Share this page
2 / 6
ne ta yi abinda ba daidai ba, da hakan ya faru gwara ta bar musu wajen. har ta kai ƙofa taji inna tana cigaba da faɗin "zamani ya chanza, budurwa zata aje yaro wanda ba'a san tushen sa ba, dan rashin ta ido idan akayi magana tace ta fusata akan ɗan...." "yaro na ba shege bane" tana faɗin haka ta shige abinta tana jin zuciyar ta na tafarfasa bata juran a dinga aibanta mata Maheer a kunnin ta. A ƙule da son ƙara ƙular da Aysha tace "Kin wa uwaki,bani ba, toh idan ba shegen bane, ki fito da uban shi mana..." Nan suka ci gaba da maganganun su na zagar mata yaro wanda duk mi suke faɗi kaf a kunnen tah, daga karshe ma earpiece ta maƙala a kunnen ta inda ta kure ƙara tana sauraran kira'a. A chan waje kuwa kallon tsaf Yusrah tabi su da shi kafin ta nufi kofa da niyar barin gidan, har ta kama labule ta tsinkayi muryan mahaifiyar ta tana faɗin "ke yanzu duk rashin mutumci da yarinyan nan tayi mana baza kice komai bah sai dai ma kisa kai zaki fita?" Juyowa tayi a hankali kamar wacce wuyar ta ke mata ciwo cikin cika ta furta "bani da ta cewa sai dai duk mi ya faru ku kuka fara, dan haka nayi nan" Tana gama faɗin haka ta fita daga gidan ba tare da jiran jin amsar umma bah. Kafin dayan su ta kai ga cewa komoi sai ga Hanifah ta fito tana wani tashin kamshi wanda har shiga kai yake, ta haɗe cikin wata material fitted. Sai wani ya mutsa fuska take, yarinyar inna kenan cikin halin mahaifiyarta ba abinda ta manta bata ɗauka ba, har taso ta fita a wasu wajajen daman ance Magaji mafiyi. Ba tare da ta dubi ko wanne daga cikin iyayen su ba ta sai kai ta bar gidan ko mahaifiyarta bata sallama ba, a yadda ta nuna kamar bata san da wanzuwar su wajen ba, suma ɗin cikin rashin damuwa suka ɗauke kai. Bangaren Aysha kuwa tunda ta saka earpiece bata yarda ta cire bah sai chan da ta daidaici lokacin shigowar Abba ta cire abin kunnin dan tasan yana shigowa ita zai hau kwalawa kira. Ilai kuwa ba'a ɗauki mintuna biyu ba sai ga tashin muryan Abba yana kwala kiran Aysha ba ƙauƙautawa. Cikin nutsuwar da ta bi mata jiki ta miƙe a hankali ta fita. Zaune suke tsakar gida suna cin abinci iya iyayen kawai sai Abba. Duƙe takai gaban shi haɗi da faɗin " sannu da dawowa Abba, gani". Sai da ya gama bin ta da kallon tsaf yace "dan rainin da ya shiga tsakanin mu kina ji ina kiran ki kikai min banza dan tsabaragen samun waje! Toh nagaji da halin nan taki da ba'a cin miriyarki sai dai ke kici, na gaji dan na lura baƙin cikin taimaka min da zaki yi ki keyi, dan haka nima nan gaba kamar yadda kike datse idanun ki kike baɗe su da toka, nima haka zan koma, in har bakin cikin zaki ci gaba da min, kin san Allah sai kin dinga biyan haya na ɗakin da kike zaune da ɗanki, kamar yadda baki tausaya min ba nima haka, ganan sauran ƴan uwanki duk sun fita nema dan su taimaka min amma keeee ɗin nan hayya ban dai ce komai ba, amma kuɗin haya kam zaki fara biyan shi inhar baki chanza hali ba Allah kuwa" da sauri ta ɗago da kai ta dube shi jin abinda yake faɗi, nan take ta saki wata uwar murmushi wacce ta tsaya iya labban ta. Sai dai bata ce komai ba, sai shi ne ya buƙaci da ta tashi ta wuce. Tun kafin ta gama barin wajen mama tace "Allah yasa ba asarar yawun bakin ka kayi ba Mallam, amma sai naga yadda ta natsu kamar zata ɗauka maganar ka, barin ma taji ance zata fara biyan haya" Inna dake gefe tace "Aikin kawai, sai ku dinga abu kamar baku san wace ita da taurin kan tsiya ba! Ai baza ta yi bane in da dai dan kanta tayi niyya toh ba makawa ko da kuwa zamuyi gunduwagunduwa da sassan jikin ta ne sai tayi......." Muƙut ta haɗe abinda yayi saura bata furta bah, dan ganin irin mugun kallon da Abba ke watsa mata. Sai da ya gama binta da mugun kallo yace. "Duk taurin kanta ai bata fi ƙarfi na ba! Anya ma ba kece ke hure mata kunni bah? Dan gaskiya na fara zargin ku, amma ku cigaba Allah ya kawo ranar da zan kama ku, da hannu dumu dumu a ciki". " Haba mana Mallam ba zai yiwu ka tara mu kai ta sakar mana magana tun ɗazun muna shanye wa ba fah, san nan a dai na daura mana laifin da ba mu mukayi ba, daga ƙarshe idan haka kake tunani haka din ne" Cewar mama. Karab kuwa inna ta chaɓe da faɗin "toh nima da baki na baza'a hana ni yin magana ba yauwa" ƙin tanka masu yayi dan idan ya biye su rikicin zai koma babba ne shi kuma bai shirya wa haka bah, cigaba da cin abincin sa yayi gefe kuma yana sauraron Radio. Koda Aysha ta koma ɗaki watsar da maganan Abba tayi dan tasan ba abu bane mai yiwa ba, sai dai ita ta karɓa daga gare su, sai dai bata fatan wan nan ranar dan Abba uba ne gare ta. Taɓe baki tayi ta samu gefen gado takai zaune. Ji tayi ɗakin gaba ɗaya yayi mata faɗi dan rabon da ta kwana ita ɗaya tun bayan haihuwar maher da tayi. Tare take rayuwa dashi a ɗaki har tsawon Shekaru huɗu da rabi, shi yasa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, hakan yasa baya yarda da kowa idan kacire Abba dake dawo masa da alawa, sai yaya Abdul. Haƙura tayi ta danne zuciyarta dan kuwa inda maher yake tamkar yana wajen ta ne. dan yana wajen babbar yayan su Anty Ramlah, ɗazun da tazo da rana ta wuce dashi duk kuwa da baiso ba. Ɗauke tunanin haka tayi ta samu waje ta kwanta abinta har bacci yayi nasarar kwasanta. Ihu da kukan yaron da ya karaɗe ilahirin gidan shi ya fiddo da mutanen da ke rayuwa a ciki, kuka yaron yake kamar wanda ake yanka namar jikin sa, a gigice Abba ya fito daga ɗakin shi jin kukan jikan shi da Allah ya daura masa son sa fiye da sauran jikokin nasa, bai jira jin komai ba ya hau sababi, "ai sai da nace kar a kai yaron nan ko ina amma sabida taurin kanta sai da ta ɗauka tun da su mutum bai isa dasu ba! Ai kaima gashi ka samu rabon ka an taso ka da daren nan" ya kare Maganar da kallon uncle Isma'il da ke tsaye riƙe da yaro a hannun sa wanda sai kuka yake, Cikin rashin damuwa Uncle Isma'il ya saki murmushi haɗi da gaisar da Abba. Abba bai amsa ba sai cewa da yayi "Bani shi nan" yayi maganar yana miƙa hannu, fir mahir ya ƙi yadda da ke akwai duhu baiga fuskar Abba ba yasa yaƙi, sai da Abba ya furta "haba aboki nine fah" jin muryan Abba daf dashi yasa ya faɗa jikin shi da sauri haɗi da sauke wata babbar ajiyar zuciya kamar wani babban mutum, Abba kuma bubbuga bayan sa ya shiga yi a hankali har kukan nasa ya lafa. Sai ɗan ajiyar zuciya da ya ke saukewa a hankali. LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* ALƘAWARIN SARAUTA Jidderh Galadima SARƘAR DUHU Oum Fadeel ALEENAH ALEEM Aid Walee INUWAR DUTSE Rabi'a wakili Duka hudu 1k Uku 800 Biyu 600 Daya 400 Via 9119359211 Moniepoint Rabi'at Sani Adamu Sai katura shedar biyanka anan👇 *** 🗻INUWAR DUTSE....🗻 _Rabi'a wakili_ Ep 03 Bismillahi Rahmanir Rahim. ★... ♡♡♡ ♡♡♡ _____________________ ꨄꨄꨄ Aysha da dake a ɗaki har bacci ya fara ɗaukar ta, kamar daga sama taji kukan maher, ba shiri ta miƙe zaune tunanin ko dan ta sa a rai ne shi yasa take jiyo kukan sa, sai dai ta tabbata ba mafarki bane jin har ta farka tana jin kukan sa, ga muryan su Abba da uncle Isma'il tana ji, har ta tashi zata fita sai kuma ta fasa, baza ta iya zuwa wajen su da sunan zata ɗauki maher ba, tana da kawaici sosai a kansa duk kuwa da irin son da take masa,fasawa tayi ta koma ta zauna, tana dai ta jin su har dai maher yayi shiru a san nan ne ta ji wucewar uncle Isma'il. Yana fita Abba ya ɗaura da faɗin, "toh sai ku wuce kuje ku kwanta koh?, banda bin kwaf mi na fitowa bayan uwar da ta haife shi ma tana ji amma taƙi fitowa sai ku yan niman suna". Babu wacce tace uffan ta koma ɗakin ta, ganin wucewar su yasa ya shiga kwala kiran Aysha kamar ba dare bah. Kafin ta fito, sai ga shigowar Hanifah ita da samha, a ɗage suka ɗaga masa hannu har zasu shige ciki a kausashe,?ya daka masu tsawa da ya haifar masu da tsayuwar dole, da matsanancin mamaki fiye da tunani sam basu yi tunanin haka daga gare sa ba, yaushe rabon da Abba ya ɗaga musu murya, yaushe rabon Abba ya yi musu haka a matsayin uba? Sun manta tun kafin sukai haka amma yau shi yake daka musu tsawa a matsayin muryan uba, ba su kaɗai bah har Aysha dake a baya sai da mamakin haka ya daskarar da ita. Jiki a sanyaye haɗi da tsoron da ya yi musu shigar ɗaya, suka juyo gare sa, sai dai abinda ya daure masu kai fuskar nan tashi na nan a sake ba wata damuwa, sauke ajiyar zuciya sukai ba su kaɗai ba har su umma da suke hange ta window, "icce kuka gani da zaku zo ku wuce sa?" Yayi maganar kamar yadda ya saba a kullum, "san nan nawa kuka samo?" Ba tare da sun amsa masa ba suka buɗe jaka zasu fiddo da abinda suka samo, nan kam murmushi mai faɗi da yalwa ya cika masa fuska, har ya tara hannu zai karɓa umma ta riga shi, ta amshe duka tana binsa da kallon banza da kallon mutum mara amfani. "Wlh Mallam bazan baka kudin nan ba, baka san ci da shan mu ba, sai dai mu mu nema mu baka? Toh ba zan bayar ba,?cefane za'a yi dashi idan Allah ya kaimu, kai ma ka amfana, amma ba zan baka ko biyar ba ka kaima gidan chacha da baka taɓa cin moriyar shi ba yauwa, ka dai jira idan ka samu kuɗin kanka sai kaje kai tayi ba dai da kuɗin yaran mu....." Hauren da ya kai mata shi ya katse ta ba shiri, ganin ya dumfaro ta a zafafe ysa ta wurga ɗakin ta, da Allah ya taimaka a buɗe ta barshi, tana shiga ta datse da key. Bubbuga ƙofar ya hau yi kamar zai ƙalle ƙofar saboda tsananin bugu. "Dan Allah Abba ka daina dare ne fa, Mutane zasu shaida halin da muke ciki fah" cewar Samha. a fusace Abba ya furta "idan sun sani sai me akwai abinda basu sani bane daga cikin Rayuwar gidan nan bane? tunda kun maida kanku yan terere" ya ƙare Maganar da buga kofar da ƙafa da ƙarfi, a dai dai nan maher da ke hannun sa ya tsaga ihu dan bugun ya firgita shi. ALLAH ya jarabce shi da son maher hakan yasa lokaci ɗaya ba shiri ya natsu ya hau buga bayan sa alamun lallashi. Har sai da yayi shiru san nan ya cigaba da buga kofar da zuba duk tijarar daya ga dama. Itama daga ciki tana maida masa da martani. "Dan Allah Abba kayi haƙuri ga wannan in Sha Allah idan Allah ya kaimu sai na cika maka sauran" nutsuwa kuwa yayi tsaf, hannu har rawa yake wajen karɓan kuɗin, bata jira cewar shi ba ta tara hannu zata amshi maher ya hana, ganin haka yasa ta shige ciki daman Hanifah ta dade da shige tun kafin su fara tijarar su. Da murna sosai Abba ya chusa kuɗaɗen a aljihun rigar sa haɗi da kwala kiran sunan Aysha. Da sauri tasa hannu ta ɗauke hawayen fuskarta na tausayin halin da suke ciki. Fitowa da ga inda take ta isa inda yake. Cikin sanyin murya kalau ta furta"Abba gani" "na ganki mana! Kin kuma kyauta, kin ma kanki, dan wulaƙanci kina jin yaron nan na kuka kuma kin san ke yake biɗa kin masa banza, dake baki damu dashi ba idan ma abin cutarwa ne sai dai ya cutar da shi kenan dan baki son sa? Kin san baki buƙatar shi mi yasa kika samo cikin sa?". Ita dai shiru bata ce komai ba, dan bata da abin faɗi, lamarin Abba ba'a iya masa, yanzu da ace ta fito sai ya shuka mata rashin mutumcin da kaf anguwar sai anji, gashi duk gudun da tayi bata tsira ba. Cigaba Abba yayi da faɗin "toh Ni Inason sa yafi min ke so dari da ƙari, dan baki da wani amfani gare ni". magana yake amma maher sai faman kiciniyar a sauke shi yake haɗi da ɗaɗɗaga hannayen sa a dole yaga mahaifiyar sa. Cikin takaici Abba ya dungure masa kai, ba tare da ya kuma cewa komai ba, ya dungurar mata da shi ya shige ɗakin sa. Yana jin sa a jikin Aysha ya lafe luff, haɗi da sauke ajiyar zuciya, shafa bayan sa tayi san nan ta shige ɗakin ta dashi. Tana shiga ta kwantar dashi bisa gado har ya bare baki zai fara mata kuka fuska ba wasa tace "Allah ya baka Sa'a kamun kuka sai na maida kai inda ka fito, tunda kai baka san kara ba, baka da yarda kamar wanda za'a je a siyar" dariya ya kyalkyace dashi dake yaron akwai sa da wayau sosai. Kwanciya tayi itama a gadon tana lakace masa pointed noise da y gada a wajen ta, dariya ya kuma yi gefen kumatun sa na dama suna loɓawa, faɗawa yayi jikin ta. Yana son cigaba dayi mata rigima, "kayi! Zan wurgar da kai ne a wajen ummo ta cinye ka" ɗif yayi babu wani jimawa bacci ya ɗauke sa daman Bacci yake ji barin ma gashi yasha kuka. Gyara masa kwanciya tayi ta shiga binsa da kallo, lokaci ɗaya tausayin yaron na ƙara shigarta a rai, da tsoro mai tsanani, tasan nan gaba idan ya girma zai tambaye ta ina baban sa, bata fatan wannan ranar, gudun haka kuwa, matsayi biyu a zata taka a rayuwar sa, wato ta zame masa uwa da uba. Shafa sumar kansa data kwanta yayi luf tayi a hankali kafin ta zuba masa ido, sak da sak yake kama da ita har hasken fata ba abinda ya baro nata da bai ɗauka ba, sauke ajiyar zuciya tayi haɗi da manna masa sumba a goshi tayi musu addu'ar bacci ta shafe masu jiki dashi. LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_ *KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA* ALƘAWARIN SARAUTA Jidderh Galadima SARƘAR DUHU Oum Fadeel ALEENAH ALEEM Aid Walee INUWAR DUTSE Rabi'a wakili ₦500 Via 9119359211 Moniepoint Rabi'at Sani Adamu Sai katura shedar biyanka anan👇 ***INUWAR DUTSE. Rabi'a wakili Epi 04 Bismillahi Rahmanir Rahim. ___________________ https://www.arewapen.com/book?id=69582540cab84f8707da2483 Washegari bayan ta kammala aikin da zatayi ta shirya maher cikin sabon uniform ɗinsa na makaranta, basket din sa da ta haɗa masa abin break ta ɗauka, san nan ta ɗauke shi suka nufi ɗakin iyayen. Duk ɗakin da suka shiga basa wani jimawa suke fitowa, su kuma iyayen ba wanda ke wa Maheer magana, shima Maheer ɗin bai nuna yasan da zaman su ba, duk da karamin yaro ne amma yana da halin fuskewa kamar wani babban, wanda yan gidan suke ganin halin Aysha ya kwasa. Dakin Abba ta shiga inda ta same sa zaune yana sauraren Radio, ganin Maher yasa ya washe baki sosai yana miƙa masa hannu, kafaɗa maher ya noƙe alamun baya zuwa. "Toh zo ga shi" yayi maganar yana nuna masa biscuit. Nan ɗin ma maƙe kafaɗa yayi wan nan karan har da daure fuska, "kai ka sani daman halin uwarka gata nan kake da, dan haka ku kuka sani, zaku ma ku kai shi idan kaya ne" ita dai bata ce komai ba sai gaisar dashi da tayi, jin ya amsa ba yabo ba fallasa yasa ta sallame sa suka fito bayan ya bawa maher biscuit. Bayan sun fito daga gidan tafiya ba mai tsayi ba ya kawo su titi, dake basu da wani nisa, ba jimawa ta samu abin hawa suka tafi makarantar su maher. A dai dai gate din makarantar mai napep din ya tsaya, bayan ta fito ta biyasa kuɗin sa, ta ɗauki maher da basket nasa suka nufi ciki, sai da suka gaisa da Baba mai gadi ta karasa. Makarantar kuɗi ce sai dai mai ɗan ƙalilan kuɗi irin namu na ƴaƴan mallam Shehu, suna daf da shiga kofar class din Maher ya juyo ta yadda zai ga fuskarta da kyau, cikin muryan sa ta yara ya furta "Mamy!?" Ya faɗa haɗi da langwabar da kai. haɗe fuska tayi waje ɗaya dan kar ya kawo mata wargi kafin tace "ya akayi ne chuchu narh?" ɗan jim yayi sannan yace "Mamy, ba zanje school gobe b..." Hararan da ta zuba masa da manyan idanun ta shi ya katse shi yayi shiru da bakin sa "da mi akayi zaka ce baza ka school gobe ba? Ko kana da abinda zakai ne?" Tura dan ƙaramin bakin sa yayi kaɗan bai kuma cewa komai ba, wai shi nan yayi fushi. ba tace dashi komai ba har sai da suka kawo ajin sa san nan ta sauke shi haɗi da faɗin "wash Allah narh" tayi maganar tana kama hannun da ta ruƙo shi dashi, ganin haka yasa maher kyalkyacewa da dariya ganin yadda take da fuska, itama dan murmushi ta saki mai laushi, haɗi da zuba masa daradaran idanun ta masu kaifi, tana jin wata sabuwar soyayyar yaron da tausayin sa na ƙara shigarta, har bata san sanda kwalla cikar mata a ido ba, sai chan ta ankara, cikin fuskewa ta ɗauke su da hannu, haɗi sa furta "chuchu narh! Ba Mamy ka kake wa dariya bah?shikenan" kwaɓe fuska yayi lokaci ɗaya yace "na dai na" "yauwa! Toh muje na kai ka wajen zaman ka kar nayi latti" "Mamy zan biki". "In da ka aike ni zaka koh? Karatun kuma ka bar ma waye? Wuce muje! Kace kai baka da yarda ko kaɗan, gwara ka chanza tun wuri" shi dai maher shiru bai ce komai ba har ta kama hannun sa suka shiga class nasa, gaisawa da malamar sa tayi san nan ta miƙa shi har wajen zaman sa ta fito, wata napep ta samu ta koma gida, sai da ta ɗan taɓa bacci sannan ta tashi ta shirya dan zata ɗan fita. Ko bayan da ta gama shiri kulle kofar ta tayi tana jefa key cikin jaka. A ƙofa tayi kiciɓis da Yusrah, duban ta tayi tace "sai ina haka?" "Zani gidan Radio amma in Sha Allah ba jimawa zanyi bah" "yau kuma AY? Inace kin ce ba ki son wajen" "ba aiki zanyi ba, ya ta kira na ne wanda ni ban san kiran ta mi bace kinga kuma ai bai kamata naƙi zuwa bah! Na tafi" ta ƙare maganar tare da ficewa dan idan ta biye Yusrah sai su shekara a wajen. Napep ta samu ya kai ta har ƙofan gate na gidan rediyon bayan ta sallame shi ta shige ciki ba ta zarce ko ina ba sai cikin reception, dake an San da zuwan ta nan aka bata izinin shiga wajen Oga kai tsaye. Dai dai ƙofan ta danna door bell daga ciki dattijon mutuminya amsa da "shigo" jin muryan sa yasa ta tura ƙofar a hankali ta shiga ciki. Mutumin da ya ke zaune a kujera ya saki murmushi haɗi da faɗin "bara na tashi na biki kujerar ai kece Oga AY! Sannu da zuwa" ba wani sakewa a fuskar ta ta amsa ma sa da "ina yini sir" zuwa yanzu ya gama karantan ta tsaf sai hakan bai dame sa ba ya amsa da "lafiya qlau! Zauna mana" ya ƙare maganar yana nuna mata kujerar dake gayaye da table ɗin. Ba musu ta zauna haɗi da maida hankali a kan sa jin ya fara magana "kiyi haƙuri d taso ki da nayi, da kuma takura dan tabbas nasan na takura miki amma kiyi haƙuri" bai bata daman magana ba ya cigaba da cewa "kamar kullum dai yau ma da ƙoƙon bara nike tafe gare ki da ki karɓi tayin da mukayi miki na zama ɗaya daga cikin ma'aikatan wannan gidan rediyon, tabbas irin ku ake buƙata a waje duba da irin jajircewar ki" numfasawa yayi kafin ya cigaba da cewa "idan albashin ne bai yi ma ki ba sai ki yanke iya yadda ki ke so, ni kuma in Sha Allah zan duba na ga ni" ya ƙare maganar yana duban fuskar ta da addu'ar Allah yasa ta amince dan gidan rediyon sa yayi ƙasa, lokacin da Aysha take nan kuwa t taimaka sosai wajen saka gidan rediyon a jerin lissafi. Ba tare da dogon tunani ba tace "sir kayi haƙuri, in da kafin yanzu ne da na karɓa" haɗe fuska yayi tamau haɗi da faɗin "kamar ya kenan?" "Na samu wani aikin ne" sai da ya danne fushin sa sannan ya ce "shikenan bazan hana ki aikin ki ba! Am ma dan Allah ki duba ki gani" miƙewa tayi kan ƙafafun ta haɗi da faɗin "Nagode" ta fice daga office din zuwa waje zuciyar ta na ta ma ta saƙe saƙe Shi kuwa da cizon ɗan yatsa ta barshi, yasan ta akwai ta da taurin kai ba lailai ta karɓi tayin sa ba. Tana nan tsaye bakin titi tana jiran abin hawa har ta fidda rai da samu haka yasa ta yanke shawarar ta ɗan taka zuwa gaba ko Allah yasa ta samu. Tafiya ke yi cikin nutsuwar da ya bi mata jiki kamar bata son taka ƙasa. Wata baƙa wulik ɗin mota ta shararo a guje kamar zai tashi sama dan titin express ne. Har motan ta gitta ta sai ga motan

Chapter 2 of 6