k'aramin da cewa ya yi ba.
Hannu Abeed ya d'aga masa a zafafe ya ce
"ta ina muka dace??? Tana matsayin 'yar mai
gadi,kuma' yar mai wanke_wanke da shara, ba
dacewa sam a tsakanin mu".
Galala mubarak ya yi, yana kallonsa, ya ce
"Abeed ai wannan sirrin gidan ku ne, ba wanda
zai san da haka, sai dai idan ku kuka fasa kowa
ya ji."
Abeed ya ce
"ta yaya za a ji zan auri k'anwata, ka ce duniya
ba ta tambayi ta yaya haka ya kasance ba,
kuma sanin kan ka ne dole'yan matan da suka yi
haukan so na, su yi mun dariya kuma ajina ya
zube k'asa wanwar, idan an ji, zan aure 'yar
maigadin gidanmu".
Mubarak ya ce
"gaskiya ka yi nisa ba ka Jin kira, amma ni ban
ga aibun wannan auren ba".
K'wafa Abeed ya yi, ya ce
"yayi kyau", daga haka bai kuma cewa komai ba
ya shuri takalminsa ya fice, mubarak yana ta
k'wala masa kira bai saurareshi ba, ya yi gaba.
Arfat kuwa tunda haka ta kasance, ta karbi
za6in da aka musu hannu bibiyu, domin ta yi
alk'awarin yi ma su mummy biyayya matuk'ar
abinda suka sakata bai sa6awa shari'a ba, abu
d'aya ta ke tunani ta yadda za ta kar6i Abeed a
matsayin miji, bayan kallon da ta ke masa na
d'an uwanta shak'ik'i, duk da dai ya hada duk
wani abu da take buk'ata a d'a namiji, murmushi
ta yi, sannan ta lumshe idonta, afrat da ke
gefenta a zaune tana daddanna phone ta ce
"sisto ke da waye ne??
Kike ta faman murmushi "?
Zaro ido Arfat ta yi ta ce yaushe?? Don bata san
ma ta yi ba,, nan da nan afrat ta d'ago ta, ta yi
murmushi ta ce
" share kawai "
Kwanaki sai tafiya suke yi, amma har yanzu
Abeed ya k'i tsayawa ya yi magana d'aya, duk
lokacin da aka taso da zancen aurensu da Arfat
sai yayi ta hanya_hanya.
Har Daddy ya gaji yau ya titsiye shi akan sai ya
gaya masa, mai ya ke nufi ne akan maganar
aurensu.
Daddy ne ke ce da Abeed
"ba ka ji abinda na fad'a ba ne ka yi shiru??
Sosa k'eya Abeed ya hau yi, ya ce
"Wallahi Daddy dama...... Sai kuma ya yi shiru,
Daddy ya ce
"dama me??
Ya cigaba da fad'in
"wai da an ba ni dama na nemi wata, saboda
gaskiya ni.... Sai kuma ya kuma yin shiru, a
zafafe Daddy ya ce
Ka cigaba da magana kar ka 6ata mana lokaci.
Abeed ya cigaba da fad'in
"gaskiya Daddy ba class d'ina ba ce saboda....
Ai bai ka ga K'arasawa ba Daddy ya d'auke shi
da mari, sannan ya nuna shi da hannu ya ce
"ban k'ara tabbatar da ba ka da tunani ba, sai
yau, to wallahi idan kana son ka ga tsantsar
6acin raina ka bijirewa auren nan, don akan
maganar nan zan iya sa6a Maka fiye da yanda
ba ka zato".
Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya fice
daga parlourn fuuuu! Mummy ma ta bi bayansa.
Auntie M Jabo 🍃 & Maman Twins
💫AN YI WALK'IYA 💫38_40
©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo
®NWA
Jiki a sanyaye Arfat ita ma ta mik'e ta nufi
dakin su, Afrat ta bi bayanta, tana rarrashinta,
don ta hango damuwa a idon yayarta ta k'arara.
Ya rage saura Abeed a wurin, yana tunanin me
abin damuwa akan abinda ya fad'a, bayan
gaskiyar abinda ke zuciyarsa ya fad'a, tabbas da
a ce Arfat iyayenta ba su kasance mak'ask'anta
ba, da ba abun da zai hana ya aureta, don tana
da sifofin da yake so macen da zai aura ta
kasance da su,da wannan tunanin ya bar wajen.
2 weeks later, tun daga ranar da Daddy ya
tadawa Abeed maganar, bai kuma ce da shi
k'ala ba har yau, ya zuba masa ido ne kawai
yana jira ya ga ya saduda, ya bada kai bori ya
hau.
Ashe shi bai san Abeed yana can yana shirin
tafiya ba, don har ya yi visa, ya siye ticket na
tafiya k'asar Cyprus, gurin Baffa Abbakar.
Sai tashi suka yi suka ga ba Abeed alamar sa,
da farko sun za ci ya je office ne,sai aka yi ta
kiran phone d'in sa is switched off, don haka
Daddy ya kira office d'in su aka ce rabonsa da
zuwa office, tun shekaran jiya, nan fa hankalin
su mummy ya fara tashi.
Wasa_wasa an doshi kwana uku ko labarin
Abeed, ba su ji ba, duk wanda ke gidan
hankalinsa ya kai k'oluluwar tashi, idan ka cire
Daddy, don shi cewa ya yi duk inda ya je, shi ne
mai dawowa da kansa.
Washe gari sai ga Baffa Abbakar ya kira, yana
shaidawa Daddy Abeed ya zo wurin su, kuma ya
sanar da shi duk abinda ya faru.
Ran Daddy ya yi matuk'ar 6aci don haka ya ce
da Baffa Abbakar duk abinda ya ke yi ya ajiye
ya taso k'eyar Abeed su dawo tare.
Baffa Abbakar ba yanda ya iya,dole ya
amince, don bai isa ya yiwa Daddy musu ba.
Bayan ya gama wayar ne ya zayyanawa Mummy
duk abinda ya faru. Ita ma ta yi mamakin abinda
Abeed ya yi, sai dai yanda ta ga ran Daddy ya
6aci, ta danne na ta mamakin, ta hau ba shi
hak'uri don ta san, in dai ransa ya 6aci irin haka
komai yana iya faruwa.
Yau ta kama asabar, wurin 2pm su Abeed suka
iso, shi da Baffa Abbakar, sun samu kyakkyawar
kulawa daga wurin mummy. Tun wurin la'asar
gidan ya fara cika da 'yan uwan Daddy kai har
da na Mummy, don duk wani d'an uwa na jiki ya
zo, sakamakon gayyatar da Daddy ya musu na
emergency meeting da za a yi after magrib.
Sai wurin magrib Daddy ya dawo, bayan sun yi
sallah gaba d'ayan su sun hallara, har Baffa
Abbakar. Daddy ya fara magana.
"Alhamdulillah! Ba abinda zan ce da Allah sai
godiya, da ya nuna mun wannan ranar da na ke
son sauke wani nauyi da ya rataya, a wuyana
shekara da shekaru, hak'ik'anin gaskiya na ji
dad'in kasancewar ku anan don ku zame mun
shaida akan abinda zan fad'a, sanin kan ku ne
abubuwa da dama sun faru a shekarun baya,
kwanakin baya an warware wani sirri da ya
dad'e a binne, haka ma yau ina tabbatar mu, da
cewa, zan bud'e d'ayan sirrin, duk da dai ku, kun
san komai, amma shi wanda abun ya faru akan
sa bai sa ni ba.
Sai ya juya 6angaren da Abeed ke zaune ya ce
"Muhammad a yau ina bak'in cikin sanar da kai
cewa ba mu muka haifeka ba, hasalima har
maganan da na ke yi yanzu ba musan iyayenka
ba....!!!
Mum Twins 😍 & Auntie M Jabo 🍃
[4/16, 16)4:36 PM] MRS SAIF ✍🏻: 💫AN YI
WALK'IYA 💫41_50
©Mrs Saif & Hauwa M Jabo
®NWA
Tashin hankali wanda hausawa suka ce
"ba'a saka masa rana " don kuwa Tashin
hankalin da muka hango cikin idanun Abeed ba
zai ma misaltu ba, don dara_daran idanunsa sun
k'ank'ance sun yi jajir kamar an zuba kwanon
barkono a ciki,ya jik'e jagab da gummi duk da
sanyin AC da ya game parlourn.
Da kyar ya iya Jan jiki, ya je gurin da Daddy ke
zaune, dafa k'afafuwan Daddy ya yi cikin k'uncin
zuciya ya fara magana, daga ji ka san yana
cikin tsananin rud'ani ya ce
"Daddy don Allah ka yafe mun abun da na yi
maka, kada ka hukunta ni ta haka, idan don
auren Arfat ne Daddy wallahi ina son ta, kuma
zan aureta, amma kar ku ce ba ku kuka haife ni
ba".
Murmushi Daddy ya yi sosai ya ce
"yaro dai yaro ne amma, idan ban da abun ka
Abeed haka kurum, zan k'irk'iri k'arya na fad'a,
har na tara mutane irin haka, ko dai ka dimauce
ne ba ka ga jama'ar da ke wurin nan ba???
To bari ka ji wannan maganar haka take duk
wanda za ka tambaya haka zai gaya ma. Don ni
da Maryam ba mu ta6a haihuwa ba, mun dad'e
muna neman haihuwa, mun yi yawon asibiti gida
da da waje amma Allah bai ba mu ba, duk in da
muka je za a ce da mu, ni lafiya ta kalau,
Maryam ce mai matsala, sai dai ko ita ana sa
ran zata iya haihuwa nan gaba, a haka har muka
share 10yrs da aure shiru, ita kuma ga ta da
masifar son yara, ni kuma tsananin son da na ke
mata ya saka ba zan iya had'ata da wata ba.
Don haka muka yanke shawarar zuwa gidan
marayu, mu d'auko yaro,don ya rik'a debe mana
kewar yara.ko da muka je kuwa mun ci sa'a an
kawo ka, wai an jefar da kai a bayan layi, to
tunda muka d'ora idanmu akan ka Allah ya
jarabe mu da tsananin k'aunarka musamman
Mummyn ku, don kana jariri sosai a lokacin,
bayan mun gama cike_ciken takardun da aka ba
mu, daga nan asibiti muka wuce don duba
lafiyarka, da kuma bawa maryam shawarwari ta
hanyar da zata bi ta samu ingantaccen ruwan
nono, don ta yi k'ememe ta ce ba za ta ba ka,
madara ba, sa dai ta shayar da kai da kanta.
Wannan shi ne takaitaccen labarinka, sai ya
yiwa Mummy nuni da ta mik'awa Abeed
takardar da ke hannunta, kar6ar takardar ya yi
hannu na rawa, yana dubawa, takarda ce ta
yarjejeniyar kar6ar yaro a gidan marayu, duk
dauriya irin na Abeed, sai da ya zubar da
hawaye, don takardar da ke hannunsa sai da ta
jik'e jagab da hawaye.
[4/16, 4:37 PM] MRS SAIF ✍🏻:
Duk wanda ke parlourn sai da ya tausaya masa,
ni kaina maman Twins na tausayawa Abeed
matuk'a, juyawa na yi wurin da Jabo ke zaune,
na ce
"gaskiya Jabo Abeed ya ba ni tausayi ba kadan
ba"
Ta ce
"gaskiya nima na tausaya masa, amma ai
gwanda da aka yi WALK'IYA fuskar kowa ta fito
ras.
Na ce
"haka ne kuma fa, kin ga AN YI WALK'IYA mun
gano fuskar Abeed a zahirinta na gaskiya, ba
wancan fuskar da mu ke gani a da ba".
Mun shagala da surutu, ashe Daddy har ya
cigaba da magana, sai tsinkayo muryarsa muka
yi, yana cewa
"don haka ke Arfat, kin ji asalin Abeed, idan kin
amince sai a saka lokacin bikin ku nan ba da
dad'ewa ba, Murmushi Arfat ta yi ta ce
"Daddy kune iyayen mu duk abinda kuka zartar a
gun mu dai-dai ne,"
Murmushi Daddy ya yi ya ce
"Allah ya miki albarka, sannan ya juya gurin
Abeed ya ce
"na dawo gareka, duk da dazu ka ce ka amince,
amma yanzu ina so na k'ara tabbatarwa shin ka
amince kuwa???
Gyda kai Abeed ya yi tare da cewa
"Daddy wallahi na amince"
Daddy ya ce
To, Alhamdulillah! Don haka na yanke shawarar
d'aurin aurenku nan da 4wks, duk wanda ke
parlourn sai da ya washe ba ki, ana fad'in Allah
sanya alkhairi.
Sannan Daddy ya ce
"idan akwai mai son magana ya zo ya yi, an ba
shi dama, kowa ya ce ba shi da magana, sai
Mummy ta ce
"ita akwai abinda za ta ce.
Ta ce "ita Jan hankalinta akan yaran ne, don kar
su ji an ce basu suka haifesu ba, tsiro da wasu
halaye, ko kuma su rik'a jajjanye jikin su, na fiso
ku cigaba da halanyanku kamar yadda muka
saba, kada ku saka wani abu a ranku, mu ne
iyayenku, kowa ya San da haka, don ko yanzu,
ba kowa zai san halin da ake ciki ba, don mun
yadda da danginmu, mutane ne masu rik'e sirri,
da haka na ke mik'a godiya ta a gareku, Allah ya
mai da kowa gida lafiya.
Gaba d'aya aka amsa da ameen.
[4/16, 4:41 PM] MRS SAIF ✍🏻:
Kwanaki na tafiya biki na dad'a kusantowa,
amma ango da amarya sai wasan 6uya ake yi,
sukan su Mummy sai shirye_shiryen su ke yi,
Abun ba kama hannun yaro.
Can muka hango amarya Arfat, ta yi hanyar
shiga d'akin angon na ta, da sauri muka bi
bayanta don kar a yi ba mu.
Akan gado ta same shi a kwance, ya yi
rigingine, da sauri ya mike Jin muryarta, tana
sallama, amsa sallamar ya yi, sannan ta nemi
wuri ta zauna, ta ce
"ya Abeed, sai da ya ji wani iri, a ransa don
yadda lafazin sunansa ya fita a bakinta, don
yanzu har ga Allah yana Jin son Arfat har cikin
zuciyarsa, kawai kunyar abinda ya faru ne, ya
saka ya kasa zuwa su fahimci juna.
Itama Arfat ta fuskanci haka, shi yasa ta ajiye
tata kunyar ta zo, sai da ta kuma maimaita
sunansa sannan ya amsa.
Ta ce
"haba ya Abeed kullum mummy sai ta yi zancen
mun k'i mu shirya kanmu ga biki sai kusantowa
ya ke, that's why na zo yanzu, ko dai har yanzu
ban yima ba, ta k'arashe maganar da sigar
zolaya.
Waro ido waje ya yi, ya ce ni na isa, kawai dai
ina tuna abinda ya wuce ne , please Arfat for
give me, I beg you".
Arfat ta ce
"come on, bros ka daina tuna abinda ya wuce,
idan ka na tuna abinda ya wuce baza ka yi
rayuwa mai dad'i ba, ni dama ban rike ka a
raina ba. Murmushi Abeed yayi.
Ya ce
"thanks so much, my everlasting wife"
Ita ma Arfat Murmushin ta yi, sannan suka jero
tare don fitowa daga d'akin, ai kuwa suka yi
kici6is da Afrat za ta wuce, sai ko ta hau tafi
raf! raf!! raf!!!
Tana fad'in mummy don Allah yi sauri ki zo ki
ga mutanen ki.
kai sisto, kin ga yadda kuka yi matuk'ar
dacewa?? Let me give you a snap, sai kuma ta
ce "af! ashe wayar ma yana parlour.
Bari na yi sauri na d'auko phone d'in, sai ta juya
da sauri, dariya suka yi sosai Arfat ta ce
"kai Afrat ba dama, sai mu yi ta jiranta fa take
nufi,Abeed ya ce
"ni kai na sai na ga hoton zai bada meaning,
kawai mu jirata, Jan hannunsa Arfat ta yi, tana
cewa mu je ni dai don ina da abin yi.
A kwana a tashi, ba wuya wurin Allah, ga shi
har an shiga satin bikin su Arfat, tun farkon
satin ake shagali iri_iri, don ayi events kala_kala
wasu ma ba mu ta6a Jin sunan su ba, har kawo
yau da dubun dubatar al'umma suka shaida
daurin auren ABEED & ARFAT akan sadaki 50k.
Dare na yi aka sada amarya da tamfatsetsen
gidanta mai kama da aljannar duniya, k'arfe
goma angon ya shigo da abokansa akayi sayen
baki na alada aka bar ango da Amaryar sa,ya
umurceta da si tashi, suka gabatar da nafila,
sannan ango ya ciyar da amaryarsa, shima ya
ci, suka yi hani'an, sai ga ni muka yi Abeed ya
nufo inda muke la6e ya ce
"don Allah ku fita haka, d'aukan rahoton kuma
ya isa haka, wanda kuka yi a baya ma ya yi yan
sa ido kawai , sai dai mu ce “Allah ya saka da
alkhairi."
Ba shiri muka fito muka yi waje Jabo sai Harare
hararee takeyi, tun daga lokacin ba mu kuma
waiwayarsu ba sai bayan 1yr, ko da muka je
mun tarar da Arfat da katon cikin, haihuwa ko
yau ko gobe.
Daga nan gidan su mummy muka je, don ganin a
wani hali su ke, abin mamaki, sai muka tarar da
mummy da ciki, katoton gaske don har ya fi, na
Arfat girma.
Bayan sati da zuwan mu mummy ta haihu ta
samu babies d'in ta twins, mace da namiji,
kyawawan gaske, washe gari Arfat ta haihu ita
ma, ta samu baby boy, mai kama da Abeed sak,
murna a wurin wannan familyn ba a magana.
Don sadakar da Daddy ya yi Allah kad'ai ya San
iyakarta, don taron sunan ma hadewa aka yi, an
yi k'ayatacciyar walima, don nuna godiar su ga
Allah, don kuwa naira ta yi kuka da Idonta.
4 month letter, Abeed muka hango da shi da
Arfat, a zaune a garden d'in gidansu, suna huta,
shi kuma babynsu mai amsa sunan SULTAN,
(kasancewar sunan Daddy aka saka masa) shi
yasa suke kiransa da SULTAN, yana zaune a
kyakkyawar walker d'in sa.
Arfat ta zuba masa ido tana kallonsa, Abeed ne
ya matso in da take, ya hure mata ido da iskar
bakinsa, sannan ta sauke ajiyar zuciya, ya ce
"babyna wai mai yasa me ki ne???
Tun dazu sai kallon SULTAN kike yi, ko ya
chanza miki ne??
Murmushi ta yi ta ce
"wallahi kawai ina tunanin yanzu yaron nan
mallakin mu ne, sai na ji kamar a mafarki."
Dariya Abeed ya yi sosai ya ce
"wato yanzu wahala ta wuce, sai dadi, a lokacin
da kina labour, har wasiyya kin ba ni, a zaton ki
mutuwa za ki yi.
Ya cigaba da fad'in "Arfat please ko nan gaba ki
daina yawan fad'ar mutuwa, Allah hankalina ya
matukar tashi, idan kin anbaci kalmar mutuwa
akanki, I know mutuwa dole ce, amma yanzu
zuciyata ta gama aminta da ke, ke kad'ai ce
burina, sai babyn mu and wasu kids d'in da na
ke saran za ki haifa mun nan gaba, babu wata
mace da zata kai ki k'ima a idona, it will be an
empty world without you, my everlasting wife".
K'ank'ame shi Arfat ta yi,
Tana fad'in "haba hubbyna na ce kadai na fad'ar
wannan maganar dukan mu fa marayu ne, I give
you my words, bazan ta6a barinka ba matukar
ina numfashi a doron k'asa.
Rungumeta Abeed ya yi tsam a jikin sa, yana
cewa na gode, k'anwata, Allah ya ba mu tsawon
kwana mai amfani tare da zuri'a d'ayyaba, a tare
suka ce ameen, tare da sakin Murmushi.
TAMMAT BIHAMDULILLAH!
Anan muka sauke wannan littafin, muna fatan
Allah ya yafe mana kurakuran da muka yi abisa
rashin sa ni, ko kuma ajizanci na d'an Adam.
Luv u ol our fans 😘😍😘
Maman Twins😍 da Hauwa M Jabo ke muku
fatan alkhairi 🍃
By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
07039625239
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels