, kasancewar ta mai son yara, don haka ba k'aramin sabo ku ka yi ba. Ba ki fi 2 years ba ta haifi Afrat , don haka Arfat sai ta koma hannun Mummy da zama gaba d'aya. A kwana a tashi ba wuya, ita ma afrat ta fara girma sai ta nuna, ta fison zama gurin Mummyn ku akan gurin ummanku, don wata rana da kuka take tafiya idan ta zo d'aukanta, Mummyn ku ta ce ita ma a kyaleta a wurin ta tunda ta fison nan, ummanku sai dai ta yi murmushi kawai, don akwaita da kawaici, kuma tana Jin dad'in yadda Mummyn ku, ke nuna k'aunarta a gare ku. Haka rayuwan mu ta cigaba da kasancewa har zuwa ranar, wata juma'a da ba za mu manta da ita ba, muna kwance misalin k'arfe biyun dare, wani irin k'auri ya tashe mu, a firgice muka fito harabar gidan, ai kuwa nan da nan muka hango wani irin hayak'i yana tashi daga boys quarters , ba shiri muka nufi can, ashe wuta ce ta kama, wadda ba mu san musabbabinta ba har yau, domin ko da muka je mahaifanku babu mai sauran numfashi, domin 90% na jikin su duk ya k'one." Hawaye ne kawai ke zubowa daga fuskar su Arfat tare da maimaita Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'un! Daddy ya cigaba da fad'in "duk abin nan da ke faruwa Abeed baya nan, yana k'asar Cyprus don tun yana da 4 years k'anina ya dage yana so a ba shi Abeed d'in don ya fara makaranta acan, don akwai makarantar da yaransa ke yi, da yake shi ya riga ni fara tara iyali, don wasu daga cikin yaransa duk sun girmi Abeed. Bai dawo Nigeria ba, sai da ya gama secondry school, sai dai mu muna ziyararsa time to time, kuma tun a wancan lokacin dama an gaya masa yayi k'anne don har pictures d'in ku ana tura masa. So that da ya dawo, ya tafi a zuwan ku kannensa ne uwa d'aya uba d'aya, don ko dangina na yi musu kashedin kar wanda ya sanar da ku, har sai lokacin da muka yanke, don ko da wannan maganar ba ta taso ba, mun yanke shawarar gaya muku, idan dai wa'adin da muka saka ya cika,sai ga shi kuma haka ta faru. Wanna shine abinda muka sani game da iyayenku". Arfat tashi ta yi daga in da take zaune, zuwa gurin da Mummy da Daddy ke zaune ta fara magana cikin kuka ta ce "Mum, Daddy ba mu da bakin da za mu gode muku, sai abinda na sani bakunan mu baza su ta6a daina muku addu'ar alkhairi ba, har sai ranar da numfashinmu ya bar jikin mu, haka iyayenmu daga yau za mu saka su cikin addu'a har ranar da Allah zai kar6i rayuwar mu, don addu'ar mu garesu shi zai sa su yi alfahari da haihuwar mu". Na yi matuk'ar farin ciki da suka, zama iyayenmu, domin babbar fargabata bai wuce a ce ba mu da iyaye ba, sai ta saki wani murmushi wanda yayi dai_dai da gangarowar wasu hawaye masu sanyi a fuskarta ta ce "Alhamdulillah! Daddy ne ya kalli gefen da Abeed ke zaune ya ce "Muhammad ka ji labarin 'yan uwanka, hope za ka rik'eta da amana tunda dai ka ji marainiya ce ". Hmm! Kawai Abeed ya ce tare da mikewa tsaye yana fad'in " ni duk na gaji dad, bari na je na d'an kwanta, na huta". Bai jira abinda za su ce ba ya wuce abinsa. Dukansu zuba masa ido suka yi, suna karantar wani abu a tare da shi, sai dai ba su kai ga lalubo amsar ba ya wuce. Yana zuwa d'aki ya zube akan gadonsa, yana sauke wata naunanniyar ajiyar zuciya, ya d'aga kan shi sama yana kallon fan, nan da nan ya Lula duniyar tunani..... Mum Twins 😍& Auntie M Jabo 🍃 [4/12, 9:00 💫AN YI WALK'IYA 💫35_37 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA Ya fi k'arfin 1hr a kwance, yana tunani sai dai ya kasa lalubo mafita, don haka ya mike tare da sakin tsaki, key d'in motarsa ya d'auka ya yi waje, daga nan bai zarce ko'ina ba sai gidan su mubarak. Ya taki sa'a kuwa ya same shi, mubarak ne ya fito da murnarsa sai dai yanayin da ya ga abokin nasa ne ya sa gwiwarsa ta yi sanyi, ya ce "mutimina ya dai??? Na gan ka wani iri, me ya faru ne?? Tsaki Abeed ya kuma ja, sannan ya ce "wallahi wata matsala ce, ta dabaibaye ni, na rasa ya zan 6ullowa al'amarin gaba d'aya kai na ya kulle shi yasa, ka ga na zo wurinka, ko akwai mafitar da za ka nema mun". Mubarak ya ce "ina jinka abokina, gaya mun abinda ya faru". Abeed ya ce "ai maganar ce, fad'arta ma abun kunya ne, a gurina don na yadda da kai ne shi yasa ma har na zo gurinka, amma abun mtsss....... Sai kuma ya yi shiru yana girgiza kai, Go on, mubarak ya fad'a, tare da nuna alamar k'aguwa ya ji zancen. Abeed ya ce "tunda na zo ai dole na gaya Maka, nan da nan ya juyewa mubarak duk abinda ya faru. Murmushi mubarak ya yi, tare da cewa "Abeed ai wannan had'in na ku, ya yi wallahi, mai abun kunya a nan?? Ni da farko da ka fara magana na d'auka wani mugun abun kunya ka...... Abeed ya katseshi sakamakon d'aga masa hannu da ya yi ya ce "ya isa haka, ban saka ka dogon surutu ba, ni dai kawai na zo ka ba ni shawarar yadda zan su6ucewa auren ne, ba tare da ran su Daddy ya 6aci ba". Mubarak ya ce "Abeed idan dai shawarar kwarai ka ke so, to kada ka yarda ka bijirewa auren Arfat, don aurenku ba

Chapter 4 of 5