Share this page
3 / 6
tana yo wa baya a hankali, dai dai saitin ta ya ja ya tsaya, haɗi da buɗe ƙofar motan. Ko kafin ta gama buɗe motan Aysha da ta cika tayi fam, haɗi da jinjina rashin mutumci na mai motan, danne zuciya tayi ta ja ƙafar ta a hankali ta fara taku da niyan barin wajen b tare da ta waiga dan taga wane wannan ba. Kyakkyawan budurwa ce yar fara wacce baza ta wuci sa'ar su Aysha ba, fuskar ta ɗauke da kyakkyawar murmushi ta shiga taka wa Aysha baya, da yake ba wani sauri ta ke ba nan ta cimmata haɗi da faɗin "Sister?" Chak taja ta tsaya bata ƙara ko taku ba, haka da wannan matashiyar ta gani ne ya bata ikon taka wa zuwa gaban ta har sannan murmushi na fuskar ta. Kamar mai ciwon wuya ta daga kanta a hankali dan taga waye dan sam bata gano mai muryar ba. Idanun ta bai dira ko ina ba sai a fuskar wan nan matashiyar, kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kai ɗan sam bata waye ta ba, kai tana iya cewa ma bata san ta bah. Sai dai gudun kar tayi rashin mutumci yasa tace "sannu" wannan matashiyar kuwa kuwa ta amsa mata da "ina yini! Ya baby?" Babu shiri ta ɗago tana duban ta d mamakin jin maganar ta na ƙarshe. Wan nan matashiyar kuwa bata jira cewar Aysha ba ta cigaba da faɗin. "Na san ba lailai ki waye ni ba, amma idan nayi miki bayani kila ki tuna! Sunana Fadila, shekarun baya da suka wuce mun taɓa haɗuwa dake a Federal university of Adamawa! Sanadin baby naki da yike ta kuka ga shi lokacin kina da exams har an fara shiga hall, ganin kukan baby yayi yawa yasa kika fasa shiga kika juya da niyan barin wajen, sai dai security da ke wajen suka dakatar dake tare da tambayar ki exams ɗin fa? Ki ka ce kin fasa! Hakan yasa suka taimaka maki suka karɓi babyn suka kira ɗaya daga cikin student dake zaune a wajen wanda ba kowa bace face ni, suka ce na taimaka na taya ki rikon yaron zaki rubuta jarabawa, idan baki manta ba har ku ka gama kika fito inda kika same ni a nan wajen security ɗin" Eh tabbas ta tuna wan nan ranar sai dai fuskarta ne ya ɓata mata dan a ranar ma ba wai tayi mata kallon tsaf bane dan Maheer ya gama ruɗa ta. "Allah sarki! Sannu" cewar Aysha fuskar nan ba sakewa. "Alhamdulillah daman fata na ki gane ni, dan Allah Anty Muje na rage miki hanya" A karo na uku Aysha ta ɗago ta kalle ta jin ta ƙaƙaba mata sunan da bata san inda ta samo shi ba, dube ta babba da ita tana wani kiran ta da Anty. Kamar zata yi mata magana sai kuma ta fasa. "Dan Allah Anty kar ki ce a'a" Dan murmushi kawai tayi wanda sai ka dube ta da kyau za ka gane haka. "Nagode" Aysha ta furta haɗi da nufan wajen motan, ganin haka yasa Fadila take mata baya nan suka shiga suka bar wajen, tafiyar tasu ta kasance shiru, sai da Fadila ta katse shiru ta hanyar faɗin "Anty wai nikam ina baby na ya ke, yanzu dai nasan ya zama saurayi?" "Yana makaranta" "ma sha ALLAH! Nikam ban san sunan baby na bah" Allah ya gani zuwa yanzu duk ta fara gajiya da surutan nan nata am ma mutumin da ya riƙe maka ɗa da amana a bayan idanun ka ai babban masoyin ka ne. "Sunan sa Muhammad Maheer" "Wow ma sha ALLAH! ALLAH ya raya a kan sunnah" Da Amin Aysha ta amsa cikin zuciya ita Kuma Fadila ta zarce da bata labarin neman ta da tayi tsawon wannan lokacin. Aysha kam bata ce komai ba nata ji ne kawai. Cikin rashin damuwa Fadila ta cigaba da zuba mata surutu bata ko tsayawa. "Ya ALLAH na manta na tambaye ki in da muka nufa afwan pls" amsawa tayi da ba komai haɗi da faɗa mata pack zata. Suna isa, da murmushi ɗauke a fuskar Aysha tace"nagode sosai ALLAH ya saka da alkhairi" "haba dai ba komai wallahi". Balle murfin ƙofan Aysha tayi kafin ta gama fita Fadila ta riga ta. Ita dai duk tunanin ta daga nan Fadila wuce wa zata yi. Kaman tasan abinda Aysha take tunani tace "ta ya za'ayi na wuce bayan kuma nice na kawo ki? Ai wasa neh" Ba tare da ta tanka mata ba ta fiddo da wayarta ta latsa wata number bugu biyu aka daga. ba tare da jiran cewar sa ba ta furta "ina a first gate" Share fisabilillah *** 🗻INUWAR DUTSE....🗻 _Rabi'a wakili_ Ep 05 Bismillahi Rahmanir Rahim. _________________ INUWAR DUTSE.... _Rabi'a wakili_ Ep 05 Bismillahi Rahmanir Rahim. _________________ Da sauri tasa hannu ta toshe baki, kwarai ta gigita da jin bautun da suke, "mi yasa wasu mutanen basu da imani ne? Mi yasa wasu mutanen basa tsoron Allah?" Zuciyarta ta shiga yana yin tambaya. motsin da taji na alamar za'a fito, bata san sanda wani kuzari shigar ta ba, ta miƙe da sauri ta bar wajen bata ko kallon inda take jefa ƙafafu. Babu inda ta zarce sai bakin titi, abin hawa ta samu ta koma gida zuciyarta na lugujen daka, tayi zurfi sosai cikin tunanin da ta faɗa wanda tayi iya yinta na ganin ta yakice haka a zuciyar ta hakan bai samu bah. Wayarta da ya shiga ruri shi yayi nasarar dawo da ita duniyar mu ta mutane. Sauke numfashi mai kauri tayi kafin takai hannu ta ɗauki wayar da take daf da katse wa. Lokaci ɗaya ƙirjinta ya buga fiye da wanda yake dazu, zare manyan idanun ta masu girma tayi dan tabbatar da da wanda yake kira din. Eh kam idanun ta basu yi mata karya ba yaya Abdul ne, tana cikin sakawa da kwancewa wani kiran ƙara shigowa, sai da ta daidaita kanta sosai sannan ta dauka cikin nutsuwa. Kafin tace komi ya katse ta cikin karaji, duk da ta razana amma bata nuna haka ko a fuska bah, ta amsa masa da "toh" tana katse wayar tun kafin ya katse.tunani ta shiga yaushe ya dawo? Tunanin ta katsewa yayi jin napep ya tsaya, sauke numfashi tayi a hankali haɗi da fitowa bayan ta sallame sa. Jiki a sanyaye ta nufi layin su, nan da nan ta kawo gida daman basu da wani nisa da titi. Bakin ta dauke da sallama ta shiga cikin gidan inda ta tadda su Hanifah, Yusrah, Samha, suna aiki, su umma kuma na cikin ɗaki da alamu dai bacci suke. Dake duk ɗin su tafi shiri da Samha yasa ta dube ta murya chan ƙasa tace "lafiya kuwa yau naga gidan shiru?" "Dakin dake a farkon gidan Samha ta kalla kafin tace "yaya ne ya dawo fah, Kuma ya tambayi inda kike, toh Allah yasa lokacin Abba na nan yace kin tafi kai maher makaranta" . Boyayyiyar ajiyar zuciya ta boye da nufin barin wajen chak taja ta tsaya, haɗi da tattare fuska gu ɗaya. Sakamakon jin muryan Yusrah tana faɗin "sannu da fitowa yaya". Kyakkyawan matashin dake tsaye a ƙofa hannayen sa harɗe a ƙirji fuskan nan tamau ba wasa, ya furta "daga Ina kike?" Duk da ta ɗan razana amma ta ɓoye, duk bin ƙwaf na mutum ba zai gano halin da take ciki bah. A hankali ta juyo sai dai bata yarda ta dubi fuskar sa bah, murya chan ciki ta amsa masa da cewa "na kai maher school ne" ido kawai ya zuba mata yana son ya gano iya gaskiyar ta, kasa gano komai yayi ya ɗauke duban sa daga gare ta, yana wurga mata wata tambayar "daga nan kika nufi ina?" Sai da ta gama binsa da kallon kasan ido sannan ta amsa masa da cewa "babu ko ina an dai samu matsalar go-slow ne" Ta kare maganar a gundire. Ba tare da ya kara bi ta kanta ba ya wuce abinsa daman fita zaiyi. ganin fitar sa yasa duk suka sauke ajiyar zuciya idan ka cire Aysha da tayi kaman abin bai dame ta ba nan kuwa kam, Allah kadai yasan fargaban da ta shiga, ta san sa ba mutum bane mai wasa, yanzu sai yace zai yi musu duka karamin aikin sa kenan, shi yasa kaf cikin yayun su sunfi tsoron sa da shi da Anty Ramlah. Sai dai nashi yafi tasiri cikin zuciyar su. Sai da suka tabbatar yayi nisa da gidan suka hau gulman sa, Aysha kuwa saɗaf saɗaf ta shige ɗakin ta dan abinda ya dame ta ya dame ta. Zubewa tayi bisa gado, ta shiga aikin sakawa da kwancewa akan batun da taji na waɗan nan mutanen, ta ɗauki tsawon lokaci sosai a haka ganin zata ɓatawa kanta lokaci yasa ta yi yaƙin yakice haka a zuciyar ta shima da ƙyar. Tana kwance anan bacci yayi awon gaba da ita. Chan tsakar gida kam su Yusrah har sun kammala aikin da suke daman ba wani aiki bane mai yawa, hakan yasa gidan yayi tsit ya natsu kamar ba mutane, sai yay kamar ba gidan da ake kwasan yan kallo cikin ta bah. Duk sanadin dawowan yaya Abdul dan har iyayen nasu shakka shakkan sa suke duk bala'i basa yi idan yana gari. Tun daga zaure Goggo take ta doka sallama ba ji ba gani kamar wacce zata tashi gidan. Sallaman nata shi ya fiddo dasu umma wanda daman duk sun daɗe da tashi kawai dai fitowar ne basu yi bah. Ba wani sakin fuska suka amsa mata sallaman bayan ta shigo shima ciki ciki wanda ba lailai bane ace taji bah. Tana shiga safna bin bayanta, sai Abbu. Basu kai ga yi masu sannu da zuwa bah sai ga Anne ta danno kai, sai wani yatsine fuska take haɗi da bin ko wacce da kallon uku sauran kwata. Ganin ta da rana tsakar nan ya basu mamaki, ba wanda yasan da dawowarta a nan kusa ma bare ace wai gata gaban su a yanzu din. Nan take kuwa duk suka sha jinin jikin su suna kuma tattare fuska waje ɗaya. Kafin su dawo dai-dai daga bazata da suka faɗa suka tsinkayi muryan Anne cikin ƙwaƙwazo "tunda nikam bani da darajar da zakuyi min sannu da zuwa ni ina yi muku sannu! Allah yasa ya faranta muku ko akasin haka zama daram dam dam eheee, sai dai duk wacce taga baza ta zauna dani bah ga ƙofa nan a hankaɗe ta fita ba takura" ɗan jim tayi haɗi da binsu da kallo kafin ta cigaba da faɗin "watam an zata a chan zan dauwama har kun mimiƙe kafafu kuna ta shan sha'anin ku! An mance da sabgata daman na san ba son zama na kuke ba, toh ba kuma yadda zakuyi dani, gani nan bari yauwa" ta ƙare maganar da turo ɗankwali gaban goshi. Shiru gidan ya ɗauka kamar anyi ruwa an ɗauke babu wacce tace mata komai dan sun san duk hayaƙin kai ta fisu. tun da yafendo ta fara magana maman safna (Goggo) take ta gwaɗa kai da yatsine fuska, jin ta kai aya tai saurin chaɓewa da. "A toh Anne naga kaman ba dawowar ki ne kawai ba'a so bah har da tamu! Yo harda mu mana duk sallmar da mukai ta dokawa babu wanda ya amsa bare muci arzikin ai mana sannu da zuwa, Allah na tuba ba haka aka so ba! Kai jama'a....." "Suwaiba!"Abbu yai kiran sunan maman safna (goggo) a dake ba wasa, wanda tun sanda ta fara magana yake ta wurga mata wani mugun kallo amma inaaaa bata san yanayi ba, tayi nisa bata jin kira burin ta dai ta guma masu gumamma. Maƙut ta haɗe sauran tijarar da tayi niyyar direwa, Abbu ba abokin wargin ta bane baya ɗaukan irin abubuwan mutanen gidan. "Wuce ciki" Abbu ya furta hakan ba tare da ya kuma kallon maman safna bah. Ai kafin ya rufe baki sum sum ta shige ciki tana jin zuciyar na mata tuƙuƙin takaici. "Dan Allah kiyi haƙuri Anne! ki samu ki huta kinga ma ga tafiyar da muka shawo, idan kin huta sai a zauna ayi magana". Dan kallon shi tayi kamar zata ce wani abin kuma ta fasa itama din dai hanyar ɗakin ta ta nufa tana jin babu daɗi, itafa ba iya haka taso abin ya tsaya ba! Toh taya za'a yi ba zai tsaya a haka bah tunda ba Abba bane daman shine bai gani ya ƙyale barin ma yaji ance da yafendo ake koda kuwa itace bata da gaskiya bayanta zai bi suyi ta raba abin faɗe a anguwa, shi kuma Abbu sanyi hali yike da,sam ba'a jin muryansa cikin hayaniyar gidan. Ganin ta shige shima ya nufi hanyar ɗakin sa, har ya shige ya barsu umma tsaye nan, sai daga baya ko wacce ta shige ciki. Ɓangaren yan matan gidan kuwa duk suna jin diramar da akayi, fitowa ne kurum basu yi ba amma dai sun leƙa ta taga. Safna kam ƙin bin goggo tayi ta zarce ɗakin da yake mallakin Aysha a yanzu, tura ƙofan tayi cikin Sa'a ƙofar ta buɗe tasa kai ciki, ganin ta tayi kwance bisa gado tana bacci. Gaɗa kai tayi haɗi da faɗin "oooh ni safna! Amma toh bara dai na tausaya miki kiyi baccin ba dan halin ki bah" ta ƙare maganar da ɗaukar frame dake ɗauke da hoton maheer akai wanda yake kaman a zahiri kyakkyawan fuskar sa ɗauke da murmushi. kai hannu tayi a hankali ta shafa fuskar maheer dake cikin frame haɗi da sake murmushi. Firgigit ta ɗago a tsorace murmushin dake kan fuskarta suna disashewa, gefe zuciyar ta na lugujen daka,waigawa baya tayi dan ganin wanda ya kwace hoton daga hannun tah, dan tasan tabbas Aysha bacci take.INUWAR DUTSE. Rabi'a wakili Ep 06 Writer's connect pens Bismillahi Rahmanir Rahim. _______________ juyowa tayi ta kalli Safna kamar wacce akayi wa dole ta furta "yaushe a gari". "Allah ya shirya min ke AY! Ba wani jimawa, dawowar mu kenan na wuto nan! Sai dai fah da babban baƙuwa muke tafe, watam Anne" da sauri Aysha ta zaro manyan fararen idanun ta har bata san sanda bakin ta ya furta "tabbb". "Ke dai bari ai dazun ma kaɗan ya rage ba'ayi ba, ALLAH dai ya taimaka Abbu yana nan shi ya hana ya lallaɓa ta amma duk da haka akwai zama na sani". taɓe baki Aysha tayi kawai, cikin zuciyar ta tana jinjina fitinar kakan tasu, gefe guda na zuciyar ta na shiga fargaba. Tashi safna tayi ba tare da jiran cewar Aysha ba ta nufi mirror ta gyara fuskar haɗi da yin rolling gyalen da ke kanta ta nufi hanyar fita. Duk abinda take da ido kawai Aysha ke binta har ta isa ƙofa. "AY bara naje na ɗauko Maher nasan lokacin tashin su yayi" "yaya Abdul na nan kin san zai ɗauko shi" Aysha ta furta cikin sanyin murya. Kamar ƙyaftawan ido sai ga safna gaban Aysha murya har zuga yake wajen faɗin "wani yaya Abdul ɗin! Yaushe ya kuma dawo?" Ta jefa wa Aysha tambayar a haɗe. Kaɗan ya rage dariya bai kufce mata ba ganin yadda safna duk ta ruɗe lokaci ɗaya, amma ta gimtse kayanta dan bata cikin yanayin tace "shima yau ɗin ya dawo". Sai da safna ta gama yi mata kallon tsaf sannan tace. "Amma ke muguwa ce AY shine baki gaya min bah kika barni na taho? Ba komai nasan zama na dake yar rainin wayau kawai" "Tunda daman kin gaya min kina hanyar tasowa yau ai dole" "Naji ban kira na gaya miki ba amma ke mi zai hana ki kira ki gaya Min?" Sai da Aysha ta mula dan kanta Sannan ta furta "abinda ya riƙe ki". Har safna ta buɗe baki zata yi magana sai ga sallmar yaya Abdul, tsaf ta haɗiye maganar ta ta chanza akalar maganar zuwa amsa masa, tashi tayi ta fita zuwa ƙofa, cikin girmamawa ta gaisar da shi cikin kamewan sa ya amsa mata haɗi da miƙa mata maheer da yake ta faman binta da kallo kaman bai santa ko gane ta bah. Tana karɓan sa ta juya ciki dan bata so ko inuwa su haɗa. "Idan ka gama gaisawa da kanwar ubanka kazo Inason ganin ka, shanyayye kawai" cewar Goggo dake tsaye daga ƙofa haɗi da watsa masa mugun kallo. Sauke kai ƙasa yayi haɗi da shafo kansa zuwa ƙeya kafin ya nufi ɗakin mahaifiyar tasu, zaune ya tadda ta tana kaɗa ƙafa da gani ƙiris take jira ta watso da abinda ke zuciyar ta. Nisa kaɗan da ita ya kai zaune "sannu da dawowa Goggo! Ya hanya? Na ma shigo ɗazun na tadda kina sallah, sai na koma da niyyar idan kin idar na dawo". Tun da yaya Abdul ya fara magana ta shiga binsa da mugun kallo kaman idanun ta zasu zube ƙas. Sai da ta ɗauki tsawon mintina kafin tace "kaga ba wannan na tambaye ka bah! Shin ban hanaka shiga safgar wanchan yarinyar da ita da shegen ɗanta bah? Toh uban mi ya kai ka harda jigilar ɗauko yaro daga makaran...." Rintse ido yayi da ƙarfi yana haɗiye abinda yayi masa tsaye a maƙoshi. Har ga Allah baya son yaji ana shegenta maheer ji yake har cikin makwallaton zuciyarsa ba zai jure sauraran sautin muryan mahaifiyarsa na shegen ta maheer bah yasa cikin nutsuwar da ya tattaro ya katse ta ta hanyar faɗin "Goggo dan Allah kiyi haƙuri tabbass nasan nayi kuskure zan kiyaye, amma dai Goggo itama kanwa take gare ni kaman yadda safna dasu Hanifah suke.... Ƙatuwar hararan da Goggo ta sakar masa shi ya tilas ta masa yin shiru ba tare da ya kai aya bah. "Sannu uba na, ai tuna min zakayi tunda ni na manta". ta faɗa a zafafe duk da ƙoƙarin dannewar da take. "A'a Goggo ba haka bane kawai dai gani nayi itama nauyi nane tunda itama ƙanwa ce gare ni Kuma sai naga...." Sai kuma yai shiru ya kasa ƙara sawa dan ba lailai ta fahimce sa bah. "Ina jinka uba na ya kayi shiru, kai ƙarshen maganar taka mana" "Wai daman am daman sai naga idan akayi haka kaman an nuna banbanci ne tsakanin su bayan du....." "Eh kam wuyan ka ya isa yanka! yo ta isa yanka mana tunda gashi ka zaunar dani kana gaya min magana uhm?" Shi dai shiru bai ce komai bah. Jin shirun nasa yasa ta cigaba da faɗan, inda take shiga ba tanan take fita bah, sai da tayi ma'ishi sannan ta haƙura haɗi da faɗin "tashi ka bacewa gani na". Har zuwa lokacin yaya Abdul bai ce bah, sai sanda yake ƙoƙarin tashi ya ƙara bata haƙuri sannan ya fito. Jin motsin fitowar sa yasa umma saurin matsawa daga jikin ƙofan Goggo, sai dai da kaga yanayin ta farat ɗaya zaka ga alamun rashin gaskiya tattare da ita duba da yadda ta shiga kame kame. Ɗauke kai yaya Abdul yayi kaman bai ranfo ta bah ya gaishe ta, tun kafin ya dire tai karaf ta amshe da "lafiya qlau ya gajiyar hanyar, ɗazun aka ce ka shigo sai da na farka Hanifah ke faɗa min". "Eh anyi haka, fatan na same ku lafiya?" "Alhamdulillah Wallahi sai ɗan abinda ba'a rasawa na yau da kullum". "Ehem ehem ehem!" Gyaran Muryar da Goggo tayi daga ƙofan ta shi ya sa suka waiga baki ɗaya suna duban ta. "Ba fita zakayi bane yayan su?". Cewar Goggo, tana binsa da kallo. "Eh Goggo! Na tafi" "Shikenan a dawo lafiya" amsawa yayi da Amin Ya fice, umma dake tsaye wajen taɓe baki tayi a fakaice kafin itama ta shige nata ganin Goggo ma ta shige. Mama dake hangar su ta window kwashewa tayi da dariya haɗi da faɗin "shishigin banza dana hofi! Kaɗan kika gani indai munafuncin da zakiyi kenan Rashida, hmmm mtswww" ta ƙare maganar da jan doguwar tsuka, har takai zaune tai zumbur ta miƙe kamar wacce ta tuna wani abu, da sauri har tana shirin kai wa ƙasa amma bata damuba burin ta dai ta isa inda take son zuwa. Kamar ƙyaftawan ido sai ga mama gaban ɗakin Goggo kamar wacce bata son aji muryan ta chan ƙasa ta shiga rangaɗa sallama. Sai da aka ɗauki mintuna biyu masu kyau kafin Goggo ta amsa, jin amsar ta yasa mama sauke ajiyar zuciya tana ƙara bin gidan da kallo, ganin har zuwa lokacin babu wanda ya fito daga mutanen gidan, tana cikin tunanin, Goggo ta leƙo ba wani sakewa tattare da ita ta dubi mama duban fisha ta ɗauke kai haɗi da faɗin "ko Lafiya?" "Ita ta kawo haka, daman nazo ne na ƙara maku sannu da hanya" tayi maganar kamar ba ita bah. "Mun gode gajiya kuma tabi jiki" tana faɗin haka ta koma ciki abinta ta bar mama nan da baki sake. Duk da abinda da Goggo tayi mata ya zafe ta amma ta shanye, dake tana niman fuska daga gun Goggo. Barin wajen tayi

Chapter 3 of 6