Share this page
gate sauri sauri.....tana tunanin watakila Yana can Yana faman koyo don yazo ya birgeta..tayi tsoki to karya tame ne? A hargitse ya shiga ajin sai wurge wurgen ido yakeyi girman Kai da nuna Isa sun Hana ya tambayi su chinyere ko sun ganta. Rai bace ya fita Nan ya Fara bin azuzuwa neman ta. Helen ta tabe baki I don't like this Anwar honestly.... Mtsew don't mind idiot abeg inji chinyere Nan gulma ta tashi. Ya cika girman Kai da nuna Shi wani ne, baya yi ma kowa magana sai abokansa uku. Surutai kala kala saboda Shi din Daman baida farin jini a class din tun zuwansu Wai ya cika fadin Rai da gadara. Tunda ga ranar bai Kara Sanya Bilkisu a ido ba yayi neman har ya gaji gashi baida no. Ta bai Kuma San Wanda zai tambaya ya bashi ba haka Kuma baisan accommodation dinta ba hostel take ko off campus. Wasa wasa abun ya Dan dameshi. Ranar da zasu Fara jarabawa da yake ta karfe uku ce tun biyu saura yake hall din Yana so ya ganta, ita kuwa tun 8 tana library sai biyu da Rabi ta fito bayan tayo sallah. Kansa sunkuye baiga shigowar taba har ta zauna bayansa. Lallai Anwar ka kyauta shine ka shanya ni rannan ko? To kayi dai dai ta fada tana faman hararar sa . Da sauri ya dago Kai zaiyi magana kenan invigilators suka shigo tare da fadin everybody out..ta rigashi fita, ko da aka Fara shiga ma tayi saurin fadawa don Zama gaba gaba. Alhamdulillah jarabawar ta mata dadi ainun domin duk abinda ta karanta suka fito. Ita ce ta biyar din bayarwa ( submitting ) bata jira kowa ba tayi masallaci don gabatar da la'asar saboda lokacin biyar da kusan ashirin. G Haka semester din ta kare ba tare da sun Kara haduwa da Anwar ba, ko kadan Bata yarda su hadu tasan karya zai shirga mata don kare kansa. Shi Dan garin Kano ne ita Kuma Abuja mahaifinta ke aiki Amma asalin su Yan katsina ne. Washegarin da suka Gama jarabawa tabar garin Anwar kuwa karfe biyar na ranar yabar dutsinma. Hutun baida tsawo sati biyu akayi aka dawo. Sun dawo da sati daya aka saki result a *portal* Murna tsalle ga Bilkisu saboda ta cinye ko wane Bata da carry over ko daya ga point dinta 4.33 Hakan ba karamin dadi yayiwa Yan gidan su da iyayenta ba. Anwar kuwa 5:00 dai dai ya samu saboda duka courses din da sukayi goma Sha daya ko wane *A* yaci. Yaja bakin sa ya tsuke. A cikin ajin kowa nata fadin result din sa daga Mai 4 point sai masu 3 point da abubuwa. Duk Wanda ya tambayi Bilkisu sai ta ce lafiya Lau ne ni Daman carry over ke bani so to ban samu ba. Bata yarda ta fada ma kowa result dinta ba. Tana zaune an gama lecture din wani mugun malami ta kura ma dan rubutun da tayi ido tana nazarin ya zata ci jarabawa da Dan wannan rubutun? Suleiman ya mata sallama. Suleiman matashi ne Shima a cikin ajin Mai natsuwa da son addini babancin say da Anwar yafi Anwar saukin Kai da yarinta. Ya zauna kusa da ita bayan ta amsa sallamar Dan Allah Hajiya Bilkisu na kasa bude portal dina ya akeyi ne? Tayi murmushi Ina wayar taka in nuna maka? Wallahi daki na barta ki nuna mun da taki.......hankalin Anwar na kansu haka kawai sai yaji ya tsani Suleiman karon farko a rayuwar sa. Ta fiddo wayar tare da tambayar sa password da matric number. Portal din na budewa ta Mika mishi wayar kaga inda zaka Danna..... Ya danyi dariya to bude Mana ai ba komai don kin gani. Ta kalleshi tana mamaki saboda tasan Portal sirrin dalibi ne ba kowa kake yarda ka nuna mawa ba. Ya Kara Yar dariya ki bude ba komi. Ki gane mun Ina da carry over? Ta ce to a sanyaye tana mamakin irin warda da yayi mata farat daya zuciyar ta cike da Jin dadi tare da ganin kimar say da mutunci. Kaiiii....ta fada tare da zaro ido ka Fadi accounting. Sai kawai yayi murmushi nasan za'a rina sai wane? Ka Fadi GST English Shikenan. Nawa ne point dina? Ta duba can kasa tana warware ido..... Okay gashi Nan 2.65. Ta kalleshi, amma Suleiman me yasa ka yarda dani haka?......Au kin San sunana kenan? Ya fada Yana kallonta cike da mamaki, tayi murmushi eh Mana nasan sunan ka Suleiman. Ina fatan ke dai lafiya lau ko? Sai kawai ta budo mishi portal din ta tace kaga nawa. Ya zaro ido kaiiiiiii...... Ta danyi murmushi Amma bana son Dan Allah ka fadawa kowa result dina. Ya Jin jina Kai in shaa Allah Zaki sameni Mai rike sirrin ki, amma Bilkisu kinyi wuta da yawa fa! Ta yi Yar dariya kawai. Allah yasa albarka. Kiban no. Ki dan Allah ko da wani Abu Yana tasowa Kuma idan bazaki damu ba Zan ringa matsowa kina tasar Dani inda ban ganewa. Ba matsala ga number rubuta........ A harzuke Anwar yabar class din tunda ga ranar sai kawai yayi baya da ita ko gaisuwa baya son suyi cikin kankanin lokaci ta Saba da Suleiman ta fahimci Yana da saukin Kai bashi da girman Kai sannan Yana da addini tare da daratta mutane. Ko da ya gane Bilkisu nada kokari sai ya like mata ko C.A zasuyi Yana manne kusa da ita baya yarda tayi mishi nisa. Ko kadan Bata da mugunta duk amsar da ta kakare mishi zata bashi ya kwashe tsaf!. Akwai wani course Mai matukar wahala gashi three credit unit ne Kuma calculation Mai rikitarwa kowa Yana Jin course din. Anwar yayi burus da ita Yana Jin kowa na kokawa Amma ya ki nuna ya iya. Kwana takeyi karatu da salloli, Ranar jarabawar course din ana ta jera layi kawai malamin yace ta zauna can, hankalin ta ya tashi ganin ya cillata gaba don yau baya take son Zama saboda ta Sami taimakon wani. Tana Zama sai taga Anwar ne a gaban ta, ita dai kawai sai addu'a takeyi tasan yau sai Allah da malaman gari. Tambayoyi bakwai be a amsa biyar tambaya ta farko dole ce gata da 'ya'ya har goma. Saura kadan ta kurma ihu saboda duka tambayoyin guda daya ne kawai ta sani itama theory ne ba calculation ba. Idanun ta suka kawo ruwa, taga tunda Anwar ya duke bai dago ba, hall din yayi tsit! Ta yi zugummm, zuwa can kawai ta Fara amsa wacce ta sani. Mafi yawancin malaman dake tsaron nasu duk sun maida hankali wurin Yan baya. Haka ta dunga rubutu Dan Allah yasa ta Sami Koda *E* ne a course din ta wuce wurin. Tana gamawa tayi zugummm kawai tana fargaba. Yadan waigo kadan ganin malaman basa kusa yace kin iya question one naga tana da wahala fa. Tayi kasa da murya wallahi question 4 kadai na iya cikin bakwai din nan ga Shi ta farkon naga 30marks ne. Ya dan gyara zaman sa kadan tare da kango mata booklet din sa yace kiyi sauri ki kwasa. Habaaaaa.....ga bilkiyda saurin rubutu gata very smart. Duba daya sai ta kwaso layi biyu. Cikin sauri ta gama shafin tace juya....Shi kansa yayi mamaki yace ke duba da kyaufa kada kiyi shirme. Wallahi na gama ka juya kawai. Haka ya bata dukan sauran question hudun da bata iya ba. Sai da ya tabbatar ta Gama tsaf sannan yaci gaba da amsa Shima question 4 din da tace tayi. Ta Dan waiga ta hango Suleiman can baya an cillashi sai zare ido yakeyi. Duk Wanda ka kallo zakaga ko Yana zufa ko Yana ta raba ido. Kije kiyi submitting...ya fada kasa kasa ta ce toh. Kowa sai kallonta yakeyi Yana mamakin yanda zata bayar da wuri haka, Wasu na tunanin kawai ta gaji ne da zama kamar yanda Suma suke zaune, tafi mintuna talatin kafin wasu tsirara suka Fara fitowa duk Wanda ya fito idanu jawur ana tsinar malamin kusan kowa ya sadakas da kawai faduwa zaiyi course din saboda rashin iya amsawa. Suleiman kawai take jira ya fito sai kuwa gashi Yana ganinta yace, Bilkisuuu..... Yau naji wuta wallahi Allah dai ya kyauta Amma question biyu kawai nake da tabbaci cikin sauran. Tabbb....wallahi ni Allah ya taimakeni Anwar ya bani duka Wanda ban sani ba....hada question one? Eh Mana. Wai da gaske kike? Wallahi kuwa. To Ina Jin keda shine kawai kuka amsa ta don ko su chinyere gasu can suna cewa Basu gane ba.......Allah dai ya kyauta ta fada tare da cewa sai gobe ta ruga hango Anwar yayi hanyar *Gate* Yana ta faman sauri. Anwar.. ta kwada mishi Kira, yasan za a rina Shi yasa yaso ma kada su hadu. Ya Dan tsaya Yana murmushi , ya jarabawar Bilkisu ya fada Yana latsa waya. Hmmm jarabawa yau Allah ya rufa man asiri bacin Kai ai Dana shiga uku. Na gode na gode Allah ya Kara ilimi......Daman ka iya course din sosai haka? Naga yanda ake ta kuka dashi Kai komai ka amsa.....hatta jamilu ma naga naka yake kwafa ( copying ). Murmushi kawai yayi yace ba damuwa. Ya wuce kawai. Ta bishi da ido. Anwar...ta Kara kwada mishi Kira.....ya juyo wallahi na gode kaji? Sai kawai ya kyalkyace da dariya ya juya abinsa. Taji dadi sosai da sosai a Ranar domin course din kadai kowa ke kuka dashi wannan semester din. Hutun ya kasance dogo akalle ankwashe watanni biyu a gida kafin a dawo aji biyu.( Su Bilkisu an Fara manyanta ) wannan karon suna gida result ya fita inda take da 4.22 ta Dan sauko kadan saboda ansha wahala matuka Shi Kuma Suleiman Yana da 2.72 Amma ya Sami carry over daya. Sun koma da makaranta da sati biyu akayi *convocation* tare da bayar da kyaututta ga first class da over all. Bata halarci wurin ba. Saboda ba kowa ya maida hankali ga taron ba. Hakan yasa Anwar zuwa tare da karbar five pointer award da Kuma overall student na aji daya da suka gama. Kamar munafuki ya karba sim sim sim yayi saurin barin hall din ganin babu alamun Yan ajin su ko wani Wanda ya sanshi. Ashe Suleiman yana wurin. Ba karamin mamaki yayi ba watan Anwar shine *Hamza Yusuf* din da ake nema cikin class Amma wallahi sai ya fadawa Bilkisu................. ************* *KADUNA RIGASA* Yana ta mamakin yanda ummi ta mishi text tana son ganin sa alhalin bata taba hakan ba. Yana zaune babban falon gidan nasu an cika gaban sa da kayan ciye ciye da lemuka kamar kullum ta shigo tana ta faman Bata rai . Ya kalleta tana ta faman karairaye karairaye......Amarya bakya laifi ko kin kashe Ahmad ( Babban yaron sa ) ya fada cikin zolaya Yana Yar dariya hannun sa rike da samosa mutumen shi Yana ci. Banga alama ba, ta fada tana taunar cingam. Ya kalleta jin maganar ta fito gatsal.... Kamar Yaya?, Ya bukata. Kamar yanda kaji. Kamar yanda naji? Ya maimaita cike da mamaki kafin ya ajiye guntun samosan bisa plate ya tattara hankalin sa duka wurin ta.....me ke faruwa ne ummi? Tayi shiru! Dake nake magana...me ya faru? Ta gyara Zama, Ina ce apartment din da kayi sabo Ni ka gina mawa Amma labari yazo cewa Aunty Amira ta koma....... Ke ya daka mata tsawa. Nan da nan ya harzuka, Ni na fada Miki Ina Miki gini? Gabanta ya fadi tayi tsuru tsuru, kinji? Munyi dake Ina Miki gini? Okay ita da Zaki aure Mata miji Bata kawo mun matsala ba sai kece Zaki fara kawo mun tsirfa? Saurara da kyau ya Mike tsaye Yana nuna ta yatsa wallahi matukar kina son Zama dani tare da Jin dadi sai kin daratta Amira kin mun biyayya kin Mata bazan dauki sakarci ko kadan ba. Dukkan ku Ina sonku to dole kowace tabi ra'ayi na, idan Kika saki na gane kina da matsala to wallahi zakiji ba dadi. Mtsew ya buga tsaki ya wuce.......ta yi zuruuuuu tana zare ido lallai ta gwada Bata ji dadi ba. Kwallah suka zubo Mata. Ta buga ma babbar yayar su waya domin ita ce abokiyar shawarar ta .....salati ta kamayi ubanwa ya aike ki? Ai kinyi sauri bari zakiyi sai kinje gidan yasan dadin ki lokacin yazo hannu tukun Amma Yanzu ai lallaba matar sa yakeyi tunda ya Mata laifi. Ki bari Zan baki ahawarwari idan na shigo gobe. Tun daga ranar Bata Kara Sanya Shi a ido ba. Tuni a Mata hudubar kada ta saki ta dauki raini ga matar sa Kuma idan ta a gidan ta Sami damar juya Shi yanda zata amshe ragamar komai. Babu yanda ba a yi dashi ba ko kamu ayi yace bai son bidi'a ba Dan komai ba kada ma akirkiri partyn Amira taji ba dadi. Ranar walima akayi mashi Sha Tara ta arziki hada mota. Yana falon sa zaune yaji marokiya na sanarwa. Shima ya Mike ya kirawo marokiyar ya bada makullin mota kirar *GLK* baka 2019 model ta kusan miliyan Tara yace yaba Amira ayi sanarwa. Nan dangin Amarya kuwa suka Fara surutai............ Ko ajikin sa. Dangin ango dana Amirai kuwa suka Fara rangada guda suna tayata Murna. Hakan ba karamin harzuka Amarya da danginta yayi ba. Nan suka Kara hure Mata kunnen wallahi sai ta tashi tsaye Dan kwato ma kanta yanci. Kuka takeyi wuiwui. Kafin karfe shida gida ba kowa duk an tafi. Ana gama sallar isha'i ya ja Amarya zuwa sashen Amira don yi masu huduba....... *Ayi hakuri da typing error please yanayin typing din ne saboda kawai ta WhatsApp nake yi Kuma gaskiya bana bi idan na Gama kawai nake turawa. *Daga zainab wowo*πŸ’žπŸ’•πŸ’—πŸ˜„βœπŸΌ 🀐 *WA ZAI FURTA?* 🀐 0⃣3⃣ *TUKUICI NE GA AUNTY RABI ALLAH YA KARA ARZIKI DA RUFIN ASIRI* *KINA RAINA MAMAN WEEDAD* *Domin ki.... blood sister khadija Dahiru wowo miji na gari I pray my besty* *DAYA TAMKAR DUBU AL'AMEEN ZUBAIRU* TANNY ALLAH YA RAYA MIKI YARON NAN YA KARA MISHI KYAU DA KWARJINIπŸ’– *Federal University dutsinma* Tunda aka dawo bai yarda sun hadu da Bilkisu ba har suyi wata magana. Tana ta kokarin su hadu Amma yaki yarda. Suna tsaye ita da su favour bakin ajin da zasuyi darasi ta hango Suleiman na taho wa, tun daga nesa suke ma juna dariya saboda Yanzu sun Zama tamkar *Wa da kanwa*, Anwar har yazo ya wuce ta gaban ta bata ganshi ba amma Shi Suleiman man din ya hango shi. Yana karasowa malamin Shima ya iso haka suka rankaya zuwa aji. Ko Zama Yanzu kusan tare sukeyi. Har Yan class din sun Fara lura da shakuwar su. Ya fakaici idon malamin ya Fara mata magana kasa kasa. Wai Bilkisu kinsan Hamza Yusuf din say ake nema ajin nan Anwar ne? Ta zaro ido *Anwar*? Eh wallahi. Jiya gaba na ya amshi award din first class da Kuma overall award ina kallon sa yayi saurin boyewa ya bar hall din da sauri. Ta rike baki. Innalillahi, wallahi sai na mishi magana naga wannan semester din ma tunda muka dawo sai wani shareni yakeyi. Hmmm, ai da yake kece, Amma Anwar inba ke ba waye ke mishi shigar kawara duk makarantar Nan. Kinsan girman kansa, jiji da Kai da kuwa maida kowa banza yasa aka tsane Shi wallahi ya cika gadara....... Duk yaji dashi nikam daga yau wallahi ya shiga uku dani. Ba abinda nake nema wurin sa inba karatun ba.....ta katse shi. Hmmm Hana wallahi nayi mamakin *Business finance* din last semester, bana fada maka cikin mintuna da Basu wuce talatin ba ya gama kusan questions 4 kowa na kuka da question one amma Shi duka yayi. *B* fa gareni course din Kuma wallahi C A da 22 na shiga......ohh ni *Balky* ai wallahi ya shiga uku dani. Suleiman man dai sai dariya yakeyi yace idan kin kwaso wurin sa Kya ringa koya mun....tabbbb tare zamu je kyaleshi ai wallahi sai na fitine Shi ga wannan semester din kurar ta tafi ta aji daya. Daya ke Anwar din Yana ta gefenta sai kawai ta yi ta kallon sa. Tun bai lura har ya fahimci tana kallon sa. Ya Dan juyo suka hada ido ta balla mishi harara Shi Kuma sai ya kawar da Kai Yana murmushi kawai. Haka sukayi tayi da sun hada ido sai yayi murmushi ita Kuma ta harareshi. Yana ta sake sake cikin Rai *Kuma yau me nayi Ni Hamza* bana iyawa rigima da fitinar Yarinyar can. Ya kawar da Kai bai yarda sun Kara hada ido ba har aka gama. Hankalin ta na kansa yana mikewa itama ta Mike. Abinka ga namiji kafin ta sunkuya ta dauki jaka har yabar ajin. Da gudu tabi ta kofar baya kawai sai dai ya ganta gaban sa. Gaban sa yayi mummunan faduwa Amma miskilancin Anwar bai yarda ta gane hakan ko a fuska ba hasali ma sai yayi Yar dariya *Hajia Bilkisu an tashi lafiy?* Ta rike kugu To yau Allah ya Kama ka, Ashe Kai ne *Hamza Yusuf*........ Har ga Allah ya Dan razana. Amma a zahiri sai kawai yayi dariya duka kumatunsa suka lo6a ....inji wane makaryacin? Ya fada Yana dan waige waige kada sauran Yan aji masu fitowa suji, Wallahi Kaine *Hamza Yusuf*.... Ta fada tana hararar sa. Tana matukar bashi dariya saboda ko gida bai taba samun Wanda ke mishi magana Kai tsaye Babu shakka ba irin Bilkisu. Yadan Sha mur Yana Dan zare mata ido ke ni bani bane ya gitta zai wuce .....Tasha gaban sa da sauri tare da ware hannuwa ba inda zakaje sai ka fada mun wanene jiya aka bashi kyauta ya boye ya gudu?......tuni hankalin mutane ya dawo kansu an Fara fahimtar meke faruwa. Ya zaro ido..... Ke ni bani bane..... Wallahi Kaine. Naji nine yanzu meye kike so? Ya fada Yana Yan waige waige kamar marar gaskiya. Zaka ringa koya mun karatu wallahi don bazan kyaleka ba....shine damuwar? Ya fada cikin kosawa, shikenan duk lokacin da kika shirya Zan nuna Miki. Ya wuce da sauri ya barta tsaye. Suleiman ya karaso kin dai gani ko? Kyaleshi ai wallahi na daina wahala daga yau addabar sa zanyi. Nan wuri ya rikice da surutai kowa na mamaki. Tun daga lokacin kimar Anwar ta Kara karuwa duk masu Jin haushin sa suka daina. Matsala daya ce Babu Mai iya tunkarar sa da maganar koyo duk ana Jin tsoro da shakkar sa. Tun daga lokacin Bilkisu ta dami Anwar ya rasa yanda zaiyi da ita ba abinda takeyi mishi sai terere kowa Yanzu yasan wanene Shi , ya rasa dalilin da baya son mata wulakanci kamar yanda yake ma kowa. Ko lecture za ayi Mafi yawan lokuta sai ta zauna kusa da Shi sai dai yayi ta dariya. Na kusa dashi mamaki kawai sukeyi yanda baya hantarar Bilkisu ko kadan don ko su din lallabashi sukeyi. Satin da ya kasance daga Shi sai na yin first C.A sun fito lecture seven to nine ( 7-9 ), Yana tsaye ta fito da sauri don kada ya gudu sakamakon daya ce kawai garesu a Ranar. Anwar muje ka koya mun *Math for Economic* din nan ban gane komai ba gashi jibi yace Shi zaiyi nashi test din. Duk Wanda ke wurin sai da ya kalli Bilkisu cike da mamaki yanda take mishi magana Kai tsaye haka, Sam bashi ma take kallo ba ko lokacin da takeyin maganar hankalin ta naga jakarta tana saka littafin da suka gama, yayi Dan murmushi ba dai Yanzu ba ko? Saboda ko break banyi ba yunwa...... Ta dago Kai da sauri Nima banyi ba ai idan mun gama duk ma tafi muje muyi. Ta nuna mishi hanya wuce muje wallahi yau ba inda zaka je......bai San lokacin da ya kwashe da dariya ba Yana ganin karfin halin yarinyar nan sosai, zai Kara magana ta rike kugu tare da tafa hannu kasan Allah ba inda zakaje...... Wuce kawai. Naji muje yayi gaba ita Kuma tabi Shi a baya. Duk illahirin wurin binsa akayi da kallo ana wani irin mamaki. Shi ya Fara Zama kafin ta zauna. Yawwa ko Kai fa....ai ka gama shiga uku dani watan Kaine Mai kokarin aji shine ka mayar damu samnoni ko? Dariya kawai yakeyi, tana surutai tana fiddo littafi da calculator. Ta Mika mishi biro da doguwar takarda ..ungo Fara daga farko..... Dariya yakeyi sosai .....daga farko Kuma? Ki dai fadi abinda baki gane ba. Ni ban gane komai ba. Ban yarda ba Allah nasan kina son wahalar Dani ne kawai gashi yunwa nake ji walhi. Ko me kakeji yau muna Nan sai ka koya mun kawai Fara. Ya bude littafin to bari mu gani ko na iya. Ta bishi da harara Yayi murmushi yace seriously. A hankali ya Fara mata solving dalla dalla. Dayake Bilkisu na da kokari da saurin fahimta hakan yasa bai wahala ba nan da Nan ya fahimci lallai tana da basira saboda da yawa idan Yana koya ma wasu sai su kusan awa hudu bisa example biyu. Akasarin Bilkisu da Mafi yawan formulas din ma ta haddace su idan yanayi da ka take kawo mishi su. Ya kalleta hajiyar dai ashe guruwa ce ko? Ya ajiye biro gaskiya na gaji wallahi duk kin iya kina son bani wahala ne kawai ko Bilkisu? Ta Dan sunkuyar da Kai haka kawai taji Yar kunya ....wallahi a'a ban iya ba. Yabi fuskar ta da kallo Yana Kara kallon yarintar da ke cike da kyakkyawar fuskar tata. Ke ni yunwa nake ji gaskiya ya fada Yana rufe littafi. Dan Allah ka taimaka saura fa biyu da mun gama sai mu tafi Zan siya maka break idan mun fita waje. Au Zaki biyani ne? Ta zaro ido wallahi a'a naga hostel zaka koma gashi har Sha daya ta kusa, Kuma yaushe kaje ka nemi abinci? Ke Kuma fa? Ni indomie zanci dana koma daki. To Nima ita zanci. Ya fada Yana ci gaba da rubutu, Ba damuwa Zan siya maka wurin Abdul Mai shayi na Nan waje ai nasan mutumun ka ne.......da sauri ya kalleta waye ya fada Miki? Tayi Yar dariya ai Ina wuce ku ta wurin Mafi yawan lokuta. Ya Dan harareta ke kin samun ido ko? Ta kyalkyace da dariya Wai ma..... Eh Mana. Rabi labari haka suka gama duk idanun sa sunyi ja....Nan da Nan ta fahimci lallai baya da jimirin yunwa yanda har ya Fara galabaita. Tare suka jera suna tafiya, baka da jimirin yunwa ta fada tana Yar dariya. Ya danyi murmushi yunwa nada sabo ne? Eh Mana Amma ga jaruman maza. Dariya yayi sosai kafin yace naji ni ba jarumi bane ba. Eh, ta fada tana murmushi Ke ni sai anjima ya fada tare da yafito Dan mashin. Ta zaro ido Ina zakaje? Hostel..... Indomie din fa? Na gode.... Wallahi baka Isa ba , Dan mashin din na zuwa tace malam tafi.....ta kalleshi Allah sai na siya maka break kafin ka tafi ko muyi rigima. Yau ni naga ta kaina....ya fada cikin zuciya. Ya kalleta, kiyi hakuri da wasa nakeyi na gode, Ni ban gode ba kawai muje ta nuna mishi hanya. Dariya ma ya kamayi. Haka suka je indomie din akwai layi tace kaga kada mu jira zo muje.... Yace to. Bin ta kawai yakeyi yana kallon ikon Allah sai sauri takeyi suka zagaya babban restaurant din wurin duk yafi ko Ina kyau da tsada, tayi mishi take-away na chips and eggs aka Sanya mishi salad da sos din hanta sannan ta siya mishi gasasshiyar kaza daya

Chapter 3 of 22