Share this page
6 / 10
biyo baya. Hajiya tace mamana duk kin samu cikin damuwa tun dazu ana nemanki. Sai a lokacin suka kula da idanunta. Mommy ta zauna a bakin gadon. Kiyi hakuri yata nasan duk abinda zan fada zakiyi tunanin ko don bani na haifeki ba. Hafsi ta share hawaye ba haka bane mommy. Hamida tace wai ni me ya faru ne shi yazo yana mana fada dazu mun shigo kuma ance ana neman ta. Babu wanda ya bata amsa. Mommy da kanta ta taimaka wa Hafsi ta tashi. Zazzabi ne a jikinki ko? A'a kaina ne kawai kuma zai dena idan nasha magani. Mommy tace ku zama shaida idan har yarinyar nan tace bazata zauna da Junaid ba sai an raba aurensu. Hajiyan dangi zancen bai mata dadi ba ta kama hannun danta. Muje Allah Ya kyauta. Kwanaki uku bayan zuwan su Tilly jikin Hafsi ya warware sosai ga kulawar da take samu daga wurin iyayen Junaid. Hajiyan dangi taso komawa kano amma dole ta zauna har a shawo kan matsalar data kunno kai gidan. Su Nafisa kuwa kowacce ta koma gidan mijinta. Kirikiri aka hana Junaid ganin Hafsi gaba daya gidan ya masa zafi. Addua da yawan sallah yanzu kamar sabon limami don tsoronsa baya wuce a raba shi da Hafsi. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐28 Fizgo ta yayi har jikinsu yana haduwa da juna. Bata yi attempting ta gudu ba ta dai ki yarda su hada ido. Thank you kawai ya ce mata a daidai kunnenta a hankali ya fice daga dakin. Tunane tunane ta rinka yi barkatai game da feelings dinta akan mijin nata. Karshe dai ta tabbatar tausayinsa kawai take ji. Sai kuma ta koma tunanin yadda zata yi da su Tilly. Ita dai bazata je tace karya suke ba kanta tsaye don tsoronsu ma take ji. Dadin abin ma tunda suka kawo kansu gidan ai sun san abinda suka taka. Ita a wa taje ta karyata su ace garin yaya ta sani. Da kunya aji amarya tana labe. Tana ta tufka da warawara ita kadai har Hajiyan dangi ta dawo. Bayan sun gaisa tace kiyi hakuri na barki aikin jira ko. Ba komai Hajiya. Flask din kunun ta kalla au ina Junaidu? A nan na barshi fa zai sha kunu. Ya sha ya fita inji Hafsi. Kan wata kujera ta zauna tace Hafsatu. Naam ta amsa. Kin sanar da iyayenki abinda ya faru kuwa? A tsorace ta dago ido. Wallahi ban fadawa kowa ba. A'ah kwantar da hankalinki ai tambayarki nayi. Munyi shawara da su Rufai ne yace zaije har kanon ya sami babanki ya sanar dashi. Domin idan akwai cikin nan dole mu tsaya yarinyar ta haihu mu karbi dan. Gashi ma dai ana tunanin gara suyi aure saboda gori a nan gaba. Ko kadan ba haka muka so ba amma bazamu yi wata barnar ba don mu boye wata. Idan har kinsan bazaki iya zama da Junaid ba a haka kada kiji kunyar sanar dani. Ta dan gyara zama. Nasan iyayenki ma bazasu taba yarda ba. Kuma bazanga laifinsu ba ko nice abinda zanyi kenan. Duk maganganun da Hajiya take Hafsi ta gane so suke suji ko zata bukaci a raba aure. Ko kadan bata so iyayenta ma su san maganar. Ai idan auren ya mutu wani kashin kazar zata shafa wa kanta. Dama ummati ta fada mata a groups din whatsapp babu irin abinda baa fada a kansu. Da masu zagi da masu kiranta karuwa ma. Ai auren rufin asiri ne gareta sosai. Dan murmushi tayi cikin kunya tace Hajiya in sha Allah zan zauna. Har ranta taji dadi kuma tayi mamakin saurin amincewar Hafsi. Allah Yayi miki albarka Ya baku rayuwa mai albarka duniya da lahira. Ta kama hannayen Hafsi ta rike. Mungode sosai kuma zan kara jan kunnensa aka neman lahira da gudun duniya. Har hawaye Hajiya tayi tace bari na tashi na sanar da su Salma don su kunyarki ma suke ji. Baki ga baban naku bai neme ki ba. Yace bai san yadda zaiyi ya kalleki bane. Ranar da Hafsi ta cika sati su Nafisa suka zo gidan zasu yini. Hira suke sosai da Hafsi kamar sun dade da sanin juna. Suna nan zaune Junaid ya shigo dakin. Rabon da su hadu tun a dakin Hajiyan dangi. Wata doguwar riga ce fitted a jikinta kanta ba dankwali Nabilan Nafisa tana ta jagwalgwala mata kai wai zata mata kitso. Yana yin sallama tayi saurin sunkuyar da kanta. Sis ina ta nemanku ance min kunzo sai Amaka ce tace kuna nan. Hamida ta ce ai yanzu mu Hafsi ce yar uwarmu. Ka zama dan karo ko Yaya? Nafisa tace Hafsi baki gaishe shi ba. Kafin ta amsa yace kyaleta bashi take ci. Nabilatu na kice kike ja min kan mata haka ko? Ku kuma duk kun kyaleta sai ta tsige mata gashi. Dariya duk suka yi kaji mai mata donma kayi saa tana mata gyaran gashi. Yace nasan dai kara kike musu to baa yiwa dangin miji haka sai su raina ki. Filo nafisa ta jefa masa. Sannu kanwa uwar hadi tun yanzu zaka fara nuna hali. Ke Hamida dauko min 'yata mu tafi kai kuma ka zauna ka gyara mata. Nabila sai ihu take da Hamida ta dauko ta...ni kichu kichu anti. Tanayi tana dukan Hamida. Sai a lokacin tayi magana. Don Allah Hamida ku kyaleta. Ganin basu saurareta ba ta dauki hijab dinta zata bisu. Kafin ta gama sun fice harda rufo kofa. Suna fita harda tafawa. Bawan Allah Ya Junaid duk ya zama abin tausayi. Kiri kiri anki kai masa matarsa gidansa. Nafisa tace nasan fushi su Mommy suka yi amma ai zasu bari ta koma. Ko ba komai yanzu da kudi Junaid bazai kara bin wasu matan ba a waje. Abinda ya wuce kuma Allah Ya yafe mana baki daya. Amin Ya Allah. Batul Mamman💖 .TUN KAFIN AURE💐27 Hajiyan dangi ce kadai ke shiga sabgar Junaid. Shiyasa kullum yana dakinta. Hafsi kuwa dakin da aka bata kusa da na Mommy ne ko fita bata yi. Ranar laraba tana zaune a daki duk shirun ya isheta ta fito zata dakin Hajiyan dangi don yau bata leko sun gaisa ba. A bakin bene suka hadu Hajiya tace ina zuwa mamana? Ta dan sunkuyar da kai, dama gaisheki zanzo yi. Tayi mata murmushi to bazan amsa gaisuwar a nan ba. Karasa dakin ina zuwa. Zanje wurin babanku ne muyi magana. Ba musu ta karasa sauka. Sai dai kuma bata san ina ne dakin Hajiyar ba gashi ba damar ta koma sama ta tambaya. Wani corridor tabi tana tafiya sai ta jiyo maganganu daga dakin. Babu shakka wadannan matan ne ke maganar. Kamar ta wuce sai ta tsaya daf da kofar. Daga ciki ta jiyo daya daga cikinsu tana magana da fada fada...kai banza so nake kawai kayi karyar kaine babana. Ka sami wasu da zaku zame min iyaye. Wallahi babbar harka zan baro mana idan kuka yi kuskure kuma Allah kashimu ne zai bushe. Sai wata tace ke komai akayi dake sai kinyi hauka ki rage muryarki mana. Wannan karon sai da Hafsi ta hada kunnenta da kofar take jin me ake fada. Bayan dayar ta gama wayar tace ni yanzu Rosie ya zanyi idan suka kaimu asibitin ayi min test. Gashi kece mai cikin bani ba. Hasbunnallahu wa niimal wakil. Ashe karya suke babu wani ciki. Bata san dalili ba amma har ranta taji dadin wannan zancen. Rosie tace kada ki damu Tilly nasan yadda zamuyi da komai. Ke dai idan kika yi kokarin yaudarata idan kika shigo gidannan sai na koya miki hankali, itama wannan matsiyaciyar amaryar tasa sai nasan yadda nayi aka saketa ko ta nemi sakin da kanta. Ni bani maganin nan na kara sha naji cikina ya fara ciwo ciwo. Gara shegen yayi ya bare kowa ya huta. Tilly ta kalleta ki hakura ki haifeshi ni yanzu da ko shege ne ina so. Ai tunda likitan nan yace mahaifata ta lalace nake jin son haihuwa. Rosie ta tabe baki...wanan dai sai suck away in kin matsu kije gidan marayu. A sanyaye Hafsi ta cigaba da tafiya. Wata mai aiki ta gani ta tambayeta dakin Hajiya ta nuna mata. Tana shiga ta tarar dashi zaune kan carfet yana shan wani abu a cup. Ganin tayi turus ita bata shigo ba ita bata fita ba yayi dan murmushi mai cike da bakin ciki. Hafsi Hafsi ko na fita ne don ki sami sakewa? Dan kwarin gwiwa da samu data tuna cikin ba nasa bane ta shigo. Ina kwana ta fada tana dan durkusawa. Ajiye kofin yayi yana kallonta cike da mamaki. Hala ta manta abinda ya faru a kwanakin da suka wuce. Kai fa ka fiye kallo kuma na fada maka babu kyau. To ranki ya dade na dena daga yau. Rufe idanunsa yayi ya dauki cup din kununsa ya cigaba da sha. Jin wani daddadan kamshi kusa dashi yasa ya bude idon. Hafsi ce zaune a kasa kusa dashi. Tayi yar ajiyar zuciya. Junaid, bata taba kiran sunansa ba sai yau shiyasa yaji wani dadi. Sai ya wayance. Ke mijin naki kike kira haka ba ko yar alkunya irin na matan hausawa. Komai bacin rai baya rabo da wasa. Kafin tayi magana yace kina hararata fa zan...sai ya kashe mata ido daya tsire miki ido zanyi. Ai kayi kama da mugaye dama. Ya mike tsaye ni din? Ashe baki da ta ido yar nan. Yadda ya rike haba yasa tayi dariya. Duk da yana tare da damuwa ya koyawa kansa hakuri. Har yana tsokanarta. Wani serious look ta gani a tare dashi. Yace Hafsi Hafsi why are u being nice to me? Ta dan kalle shi, saboda i believe you. Bangane ba ya fada cikin rashin fahimta. Bazan miki karya ba nasan Tilly kuma cikin jikinta maybe nawa ne. Na sani ta bashi amsa. Na dai yarda ba...ba raping dinta kayi ba. Tana gama magana ta mike zata gudu. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐29 Hannun kofar ta kama amma saboda yadda take hanzarin fita sai ta kasa budewa. Hijab din ma saboda karar jan kofar da Nafisa tayi a baibai ta saka shi. Duk abinda take idanunta na kansa don tsoro take kada ya karaso inda take. Wani irin kallo ya rinka yi mata ko kifta ido baya son yi. A hankali taga yana matsowa inda take. Cikinta har wani sauti yake bayarwa saboda yadda ta kideme. Da kyar ta iya cewa nifa bana son kallo. Bai dakata ba da tafiyar sai da yazo gabanta. Da zaa taba kirjinta sai anji bugun zuciyarta da sauri da sauri. hannunta ya kama ya jawota ciki ya zaunar da ita kan kujerar gaban dressing mirror. Ji yadda jikinki ke bari kamar kinga wani dodo ko irin kinzo yi min sata na kama ki. Yadda yake maganar ne ya sata dan guntun murmushin yake. Shiru tayi tana tsoron kada Hajiya ko Mommy wani cikinsu ya shigo dakin tunda suna shigowar kullum. Ganin yana neman cire mata hijab ta fara kokawar rikewa. Ya kalleta ya sha kunu wai ni da jikina ki rinka rufe min. sai anyi magana ki rinka wani abu kamar wata malama. Ta zumburo masa baki, to yanzu me kake so ayi. Da faraarsa yace ki cire na gyara miki gashinki ko baki ji me Sis ta fada ba. Tayi masa fari da ido ai da ka sani salon ka bude sai ka rinka gyaran gashi. Gaba daya ta ruda shi da yadda tayi masa fari da ido har ya kasa magana. Tana ta surutu ita daya sai gani tayi yana kici kicin cire mata hijab. Ihu ta fara masa wallahi idan ka matso zan bude murya. Ganin duk a tsorace take yayi dariya duk wanda ya shigo taimakonki sai ya tayani cire miki hijab din, bari ma na kulle kofar kinsan leke dakin newly weds hatsari ne. Yana zuwa bakin kofar duk cikinta ya gama durar ruwa sai kawai taga zai fita daga dakin...take care Hafsi Hafsi. Murmushi ta sami kanta da yi bayan ya kulle kofar ta fada gado ta kwanta. Hajiyan dangi suka gani a dakin Mommy suna ta hira. Suna zama Mommy tace dama jira nake ki fito Nafisa. Lafiya dai ko Mommy? Ta tambayeta. Eh to wannan makociyar taki nurse nake son ki kira tazo gida tayiwa yarinyar can test a tabbatar da cikin. Hamida tace Mommy ana yin scanning fa dashi ake fadar EDD. Nafisa ta buge mata baki to banza wa ya fada miki we are intrested muji lokacin haihuwar. Hajiya tace kunga ni ku nutsu idan kinje gida ki fada mata ko zuwa gobe ne sai kuzo tare. Amma abinda Hamida ta fada gaskiya ne. Idan anyi mata gwajin sai ayi scaning din. Nafisa ta mike bari naje na fada musu don su zauna cikin shiri. Hafsi tana fitowa zata dakin Mommy ta ga Nafisa tana dawowa daga dakinsu Tilly. Hannunta Nafisa taja suka shiga wani karamin falo. Suna zama Nafisa ta ce Hafsi what do you think of Junaid? Kasa ta sunkuyar da kanta. Tana jin nauyin Nafisa sosai don ma ita din tana da wayewa ta iya jan mutane a jiki. Ta dan taba ma Hafsi kafada ina jinki kanwata. Jin ta sake yin shiru tace nasan Junaid ya taba rayuwa mara kyau irin ta 'ya'yan masu kudi marasa kwaba amma duk irin halayensa he is not a rapist. Kuma a irin ji da kansa na da fa banda yanzu, bazai kula mai kati ba. Ko da wasa bamuyi tunanin zaiyi aure ba nan kusa amma sai gashi yana ganinki ya canja sosai. Banda degree yana da masters har biyu amma yaki aiki sai kashe kudi. Sai gashi jiya Alhajinmu yace yayi masa maganar yana son fara aiki. Hannayen Hafsi ta kama ki daure ki zauna dashi don Allah na tabbatar he will be a better person. Ganin Nafisa na hawaye Hafsi ta suma kuka itama. Cikin kukan ta fadawa Nafisa abinda taji daga dakinsu Tilly. Murnar Nafisa har zuci tace kada ki fadawa kowa da sannu asirinsu zai tonu. Scanning zan kaita shegiya gayyar tsiya. Har suna da guts din shigowa gidan nan. daga nan suka zauna suna tattauna yadda zasuyi karshe Nafisa tace idan kin amince zanyi magana a kaiki wurin mijinki. Dammmm zuciyarta tayi don tsoro. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐30 Washegari gari da safe Nafisa tazo da Mariya nurse. Ita tayi musu jagora zuwa dakin su Tilly. Senator Rufai tun da suka zo gidan zama ya gagare shi ko kadan baya kaunar haduwa dasu gashi bazai iya korarsu ba har sai sunga yadda al'amarin zai kasance. Tun daren dama Tilly ta gama tsorata Rosie tace ki kwantar da hankalinki nifa abu irin wannan baya tsorata ni. Zamu sami mafita cikin ruwan sanyi. Ko da su Nafisa suka shiga dakin a kwance suka tarar da Tilly , Rosie tana rirriketa tana ta amai. Laulayi dai kamar gaske. Nafisa ta kawar da kai gefe dama bata sanar da Mariya ainihin alaqarsu ba. Ita ko sunansu ma bata sani ba. Ta yi mata kallon banza ki tashi za'ayi miki test. Rosie ta yi kalar tausayi to bari na taimaka mata ta gyara jikinta. Mariya tace ai fitsari kawai nake bukata ma idan kun shiga ga wannan robar ta mika mata irin sample bottle din asibiti sai ku kawo min a ciki. Kadan ma ya isa. Nafisa tace kiyi mata na jini kawai ance yafi nunawa. Nan da nan suka hada ido a tsorace. Tilly ta fara hawaye don Allah kuyi hakuri bana son allura. Nafisa tace ke da zaki haihu meye abin tsoro a allura. Mariya tace ki bari kawai muyi na fitsarin idan bai zama clear ba sai na debi jinin. Rosie ce ta kamata tana tafiya a hankali har suka shiga toilet suka rufo kofar. Tilly ta gyara jikinta tana tsaki ta sassauta murya kinji waccan yarinyar wai blood test? Idan ta shiga hurumi na bazan mata ta dadi ba. Rosie ta rufe mata baki sai an ji mu. Ungo ni ta mika mata robar data cika taf da fitsari. Kamar ta rike kashi haka Tilly ta karba ta fito ta ajiye a gaban Mariya. Duk suna kallo ta saka PT strip din a cikin robar ta fito dashi ya nuna layi biyu alamun ciki. Mariya tace ai kinga ma Nafisa ya nuna basai munyi na jinin ba. Nafisa a ranta tayi kwafa dama tunda suka shiga toilet tare tasan akwai abinda zasuyi. Ta kalleta harda dan guntun murmushi sannu Allah Ya raba lafiya. Yanzu gobe zan kaiki asibitin da nake zuwa sai ayi miki ultrasound gara mu gani kila ma biyu ne babies din. Nafisa dai dariyar da take harda ta mugunta suka fice ita da nurse. Suna rufo kofar Tilly tace na shiga uku ya zanyi ne Rosie gobe asirina zai tuno. Kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Wannan yar kwailar matar tasa zamu kullawa. Idan zai aureki ai gara ki zauna ba kishiya muci karenmu ba babbaka Talatu. Suka tafa sannan tace akwai dan taimako daga wurin malam fa sunansa makalemata. Idan lokaci yayi zan baki ki yi amfani dashi. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐32 Wani irin radadi ne ya ziyarci kafafunta duka biyun ta runtse ido ko motsi ta kasa yi saboda duk wurin pieces din glass ne. Tilly kuwa kwanciya tayi wanwar a kasa tana kwarma wayyo cikina, wayyo ta kashe min da na shiga uku. Rosie tace kiyi hakuri Talatu ki mike tsaye. Hafsi ta kallesu tana cewa sannu amma duk kafafunta sun kone saboda zafin abincin harda cikinta don karamin mayafi ta yafa sanin cewa babu ma aikata maza da ake bari su shigo cikin gidan. Ga plate din da ya tarwatse wasu duk sun soke mata saman kafafunta. Duk da haka bata damu ba ta duka tana son taya Rosie ta daga Tilly tsaye. Hannunta taji Tilly ta make tana kara sautin murya. Muguwa azzaluma don kawai ina da cikin mijinki shine kike son zubar min dashi. Wallahi duk abinda ya sami dana kotu ce zata raba mu. talakar banza. Wawan mari Talatu taji an dauketa dashi. Mommy ta sake daga hannu Hajiya ta riketa yi hakuri Salma muji abinda ya hadasu. Rosie cikin kukan makirci tace Talatu ce ta fito zata sha iska tace dakin yana tayar mata da zuciya. Tana fitowa wannan yarinyar ta nuna Hafsi, mommy kuwa ta make hannun karki sake nuna min yarinya da yatsa wallahi. Rosie ta share ta cigaba da magana kawai tana ganin Talatu sai tace mata zanga yadda zaki haifi dan shege a gidannan. Tray din da plates din da ke kai duk ta tura mata a ciki. Hajiya ko kadan bata gaskata zancen ba ganin yadda Hafsi ke kuka tace mamana me ya faru. Hafsi ta fadi iya abinda ta sani. Mommy ta kama hannunta su koma falo ayi maganar. Sai a lokacin suka kula da yadda jini ke bin kafar Hafsi ta dama Mommy tace maza a kira mata Junaid yazo ya kaita asibiti. Da fara'arsa ya shigo falon. Mommy daga nasa yarki dafa min indomie sai ace in kaita asibiti. Ko ta kitse albarka. Gunjin kukan Tilly yaji daga bayansa ya juya da sauri lafiya? Rosie hade rai ka tambayi matarka da take son zubar wa Talatu da ciki. Yace au ashe sunanta Talatu ai na zata Tilly ne. Muryar Mommy yaji tana kiransa. Ya zan aika a kira ka sai kazo kana wani zancen daban. Ka dauko key mukai yarinyar nan asibiti nace. Ya kalle Hafsi duk fuskarta hawaye yayi saurin karasawa gabanta. Me ya faru Hafsi garin yaya kika ji jiwo? Mommy tace ka tashi mana ka zauna kana mata tambayoyi. Suna shiga motar Nafisa na isowa Hajiya tace ta debo su Rosie su taho tare. Amma ta taho da security don kada su zama su kadai. A motar Junaid kuwa Mommy tana ta balai ya dauko musu masifa har gida. In Allah Ya yarda sai cikin ya zube. Ga Hafsi nan ki saki jiki kiyi ta zuba masa 'ya'ya tunda su yake so. Hajiyan dangi ta gama waya da senator ta sanar dashi halin da ake ciki sannan ta dubi mommy tana bata hakuri. Junaid kuwa banda sannu babu abinda yake fadawa Hafsi. Hawaye ne wani ke bin wani a idanunta don ita kadai tasan me take ji musamman a cikinta. Ga babban mayafi ta yafa wani karin zafin a cikin. Suna isa asibiti Junaid daukarta yayi don ganin yadda kafar taki dena jini. Emergency aka shige da ita da Tilly. Kururuwa kawai Tilly take yi ita tasan danta ya mutu. Ai kuwa basu dade ba nurse ta fito tace Tilly tayi bari. Nafisa ta rike baki cike da mamaki wato don sunji yau zaayi scanning suka bullo da wannan abin. Dariya tayi tana gyada kai sai tayi maganin mutanen nan. Junaid yana tsaye doctor ya zare glass dinda ya shige kafar Hafsi yana ta mata sannu. Bayan an gama cirewa ansa plaster ya lura ta kasa kwanciya da kyau yace Hafsi akwai inda yake miki ciwo bayan kafar ne? A hankali ta daga kanta tace cikina. Fatar ta daye. WHAT??? Shima ya gama tsorata yayi saurin cire mayafin ya nunawa doctor din. Da almakashi ya yanke barin rigar daya kwanta akan cikin yace yi hakuri fatar bata cire ba. Ya dauko magani zai saka mata Junaid ya karba don tuni ya kule da kallon da yake mata. Dr bai ma san me yake ba ya nuna masa yadda zai shafa ya fita. Ba karamin tausayi ta bashi ba yana shafawa tana runtse ido duk hawaye. Sai da ya gama ya duka yana hura mata cikin tuni ta hadiye kukan. Ya dago kansa sannu kinji Hafsi rabin raina. Ashe tsautsayi ne yasa nasa ki girki. Amma me ya hadaki da waccan. Fada masa komai tayi yace ba komai. Allah Yayi mana jagora. Dr Sunusi yana fita Nafisa ta ja shi suka yi magana tace dr ina jin yarinyar nan cikin karya gareta. Yace ya akayi kika sani tace yar uwarmuce ce daga garinmu ina jin karya take ta matsu ne ta haihu sai tayi ta kiran cikin karya gashi kwanaki tayi bari baa wanke cikin ba. So nake don Allah kayi mata wankin ciki zan biya ko nawa ne. Bani da burin da ya wuce Talatu ta sami haihuwa. Ta dan matse hawaye. Dr Sunusi yace ba komai Hajiya ki kwantar da hankalinki. Yana fita Nafisa tace shegiya ai karen bana shike maganin zomon bana. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐31 Senator Rufai ranshi duk a bace da aka sanar dashi result din test din. Ya kalli Hajiya ni yanzu ya zanyi da Hafsatu? Duk irin abinda ya faru kafin a bashi aurenta gashi kuma baaje ko ina ba rayuwarsa ta baya tun kafin yayi aure tana dawo musu. Hajiya tace ni dai idan zaka dauki shawarata Rufai kabari yarinyar nan ta tare. Kullum mu kwana mu tashi da ita bata san makomar aurenta ba ai kaga ba dadi. Irin wannan ne idan iyayenta suka sani lamarin sai ya baci fiye da yanzu. Mommy tace anya Hajiya a bar shi da yar mutane kuwa? Bafa kowacce mace bace zata yarda ta zauna da mutumin da yake da da a waje ba. Wata ko dan kishiya bata so bare dan kafin fatiha. Senator yace to ku bani zuwa wata asabar din sai a kaita. Kisa su Hamida su tambayeta irin kalar motar da take so ma. Mtsw Ya danyi tsaki yaron nan bai min adalci ba wallahi. Gara tun da sauran mutumci na naje har gida muyi magana da babanta. Zaman dakin duk ya isheta tana ta canja tashoshi babu wani abin kallo ta mike ta daga labule tana kallon waje. Tun jiya da su Nafisa suka zo da nurse bata sake fita daga dakin ba, Nafisa dai ta fada mata zasu dawo ta kai Talatu scanning. Tun dazu take jiran zuwansu ko ta sami abokin hira. Su mommy suna iya kokarinsu wurin debe mata kewa sai dai kuma suna cikin damuwar maganar cikin nan. Tana dan tunaninta ne ta kalli kasa suka hada ido da Junaid. Wani abu ne ya ratsa mata zuciya har kafarta. Murmushi yayi mata tayi saurin sakin labulen. Ta koma ta zauna bakin gado. Meyasa take saurin rikicewa ne akan Junaid..abinda take tambayar zuciyarta kenan. Meyasa zata masa rowar kyakkyawar fuskarta ne. Su Hajiya suna masa gashin kuma gashi yanzu yana cikin jindadin kallonta ta gudu. Girman laifinsa yasa ya danne zuciyarsa bai

Chapter 6 of 10