Share this page
jiji da Kai amma Ni wallahi nace surutu gareka ga roko....... Ya Kara yin dariya.... Ke Kuma rowa gareki ko? Rowar me? Meye ka ce na baka na Hana? Abinci. Mtsew...tayi murmushi badai zance kazo kaci ba . Muma ga sadeeq na dafa Mana shinkafa Mai dadi Ni na kawo Miki?..... Na koshi aci lafiya. Allah kuwa..... Bana ci na gode malam . Kai lazy baka dahuwa sai an dafa an baka ko? Inji waye? Nafi sadeeq iya girki ko kina musu? Eh. In dafo in kawo Miki Zaki ci? Noooo, ta fada da sauri. Yayi murmushi yarinyar da kinji akul. Ta ce hmm. Zan zo anjima kinji ko? Okay. Ki gaishe mun da Aishar Bari na dauki wata waya...... Ya katse Kiran. Ta kalli Aisha Anwar case ne. ......... Gaskiya ai Yana bala'in yinki. Anwar Dan gadara Shi yake Kiran mace kinji yanda ake surutun miskilancin sa kuwa? Inaji amma nake ga kamar hada Sheri..... Wallahi da gaske ne. Yan matan ne basu da zuciya. Kinga wulakancin da ya ringa yi ma khausar har kuka take mishi.... Jakka kuwa ki Sami fareeda yarinyar nan Bata da zuciya wallahi..... Ke Aisha namiji munafuki ne kedai baki sani ba ko Yana gewaye wa. Last semester gab da za ayi hutu da yazo cewa yayi zance ya fito ya biyo wurina Kuma kema kinsan kilan bai wuce mufeeda ko wannan dayar banzar Yar aji hudu. Hmmm, kawai Aisha tace. Salim bai dawo ba Ina Zan Sami aron mashin? Sadeeq ya Fara maka mishi uwar harara ai taurin Kai da wulakanci ya Hana ka siya Mana sai kaje ka hau kabu kabu......... Wohohoho..... Wai nawa mashin din yake in siya a huta? 150-200k wannan range din. Mtsew...... Ka shirya gobe ka shiga katsina ka siyo Mana...... Ya buga ihu. Ya shako wuyansa..... Koda wasa ka nuna inada alaka da hakan ubanka zanci..... Bazan fada ba cika ni mugu...... Ya wuce har ya Kai bakin kofa ya waigo wane police station ne DPO ke Zama a garin Nan??....... Ya zaro ido DPO? Lafiya meye zakayo wurin DPO? Zan sa ya ma Dr Dan Musa warning da Suleiman akan Bilkisu.......... Wata muguwar dariya ya saki munafuki karshen tuka tika tik... Yanzu ka *FURTA* mun abinda nake son...... Dawowa yayi zai Kara shako Shi yayi bisa gado.... Allah ya baka hakuri. Amma Ina baka shawara zaka tona asirinka a banza saboda zasu so sanin wanene....inji waye? Ba zai fada ba. *This is legal warning* ...... Ya fice da sauri Yana duba agogo. Ya daga murya inzo in raka ka??....... Da ga can waje yajiyo Yana surfa mishi zagi. Yana sauka achaba Aisha na zuwa zata tsallaka titi..... Aisha. Ya Kira sunan ta. Laaa Anwar Barka da dare an dawo lafiya? Qalau, je Kira mun Bilkisu..... Tayi jimmm sannan ta ce toh ta juya Shi Kuma yayi tsaye maimakon yabi bayanta. Tana tafe tana masifa, je Kira mun Bilkisu kamar wata barar sa..mtsew. Haushi na da Shi Sam bai da manner of speaking Yana magana a gadarance da Isa na tsani wannan wulakancin wallahi. Tana wankin toilet ta shigo.... Kizo inji Anwar. Ta dafe kirji...kin ban tsoro wallahi. Ta harareta kawai zata juya..... Aisha Wai ya akayi? ....... Pad Zan jarbo Ina sauri ya ganni kawai ba wata magana Wai *je Kiran Bilkisu* irin yarinyar nan wacce ya ajiye.... Kiyi hakuri kin dai San Hali...... Eh amma ki ringa kwatanta mishi wata rana Zan yankwana Shi..... Kiyi hakuri dai, jira mu fita tare Dan Allah. Idan mun Gama Zan rakaki..... Wai injira ki wurin sa? Baki da hankali wallahi idan yamun wani dizgin inyi Yaya dashi?, Bazaiyi ba, idan ya ganmu tare bazai...... Wallahi bazan je ba. Kina tare da Anwar seems like you don't know him ko? Mtsew taja guntun tsoki ta fice abinta. Ikon Allah. Kai Anwar nikam tawa ta sameni........ A yanda yayi rantsuwa tabbas idan ban fita ba shigowa zaiyi. Ta dauraye hannun ta, Daman Riga da wando ne jikin ta, ta zumbula hijab har kasa ta Dan fesa turare kadan ta fito..... Bashi babu alamar sa, ta juya ta waiga ba kowa, tana niyyar komawa ciki har ta saka kafa daya ciki kiransa ya shigo...... Ta dauka hello....... Kin fito Kuma kin koma. Ni Banga kowa ba kana Ina? Bakin titi..... Bakin titi Kuma? Eh. Ki karaso.... Meye zanyi a bakin titi? Kina da gardama ne Wai? Just come here simple and short why are you arguing?? Ya kashe wayar. Wai ni zai mulka? Irin yanda yake juya Yan matansa Nima haka zai juyani? Ta doka tsoki ta wuce ciki..... Kofar taki buduwa daman tanayin haka some times, da kyar ta bude tana saka kafa Yana saka tashi...... Ta firgita, ta tsorata sannan ta razana ainun. Gabanta yayi mummunan faduwa ta zaro ido tare da bude baki zatayi magana .....ya riga ta, kina daukar maganata wasa ne? An fada Miki akwai Wanda nake tsoro ko shakka duk dutsinma?..... Babu, Dan girman Allah kayi hakuri muje tayo hanyar fita yasa hannu ya maidata... Ban gama ba....... Sai kawai tayi kneel down na tuba Dan girman Allah muje waje idanunta sun Fara kwal kwal alamar zata Fara kuka...... Ya buga tsoki ya juya. Ta Mike da sauri ta janyo dakin ta datse ta bishi da gudu. Tafiya yakeyi yaki tsayawa..... Ta Kara sauri ta tari gabansa Wai Ina zame je ne saboda Allah? Me yasa kika zabi bani wahala da bin yarda nake so?. Kayi hakuri wallahi daddy ya ce baya son fitar dare Anwar kada a sanar dashi zanji Babu dadi....... Da Yan iska yake nufi ni Kuma ba Dan iska bane...... Ikon Allah ba haka nake nufi ba. Okay to wuce muje..... Zan siya miki sweet ne da kudin aikina...... Wallahi da wasa nakeyi maka kawai na fada ne..... Ni Kuma da gaske na dauka saboda haka wallahi sai munje. Shikenan, suka jera. Tayi murmushi ko ke fa? Amma ke komai sai anyi tsiya tukun. Me kike so? Duk abinda ya maka....... Kinga agogon ya mun kyau? Ya nuna Mata . Um, kawai tace . Na gode fa, Allah ya Kara dalili. Amin. Zaki ci nama suya? A'a na gode. Kaza fa? Bana ci. Shawarma...... Nifa bana bukatar komai. Lallai yau zamu kwana a titi...... Ta kalleshi da sauri. Ya bita da ido Daman so kawai yakeyi su hada ido..... Allah matukar Baki ce ga abinda Zan siya Miki ba haka zamu kwana...... Biscuits. Tayi saurin cewa. Muje ka siya mun biscuits. Ya yi Yar dariya ko kefa?. Napep! Ya daga murya. Shi Kuma ya tsaya. Ta kalleshi da sauri...... *Abis supper market* zamu je Nan kadai Zaki Sami biscuits din da kike so..... Anwar, biscuits ko anan akwai Dan Allah...... Mtsew Allah ya raba ki da gardama. Muje ko in daukeki...... Kafin ya rufe Baki har ta tsallaka titi. Ya dunga mata dariya. Ta turbune fuska..... Gaskiya bana Jin dadin abubuwan nan Anwar bana son abinda kakeyi mun..... Kiyi hakuri. ....Ina zakuje ne? *Abis supper market* Anwar din ya fada Yana kallonta . Ta harareshi kallon Kuma na menene? Wallahi na tsani kallo rayuwata...... Na sani. Yace Yana dariya. Ka sani Kuma bazaka daina ba? Ya kyalkyace da dariya Nima na tsani kallo fa ta Yaya Kika San Ina kallon ki?. Yanzu Ina amfani wani ya ganmu a Sanya Ni a bakin fudma ace har mun Fara fitar dare sai ma a ba abun wata fassara wallahi. Mtsewww. Fassarar me? Ta mishi banza..... Kinji? Ta harareshi, ya kamata ka daina zuwa mun da dare gaskiya bana iya masifar Yan matanka kullum sai an mun zobe kamar za a dakeni...... Basu iyawa. An fada mun tsoronki sukeyi tun lokacin da Kika Mari kawar mufeeda...... Au ka sani ma ashe. Yap. Yace Yana murmushi. Dai dai sun kawo ya Mika mishi kudin suka shiga. Ranka ya dade..... Ma'aikatan suka taso . Ta kalleshi da alama regular costumer ne Kai. Murmushi kawai yayi. Kije ki zabo biscuits din da kike so. *Short bread* daya is okay..... Ke bana son gidadanji kije ki kwashi Kaya kinji ko idan kina Jin kunya Kuma muje na Taya ki ya zungureta da hannu.... Kamar ta bude kasa ta shiga don kunya yanda aka Mata ratai da ido. Sam ta kasa nuna ko daya...... Ya Kira yaron ya ce duk layin Nan sauko shi, tayi Yar dariya tunanin ta zolaya ce yakeyi. Da sun Kara gaba yaga wani kalar biscuits din sai yace wadannan ma duk safko dasu....... Wasa wasa ta ga abu da gasken gaske bata San lokacin data janyo Shi baya ba *Kana qalau* kuwa?. Ya Kai fuskarsa daidai saitin tata kamar zai yi kissing dinta...tayi baya da sauri yayi kasa kasa da murya *Yi kokari ki dizga ni*..... Kamar zatayi kuka ta kalleshi ka dubi girman Allah..... Me yasa kike son yi mun irin wannan magiyar Mai tsada? Ya katseta hannuwan sa duka a kirji. Ka ce su mayar da biscuits din can..... Wallahi duk wadanda suka sauko bazasu koma ba, idan Baki sa hannu kin dauki Kaya ba Zan siye duk biscuits din dake super market din Nan...... Ta zaro ido.... Kamar me Zan Dauka? Na bani ni Bilkisu kawai take nanatawa a zuciya...... Duk abinda kike so perfumes, cosmetics, drinks... everything. ...... Dabara ta fado Mata, okay na amince amma kaga Yanzu duk Ina dasu ka Bari semester tayi nisa Zan biyoka...... Yau fa sai kin dauka Kuma zamu Kara dawowa hakan ma ba laifi bane. Kamar ta daura hannu a ka ta yi ta ihu.... Ta kalli yaron kaga zo daukon *women million din can please*, Kuna da Apple juice? Eh hajia Mai sanyi ko marar sanyi..... Kamar ta zageshi don takaici, ta daure tace bani marar sanyi. Suka Kara zagayawa ta dauki robar chewing gum banana. Ta kalleshi wadannan sun isah na gode. Are you sure? Um. Tace da kyar. Biscuits din da yasa aka kwaso anata packaging a kwalaye manya...... Assorted biscuits ne na kwalaye da gwangwanaye... Tayi tsuru duk da diririce. Watau Anwar gidansu akwai kudi shine yake boyewa yace karkashin sadeeq yake komai sai ya nuna sadeeq ke dashi ko zaiyi. Hmmm, kawai take cewa. Yasa hannu ya fiddo ATM wasu dunkulallun dollars suka fado........ Ta bishi da ido jikinta sai karkarwa yakeyi ta Fara tsorata da al'amarain sa. Ya Dan kalleta Yana Yar dariya, ajiyar sadeeq ne.....mtsew taja guntun tsoki tayi gaba. Ya biyota da sauri ki jira zasu bayar da mota akai mu kayan sunyi yawa....... Ta rike kugu ta tsare Shi da ido sannan tace *WHO ARE YOU??gg?* **************** *KADUNA RIGASA* Ta fada bisa gado ta saki kuka..... Ya karaso Ummi tashi ya dagota.... Kiyi hakuri wallahi ba abinda kike tunani bane I just hugged her..... I don't want hear about it. Naji but kiyi hakuri ya rungume ta, I was confused these days. Tsakanin Miji da Mata sai Allah cikin second zancen ya sauya launi ya shawo kanta .... Kuka sosai Amira keyi tana cewa tabbas na ma kaina wauta me yasa na bayyana Mata abinda yake so da Wanda baya so? Me yasa na sakar Mata ragama... Tabbas ya shiga rudani ya kasa tantance daya cikin biyu... Ta Kara rushewa da kuka. Yayi lamooo bisa cikinta, ita Kuma tana shafa kansa.... A hankali take magana. Kafi son matarka Dani, har Yanzu ka kasa sabawa da ni matsayin matarka, a kullum... Ya rufe mata baki da hannu, I'm sorry baby, Ina sonki musamman Yanzu da Kika dawo normal wife kina biyayya ga sharudda na sannan kina kula dani.... Me yasa kake saurin kamuwa Koda kuwa wani abun munyi shine saboda makircin mu na Mata?.. Yayi shiruuuu..... Ya kasa magana hakika ya gano inda zancen ta ya nufa, ta yi murmushi hakika Yana da kyau ka Zama jarumi Mai iko da bukatar sa. Kiyi hakuri please I'll change..... Hmmm Allah yasa zaka iya. Kuma Ina rokon ka Dan Allah idan kasan har Yanzu kana kokwanto akan son da kakeyi mun.... Ba wannan maganar Ummi ya fada tare da janyo ta jikinsa..... Wallahi Ina sonki fiye da yanda kike tunani sometimes Ina rasa meke damuna amma na gano bakin zaren na Miki alkawarin zakiga canji. Please am sorry dear. Ya Kara rungume ta........✍🏼 *Zainab wowo ce*💖🤐 *WA ZAI FURTA?*🤐 1⃣6⃣ *Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.* ( Allah ya Kara tsareki daga sharrin munafukai Kuma azzalumai ). *KINA RAINA MAMAN WEEDAD* *Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray* ************ *Federal University dutsinma* ......Ta rike kugu ta tsare shi da ido sannan ta ce *Who are you?* Ya kyalkyace da dariya *Nine Anwar*..... Wallahi ka Fara bani tsoro ni ban yarda da Kai ba,kawai ta firgice mishi tana baya baya...... Tana neman Tara mishi jama'a ya Fara magana a hankali ```look calm down please I'll explain let's go```.......ba inda Zan bika sai kwallah sharrrr, duk jikinta ya tsinke da rawa. Ya zaro ido yace ```this is serious```....... Yallabai an saka a mota.... Please zanyi magana bani minti biyu just go away... Bilkisu please kizo muje Zan Miki bayani.... Wallahi bazan bika ba. Kai Bari na fada maka ni ban ma yarda da dakai ba......sai kuka. Ya runtse ido yace ohh my God this girl nawaoooo. Ya fiddo waya, ya Kira sadeeq.... Sadeeq please come to Abis super market now am there with Bilkisu... Ya latse wayar..... Kiyi shiru Dan Allah ke ba ki wuyar kuka what's wrong with you??? Ta mishi banza... Ya sa hannu zai kamota tayi baya saura kadan ta fada cikin kwalayen lemuka.... Zaki Fadi fa ya daka Mata tsawa. Ta makure wallahi kana tabani Zan maka ihu. Ya kura mata ido kawai ya maida hannuwa ya rungume. Yana hango sadeeq mashin ya ajiyeshi ya fita da sauri..... Please save me she's suspecting me...mtsew ya doka tsoki ya wuce Shi. Tana tsaye ko motsi ta kasayi, sadeeq ya kalleta zo muje Bilkisu kinji. Duk jikinta ya mutu ta biyo shi, ya bude Mata mota tana Zama shima ya shigo ya rufe kofa, Sadeeq ya shiga gaba suka tafi. Bayan an sauke kayan kaf, sadeeq ya kalleta ya akayi ne Bilkisu me ya faru? Kwallah suka zubo mata, Dan Allah kiyi hakuri kiyi shiru menene ya faru? Idan Kuma kina da tamabaya akan Anwar kiyi mun Zan baki amsa wallahi...... Wanene Anwar?, Wallahi ni ban yarda dashi ba, duba ka gani ta nuna mishi tulin kayan da hannu wannan siyayyar hankali ce? Kuma naga dollars sun fado aljihun sa yace ajiyar ka ce he's always hiding something from me why?.….. Kiyi hakuri...... Wallahi bazanyi hakuri ba yace mun Shi a kauyen Kano yake Yana business da wani ubangidan sa Kuma...... Karya yakeyi. Sadeeq ya katseta. Ya kalleshi da sauri, me kake nufi? Ina nufin gidan ku akwai kudi Kuma cikin garin Kano kake ba kauye ba. Ya kalleta what else do you want to know?........ Ya ingijeshi shikenan ka tafi tunda taji daga bakin ka Zan Mata bayanin saura. Ya yi dariya, wannan rawar kafar da kakeyi Shi ke tona maka ASIRI..... I said go ya Kara tura shi. Allah ba inda zanje. Bilkisu karya yakeyi babba gida ya fito. Ni meye nawa a ciki da yake boye mun? Ta fada tana hararar sa, ya yi murmushi hankalin ki ya kwanta Yanzu? Ban sani ba ta juya...... Ya kamota, me yasa baki ganewa ne ke? Nace idan Ina Miki magana ki daina tafiya bazaki daina ba ko? Sai ranar dana kamaki gaban wadanda kike ji ma kunya Zaki.....Amma Kai iyakar Dan iska ka Kai. Saketa wallahi. Ya saketa Yana Yar dariya. Kinga Bilkisu je kirawo kawayenki su shigar Miki da kayan Nan.....bazata dawo ba Kuma wallahi binta zanyi ciki Kama fada Mata. Don't mind him jeki abinki. Ya bita da ido....... Zaka rikita Yar mutane Anwar wallahi ta tsora fa da gaske...... Ya kwashe da dariya kawai. Asirin ka ya Fara tonuwa sai ka yi kokari Kuma Yanzu ka *FURTA* Mata.... Uwarka.... Yakai mishi duka. Yarinyar can sadeeq rigimammiya ce Kuma shagwababbiya...... Komai sai ta bude Baki tana kuka. A gaskiya ka takura mata..... Fitowar su yasa ya tsayar da maganar. Ko kallonsu baiyi ba ya ce Bilkisu minti biyu..... Ya danyi gefe can nesa. Tayi tsaye, sadeeq ya kalleta kije kada ya Kara Mata Mana lokaci I'll talk to him please. Ta wuce kanta kasa, ta rasa inda zata sa ranta. Ta tsaya nesa dashi, Ya kalleta ki matso koni nazo Nan.... Ina jinka daga na...... Taku daya ta ganshi gabanta wallahi kina motsawa Ina kamaki, ya fada. Tayi kasa da Kai.... *tawa ta sameni ni Bilkisu* tace a zuciya. Ya kamata kiyi mun godiya ko? Ko nayi laifi ne? Hmmm, na gode Allah ya biya. Good, yace Yana murmushi. Ya kalli hannun sa *I really like this watch honestly* Ta ce hmm, kawai. Yanzu hankalin ki ya kwanta kin Kuma yarda dani tunda kinji na fito daga babban gida? Um, ta ce a takaice. Gobe ba lecture ko? Ta ce um. Sai dare kenan zamu hadu?..... Anwar Dan Allah ka rage zuwa wurina bana son abinda zaiyi affecting karatu na gaskiya. Ya kura Mata ido yayi shiru.....har sai da ta dago ido ta kalleshi. Ta mayar da Kai kasa. Kamar zaice wani Abu sai Kuma ya fasa yace okay I'll try. Ta ce na gode, sai da safe..... Ya matsa baya kawai ya bata wuri ta wuce. Ta Dan kalleshi kadan fuskar sa ta canza alamar damuwa.... Kirjinta ya buga da karfi. Kamar tayi magana Kuma ta fasa ta wuce. Sadeeq na tsaye su Aisha Kuma sun shiga da kayan, ta mishi sai da safe ta wuce.... Har ta shige idon sa na kanta ya kalli sadeeq shi Kuma ya banka mishi harara, wannan rawar kafar ita zata......I don't know how to control my self. Abun ya Fara damuna. Wata muguwar dariya sadeeq ya saki tare da fadin *Anzo wurin.* Murmushi kawai yayi. Kana hauka ne kayi Mata irin wannan shopping din? Mtsew wallahi Bilkisu da kake gani ta banbanta da ko wace irin mace class din yarinyar yayi yawa could you imagine she refused to take abinda takeso sai da taga da gaske Zan kwashe kayan shagon?. Da sai ka bita a haka for once gaba gaba idan kun Kara sabawa sai ta dauka...... I don't think so. Kuma wadannan banzayen dollars din ne suka rikitata cos har muka Kare she was shocked but couldn't..... Gaskiya ta firgita. Ya kamata fa ka Kama kanka gaskiya wallahi kada ta birkice maka kuma ko ta tsorata tsoron yasa ta gujeka. Mtseew.... I said I'll try. Ya fada Yana yarfa hannu. And ka rage kakkamata fa..... Ba laifina bane wannan fa, sadeeq yarinyar nan fa baza ka gane ba. Wallahi sai muna tsaka da magana sai ta nemi guduwa I told her this is what will happen idan tayi she refused to listen....and I have no choice than.... This is not an excuse idiot. Ya katse Shi. Ya kamata fa ka duba kada kazo ka kasa shawo kanta bayan ta rikice maka..... Mtsew naji Zan jaraba. Yanzu ai hankalin ka ya kwanta ka fada Mata Ina da kudi..... Kuna da kudi dai ba kana dashi ba. Bari kaji na fada maka a yanda kayi Mata Yanzu wannan kadai ce hanya da zata fisshe ka. Kana tunanin Koda kudi nane da gaske kana iya wannan gabatar? Kayi abinda hankali zai dauka Mana. Amma Yanzu na fada maka Kuna da kudi komeye ta dauka zata ajiye. A yanda ta firgita some muka fada Mata bayan wannan wallahi Koda ta yarda a fili a zuciyarta zata ci gaba da wasi wasi Kuma hakan zai haifar Mata da bincike akanka... Kayi tunani Mana. Kuma fa hakane. Yawwa. Amma Yanzu kaga tasan Kai Dan masu kudi ne zaka iya komai shikenan. Yayi ajiyar zuciya *I too much like you sadeeq* Suka kyalkyace da dariya tare da tafawa...... Aisha kadai ta tarar dakin a zaune ta tasa Kaya gaba tana kallo. Ko takalmi bata cire ba ta fada bisa katifa....... Aisha na shiga uku. Wai ya akayi ne? Fada kukayi da Anwar din bayan fitar ku? Naga alamun kinyi kuka Shi Kuma sai babbata Rai yakeyi...... Aisha Anwar yafi ciwon ciki.... Ta kwance Mata zance kaf! Ko kadan Aisha bata razana ba. Sai tayi murmushi tace, ni wallahi nasan Anwar Dan manyan mutane ne. Haba kiyi tsam da Rai ki kalleshi da kyau ya Miki kama da mazauni kauye? Ko fatar jikin Anwar Kika kalla kinsan ana rayuwa cikin A/C da Jin dadi. Bari in Baki karamin takadiri ki kalli yanayin shigar da yakeyi duk kayan Anwar tsadaddu ne daga manyan kamfuna manya manya irin su *Gucci, M&S, C&K* ke gasu nan. Ji takalmomin da yake sawa..... Haba mutane, Ni wallahi nasan karya ne ace duk sadeeq ke musu sai dai na yarda shikeyi ma sadeeq saboda ko dressing yanayin dauka a jiki ma ba daya ba Koda kuwa iri daya suka saka . Ji lokacin zuwan su daddy ke baki lura bane Amma wallahi wani taku da Anwar keyi nasan yaron yaji bariki wallahi..... Ke ni al'amarin sa ya Fara bani tsoro Aisha...... Hakuri zakiyi sonki yakeyi Kuma ya kasa *FURTAWA* kawai idan ya Miki kina sonsa Ina Baki shawarar kada ki Bari wata tayi Miki shigar kutse sannan kada ki yarda ki nuna kin San inda ya dosa ki barshi har ya gaji ya *FURTA* idan da gaske yakeyi. Koda yake wannan hauka haukan da ya Fara tabbas saura kiris ya *FURTA*....... Aisha bana iya wa Anwar har ga Allah..... Ba Kya son sa? Ta tsare ta da ido...... Tayi shiru ta kasa magana. Kinji? Idan bai Miki ba ki fada mishi ya rabu da ke, naga dai yanda Yan Mata ke neman kashe kansu saboda Shi Amma ke ya zabe ki kamar tumun dare Zaki..... Understand me please. I'll never understand you. Namiji kowa da kalar soyayyar sa, Anwar miskili, gadararre, Wanda ya Raina kowa kije kina bada labarin da kike bani Yanzu wani sai ya mare ki saboda cewa zasuyi karya kike yi amma Ni ganau ce ba jiyau ba. Amma ji yanda yake Miki rawar kafa. Wallahi Yanzu dan ana farkon dawowa ba mutane Amma tabbas ni nasan wannan semester din akwai daru za 'ayi kallo. Sai ki dage..... Abinda ke tayar mun da hankali kenan wallahi. Tayi dariya zai tare Miki nasan dole ya..... Wani abun ba agaban sa zai faru ba Aisha.... Yanzu ni ya zanyi da wadannan Kaya ni Bilkisu.... Ci zamuyi. Yanzu fa aka dawo. Ai wallahi mun gode......... Wayarta ta Fara Kara. Ta kalli Aisha Anya Anwar zai barni nayi abin kirki wannan semester din?.. Tayi dariya ta kwashi biscuits da wasu tarkace tace keni sai da safe...... Taja Mata kofa. Ta kanga wayar a kunne ba tare da tace komai ba... Ko har wayar ma an Sanya Mata doka?. Ya fada Yana Yar dariya. Hmmm, kawai tace. Ke na gaji da hmm, dinnan da kike neman ki ringa kawoshi bana son sa ki bude Baki kiyi mun magana kinji ko?. Toh, tace a hankali tana murmushi. Da gaske ba Kya so Ina zuwa wurinki? Eh, tace da sauri. Saboda me? Ta runtse ido anya mutane sun San Anwar kuwa da ake mishi shaidar baya magana?... Kinyi shiru. Ya katseta. Haka Nan, Baiyiwuwa ki fada mun dalili ko Kuma gobe ki ganni...... Dokar daddy ce, sannan zuwan naka zai rinka haddasa mun fitina tsakanina da Yan matanka, idan Kuma aiki yayi nisa Zan Sami raunin karatu...... Zuwa gidan naku? Eh, Fine. Zan daina zuwa shikenan ko? Eh, ta ce tana murmushi. Idan Zan ganki muyi magana Kuma fa? Sai na sameka class....fine, gobe mu hadu new lecture rooms by four. Yana fadin haka ya kashe wayar. Ta bi wayar da kallo tace ikon Allah..... Allah ya kawoni ni Bilkisu..... Tayi shiri daga sallar la'sar, a hankali take tafiya ga nisa daga masallaci zuwa classes din, kanta a kasa kadan kadan take gaisawa da mutane. Kugin mashin taji a bayanta tayi saurin Kara matsawa gefen titi, gabanta suka tsaya, ya sauko sanye da kananan Kaya kamar kullum ya rufe ido da facing cap... Ajiye ni a nan. Ta dago ido da saurin Jin maganar sa. Shida sadeeq ne bisa sabon mashin fari duk leda jikinsa. Sadeeq Ina wuni ta fada tana murmushi. Lafiya Lau Bilkisu. Ta Dan kalli gefen sa Ina wuni. Yayi kamar baiji ba, ta ce ai kaji tsiyar Shi dizgi wurinsa bai daukeshi bakin komai ba. Ka kawo man upstairs Yanzu please ya

Chapter 12 of 22