Share this page
5 / 10
wani shishshige musu take taga kudi. Ranar dinner wasu kaya da mama ta kure basira ta dinka Hafsi ta saka. Ummati tana zuge mata zip din rigar Hamida ta shigo da wata riga da skirt na lace ne ko material gashi nan dai abin mai daukar ido golden brown. Tunda aka fara biki ta likewa su ummati sun zama kamar kawaye. Kayan hade suke da takalma da head and veil. Hafsi ta bata rai ni fa wanan zan saka mama ce ta dinka min. Hamida ta marairaice haba matar yaya anko yake son kuyi da kansa ya bayar aka dinka miki. Suka shiga ban baki ita da Ummati amma sam Hafsi taki yarda har zancen yakai kunnen mama. Nan tayi musu sulhu gobe idan zaa kaiki sai kisa nawan zan ga mai hanaki amma yau dai ki saka na angonki. Maman ummati tayi dariya to yar shagwabar Mama gobe dai zanzo da bokitin share hawaye. Taro yayi taro wuri ya cika da mutanen da suka amsa sunansu a naija. Yan mata anyi dinkunan rashin mutumci suna tafiya kamar sanduna babu lullubi. Matan aure sai hura hanci wai kar a raina su. A mota aka tsayar da hafsi har Junaid ya iso. Ko da ya fito da shaddarsa golden brown bata gane shi ba. Duk da yasa hula ta kula yayi aski, ya gyara fuska gaba daya ya canja. Shima kallonta kawai yake har ya karaso. A kunnenta ya rada mata ni kada ki cinye ne da kallo, it has been three weeks, kin kara kyau kema. Cak ta tsaya saboda yadda yayi kusa da ita. Ana fara musu alamar su shigo cikin hall din taji yana kokarin kama mata hannu. Kokarin fizgewa tayi shi kuwa ya matse hannun ga zobba a hannun har ta fara jin zafi. A hankali tace kaci bashi wallahi. Ya sassauta rikon suka shiga. Dinner tayi kyau kuma ko liki baayi ba wannan kuma dokar Hajiyan dangi ce. Tilly da aminiyarta Rosie ma sun sami shiga a wurin daukar hoto Junaid ya gansu. Tsoro ne ya kamashi ya hau adduar kada tayi masa wani haukan a wurin don bai ma tsaya tunanin yadda suka sami katin shiga ba. Bayan sun dau hoto ta bashi wani envelop congrats Juni boy. Hafsi ta dan kalle ta Tilly tace amarya mun dai rigaki lasar zumar muna fata tayi miki dadi yadda....junaid ne ya katse ta get out...ba musu ta kama kawarta suka fita don idanunsa sunyi jazur tasan halinsa sarai. Babu wanda ya kula sai Hafsi kowa na shaanisa. Dreba ne a gaba sai Ummati baya kuma Junaid da Hafsi don ya nace shi zai mayar da ita gida. Tayi kokarin daurewa ta kasa can kasa kasa tace wace wannan matar ne. Dama ransa ya gama baci gashi yana son dena shaye shaye babu ko taba a aljihunsa ya harareta idan zaki bude baki kiyi magana ki bude sai wani kasa kasa kike da murya kamar wata mumina. Ummati ta juyu don taji me yace...zare mata ido yayi ke bana son gulma me kike kallo. Ba shiri ta juyar da kanta. Tooooh wannan ne mijin da Hafsi zata zauna dashi. Hafsi dai shiru tayi tana kallon fuskarsa. Sai tayi da gaske akan wannan mutumin. Abu daya ta sani dai da yana cikin farin ciki kafin yaga wannan matar. Babu ko sallama suna zuwa gida suka fita yace da dreba yaja motar su tafi. Daki ya shiga hankalinsa a tashe yana tarrabin abinda ke cikin takardar da Tilly ta bashi. Juni boy Nasan kana cikin farin cikin auren da zakayi gobe nima ina taya ka murna. Sai dai ina me tabbatar maka gobe zanzo Abuja a tawagar amarya. Ga wedding gift nan. Luv Tilly Bude daya takardar yayi gumi ya karyo masa ganin reult ne dake tabbatar da Tilly na da ciki har wata uku. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐 22 Ko kayan jikinsa bai canja ba ya fita zuwa hotel din da abokinsa Imran yayi masauki. A waje ya tsaya yayi masa waya. Sai a karo na uku ya dauka ya sanar dashi yana wurin parking ya fito. Suna hada ido Imi yace yace ya mutumin you sounded worried fa. Me ya faru ne? Envelop din Junaid ya mika masa. Imi ya rinka dariya bayan ya karanta harda hawaye a idonsa. Can ya daki kafadar junaid...haba mutumina kada ka bada ni mana. Yanzu har akwai wata chick da zata ce kayi mata ciki ka yarda? Matan nan fa sun fi mu tsoron faruwar hakan tunda su ke da wahala. Wani abin kawai take so. Fuskar Junaid babu sauran kwanciyar hankali uhm uhm Imi aure fa zanyi kuma Allah Ya sani ina son yarinyar ina kuma son gyara rayuwata. Kaima Allah Ya baka tagari. Kayya yaro gigin soyayya ke dibanka bari romon ya kare zaka neme ni ne. Bayan ina kallo dazu amaryar taka ta murguda maka baki. Kansa ya shafa yana dariya da irin tsokanar fada ne yaga tana kulashi shiyasa yake mata haka a fili yace Kai kam kamar ana kada maka gangar shaidanu..ya ina cewa zan shiryu kana min mugun baki. To yi hakuri na Hafsa Imi ya fada yana dariya...yanzu dai ka manta da wannan yarinyar kada ma ka sata a rai. Idan ta sake nemanka kaci ubanta da kyau wallahi zata kyaleka. Kada ma ka fara bata kudi don sai tayi blackmailing dinka. Nan suka yi ta shawara sai wurin ukun dare Junaid ya koma gida. ****************** Bacci sam yaki zuwa idanun Hafsi sai tunani take kala kala. Wannan Junaid din dabiunsa na bata tsoro( wai ma don ya rage!) Gashi haka hankalinta bai kwanta da matar da ta bashi envelop ba. Maganar Tilly duk ta tsaya mata a rai wai sun rigata lasar zumar.....ehew abin kyankyami ma zancen ta fada a fili tana yamutsa fuska. Anya ba yan is...sai tayi shiru zargi babu kyau don haka mafitar ta daya shine ta mike ta dauro alwala ta tayar da sallah. Haka tayi ta nafila har asuba tana addua sannan ta yi bacci. Sai wuraren goma na safe ta farka. Shima Hadiza ce ta tasheta da dundu...to kasa ana shirin fita daurin aure kina kwance kina bacci hankali kwance. Mutssika idanu tayi ta mike...ina ummati ta tafi Yaya? Debo miki ruwan zafi kiyi wanka. Kinsan dai baffa yace karfe biyu zaa bar kano so kiyi da jiki kafin a dawo daga daurin aure. Ta kalli agogon wayarta...Allah sarki nan da mintuna arbain da bakwai kin zama matar aure. Cikinta taji yace kulululu da gaske abin yazo. Kuka tasa wa Hadiza inama basuyi wadannan hotunan ba tun kafin aure da yanzu Saif ta aura. Ummati ta ajiye bokitin hannunta ki gode Allah baa daura dashi ba don yadda aka ce Junaid yayi bayan yaga hotonki da kila a gidan auren zai biyo ki ko ma ya kashe auren. Hadiza tace kyale ta ummati ai tasan wani baya auren matar da ba tasa ba. Kayan da mama ta dinka da aka hanata sawa daren jiya su tasa ai kuwa tayi kyau sosai. Katon mayafi ta yafa ga kamshi ko ta ina. Taro yayi taro don manyan mutane na kusa da nesa sunzo bikin dan manya. Junaid yasha cream shadda harda babbar riga da brown din takalmi da hula maroka suna ta sanaar su. Daga karshe dai Liman ya daura auren Junaid Rufai Bukar da Hafsa Aminu Garba. Mijin Hadiza ne ya bugu ya sanar da ita an daura auren kan sadaki dubu dari gida ya cika da guda da hayaniya. Wata 'yar makarantarsu tace gaskiya Hafsa Aminu kinyi saa muma Allah Yasa mu a danshinku. Yan Amin kuwa suka amsa. Ansha koke koke lokacin dasu Hajiyan dangi suka zo daukar amarya. Mama kasa daurewa tayi ta kulle kanta a daki. Baffa ma yana mata nasiha yana sharar kwalla. Bai taba tunanin zata yi auren nesa ba, aure ma irin na gidan Senator Rufai Bukar. Motoci har wajen layinsu Hafsi. Cikin motocin kuwa harda wadda Rosie da Tilly suka dauko haya suka bi ayarin kai amarya. Don karfin hali har mutane uku suka dauka aka dauki hanyar abuja. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐 24 Dakata Imi zanyi maganinta da kaina. Cheque ya bata na dubu dari biyu. Idan na sake ganinki duk abinda ya faru dake ki kuka da kanki. Suna jan mota ta fita ta tari taxi don yau Rosie bata biyo ta ba saboda laulayi daya fara damunta. Murna take sosai don wannan cheque din sabon makami ne a gareta. Daki aka bawa Hafsi da kawarta sauran yan biki suna wani masaukin. Nafisa ta tafi da yayarta Hadiza gidanta ita kuwa Hamida ta nace tare zasu kwana da amarya kafin washegari a kaita side dinta. ****************** Wani sabon kukan Hafsi da Ummati suka dasa lokacin da aka fito rakasu bakin motocin da zasu mayar dasu kano. Yanzu haka zata zauna da mutanen da bata gama sanin halinsu ba. Ga uban gayyar wato Junaid ko doriyarsa bata sake ji ba tun a wurin dinner. Kamar yasan tunaninsa take sai gashi ya fito da kananan kaya a jikinsa. Yau ma yayi kyau tunda kayan ba oversize bane. Har kasa ya durkusa ya gaishe da gwaggwaninta dasu Maman Ummati. Hadiza ta rungumota tana ta bata baki akan ta dena kuka haka. Kyaleta Hadiza na gulma ne fa kuna tafiya zata sake. Harararsa tayi yace ai gara ki nuna musu halin da kike min. Hajiyan dangi ta kama hannun Hafsi rabu dasu zan miki maganinsu. Anisa ta Amira ma sunyi nasu kukan da alkawarin zuwa idan anyi hutu. Haka dai suka rabu abin tausayi ana janye Hafsi daga jikin Ummati. Bayan duk sun tafi aka dawo falo. Hajiya da mommy suka yi musu nasihohi da fatan alkhairi. Nafisa da Hamida suna gefen amarya suna kula da masu dada share wurin kafin su kaita. Sai da aka gama fadan Junaid yace to Allah Ya saka da alkhairi amma yaushe zaku bani matata? Mommy ta cire takalminta ta jefa masa to tsohon mara kunya ai gara ka nuna hali. Ya dafe kai Hajiyan dangi tana duba masa...yauwa Hajiya duba ki gani ko kan ya fashe. Hafsi kuwa dariya tayi har sauti ya fito yace kinci bashi Hafsi Hafsi. Nan suka zauna ana ta raha sai kawai suka ji sallama. Mata ne biyu sunsha hijab daya sai kuka take dayar tana bata hakuri. Dif Junaid yayi ya dena dariyar da yake saboda ya gane mai muryar. Zuciyarsa ke bugun uku uku yaji yawon bakinsa ya kafe. Itama Hafsi ta gane yarinyar ko baa fada ba tasan akwai matsala don ta kula da yadda ya kidime da ganinsu. A fusace ya kallesu ubanwa yace ku shigo har nan? Wai ma waye ya baku izinin shigowa. Mommy da Hajiya cikin rashin fahimta suke kallonsa. Junaid kana hauka ne zaka ga baki kayi musu irin wannan tarbar? Rosie ta kiyi hakuri Talatu an gama cutarki shine zaa ci mutumcinki saboda baki da galihu. Mommy tace ku zauna muji abinda ya kawo ku. Tilly harda fyace majina ai yafi kowa sanin dalilin zuwanmu. Idanun Junaid kamar an bada masa yaji yayi kanta yana sirfa mata zagi. Kana tabata zansa a kulleka mara mutumci kawai. Daga kai yayi suka hada ido da Senator Rufai. Alhaji wai me ke faruwa ne? Yace ku zauna muyi magana. Su Rosie aka wani rakube a kasan carfet ita da Tilly. A bakin gate na gansu suna fada da security yarinyar can ya nuna Tilly tana ta kuka. Ganin haka na tsaya aka kirasu tayi min bayani. Cheque ya dauko daga aljihunsa ta mikawa Mommy. Kingani kudin daya bata jiya wai taje a zubar mata da ciki. Kinga goshinta inda ya fashe lokacin da yake dukanta ta fadi. Kamar anyi masa wanka da ruwan zafi haka yake ji. Me tilly ke nema ne a tare dashi? Kokari yake su hada ido da Hafsi ita kuwa idonta na kasa tana kuka a hankali. Salati su Hajiya suka hau yi tace lalacewar taka har ta kai ka bada kudin yin kisa. Kuka ne ya kwace musu ita da Mommy. Junaid yana ta basu hakuri. Hafsi ta mike zata shige daki don taga zancen kamar ba nata bane. Dawo dawo ai gara kada a munafunce ki Hafsa. Senator ne ya kirata ta dawo ba musu. Ya maida kallonsa ga Junaid. Ka san yarinyar nan? Eh na santa amma wallahi ban dake ta ba. Rufa min baki shashasha. Kullum yadda zaka zubar min da mutumci yake nema. Ko tsoron mutuwa baka yi. Ke ya daka ma Tilly tsawa ta dago a firgice garin yaya kika amince masa. Ta kara jan majina ta fara bada labari. Ni ina sayar da kati ne kusa da wani club da suke zuwa a gidan wannan yayartawa nake da zama shine ya biyoni wai yana sona. Rannan rannan sai kuka....Rosie tace kudin kati yace taje ta karba shine yayi mata fyade. To ganin cewa danka ne bamu daga zancen ba. Wallahi Álhaji karya suke duk karuwai ne....bakinsa yaji Hajiya ta make. Rufa mana baki. Rosie ta cigaba to da mun hakura sai kuma ga ciki shine muka neme shi kawai jiya sai yazo har gida ya bata cheque ita kuma ta karba don taga bana nan. Hafsi tayi saurin daga kai tace ba kece kika zo wurin dinner ba kuwa daren jiya? Junaid yace yauwa Alhaji wallahi kaga itama zata min sheda wurin dinner ta biyoni ba raping dinta nayi ba. Mommu tace Hafsa kada ma ki fara kare masa don bakisan waye Junaid ba. Duk abinda akace yayi zan yarda. Allah wadaran iskanci yau mahaifiyarsa ma taki yarda dashi. Senato Rufai ya kalli dansa cikin bacin rai yace ka taba ganinta? Eh ya amsa masa. Muamala ta shiga tsakaninku? Shiru ya kasa magana. Ya daka masa tsawa kai kurma ne. Hawayen da yake boyewa ya sauko yace eh. Innalillihi wa inna ilaihi rajiun. Koda ba auren so suka yi ba amma ace mijinka yana neman mata akwai ciwo. Hafsi duk auren ya kara fice mata a kai. Senator yace to ke zaa kaiki asibiti a sake miki gwaji idan ya tabbata da gaske yayi wa Junaid wani mugun kallo zamu jira ta haihu a aura maka ita. Mikewa yayi a fusace su Hajiya suka bi bayansa. Batul Mamman TUN KAFIN AURE💐23 Tunda suka hau hanya basu tsaya ba sai a garin Abuja. Motar da Baffa ya hado da kayan da yayi wa 'yarsa ita ce ta karshe cikin jerin motocin. Duk girman gidan ba duka motocin bane suka sami shiga ba saboda yawansu. Shima gidan cike yake da mutane gashi basu iso da wuri ba. Dakin mommy su Hamida suka kai Hafsi. Ita dai kanta a kasa taki dagowa ta kallesu. Mommy cike da murna tace nasan kun gaji ga magriba ta kawo kai a kai su masauki suyi wanka aci abinci sai su shirya akwai wata dinner din karfe takwas. Hafsi ta kankame hannun ummati sai Nafisa tace mommy wanan fa aminiyarta ce tare zasu zauna kafin anjima ta dan kanne ido ai sai kamarsu ta Junaid ta kara fitowa Hafsi tayi saurin dauke ido. Suna idar da sallar magriba akace Hafsi ta shiga wanka. Komai na toilet din daban yake...oh su Hafsi a toilet din matar sanata. Tana fitowa Hajiyan dangi ta tarar suna hira da mommy sai ta kasa fitowa. Hadiza da Nafisa wadanda tuni jininsu ya hadu kamar sun dade tare suka fara mata dariya. To yan nema da girmanku kuna tsokanarta ko. Fito kinji Mamana ni da nake so nan da yan watanni nazo yi miki wankan jego. Ai Hafsi ji tayi kamar ta nutse a kasa Mommy tace Hajiya banda kwacen 'ya fa. Fita suka yi aka hau shirin amarya. Kwalliyar yau tafi ta sauran events din. Suna gamawa kowacce ta dau ado jiki da fuska aka fito. Motar da tafi kowacce kyau daga tsakiya wani abokin Junaid ya bude mata kofa ta shiga ya rufe. Taso kwarai Ummati ta shigo sai kawai taga angon nata ya bude kofa ya shigo. Ko tari bata yi ba don ganin yadda yake mata wani irin kallo. Ganin abin yayi yawa tace ya dai? Kamar ya, ya bata amsa. Ta dan turo baki kallo dai idan yayi yawa kuma zai shiga babin haramun. Yayi yar dariya Hafsi Hafsi kenan malaman karya. Wa ya fada miki kallon miji ga matarsa yana ciki. Yadda tayi da bakinta yasan sarai murguda masa shi zata yi. Yarinyar nan akwai tsiwa. Yace to basai kin murguda min baki ba idan kina son kiss, you just need to ask. Sakin baki tayi tana kallonsa lallai ma mutumin nan..dole ta fasa ta kara hararsa. Yayi dariya sannan yace karamar mara kunya kawai.Hular kansa yasa ya rufe fuskarsa. Idan mun isa ki tasheni jiya banyi baccin kirki ba. Ko kula shi bata yi ba ta juyu tana kallon garin da bata taba tunanin zuwansa ba nan kusa. Nicon Hilton suka shiga. Manyan mutane da dama sun halarci taron. Su mommy ma da sauran matan manya sunzo amma shadaya suka koma gida. Sai wurin shabiyu da kwata mommy tayi wa Junaid waya kan su taho gida haka saboda Hafsi da suka yi zaman mota. Ummati da Hafsi suna ta hira kafin motar da zasu shiga su karaso gabansu idon Hafsi yakai kanta. Tabbas matar da tazo wurin dinner dinsu ta kano ce. Matsowa tayi gaban Hafsi tana tafiya duk jikinta na girgiza amarya mun sake haduwa ko. Ga naki gift din nasan Juni boy da rowa baiyi sharing nashi dake ba. Wai wacece matar nan ne ta tambayi kanta? Tana mika hannu zata karba Junaid ya doke hannun. Da bomb ne ma haka zaki karba ko ya fada yana zare mata idanu. Mota na tsayawa yaja hannunta ya tura ta ya kalli ummati kema shiga zan biyo abokina. Yana rufe musu motar kafin su fara tafiya Hafsi taji yace cikin daga murya what the hell do you want? Suna tafiya a zuciyarta Hafsi ta kara yarda akwai wata a kasa tsakanin Junaid da yarinyar nan. Ka zama uba ga abinda ke cikina. Ka rabani da rayuwar da nake ciki. Maana ka aureni. wadannan ne amsoshin da Tilly ta bawa Junaid. Imi dake ta yiwa Junaid horn ya shigo su tafi ya fito daga mota ganin yadda abokin nasa ya rude. Ya mutumina wannan ce akuyar dake neman daga maka hankali? Ai ka barni da ita na farfasa mata jiki kawai. Yana magana ne yana kokarin dauko wani katon dutse cikin wadanda akayiwa wurin ado dasu. Imi baya daukar raini shiyasa Junaid ya tabbatar yana daukan dutsen nan jikin Tilly zai dire shi. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐25 Rigar jikin Junaid ta gama jikewa da gumi saboda tashin hankali. Yana ganin iyayensa sun shige yayo kansu ita da Rosie sam ya manta da Hafsi a falon. Ke don ubanki me kike nema ne a tare dani? Idan ciki ne dake ki sa a ranki har abada Junaid bazai taba zama uba ga abinda ke cikinki ba. Hafsi tana jin furucinsa ta nemi hanyar barin falon rasa wurin shiga tayi don bazata bi su mommy ba a wannan yanayin da suka tashi. tana turo kofar dakin da take tsammani ma na masu aiki ne taji yo Tilly tana dariya...haba Juni boy ai kowa yaci tuwo dani miya ya sha. Ni ka zane a lagos daga na fadi abinda baiyi ma dadi ba. Rosie ta dan dake ta to banza rage muryarki. Ta maida kallonta ga Junaid ai kai karamin dan iska ne don giyar kudi ce ta kaika tashar iskanci mu kowa, ta nuna kanta da Tilly wahalar rayuwa ce ta kawo mu kaga dole mu fika rashin imani. Tsayawa yayi ya rasa yadda zaiyi dasu. Ya juya ya fita daga falon tare da buga kofa da karfi har sai da gaban Hafsi ya fadi. Masu aiki ya tarar a barin nashi ya ma manta wai shara akeyi da sauran gyare gyare. Get out ya fada cikin karaji har su Nafisa suka fito daga ciki ita da Hamida. Sauri tayi ta dafa masa kafada Junaid what is wrong? Ban sani ba wannan karon hawaye yake sosai. Ku fita wallahi ko wani yaji ciwo. Ba shiri duk suka yi waje shi kuma ya shiga sabon bed room dinsa. Bai taba tunanin first day dinshi da Hafsi zai zo masa a haka ba. Tsakani da Allah yake sonta don a yadda ya tsara ma kansa ma bashi da niyyar takura mata. A hankali zai bita ya koya mata sonshi don yasan yanzu baya gabanta. Gashi yar tsiwarta da fadan da suke suna burge shi. Drawers ya rinka budewa kamar mahaukaci yana neman kayan maye ko yaya ya gusar masa da hankali ya manta da bacin ransa. Wata taba dogowa ya dauko wacce Imran ya kawo masa tsaraba daga Italy. Kujera ya hau ya rufe idanunsa. Yana kunnawa yaji an fizge ta daga bakinsa yayi saurin bude ido. Hajiyan dangi ce tsaye kansa fuskarta jike da hawaye. Haba dan albarka. Yanzu ashe akwai wani maganin bakin cikin rayuwa bayan ambaton Allah da karatun Quran ko sallah? Ashe duk abinda ake fada maka bayan kunne yake bi. Bakin gado ta zauna dora kansa a kan cinyarta ya saki kukan da yake ta kokarin boyewa. Kyale shi tayi yayi mai isarsa har yayi shiru don kansa. Bai tashi daga kan cinyarsa ba yace Hajiya sai da nake son na canja halayyata kuma sai wannan masifar ta taso min? Kul ta ce masa tana girgiza masa kai. Allah sarki ne mai dinbin rahma da jinkai ga bayinSa. Shekararka nawa kana saba masa Yana hakuri da kai? Meye baka sha ba da aikin neman mata duk sai yanzu don Ya jarrabe ka kake neman kara fadawa ga halaka. Shin ka sani ma ko silar shiga aljanna ce wannan jarabawar? Dago kansa yayi yana kallonta. Hajiya wallahi yarinyar nan karuwa ce. Na rantse miki da Allah ita ta fara nema na a club. Abinda ta fada duk karya ne ya dan sunkuyar da kansa maganar cikin dai bazan karyata ba kila da gaske ne. Kayi hakuri ka daure kaci jarabawar nan. To Hajiya zancen Hafsa fa? Ya zanyi da ita idan taki ni. Murmushi Hajiya tayi ,kasa Allah a ranka yarona komai zaizo da sauki. Hafsa tayi min yanayi da mutanen kirki idan ka nuna mata kai mutumin kirki ne sai kaga Allah Yasa ta zauna da kai lafiya. Batul Mamman💖 TUN KAFIN AURE💐26 Neman Hafsi aka rinka yi a cikin gidan an rasa ina ta shiga. Mommy sai kuka take ko don taji zancen ciki ne ta gudu. Wata mai aiki mai suna Amaka ce ta tafi bakin gate ta tambayi securities din wurin ko sunga fitarta. Kusan awa biyu ana abu daya har Hajiyan dangi da Junaid suka shigo gidan don ta matsa masa akan yazo ya nemi gafarar iyayensa. Ganin gidan a hargitse Hajiya tace Salma me ya faru ne haka. Mommy cikin kuka tace bamu ga Hafsa ba Hajiya. Kinga har babansu ya fito nemanta. Tunda akace Hafsi ake nema Junaid ya dena gane me ake fada. Na shiga uku Mommy ta gudu. Tilly da Rosie dake zaune a gefe ko a jikinsu. Ya nufo su cikin tsananin fushi ku sa a ranku indai banga matata ba wallahi kun gama ganin farinciki a duniya. Banzaye Matsiyata, karuwai....kafin ya kara magana Amaka mai girki ta fito daga dakinta da gudu. Madam amariya dey for my room. Bangaje ta Junaid yayi ya shige dakin. A daidai lokacin Senator ya fito yana waya da IG na police kan a baza masu nemanta. Me zai fadawa Mal Aminu? Duk kudinsa mutumin kwarjini yake masa sosai. A kwance ya sameta kan gado tana ta rawar sanyi. Hafsi me ya faru ya fada yana shirin taba ta. Doke masa hannu tayi da kyar don wani zazzabi ne ya kamata sosai bayan tayi kuka mai isarta. Zuciyarta a cushe take da tsananin bakinciki. Badon abinda tayi ba tun kafin tayi aure tasan Allah bazai hadata aure da mazinaci ba.(don ma bata san yayi shaye shaye ba). Ganin yadda ta hade fuska ga wasu hawayen sun taro a jajayen idanunta. Kasa ya sunkuyar da kansa kiyi hakuri Hafsi ki bari na taimaka miki ki tashi naga kamar ba kya jindadi. Harararsa tayi tayi tsaki a hankali zata mike. Ke ba kya gajiya da harare harare ne , wata rana sai na tsire miki ido. Duk da suna tare da damuwa da bacin rai amma sai da duk sukayi murmushi. Nafisa ce ta fara shigowa sannan su Mommy suka

Chapter 5 of 10