Share this page
2 / 10
ta feshe jikinta da turare mai kamshi abinda bata saba ba domin tasan rashin dacewar mace ta tsaya gaban saurayi tana kamshi irin wannan banda zunubi a addinance. Sai dai ita kanta ta rasa gane dalilinta na yin hakan. Annabi SAW yayi gaskiya da ya fada mana cewa shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake gudu. Shi aikin sabo da kadan muke farawa sai a hankali ya zame mana jiki. Mu kiyaye don Allah da yadda muke langabewa jikin maza ayi hoto wai da sunan pre-wedding pictures. 'Yar uwa idan baki aure shi ba meye makomar rungume rungumen da ku ka yi duk da sunan wayewa? Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐5 A mota Hafsi ta sami Saif yana jiranta. Tana shiga wani kamshi mai dadi ya bakunci hancinta tare da sanyin AC. A kunyace ta zauna tare da gaishe shi. Matar kinyi kyau sosai ga kamshi mai dadi da kike yi. Fari tayi masa da ido har na kai ka kamshi Saif? Har kin fini ya bata amsa yana dariya. Yana tuki suna hira bata ankara ba taji ya kama mata hannu ya dora akan gear ya hada ya rike. Tana kokarin kwacewa ya matar kina son muyi accident ne kike neman canza min gear? Cikin muryar shagwabar da ta saba magana tace da hannuna fa ka hada Saif. Au hannunki ne ma ba nawa ba. Naka ne mana amma ba'a gama baka ba sai an daura aure. Ku mata komai sai an daura aure ne? Ko kin manta ansa mana rana. Ai yanzu abinda ya rage tsakaninmu kadan ne. Suna shiga unguwar ta fada masa su bi ta bayan layinsu Ummati sai ta sauka. Ba musu layin suka shiga da yake a tsuke yake ba mutane sosai. A nan Saif ya sami damar kebewa da Hafsi don a gidansu akwai idon jama'a. Rikota yayi ya hanata fita....matar ni fa duk kin rikita min lissafi tun ranar saturday da muka yi hoto. To yanzu me kake so ayi. Wayarsa ya dauko yana nuna mata pictures din. Hafsi ta sami tarbiya daidai gwargwado kuma shima Saif din ya fito ne daga gidan mutumci sai dai koyi da tarbiyar nasara yasa idanunsu ke neman rufewa. Ganin hotunan yasa suka fara shiga wani yanayi. Yadda ya riketa kamar ba zai saketa ba yana kokarin hada bakinsa da nata itama kuma bata yi yunkurin hana shi ba. Tun shigowarsu layin Mal Aminu ya gane motar sai dai bai gane yarinyar da ke gaba ba saboda yadda take ta kokarin rufe fuskarta. Ganin motar ta shige wata kwanar ba hanyar gidansa ba yasa yayi mamaki kamar ya wuce sai yaga anyi parking dinta a karkashin bishiyar darbejiya shiru ba'a bude kofa ba. Karasawa yayi ya tambayeshi gidan wa yake nema tunda dai a iya saninsa gidansa yake zuwa a unguwar. Jin ya fara kissing dinta jikinta yayi sanyi hankalinta gaba daya ya tashi. Ashe akwai ranar da zata aikata irin abinda take ji a labari tana ganin bakin masu aikatawa. Wai a zamanin yanzu a haka ne kawai masoya zasu nunawa junansu kauna. Wazu hawaye taji sun zubo mata. Hankalin Saif ya tashi...matar kiyi hakuri wallahi rudin shaidan ne amma bani da mugun nufi a kanki. Yana cikin share mata hawaye suka ji an bude kofar gefen da take zaune.....idanu ta bude a tsorace ganin waye a tsaye cikin rawar murya tace BAFFA!. ******************* Yau ma a cikin maye ya shigo gidan anyi sa'a ma wurin shabiyu da rabi na dare ya shigo. Fito ya shigo yana yi yana karkada keys din hannunsa. Kamar daga sama yaji kira...Junaidu....ba don namiji bane da gabansa sai ya fado kasa yadda ya mugun tsorata. Cak ya tsaya kamar gunki. Don ubanka juyu ka kalleni. Mommy da ke zaune a gefe shiru tayi. Babu wanda baya tsoron Hajiya Ramatu. A kano take aure a gyadigyadi wurin da aka fi sani da dangi, shiyasa ma ake kiranta da Hajiyan Dangi. Tsawa ta daka masa bazaka zo ba ne. A hankali ya dawo ya zauna a kan kafet. Hajiyan Dangi doguwar macece kamar mahaifisu ga jiki. Ita kadai ce mace a gidansu kuma ita ce babba. Allah bai bata haihuwa ba sai dai ta rike yara da yawa daga danginta har na mijinta. Cikinsu harda Senator Rufai kaninta. Mace ce mai riko da addini kuma mai sa ido akan tarbiya. Yanzu Junaidu wannan wannan rayuwar ka daukarwa kanka? Tana magana ta soma hawaye gidan malamai manyan mutane muka fito amma saboda giyar kudi na dibanka kana neman lalata rayuwarka. Ta kalli Mommy yanzu sai da lamarin ya baci haka kika sanar dani. Mommy dai hakuri ta ba ta. Bandanan kansa Hajiyan dangi ta fizge. Gobe kaje ka aske wannan shegen kan kuma kazo ka nuna min. Ko ci kanka bai ce mata ba haka ya tashi ya basu wuri. Yana shiga daki tabarsa ya kunna ya fara busa hayaki kai ka ce bakinsa salansar mota ne. A haka Junaid ya tuna bai yi sallar laasar, magriba da isha ba. Tsaki ya ja tare da mikewa ya nufi toilet. Haka ya yi alwala irin yadda kwakwalwarsa ta karanta masa sannan yazo ya fara ramuwar sallolin da bai ma san abinda yake karantawa ba. A dakin da take sauka kuwa Hajiyan Dangi ce ta yanke shawarar ba zata koma kano ba sai kaninta Rufai ya dawo daga Australia sunyi magana akan Junaid. Babu abinda taki jini kamar yaro yaki ya rinka keta dokokin Allah ba tare da an dauki mataki akansa ba. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐6 Jikinta ne ya hau bari kamar wadda akayiwa wanka da ruwan sanyi a watan december. Iya karfinta ta sa ta fito daga motar har tana ture baffan nata. Da gudu ta tafi gida kafarta ko takalmi babu. Saif kasa motsi yayi a cikin motar ya sunkuyar da kansa. Baffa bai ce masa komai ba ya juya ya nufi gidansa. Yadda ta shigo a firgice yasa Mama saurin tashi. Hafsa lafiyarki? Me ya faru? Me ya sami yayarki? Ko daya cikin tambayoyin bata amsa ba durkusawa kawai tayi a gabanta tana kuka. Amira ce ta kula da kafarta ta dama tana jini. Mama kinga kafar Hafsi jini take yi. Subhanallahi ke ko hatsari ku ka yi a hanya ne? Ana magana kinyi shiru kamar wata bebiya. Cikin Hafsi har wata kara yayi da jin sallamar Baffa. Bai jira an amsa ba yaja hannun Hafsi zuwa dakinsa. Garammm ya banko kofar har gaban su Mama ya fadi. Ihun Hafsi kawai suka ji tana bawa Baffa hakuri. Tuni Mama ta karasa bakin kofar dakin tana bugawa. Su Amira kuwa sai kuka don tun suna jin kukanta har murya ta dashe. Babu irin magiyar da Mama bata yi masa ba amma yaki budewa. Baffa ya bude kofa Hafsi na kwance a kasa Mama ta shiga dakin hankali a tashe. Baffan yara me ya faru...ke Hafsa me kika yi? Da kyar Baffa ya iya fada mata tana ta kuka. Ita kam Hafsi hawayenta ba na zafin duka bane kawai. A yau tayi dana sanin abinda ta aikata. Tayi Allah wadarai da maza da matan da basa jin komai lokacin da suke hada jikinsu da juna alhali babu aure a tsakaninsu. Yau ina ranar son zuciya da biyewa shaidan da mukarrabansa wadanda suke tallata irin wannan watsewar da sunan wayewa. Mama da bata zagi yau duk wanda yazo bakinta dankarawa 'yar tata take yi. Tashi ki bani wuri mara mutumci tasa kafa ta haure ta. Jiki a sanyaye haka ta fita tana share hawaye. ******************* Yau kwana biyu kenan Junaid yana wasan boya da Hajiyan Dangi da mommyn sa. Tun sallar asuba yake fita sai tsakar dare yake dawowa. Hajiyan Dangi lamarin ba karamin bata mata rai yake ba. Sai da ta cika sati a gidan Senator Rufai ya dawo. Bayan ya huta cikin dare wuraren karfe tara yaje dakin da yayar tasa ta sauka. Hajiyarmu babbar Hajiya zama da tashi cikin girma. Kirarin da ya saba yi mata kenan yau ma bayan yayi sallama tun kafin ta amsa ya fara. Murmushi tayi tana kallonsa Rufai bazaka girma ba. Ai indai ina ganinki bazan girma ba Hajiya. A kan kafet ya zauna kusa da ita. Bayan sun gaisa tace Rufai kayi min laifi gaskiya. Nasani Hajiya kiyi hakuri don Allah. Lamarin Junaid ba karamin bata min rai yake yi ba amma na rasa yadda zanyi da yaron nan. Dole ka fadi haka mana tunda aiki yafi maka akan rayuwar iyalinka, wannan karon cikin fushi take maganar. Kana gefe kana turowa yara kudin da yafi karfin aljihunsu dama me kake tsammani ga yaro da kudi. Shiru yayi don sam baya iya mata musu kuma ma yasan gaskiya take fada masa. Tace to ni na yanke shawara ayi masa aure kawai. Tun zuwana garin nan yaron nan yake gudu na. Anya zaka iya haduwa da Allah akan yadda kayi wasarairai da amanar da Ya baka na yara? Ni bama wannan ba Rufai kaga Allah Ya baka matsayi a cikin al'ummar kasar nan kuma ni da kai munsan ba iyawarka bace tasa ka samu. Zabi ne kawai na Allah saboda haka ina dada baka shawara kamar kullum ka tsaftace dukiyarka. Ka kiyaye haram don ita kadai zata wargaza duk wani al'amarinka. Kafin ta gama magana idanun senator sun cika da kwalla. Dukiya kam suna kai suna wasa da ita son ransu. Ya Allah Ka bamu ikon gyarawa ya fada a zuci. Gyara zama yayi to Hajiya wa kike jin za'a aura masa? Sayyada ta bashi amsa a takaice. Sayyada ya maimaita shima ban gane ta ba. Bama ka santa ba. Yar wajen Atika ce kanwar Baba(maigidanta). Tun da ta gama secondary ta dawo hannuna bana ma zata gama Buk. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma bata daukar wulakanci shiyasa nake ganin zata taimaka wajen shawo mana kan Junaidu. Har zuciyarsa yayi murna. Yace Allah Ya shige mana gaba kuma don Allah a taya mu addua. Junaid yasha fada wurin mommy karshe tace yaje ya bawa Hajiyan Dangi hakuri. Yana zuwa bakin kofar dakin yaji maganar da suke yi da babansa. Wata dariya ce taso kubuce masa...wa yaga Junaid da auren dole. Ai ko zai dena holewarsa a waje zancen aure bai ma taso ba. Juyawa yayi a hankali tare da yankewa kansa shawarar barin garin a washegari daidai lokacin da yaji Alhajinsu yana cewa idan Hajiyan Dangi zata koma kano zasu tafi tare. Batul Mamman TUN KAFIN AURE💐7 Tamkar mujiya haka iyayenta suka mayar da ita. Babu mai kula ta sai kannenta suma a tsorace don sun fuskanci su Mama fushi suke da ita kada abin ya shafe su. Zaune take kan abin sallah tana addua bayan ta idar da sallar walha. Idanunta duk sun shige ciki ga ramar da tayi saboda rashin cin abinci. Sallamar Mama taji ta dago kai a hankali ta amsa. Ko kallonta bata yi ba ta shige tana tashin Anisa ta sha magani saboda ta kwana da zazzabi. Mama ina kwana, an tashi lafiya? Kau da kai tayi amma har zuciyarta tana tausayin Hafsi. Ta kuma yarda kaddara babu yadda bata zuwa ga bawa domin duk cikin 'ya'yanta ita ce mutum ta karshe da zata yi tsammanin zata aikata abinda tayi. Auta tashi ki sha magani kinji ta fada tana shafa kanta...mama baki ji Hafsi tana gaishe ki ba ne. Tsaki tayi naji...karbi ki sha sai ki koma baccin. Ficewa tayi ta koma dakin Baffa ita ma kukan tayi na tausayin halin da yara harma da manya ke fadawa a wannan zamanin. Fitar mama kenan Amira ta fito daga toilet ta tsugunna gaban Hafsi. Wai ni don Allah me kika yiwa su Baffa ne Hafsi? Anisa dake kwance tace yanzu ko gaisuwarta ma Mama bata amsa ba. Share hawaye tayi babu komai ku dai cigaba da taya ni addua. Tana gama magana ta tashi ta tafi dora girki don yau duty dinta ne. Ko da ta fita kannenta shawara suka yi karshe suka kira yayarsu Hadiza a waya aka sanar da ita abinda ke faruwa. ******************* Juni ba wayarka bace take ringing tun dazu. Tsaki yayi ya sha giyar dake hannunsa kyale shi Old Man dina ne. Ai tun shekaranjiya dana bar Abuja yake nemana wai ni zaiyi wa aure...what a joke. Chuks ya kalle shi ku fa hausan nan haka kuke sai ku auri yarinya ku sakata a family way at a very young age. Chai, its disgusting. Karshe ta sami VVF wurin haihuwa kuyi mata saki. Hannu Juni ya daga masa kai Chuks dakata bana son wulakanci. Gara mu aure muke yi da wuri kai at what age ka fara having sex. Wata irin dariya yayi har mutanen dake cikin club din suka fara kallonsu...my friend I was 13 fa. Wata yarinyar neighbour dinmu ce na ma girmeta. Ita ta koya min. Juni yace ka gani ko ashe kune manyan 'yan iskan. Kun iya bibiyar kananan yara amma idan musulmi sunyi aure sai ku ce child molestation. Hypocrates kawai. Abeg no insult me Juni.....ai kaine ka fara zagin hausawa nasan karshe kan musulmi zaka koma. Ha! Kai ai baka son islam Juni you drink like a fish and sleep with every prosti...kafin ya karasa Junaid ya kai masa naushi a baki. Kan kace kwabo bakin Chukwuma ya fara jini nan yan uwansa suka tarar wa Juni ashe akwai 'ya'yan hausawa. Cikin karamin lokaci sai fada ya kaure tsakanin musulmi da kishiyoyinsu na wani addinin. Ana ta fashe fashen kwalaben giya. Karshe dai sai da police suka shigo cikin lamarin duk aka kama su. Tilly na kwance akan gado tare da wani hamshakin dan kasuwa taji waya. tayi mamakin ganin sunan Juni ta dauka cike da farinciki. Nan yayi mata bayanin yadda suka yi da police amma jin ko dan waye kuma ya jika su da kudi sun sake shi. Karshe dai yana bukatar account number dinta zai turo mata da kudi ta biyoshi Lagos. Ko sallama bata yiwa mutumin da suke tare ba ta tashi bayan taji alert....lallai Juni na ji da kudi. ******************* Cikin kuka Mama tayiwa Hadiza bayanin abinda Hafsi tayi. Itama kukan take...wallahi Mama yanzu irin wanan masifar ake fama da ita. Ana zance ana shafar juna karshe inda kaddara ayi ciki. Mama tace abin ne ba kama ba don ni na haifi Hafsa ba amma wallahi nayi mata shaidar alkhairi. Allah Yasa mufi karfin zukatanmu. Amin Mama amma don Allah kuyi hakuri don idan muka nesanta kanmu da ita sai tayi wani abin ma babu wanda ya sani. Hafsi da Ummati suna ta shawarwari Hafsi tace kinsan har yau babu waya ko text din Saif. Idan na kirashi ba waya a kashe abinda ya kara batawa Baffa rai kenan don shi so yake a sanar dashi a matso da bikin. To aje gidansu mana don bai isa ya jawo mana jangwam ya tsallake ya barmu a ciki. Ke ummati kila a tsoro yaji. Ai ni dadi na dake shegen son saurayi. Ni wallahi daga yau kara kama kaina zanyi har sai anyi aure. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐 8 Juni dear....yes Tilly ya amsa mata yana daga kwance. Jin tayi shiru ya taso ya dafa bayanta Tilly ya akayi ne? Ko akwai abinda kike so ne? No tambayarka kawai zanyi. Nawa ne kudin hotel dinnan ne per night? N150,000. Wage baki tayi ko wane kwana daya? Eh menene wai duk kin wani rude. Gani nayi kudin da yawa kuma gashi yau kwanan mu hudu banda abinci da kudin da kake kashewa a club. Wani shekeke ya kalleta kin ma raina ni to ko don ban biya ki naki kudin bane...yana gama magana ya mike daga shi sai gajeren wando ya jefo mata cheque. Ganin kudin dake jiki dubu dari biyar ba shiri ta rungume shi tana ta murna. Hmm kudi a kasar nan yana hannun masu shi suna kashewa kadangarun bariki da kayan maye wani lomar tuwo ta gagare. Masu kudi a rinka cin halal dai. ******************* Hajara tana kwance tana chatting da kawayenta a group taji shigowar messages. Tana dubawa hotuna ne kamar bazata bude ba don bata da data sosai sai ta bude daya. Zumbur ta mike ta bude sauran. Babu shakka ita ce a duka hotunan biyar. Wadda ta turo cewa tayi ga wani style din pre-wedding pictures. Nan da masu cewa sunyi kyau da masu zaginsu. Wani gumi ne taji yana karyo mata lallai baa shaidar mutum, yarinyar da kullum take shigar mutumci ita ce a haka. Tsam ta tashi ta dauki mayafi ta sauka kasan gidanta wurin makociyarta. A'a Hajara shigo mana ina kitchen...a sanyaye ta karasa dama wani abu zan nuna miki a waya. Maimakon kiyi min forwarding, menene mu gani. Ruwan ruden tuwon da take ne ya fallatso mata a hannu da gefen fuska saboda tsabar rudewa. Na shiga uku ni Hadiza me zan gani haka. Hajara tace a group na gani shiyasa na nuna miki don nasan wace Hafsi. Muciyar ta karba ganin yadda hannun Hadiza ke rawa ta karasa mata tuwon. Daren ranar bata yi baccin kirki ba. Mijinta zai tafi office ya ajiyeta a gida duk da bata fada masa abinda ke faruwa ba yasan babu lafiya. A falo ta hadu da Baffa zai fita ta gaishe shi. Lafiya dai Hadiza irin wannan sammako ko duk saurin ki taya ni cin kosai ne. Murmushin karfin hali tayi. Baffa akwai wasa sai dai baya sake wa yara suyi yadda suke so. Ganin bata biye mishi ba ya mike muje ciki. Mama na shafa mai suka shigo dakin. Hadiza lafiya kuwa...nan taji tsoron nuna musu hoton sai dai tasan yadda irin hotunan nan ye kawo a social media. Wasu mutanen basu da aiki sai ture turen abinda bai shafesu ba karshe su kunna wuta mai wuyar kashewa. Wayar ta mika wa Mama shima Baffa ya zauna kusa da ita yana gani. Hankalinta bai tashi ba sai da taga 'yarta babu ko dankwali ta shige jikin namiji sai kace kanin uwarta ko na ubanta. Nan take numfashin Mama ya fara sama sama dama ita haka take idan ranta ya baci. Haka ta fita daga ita sai daurin kirji ta shiga dakin 'yan matan. Wayar chaja ta fizgo daga jikin bango ta fara tsula mata. Hafsi ji tayi kamar a mafarki ana dukanta tayi saurin tashi. Yaya Hadiza ta gani sai kannenta. Cikin rashin fahimtar laifinta ta fara rokon gafara. Sai a lokacin Baffa ya shigo ya dakatar da dukan. Kyaleta haka ku zauna. Wayar Hadiza ya bata hoto daya ta kalla ta kama kafar Mama tana kuka...don Allah ku yafe min wallahi bazan kara ba. Ki ma kara mana don ubanki...wai ni dame muka kuskure miki ne Hafsa. Lokaci guda kin fara taka rawar gangar shaidan. Wai ma yaushe akayi wannan hoton? Shiru tayi ba amsa. Nace yaushe akayi hoton nan...lokacin...lokacin. Hadiza ce ta katse ta lokacin me? Uhm lokacin da muka ce miki zamu daukar hoto da ummati. Nasan za'a rina cewar Baffa. Dama nasan da taimakon wani a lalacewar da kika soma yi. Amma wallahi ba a gida na ba. Gidansu Saifullahin zani in nunawa mahaifinsa, ki kwana cikin shiri aurar dake zanyi cikin kankanin lokaci mutuniyar banza. Nan dai ya hada duka yaran nasa sun sha fada da nasiha. A dakinsa kowa yace da Mama ta tabbatar ta tuntubi Hafsi ko babu wani abu da ya shiga tsakaninsu domin shi yanzu ya tsorata da halin yaran zamani. Batul Mam TUN KAFIN AURE💐 9 Wani irin kuka ne mai tsuma zuciya take yi tunda Mama tayi mata wannan tambayar. Wai ko wani abu ya shiga tsakaninsu??? Lallai ta jawo wa kanta tunda an fara zargin ko lalacewar tata ta kai nan. Gabadaya filon ta gama jika shi da hawaye dadin bakin cikinta ma rashin duriyar Saif. A wannan yanayin Ummati ta shigo itama kukan take yi don a falo Mama da Maman Ummati suka hada su ana ta fada gadon itama ta hau suka jeru kamar masu gasar kuka. Iyayensu sunyi fushi sosai. Tayi nisa da tunani kamar daga sama taji wayarta na ringing. A firgice ta tashi don tasan ko waye me kiran. Ringtone dinsa daban ne....ummati ce ta doke mata hannu da sauri tana kokarin dauka. Ta galla mata harara to banza mara zuciya..duk abinda ya samemu a dalilinsa sai yau zai wani nemeki. Cikin muryar data dashe saboda kuka tace bafa ki san me ya same shi ba. Don Allah ki bani wayar Ummati. Ni wallahi haushi kike bani mtww karbi ni ta dangwara mata wayar ta koma gefe. Ba zancen fita don iyayensu mata suna falo ana ta maida zance. (Matar ina kika shige ina ta waya.) Kaji rainin hankali yau fa kwanansu shadaya bata samunsa a waya(kai zan yiwa wannan tambayar. Sai da kaga matsala ka guje ni Saif) kuka ne yaci karfinta. Shima a hankali yake magana( kiyi hakuri ni kunyar sake haduwa dake da kuma Baffa nayi. Matar ina tsoron zama sirikinsu har abada Baffa bazai dena ganina da wannan tabon ba) Wani irin faduwar gaba taji (me kake nufi? Baffa fa sun taho gidanku tare da baban ummati) (Nasani na kuma nayi musu bayani. Tun ranar da ya ganmu na sanar da umma don bana son rufafa a maganar aure. Kunya tasa na guje ki don naci amanar Baffa. Kiyi hakuri muyi rabuwar arziki amma bazan iya aurenki ba.) Yana kashe wayar wani kuka ya kwace mata har su Mama suka shigo. Ummati suka fara tambaya tace bata san me ya faru ba. Kasa fada musu tayi tana ta kuka. Gajiya suka yi da tambayar aka kyaleta. Sai da Baffa ya dawo ya sanar da Mama yadda sukayi mahaifin Saif yace aure ba fashi tare da basu hakuri shi kuma dan yace bazai iya sake kallonsa ba. Zai fadi haka mana tunda yaso gurbata mana rayuwar yarinya. Suna ta maganganu Hafsi na jinsu daga daki tana kara tsanar kanta da abinda tayi. ****************** Junaid mutum ne mai son jindadi, bashi da magana sosai sai ta zama dole. Ko kadan baya daukar raini wannan kuma hali ne ya tarar da dukiyar da ya taso cikinta. matashi ne dan shekara 30 ga tsaho ga kyau ga fatarsa mai kyau saboda tana shan hutu. Gashin kansa da saje kuwa a kwance yake don kudin da ake ajiyewa don gyara shi daban ne. Yana son kula da gashin kansa ko kadan baya son abinda zai bata shi. Yana kwance kan kujera kansa a cinyar Tilly tana fara shafa masa kai. Doke mata hannu yayi yana magana kasa kasa ki dena taba min kai I hate it. Dan tabe baki tayi to yi hakuri naga ko wanka baka yi ba meye abin bacin rai don na taba? Tashi yayi ya bude fridge ya dauko lemon gwangwani ya fara sha. Ki shirya muje party amma bana son wannan faratan naki kamar mayya ya juya mata baya ji yadda kika kusa kwashe min baya. Yi hakuri Juni ta fada tana murmushi bari na cire su nayi wanka. Lallai ma yarinyar nan wallahi kinyi kadan abinda ya fada kenan lokacin da ya fito daga wanka ya kama Tilly tana satar masa kudi. A fusace ya karaso gabanta tasha mari hagu da dama. An fada miki bani da hankali ne? Kumatu ta rike tana kuka ni ka mar Juni? Ke 'yar waye da bazan mareki ba? Barauniya kawai get out of my room. Kafa yasa yana kai mata duka tana ta ihu. Da kyar ta rarrafa ta fita ya jefo mata jakarta waje ta ce zaka san ni kayiwa haka Juni sai na bata maka rayuwa. Ta mike da kyar tana dingisawa mugu ko kudina bai bani ba duk kwanakin nan dana yi. ******************* Dai dai yake kallon mutane kowa da budurwarsa ana ta sha'ani. Shegiya Tilly da nasan haka take ai da tun wuri na nemi me rako ni nan. Kai da wa kake magana Juni? Shafa kansa yayi zancen zuci ne ya fito fili birthday boy...Imi dan wani gwamna ne abokin Junaid ne tun suna secondary duk watsewarsu tare sukeyi. Ina babe din da na ganku tare ne jiya? Tilly barauniya? Ai na bata takardar sallama dazu....sata fa tayi min don rainin hankali. Imi da buduwarsa suka fashe da dariya ai abokina ka fiye kwashe kwashe ne. Ya rungumo yarinyarsa ya Simy akwai wata a kasa ne kada yayi kwanan kadaici yau. Kai kyale ni kawai. Maybe na tafi portharcout gobe. Dont worry I will pay bana son ganinka so quite. Wayarta ta dauko ta mika masa ga hotunan wasu nan duk kawayena ne idan ka

Chapter 2 of 10