ihu ya yi saurin rufe bakin da nasa..... Ta rasa inda zata sa kanta....ya riga ya cimmata.... Wasu zafafan hawaye kawai ke fita..............
Ya saki ajiyar zuciya a hankali ya Kara rungumeta a kirji ya lumshe ido ya kasa magana baya iya cewa komai..... Tayi tayi ta tureshi ta kasa ya riketa gammm. Ta Kara sakin kuka ta sunne Kai jikinsa, duk jikin ta yayi tsami....... Yaja blanket ya rufe su..... Ajiyar zuciya kawai takeyi Shi kuwa ya rasa abin yi duk ya gama kidimewa ya kasa kwakkwaran motsi..... Zuwa can yaji ta Fara sakin numfashi a hankali alamar tayi barci....ya Kara mannata jikinsa kirjinsa na harbawa a hankali..... Shikam cikin kunnensa aka Kira sallah..... Ya zame a hankali ya fada toilet.
Kasa zuwa masallaci yayi. Ya saka jallabiya Mai karamin hannu ya feffesa turaruka ya shiga wani daki ya fito da doguwar Riga, pant, bra da under skirt ya ajiye Mata bisa abun sallah..... ya koma gadon ya shige bargo ya Kara janyota jikinsa......
Barci Mai nauyi yayi awon gaba dashi.
Tafi mintuna goma da farkawa..... Tayi shiruuuu ta tabbatar da lallai barci yakeyi ta zame jikinta a hankali ta sauka gadon, tayi toilet da sauri..... Tana shiga ta zukunna ta Kara sakin kuka.... Sai da tayi Mai isarta sannan ta fada cikin kwami.
Ba wani extra towel Dole Wanda yayi amfani dashi ta daura.
Ta leko a hankali har lokacin barci yakeyi ta sadado ta dauki kayan da ta hango ta koma da sauri....
A toilet din ta shirya, ta fito. Tana cikin yin sallah ya farka...... Lokacin da ta sallame taji motsinsa sai kawai ta koma tayi sujada Bata Kara dagowa ba....... Ya kyalkyace da dariya ya taso.
Tana Jin Yana yowa inda take sai kawai ta Fara kuka......
Ya sungumeta yayi bisa gado Yana fadin ai na Sami Baki yanzu Zan bada hakuri wannan laifi Dana tabka....... Ta sunne Kai.
Ya dagota Bilkisu Allah yayi Miki albarka ya sa daddy da mommy aljannah firdausi... Hakika sun Baki tarbiyya Mai kyau a rayuwa.
Ya rungumeta kiyi hakuri wannan Shi ake Kira *Aure* Kuma wannan kadai zai tabbatar Miki da *how much I love you* kinji ko?
Ta yi shiru.....
Lafiyata Lau jiya Yar dabara nayi ki Samu kici abinci saboda na tabbatar bana iya kyaleki jiya Kam .....
Zo muje ya figi hannunta...... Tafiya sukeyi bayan gidan suka zagaya can...... Sai gasu sashen Hajiya.... Tayi saurin janye hannunta... Yayi dariya kunya kikeji?
Idan Kika ringa wannan sum sum din Zaki to nawa kanki asiri ace jiya..... Ta Kai mishi duka dai dai hajiyar na fitowa.... Ya buga tsalle Yana dariya... Hajiya ta washe Baki...... Bilkisu mijin ake duka?
Ta kusa Suma don kunya ta zukunna da sauri ta ce *Ina kwana*
Ta yi Yar dariya lafiya Lau kuxo ga break din can......
Sai kusan azahar suka bar sashen ta dan sake kadan....
Suna shiga ya rikota zo ki gani..... Yabi da ita wani corridor suka shiga wani falo ya ce nan ma naki ne fa, ya bude bedroom din sai ga wasu irin set na gado royal masu kyau gefe jakun Kuna ne set talatin da shidda ya ce ga lefen ki Zaki gani Yanzu ko ba Yanzu ba?
Ta sunne Kai jikin sa kawai.... Ya danyi dariya *Bilkisu kunya*...............
Ya kamota ya zauna a kujera ita Kuma tana bisa cinyarsa.
Gaskiya kin saka ni farinciki Bilkisu naji dadi jiya har mutuwa nayi na dawo..... Bata San lokacin da ta kyalkyace da dariya ba .... Shima ya Kama dariyar ya ce Allah kinji nayi magana? Ai kasawa nayi.
... Next week zamu tafi Dubai a can zamu zauna Ina da gida a can, sadeeq zai ringa taking care na business din Nigeria tare da taimakon su Suleiman...... Ni Kuma Zan ci gaba da duba na sauran countries din nida su Alhaji murtala..... Kina son Zama Dubai?
Ta danyi murmushi ta ce um.Daga nan Zaki dauki Yan aiki ko kina son na can?
Duk yanda ka gani.... Yayi murmushi.
Zan baki appointment idan result ya fito kema kina amsar albashi kin San hausawa na cewa *Da namu gwamma da nawa* ya karasa maganar Yana dariya.... Kin San duk wakokin bikin Nan nafi son wakokin da *Aliyu nata* yayi Mana?
Ta danyi dariya gaskiya ya iya Waka, ya ce sosai ga babu zagi, ba habaici babu maganar banza yaron ya zo da basira Mai tsafta Shi yasa ake rububinsa..........
Ya Dan taba cikin ta Allah yasa jiya Yara sun shiga...... Ta soke Kai jikinsa..... Ya kyalkyace da dariya.............✍🏼
*KARSHE*
Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Muna rokon Allah ya karemu daga cututtukan zamani.
Abinda muka karanta Allah yasa mu amfana da lesson din ciki na Shi mutunci Riga ne, ya kamata mu sani kunya na daya daga cikin abinda ke daga darajar mace a duk inda take.
Kwadayi baya Kai mutum ko Ina sai tushen wulakanci da Kuma nadama.
Mai kudi da talaka duk bayin Allah ne, masu kuci da ke nuna Basu iya rayuwa tare da talakawa ku sani rayuwar dasu bazai rage ku da komai ba sai dai na ku Kara samun daukaka, mutuncin ku zai karu, zaku Sami lada a wurin Allah. Akwai fa'idoji da dama masu amfani akan Haka. ..... Abinda na hakake a labari shine Jan labari ba shine ba, matukar sakon da kake son isarwa zai je to a layi biyu ma ya wadatar...... Kadan Mai albarka yafi Mai yawa yuyuyu.
Rubuta batsa, maganganun banza da rashin kunya ga labari ba shine ke kawo wa mutane kwarjini ga labari ba. Ma'anar labarin , tsabtar sa da Kuma kyautata rubutu saboda Allah. Duk abinda muka rubuta zamuyi depending din sa a wurin Allah. Ya Allah kada ka kamamu da laifin da mukayi bisa ga tunanin munyi da kyakkyawar niyya. Allah ka yafe Mana ka shirya Mana zuri'a.
Qalubale ga itaye, ku daina tura yaran ku makaranta ba tare da binciken abinda sukeyi ba, ku ringa Kai masu ziyarar bazata Kuna saka ido ga yaranku musamman mata, mazan ma abin kula ne Yanzu.
Yan Mata ku sani bin namiji ka nuna kana sonshi bance haramun bane Amma ku sani kunya ma cikon Imani ce, duk abinda musulunci yazo dashi muna daukarshi da muhimmanci .
Allah ya sada mu da alkhairi.
Wanda labarin bai mawa ba sai yayi hakuri.
Sai mun hadu a wani sabon labarin bayan sallah idan Allah ya kaimu.
*Zainab wowo*💖
*MAMAN AL'AMYN, AMINATU AND ABDALLAH*a
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 22