Share this page
6 / 6
da kanta ke ƙasa tun bayan da ta sunkuyar bata ƙara ɗagowa ba, tana sauraren bugun zuciyar ta gefe kuwa tana jin nauyin kallon fuskar Anty moon. Da kyar ta ɗaure sai dai bata ɗago ba tana a Yadda take tace "Ina yini Anty?" Anty moon dake ta lura da ita ta saki murmushi da jinjina halin ta dan a ɗan Kasancewar nan tasu ta gane Aysha miskila ce. Watsar da tunanin komai tayi ta amsa da "Alhamdulillah! Ina Maheer?" Shiru bata amsa ba sai Anty Ramlah ce ta amsa da faɗin "ai wannan kanwa taki Kunya ke gare ta! Maheer kuma yana cikin babu Lafiya" "subhanallah! Mi ke damun sa" cewar Anty "ai tun jiya aka kwantar damu! Amma jikin yanzu Alhamdulillah yana ciki ma ai yana ta shan bacci" "ALLAH ya sawwake zamu iya shiga mu duba sa?" "Ikon ALLAH! Ai ku tafi kanku tsaye Wallahi an zama ɗaya ai, barin ma ai ita mahaifiyar tasa ta sanku, kuma kun santa don haka ku shiga kanku tsaye" Cewar Anne. "Toh mun gode Hajiya mama" cewar Anty Moon ita Kuwa Anne baki har kunne jin ance mata Hajiya. Duk kwasa sukai suka shiga ciki sai dai su Abba Basu shiga ba haka ma Aysha. "Kedai Aysha Allah ya yaye miki wannan hali taki! Kowa ya tashi dan ya duba jikin yaro amma banda ke! Allah ya kyauta ya yaye miki" cewar Abba. Bata ko ɗago ta kallesa ba dan abinda take ji yana mata yawo a ƙirji ya fi gaban wasa. Basu wani dade ba sai ga Anty da su fadeelah sun fito tare da Anty Ramlah da Anty Ameerah inda aka bar Anne kawaii a ɗakin. "Mun gode ALLAH ya bada lada ALLAH yayi albarka" cewar Abbu" Amin ya ALLAH mun gode Baba! Zamu karasa ciki in Sha Allah zamu dawo zuwa anjima" "madallah a gaisar da masu jiki muna nan shigowa dai in Sha Allah! Ramlah da Ameerah ku bita kuje ku dubo marar lafiyar tasu" amsawa sukai da toh, suka bi su Anty dan duba masu jiki. "Aysha wai ina kika samo waɗan nan mutanen ne? Anya ba kya ɓoye mana wani abu da ya kamata ace mun sani?" Cewar Abbu yana duban ta. Shiru babu amsa dan bata san amsar da zata basa ba.... "Dake nike magana fah Aysha! Ina kika San family Aliyu Bashir Sardauna?" Abbu ya kara wurga mata wata tambayar a karo na biyu. "Mi kake faɗa ne haka? Wani familyn Aliyu? Ba dai shahararren dan kasuwan nan bah?" Cewar Abba yana kallon Abbu da jiran karin haske. "Eh yaya familyn Aliyu Bashir Sardauna kenan" jin hakan yasa Abba samun waje ya zauna yana kallon Aysha Irin kallon tuhumar nan, rasa abin fade da yayi ne yasa ya tsuke bakin sa yayi shiru ba wai dan babu bane a'a sun yi masa nauyi. Sai chan yace "Ni tsoro kike bani Aysha! Ni kar Muna zaune watara ki sayar da mu dan kam ke din nan abin a kiyaye ne! Ka barta wannan mai mugun zurfin cikin ba fadi zatai ba, Idan kuma ka matsa ta tara maka mutane a nan yauwa" "shikenan yaya yadda kace din haka za'ayi idan mun koma gida sai a yi a chan". Haka dai suka tsaida magana suna a haka saiga su Anty Ramlah sun dawo sai dai wannan karan basu zauna a waje ba suka koma ciki, da yake dakin yana da fadi sosai, ga shi kuma Maheer ne kawai ke ɗakin wanda har zuwa sannan bacci yake ta faman sha. ********** Jikin Mommy yayi sauƙi sosai daman tsoro ne ya Shige ta. Dan har an basu sallama. Sai da suka gama kwasan komi nasu ne suka shiga dakin da Baffa yake da Maleeka da ke ta faman zunburo baki gaba. Sai dai jin kamshin tularen AY a ɗakin yasa ta natsu kamar wata na ALLAH ta shiga gaida modɗibo da yafendo d tambayar mai jiki. Banda ganin AY a wajen da baza ta gaisar da ko wasu mutane bah. Nan ta shiga satar kallon sa sai dai ganin fuskar nan tasa kadaran kadahan ya sa bata karasa gare sa bah. "Toh modɗibo ALLAH ya kara sauƙi bara mu lallaɓa mu koma gida sai in na dawo zuwa anjina" amsa masa modɗibo yayi, shi kuwa Daddy ya kama hannun Maleeka suka fice daga ɗakin. Intisar da fadeelah dake laɓe a wajen kuwa ganin tafiyar su Daddy ne yasa suka fito daga moɓuyar su suka nufi wajen Aysha. "Modɗibo ya maganar binciken da ake yi ya kamata zuwa yanzu ace an gano bakin zaren amma shiru ba wani labari" cewar Anty. "Haka na so amma gashi nan shi ya dakatar da binciken wanda ban san dalilin sa nayin haka ba" modɗibo yayi maganar yana nuna AY dake ta fama da waya. "Toh ALLAH yasa haka shi yafi alkhairi" "amin Ya ALLAH" suna cigaba da wata zancen jifa jifa yafendo tana saka masu baki. Suna a haka sai ga sallamar su Intisar bayansu kuma Aysha. "Ikon ALLAH yanzu Mommarh nah sai da kika taso bayan kin baro yaro babu lafiya?" Cikin sanyin murya ta amsa da "Anty Ramlah suna nan" Kafin ta zarce da gaishe su cikin karfin hali dan tunda ta shigo take Jin kaifaffun idanu a kanta daurewa kawai tayi, tayi abinda ya kawo ta. "Moon wace wannan ɗin kodai surukarki ce" a kusan tare AY da AY suka daga kai suna duban sa kafin kuma su ɗauke a tare AY yana maida nashi kan AY da ta shiga wasa da yatsun hannayen ta tana jin zuciyarta tana bugu. Motsa pink lips nasa yayi kaman wanda zai saki murmushi sai kuma ya gimtse kayar sa. Yana jiran jin amsar d Anty zata bada. "A'a fah! Ita ce mahaifiyar yaron da muka shiga dubawa Kafin mu shigo nan" murmushin manya modɗibo y saki, Idan ya dubi AY ya maida duban sa ga Aysha. Wanda hakan yaso ɗaure wa su yafendo kai. Sai chan da sauran murmushi kan fuskar sa yace "ALLAH ya raya Muhammad Maheer" a 360 Aysha ta ɗago gaba ɗayan ta tana duban modɗibo da tunanin inda ya san full name nasa. Wata kaukauran yawu ta haɗiye tana maida kanta ƙasa. Shi Kuwa AY a Wannan karan kasa ɓoye murmushin sa yayi yana cigaba da satar kallon ta, shi kuwa modɗibo na Nazarin sa. "ALLAH ya ƙara sauki" Aysha ta faɗa tana miƙewa da niyyar tafiya. Ganin haka sai yafendo da Anty dasu fadeelah suka tashi danyi mata rakiya daga nan yafendo ta duba jikin Maheer. "Ku zo nan" Cewar AY sai dai idanunsa yana kan wayar sa, ƙululu cikin su ya shiga halin ƙugi jiki a sanyaye suka dawo su Anty moon Kuma suka fice, sai ɗakin ya koma daga modɗibo sai Baffa dake bacci har zuwa lokacin sai su fadeelah da ya dakatar. Ba tare da ya dube su ba yace "kan ku yana mosti ko? Zan baku last warning kar ku ƙara fadawa mutum haka a jiki.... Live my site" jiki na rawa sosai suka fice daga ɗakin. Modɗibo kam murmushin manya ya saki kafin ya ce "waye suka danne halan dan in anga kayi magana To tabbass abin yana da matuƙar muhimmanci" manyan idanun sa ya zuba kan modɗibo kafin ya ɗauke yana tashi ya bar dakin gaba ɗaya "gulmamme ai zaka magantu ne" modɗibo ya faɗa da dariyar dauke a fuskar sa. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6