Share this page
hakuri..... Idan kin lura ta na nemana da rigima sosai...... Kayi zuciya ka kyaleni daga yau a fita harkar Bilkisu..... It's alright take care, Kawai ya fada mota yaja ya tafi .... Gabanta yayi mummunan faduwa, ta yi shiruuuuu kafin Ta figi hannun Aisha zo muje. Suna zuwa daki ta fada katifa ta saki kuka.... Ai kinyi kuskure me yasa zakiyi mishi irin wannan wulakancin Bilkisu...... Ta dago fuska jage jage da hawaye.... Aisha na rasa gane inda Anwar ya dosa, masifar nan tashi ta isheni gara ya kyaleni na huta.... Wallahi bazaki huta ba. Ta Kara kallon ta da sauri, yes bazaki taba hutawa ba saboda kina matukar kaunarsa.... Bilkisu nasanki nasan wacece ke, gwargwado nasan waye Anwar shima wallahi tallahi matukar baku fito Kun fadawa junanku surrin da ke zukatanku ba tabbas zaku kashe kanku a banza...... Ni na taba ganin jarababbiyar soyayya irin taku? Ko wane idan kishin Dan uwansa ya motsa sai ya Kare kansa?...... Ta kife Kai a filo ...ta Kara sakin kuka a hankali....... Idan kin gama ki tashi kiyi parking, ga maganin nan na dauki kwaki goma .... Ta fice jikinta duk ya mutu tana mamakin irin wannan soyayya wacce ko a littafi Bata taba karanta irin ta ba. Gaban sadeeq ya Fadi....... Anwar lafiya na ganka a firgice haka ko jikin....... Tashi ka shirya mu tafi Kano. What? Ya mishi wani kallo gaban Sadeeq ya Fadi ya tsorata Anwar lafiya? Zaka je ko na tafi? Ya kamo Shi ......ya fizge sadeeq Dan Allah ka kyaleni *I hate this world*........ Ya ci gaba da harhada Kaya...... Dole sadeeq ya Mike shima ya Fara hada jaka..... Amma wallahi bazaka tuka mu cikin wannan mood din ba ... Bai rufe Baki ba ya wurga mishi keys din a kirji ya figi jakar sa yayi waje..... sadeeq ya bishi da gudu tare da rufe dakin....Sha biyu da Rabi na dare suka bar dutsinma yana kwance a sit ya Dora kafa daya a dash board ya kwantar da sit yayi filo da hannayen sa idanun sa rufe..... Kadan kadan sadeeq na lura dashi sai faman tsoki yakeyi. Batayi tunanin abin zai dameta ba sai da ta koma gida, kwana daya , biyu...sati. Anwar bai nemeta ba. Suleiman kuwa yayi Kiran duniya ta kasa dauka kamar tana son Jin haushin sa ganin shine jigon wannan fitina. Gaba daya gidan an ga canjinta, bata walwala, kullum tana daki kwance. Ranar da tayi sati biyu da dawowa mommy ta sameta daki, ta zauna bakin gado, Bilkisu mi ke damunki? Na lura tunda Kika dawo Baki da walwala, meke damunki? Saboda har dadyn ki ya Kai ga yin magana...... Ko maganin da Kika ce Anwar ya siya Miki ne kike ganin yayi yawa?....sai kawai taga kwallah na zubo Mata.... Hankalin momy ya tashi ko dai daukar magana Yar tata taje......subhanallah. tayi saurin kawar da tunanin. Ta janyota fada mun menene? Ta goge hawayen mommy bana Jin dadin abinda Anwar keyi mun...... Ta Bata labarin duk abinda ya faru..... Sai kawai taga mommy na dariya. To Bilkisu Anwar ai kishi ne ke damunsa tunda baya son ki kula Suleiman din sai ki kyaleshi.... Ina wayar ki? Ta Mika Mata kawai..... A'a Anwar din Zaki Kira kice yayi hakuri tunda ke kin damu bai Kira ba..... Tabbb wallahi bazan kirashi ba mommy..... To ya Zama dole ki fitar dashi a Ranki domin Shi da alama ya manta da ke kamar yanda Kika mishi gargadi...... Kirjinta ya buga da karfi kwallah suka Kara cika idonta ...mommy ta mike wannan shine sai ki zabi daya cikin biyu, Amma bazan dauki wannan dararewar ba da kikeyi cikin gidan Nan... Tana Gama fada ta fice tare da Jan kofa gammmm. Tayi zugummm, dabara ta fado Mata kawai Bari ta Kira Sadeeq...... Anwar kuwa yafi Bilkisu shiga tashin hankali, ya koma kurman karfi da yaji, hankalin Hajiya yayi mummunan tashi tana zargin ASIRI ne ke son kamashi. Ita kadai ke shiga dakin sa sai kuwa sadeeq, kullum sai ta lallasheshi yake cin abinci.... Abun har ya Fara affecting kasuwar sa, kowa shakkar kiransa yakeyi a waya saboda masifa da bala'i. Tana zaune ta tsareshi ya shanye tea din ta Sha mur alamar ba wasa kamar kullum, ya Sha mur, ya tsuke fuska rabonsa da dariya tun ranar da ya rabu da Bilkisu Yana cusa kwai a Baki jinsa yakeyi kamar madaci. ....... Sadeeq ne ya turo kofa Assalamu alaikum. Hajiya yau kina ciki? Eh sadeeq maraba, Wa'alaikumus Salam. Kamar zatayi kuka ta kalli sadeeq na rasa ainahin meke damun Anwar, shin ko ta sanar dakai ......ya wurga mishi harara Yana horonsa da ido kamar kullum akan kada yace wani Abu...... Hajiya ina ga malaria ce, kin San fa dutsinma akwai sauro sosai Daman ya Saba duk hutu sai ya kwanta ..... Ba irin wannan kwanciyar ba. Yaro ya takure ya makure sammm Anwar ko murmushi ya daina yi...... Zai dawo normal hajia aci gaba da addu'a. Ta Mike , kaima ai bakin ku daya, ko ma menene bazan yarda da wasa da abinci ba... Ta fita. Ya kalleshi ...ya kamata ko don tsohuwar nan ka daina wannan abun, nasan wallahi duk wannan damuwar Bilkisu ce... Ta kirani dazun ta fada mun duk abinda ya faru hada kukanta, ta ce wallahi Babu abinda ke tsakanin ta da Suleiman, Anwar hakuri akeyi..... Please sadeeq ka kyaleni..... Bazan kyaleka ba tunda kaima baka kyale kanka ba . Ta ce na baka hakuri....bazanyi ba tace na Kyaleta hakurin me zata bani?..... Har wannan maganar ta fada mun ta ce kuskure ne bacin Rai yasa ta Fadi hakan..... Karya takeyi. Tana son bani haushi ne don na Mari Suleiman...... Wannan zafin kishin naka bazai taba sany.... Kishin ubanwa zanyi? Ya Mike ....ya kamoshi da karfi ya mayar.... Dan Allah kayi hakuri Anwar tunda wallahi Koda mukayi ways kuka takeyi..... Kaine zata Kira taba hakuri ba ni ba? Tunda Kaine tayi wa laifi ko? Ikon Allah.... Tana tsoron kada ku Kara wani fadan ko kaki dauka ....... Ni zaka zo ka tsara sadeeq??? Tsari??? Wallahi da gaske nake ita ce ta kirani....ya fiddo waya aljihu...duba ka gani ni na Kira ko ita? Minti nawa ka gani? Sai kawai yayi murmushi ko kadan bai San yayi ba.....ya zaro ido are you smiling????? Ya Kai mishi duka ya goce..... Munafuki ni na dade da sanin wannan cutar taka Bilkisu ce.... Dan Allah fada mun tayi maganar cikin damuwa? Wallahi kuka takeyi lokacin da muna maganar alamar abun ya dameta...... Mtseww ita ce ke Sanya mu damuwa ai..... Iye? Sadeeq ya fada , ya banka mishi harara Yanzu dai kirata kace ta kirani da kanta ta bani hakuri..... Message ya shiga wayar Anwar din karammm..... Ya dauko da sauri jin alamar shigowar message din ta ne, ```I'm sorry very sorry please and I don't mean to hurt you```..... Sai kawai ya washe fuska.... Sadeeq Bilkisu ce.... Dan Allah Kira mun ita.... Suna Kira wayar a kashe. Abu kamar wasa kusan kwana uku duk lokacin da aka Kira a kashe..... Shi kansa ya nema Amma bai Samu ba.... Hajiya dai taga Anwar lokaci guda an warware har Yana fita tawon *Bike* da suke zuwa da marece Shi da yaran governor. Ta warware amma duk ta Dan rame kadan..... Kullum tunanin Anwar. Ta kasa bude wayar ta saboda tana Jin kunyar idan ya Kira me zata fada mishi bayan ita ce ta bayar da hakuri? Ta Kama lahadi suna gida duka har daddy, tana sanye da Riga da skirt na atamfa super Holland Mai flower yellow dinkin ya bi jikinta, dogon hannu ne na *net* yellow duk atamfar yayyabe flowers din suke da stones masu sheki kamar diamond. Kanta ba kallabi ta maida gashinta baya ta kulle jelar kwance bisa bayanta..... Motsin get suka jiyo. Daddy ya Mike da sauri ya daga labule....jibga jibgan motoci ne bakake suke shigowa.... Ya ce innalillahi.. waye zai bamu surprise visit Haka?.. aka Fara fitowa yaga securities ko wane da abin magana a kunnensa ya saki labule da sauri, ya kallesu inajin foreign affairs minister ne ..... Yayi ciki da sauri.. Suka tashi duk suka fada daki. Bilkisu ma ta shige nata. Ya fito Yana gyara hula, falon kamshi kawai ke tashi na freshner ta ko Ina .... Ga A.C ta gauraye ko'ina.... Ring bell ya Fara kadawa a hankali... Da daddy da kansa ya bude..... Ya bude ido sosai cike da mamaki compound din gidan makil da securities suna tsaye ya Sha fararr gizna dinkin falmara ce yasha aiki kansa cikin kube murjin kanawa...... *Waye in ba Anwar ba*....... Anwar??? Daddy ya fada ....sukayi saurin zubewa shida Sadeeq daddy Barka da yammaci...... Ku tashi .... ku tashi.... Ya kamo Anwar.... Ya riko hannun sa suka shigo ya kwadawa mommy Kira ta fito da sauri.... Tayi turus ganin Anwar tare da washe Baki *Anwar a gidan mu*? Sai sumke Kai yakeyi.... Daddy ya zauna suka gaisa sosai ya kasa hada ido dashi sai sadeeq ne ke faman amsawa . Tuni mommy tayi ciki tasa Rahina Mai aiki ta fara kawo musu abin Sha.... Daddy ya Mike ya haye sama. Mommy ta shigo suka Kara gaisawa ta koma ciki.... ya kalli sadeeq Dan ubanka ka tamabaya kace Ina Bilkisu?????...... Ya zaro ido ya Kai mishi duka...... Tana kwance ta kunna t.v din ta tana kallon wani Korea series *Innocent man* Mommy ta shigo, ke kullum idan anyi Baki sai ance kizo ki gaishesu??? Tayi zumbur Ina da niyya mommy ayi hakuri..... Ta galla Mata harara.... Tabbas kowa yasan surprise visit ya Bata don me zata fada Mata.... Gara ta fita idanunta su gane Mata. Ta dauki dan mitsilin gyale ta Yana a fuska bai ko rufe rufe rabin gashinta dake kwance a baya ba..... Ta raba momyn ta wuce .. Assalamu alai........ Ya dago da sauri sukayi tozali.... Sai kawai ta dafe kirji tayi baya da sauri kamar wacce taji tsoro , mommy na tsaye bakin kofar dakinta Bata fita ba.... Ta ruga ta makalkaleta..... Mommy da gaske Anwar ne?.........✍🏼 *Zainab wowo*πŸ’– πŸ‘‰πŸΌπŸ˜‘ AlaweezIDAN KUNNE YAJI πŸ‘‚πŸ€ *WA ZAI FURTA?*🀐 2⃣1⃣ *Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.* *KINA RAINA MAMAN WEEDAD* *Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray* πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’• *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜. ************** *ABUJA NIGERIA* Ya kyalkyace da dariya, ya kalli sadeeq she was shocked..... Ai dole ta razana wannan babban surprise ne. Ya Kara dariya. Yeah I like surprise ...... Da gaske Anwar ne mommy???? Tayi Yar dariya shina halan bai hwada Miki zai zo ba? Bai hwada min ba mommy muje ki raka Ni..... Walla Baki da hankali ni Zan kaiki inda Anwar? Ta Fara dire diren shagwaba. Walla bani rakaki keji min ja'ira..... Ki kaisu can Fallon daddyn ki na baki zasu fi sakewa naga Anwar duk ya takura.... Mommy Dan Allah muje ki raka Ni..... Ta kyalkyace da dariya yau naga ikon Allah.... To Wai ya ankayi yasan gidan mu? Idan kinje Kya tambayeshi. Ta tura ta waje daya ta fito da sauri..... Ta biyota da gudu mommy jirani.... Ta boye bayan ta, Koda yaga mommy ce ta fito yayi saurin yin kasa da Kai.... ta wuce abinta tana dariya. Tayi tsaye tana Yar kyarma tana murmushi kanta kasa. Sadeeq ya tsura Mata ido kinyi tsaye ki karaso Mana Bilkisu. Tayi Yar dariya sannun ku da zuwa ya hanya..... Sadeeq ya ce qalau. Ta bi bayan kujeru kuzo muje tayi gaba kadan duk suka Mike..... Tana zuwa saitin kujerar sa ya yi charaf da hannun ta ya kalli sadeeq Dan ubanka shiga gaba.... Ya tuntsure da dariya, idan na shiga gaba in kaimu Ina? Kwatanta mishi Bilkisu...... ta fizge hannun ta lokacin ne ta Sami damar kallonsa don ta bashi harara.....kyaleshi sadeeq muje..... Ya dawo da ita da sauri jeki sanyo hijab...... Ta kalleshi zaka Fara ko? Gidan namu ban tsira ba? Yasha mur jeki sanyo hijab wallahi kada mu sayar da Hali anan...... Dole ta juya tayi daki ya bita da kallo har ta shige ya hadiye wani tsinkakken miyau ya dawo Kan sadeeq ya Kai mishi uban duka Allah ya Isa Dan ubanka ka ga harammmm..... Wata muguwar dariya sadeeq din ya saki .... Kayi a hankali fa... Ashe duk dramar nan mommy na kitchen na hangen su..... Ta Kama dariya ita kadai....lallai Bilkisu tana da aiki. Ta fito da doguwar hijab har kasa ta banka mishi harara muje..... Suka bi bayanta.. Ba sadeeq ba, Anwar kansa falon ya tafi da imanin sa, ya zauna bisa two sitter sadeeq Kuma ya zauna kujerar dake can karshe Shi kadai ya ma t.v kuriiiii ganin ana best film dinsa *mortal combat* Ta zauna bisa three sitter tana facing sadeeq ta Kara gaishesu Sadeeq ya kalleta Yana dariya sai Kika ganmu ko? Tayi murmushi hmm, Hakuri muka zo badawa..... Ke ki dawo Nan kin mun nisa... Ya fada Yana kallonta. Tayi kamar Bata ji ba, sai kawai taga ya Mike tayi saurin kallonsa... Yana tasowa ya figo hannun ta Yana fadin ke wallahi wata bagidajiya kike wancen Dan iskan ba dashi zakiyi fira ba ni ne bakon...... Ta fizge hannunta... Akwai CCTV ta nuna mishi da hannu.... And then? Ta zaro ido.... Kai Wai baka da tsoro? Mtsew yaja guntun tsoki tare da figarta da karfi ya zaunar da ita kusa dashi, just sit down here. Kaii Allah ya raba ka da rigima..... Allah ya rabaki da gardama kema. Rahina ta shigo da tray cike da kayan marmari da lemuka masu sanyi ta Fara jerawa a dining table sannan ta fita tana kawo kuloli kala kala..... Baza mu ci abinci ba fa saboda bamu sanar ba kada a takura ayi Mana. Har an gama ai, idan baku ci ba mommy zataji babu dadi? Me yasa Kika kashe wayar ki? Tayi shiru tana murmushi. Kinji? Duk kin rame kinyi rashin lafiya ne? Um, ta ce. Ko dai tunani na ne? Ta galla mishi harara , ya kyalkyace da dariya ni ma na rame ko? Um, ta ce. To ki tambayeni dalili Mana ...... Ta danyi murmushi kaiiiiiii Anwar. Me yasa Kika koma da gudu bayan kin ganni? Tayi Yar dariya.... Murna CE? Ta Kara galla mishi harara. Bacin wancen Dan iskan da Baki sako hijab din nan ba kayan sun Miki kyau kin San Haka? Ta ce hmmm, kawai. Gobe Zan dawo ni kadai kada ki Sanya hijab kinji ko? Ta harareshi kammmm. Yayi murmushi Dan Allah kisa irin gyalen dazun.... Bafa Zan saka ba dazun ma na manta ne..... Zan cireta idan Kika saka wallahi...... Anwar Nan fa gidan mu ne nidai ka rufa mun asiri. Ni Yanzu ka janyo mun anjima dole in amsa tambayoyi wurin daddy? Na mene? Dalilin zuwan ka ko? Kice fada mukayi gashi kin kashe wayarki nazo bayar da hakuri...... Nidai Dan Allah da baka zo ba saboda zai...... Ya tsareta da ido. Tayi shiru. Uhum, Ina jinki saboda zai ce meye? Nidai shikenan. Ya kalli sadeeq jeka ci abinci fa, okay ya Mike ya nufi wurin ....ke Kuma kawon nawa anan inci. Saboda me? Saboda bana son kimun nisa Kuma bazan yarda gani ga ki ga sadeeq a wuri daya ba muna ci...... Wai Kai meke damunka....???? Yayi dariya kawai. Suleiman ya kiraki? Gabanta ya Fadi, wace amsa zata bashi kada Kuma ya Kara hasala saboda ta lura tabbas baya kaunar Shi. Bari kawai na fada mishi gaskiya..... Ya yi ta Kira Amma ban dauka ba wallahi...au haba? Allah kuwa. Ko shine dalilin da yasa Kika kashe wayarki? A'a ba Shi bane. To nine? Tayi shiru. Saboda me Kika ki daukar wayarsa? Anwar ka daina kawo maganar Suleiman tunda ita ke kawo Mana sabani..... Dole ki canza layi..... Ta zaro ido dole fa kace . Yasha mur tabbatas and I mean it. Ta Mike kawai tana hararar sa, ya Kai hannu zai kamata tayi baya da sauri tana fadin Zan kawo ma abinci ne.... Sadeeq ya banka mishi harara kaidai wallahi bakayi ba..... Yayi murmushi ka Gama kazo ka bar Falon nan ka isheni haka Nan .... Babu inda zaije. Ta fada tana zuba mishi farfesun Koda da dankalin turawa.... Ki hanashi din ki janyo ma kanki Yanzu in ci ubansa anan har su daddy suji.... Gabanta ya Fadi tasan karamin aikin sa ne. Ta kawo Masa ta Dan janyo stool ta ajiye ta koma ta dauko mishi juice exotic Mai sanyi na kwakwa da abarba. Ke ce kikayi? Ya kalleta lokacin da yayi lomar farko...... Mommy ce. Yayi dadi amma gobe komeye za'ayi kiyi mun kinji ko? Ta galla mishi harara kawaiyayi murmushi Ina dai Shan harara Ni Anwar. In tambayeki??? Ya tsareta da ido. Um, Tsakanin ki da Allah kinji dadin zuwa na? Tayi Yar dariya kawai..... Kinji? Wai ya akayi kasan address din nan gidan? Yayi murmushi sirri ne. Ta Dan harareshi ka Sanya mun ido da yawa me yasa ka damu dani haka? Saboda....... Yayi shiru Yana Yar dariya. Ta tsareshi da ido, saboda me? Saboda kawata ce ke my best friend.... Ta buga tsoki.... Ya kyalkyace da dariya. Yana ci gaba da Shan pepper soup din. Sadeeq ya Mike Bilkisu bude mun kofar can naga exit ce ko? Eh, amma ya zaka fita zaka biye maganar sa ne? Yayi murmushi a'a Zan dawo ne shidin banza ya hanani Zama anan? Ya bisu da kallo kawai Yana Shan lemu. Tana budewa ta hango iyayen motoci da katti sai gewaye gewaye sukeyi suna mazurai..... Ta dawo da sauri, Wai Kaine kazo da waccen bataliyar? Ta tsaya gabansa tare da rike kugu, ya daga ido Yana murmushi tsiwar ce ta tashi? Anwar waye baban ka?...... Ya fesar da lemun bakin sa saboda dariya. Ta tsuke fuska, ya fizgo hijab dinta tayo kansa zata fada yayi saurin mayar da ita gefensa ta zauna..... Innalillahi, Kai Wai wane irin mutum ne? Idan za 'ayi tambaya Zama akeyi ba tsayuwa ba bakauya.... Nice bakauya ? Eh ya fada Yana hararar ta, Ka amsani ........ Maganar ta makale ganin ana shigowa da jikkuna set/set..... Ta zaro ido ko yazo neman auren ta ne????? Ta kalleshi da sauri meye ake shigowa dashi kamar wani lefe?????? Ya kyalkyace da dariya lefe Kuma an fada Miki na Isa Aure ne? Ta daka mishi tsawa to na menene? Calm down ya fada a hankali ganin tana neman tayar da hankali...... Na kawo Miki tsaraba.... Tsaraba ta mecece? Anwar wanene baban ka a Kano? ....Kai Ina son in San waye Kai ayau... Dai dai sun gama ajiye jakunkunan set hudu ta daka musu tsawa ku mayar dasu mota bazamu karbi kayan Nan Haka ba fa.... Sadeeq zaiyi magana ya daga mishi hannu yace jeka kawai Zan Mata bayani...... Anwar ko hakan zai Zama batawar mu ta har abada...... Ki dubi girman Allah ki daina janyo mun tashin hankali ki jira na amsa Miki duk wata tambaya da Kika rasa amsar ta. Zan amsa Miki wanene baba na a Kano.... Ta tsareshi da ido, ya yi Yar dariya. Baba na ya rassu Ni maraya ne...... Jikinta yayi mugun sanyi. Tayi saurin kallon sa kamar zatayi kuka...kayi hakuri Anwar ban San Haka ba. Ta Fara magana a hankali Allah ya jikansa da rahama yasa mutuwa hutu ce, yayi murmushi cike da Jin dadi Amin ya Rabbi. Sai kuma me? Waye Kai? Ko Kuma wanene marikin ka? Yayi Yar dariya nine *Hamza bushara*..... Ta dago Kai da sauri taja baya ta koma karshen kujera kamar wacce taga abin tsoro.... Ya Kara Yar dariya.... Bilkisu nine *Bushara* Wanda Kika ji ana fada a *Nigeria*.... Na shiga uku ta fada da karfi.... Ke kwantar da hanka... Ta Mike da sauri shima yayi saurin mikewa...... Idan Kika gudu Zan biki har gaban mommy wallahi.... Dan Allah me kake nema wurina Anwar?.... Na shiga uku. Ta Kara fada duk jikinta ya tsinke da rawa...... Zauna in Baki amsa ta Kara ja baya.... Ka kwashi kayan can kabar gidan nan tun kafin ma..... Ke Wai ya akayi ne ya daka Mata tsawa. ..... Ta daga hannuwa kayi hakuri na tuba *Bushara* ta Kara maimaitawa a hankali..... Ya buga tsoki ke bana son gidadanci zo Nan ya Mika hannu..ta ja baya . Ya fiddo ido...ke me yasa kin cika kawo matsala? Yasha mur kina son in kamaki ko? A'a, ta fada tana girgiza Kai, oya come and sit down let's sort out where the problem is...... Ta zauna a dosane..... Ya kyalkyace da dariya ji yanda Kika canza lokaci daya..... Kin taba ganina a TV? Ta ce a'a. Jarida fa? Ban gani ba. To Kuma. Kika sani ko Ina zolayar ki ne? Ta Dan kalleshi. Yayi murmushi eh Mana . To ko da wasan kakeyi? Ya kyalkyace da dariya kawai. Ta bishi da kallo. Ke Ina Kika San *Bushara*? Ta harareshi a Nigeria waye bai San wadannan sunayen guda biyu ba *Dan gote da Bushara*? Ya Kara yin dariya..... Yayi saurin matsawa kusa da ita ya chafki hannuwanta.... Yawwa ya fada Yana murmushi....nine *Bushara* ki kwantar da hankalin ki nothing will happen sai alheri...... Kwallah suka shatato Mata ita kanta Bata San ko na menene ba...... Kuka again? Ke bakya da wahalar kuka? Bana son kayan can daddy zai tambayeni na menene Kuma zai mun tambayoyi akanka......Yanzu kukan na menen ciki? Kayan ko kuwa sanin da kikayi nidin waye? Kai nidai gaskiya ka kyaleni.... In kyaleki? Kin Kara maimaita wannan kalmar Dana fi komai tsana ko? Ta kalleshi Anwar me yasa ka mun waccen hidimar? Ya saketa tare da watsa hannuwa kawai I feel to..... Ba yiwuwa ka fada mun me yasa kake wannan over acting din? Na ce Miki kawai na siyo miki tsaraba ne bana son zuwa hannu biyu..... Ta Mike bazan karba ba ka mayar dasu gida idan ka Isa Aure ka hada wa matarka..... Ya Mike ta nemi kwasawa da gudu ya yi saurin rike hijab dinta. Wallahi sai ka sakeni haka kawai daga muna course mate zaka jibgo irin wannan hidimar ka kawo mun..... Kawai ne Bilkisu? Ya fada Yana matsawa kusa da ita.... Kawai ne wallahi, I don't value friends lemme tell you. Kina son ki kunyata ni ne? Ta galla mishi harara Ni ma ai kunyata ni zakayi idan daddy ya tambayeni sai kawai ince abokai..... Kice *INA SON KI* ne.... Ta zaro ido jiri ya nemi daukar ta.........✍🏼 *Zainab wowo ce* *Assalamu alaikum* Masoyana Ina alfahari daku. Nazo da wata tsaraba, hausawa na cewa kula da Kaya....... 1. Ina wacce ke fama da karancin ni'ima? 2. Wacce ke fama da budewa tana son jinta a matse da ni'ima sosai? 3. Ko kinsan yawan zubar da ruwa wani lokacin matsala ne? Wacece keson taji ta adai adai? 4. Wacece mijinta baya gamsar da ita? 5. Suwa ke fama da infection? 6. Akwai matan da har yau Basu San dadin Aure ba sam Basu Jin sha'awa ko kin San dalili? 7. Wacece keson ta gyara nonon ta da jikinta yayi luwai luwai? 8. Ina wadanda mijinsu baya gamsuwa dasu? 9. Wacece kullum sai tayi amfani da lubricant saboda karancin ni'ima? 10. Ina wadanda miji ke musu gani gani da hargagi kullum? Akwai supplement masu kyau na dukkannin matsalolin aure daga zainab wowo, direct order ne muna turawa ko wane gari Amma Kano, Abuja da katsina zaku sameshi free delivery in shaa Allah. Masu bukata su tuntube Ni. Darajar annabi da alqur'ani serious buyer nake bukata Dan girman Allah na rokeku. Ga number ta 08089973394 in shaa Allah.🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐 2⃣2⃣ *Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.* *KINA RAINA MAMAN WEEDAD* *Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray* πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’• *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember

Chapter 15 of 22