suna gaishe ku”
“Muna amsawa masha Allah, amma zaka kai dare ai koh tunda gashi naga har yamma ta fara yi”
“Ah ah yanzu zan wuce but zan dawo gobe in sha Allah” Sai a lokacin Umminsa tayi magana tana kallonsa tace
“Ce maka akayi kar kayi dare a nan ɗin kenan” ya dubeta a hankali amma bai ce komai ba.
“Da sun sani ai kar ma su barka ka zo kwata kwata, ko da kai ko ba kai zan rayu” tana faɗa ta miƙe zata wuce ɗaki, Aryaan ya miƙe ya tsaya yana kallonta yace
“Ummi..” juyowa tayi tana kallonsa, yana kallonta shima yace
“What wrong have i ever done to you? Miye laifina a duk abubuwan da suka faru? Meyasa laifin wasu ke shafana? Meyasa kika tsaneni? Me na miki?” Kallonsa kawai take idanunta yayi ja, har ta juya sai kuma ta dawo tana kallonsa tace
“Idan har abinda zai kawo ka kenan Aryaan kar ka sake zuwa inda nake! Kaje can wajen dangin ubanka da suka fini, zuwan ganin daman da kake mini ma bana so na yafe!” Tana kaiwa nan ta juya zata wuce, Aryaan yayi wani murmushi mai ciwo kafin yace
“Ko da ban zo ba na san ba zai dame ki ba ummi.. cause u never cared, idan da ace u cared bazaki barni at five years ba, da zan iya da na jima da daina zuwa inda kike…” pauuu marin da ta ɗauke shi da shi ya sa ya tsayarda maganar ba tare da ya ƙarasa ba da sauri Ummah ta taso tana ƙoƙarin riƙeta, Malam yana kallonta yace
“What kind of behaviour is this Asiya” tana huci ta kalli Aryaan tace
“Idan ka kuma mini magana in that tone zaka san ni ce nan na haifeka ba kai ka haife ni ba! Rashin tarbiyyarku ta gidanku ta tsaya iya gidan ubanka! And get out of my house!”
Malam zai kuma magana Abbah ya masa alama da ya barta, tsayawa Aryaan yayi dafe da kuncinsa idanunsa sun yi ja, Ummi ta fizge hannunta daga na ummah ta tafi ta kama hannunsa ta ja shi har ƙofa a zuciye, binta kawai yake yi dafe da kuncinsa ta buɗe ƙofa ta tunkuɗa sa waje tana kallonsa tace
“Sanda ka koyi respecting uwarka da iya magana da ni u come back! I’m still your mother ko ma miye za’a yi brainwashing ɗinka a nuna maka ba zai taɓa canza matsayina na uwarka ba and for that bazan ɗauki disrespect from my own child ba” tana gama faɗa ta rufe ƙofan.
#banidahujjah
#Maimoon
09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH🌺
Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
9.
Ya kai three minutes a tsaye dafe da kumatunsa kafin ya juya a zuciye ya nufi motarsa kamar zai tashi sama, ba tare da ya ko kalli Haidar da ke zaune yana waya a compound ɗin ba ya buɗe motar ya shiga mai gadi ya buɗe masa gate ya fice a gidan Haidar ya bishi da kallo.
Driving kawai yake amma zuciyarsa wani irin mugun bugawa da ƙuna da ciwo take masa, dukan steering yayi karo na babu adadi wanda instead of hakan ya sanyaya masa zuciya sai ma sake zafi da zuciyarsa ke yi!
Ganin idanunsa ya fara zama blurry yasa ya gangara gefen hanya ya fara bincika cikin motar inda yakan ajiye cigarette ɗinsa har ya samo kwalin, ya buɗe motar ya fito ya zaga gefe ya fara kokarin kunna lighter a jikin tabar, da ƙyar ya iya kunna cigarette ɗin da ya saka a baki saboda yadda hannunsa ke shaking ya zuƙa tabar sosai kafin ya furzar da hayaƙin yana jin kamar zuciyarsa zata kama da wuta.
Sai Wajen ƙarfe shida ya shigo gidan, sau ɗaya ya kalli motar hamza da ya kusa bumping into him wajen gate saboda how reckless yake driving amma ko kaɗan bai biye masa ko ya bi ta kansa ba ya wuce part ɗin Mami, yana gama parking ya fito har sannan idanunsa bai washe daga jan da yayi ba, ƙofar shiga gidan ya nufa dai dai lokacin salwa ta fito daga cikin gidan riƙe da babban textbook na anatomy da wayarta a hannunta Siyama dake bayanta tana tambayarta ko zata shiga school gobe dan a goben zasu yi resuming, dama ita da siyama suke studying same thing madicine suna 200level yanzu haka, apart from rashin ji Salwa is a gifted child, in dai ƙwaƙwalwar kwashe karatu ne Allah ya bata, Lailerh kuma mass communication take yi itama tana 200level ɗin.
Ko amsa gaisuwar da Siyama take masa bai yi ba ya wuce cikin gida, Salwa tayi dariyar mugunta tana kallon siyama tace
“Ba ke iyayi ba? Ni kinga na gaishe sa ne? Wani yaya ina wuni.. gashi nan ai ya dizga ki maganinki wallahi Allah ya ƙara”
Siyama tace “sai miye idan bai amsa ba ni dai ba ruwana gwara ke wallahi bazan ƙi gaishe sa ba ya ci ubana…”
Salwa zata yi magana lailerh ta fito tana tura baki da key ɗin motar Aryaan a hannunta, ta ƙaraso inda suke dan dama gidansu Salwa zasu karatu, tana kallonsu tace
“Yaya yace mu kwaso masa boxes ɗinsa mu shigar ciki” Siyama ta tsaya sororo tana kallon Lailerh da ta nufi motar, Salwa tayi wani dariya tana tauna chewing gum ɗin bakinta tace
“ƙannen yaya ku je ku kai masa kayansa ciki ni kinga tafiyata” da sauri Siyama ta riƙo hannunta tana kallonta tace
“Dan Allah ki jirani, gashi can lailerh ta fito da shi guda uku ne kawai yanzu zan shigar in zo mu tafi…”
Kallon hanyar gate tayi kamar bazata haƙura ta jirata ba sai kuma tace
“yi sauri toh, let me sit there” ta faɗa tana nufar kujera da ke compound can ƙarƙashin flowers, da sauri siyama ta juya ta nufi motar, ta ɗauki akwati ɗaya cikin biyu dake wajen dan lailerh har ta shigar da ɗaya, lailerh ce ta sake fitowa ta ɗauki na ƙarshe tana kallon Salwa irin kallon kin shiga uku sai kuma ta koma ciki ba tare da ta ce mata komai ba, kusan five minutes shiru basu fito ba ta ja tsaki ƙasa ƙasa tare da miƙewa ta nufi gate, har zata fita sai kuma ta fasa ta juya ta nufi cikin gidan dan ganin uban abinda ya riƙe siyama ɗin.
Buɗe ƙofar palourn tayi bata lura da shi ba har sai da ta shigo tsakiyan palourn ta ganshi a zaune babu kuma siyama bare lailerh a palourn sai akwatunan da suka shigo dashi duka uku a palourn a gabansa, tana ganinsa ta juya da sauri zata nufi ƙofa, buɗe idanunsa da ke lumshe yayi yana kallonta idanunsa sun sake kaɗawa yace
“Come back here! Ke wato kin fi ƙarfin ki ɗauko boxes ɗin right?”
Juyowa tayi ta kalleshi amma ta gagara magana! Fuskarsa kaɗai ta kalla ta san akwai abunda ke damunsa daban bayan zancen akwatuna! Ya daka mata tsawa yana kallonta yace
“Ba dake nake magana ba!”
“Lailerh fa bata ce da ni ba” ta faɗa a shagwaɓe hawaye na ciko idanunta tana dana sanin shigowa gidannan, da ta sani tayi wucewarta bakinta alaikum.
“Kwashesu ki kai sama kafin in fara ball dake” ya faɗa babu wasa a tone ɗinshi.
“Duka?” Ta tambay tana ɗan zaro masa idanu irin sun mata yawa ɗinnan, shiru yayi yana kallonta , ganin irin kallon da yake mata ta yarfe hannu tare da ajiye textbook ɗin hannunta da wayarta hawaye na gangarowa ta nufi boxes ɗin ta kama ɗaya, mai da kanshi yayi ya jinginar ya lumshe idanunsa sai dai duk kiciniyar da take da boxes ɗin yana kallonta sarai ta ƙasan idanunsa, tanayi tana yarfe hannu tana hawaye! Da ƙyar ta kai ɗaya sama zuwa bedroom ɗin Ameen, ta sake saukowa tana kallon palm ɗinta wai ko yayi ja, haka ta sake ɗaukar ɗayan tana yi tana kallonshi amma taga idanunsa a lumshe,ta tura baki ta ja akwatin ta fara ƙoƙarin hawa da shi sama, daga ta koma ta gaban akwatin ta tura sai ta koma ta baya ta ja shi ƙiii, danne zuciyarsa kawai ya dinga yi kar ya tashi ya kife ta da mari ganin abinda take masa da akwati amma dai ya shareta, haka ta kai na biyun ta sauƙo zuwa lokacin kukan gaske takeyi dan hannunta da gaske zafi ya kama yi mata gashi yayi ja.
Tana kuka ta kama na ukun, ta dinga ja da ƙyar ta kaishi rabin stairs, ta zauna a wajen tayi shiru tana kallon tafin hannunta, bata ankara ba ta ga ya miƙe daga kwance da yake da sauri sauri ta miƙe tsaya ta kama akwatin tana kallonsa a marairaice, bata san sanda ta sake akwatin ba ganin ya nufota ta kwasa da gudu tayi sama, ya ja tsaki ƙasa ƙasa ba tare da ya bi ta kanta ba ya wuce ɗakin Ameen ya kwanta, kusan ten minutes sai gata nan ta shigo da last akwatin, ta lallaɓa ta ajiye shi kusa da ƴan uwansa ta juya ta fice a ɗakin a hankali, dan a zatonta bacci ne ya ɗauke shi, shi kuwa sarai yana jinta kawai baya son huce haushin da yake ji ne a akanta dan zai iya karya waɗannan kararen hannuwan nata.
“Kai wa yace maka Aryaan ya dawo gidannan?”
“Mummy wallahi ya dawo! Yanzu ma saura kaɗan muyi clashing a gate, ai na so na bi ta kan ɗan iska da mota kuma dama naji ƙishin ƙishin wajensu kamal wai Dad ɗinsu yace musu Aryaan was instructed da ya dawo cikin gida….” Katseshi mummy tayi ba tare da ta ƙarasa ji ba dan hankalinta na ka first sentence ɗinsa da yace sun kusa clashing da Aryaan ɗin.
“Ni bana son shahshanci kana mota yana mota kake gangancinnan, idan abu ya same ka kuma fa?”
“Ba abinda zai same nj mummy” hamza ya faɗa yana ɗaukan slice ɗaya na Apple cikin wanda mummyn tasa ke ci, Abida da ke danna wayarta ta miƙe zaune tace
“Yaya Hamza da gaske yaya Aryaan ya dawo?”
“Ban sani ba dan ubanki! Dama in ganki kina nane masa ɗinnan wallahi sai na taka wuyanki wawuya” mummy ta haɗe rai tana kallonsa tace
“Miye haka hamza? Kai meyasa bazaka ja ƙanwarka a jiki ba? Kana da wacce ta fita ne? Ku biyunnan fa kune gatan juna ko bayan raina, miye ne dan tana murnar ya dawo? Haba hantarar ai yayi yawa kuma”
“Mummy kin mance haukan yarinyarnan koh? Wai sonshi fa take yi dan bata da hankali, ki rasa wanda zaki so sai maƙiyina”
“To ina ruwanka idan tana sonshi? Kai da ubanka halinku ɗaya hamza sam hankalinku baya kan abinda nake so! Hanyar da zaku mulki gidannan ya dawo sai abindq kuka ce! Ba gwara ita bama tunda ko ba komai wanda take so matakala ne na cikan burina, kai kuma fa? Ka rasa wacce zaka ce kana so a cikin family ɗinnan sai Salwa! Allah ya sauwaƙe in haɗa iri da Ameenu wallahi”
“Taɓdi maganar kuma kike so mummy! Ai wallahi kinma haɗa an gama, ni fa Salwa ita zan aura gwara ma ki daina wannan maganar taki, kowa ma yaje ya auri wanda yake so in dai dan na hana Abida auren ɗan iskan can ne to taje ta aureshi a bar mini salwata”
Abida ta taɓe baki dan ita da salwa ko ga maciji basa yi tana kallon hamza tace
“Taɓdi wallahi yaya da ka auri salwa gwara….” Ko ƙarasawa bata yi ba yayi kanta yana faɗin
“Kutumar ubanki shegiya annamimiya! da in aureta gwara miye? Wato ke kike zuga mummy koh dan uwarki”
“Hamzaa” mummy ta buga masa tsaya, ya dakata ba tare da ya doki Abida ba kawai ya wuce fuu ya fice, ita kuma Abida ta bishi da harara harda tsaki, duk da can ƙasan zuciyarta zumuɗi ne da son ganin Yaya Aryaan da ta mallaka ma zuciyarta ya dasa kujera ya zauna a cikin zuciyarta ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya yayi kane kane, kuma mummynta ta mata alƙawari cewa bata da miji bayanshi.
Washegari Mami na zaune a palour tana kallon daily soap Salwa ta shigo cikin palourn, tana sanye da pencil skirt da top, braid guda huɗu da amminta ta mata da gashinta ta sakosu ta gaba, ta ɗaura veil ɗinta kamar ɗankwali hannunta riƙe da wayarta ta shigo cikin palourn, Mami ta ɗaga kai tana kallonta tace
“Baki je school ɗin bane Salwa?” Ɓata fuska tayi tana ƙarasowa ciki tace
“Bani da lafiya” Mami ta mayar da hankalinta sosai kanta tana kallonta tace
“Subhanallah me ya sameki?” Gefen kujeran da Mami ke zaune ta zauna tana nuna mata hannunta tace
“Ba yaya Aryan bane ya sani kai akwati sama jiya shine hannuna yayi red sai da na shafa balm, da asuba da Ammi ta tashe kuma naji kamar zazzaɓi shine daddy yace kar inje in bari gobe” Mami dai kallonta kawai take yi har ta kai aya kafin tace
“Toh sannu Allah ya ƙara sauƙi”
“Amin” ta amsa tana kai hannu bowl ɗin dake center table ta ɗauki chocolate guda ɗaya. Mami ta cigaba da kallon da take yi can kuma tace
“Ko zaki rakani gidan baffanku Sageer? Wai Tahir bai ji daɗi ba kuma an kawo kayan auren safna kinje kin gani?” Girgiza kai tayi tana ɗaukan wani chocolate ɗin shekaran jiya Amminta taje kuma sai da tace tazo suje taƙi zuwa, duk da duka gida ɗaya ne amma mutane dayawa cikin ahalinnan sai su jima basu ga salwa ba, dama gidan da tafi shiga daga na Mami sai kuma part ɗin grandparents ɗinta.
“Ya kamata ki je ki gani ai ki mata Allah ya sanya alkhairi, bari musa ya dawo na aikesa sai ya kaimu yanzu”
Gyaɗa kai tayi sai kuma ta miƙe tana kallon Mami tace
“Let me go change my clothes da sauri kafin ya dawo!”
“Me ya samu waɗannan ɗin”
“Nikam zan canza…” ta faɗa tana nufar ƙofa da sauri! Tana buɗe ƙofa ta kusa cin karo da shi dan ya kawo hannu zai buɗe kenan yaga an buɗe ƙofar, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta yana sanye da black tshirt da ash sweatpants ƙafafunshi cikin sneakers, daga gani kasan daga workout yake, fuskarnan kamar kullum kamar ko yaushe a haɗe, haɗe ranta tayi itama tana matsawa daga bakin ƙofar ta bashi hanya ya wuce ta ya shige ciki ba tare da ya bata second look ba, ta bi bayanshi da harara kafin ta fice a gidan tana ayyana a ranta abinda zata masa ta rama duk abubuwan da ya mata.
Da yammacin ranan Aryaan na kwance yana duba project ɗin da yake aiki akai, Ameen kuma na toilet yana wanka dan tun da ya dawo daga office ya kwanta bacci sai yanzu ya farka shine ya shiga wanka.
Gajiya yayi da duba project ɗin ya ajiye laptop ɗin ya janyo wayarsa, ya fara scrolling a IG har yanzu mood ɗinshi is very off. Har ya wuce post ɗin ya dawo yana kallon hoton da tayi posting twenty minutes ago, da ita da wata da bai san wacece ba yarinyar ta rungumota ta baya ita kuma ta buɗe haƙora duka tana dariya, sosai hoton ya fita yayi matuƙar kyau amma sam ko misƙala zarratin bai burgesa ba ya duba caption ɗin yaga ta sa BFF sai kuma tag na account ɗin wacce ke hoton tare da ita wato Raliya, ga nan likes da yawa da comments kaca kaca wanda mostly na maza ne masu yaba kyawunta.
Tsaki kawai yaja ya fice a instagram ɗin, yau da su lailerh ne da tabbass sai ya taka wuyansu akan post ɗinnan amma anything that involve Salwa and her dad ya tsame hannunsa a ciki, tayi duk abinda pleases her.
Wayar da ya ajiye ya lumshe idanunsa ne ya fara ringing, buɗe idanun ganin sunan Dad ɗinsa a screm ɗin ya sa ya tashi zaune da sauri! Ta ɗauki wayan yayi picking ya kai kunne tare da sallama. Ko amsa sallamar Dad baiyi ba yace
“Meet me now a part ɗin bappah! Immediately” yana gama faɗin haka ya katse wayarsa ya riƙe wayar a hannunsa yana kallo da tunanin what happened kuma again this time around dan he can sense ɓacin rai sosai ba kaɗan ba a voice ɗin Dad ɗin nasa.
Ameen da ya fito yana tsane kansa yace
“Me ya faru?” Ya buɗa masa hannu alamun bai sani ba, sai kuma ya sauƙa a gadon ya nufi ƙofa!” Aryaan ya bishi da kallo yana wucewa dan ɗaukan kayan da zai saka.
Mutanen da ya tarar a palourn ya sa bugun zuciyarsa ƙaruwa dan ya tabbata ba lafiya ba, dan uncles ɗinsa kaf suna zaune a palourn kuma dukkaninsu fuskarsu babu fara’a suke kallonsa, babu wanda nasa yafi basa mamaki irin bappah, ya ƙaraso ciki da sallama sai a loakcin ya lura da Aneela da ke zaune can other corner na ɗakin idanunta jajir a kumbure suntum.
#banidahujja
#Maimoon
#09041426598
https://whatsapp.com/channel/0029VbB1qGBFMqrVuPRZ5f2Q
🌺BANI DA HUJJAH🌺.
Assalamu alaikum lovelies Bani da hujjah is a paid book, free pages kuma basu da yawa sosai, pls support me by making your payments kafin end of free pages! Thank you so much as you do, ga masu bukatar biya zasu tura 500 kacal zuwaga
7039695535
Palmpay,
Maimunatu Abdullahi muhd
Sai ku tura min evidence of payment ta 09041426598 on whatsapp
Idan kuma katin waya ne zaku tura 500 zuwa ga 07039695535
Thank you❤️
10.
Gyara zamansa Aryaan yayi yana sauraren Aneela da ke magana bayan bappah ya bata izinin maimaita abinda duk ta faɗa, he is not even suprised at all bai san meyasa ba, ba kunya babu tsoron Allah take labarta ƙarya da sharri a gabansa da iyayensa without thinking about the consequence, the only thing da yake yawo a kansa a lokacin shine Al’ameen was damn right ta yaya ma yayi tunanin zai iya auren Aneela in the first place? Wannan abinda da ta aikata ya sake tabbatar masa cewa he made the perfect choice by breaking up with her, mamaki ma yake yadda ta iya shigowa cikin gidan har gaban bappah who allows her in? ya tabbata dole da saka hannun wani cikin family ɗinnan kafin ta iya isowa har gaban bappah, ya ɗaga idanunsa ya kalli uncle Ameenu da uncle muhammad da ke zaune suna kallonta tana bayani, idan ba idanunsa suka masa gizo ba gani yayi ma kamar murmushi ne tucked a lips ɗin uncle Ameenu, ɗauke idanunsa yayi a hankali daga kallonsu ya mayar ƙasa ba tare da ya yarda ya sake kallon face ɗinsu Dad ɗinsa ba dan sosai suka nutsu suna saurarar ƙaryar da take shirga musu suma ransu a ɓace, wani smirk yayi a hankali jin wai har abotion ya sha sakata tana yi and that babanta sent her to school here amma shi ya hanata ya ajiyeta yana biyan bukatarsa da ita with the promise cewa zai aureta! Girgiza kai yayi a hankali yana jinjina hauka da rashin lissafi irin na Aneela, a tunaninta all these da tayi zai saka ya aureta ne? Ko su zasu tursasa shi ya aureta ne? Infact his own family dai da ya sani this alone da tayi ko shine da kansa yanzu yace zai aureta bazasu taɓa lamunta ba! This is the height of rashin kunya da rashin tarbiyya shi a ganinsa.
Maganarta ne ya katse masa tunaninsa, tana shesheƙar kuka take faɗin
“Shiyasa na kawo kukana gareku, dan Allah ku mini adalci sir” ta faɗa tana share hawaye
Ajiyar zuciya bappah ya sauƙe bayan ta kai aya ya juya ya kalli Aryaan da har sannan ya kasa haɗa idanu da kowa kamar yadda Aneela taƙi yarda ta kalli sashin da yake.
“Muhammad” bappah ya kira sunansa, a hankali ya ɗago kansa yana kallon bappah yace
“Na’am bappah”
“Ka san wannan yarinyar?” Ya tamabaya yana nuna masa Aneela, gyaɗa kansa yayi a hankali ba tare da yace komai ba, Dad ɗinsa ya dinga kallonsa da mamaki tare da takaici duk a haɗe!
“Ka santa kace?” Ya sake gyaɗa kansa ba tare da ya ce komai ba,
“Duk abinda ta faɗa gaskiya ne kenan?” Girgiza kai yayi a hankali ba tare da ya ɗago ba, Uncle Ameenu yayi caraf yana kallon Aryaan rai ɓace yace
“Maƙaryacin banza maƙaryacin hofi!” Dad Umar ya kalli Ameenu bai dai ce komai ba,
“Sharri kake so kace tayi maka? Mu ba ce mana kayi baka da wata mace da kake nema ba? Ba zaka kuma iya providing mata a wata biyu ba, mu zaka zubar wa mutunci? Mu zaka ɓatawa suna? To wallahi billahi baka isa ba! Tunda har kace ka santa that means duk abinda ta faɗa akanka gaskiya ne, kuma zaka aikata” Uncle Ameenu ya cigaba yana yi yana nuna Aryaan ɗin da yayi shiru kawai yana saurarensa ba tare da yace komai ba.
Bappah ma kallon Aryaan ɗin kawai yake yi, duk labaran da ake kawo masa na rashin jin Aryaan bai taɓa yarda one hundred percent ba sai yau, he’s so disappointed in him, wai ace jininsa ne ke irin wannan bayahudiyar rayuwa! Da ƙyar yayi composing kansa ya dubi Aneela dake share hawayen har sannan yace
“I’m deeply sorry for this my daughter!” Da sauri Aryaan ya ɗaga kai ya kalleshi, he cant believe wai bappah haƙuri yake bawa Aneela, ya buɗe baki da ƙyar yace
“Bappah….” Ɗaga masa hannu bappah yayi, ya cigaba da maganarsa yana kallon Aneela yace
“Idan har everything you have said is true ni na miki alƙawari i will not let it go..” ta gyaɗa masa kai a hankali tana wani sussunkuyar da kai
“But for now ina so ki bamu time, ki je gida we will handle this” gyaɗa kai ta kuma yi duk da ba haka ranta ya so ba, so tayi su ce dole sai ya aureta bayan abinda ya aikata mata, ta ɗan kalli side ɗin uncle Muhammad da Ameenu da ba ita suke kalla ba dan ba haka tayi da su ba amma dai sai bata musa ba ta miƙe a hankali ba tare da ta sake kallon kowa a palourn ba ta nufi ƙofa tana jan ƙafa ta fice, duk suka bita da kallo banda Aryaan da dad ɗinsa.
Shiru palourn ya ɗauka na few seconds kafin dad Umar yana kallon bappah yace “i’ll head to barrack now akwai abinda zanyi yanzu a can bappah” gyaɗa masa kai bappah yayi dan yasan ba ƙaramin ɓaci ran Umar ɗin yayi ba, Dad Umar ya miƙe ya nufi ƙofa ba tare da ya kalli sashin da Aryaan ke zaune ba, bin mahaifinnasa yayi da idanu, deep down yana jin disappointment in himself for constantly hurting his Dad, ya sauƙe idanunsa ƙasa yana jin wani kalan tsanan Aneela har ƙasan ransa, da dana sanin irin rayuwar saɓon Allah da suka yi da ita dan tabbass wannan ne ya bata lasisin yi masa wannan akuyancin.
Miƙewa Uncle Ameenu yayi yana kallon bappah yace
“I’ll also take my leave” yana faɗin haka ya nufi ƙofa, uncle muhammad ya miƙe ya bi bayansa, dan suna buƙatar iske Aneela kafin ta bar estate ɗin, dama can su suka shigo da ita, uncle muhammad ya zo zai shigo ya ganta a tsaye sojoji sun hanata shiga suna ƙoƙarin humiliating ɗinta, ya sauƙe glass ya tambayi whats happenening suka ce masa wai wajen Aryaan ta zo amma ta gagara kiran line ɗinsa, jin Aryaan yasa yace su barta ta shigo, suka kuwa barta ta shiga motarta ta bi bayansa, sai da ya fara tabbatar da abinda ya kawota zai musu anfani kafin ya sanar da Ameenu shi kuma ya escalating maganar har gaban bappah tare da mata alƙawarin Aryaan ya aureta an gama, now that ta ga ba haka ba they need to silence her ko