Share this page
5 / 8
gyara zamansa yana kallon bappah yace “Ban san me yasa duk abinda yarinyar nan za tayi a gidannan kuke kyaleta ba bappah, infact she’s becoming a bad influence to sauran yaran gidannan! Babu mai mata faɗa babu mai taka mata birki fisabilillah?” “Inji wa ba’a mata faɗa” daada ta katse shi tana kallonsa, ya mayarda kallonsa gareta yace “Okay kinsan cewa morocco zata je wani stupid birthday wai na friend ɗinta, bday ya wuce all states na nigeria har sai sunyi flying out? Kuma kowa ya zuba mata idanu babu mai kwaɓanta? As small as she’s har zata iya flying out alone for birthday tsakani da Allah fa?” Da mamaki bappah da Daada suke kallonsa dan sam basu san da maganar ba ko da suka ji ta shiru fiye da sati bata lekosu ba Ameenu cewa yayi ta tafi relative ɗin Amminta! Daada ta tafa hannuwa tana kallonsa tace “Amma Ameenu dai bashi da hankali! Kai innalillahi” ta juya ta kalli mijinta da shima ita yake kallo tace “Kuma fa babanne ya goya mata baya haka wallahi na sani yanzu haka Amminta ta hana suka ƙi hanuwa” Bappah ya gyaɗa kai yace “you did right amma da ka sani you report to me or your dad ba ka ɗauke ta ka kaita wani waje for this long ba, duk da anyi avoiding drama ɗin da suka faru saboda hakan” Aryaan ya gyaɗa kai a hankali tare da faɗin “toh ayi hakuri in sha Allah it wont repeat itself” a zuciyarsa kuwa shi ya san ba iya wannan dalilin bane ya sa ya rufeta! Ya jima sosai yana tarata dama already kwata kwata yarinyar bata yi masa ba rawan kanta da rashin kunyarta yayi yawa da ya sa ko kadan baya son yarinyar! Duk cikin ƙannensa she’s one da baya son ko ganinta saboda ya tsani sangarta a rayuwarsa, but duk da haka ba zai iya canza ta a matsayin jininsa ba hakan ya sa da yaji labarin she’s flying out for birthday a bakinsu lailerh kuma wai har Amminta ta hanata amma Uncle Ameenu yace a barta tayi abinda take so ya ƙudurta bazata je ba! dan birthday ne irin na marasa ji marasa kuma Kamun kai zasu je yi can ɗin! Hakan ya sa ya aikata abinda ya aikata, kuma ya tabbatar sai after birthday ɗin kafin yayi releasing ɗinta shima kuma cause of her school da zasu yi resuming cikin week ɗin, cikin satin da take wannan gida ko kaɗan Uncle Ameenu bai kawo Salwa bata Morocco bane saboda Aryaan always replies his messages da yake turawa salwa time to time! Wannan yana cikin dalilin da ya sake harzuƙa uncle Ameenu ganin rainin wayon ya kai rainin wayo! Aryaan wish yarinya ce da zai iya hukuntawa kamar su lailerh da tabbass duk wani rashin ji wallahi sai ta daina shi saboda yadda zai gyara mata zama amma inaa, duk wani abu da ya haɗa da Uncle Ameenu baya son shigarshi, shima wannan ɗin dana sanin shiga maganar yake da ya sani ya barta taje duk abinda tayi ruwanta ita da babanta. “Allah ya kyauta” muryar bappah ya katsesa dan duk maganar da suke ma shi bai ji ba, bappah yana kallonsa yace “To kai kuma back to maganar da baka so, akwai ko babu” Murmushi yayi yana shafa kansa ya kishingiɗa da kujera yace “Babu Allah bappah” bappah ya daina murmushin da yake yi yana kallonsa yace “Ban gane babu ba ka ɗauki abinnan wasa koh?” Langaɓe kai yayi yana kallon bappah yace “Dan Allah bappah kayi ma daddy magana wallahi ni bani da kowa ni ban shirya ma aure ba bappah, Daada pls talk to them! Ga nan Ameen shima ace ya kawo mata mana bappah” “Sai yaushe kenan zaka shirya ɗin? Banda shashanci shekara kusan talatin kace baka shirya ba! Shi Aminullah ai baya rashin ji shiyasa basu damu ba ko da yaushe ya gabatar da mata is fyn amma kai kam dole kayi aure idan ka ajiye iyali zaka fi natsuwa i’m with your dad and uncles on this” “Innalillahi! Daada talk to him pls he listens to you! Wallahi idan ba dai auren dole zaku mini ba ni bani da wata i’m serious, kuma a wata biyu ni bansan a ina zan samo ba” Shiru bappah yayi yana kallonsa kamar wanda wani tunani ya zo masa sai kuma yayi murmushi yace “Its alright! Tashi kaje ka bawa babanka hakuri kaje sai da safe” ganin yanda bappah ke murmushi yasa yace “Thank you bappah for understanding me, dan Allah ka musu magana” “Zan musu, tashi kaje” tashi yayi yana shafa kansa yace “Nagode bappah, sai da safe! Sai da safe Daada!” Suka amsa masa da “Allah ya tashe mu” ya juya ya nufi barin ɗakin, sai da ya fice kafin Daada ta kalli bappah “Amma da ka bari yayi auren wallahi ni bana son rashin jinnan da yake yi wallahi” “Zaiyi! Kafin ma wata biyunnan zaiyi kar ki damu” “Ta yaya?” Ta tambaya tana kallonsa “I just thought of something yanzunnan……..” Later that day da dare suna zaune a dining suna cin abinci, Mami ta kalli Aryaan dake ta juya cokali amma ko loma ɗaya baiyi ba har sannan, kallon Ameen tayi da ke cin abincinsa a nutse ta ajiye cokali tace “Aryaan ci abinci mana” Ameen ya ɗaga ido ya kalleshi sai kuma ya fara dariya! Mami ta kalli Ameen tace “Kai kuma fa?” “Wai fa Daddy Umar ne yace masa ya kwaso kayansa ya dawo cikin gida ya bar wancan gidan nasa with immediate effect shine tun da ya baro wajensa yake ta cika yana batsewa!” Mami ta ɗanyi murmushi tana kallon Aryaan da ya ɗaga idanunsa yana kallon Ameen fuskarsa a mugun haɗe. “Da yaushe ne yace maka hakan Aryaan?” Mami ta faɗa tana kallonsa, ya sauƙe idanunsa yana juya rice yace “Ɗazu ne” “To miye abin damuwan dan ance ka dawo cikin gatanka Aryaan! Cikin ƴan uwanka!” Shiru yayi bai ce komai ba, ta zuba masa ido tana kallonsa kafin tace “Idan ma baka son zama can part ɗinku ga nan gidan sai ka tattaro kayanka ka dawo nan kawai kaaji” sai a sannan ya kalleta ya gyaɗa kansa a hankali, feeling a little bit relieved dan tunda Dad yace ya tattaro ya dawo gidan babu abinda yake tunani irin zaman gidan Dad ɗinnasa da baya jin zai iya! Ameen dake murmushi yace “Gaskiya ya tafi gidansu kar ya takura mini” “Sai dai kai ka tafi gidanku shikam nan ne gidansu” Mami ta faɗa tana murmushi. “Yanzu yaushe zaka kwaso kayannaka?” “Gobe in sha Allah” “To Alllah ya kaimu” duk suka amsa da “Amin” Salwa ce ke saukowa daga sama waya kare a kunnenta tana magana da raliya da sai jiya suka dawo daga morocco ashe, tana sanye da girlfriend jeans da top mai kyau da ya nuna flat tommy da perfect figure ɗinta, kanta ba ɗankwali sai siririn headband da ta sa a ta gaban gashin, ganin Amminta a palour tayi ma Raliya sallama tana ƙarasawa cikin palourn ta ɗan rungume Ammi ta baya kafin ta zagayo ta zauna a ƙasa kusa da ita, Ammi na kallonta tace “Kinyi isha’i?” “Nayi Ammi” “Tsakaninki da Allah kinyi” “Wallahi Ammi fa nayi” ta faɗa a shagwaɓe “Idan ma baki yi ba ke kika sani! Tsakaninki da ubangijinki, kuma kin sani Allah yana kallonki” “Ammi nayi fa” Ammi bata sake kulata ba ta cigaba sauraron voice note ɗin da only sister ɗinta ta mata on whatsapp. Miƙewa Salwa tayi ta nufi hanyar ƙofa Ammi ta kalleta tace “Ina zaki da darennan!” “Wajen Siyama zan duba abu ne a anatomy textbook ɗinta” “A haka zaki fita babu ɗankwali? Ke kam miye ɗankwali ya miki ne a rayuwarki Salwa? Wallahi ni banga anfanin islamiyyar da kike zuwa ba Salwa kin fi so ki dinga yawo da kai a buɗe mala’iku na tsine miki koh? Kin fi so ki je ki kwaso ma kanki abinda bazaki iya ba koh salwa! Wallahi na gaji da magana akanki ki kiyayi randa zan fara saka hannu a jikinki saboda ɗankwali Salwa!” Tsayawa tayi a bakin ƙofa tana kallon Ammi a shagwaɓe kamar zata yi kuka, ganin Ammi ta miƙe ya sa ta wuce sama da gudu tana hawaye, Ammi ta bita da kallo tana faɗin “kuma ki cire cingam ɗinnan a bakinki dan ubanki..” ganin har ta riga ta haura ya sa ta koma ta zauna tana cigaba da replying sister ɗinta wanda ba maganan kowa suke ba face na Salwa still. #banidahujja #Maimoon 09041426598 https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q 🌺BANI DA HUJJAH🌺 Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga 7039695535 Palmpay, Maimunatu Abdullahi muhd Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535 Thank you❤️ 8. Kamar yadda ya faɗa ma Mami washegari ya je gidan dan ɗauko boxes ɗinshi, har cikin zuciyarsa ba son komawa family house ɗinnan yake ba amma yadda ran Dad ke ɓace ba yadda ya iya, babu any room for musu. Boxes uku yayi na kayansa waɗanda zai buƙata dan ya riga ya sa a ransa ba wai ya koma gidannan bane forever, ko ya zaiyi zai shawo kan dad ya barsa ya bar gidannan, yanzu dai he’ll be there for the meantime tukunnan. Dakatawa yayi da haɗa kayan ya riƙe jikin siff ɗin yana kallon akwatunan sai kuma ya ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa, kwata kwata rayuwarsa is messed up! Baya jin daɗin rayuwarsa ko misƙala zarratin! Duk da kasancewar mahaifinsa babban soja, family ɗinsa well reputed sunansu ya zaga ko ina, amma deep inside of him ya rasa what is the missing piece da babu a rayuwarsa da yake sa yake jin rayuwar a wargaje, menene wannan missing piece ɗin da ya kamata ya tattaro rayuwarsa duka ya saka glue ya manne su waje ɗaya. Yana saukowa da akwatinan palour ya fara kakkashe appliances na gidan aka buɗe ƙofa, ya juya ya kalli Aneela da ta shigo cikin palourn tana kallon boxes ɗin da ke palourn kafin ta mayarda idanunta kansa ganin ya kashe tv da wutan passage ɗin yana ƙoƙarin kashe wutan palourn gabaɗaya tace “Love” kamar bai ji ta ba ya wuce kitchen few seconds later ya fito, tana nan tsaye inda ya barta tana ta kallonsa confused. “Baby whats going on?” Ta faɗa finally bayan tayi mastering enough courage ta ajiye jakarta ta ƙarasa ta riƙo hannunsa. “Ina zaka haka da duka boxes ɗinnan?” “Gida” ya bata amsa a taƙaice “Wani gida?” Ɗan kallonta yayi ya zare hannunsa a nata ya ɗauki box ɗin ya kai bakin ƙofa ya dawo sai sake ɗaukar wani “Okay kafin ka tafi can i talk to you for a moment?” Ya ajiye akwati ya rungume hannunsa yana kallonta da idanunsa da ya sa taji jikinta ya mutu, ta ɗan langaɓe kai ta ƙaraso ta rungumesa a hankali duk da baiyi hugging ɗinta back ba amma bata damu ba ta cigaba da magana “Baby ka min magana mana, me yake damunka? Yaushe rabon da ka ɗaga wayata? Yaushe rabon da ka zo apartment ɗina ko school ɗinma na manta rabon da ka zo da sunan ganina, dan Allah dont punish me for laifin da bansan na aikata ba kaji kasan ina sonka sosai kai ne rayuwata ka sani” ta faɗa tana zagayo hannunta a wuyansa ta ɗago face ɗinta tana kallon nasa, ta ɗan ɗaga ƙafarta to match his height da niyyar sumbatarsa. Sai a lokacin ya warware hannunsa yayi wrapping around bayanta ba tare da ya bari ta sumbace shi ɗin ba, ya juyata ya jingina ta da bango yana kallon cikin idanunta, murmushi tayi tana kallonsa itama tare da cije lips ɗinta, ta kama hannunsa ta ɗaura akan ƙirjinta a hankali tana kallon idanunsa, ya sauƙe idanunsa ya kalli inda ta ɗaura hannunnasa kafin ya saketa ya ɗan ja baya a hankali, da mamaki ta dinga kallonsa ya ƙarasa zai ɗauki akwatin da bai ɗauka ba ɗazu tayi saurin riƙo hannunsa idanunta cike taf da hawaye tace “Aryaan! zaka aureni pls?” Ɗan kallonta yayi na few seconds cause bai tsammaci wannnan tambayan ba, sai kuma ya kamo hannunta ya jata har kujera ya zauna ya zaunar da ita, ya kamo fuskarta ya ɗan sunkuya ya sumbaci goshinta kafin ya ɗago yana kallonta yace “Lets talk” ta gyaɗa masa kai kawai tana kallonsa dan a halin yanzu babu abinda take son sani irin abinda ke zuciyarsa game da ita. “Aneela ba tun yau ba kin tambayi this same question idan zan aureki ko ah ah, the answer is No! Aneela kuma kema kin san dalilin da yasa amsata ya kasance haka!” Hawaye ya gangaro idanunta tace “Saboda Al’ameen yace kar ka aureni koh? Saboda yace maka ni ƴar iska ce koh? Idan ma iskancinne ai tare mukeyi meyasa ni kaɗai zan karɓi consequence ɗin banda kai” guntun murmushi yayi ya ɗan kau da kansa daga kallonta kafin ya koma yayi relaxing da kujera yana kallonta yace “Da ni kike iskanci?” Tayi shiru tana kallonsa, “okay lets get this over with, na farko! Ameen ba shi zai faɗa mini wacce zan aura da wacce bazan aura ba since ba shi zai zauna mini da matar ba! I never said i was gonna marry you Aneela, kuma ke kinsan dalilin da ya sa bazan aureki ba, kinsan dalilin da ya sa i never crossed the line with you, saboda duk abinda i cant own i dont keep, duk abinda is not fully and completely mine i dont attach myself to it.” Kallonsa kawai take, kafin tace “bangane nufinka ba?” “Kinga no need for tone tone! I’m been honest with you, idan har kina da wanda kike ganin is more serious gwara ki bashi chance” yana faɗin haka ya miƙe itama miƙewa tayi tana kallonsa tace “Amma you are a wicked person Aryaan! Ni zaka ci amana? Bayan ka gama ruguza mini rayuwata, bayan komai da na sadaukar saboda kai? Bayan duk soyayyar da na nuna maka? This is what you say? This is how you pay back my love for you? To wallahi billahi Aryaan idan har ina doron duniya kuma ina numfashi ni ce nan matarka kuma baka isa ka auri wata mace a duniya bayan ni ba!” Daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo kafin ya harɗe hannunsa a ƙirji, “Na ruguza miki rayuwa in what way? By paying your rent and your school fees? By sponsoring your lifestyle? Sadaukarwa saboda ni? Wanne kenan enlighten me, kinga Aneela i’m not in for this rubbish!” Katsesa tayi saurin yi tana kallonsa tace “na baka lokaci na, na baka jikina, na baka respect da duka emotions ɗina” bai san sanda yayi dariya ba yana kallonta yace “Dont deceive yourself kika bani jikinki? Sanin kanki ne i never crossed that line! Saboda kamar yadda na faɗa miki duk abinda ba nawa bane completely bana buƙata” “Wai kana nufin i sleep around ko miye?” Bai tankata ba ya ɗauki other boxes ɗin ya fitar a palourn ta biyosa tana cigaba da magana, komawa yayi ya rufe ƙofar palourn bayan ya kashe sauran appliances ɗin duka ya ɗauko jakarta ya ajiye a waje, tana biye da shi tana maganganu marasa kai da gindi tana hawaye, ya fito compound ɗin ya nufi motarsa ya buɗe ya saka boxes ɗin, yana saka box na ƙarshe a baya ya rufe motar tare da buɗe murfin gaban motarsa zai shiga ya bar gidan sai a lokacin ta fara kukan gaske ta riƙo hannunshi tana kallonsa tace “Are u breaking up with me?” Ya wafce hannunsa yace “I already did! Goodbye” fashewa tayi da kuka tana riƙosa tace “Pls baby No! Ko bazaka aureni ba na yarda amma kar ka rabu da ni pls” wafce hannunsa yayi ya shiga motarsa ya rufe ta fara buga glass ɗin kamar mahaukaciya tana kiran sunansa, reverse yayi da ya sa ta matsa daga jikin motar tana zunduma kuka ya nufi gate, mai gadi dake zaune tuntuni yana kallon drama ɗinsu ya taso da sauri ya buɗe masa gate! ya dakata ya sauƙe glass ɗin yana kallon mai gadin yace “Ta fita ka rufe mini gida! Kar wanda ya sake shigo mini gida without consent ɗina, nima zanyi tafiya i wont be around idan kana so zaka iya zuwa kaga gida” gyaɗa kai kawai mai gadi yake yana amsawa da “Toh ranka ya daɗe” ganin Aneela ta nufo gate ɗin da saurinta ganin yana magana da mai gadi ya sa ya ɗauki kuɗin da ke dashboard ɗinsa ya miƙa masa yana karɓa ya ja motar ya fice a gidan bai ko tsaya sauraren godiya da yake ta masa ba, ficewarshi yayi dai dai da isowar Aneela gate ɗin, ta dakata tana kallon motar har ya ɓace kafin ta rushe da kuka, ta tsuguna a wajen tana tayi, shi dai mai gadi komawa yayi ya zauna yana kallonta, tausayin mata masu hali irin nata na ratsashi, dama a haka suke ƙarewa kullum suna hanyar zuwa wajen maza ƙarshe mazan su wulaƙanta su saboda dama tun farko basu ɗauke su a masu daraja ba, girma, mutunci, ƙima da daraja da Allah yayi ma ɗiya mace duk sun zubar da tasu a gaban mazan, ta yaya bazasu bi kai su taka su wuce ba? “Allah ya shirya mana haula” ya faɗa a hankali yana gyara zamansa a kujera yana kallonta. Sai da tayi kukanta mai isarta kafin ta miƙe ta tafi ta ɗauko jakarta da ke yashe a compound ɗin ta nufi gate fuuuu, kamar zata tashi sama dan wallahi yayi kaɗan yace bazai aureta ba, wallahi bashi da mata a doron duniya bayan ita zata iya zuwa ko wani extent dan ganin hakan ya faru. From there Aryaan gidansu Umminsa ya wuce straight, Gidansu Umminsa madaidaicin gidane mai kyau single storey building, yayi horn mai gadi ya buɗe masa ya shigo da motarsa compound ɗin yayi parking. Sai da ya ɗauki kusan three minutes cikin motar kafin ya buɗe motar ya sauƙo riƙe da wayarsa ya nufi cikin gidan. Tun kafin ya ƙarasa palourn yake jin hayaniyan yara sama sama, ya tura ƙofar palourn da sallama ƙasa ƙasa ya shiga, Umminsa na zaune a kan kujera hannunta riƙe da Marwah tana bata indomie sai juya kanta take bata son ci, Maman marwah ƙanwar umminsa na zaune itama a palourn tana dariya ganin yadda marwah ke kuka bazata ci ba ummi kuma tace sai fa taci yarinya kwata kwata taƙi abinci sai Nono ƙatuwa da ita, babban yayan su Ummi dake zaune shima a palourn yace “Asiya ki rabu da ita idan bazata ci ba dan Allah” sauƙeta tayi ta ɗan daki jikin pampers ɗinta da wasa tace “jeki ƴar ƙaniya” dai dai lokacin suka ji sallamarsa, duk suka ɗaga ido suna amsa sallaman. Ganin wanda ya shigo ya sa Abbah Usman sakin fuskarsa sosai yana faɗin “Ahh Aryaan kaine?” Ya cire glasses ɗin idanunsa yana ƙarasowa ya zauna a ƙasa yace “Ina wuni Abba..” ya juya yana kallon maman marwah yace “ina wuni ummah” itama tana murmushi tace “Ahh lallai Aryaan yau dai da rabon zamu haɗu ashe a gidannan! Wato sai dai a haɗu da kai a hanya kai baza dai kazo ma mutum har gida ba koh?” Murmushi yayi ya juya ya kalli umminsa da ta daina murmushin da take yi tun shigowarsa yace “Ina wuni Ummi” “Lfy lau” ta faɗa tana miƙewa ta nufi kitchen dan taimakawa anty husaina matar Abbah usman dan yau full house gidan yake sun zo duba jikin gwaggo. Ummah ta miƙe ta nufi ɗakin gwaggo tana faɗin “Gwaggo guess wa ya zo gaishe ki…?” Shi dai Aryaan binta da ido yayi har ta shige ɗakin kafin ya kalli Yayan Umminnasa yace “Abbah haidar fa?” Second son ɗin Abbah sa’an Aryaan ɗin, dan ya ma bawa Aryaan ɗin watanni. “Tare muke da shi ai, yaje kai Malam check up ne na san sun kusa dawowa ma, bakwa magana a waya da shi ne” “Munayi” Aryaan ya amsa yana gyara zamansa Abbah yace “to yayi kyau, Ka shiga ka duba gwaggon” gyaɗa kai yayi a hankali ya miƙe ya nufi ɗakin gwaggo,mahaifiyar umminsa, farar tsohuwan na kwance a kan gado kana ganinta kasan tana ɗan jin jiki duk da yadda Ummi ke kula sosai da ita, tana ganinsa ta miƙa masa hannu tana murmushi, ya ƙarasa ya zauna a gefen bed tare da sa hannunshi a nata ita dai ummah na zaune a bedside tana kallonsu ɗauke da murmushi, hannun ya kai bakinsa ya sumbata yace “Ya jikin gwaggo?” “To Alhamdulillah muhammad, ina ta cigiyarka shiru abinka” “Aiki ne ya ɓoye ni gwaggo kuma bansan baki da lafiya ba” “Aikam dai jiki yaƙi daɗi, sai fatan Allah ya sa mu cika da imani” “To ke wa ya faɗa miki cuta mutuwa ce? Sai ki ga na rigaki mutuwa ma..” da sauri ta girgiza masa kai tana kallonsa tace “Kul, in sha Allah ba yanzu zaku mutu ba Aryaan sai ka ga ƴaƴanka har da jikoki, nima in sha Allah sai na ga har ƴaƴanka in sha Allah” murmushi yayi ya ɗaga idanunsa ya kalli Ummah ta harareshi, ya shafa kansa a hankali yace “Ummah tun yaushe ne bata da lafiya?” “Ban sani ba, ai da ka damu da sani da ka sani” shiru yayi bai sake cewa komai ba, After some seconds ya kalli gwaggo yace “kina son wani abu ne gwaggo in je in samo miki?” Shiru tayi tana kallonsa sai kuma girgiza masa kai “In sayo miki fruit?” Ɗan murmushi tayi kafin ta jinjina masa kai, yayi murmushi shima ya miƙe ya nufi hanyar fita Ummah ta bishi da idanu. Fita yayi a palourn Abbah na tambayarsa inda zashi yace yana dawowa. Bayan Thirty minutes ya dawo gidan da niƙi niƙin kaya, Abbah ya zuba masa idanu har ya gama shigowa da duka cefanen da yayi kafin yace “Yanzu wa ya saka ka wannan aiki Aryaan” ya sunkuyar da kansa yayi shiru “Toh Allah yayi albarka” da “Amin” ya amsa ya ɗauki ledan fruits ɗin gwaggo ya wuce ɗakinta, sai a lokacin Abbah ya kalli Ummi dake zaune a palourn yace “Asiya meyasa kike haka ne? Idan baki ja ɗanki a jiki ba wa zai ja miki shi ne wai” shiru tayi bata ce komai ba, ya sauƙe ajiyar zuciya yana miƙewa yace “Allah ya kyauta! Bari in ɗauko su malam a hospital wai motar Haidar is faulty” “No wonder naji su haryanzu shiru” ta faɗa tana kallon yayannata , bai ce mata komai ba dan haushin yanda take treating ɗanta yake ji har ransa ya nufi ƙofa ya fice abinsa. Bayan fitansa Ummah da anty husaina suka fito daga ɗakin gwaggo, ummah ta zauna tana kallon Ummi ganin yadda tayi shiru lost in thought kuma tasan baya rasa nasaba da zuwan Aryaan gidan. Anty husaina tace “Yanzu Asiya har yanzu bazaki cire abinnan a ranki ki nunawa ɗanki soyayya ba? Kina wahalar da kanki kina cutar da yaro?” Ummah tayi ƙwafa tace “wallahi anty husaina lamarin yaya Asiya sai ita! Dan Allah shi miye laifinsa a duk abubuwan da suka faru yana ƙarami! Me ma ya sani shikam?” Kafin ta basu amsa Aryaan ya fito a ɗakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar malam tare da Abbah da yana fita yaci karo da sunyi bolt ma ashe har sun iso sai kawai ya dawo ciki tare da Malam ɗin ya bar Haidar a waje yana waya. Malam na ganin Aryaan ya buɗe ido yana faɗin “Ahhh lallai manyan baƙi ne a gidannamu ashe” murmushi yayi a hankali yana gaishe sa, Malam ya zauna a kujera yana faɗin “Kuma a cikinku a rasa mai sanarmin Muhammad ya zo?” Ya faɗa yana directing question ɗin to su Ummi. “Ban daɗe da zuwa ba ai” ya faɗa yana ƙarasowa ya zauna a ƙasa gefensa, “Toh masha Allah ya gidannaku? Ya bappahnku da su Daada, how’s your Dad? Da kowa kowa?” “Lafiyansu lau Alhamdulillah

Chapter 5 of 8