Share this page
3 / 5
mota ya ja da k'arfi da niyyar ficewa daga wurin, dai_dai lokacin Fadeela ta fito.......................... Www.hauwajabo.blogspot.com Www.jabohauwa.WordPress.com By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 M Twins 😍 & Auntie M.Jabo ✍🏾🍃 [4/11, 2:54 PM] 💫AN YI WALK'IYA 10&11 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M Jabo ®NWA Bayan kwana uku Mufeeda da Fadeela suka yi shirin zuwa gidansu Abeed don gaishe da Mumy, sun taki sa a kuwa don sun tarar da Arfat da afrat suna gida, su na yin sallama, Arfat ta taso da sauri ta rungume Mufeeda tana fad'in "oyoyo! Mufeeda yau a gidanmu" ? Kafin ta yi magana, Mumy ta fito, nan da nan ita da Fadeela suka zube su na gaisheta, cikin fara'a Mummy ta amsa musu, sannan ta ce "Mufeeda shiru kwana biyu kin daina lek'o mu". Mufeeda ta ce "eh wallhy Mummy school ne ya 6oyeni", mummy ta ce " ayya!, nima nasan Mufeeda akwai zumunci, to Allah ya ba da sa a", suka ce ameen ". Sai kuma ta kalli Fadeela ta ce da Mufeeda" Wannan k'awarki ce "? Murmushi Mufeeda ta yi tana kallon Fadeela ta ce" eh, Mummy k'awa ta ce " Allah sarki ya sunanta"? Tace" Fadeela ", sannu Fadeela Mummy ta fad'a tare da mik'ewa ta na cewa" Arfat haka za ku bar bak'in naku ba d'an abun ta6awa "? Afrat ta ce" Mummy dama yanzu na ke son tashi", ya dai kamata Mummy ta fad'a tare da shigewa kitchen. Sun sha hira sosai, sannan daga bisani Mufeeda take ce da Arfat ya Abeed na nan kuwa?? Arfat ta ce "a'a, ina za ki ga ya Abeed yanzu, ai sai wurin k'arfe biyar yake dawowa daga office". Mufeeda ta ce "ok, Arfat ta ce" ko ta samu ne "ta fad'a tana murmushi, ita ma Mufeeda murmushin ta yi, sannan ta ce "sosai kuwa, Fadeela ce ke masifar son ya Abeed," Arfat ta ce "wow! ai kuwa ina ganin Fadeela na ji ta kwanta mun a rai, Allah ya sa ya Abeed ya amince, gaskiya da ya yi mata". Sai kuma ta mik'e da sauri ta na fad'in bari na je na sanarda Mummy ta zo ga sirikarta", Fadeela ta hanzarinta ta rik'o hannun Arfat tana Murmushi ta ce "don Allah kar ki gaya mata yanzu bari sai mun tafi Allah kunya nake ji, ita kanta Mufy ta san ba halina ba ne cewa ina son wani kawai na d'auki son yayanki a wani 6angare na k'addarata, amma kwata_kwata mace ta ce tana son namiji baya burgeni", ta k'arashe maganarta da d'an guntun hawaye. Dukan su jikinsu ya yi sanyi Arfat ta ce "in dai mummy ce ba ta da matsala Allah ki daina ma Jin kunya don ta saba ganin 'yan mata kala_kala masu zuwa neman ya Abeed". Har wurin k'arfe shida Abeed bai dawo ba, don haka suka yi shirin komawa gida, mummy ta had'a musu sha tara ta arziki, sannan ta saka driver ya kai su gida. Sai wurin k'arfe bakwai ya shigo gidan , bayan ya yi wanka ya ci abinci, mummy ta same shi tace ta na son yin magana da shi. Murmushin gefen kumatu ya yi sannan ya ce "ina Jin ki Mum". Mummy ta fara magana "Abeed dama akan maganar aurenka ne, gaskiya ya kamata ka nutsu kasan mai kake yi zuwa yanzu, ka ajiye duk wani shirme da ke ranka, ka za6i matar aure ka yi aurenka ya fiye maka, kuma mu ma zamu fi samun kwanciyar hankali, don na gaji da zaryar da 'yan mata ke mana a cikin gidan nan". Juyo da dubansa ya yi sosai gareta, sannan ya ce "Mum yau ma wata ta zo kenan"? Mummy ta ce "eh yarinya mai hankali da kunya da za ka bi maganata da ka nemeta, don daga gani ' yar gidan mutunci ce". Yace "Mum ba ki gane ba ne ni fa duk 'yan matan da ke zuwa gidan nan ba ni na ke cewa su zo ba,in fact wasu ban ma ta6a ganinsu ba, kuma har yanzu ban samu wadda na ke so ba, please Mum adaina takura ni akan wad'ancan ' yan matan wahala ce bata ishe su ba that's all". Da haka ya mik'e yana shirin tafiya Mummy ta ce "yanzu Abeed za ka so ' yan uwanka su Arfat su fad'a irin Wannan halin a fad'i irin abinda ka fad'a a kansu, don nasan yadda ka ke son su". Ya ce "no Mummy nasan ba za su yi irin wannan halin ba, Mummy ta ce" shi kenan dai, idan Daddynku ya dawo za mu tattauna akan maganar, je ka kawai".............. Mum Twins 😍 & Auntie M Jabo 🍃 [4/11, 2:54 PM] 💫AN YI WALK'IYA 21&22💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Haka kuwa aka yi, don bayan teema Daddy ya nemawa Abeed auren 'yan mata sun kai uku, duka' ya' yan abokan sa ne , amma yanda ta kasance da sauran suma haka takasance da su, don duk a cikinsu bai katarin samun yarinyar da ya ke mafarkin aura ba, don haka bai yi k'asa a guiwa ba, wajen neman mafita ba, d'aya bayan d'aya sai da ya nemi hanyar rabuwa dasu. Daddy kuwa ransa ya kai k'ololuwar 6aci, don Abeed ya kunya ta shi a idon abokan sa, kuma ya watsa masa k'asa a ido, yanzu haka yana cikin fushi da shi, kuma har yanzu yana nan akan bakansa, na sai an yi auren kafin lokacin da ya ce ya cika. Yau kamar had'in baki, Mrs Saif dani M Jabo duk mun makara zuwa gidansu Abeed don d'auko muku rahoto, sai after 10pm muka isa gidan, kaitsaye babban parlourn gidan muka nufa, sai dai wayam ba kowa a ciki, said k'arar A.C da kuma T V da ke ta 6a6atu ita kadai, ni kam d'aya daga cikin kujerun dake parlourn na samu na zauna, na juyo da dubana in da Jabo ke tsaye, na ce "Anya Auntie jabo yau za mu samu wani labari kuwa"? Jabo ta ce "ni ma abinda na ke tunani ke nan maman Twins, kalli fa hatta 'yan aikin dake saraftu ko yaushe ba kowa duk sun shige, ko motsin su ba a ji." Na ce "ko dai d'aki za mu bi su ne kawai"? Jabo ta ce "haka ma za mu yi, maybe baza mu rasa wani abu acan ba, nan da nan kuwa na mik'e, muka nufi d'akin Abeed, ko da muka shiga mun tarar ya baje a lafiyayyen gadonsa sai sharar barci sa yake yi, adole muka fito daga d'akin, tunda babu abun rubutu a nan, d'akin su Arfat muka nufa daga nan, sai dai suma duk maganar d'aya ce, don kuwa suma sharar barcinsu suke yi hankali kwance, bayan mun fito daga d'akin su afrat, Jabo ke cewa "ni kuwa Mrs Saif lafiya mutanen gidan nan yau suka yi barci da wuri haka"? Na ce "hmm! Ke ma ke fad'a kin riga ni fad'a ne kawai, amma nima tunanin da na ke yi ke nan, amma bari mu koma part d'in Mummy mu gani ko akwai wani abun d'aukowa a can". Side d'in mummy muka nufa gadan_gadan, parlor muka fara shiga, ba kowa, daga nan muka sulale muka fad'a bedroom d'in ta, nan ma shiru ba kowa, sai muka yi zaton ko tana toilet ne, muka d'an saurara amma ba mu ji alamar mutum a ciki ba , almost 10mnts muna tsaye muna jiran fitowar Mummy ammma shiru, har sai da muka tabbatar wa kanmu cewa Mummy bata part d'in ta kwata_kwata. Ni kam Mrs Saif har na fara tsorata, na juya na cewa "Jabo gaskiya gidan nan ba lafiya ba". Auntie jabo tace "Nima abun ya d'aure mun kai, amma idan ba lafiya ba, ta yaya su Abeed za suna sharar barci irin haka"? Na ce "Da haka kuma, nima ga shi har na fara Jin barci,gaskiya mu je kawai gobe ma dawo, M Jabo tace "ni kaina barcin na ke ji". Har mun fito, da niyyar tafiya sai muka ji kamar sautin kukan Mummy yana tashi daga part d'in Daddy, kasancewar ba nisa tsakaninsu, inkiya Jabo ta yi mun akan na k'araso na ji kunsan Jabo ba Dama wajen jin kwakwaf, sai da na matsa daf da windown da ke d'akin na tabbatar da Mummy ce ke shar6ar kuka, kallon_kallo muka tsaya yi, muna tunanin mai ya saka Mummy kuka irin haka, a cikin Daren nan, maganar Daddy ce ta katse mana tunani, don son Jin abinda ya ke fad'a ba mu San lokacin da muka fad'a parlourn ba, Allah ya so suna cikin d'aki, da asirin mu ya tonu. Abinda muka ji Daddy na fad'a ne, ya tilasta mana saka hannayen mu akan bakunan mu, kada mu yi baran 6aramar fitar da sauti har su an kara da mu a wajen. Mummy muka jiyo tana yiwa Daddy magiya akan ya hak'ura da maganar, koda Abeed zai tabbata bai yi aure ba, Daddy ne ya fara magana a hassle ya ce "kin ga maryam, maganar nan dole a fade ta, don komai lokaci ne, kuma ita magana lokacin fita ne da ita, idan lokacin fitar ta ya yi, dole ta fita." Mummy muka hango ta yi baya ta zauna sharaf, mu ma muna ganin haka, muka tattara inamu inamu muka yi waje. Bayan mun fito ne muke tattauna girman maganar da muka ji su Daddy na yi, Auntie jabo ce ta ce "gaskiya Mum Twins maganar nan ta d'aure mun kai," na ce "Ai ba ke kadai ba, nifa da ba tare muke ba da sai nace ba daidai naji ba, ni kai na burina bai wuce Allah ya kai mu gobe ba, mu zo mu ji yanda maganar take dalla_dalla ba," M Jabo ta ce "Ai ni ji na ke yi kamar yau na kwana a gidan nan, don kar mu makara zuwa," na ce "Ai kam dai. Kuma readers sai ku biyo mu don Jin abinda za faru..... Mum Twins 😍 & Auntie M. Jabo 🍃 💫AN YI WALK'IYA 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA K'arfe bakwan safe a gidansu Abeed ta yi mana, ko da muka shiga gidan suna ta hada_hadar had'a breakfast, kasancewar ta weekend, Arfat da Afrat muka hango a kitchen suna ta faman aiki, tare da 'yan aikin gidan, don mummy ta riga ta sabar musu da aiki musamman girki don duk ranar da ba school tare suke shiga kitchen har Mummy. Arfat ce ke wanke hannunta a jikin sink, afrat ta je ta ce da ita "ya Arfat na ga har yanzu mummy bata fito ba, ko lafiya "? Arfat ta ce "Yanzu nima na ke shirin dubata, ki cigaba da duba girkin bari na je, na dawo". Afrat ta ce "to " Sallama Arfat ta ke ta kwad'awa tunda ta shiga parlourn Mummy, har ta K'arasa bedroom, sannan ta jiyo muryar Mummy tana amsawa kasa_kasa, da sauri Arfat ta K'arasa kan gadon ta yaye bargon da Mummym ta kudundune a ciki, tana fad'in "Mum lafiya,?" Cikin raunananniyar murya Mummy ta ce "lafiya lau" Arfat ta ce "Amma shine Mummy ba ki fito ba tun dazu"? Mummy ta ce "jikin ne yau bana Jin dadin sa, amma je ki ga ni nan zuwa". Jiki a sanyaye Arfat ta ce "to mummy sai kin fito," tare da Jan k'ofar d'akin. Amma a can k'asan zuciyarta tana tunanin mai ya samu Mummyn su don ba ta saba ganinta a irin wannan yanayin ba. Bayan sun kammala breakfast ne Daddy ya ce su zauna dukan su yana da magana, Mummy kuwa da tun shigowarta, ta kasa sakewa don ko abincin kirki bata ci ba, haka su Arfat ba su iya tsayawa sun ci abincin ba kamar yadda suka saba, saboda don duk sun takura ganin halin da Mummyn su ke ciki. Daddy ne ya yi gyaran murya ya fara magana da cewa "Muhammad!" Yanayin yadda ya fad'i sunan ya saka Abeed saurin juyawa ya ce "Na'am," wadda sautin ta bai fita ba, don ko Arfat dake zaune kusa da shi bata san ya fad'a ba. Daddy ya cigaba da fad'in "Tunda abin na ka ya zo da haka, ka riga kasan alkawarin da na yi akan aurenka, kuma kasan ba zan ta6a warware shi ba, don haka muka yanke shawara ni da mahaifiyarku akan za mu had'a aurenka kai da 'yar uwarka Arfat,......!!!" Tashin hankali muka gano a idanunsa k'arara, don kuwa ba Abeed ba har Arfat ta shiga rudani, don wata zabura ta yi, wadda ta yi dai_dai da tashin Abeed, hakan ya haddasa gwaruwar kawunansu, lokaci d'aya suka yi baya, kowa dafe da kan sa. Ita kuwa Mummy wasu zafafan hawaye ne, suka biyo kumatunta, don tasan a rina. Abeed ne ya yi k'arfin halin cewa "Dad ban gane mai ka ke nufi ba?, ka fahimtar da ni, Dad ko ka manta we are the same blood, if am not wrong, Arfat ita ke bina fa. sannan nan k'aramar k'anwar mu Afrat". Arfat kuwa da gudu ta je, ta fad'a jikin Mummy tana kuka, ta ce "Mummy ban ga ne abinda Daddy ya ke fad'a ba, how comes zan auri yayana, the same Mum & Dad fa, ban ta6a ji ba, ko a lokacin jahilan farko ba,....!!!" Wata iriyar tsawa Daddy ya daka mata tare da cewa "Me kike nufi?, kin fi ni sanin abinda ya kamata na yi ne?? " Mummy ce ta ce "Alhaji sanin kan ka ne, idan yaran nan suka ji wannan maganar sai sun dimauce har su kasa controlling kan su, don haka hak'uri za ka yi abi komai a hankali." Mikewa Daddy ya yi tare da nuna Abeed da hannu ya ce "Kai ka jawo duk abinda ya faru , don haka ka shirya d'aukan duk abinda ya biyo baya." Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice daga parlourn. Abeed K'arasawa ya yi gurin da Mummy ke zaune ya ce "Mum sai yanzu zuciyata ta fara hasko mun, abinda tun d'azu na kasa ganewa, tabbas na fuskanci akwai wani B'OYAYYEN AL'AMIRI (Bebeelo ) da ya shafe mu, amma ba ku sanar da mu ba, don Allah Mummy ki fad'a mana mai ya ke shirin faruwa da mu ne"?? Mummy kam ba ta san lokacin da ta rushe da wani irin kuka ba, dama tun d'azu take rike shi, gaba d'ayansu rungume Mummym suka yi, suna rarrashinta ,, duk da Arfat da afrat suma kukan suke yi. Arfat ce ta d'ago da kanta ta fara magana cikin kuka ta ce "Mummy gaskiyar ya Abeed, don ni kaina na fara wannan tunanin, ko ma miye Mummy gwanda ku gaya mana, akan ku bar mu cikin duhu." Dakyar mummy ta samu ta tsaida kukan da take yi, ta ce "ku yi hak'uri 'ya'yana, za ku ji komai, tunda har Alhaji ya taso da maganar nan, tabbas na san zai gaya muku duk abinda ya faru, don haka ku kara hak'uri zuwa an jima za mu k'ara wani zaman". Ba don ransu ya so ba suka amince, kowa ya tashi ya nufi nasa guri zuciyoyinsu cunkushe da tunani kala_kala........ Mum Twins 😍& Auntie M Jabo 🍃 [4/11, 2:54 PM] 💫AN YI WALK'IYA 16&17 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Adaidai k'ofar shiga parlourn su ta tsaya don daidaita natsuwarta, don kar a gane yanayin da take ciki, sabida lokacin da zata fito tana ta gwalli da iyayi, a dole ga matar Abeed, bayan tasan tana da 'yan adawa don akwai stepsisters d'in da suke sa'anni, kuma kowacce ta so ace ita Abeed zai aura, amma sai Abbansu ya ce hafsat aka ba shi, don haka tasan idan suka san yadda ta kasance musu da Abeed lallai za su yi mata dariya, ai kuwa tana shiga kaitsaye d'akinsu ta wuce, ta fad'a gado sharaf, tana tunanin mafita don gaskiya tana son Abeed, domin tasan idan ta yi nasarar aurensa ta more miji kuma ta tsere sa'a. Amma da ta tuna kalamansa sai jikinta ya yi sanyi, wannan shi ake kira ga k'oshi ga kwanan yunwa. ******** Abeed kuwa bayan ya koma gida, wanka ya yi sannan ya ci abinci, ya yi shirin kwanciya barci, a sannan ne yake tariyar abinda ya faru tsakanin sa da hafsat, tsaki ya ja, sannan ya ce "idan ban da abun Daddy ta yaya waccen yarinyar zata had'a kan ta da ni, ai kwata_kwats ba aji na ba ce" ni da na fison mace natural beauty, amma ga shi ita duk kyan na ta artificial ne, amma haka ga ni ta ke yi ta had'u, ba ta san ni ganinta na ke yi kamar wata horror ba," ya kuma Jan wani tsakin, tare da rarumo pillown sa ya k'ak'ume da niyyar fara barci, nan da nan kuwa ya lula duniyar masu barci, mu kuma mu ka ja masa k'ofa muka fice daga d'akin. Kusan 6 weeks da zuwan Abeed gidansu Hafsat, amma ko da wasa bai kuma lek'awa ba, kullum da uzirin da ya ke bawa Mummy idan ta yi masa maganar, har ta gaji ta saka masa ido. Hafsat kuwa kullum sai ta kirashi, shi kuma ya yi ta mata wulak'anci da cin fuska, daga k'arshe ma sai ta daina samunsa, don karya sim card d'in ya yi , ya chanza wani, don karya layi a gurin Abeed ba wani abu ba ne, halinsa ne ya saba haka tuntuni, da ga ya yarinya za ta takurashi da kira zai chanza wani layin. Hafsat tun abun baya damunta har ya fara damunta, don har 'yar rama ta yi, ga shi ta kasa gayawa kowa maganar har ummansu......... Auntie M Jabo 🍃& Maman Twins💫AN YI WALK'IYA 17&18 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA A kwance ta ke a d'aki tana aikin na ta, na neman mafita, kwatsam ta jiyo muryar babbar aminiyarta, Safiyya tana kwad'a sallama, a hanzarce ta mik'e ta rungumeta tana fad'in k'awata yau a gari? Kamar kin san ina neman ki, don da gobe na ke sa ran zuwa gidanku". Murmushi Safiyya ta yi ta ce "kamar da gaske"? Hafsat ta ce" wallahi da gaske na ke yi, domin akwai wata muhimmiyyar magana da na ke son gaya miki ki ba ni shawara". Safiyya ta ce "ok, to gaya mun ina Jin ki, tunda ga ni na zo", nan da nan Hafsat ta juyewa Safiyya abinda ya faru tsakanin ta da Abeed, a jiyar zuciya Safiyya ta sauke, sannan ta ce "Hafsat shawara kike so na ba ki ko? Hafsat ta ce eh" Safiyya ta cigaba da fad'in "kin san ita gaskiya d'aya ce tak, kuma d'aci ne da ita, i hope idan na gaya miki za ki daure ki yi amfani da ita?" Hafsat ta ce" eh insha'Allah" Safiyya ta ce "ni a gani na ki hak'ura da Abeed zai fi, don alamu sun nuna ba ya son ki, kuma baya muradin zaman aure da ke, to hak'ura da shi zai fi alkhairi, don gaba na ke jiye miki, ki manta da duk wani buri da ki ka Sakawa zuciyarki akan auren Abeed, ki yi watsi da maganar, ki nemi za6in Allah kawai". Jinjina na kai kawai Hafsat ke yi, alamum maganar ta shigeta, ta ce "dama nima zuciya ta, tana ta mun waswasi akan maganar, amma tun da yanzu kin haska mun inda na kasa ga ni, insha'Allah na janye daga yau, dama umman mu tana ta tambayata akan maganar tana son ji yadda mu ka yi da Abeed, ina ta mata hanya_hanya, tunda abun ya kasance haka zan sanarda da ita na fasa kawai, ta sanar da Abbanmu, tunda dama ba dole aka mun ba, za6i aka ba ni". Safiyya ta ce "gaskiya kam, Allah ya sa hakan ya zama alkhairi," ameen k'awar kirki Hafsat ta fad'a tare da mika mata hannu suka tafa su na dariya. ***** Yau Daddy tunda ya dawo ya ke zabga fad'a, mummy ce ta sauko tana fad'in Alhaji lafiya? tun daga sama na ke jiyo maganar ka, mai ya faru ne? Daddy ya ce "ni da yaron nan ne Muhammad, d'azu Alhaji Usman ya ke gaya mun, wai yarinyar wajensa ta janye maganar aure tsakaninta da shi, kuma na san ba komai ya saka ta yi hakan ba, sai dan bak'in hali da ya ke nuna mata, tunda tun fil'azal ya nuna baya son aurenta kawai dai tilasta shi mu ka yi". Mummy ta ce "yi hak'uri Alhaji, bari ya zo, na tambaye shi yanda suka yi da yarinyar," Cikin 6acin rai Daddy ya ce "ba na son Jin komai daga gare shi, kawai idan ya dawo ki sanar da shi cewa na yanke hukuncin ba zai kuma yin wani azumi a gidannan ba, sai a gidan aurensa, don haka ya shirya kafin azumin nan mai zuwa za a yi aurensa , gobe_goben nan zan sanar da shi yarinyar da zan kuma nema masa, don haka ya yi gaggawar zuwa su shirya kansu". Daga haka bai kuma cewa komai ba, ya wuce fuuuu ya haye sama, Mummy kam tsayawa ta yi baki bud'e, don tasan mutumin na ta, idan ya ce eh, baya ta6a dawowa ya ce a'a...... Mujee zuwa Auntie M Jabo 🍃 & Maman Twins 😍 : 💫AN YI WALK'IYA 19&20💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Abeed na dawowa, Mummy ta same shi domin isar da sak'on Daddy, nan take ta zayyana masa hukuncin da Daddy ya yanke akan maganar aurensa, zare dara_daran idanunsa waje ya yi, tare da fad'in "Mummy kafin azumi fa kika ce ni duk kun bi kun saka min ido ga mata nan ba'a tsangamesu ba saini, tsakani da Allah azumin da bai fi 3 months ba, how comes zan iya aure kafin lokacin, bayan na san ko yanzu wadda Daddy zai nema mun ba lallai ta dace da ra'ayina ba," Jinjina kai Mummy ta yi tare da fad'in "Abeed har yanzu ba ka hak'ura da wannan mummunan k'udirin naka ba ko?, nidai kan gani nake Ka yi hakuri ka kar6i za6in mahaifinka ya fiye ma ka." Abeed ya ce "Mum ba wai na k'i bin maganar Daddy ba ne, Noo, ki gane mana, nima fa ya kamata a duba uzurina a yi mun adalci, don ni ba k'aramin yaro ba ne, da za a ce bani da hankalin da zan za6i matar da ta dace da ni, kuma ni ba mace ba bare a mun auren dole," ya had'e hannayensa wuri d'aya, ya cigaba da fad'in "please mum ki taimaka ki gayawa Daddy ya hak'ura da zancen auren nan yanzu, har sai na samu irin macen da na ke son aura". Ajiyar zuciya mummy ta sauke, sannan ta ce "Abeed ka san halin Alhaji sarai, tun da ya taso da maganar nan, Allah kadai zai hana a yi aurenka a tsukun lokacin da ya fad'a , ni dai shawarar da zan ba ka, ka daure ka amince da abun da mahaifinka ya fad'a". Ba don ransa ya so ba, ya ce "to" saboda ya fuskanci ita ma mummy ta kasa fuskantar in da ya sa gaba. K'ofa mummy ta nufa tana fad'in "Ni dai sai da safe, don har na fara Jin barci," Abeed ya ce. "Allah ya tashe mu lafiya". Tunda safe Daddy ya sa aka kira masa Abeed, nan da nan kuwa ya hau kora masa bayani akan yarinyar da ya kuma nema masa don sun riga sun gama magana da mahaifin ta, ya ce "Muhammad ai kasan Alhaji sulaiman ko"? Gyd'a kai Abeed ya yi don kaf abokan Daddy ba wanda bai sa ni ba, Daddy ya cigaba da cewa "To ya baka babbar 'yar sa, sai ka je ku daidaita kan ku, shiru Abeed ya yi na dan lokaci, sannan ya ce " to tare da mik'ewa ya na fad'in "Bari na je na yi shirin zuwa office kada na makara". Daddy ya ce "ya yi kyau, Allah ya taimaka", Abeed ya ce "Ameen" tare da fitowa. Bayan ya dawo daga office, wannan karon bai jira Mummy ta yi masa maganar zuwa ganin yarinyar da aka kuma ba shi ba, ya shiga shirin zuwa, nan da nan ya fesa wankan shi, ya d'auko wata dakakkiyar shadda grey colour ya saka, ya murza hularsa kalar shaddar, ya sha perfumes masu sanyin k'amshi, ya fito fes da shi, a parlor su ka had'u da mummy ta kalleshi ta ce "sai ina kuma"? Murmushi ya yi wanda bai kai ciki ba, ya ce "Mummy wurin yarinyar da kuka ba ni mana" murmushin Jin dad'i mummy ta yi, ta ce "yawwa my boy, haka na ke so, Allah ya kiyaye hanya, Allah kuma ya dawo mun da kai lafiya," ya ce "Ameen Mum," tare da ficewa daga parlourn. Driving ya ke yi, yana sauraren wani cool music, amma duk da haka zuciyarsa ba ta daina masa tuk'uk'in da ta ke yi ba, don dai ya fito zancen nan ne don ya cimma burin da ke zucuyarsa, lokaci d'aya kuma sai ya saki wani murmushin Jin dadi don tuna abinda ya k'udire a zuciyarsa, hakan ya yi dai_dai da k'arasowarsa gidan Alhaji Sulaiman... Auntie M Jabo🍃 & Maman Twins 😍 💫AN YI WALK'IYA 💫 ©Mrs Saif & Hauwa M. Jabo ®NWA Horn ya yi mai gadi ya wangale masa gate ya shige, wannan karon direct parlourn gidan ya nufa, bayan ya shiga sun gaisa da mutan gidan, aka ce ya zauna a turo masa yarinyar mai amsa sunan Teema, gaishe shi ta yi cikin kunya da ladabi, ba laifi shima ya d'an saki fuskarsa, don ya ga alamun zata yi hankali, amma duk da haka natacciyar zuciyarsa na masa hud'ubar tsiya, don haka nan da nan ya fuske, ya hau zayyana mata sharuddansa,ita ma ba ta tsaya wani dogon nazari ba tace da shi dama tana da wanda take so, don dai babanta ya zo da maganarsa ne shi yasa ta amince, amma tunda abun haka ne idan don ita ne ta janye akai kasuwa, murmushin cin nasara Abeed ya yi, don dai ya lura ba za a samu matsala ba a wurin teema ba, don haka cikin wayo da dabara irin na d'a namiji ya nuna mata, ta sanarda daddynta ya yi hakuri ya janye maganar auren su, tunda tana da wanda ta ke so, teema ta ce "Ba damuwa idan dai Daddy na ne bai da matsala zai fahimce ni". Murmushi Abeed ya yi tare da mik'ewa ya ce "To ni zan ta fi" teema daga nan zaune ta ce "Allah ya kiyaye hanya". Ya ce "Ameen" tare da fitowa daga parlorn, cikin nishadi ya ke driving d'in sa har ya zo gida. A parlor ya tarar da Mummy a zaune, tana kallon T.V, ta ce "welcome back, yarona har ka dawo ke nan"? Ya ce "Eh mummy ba ki yi barci ba ne "? Tace "Eh ina nan, ina jiran dawowarka ne, amma daga ganin alamun fuskar nan ta ka an dace," dariya ya to tare da fad'in "i hope so", Mummy ta ce "Allah ya sa" yace "Ameen " tare da fad'in "Mummy bari na je na kwanta, wallahi duk a gajiye na ke". Mummy ta ce "Ai ko ni tashi zan yi, don su Arfat tun d'azu suka yi barci, nima don na tsaya jiranka ne. " Yau ta kama asabar daga Daddy har Abeed ba wanda ya je aiki, suna hutawa a gida, don haka sai can wajen yamma Alhaji Sulaiman ya yi tattaki zuwa gidan don sanarda da Daddy halin da ake ciki game da auren Abeed da teema, tunda ya gaya masa baya son a

Chapter 3 of 5