ɗinsu tunda itama retired lawyer ce kuma field ɗinta ne.
Ganin Aryaan zashi masallaci ya miƙe shima ya ɗauro Alwala a banɗakin palour ya bi bayansa zuwa mosque.. suna dawowa Aryaan ya kuma haurawa sama Ameen kuma ya yi zamansa ƙasa.
Mami tana kallonsa tace
“Aikin miye Aryaan kam yake yi ne? Yau fa wuni yayi aiki da ƙyar na samu yaci abinci..”
“Hmm” kawai Ameen ya faɗa yana danna wayarsa, Mami tace
“Why humming?”
“Salwa ce wallahi ta goge masa wani project da yake yi kusan wata huɗu fa kenan kuma next week zaiyi submitting ɗinsa..” Mami ta ɗan buɗa ido tana kallonsa tace
“Kai haba dai? Subhanallah amma gaskiya bata kyauta ba miye ma ya aiketa taɓa masa aikinsa ko bata sani bane?”
“Ta sani wallahi” ya faɗa yana miƙewa tsaye, Mami ta yi shiru tana ta kallonsa har ya fara haurawa kafin tace
“Amma zai iya sakewa ne a wannan guntun lokacin, tunda kace next week ya kamata ya bayar?”
Ameen ya ɗanyi murmushi kawai yana haurawa yace
“Maybe zai iya, kinsan shi da naci kamar kuturu, amma gaskiya fa kamar wuya…”
“Kai Allah ya kyauta, amma gaskiya ban ji daɗi ba wallahi” Ammi ta faɗa tana jin haushin abinda salwa ta aikata masa da kuɗira aniyar idan dai ta shigo sai ta mata faɗa.
A zaune Ameen ya tarar da shi still yana aikinsa, Ameen ya zauna gefen bed yana cire takalminsa yace
“Take it easy on yourself pls, kaima kasan bazaka iya sake yinshi kafin due date ɗin ba…” ko kulasa Aryaan bai yi ba, Ameen ya shiga wanka.
Bayan Sallar isha’i Aryaan ya fito toilet yana gyara gashin kansa da ya jiƙo da ruwa ya zauna a gaban side mirrow yana goge gashin da towel! Ameen da ke shan coffee yayi murmushi yana kallonsa yace
“Toh wa yace maka zuba ruwa a kai yana rage ciwon kai ai sai dai ma ya ƙara!” Shiru ya masa, Ameen ya kuma murmushi yana cigaba da kallonsa yace
“To ni yanzu laifin miye na maka kake wani shashshareni sai kace ni na goge maka aikinnaka…” sai a lokacin ya kallesa, fuskarsa a haɗe yace
“Kasan Allah either you ko babanta gwara ku fara neman kuɗin biyana abinda ta mini asara idan ba haka ba wallahi duk abinda nayi ma yarinyarnan a gidannan babu ruwan kowa da ni..”
“Mu biyaka? Mu biyaka fa ka ce…” Ameen ya faɗa yana dariya, kafin Aryaan ya amsa, wayar Ameen ya hau ringing ganin bappah ya ɗaga tare da gaishe shi har sannan da murmushi fuskarsa…
“Eh muna tare da shi gashi nan…Okay..toh” kallon Aryaan yayi bayan ya katse kiran yace
“Meyasa ka kashe wayarka ana ta nemanka” ya ɗaga idanunshi ya kalli Ameen
“Wa ke nemana?”
“bappah ne ya kirani yanzu wai idan muna tare da kai kaje yana nemanka yanzu” ɗauke kansa Aryaan yayi yana ajiye towel ɗin da ya gama goge kansa
“Kaji ina?” Ameen ya maimaita masa yana kallonsa da sipping coffee ɗinsa
“Ba zuwa zanyi ba.” Ya faɗa yana miƙewa daga gaban mirrow ya nufi kan gado..
“Kiran bappahn?”
“Eh” ya amsa a taƙaice
“And why is that” kamar bazai amsa ba sai kuma yace
“Aneela ce ta je ta same su wai na mata ciki na sa tayi aborting and many other sharri su kuma they believed her, bappah yace ta je zai ɗauki mataki shine wato har ta dawo saboda ita mayya ce.” Ameen ya buɗa ido sosai yana kallonsa yace
“Is she Mad?, why on earth will she do that!”
“Yes She’s indeed Mad, a kuma gabana ta faɗa”
“Amma lallai yarinyar nan ta cika mahaukaciya, kai kuma sai kace musu miye? Kaga irin yarinyar da kake so ka aura ina koh? yanzu a gaban su bappah tace ka mata ciki?.”
“You dont have to remind me” ya faɗa yana jingina kansa da allon gado..
“Yanzu dai tunda na riga na ce masa ga ka nan kawai kaje kar ka ƙara ma kanka laifi, da na san hakane da cewa nayi ma bama tare..”
“Ka rakani toh…” Aryaan ya faɗa yana kallonsa daga kwance
“Ah ah kaje dai zan zo kafin ka dawo bari na gama shan wannan..” ya faɗa yana ɗaga masa cup ɗin hannunsa, amma a zahiri shima tsoron zuwa yake yi kar a je a haɗa da shi
shiru yayi kamar ba zai tashi ya je ɗin ba sai kuma ya miƙe kawai ya nufi ƙofa yana gyara white shirt ɗin jikinsa Ameen ya bishi da kallon yana kai cup bakinsa..
Duk da dare ne amma ko ina tarr da haske ƙoyayen fitulun waje, a nutse yake tafiyarsa ransa duka a dagule, abubuwa ne da yawa suka haɗe masa a yanzu da ya rasa yadda zaiyi da su, kamar ance ya ɗaga kai ya hango salwa zaune saman motar Hamza, shi kuma yana tsaye a ƙasa, ta tanƙwashe ƙafafunta tana danna waya suna hira, ya kalli agogon hannunsa ƙarfe takwas da rabi, kasancewar dole ta gabansu zai wuce yasa suka hangosa tun kafin ma ya iso, buɗa idanunta Salwa tayi ta soma ƙoƙarin sauƙa a saman motar tayi ta kanta Hamza na mata magana ma ko kulashi bata yi ba ta samu ta sauƙa zata ɗiba da gudu, dan bata san meyasa ba haka kawai wani irin tsoronsa ne ya ɗarsu a ranta tun bayan abinda ta aikata masa, tana ƙoƙarin guduwa amma tuni Aryaan har ya iso wajen saboda yadda Hamza ke ƙoƙarin hanata guduwa yana tambayarta abinda ya haɗata da Aryaan ɗin da zata gudu dan ta gansa.. wafce hannunta tayi daga na hamza bayan ta galla masa uwar harara ta ɗiba da gudu Aryaan ya rufa mata baya, ko kaɗan bata kai labari ba dan bata yi nisa a gudun nata ba Aryaan ya cafkota tare da haɗe hannayenta biyu waje ɗaya ya ɗauke fuskarta da Mari, da sauri hamza ya nufo su kafin ya ƙaraso har Aryaan ya ƙara ɗauke ɗaya gefen da mari ya ƙara mata da ranƙwashi mai azababben zafi ta kurmu ihu tare da fashewa da mugun kuka, Hamza ya hankaɗa Aryaan ɗin yana faɗin
“Kai mahaukacin ina ne? Uban miye ta maka” dai dai lokacin Ameen da ya biyo bayansa ya hango abinda ke faruwa, ya nufosu da sauri yana faɗin “Subhanallah” Aryaan ya sa hannu duka biyu ya hankaɗa Hamza har sai da ya bugu da mota, ya juya ya koma kan Salwa da ke kuka wiwi tana bashi haƙuri, ganin yana ƙoƙarin zare belt ta fara ƙoƙarin riƙe hannunsa amma sam ta gagara miƙewa tsaye bare ta saka ran guduwa.
Ameen yayi saurin riƙe belt ɗin da ya ɗaga zai sauƙe a jikinta yana faɗin
“Aryaan miye haka!” Wani kallon banza ya masa tare da sake masa belt ɗin da ya riƙe ya kalli Salwa da ke hawaye ga shatin hannunsa kwance a farin kumatunta ya nuna ta da yatsa cike da kashedi yace
“Ban gama da ke ba…” yana gama faɗin haka ya nufi part ɗin bappah! Ameen ya ɗago Salwa da ta ƙara ƙarfin kukanta kamar zata shiɗe, Hamza ya miƙe zai bi bayan Aryaan Ameen yayi saurin hanashi yana faɗin
“Dan Allah ka rabu da shi kar ka biye masa, ba girmanka bane” kallon banza shima yayi wa Ameen ɗin zuciyarsa na tafarfasa ya juya ya nufi part ɗinsu, Salwa dai banda gunjin kuka babu abinda take yi, Ameen ya sa hannu yana duba face ɗinta da yayi ja yatsun Aryaan kwance ɓaro ɓaro yace
“Salwa bakya ji, yanzu dubi abinda kika ja ya miki, baki kyauta ba, wata da watanni ya ɗauka yana aikinnan kuma cikin sati mai kamawa zai yi submitting gashi kin masa asararsa, yanzu gashi kin ja ya doke ki a banza da hofi… sorry!” Ya faɗa cike da rarrashi
Sheshsheƙan kuka kawai take yi tana sauƙe ajiyar zuciya kamar zata mutu tana kallon wrist ɗin both hannayenta da suma suka yi ja saboda riƙon da yayi mata, rabonta da a dake ta har ta manta lokacin, shi dai Ameen ya cigaba da rarrashinta dan ko kaɗan baya son kukanta amma kuma this time around bashi da bakin magana tunda itace bata da gaskiya…
Sai da ya tsaya yayi composing kansa kafin yayi sallama tare da shiga palourn bappah, yanayin fuskokin parents ɗinsa a yau ya sa haka kawai yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi! Bappah na zaune fuskarsa expressionless, Uncle Ameenu ma na zaune idanunsa sunyi jajir har wani ruwa ruwa ne a cikin idanun na ɓacin rai, kasancewarsa fari yasa farar fuskarsa har jajaja tayi tsabar ɓacin rai, Dad ɗinsa ma fuskarsa a matuƙar haɗe, ransa a ɓace irin ɓacin ran da ya jima bai gani tattare da shi ba, uncle muhammad sammakal, kai harta uncle lawal da bai cika ɓacin rai ba shima yau fuskarsa a haɗe yake tamau! This time around harda Daada a zaune gefen Bappah itama fuskarta babu yabo babu fallasa…
Waje ya samu a ƙasa ya zauna yana lissafa duk wani laifi da he possibly did da zai ɓata musu rai har haka amma bai iya tuno ko da ɗaya ba.
A nutse ya gaishe su, bappah da Daadah ne kaɗai suka amsa sai uncle lawal. Bappah ya gyara zamansa ya fuskancesa tare da fara magana, daga yadda yake magana kaɗai ya tsinci ɓacin rai shima a muryarsa..
“Muhammad!” Bappah ya kira sunansa, amsawa yayi yana ɗaga idanunsa ya kalli bappah, strictly bappah ya soma magana
“Na yanke hukunci muhammad mai girma wa rayuwarka wanda bai yi ma iyayenka daɗi ba! Sai dai ina mai tabbatar maka cikinsu duka babu wanda ya isa ya hana hukuncin da na yanke! Ina kuma fatan kai bazaka yi jayayya da hukuncin da na yanke akan rayuwarka ba dan sanin kanka ne bazan taɓa cutar da rayuwarka ba” gyaɗa kanshi yayi a hankali ya gagara cewa komai,yawun bakinsa ma ji yayi ya ƙafe rashin sanin wani hukunci ne wanann da ya shafi rayuwarsa da har ya ɓata ran kowa har haka?
“Muhammad Aryaan ni bappahnka Wazeer na ɗaura maka aure a yau da Salwa Ameenu Wazeer, auren da nake buƙatar ku kasance tare ƙarƙashin inuwarta har ƙarshen rayuwarku!” Dummmm kansa ya sara da ƙarfin gaske yayi dai dai da bugun da zuciyarsa yayi kamar zai faso ƙirjinsa ya fito!
Ya ɗago idanunsa yana kallon bappah speechless, gyaɗa kansa bappah yayi yana kallonsa yace
“Idan kuma kaima iyakata zaka nuna mini bismillah!” Girgiza kai ya hauyi amma ya gagara magana! Salwa? Why Salwa? Cikin duka matan duniya a rasa wa za’a aura masa na dole sai Salwa? Salwa fa? Inaaaa bazai yiwu ba, ba zai taɓa yiwuba, ba zai taɓa iya rayuwa da salwa a matsayin matarsa ba kwata kwata bazai yiwu ba…
“Ka tashi kuma ka je ka taho da matarka yanzu ina so in yi magana da ku a tare!”
Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen free pages from the book bani da hujjah, ku garzayo ku zo kuyi making payments dan kar ayi tafiyarnan ba tare da ku ba, amsoshi ga tambayoyinku duk zaku same su ne idan kunyi subscribing
Ya makomar auren Aryaan da salwa?
Shin iyayensu zasu amince da zamansu?
Su kansu couples ɗin zasu zauna ɗin?
Menene tarihin Turaki Family
And many more…..
Support me pls❤️
Zamu ɗauki hutun posting na sati ɗaya both on whatsapp and arewabooks dan tantance payments, nagode sai na ji ku..❤️
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
#banidahujja
#Maimoon
09041426598
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels