ba, ya ƙarasa ya shiga gidan, buɗe ɗakin yayi bayan ya saka black shades a idanunsa, a zaune ya sameta tana wasa da roban takeaway ɗin da yayi mata da safe, ta ɓaɓɓarka ledan gabaɗaya.
Ba tare da yayi magana ba ya tura mata ledan hannunshi gabanta,
bata ko kalli ledan ba ta ci gaba da wasa da yatsunta, har ya kai ƙofa zai fice sai kuma ya juyo yana kallonta,
"SALWA!!"
Ya kira sunanta strictly yana folding hannayensa a ƙirji
Idanunta da zuwa yanzu sun koɗe da kuka ta ɗago tana kallonsa da su, wani irin very Innocent face take dashi, wanda zaka yi tunanin ko yatsa aka saka mata bazata taɓa cizawa ba, wanda ke ɗauke da round face da big eye balls ɗinta masu masifar ɗaukar hankali, tana da hasken fata tare da very cute ƙaramin baki ga dimples guda biyu wanda ko da magana take ko kuka ko dariya lotsawa suke a hankali.
kallon second 10 tayi masa ta mayarda kanta ƙasa tana wasa da ƴan siraran yatsunta masu kyau, wasu hawayen da take ta riƙewa tuntuni kar su zubo suna biyowa shar agefen fuskarta.
daurewa yayi kamar baya so, ya furta
“Eat ur food"
daga haka ya juya, har ya ɗaura hannu akan handle ɗin sai kuma ya tsaya cak sakamakon tsinkayo sassanyar muryarta da yayi, Cikin rawar murya na kukan baƙinciki da ke cinta ta soma magana
"Yaya Please ka mayar da ni wajen Ammina, ka min rai, zan mutu anan, ni bana son wajennan, tsoro nake ji wallahi yaya kullum idan baka nan, ni kam ka kaini wajen daddyna...." tana kaiwa nan ta fashe da shagwabaɓɓen kuka that irritates him.
Sai da ya jira ta kai aya kafin ya buɗe ƙofar ya fice abinsa, Wani irin kuka ta sake fashewa da shi tana kallon ƙofa, wannan wace irin rayuwa ce, idan kasheta zai yi gwara mata ya kashe ta ta huta, idan har lissafinta dai-dai ne to aƙalla zata yi sati ɗaya da kwana ɗaya kenan a wannan gidan da ko falo bata ƙaunar fita, eight days fa kenan innalillahi wa inna ilahi raji’un.
Ganin idanunta har wani zafi suke mata da wani irin hazo hazo ya sata lumshe su a hankali tana jinginar da kanta a jikin bangon ɗakin. A hankali take furta “daddy…” cike da shagwaɓa wanda nature ɗinta ne magana a haka.
Sai da ya tsaya yayi isha’i kafin ya wuce gidan, a ranshi yana jin kamar ya fasa zuwa ya wuce gidansa.
Sauƙe glass ɗin motarsa yayi yana kallon soldier ɗin da ke riƙe da bindiga fuskarsa a matuƙar haɗe, ɗaya daga cikin abinda ya sa ya tsani gidannan kenan, ba tare da ya kula maganar da yake masa ba ko na sauran soldiers ɗin da ke gadin wajen ya zuge glass ɗin ganin sun basa hanya ya wuce ciki
A tangamemen gate ɗin estate ɗin yayi horn, ɗaya daga cikin sojojin da ke gadin gate ɗin ya leƙo da kansa, ƙaramin tsaki ya ja ƙasa ƙasa yana kallonsa daga cikin motar, ganin motar Aryaan ɗin ya sa sojan buɗe masa ƙofa da sauri, babban family house ne ko ince estate na gasken gaske wanda yaji komai na rayuwa, ajikin makeken plate name ɗin da ke gefensa an rubuta ‘THE TURAKI'S’. kai tsaye cikin gidan da yake nan tarrr da haske kamar ba dare ba ya nufa da motarsa, sai da yayi tafiya ta atleast 15 minutes akan shinfiɗaɗɗiyar titi dake ko ta ina a cikin gidan yana wuce gine gine wanda dukansu iri ɗaya ne, sai dai banbancin girma da decorations da wasu suka fi wasu, sannan ko wani gidan yana da gate ɗin da zai sada ka da shi, da security mai gadin wannan gate ɗin, a ko wani gate da sunan mai shi a jikinsa wanda duka ƙarshensa ke ƙarewa da TURAKI.
Tun da ya tunkaro gate ɗin gidan mahaifinsa yake jan tsaki ƙasa ƙasa saboda sojoji da ke nan burjik suna gadin gate ɗin kamar zasu hana waɗanda ke ciki mutuwa, tun kafin ya ƙaraso ya fara horn har ya iso gaban gate ɗin wanda da alama ginin wannan gidan yafi na kowa a cikin Family house ɗin gabaki ɗaya, duk kuwa da yawan gidajen dake cikin estate ɗin.
Buɗe masa gate ɗin sukayi ba tare da sun kula shi ba kamar yadda shima bai kula kowa a cikinsu ba, gate ɗin mai kyau sai dai bai kai na Main entrance na gidan girma ba, a gaban wannan part an rubuta CDS. UMAR WAZEER TURAKI, a babban parking space ɗin da zai iya haɗiye a ƙalla motoci 10 ko ma fiye yayi parking, sannan ya fito daga motar yana sake haɗe fuskarsa, a hankali yake tafiya kamar baya son yayi ya nufi main entrance na wani babban part wanda yafi ko wani part girma a gidan, murɗa ƙofan falon yayi a hankali ya shiga bayan ya zare glasses ɗin idanunsa, ya ƙare ma babban falon da ya gaji da tsaruwa kallo, ƙamshi ne kawai ke tashi a falon mai sa nutsuwa ga sanyin ac da ya ƙarama wajen wani pleasant daɗi, ba tare da ya zauna ba kawai ya wuce ya fara hawa stairs don ya tabbata kowa na gidan na ɗakinsa, sanin yanayin mai gidan na rashin son hayaniya sam yasa komai a nutse a keyi a gidan. har yakai sama sannan ya dakata yana kallon ɗakunan da ke jere a saman guda uku ta gefen daman sa bai bi ta kansu ba ya murɗa wata ƙofa dake gefen hagunsa, wata haɗaddiyar falo ne ta bayyane mai matukar kyau wanda ke ɗauke da ɗakuna biyu kacal a cikinta, sai wani ƙofa da zai sada ka da falo na biyu, sosai ya lumshe idanunsa jin kamshin da ke tashi a falon kafin ya ƙarasa ciki, nan ma babu kowa, ɗan jim yayi kafin ya nufi ɗayan falon yana addu'ar samun Dad anan.
Tura ƙofan yayi a hankali da sallama ɗauke a bakinsa, a zaune ya samesa a kan ɗaya daga cikin manyan kujeru na alfarma, a falon da ya ma gaji da tsaruwa, dan ya ma fi falon farko kyau sai dai bai kaisa girma ba, ƙafansa ɗaya akan ɗaya ga cup akan center table ɗin gabansa, da wata ƴar karamar littafi da yake rubutu a ciki that looks like jotter or a diary book.
ɗago idanunsa dake cikin fararen medicated glasses yayi ya zuba ma ɗan nasa idanu, kafin ya kawar da kai daga kallonsa ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya amsa sallaman ba, a hankali Aryaan ya ƙaraso gabansa, ya zauna a ƙasa ya sunkuyar da kansa yana kallon haɗaɗɗen carpet ɗin dake malale a ƙasa, cikin sanyin murya yace
"Ina wuni DAD"
bai amsa ba sannan bashi da niyyar amsawa sai ma miƙewa da yayi, yayi folding hannuwansa a baya ya soma tafiya towards ɗakin dake cikin falon.
Cikin sauri muryarsa har rawa take Aryaan yace
"Dad please!"
ɗan dakatawa yayi kafin cikin dakakkiyar voice ɗinsa da ke cike da command yace
"ARYAAN UMAR TURAKI! Leave immediately, sannan saƙon da baffaninka suka isar maka, make sure ka cika umarni, kwanaki 59 suka rage cikin sittin ɗin da na ɗibar maka, bring a wife before then if not you will leave me with no choice bayan na ɗaura maka aure da koma wacece, in tura maka gidanka, since ka fi ƙarfin zama a cikin ƴan uwanka".
daga haka yayi shigewarsa ɗaki tare da rufo ƙofan.
Wani irin zuciya ke cinsa yana dannewa, why! Me yasa shi da mahaifinsa are not in good terms at all, ya zo ne ya gana da shi akan aurennan but sam yaƙi sauraransa, ya ake so yayi? Ta ina zai nemo mata a wata 2 kamar wani magnet? Aneela ce ta faɗo ransa cikin sauri ya shiga girgiza kai
"Nooo banda Aneela" sai kuma ya miƙe dan yasan bayi da choice bayan Aneela ɗin.
#banidahujja
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH!!🌺
By Maimoon
3.
Zuciyarsa a dagule, fuskarsa a haɗe ya fito daga sashen mahaifinnasa, yana kokarin ficewa daga ɓangaren gabaɗaya suka kusa cin karo da mummy ya matsa baya a hankali ya bata hanya ganin shiga zata yi wajen Daddy, a taƙaice ya gaishe ta shima ciki ciki
“ina wuni” ko kallonsa bata yi ba ta shige ciki abinta ya bita da side eye kafin ya buɗe ƙofar shima ya fice a gidan, ba tare da kallen kallen komai ba ya buɗe motarsa ya shiga ciki ya tayar aka buɗe masa gate ɗin Cds. Umar wazeer turaki ya fice yana driving gently, a gaban gate ɗin barr Ameena wazeer turaki yayi horn ba tareda ya ko kalli opposite house ɗin da shi kuma aka rubutu DR Ameenu Wazeer turaki ba, aka buɗe masa gate ɗin ya shiga yayi parking yana kallon motar AMEEN dake parking space ɗin which means yana gida as expected. Bai samu kowa a palourn ba sai sanyin ac da ƙamshin turaren wuta mai daɗi nan ma, stairs ya nufa kanshi tsaye yana jujjuya key ɗin hannunsa.
“Aryaan?” Dakatawa yayi tare da juyowa yana kallon Mami da fitowarta kenan daga kitchen, ta ɗan buɗa ido tana kallonsa tace
“ashe dai kai ɗinne hamshaƙi” ɗan murmushi yayi kaɗan ya fasa haurawa ya dawo palourn ya zauna a kujera yana sake ƙirƙiro murmushi
“ina wuni Mami”
“Da ban wuni ba zaga ganni ne aryaan?” Shiru yayi kawai dan ya san dama dole sai tayi ranting in dai ta gansa, rabonsa da gidan ya kwana biyu tayi mita har ta gaji.
“Yau kuma Allah yayi ka tuna mu kenan Aryaan, yanzu abinda kake yi ya kyautu kenan? Yaro ɗan gata amma ka mayar da kanka kamar maraya?” Ta faɗa tana zagayowa ta zauna a kujerar da ke facing ɗinshi tana ta kallonsa keenly, Nan ma bai ce mata komai ba sai murmushi kawai da yayi, ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali tace
“To Allah ya kyauta, ya kake toh? How have u been?” Sai a sannan ya amsa da
“Alhamdulillah Mami”
“Are u sure?” Gyaɗa mata kai yayi, tace
“Toh Allah yayi albarka, ya tsare gabanku da bayanku, ya baku abinda kuke nema duniya wa lahira, a cigaba da hakuri a kuma cigaba da yayyafawa zuciya ruwan sanyi, zama lafiya da kowa ya fi zama ɗan sarki, komai lokaci ne da shi haka zaka ga watarana kamar ba’a yi ba”
“Amin Mami” ya amsa yana jinginar da kansa da kujera, miƙewa tayi tana kallonsa tace
“AMEEN ɗin ai yana sama kaje bari nima in duba girki ya kusa gamuwa ma su lailerh zasu kawo muku” gyaɗa mata kai kawai yayi bashi da niyyar tashi, ta miƙe ta wuce kitchen, 10 minutes later ta kuma fitowa, da mamaki take kallonsa ganin har sannan yana zaune a wajen yana danna wayarsa, hakan yasa bata kulashi ba ta wuce sama dan kiran Ameen ɗin da kanta, tare suka sauƙo da wani matashin saurayi kyakkyawa wanda zasu yi sa’o’i da Aryaan sai dai ya fi Aryaan hasken fata da glasses a idanunsa dressed casual, ya kalli Ammi bayan ya sauƙo cikin palourn yace
“Ammi where is he?” Ammi ta ƙaraso cikin palourn tana kallonsa tace
“Ji iskanci! Anan fa na barsa shine ya kama hanya ya wuce bai ce min zai wuce ba? Kuma fa har abinci nace ya jira amma shine ya wuce ya tafi abinsa koh? Kirawo min shi kace nace ya dawo yanzu ya zo yaci abinci”. Ameen ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya yana zama a kujera yace
“Ki ƙyaleshi kawai tunda ya tafi ba juyowa zaiyi ba kin sani” zama tayi itama a kusa da shi tace
“Al’ameen me ke damun ɗan uwanka ne?” Ya buɗa mata hannu alamun bai sani ba shima yana murmushi,
“Ya zaka ce min baka sani ba, bayan ure closer to him than anyone”
“Allah Ammi ban sani ba, but bari na watsa ruwa inje gida in same sa inji if there’s anything i should know” gyaɗa masa kai tayi tace
“Idan ya faɗa maka pls ka zo ka faɗa min”
“Okay Mami” ya faɗa yana miƙewa ya wuce sama murmushi kwance a fuskarsa
“Lailerh ta kawo maka abinci yanzu?”
“Ah ah idan na dawo zanci”
“Toh” ta faɗa tana kallonsa har ya haura kafin ta wuce kitchen dan duba abinda su lailerh da siyama ke yi.
Yana driving yayi dialing lambarsa yana ajiye wayar a gefensa bayan yayi connecting da speaker ɗin motar, sai da kiran ya kusa yankewa kafin ya ɗaga, Al’ameen yayi gyaran murya yace
“Malam kana ina ne?”
“Why?”
“Ban sani ba! Kana gida ko baka gida?”
“Bana gida!”
“Kana ina?”
“Doesnt concern u!” Murmushi Ameen yayi kawai ya katse kiran yana nufan gidan nashi bayan ya kalli agogo ƙarfe 10 saura.
Buɗe masa gate mai gadi yayi bayan yayi horn once, ya shiga yayi parking a kusa da motar Aryaan dake space kafin ya fito ya nufi cikin gidan, ba tare da knocking ba ya tura ƙofar palourn ya shiga ciki yana kallon ko ina, ganin baya ciki ya gyara glasses ɗin idanunsa ya nufi hanyar sama da takalmansa, motsi da yaji a kitchen ya sa ya dawo da baya ya nufi kitchen ɗin, a bakin ƙofa ya tsaya ya harɗe hannu a ƙirji yana kallonsa, yana tsaye a jikin counter da singlet baƙa a jikinsa against fair skin ɗinsa, yayi pairing ɗinshi da three quarter iya guiwarsa dat looks loose, Al’ameen ya kalli plate ɗin scrambled egg dake plate da toasted bread guda biyu a gefe, black tea da yake haɗa ma kanshi a lokacin ya kalla kafin yace
“Yaushe ka koyi girki bawan Allah” ko kallonsa baiyi ba, barin jikin ƙofan yayi ya nufe shi yana faɗin
“Wulaƙanci ne bana so, sai in juya in koma in da na fito, da ina da zuciya ma wallahi ba zaka ganni a nan ba, ko da yake Mami ce tace na zo ka je kana acting weird a gida kuma before in sauƙo ka wani wuce ka tafi, idan ka san baka so in zo waya ce ka zo gidanmu nemana?”
“Says who kai naje nema?” Ameen ya hararesa yace
“To me kaje yi?” Sai da ya ajiye cup ɗin a gefen tray ɗin kafin yace
“Mami naje gaisarwa” Al’ameen yayi wani dariya da ya sa Aryaan kallonsa yace
“Ko ba gaishe da Mami ba, u that i know ɗin koh? Kai dai faɗi me ya kaika kawai, amma kafinnan haɗa black tea ɗin da ni banci abinci ba na fito” ko kulasa baiyi ba ya ɗauki tray ɗin ya fita a kitchen ɗin, Ameen ya ƙarasa ya ɗauki well cleaned cup da spoon ya biyo bayansa yana faɗin
“Wannan ɗin zai ishemu ne?” Bai kulasa ba ya ajiye tray ɗin akan dinning, tun kafin ya zauna Ameen ya ja kujera ya zauna tare da ɗaukar toasted bread guda ɗaya ya bar masa ɗaya, ya saka spoon ya ɗibi scrambled egg ɗin ya kai baki, zama kawai shima yayi ya ɗauki ɗayan bread ɗin ya soma ci, Al’ameen ya ɗauki cup ɗin black tea ɗin ya zuba a cup ɗinsa ya raba musu daidai da daidai, kafin ya tura masa nasa gabansa, komai bai ce masa ba ya ja ya fara sha yana ɗan danna wayarsa fuskarsa a haɗe, sai da suka conye duka kafin ya miƙe ya koma cikin palour ya zauna yana danna wayarsa, kwashe kayan Al’ameen yayi ya kai kitchen ya ajiye a sink ya buɗe fridge ya ɗauko bottled water guda biyu ya fito da su a hannunsa, jefa masa ɗaya yayi ya cafe shi kuma ya ƙaraso yana shan ɗaya, ya zauna a wani kujeran daban ba wanda Aryaan ke kai ba yana cigaba da shan ruwan, sai da ya gama sha ya ajiye sauran a center table kafin ya kalli Aryaan dake buɗe ruwan hannunsa a lokacin zai sha, yace
“What happened bro? Tell me mana why are u acting all up haka?” Aryaan ya rufe ruwan ya ajiye tare da ɗan dafe kansa, hakan yasa Ameen putting serious face ya miƙe ya dawo kujeran da yake zaune yace
“Me ya faru ɗan uwa?” Ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali ya ɗago ya kalli Ameen da idanunsa da suka ɗan yi ja yace
“I’m tired Ameen! Please tell me miye nayi ma Daddy?”
“What happened?” Ameen ya tambaya sounding concerned! Duk abinda ya faru ya kwashe ya faɗa masa from zuwan su uncle Ameenu zuwa zuwanshi gidan, Al’ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yana kallonsa har ya kai aya kafin ya dafa kafaɗarsa yace
“Calm down bro! Yanzu iya wannan abinne ya saka ka ɗaga hankalinka haka? Har ya nuna a face ɗinka cewa ure tensed? Haba aryaan” wani mugun kallo Aryaan ya masa yana ƙwace kafaɗarsa yace
“Bangane iya wannan abin ba, shey u no comprehend abinda nace maka? Cewa fa nayi Dad and his brothers so suke in kawo mata nan da two months, how is this possible Ameen? Meyasa sai ni kaɗai suka gani? What happen to u and hamza and the others? Kai da hamza da kuka girmeni ba’a ce ku kawo mata in so so so time ba sai ni?” Al’ameen ya gumtse dariyarsa yana kallonsa yace
“Wato yanzu ka yarda mun girmeka da yake zancen is not in ur favour, what happened to watanni ba girma bane? Kuma da kake zancen mu ba’a ce mu kawo mata ba, kai ai ka san dalilin da ya sa suka ce ka kawo mata, baka jin magana Aryaan, i’ll be so happy wallahi idan ma kayi auren ko wasu abubuwanka zasu saitu” Ganin yadda ya haɗe rai ya sa Ameen ya ɗan bubbuga kafaɗarsa yace
“Sorry bro, ka kwantar da hankalinka za fa ka samu mata nan da wata 2” jingina kansa yayi a jikin kujera yana kallonsa yace
“I was thinking about Aneela…” tun kafin ya kai ƙarshe Al’ameen ya haɗe rai tare da hararansa yace
“Over my dead body ne zaka auri yarinyar nan, kai tsakaninka da Allah idan aka barka sai ka auri yarinyarnan? Sai kace ma yaranka wace irin uwa ka zaɓa musu kenan?” Kallonsa kawai Aryaan yake baice komai ba, Al’ameen ya ɗauko wayarsa dake ringing ganin Mami yace
“Mami ce, let me come and get going home”
“Spend the night here mana” ya faɗa yana kallonsa, ɗan shiru yayi sai kuma ya ɗaga wayan yana sauraren Mami tare da kallon Aryaan da ya lumshe idanunsa, can yace
“Eh Mami, ill spend the night here gobe zamu shigo tare da shi” shiru yayi sai kuma ya amsa da
“Amin” daga haka ya katse wayar yana kallonsa yace
“Duk ta damu ta ɗauka wani babban abu ke damunka”
“Okay yanzu ƙarami ne ke damuna kenan”
“Eh mana daɗi ne yayi maka yawa, ni ace in fito da matar a gani mana da tuni na kai an wuce wajen”
“To yanzu ma idan ka kai ai ba zasu ƙi yi maka ba” ya faɗa yana miƙewa
“Ah ah barsu dai su tambayeni first ni ai ina da wacce nake so, jira kawai nake a tambayeni in gabatar da ita gaban kowa da kowa, ba irinka bane ni da kake tunanin auren mace irin zaleena sunanta ko aleena….”
“Aneeela..” suka tsinkawo muryarta daga bakin ƙofa, duk suka ɗaga kai suna kallonta, idanunta cike taf da hawaye take kallonsu hannunta rike da jakarta sai wayarta a ɗaya hannun tana sanye da tshirt mai maɓallai fara da blue jeans, attachment ɗinta ya xubo har gadon bayanta, sai siririn ɗankwali da ta ɗaura a kai as usual.
Kallo ɗaya Al’ameen ya mata ya haɗe rai tare da miƙewa da nufin haurawa sama yana mamakin irin rashin kamun kanta, yo rashin kamun kai mana idan ba haka mai zai kawo mace da ta san darajar kanta gidan mijin da ba nata ba da wannan daren? Halinta disgust him, Ko da yake its not entirely her fault har da na mai gayya mai aikin dan shi ya bata daman haka shi yayi welcoming ɗinta a gidansa anytime idan ba haka ba ai bazata zo ba, wani takaici ya takure shi a wuya ya ja tsaki tare da ɗaukan wayarsa zai wuce sama, ajiye jakar tayi ta ƙaraso palourn tare da shan gaban Ameen tana kallon cikin idanunsa tace
“Al’ameen miye na taɓa yi maka a rayuwarnan da ka tsane ni? Baka ƙaunata baka ƙaunar gani na tare da farincikin rayuwata, mai nayi maka da zafi har haka da kake ikirarin over your dead body ya aureni” wani kallo yake mata irin na malama na miki kama da wanda kika zo wajensa ne, kamar bazai kulata ba sai kuma yace
“I’m glad uve been eavesdropping tun ɗazu kuma kinji duk abinda nace, aryaan bazai taɓa auren mace irinki ba God forbid” juyawa tayi ta kalli Aryaan dake kallonsu kansa a kishingiɗe da kujera, kafin ta juyo ta bawa Ameen amsa ya raɓata ya wuce sama abinsa, ta bishi da kallon tsana kafin ta juyo ta dawo kujerar da Aryaan ke zaune tace
“Love ka ji abinda yake faɗa koh? Pls dont listen to him, ure my life ka sani” miƙewa yayi shima zai wuce sama tayi saurin kamo hannunsa ya juyo yana kallonta, ganin yanda take kallonsa idonta cike da hawaye ya sa ya janyo ta jikinsa yana kallon face ɗinta ya sa finger ɗinshi yana share mata hawayen dake kumatunta, ƙasa ƙasa yace
“Go home zamuyi magana later okay?” Ta gyaɗa masa kai tana kallonsa, ya sake ta ya ja da baya yana kallonta da guntun murmushi akan fuskarsa, ƙarasawa tayi ta ɗauki jakarta har ta buɗe ƙofa ta sake juyowa ta kalleshi, kashe mata ido ɗaya yayi, tayi murmushi tana share hawayenta ta fice tare da jan ƙofar, yana juyawa ya ga Al’ameen a tsaye a jikin stairs ya harɗe hannu yana kallonsa, suna haɗa ido ya haɗe rai, kallonsa kawai Ameen keyi har ya zo zai wuce kafin ya ja tsaki da ya tabbatar yaji ransa a ɓace ya furta
“kayi asara” ko kulashi bai yi murmushi kwance a fuskarsa ya wuce sama, juyawa yayi ya bi bayansa saman ransa a mugun ɓace.
Not edited
#Banidahujjah
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH!!🌺
4.
Al’ameen na fitowa daga bayi da pyjamas ɗin Aryaan a jikinsa ya zauna a gefen bed yana kallon Aryaan dake zaune a kan bed yayi resting bayanshi da headboard, macbook a buɗe akan cinyansa, hankalinsa duka yana kan abinda yake yi a ciki
“Wai haryanzu baka gama project ɗinnan ba?”
“Uhm” ya amsa a taƙaice, jin Al’ameen yayi shiru ya ɗago ya kalleshi yace “ko zaka ƙarasa min?”
“Hmm” kawai Ameen yace yana miƙewa ya dawo bedside ya leƙa screen ɗin yana kallo yace
“Still on commercial complex?” Aryaan ya bashi side eye ba tare da ya amsa ba yana zooming da adjusting kyakkyawan zane dake screen ɗin, Ameen yayi murmushi yana kallon abinda Aryaan ɗin ke nuna masa a screen ɗin, 3D model ne na building ɗin da yake aikinsa yanzu ya dinga rotating yana nuna ma Ameen ɗin ba tare da yace komai ba, sai da ya gama nuna masa kafin ba tare da ya kalleshi ba yace
“Kasan mutuminnan canja facade ɗin ya sake yi?” Ameen yayi guntun murmushi yana kallonshi yace
“Sau uku fa kenan yana canzawa, wannan client ɗin naka sai kai”
“Fourth…” ya faɗa calmly yana jan wani layi across screen ɗin, kafin ya canza zuwa wani tab ɗin daban wanda ke ɗauke da finishing materials, shi dai Ameen jingina bayansa kawai yayi yana kallon aikin cike da burgewa.
“Previous design ɗin kwata kwata baiyi balancing da structural load ɗin ba, idan na biye masa na bi irin abinda yake so blindly, kwata kwata ginin bazai yi making sense ba” Ameen ya gyaɗa kai yana miƙewa feeling impressed but not suprised dan ba tun yau ba yasan Aryaan is perfect at what he does.
“Kaga barmu a bar da cases, mun bar muku buildings ɗin”
“Gobe zaka rakani somewhere” Aryaan ya faɗa yana ɗago kanshi
“Where?”
“Zaka gani goben”
“Hope its after mun je gida?” Ganin ya maida kanshi