An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*_🗻𝙄𝙉𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘿𝙐𝙏𝙎𝙀...🗻_*
*_Rabi'a wakili_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
*_Book 1_*
*_Episode 1_*
_______________________
Kowane ɗan adam yana ratsa sararin duniya ne ɗauke da wani tsari na daban wanda Allah Ya tsara mana a rayuwa. Wannan tafiyar ba ta da wata fuska ta zahiri, kuma ba ta da siffa ko launi da za a iya kallo da idanu muddin mutum yana raye, sai dai nauyinta da zafinta suna sauka ne kai tsaye a kan zukatan da ke ɗauke da ita. Akwai lokutan da walwala da daɗi ke bayyana a fili tamkar farin wata, akwai kuma lokutan ƙalubale masu ɗaci da ke girgiza jiki da firgita tunani, har ya kai ga mutum ya ringa gani a ransa tamkar dukan kofofin mafita da hanyoyin samun sauƙi sun riga sun datse, an bar shi shi kaɗai tsakanin tsananin fargaba da fita tsammani. To sai dai, a daidai lokacin da hasken rayuwa ya dusashe, sa'ad da dukan kewayen mutum ya turnu da baƙar inuwa ta tsananin rudani, makami mafi ƙarfi da ke share fagen samun mafita shi ne natsuwa ta dindindin gami da jajircewa ta gaskiya. Kowa ya sani, Zaman jiran dadi, sai mai babban bargo.Haka kuma, duniyar nan ta zama tamkar igiyar ruwa, tana juyawa da kowa yadda ta ga dama, ba ta taɓa tsayawa a guri guda ba. Saboda haka, ikon tsayawa tsayin daka a lokacin da wannan igiyar ruwan ke kwasar mutum zuwa ga gaɓar da bai sani ba, wani babban matsayi ne da kwarjini na daban wanda ba kowa ke iya kaiwa gare shi ba. Mutumin da ya siffatu da wannan juriya, ya riga ya buwayi dukan wata barazana da kowace irin maƙarkashiya da ke tunkaro shi daga kowane sashe na rayuwa. Jajircewa kuwa ita ce danyen ƙarfin da ke tursasa wa mutum ci gaba da takawa, tana tilasta wa ƙafafunsa ci gaba da takawa a ƙasa ko da gangar jikinsa ta gaza ɗaukar nauyin kanta saboda tsananin gajiya da wahala. A cikin tsarin tafiyar duniya, fuskantar matsaloli ko kaɗaitawa a cikin damuwa ba ƙasƙanci ba ne, kuma ba yana nufin an ƙare ba ne; wata koyoce ta musamman, wani darasi ne mai tsada da ke gina mutum, yake ƙara masa kaifin basira domin ya shirya shi da dukan dambarar da zai fuskanta a gobe. Wannan rayuwar ba ta taba tafiya daidai da burinmu ko yadda muke tsara ta a cikin zukatanmu ba. Idan igiyar ruwan ƙaddara ta taso da ƙarfi, tana juyawa ne kawai a kan sahihin tsarin da Mahalicci Ya riga Ya ƙaddamar tun kafin halittar komai, domin a ƙarshe kowa ya gane cewa matsalolin da ke zuwa ba su da manufar ruguza mu ko share mu daga doron ƙasa, illa gyara mu da za su yi, su fito da ainihin juriya da ƙarfin da ke ɓoye a cikinmu. Duk wanda ya fahimci wannan ma'ana ta sirri, ba ya fargabar tsayawar al'amura, kuma ba ya tsoron shiga cikin sabon rikici ko wata turkaturka ta rayuwa, domin ya san cewa tafiyar duniya ba ta taba kayar da wanda ya iya dakatawa ya bar wa Allah ikonsa ba. Haka kuma, mutumin da ya karɓi dukan abin da ya zo masa da zuciya ɗaya gami da gamsuwa ta ciki, ya sanya juriya a matsayin garkuwarsa ta yaƙi, sannan ya dogara ga ALLAH, lallai ne zai riski nasarar da aka riga aka rubuta masa, zai kuma taka da ƙafafunsa a kan daukakar da aka yi masa alkawari ko da dukan hanyoyin da za su kai shi gurin a halin yanzu sun Lulluɓe da baƙar inuwa ta duhu mai ban tsoro. Domin a ƙarshe, rayuwa gaba ɗayanta, arziƙi, matsaloli, da daukaka, duka suna naɗe ne a cikin babban shirin nan na ƙaddara, wata doguwar hanya ce da kowa ke bi yana takawa daki-daki cikin duhun dare, ba tare da ya san wace irin dambarawa ko jarrabawa ce ke jifansa a gaba ba, sai dai kawai amincewa da juriya da kuma dogara ga ALLAH, shi ne hasken da ke haska masa kowane taku.
________________
Kano state Nigeria.
Yammace saƙaliyan ana gab da magrib, wani mutum na hango, bai cika kiɓa ba, Sauri yake ta zubawa kamar wanda zai tashi sama, babbar rigar da ke jikin shi wacce ta sha ruwa sai tashi da sauka yake, kamar wanda zaiyi tsuntsuwa ya fire sama, tafiya yake baya ko kallo inda yake saka ƙafa, kamar yadda baisan inda yake takawa ba, haka zuciyar shi ta kasance tana chan wani wajen daban. Burin shi kawai ya koma gida, ko ya samu sarari na daga abinda ya taru yai masa yawa.
Tun da ya doso farkon layin anguwar ake binsa da kallo, kallon da ke mishi inkiya da gagarumin matsala, eh kam dole ya ambaci haka da matsala mana, dan babu rana na ALLAH da zata zo ta wuce bai samun irin waɗan nan idanun a kansa ba, wanda ba yau farau ba, yana kuma da babban tabbacin ba ƙarshe bah kenan, matuƙar yan kokawan gidan sa suna nan, ai shikenan.
A maimakon yanayin sa ya chanza, amma ina babu alamun haka tattare da shi, inda sabo ya saba, dai dai da kwayar zarra hakan bai taɓa ci masa tuwo a kwarya ba, idan sun kashe kansu maƙabarta har yau har gobe kai har wani shekara bata cika ba, toh akan mi zai na dinga wahalar da rayuwar sa a kansu, su bar sa da abinda yake damun sa mana.
"Mmmtwwwsss" ya ja doguwar tsuka dai dai ƙofar wani ɗan matsakaicin gida da hayaniya ke tashi daga ciki babu ƙyaukyautawa, wanda sautinsa yake tashi ana ji har ƙofar gida da maƙota.
Shiga ciki yayi, Inda ya tarar da su a hargitse, sai faman yaɓawa junansu magana da son maida martani a zafafe cikin fusata dan a kular da abokin faɗan. Hakan ba sabon abu ba ne cikin rayuwar gidan ba, domin ga wanda bai san su ba sai ya yi tunanin sun haɗa tsatson ƴan dambe ko kuma maguzawa, ta yanda ba sa raina ruwan shuka, kamar jira suke yi a ce kule suce as.
Ɗauke kai ya yi tare da jan doguwar tsaki da nufin barin wajen. Babu shiri babu tsammani ya ji sauƙan bokiti a bisa goshinsa, take ya cije leɓen sa tare da dafe goshinsa da tafukan hannayensa saboda azabar zafin da ya ziyarci har cikin ƙoƙon kansa, nan take malolo makure sa a wuya.
Shiru ya mamaye wajen tamkar an yi ruwa an ɗauke, duk wannan hayaniyar ta gushe tamkar yadda ruwa da sabulu suke gusar da ɗauda. Ba komai ya haddasa hakan bah illa ganin kwaɓar da suka kwaɓa, watsar da makaman yaƙin da suka yi niyyar tadawa suka yi yayin da kowa ya sha jinin jikinsa.
Da sauri ya ciro hannun sa akan goshin dan tabbatar wa shin da gaske ɗin sun raunata sa? Cikin sa'a ba ciwo ba kuma jini, a ɓoye ya sauke ajiyar zuciya da hamdala ganin ba su zudda masa da jini a banza da wofi ba, dan ba yi da hanyar kuɗin magani balle a ɓallo masa wata jinyar.
Ƙara ɗaure fuskarsa ya yi waje guda tamkar magribar ɗinya, ya na cin magani haɗi da bin su da kallon ɗaya bayan ɗaya, Ji ya yi wani sabuwan baƙin ciki ya ƙara shigewa kai tsaye har cikin ƙasan zuciyarsa, dan takaicin ganin yadda suka nuna rashin damuwa sai ma kallon da suke bin sa dashi kamar da shi za su ci gaba da dambarwan, nan take malolon sake linkuwa fiye da wanda yake ciki, a yanzu hakan kuwa ya taimaka wajen ƙara tunzira shi, ga takaicin su da takaicin ya dawo bai samu abin da ya fita nema ba, abin sai ya haɗu ya haɗe masa goma da ashirin. Hakan ya ƙara taimakawa wajen tafasar da zuciyar dake kwance cikin ƙirjinsa.
A fusace ya soma cewa "Uban wa ya halbo ni? Wallahi idan kuma ba haka Allah sai na lahira yafi ku jin daɗi, a waje mutum bai huta ba, a ce cikin gidansa ma ba zai huta ba? Duk kun ƙarar da ni dan masifarku kamar wanda Maye ya yi wa ajiya. Na ce uban waye ya halbo Ni?" Ya ƙare maganar yana mazurai cikin maɗaukakin ɓacin ran da ya bayyana har a cikin kalmominsa.
Duk tsam sukayi suna binsa da kallo, kamar sunga wani sabuwar halitta, ko wani majigi. ko ma ace kamar waɗan da basu gane yaren da yake yi ba ma bare su fahimci inda ya dosa.
manyan mata ne su uku da yan mata uku, chan ƙarshen gidan wata matashiya ce zaune a ƙofan madafa sai dai ta juya musu baya, duk wannan masifar da suke ko ɗagowa ta kalli halin da suke ciki batayi ba, bare ta ce wani abu, idan ba ka lura ba, ba za kace akwai mutum a wajen ba, dan gaba ɗaya yanayin matashiyar ya nuna bata ma san halin da suke ciki ba. "Ooh ga ɗan iska na magana ai dole ku maida ni tataccen haihuwar ƙasar gada! Dan....."
Cikin sauri mama ta tare shi jin zai fara sakin ashariya tace "haba mana mallam kasan dai mutum ɗaya zaiyi wannan aiki ba wai duk mutanen da suke a wajen nan ba koh? bare kuma kazo kana wa mutane kwakwazo, da son tarawa mutane jama'a cikin gida?, Kai ma kasan ba aikin kowa bane sai ta yar gaban goshin ka, dan haka ka juye a kanta ba wai waɗan da basu san hawa da sauka ba".
Wata muguwar kallo ya wurga mata wanda yake cike da takaici da ɓacin rai mai tsanani, ba mama da yake watsa wa kallon ba har su Umma duk sun sha jinin jikin su suka tsime waje ɗaya, sanin kansu ne kwaruru ba sa'an wake bane, banda ALLAH yasa gwiwa ta faɗi ƙas wanwar da wane mutum naji mutuwa, Inda a lokacin da yake amsa sunan sa ne, da wata magana ake ba wannan ba, a fagen rashin mutunci baya ya basa ba gaba bah, duk wani nau'ikan rashin mutunci da suke fama dashi a ƙarƙashin ƙafar sa suke, dan kuwa kam sai sun jira sa.
"Nace uban waye ta hal ban? Wan nan itace ta ƙarshe ba zan kuma magana ba, amma zan yanke hukunci ga wanda yayi bai faɗa ba, dan nasan ko wace, walau yayi ma mutum daɗi ko akasin haka". Ya faɗa a tsawace har jijiyoyin wuyansa suna tashi.
Binsu da kallo ya shiga yi kafin ya gyada kai yana ƙara tabbatar da cewa eh kam lailai ya cika ɗan iska haihuwar ƙasar gada, yo to inba ɗan iska ba waye zai ta ɓaɓatu a rasa mai tanka mai? Nan da nan ransa ya ƙara ɓaci, fiye da wanda ya shigo dashi gidan, Fiye da wanda suka ƙara masa.
"wa.." da sauri umma ta katse shi dan tasan shi tasan halin shi sai dai ma su ba wasu labari, dan ba mutunci ne dashi ba, yanzu yana iya mata duk abinda ya ga dama gaban kishiyoyi, "kayi haƙuri mallam nice! hakan ta faru cikin rashin...
"Isassa, shafaffa da mai, hamshaƙiya, wallahi ALLAH ni nasani, tunani na bai tafi a banza ba dan nasan kaf gidan nan kece zaki aikata min haka, san nan tsabaragen rainin da kikayi min ina tambaya sai kallo na kike da fiƙiƙin idanun ki Kamar kinga mahaukaci sabon kamu"
Nifa ba da gangan na jefe ka ba, bare ka taso ni gaba da maganganu kamar wacce ta burma maka wuƙa a ciki, alhalin ɗan bokiti ne fah ya same ka a ka, naga kuma bai kumbura ko zub da jini bah! Ka daiyi haƙuri Mallam ba kai nayi niyyan halba ba sai matar ka zuhura, amma Wallahi ko yanzu ɗin ma ba sha tayi ba, ALLAH sai nayi abinda nayi niyya".
Nan fa ta shammaci kowa ta wurga wa Inna lariya, cikin Sa'a kuwa ya sauka kan goshin ta, dake lariyar ƙarfe ce Kuma ta ɗan ɓalle hakan ya bada daman kartan mama a goshi kaɗan.
"Kan bala'in nan......har ni zaki zubda wa jini? Lailai Rashida kin ɗebo abinda yafi ƙarfin ki, ya kuma fi ƙarfin dangin ki". Tana kaiwa nan tahau dube duben abinda zata maida raddi itama.
"Ke awaaa....? Tsaf umma ta haɗiye Maganar da tayi niyyar furtawa, sakamakon ganin mama ta dunfaro ta wuƙa kai tsaye.
tabbass ta tsure jinin jikin ta duk sun dawo kan kumba, sai dai gefe na zuciyar ta tana gaya mata kar ta gudu, idan ta gudu ai sai mama taga lagwan ta.
Ƙara gyara tsaiwa tayi tana jiran tazo ɗin taga iya gudun ruwan ta. Saidai kafin mama ta ƙaraso gare ta Samha da Hanifah sun riƙe ta kam wanda hakan yaja mata dakatawar dole.
"Ku sake Ni, wallahi ni ko ita cikin gidan nan, har ni zata zubda wa jini?"
"Ke Hanifah ku sake ta! Ke kuma idan kin fasa chaka mata wukar baki haihu ba, na bar muku fili, ku cigaba amma a bakin auren ku, ni Muhammad na gama magana".
Shiru ya mamaye ilahirin gidan kaman anyi ruwa an ɗauke, wanda har Abba ya bar wajen basu samun zarafin cewa uffan bah.
Shi kuwa yana gama faɗin haka ya bar su nan tsaye ba tare da ya dube ko wanne su ba.
ɗaukar buta yayi ya nufi hanyar makewayi. Anan ya lura da ita, daman duk ɗinsu bai jituwa da ita dan bata bashi abinda yake so, wato kuɗi!, shikuma mutum ne da idan kana bashi to fah zakuyi mutumci rana ɗaya ka tsallake bakai haka ba, shikenan ka shiga sahun waɗan da basu da amfani, shi yasa yaran duk basa basa wani girma, duk kuwa da cewa shi ya haife su. bayan su suna da yayu guda uku da suke a gidan ma'auri "sannu da zuwa Abba! Ina yini?" Ta miƙa masa gaisuwa cikin girmamawa,. ko kallo bata ishe shi ba, Ya shige banɗaki, sai da ya fito san nan ya dube ta yace "gwara ki chanza mugun halin nan naki ki waye ki zama kamar sauran ƴan uwanki,ba wai ki zauna kina jiran sai an miki ba! bani zaki taimaka ba sai kanki, shawara nike baki dan ki amfani kanki da ɗan ki" yana ƙare faɗin haka ya bar wajen.
Har Abba yayi alwalla yazo zai fita a gidan Basu samu zarafin cewa komai ba, dan maganar da yayi ya zame masu kamar gubar da ke ƙona jinin jikin ya hana Mutum moruwa haka suka kasance a tsai a nan kaman wasu mutum mutumi.
"masifar da kuke nima ya tsaya kanku! idan ku ka jiwa juna ciwo biyar na baza tayi kuka ba, idan kun so ku kashe kanku". Cewar Abba da ke shirin fita daga gidan.
Ganin fitar sa yasa duk suka watsar da makaman yaƙin su Kamar basu ne suka so tada wata babbar husuma a cikin gidan ba.
Sai dai ba'a hana ɗan sabo da abu, nan fa suka koma kan wannan matashiyar dake a ƙarshen gidan dan duk maganar da Abba ya yaɓa mata a kunnin su, nan fa suka shiga sukar ta da aibanta mata yaro, Kamar sun manta da ƙaddara tana kan kowa.
bata ɗago ba bare ta nuna tasan sunayi, sai cigaba da kaɗa miya da tayi. Wannan halin nata na nuna rashin damuwa na ɓaƙanta musu zuciya, shi yasa basu cika bi ta kanta ba sai ta yaron ta wanda gaba ɗaya bata ragi, tanan ne kuma mutum zai gane tana da baki da tsiwa. Sai dai duk da irin soyayyar da take wa Maher hakan bai hana ta tsayu tsayin daka wajen ba shi ingantacciyar tarbiyya da uwa ta gari take baiwa yaranta ba.
"Su inna an daiyi sallah, san nan dan Allah ku barta ta huta, ai ba kanta farau ba kuma ba ƙarau ba! ƙaddara ai tana kan kowa Haba mana" cewar Samha, ɗaya daga cikin yan matan nan uku.
Doguwar tsuka umma taja haɗi da faɗin "Kece bakin ta, ita bata iya magana ba ne? Toh ahir ɗinki! Kar ki kuma ana mata magana kina sa baki,nasha kwaɓan ki bakya ji! Amma..." Ta ƙare maganar da jijjiga kai.
"Sa'a ki ka ci bakya a kusa dani da na buge maki baki gobe baza ki kuma ana ma wata magana ki saka baki bah" Cewar Mama..........✍🏻
Toh jama'a wannan karan ina muka kawo kan mu ne haka?🤔
***
Shere fisabilillah
*** 🗻INUWAR DUTSE....🗻
_Rabi'a wakili_
Ep 02
Bismillahi Rahmanir Rahim.
★...
♡♡♡ ♡♡♡
__________
ꨄꨄꨄ
"O'o'o a gaiyar wa zaki taɓa min ƴa? tab da anyi tashin tashina a gidan nan! Bar ganin Mallam ya wani kafa doka Wallahi take shi zanyi, sai mi toh tunda nasan ba Ni ɗaya zan fita bah, bana kuma so ina wa yarinya ta magana wasu na saka baki, dan ku ɗin ma ba so kuke ba, dan haka kowa yaji da lalurar da ta dame shi banda shishigi, bama ka gama da taka matsalar ba kana shiga wani, ɗan daurawa kai abinda Allah bai ɗaura muku ba?".
"ALLAH sarki! ALLAH ya baki haƙuri, Daman daga ƙin gaskiya sai ɓata, ALLAH ya kyauta" ta ƙare maganar da miƙewa ta ɗauki buta dan alwalla. Sai ya rage da umma sai mama da suke ta antaya wa junan su kallon tsana. sauran yaran kam duk sun shige ciki. Ganin haka yasa suma ɗaura alwalla suka shige inda aka bar wannan matashiyar a wajen. Ganin duk sun bar wajen yasa ta sauke ajiyar zuciya ta ɗaura alwalla ta shiga wani ɗaƙi daban, kyakkyawa ce ajin ƙarshe fara fet masha ALLAH, tana da ƙira mai kyau da jan hankali.
Tana idar da salla ta fito dan cigaba da aikin da take daman bata gama ba. Shimfiɗa tabarmu tayi a tsakar gidan da yasha siminti ga yasha shara, ɗauko tuwo da miya tayi ta aje su anan. Shima na Abba ta aza masa bisa tabarmar da yake nashi. Har zuwa lokacin cikin su Umma babu wanda ya leƙo.
Komawa chan ƙarshen gidan tayi kusa da madafa ta zauna, tana ɗan danna wayarta da ta kasance yar shafa, sai dai ƙarama ce.
"Aysha!?" Matashiyar da take zaune ta ɗago cikin nutsuwar data riga tabi mata jiki da jini a hankali, haɗi da watsa mata manyan fararen dara daran idanun ta da suka kasance kamar mai mai suna walƙi. Ɗauke kai tayi ta maida ga abinda take. Cikin rashin damuwa yusrah ta furta "idan su umma sun fito kice musu na fita sauri nike bazan tsaya shiga wajen su ba" ɗagowa tayi ta duɓe ta a karo na biyu wanda sai yanzu ta shiga binta da kallo, sauke ajiyar zuciya tayi ganin kayan da suke jikin ta da ɗan sauƙi akan waɗan da ita karan kanta ke sawa a baya. Cikin sanyin murya ta furta "idan kinje karki daɗe, a matsayin ki na ƴa mace bai kamaci a ce kina waje a wannan lokacin ba, ki kula".
bata ko gama rufe baki ba umma ta chaɓe da faɗin "Allahu Akbar inji mai kiran sallah, iyeeee tubabba kewa wata wa'azi! Ikon Allah! Wai kin manta lokacin da kikayi naki ne, uban wa ya sani? Inace sai randa sakamako ya baiyana? Dan haka ki ƙyaleta ta sakata ta wala a gidansu, tana kuma tare da addu'ar uwa, dan ni ba irin uwarki bace da ta yasar dake ta gudu ta bar mana ke ciwon ba, bugu da ƙari in Sha Allah ƴata gata nan, gani nan bari nan kazan mayu, baza ta aikata irin naki ba". umma ta ƙare maganar cikin fusata.
inna da ta fito dan taji abinda ke faruwa ta furta "sakamako kuwa da guzirin ɗan gaba da fatiha!!! dan an buga an buga an rasa yadda za'ayi da shi, shi yasa ya wanzu a yanzu yake rayuwa, idan ba dan haka ba baza mu san anyi ba" .
Da sauri ta rintse idanun ta da lokaci ɗaya suka kaɗa sukai jawur dan jin furucin inna, ji tayi har tsakar kanta kaman an kwaɗa mata guduma, danne zuciya tayi kawai ta miƙe tsaye ta nufi hanyar ɗakin da take rayuwa da yaronta, tasan zaman ta a wajen zasu tunzira ta