Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:01 KANO STATE. *Unguwar kwanar ƴan dadawa* Tafe take tana ƙwambo,ta ɗage kafaɗarta ɗaya irin yadda nigogi keyi,jikinta sanye da wata ƙatuwar riga irinta maza da wando shima ƙato,kanta sanyeda pcap,zariyar wandon harkusada gwiwar ta,ƙafarta sanyeda wani ƙaton boot na maza baƙi, duk ya tsufa yasha faci,kayan jikinta kuwa sunyi uban squeezing,se ƙwambo take tana hura hanci,tafiyarta ma tanayi rana ɗage kafa ɗaya kamar namiji,hannunta riƙeda ƙaramin bucket fari wanda ake cewa fallasa na talla,shaƙe yake da awara me miya. Tana tafiya tana ɗage kafada irin yadda maza keyi,duk inda ta gitta yara da manya sekaji ana kANDE mai awara,ita kuma tana ɗaga hannu kamar wata ƴar siyasa tana faɗin "eh mana,dawa dai, kuhuta kawai". Tana kawo wa wata chamber samari guri ya kaure da ihu suna faɗin zaa kand, zaa kand,itakuwa se wani ɗage kafada take tana ƙwambo,tana basu hannu suna kashewa kamar yadda maza ke gaisawa da junansu. Cikin karkace baki kamar namiji tace "eh maza yane?, ya ake ciki ne eye?,kun haɗo min balance ɗina ko yaya?" Ɗaya daga cikin samarin yace "ai tuni na cake miki uwar kuɗin ki zaa kand, d one nd only ƙanwar maza in the ƴan daddawa village" wani juyowa tayi ta kallesa ta karkace baki ita adole namiji ce tace "zakarius asswear zan bubburma maka hannu a hanci,see zis tsamius want to read me nonsenseus eh,tsohon waye yake a village din iye? Zakarius zafa mu raba tawun(town) da kai fa,Allah wlh, Ni kar ka sake cewa unguwar mu village garama kawai ka mata zigidir ka kirata local getto yafi yawwa", tafada tana wani dire bokitin awarar ta. Tamika maka hannu tace "giv me zaa yastazey(yesterday)balans",miƙa mata kuɗin yayi,ta amsa ta gyara p cap dinta ta laƙwato miyau tafara ƙirga kuɗinta. "Wan,su,siri,foo,fai,sis,sabin,ess,nai,sen" haka ta dinga fillila ƴan hamsi2 tana kirgawa ita adole turanci take,samarin wurin sunmata yuuu da ido suna kallon ɗan bakinta kamar gidan tsutsa gashi jajur wai ita anan namiji ce,kaf faɗin unguwar batada ƙawa duka maza ne abokan hurɗarta,acewarta ita ƙanwar maza ce sbd haka itama namiji ce ba ragguwa ba,ƙawarta ɗaya ce layuza,itama sbd tsananin haƙurinta da juriya yasa suke ɗasawa,saboda tun suna yara ita kaɗai ce take jure wahalar bala'in kande shiyasa har suka girma suna tare,kuma bata sauyaba duk ko yadda suke da mugun banbanci in person. Iyayen layuza sunyi2 suraba wannan abota saboda yadda kande ke tafiyar da rayuwarta kamar ba mace ba, komi nata a tsaitsaye take yinsa tamkar namiji kasancewa duk yayyenta su takwas maza ne,ita kaɗai ce mace,se yaran kawunnanta mata biyu. Wani siririn saurayi ne yazo chamber yana wani hura hanci,tana tafiya yana kakkaɓe wandonsa da hankacif,ta inda ta ajiye bokitin awarar yabi ze wuce,be Ankara ba ta finciko rigarsa ta baya da hannu ɗaya tadawo dashi inda take tsaye tace "kai yane? Bakaga manyan guys bane zaka wani taho siii kamar dodon koɗi kana nema ka yimin tamola da bucket of my awaras" cikin broken english dinsa yace "hey u mara foka, liv my t-shirt alone,wat do you say,i will eat ur fada, daughter of air kawai". Cikin ƙaraji tace "hey wat do u nufi iye? Is me ka kira dota of air iye? Hey gayis ku cafa min shi anan gurin,Ni ze nunawa karyar turanci harda zakigina,kamar ni zaa soja of gidan ustazu habu me kayan koli,zecewa dota of air,nice ƴar iska,dama ɗan iska kace dana maka afuwa,gayis oya ku tara masa na yashi abaka" aikuwa rana rufe baki ɗan kanzaginta zakarius ya fizgo wnn lamushshsem saurayin yafara talle masa ƙeya,yana faɗin "hu are u iye?,do u know zaa soja of ƴan daddawa getto iye,zis is zaa kANDE, me awara and zaa one nd only soja of zis tawun". Dasauri wani saurayi ya taso yana cewa "easy zaa kand, baki gane wnn bane eh?". Cikin hura hanci ita adole uban daba tace "hey Boris don't firgita me, don't do yawa,kawai ka bari nasa zakarius da duna sumasa ɓalli-ɓalli a hammata,Allah wlh yanzun nan se nasa su mayar dashi kangaroo hannuwa aɗage" tafaɗa tana keɓe baki gefe. Boris yace "dawa de zaa kand wnn fa she is jikan mai unguwa Bello,kin mantashine?, tun muna yara aka kaishi bauci karatu gurin ƴan uwansu,baki gane shiba?".su adole se sunyi turanci,dama haka suke duk ƴan gang din kande Mayun turancine,dolema kayi turancin nan na dole inde kana tare da kande. Se lokacin taƙare masa kallo tace kai "Bello sagalo, innalillahi wai wnn Bello sagalo ne wanda yake shan majina muna yara, innalillahi yee gurin ya kaure da ihu,Bello sagalo haka akayi ta ihu ana kashewa,suna tambayar sa yakaratu, yanata zuba musu ƙarya yace ai yagama degree dinsa a harkar noma,shi yanzu she is piropeshonal farmer ne in d ƴan daddawa tawun. Kallonsa kawai suke suna ta ihu yana basu labarin ƙarya bayan ance musu almajiranci aka kaishi,amma se gashi yana ce musu shi yagama degree dinsa,se zabga musu turanci yake. Kande ta daga murya tace "oya kip kwayet,oya zakarius ɗauko min awarar cen kowa yasiya kuma yau ba bashi wlh, asawata(mamanta) tace kitty zatakai hospital bcos of she is not well,sbd haka kowa yau seya biya zeci". Boris yace "dawa de zaa kand wlh yunwa nakeji kuma banda ko ƙarfanfan yau,yau emti nake alqur'an,atemaka abani har gobe" kallonsa tayi tace "yawa kake zakarius eh,meye haka ne,Allah yau sede Kaci tuwon asawarka,kanaji fa nace kitty ba lfy yau Allah no loan of my awaras". Nan danan aka wawashe awarar suna tsaka daci Bello jikan me gari yace "kawarmu amma awarar nan wlh da dadi" cikin jin haushi tace "kai sagalo wlh zansa zakarius yamaka askin rabin hanci,dan me dafa muku tuwo agidanku wanene kawarku?, ni am soja,zaa one nd only soja of gidan ustazu habu me kayan koli,ko kace zaa kand,da nayi niyyar nayafe maka kuɗin awarar amma nafasa,kuma wlh dan ma awarar ta shekaran jiyace datafi hk daɗi". Duk kallon ta sukayi jin abinda tafaɗa wai awarar ta shekaran jiyace,masu lashe hannu duk aka tsaya ana kallon. Sauran guda huɗun da ta rage tace zakarius ya ɗauka ya cinye tabashi kyauta. Wato ita kande haka take duk bala'i seta faɗi gsky sede a mutu. Gata da kyauta,abunta baya rufe mata ido sam. .......... Hanyar gida ta nufa bayan tagama haɗa kan ƴan cinikinta,tana tafe tana wakar bobmali tana wani buɗa kafaɗu,duk inda ta gitta zakaji ana zaa kand tana Sa'a de mutanena, tana ɗaga hannu kamar meneman ƙuri'a. Dede wani gida madedeci yasha suminti taja birki ganin maza na fitowa daga zauren gidan nasu da alama yanzu aka idar da sallar azahar,dama idan aka aka zauna ɗaukar karatu agurin babanta se anyi sallar azahar sannan ake watsewa, gefe taja tana fito se wani kallo mazan da suka kasance samari da magidanta harma da tsoffi suke mata,wasu na mata kallon tir da ita batayi halin ubanta ba wanda yakasance babban malami a unguwar kuma liman. Yayinda wasu suke mata kallon marar kamun kai kuma marar hankali,wasu ma kallon da suke mata ma'anarsa aboye take. Ganin sungama wucewa ne tazo tana bouncing tashige cikin gidan itama,a zauren ta haɗu da babanta mlm babu me kayan koli,tana shiga tace "Sa'a de dagus, zaa imamu sannunka de da hutawa" kallonta yayi murmushi kwance akan fuskarsa cikin Muryar ustazai yace "a'a ya kande,ainafin daga gurin tallar ake ne?" "Dawa de dagus,dagacen nake kuma an siyar,duk da na faɗa musu ta shekaran jiyace amma haka suka lamushe suka caken balans ɗina,kasan innata akwai iya sarrafa hatsi,duk taurin kan hatsi yana tsoron masifar inna,shiyasa kaƙi kara aure dagus,hehehe Kai dagus nawa,zaa imamu sekayi Allah wlh" tafaɗa tana keɓe baki gefe tare da sheqewa da dariya ganin yadda baban nata sauke tabaransa yana mata kallon ƙasan ido. Cigaba tayi "wai dagus ina zawarar nan taka ne batula iye? Kasan fa cikar nan tana bala'in ƙaunarka iye, she is love you lodi lodi asswear,yawa kake imamu,kawai karufe ido kayi wuff da batula,kadena tsoron inna ni na tsaya maka,kalli batula ƴar caras da ita eyane" ganin tana neman gurin zama yasa cikin lallashi yace "ainafin yake uwata kisamu kishiga daga ciki ki kai kuɗin tallar naki,seki samu ki watsa ruwa ajikin ki ko yaa kande" sheqewa da dariya tayi tamiƙe ta ɗauki bokitinta tace kai innata Allah yasa de ƴar aljanna ce,duk ta rikita mana zaa imam da bala'in ta,imamu guda amma yana tsoron matarsa hehehe" takara sheqewa da dariya tana fito. Ball take da duk abinda yatari gabanta,tana faɗin "asswear Sena saka ƴan gidan nan adashen robobi,tunda kun zama non living things,ko Ina se kun karkasa kaya sekace gidan kutare, ƴan yawa kawai, Alqur'an inde bazaku zama living things ba sede kuyita siyan sabbin kaya,dan kullum Sena fasa wanda nagani a tsakar gida", wata matace tafito daga ɗakin ta tahau durawa kande zagi ganin tayi mata fatali da sabon bahonta data jiƙan kayan wanki,gashi se yararin ruwa yake da alama ya fashe ne. Ko kallon inda take kande batayiba ta afka ɗakin innarta ko cire takalman ƙafarta batayiba,wani baƙin cikin ne ya tokarewa umma amaƙoshi ganin ko kulata kande batayiba duk irin manyan ashariyar datake sauke mata,ga sabon bahonta agefe ruwan ciki yagama tararewa aƙasa sbd babbar hujewa da yayi,ƙwafa tayi ta juya ɗakinta inda tabar baƙuwarta. Aɗakin su kande kuwa, tasamu innarta ta idar da Salla takalleta tace, "uwar masu gida ya akayi naga bokiti, incede ba bashi kika rabar da awarar ba yauma?" "Ga balans ɗinki nan yau ba arnen dana baiwa bashi,kowa seda yaban ƙudina,kuma na gaya musu awarar shekaran jiyace datayi cimbi amma dashike hannunki na daurine sunsiye harda lamushe hannu,kai inna hoo ke,hoo ke ga masifa ga iya girki,ga kyau kamar birin wasa,zaa inna ta,matar imamu,kin mallake mana liman guda duk masifarki amma yaƙi kara aure,yafita gari ana girmama shi,amma daga shigo gida seya koma kamar zakaran da ruwa yayiwa bugun dawa,kai inna Allah de yasa kishiga aljanna" tafaɗa tana shafa ƙatuwar magen dake kwance akan gadon innarta ta,duka inna ta kaiwa kande ta goce tana dariya tace "zanci ubanki fa uwar masu gida,nikike fadawa Allah yasa zan shiga aljanna? Yo idan aljannar ta ubankice kice karya sakani". "Sa'a de inna kema kin san idan aljanna a hannun dagus take da tunkan ki sheqe ma ze wullaki cikinta,Kodan jarabar ki,ni jiyama batula ta tareni a hanya tace ina imamu nata,harda sabulu tabani" da gudu inna ta biyo kande aikuwa takwasa aguje se dakin kakarta Amo,kan ta shige ɗakin tasakeyin ball da bahon umma na ɗazu aikuwa yarabe biyu,ko waiwayawa batayiba ta afka ɗakin Amo kakarta, cikin ihu irinta bebaye Amo tace "na shiga uku takwara, waya biyoki ne kike neman kayar dani?". Acen waje kuwa inna wani aikin takama ta fita batun kande,dan tasan ko giyar wake tasha bazata fara binta ɗakin Amo ba wacce yaran gidan suke kira da gwaggo,dan ko bazata bari ta daki kande ba koda lefin me tamata balle yanzu da suke ba'a. Tana cikin haɗe kayan wanke wankenta Sega umma ta fito daga ɗaki ta rako baƙuwarta kallon banza sukayiwa inna suyi hanyar zaure, umma se sakewa inna habaici take., Ko ci kanku inna batace musu ba,sukayi hanyar waje suna ƙus-ƙus,cikin ƙasa da murya umma take cewa,"dan Allah lami ki tabbatar kinje min gurin nan,wlh kullum na kalli waccen shegiyar me suffar maza banajin na gamsu,sonake talalace takoma kamar karya,ganin ta ahaka be isheniba sonake takona magajiyar" takarasa tana kashewa lami ido,shewa sukayi suka tafa. Koda umma tadawo daga rakiya tasamu bahonta adagargaje wata ashariya me rai ta lailayi tana sakewa,"wani ɗan kaza kazane ya dagargaza mata sabon bahonta,wane tsinanne ne,ɗebabbe,tanbaɗaɗɗe", tanayi tana karasawa kusada inna,tana zuwa ta duƙa ta dau fasasshen bahon nata tana bangaje inna ai kafin tayi motsi ba biyu inna ta kwashe ƙafarta Sega umma aƙasa kamar an juye buhun dawa,ihu tasaki dede Lokacin da ƴarta Ikilima ta sanyo kai,ganin uwarta aƙasa tana zabga ihu ga inna agefe kamar batasan abinda akeyiba dan ko kallon inda umma take tule aƙasa bata kallo kamar ba ita ta juyeta aƙasanba. Aguje Ikilima ta rugo tana faɗin "innalillahi umma sannu,garin yaya kika faɗi,gashi dan baƙin hali bawanda yatemaka miki" tafaɗa tana zabgawa inna harara, cikin kururuwa umma tace "ga baƙar muguwar data kwashen ƙafa nan,sbd nayi magana akan tsinanniyar ƴarta me suffar maza,ta fasamin baho,wayyihuhu kashin aguɗina ze balle,yiiiihiii duwaiwaina". Cikin masifa Ikilima tasani ummanta tayo kan inna tana zage zage da niyyar tureta,aikuwa tana sakin umman tasake tafiya rijib tazube aƙasa tasake ƙwallah ihu,ko waige Ikilima batayiba burinta ta ture inna wacce ke tsaye tana kallon yadda Ikilima ta zaburo kamar zatayi faɗa da Sa'arta, tana zuwa gaban inna taja ta tsaya kamar an riketa takasa tureta sbd wani irin kwarjini da taga innar tayi mata,dede lokacin kande ta fito daga ɗakin Amo tagama cika cikinta da fura. Duk abinda ake tanajinsu, tana zuwa ta kwashe fuskar Ikilima da wani mari, tasa ƙafa fa kwashe kafar Ikilima tahau jibagarta sekace soja ya kama kwarto,ihu Ikilima keyi da kururuwa itada ummanta,sunata aikawa kande zagi da jafa'i kala2. Ihunsu ya janyo hankalin sauran ƴan gidan aka firfito ana kallon wnn dramar,aka rasa wanda ze kwaci Ikilima a hannun kande,seda tanata lilis sannan ta kyaleta,inna kuwa aikinsa taci gaba da yi kamar bata gurin,kande tana gama jibgar Ikilima tasa kai tayi hanyar waje tana buɗa kafaɗa da hura hanci. Seda ta fice sannan aka fara cece kuce, ana mayarda yadda akayi,umma se kururuwar ankashe mata ƴa take,tana jifan kande da munanan alkaba'i. Amo kakar su kande tana ɗaki tana kallo batasan ma me ake ciki agidan ba, kasancewarta bebiya ce,se akusa cinnawa gidan wuta da bala'i batasan anayiba. Kallon da takeyima in za a kasheta batasan me ake cewa ba,sede tayi ƙuru da ido tana kallon hoto tunda bajin abinda ake faɗa take ba. Wai wacece kande ne. _Ina masoyan MOMSANI ina wanda suka daɗe suna jiran wnn zazzafar tafiyar ta labarin kANDE,zaa kanwar maza,zaa soja,zaa kAND,to albishirinku yaude Allah ya nufa kuma yakawomu acikin wnn daddaɗan labarin me suna kANDE,bakijiba ne nace kANDE zaa tomboy_ _shin dake akayi daddaɗar tafiyar nan ta labarin Asma'u da Muhammad Mahii ,SAURAYIN YAYATA,kin karanta labarin SIRIKATA,ko a'a,to albishirinku yauma momsani tasake dawo muku da wani daddaɗan labarin me dogon zango wato kANDE THE TOMBOY,in Sha Allah hajiyata bazakiyi nadamar karanta wnn labarinba_ _zazzafar tafiyace me ɗauke da zazzafan darasi,tare da nishadi,haɗi da ban tausayi,tattareda zazzafar soyayya,gamida cin amana dakuma butulci,bazan cika baki ba,bakuma zan cikaku da surutu ba,amma in Sha Allah karki bari ayi wannan mysterious journey din batare dakeba_ *kANDE littafin kuɗi ne akan farashi me sauki, Naira ₦400 kacal,idan kin shirya ki tura kudinki fa wnn asusun0591819457 SADIKA IBRAHIM gt bank,seku tura shedar biya ta wnn layin 07088282153,se na jiku masoya,i promise u will never regret* Magoya ƴan amana Sena jiku,mom sani tana jiran ganin kauna daga gareku,love you all😘 Share fisabilillahi 🤲 🌹kANDE🌹 (_The tomboy_) Paid book. Na.*SADIKA IBRAHIM.* *MOMSANI* *Marubuciyar*: # saurayin yayata free # sirikara free And now # kANDE paid. Free page:02 Bismillahirrah manirrahim. Mlm Hamza shine sunan mahaifin malam habu me kayan koli mahaifin kande,yanada mata biyu Amina da Hafsatu, Amina (Amo)itace uwar gidansa ta Daɗe bata haihuba har seda mlm Hamza yakara aure ya auro ƴar uwarsa Hafsatu ta haifi yaro namiji ana cemasa Musa,ko shekara beyiba Allah ya baiwa Amina ciki, tahaifi namiji itama aka sanya masa Abubakar, shekarar sa biyar Hafsatu takara haihuwar namiji aka sanya masa Mudassir. Suna zamansu lfy daga baya Amina tafara wani irin ciwon kai da kunne harya kai tana ficewa a hayyacinta,idan ciwon ya taso seyayi kwana uku batasan inda kanta yake ba,anje asibiti sun kasa gano ainahin meyake damunta,haka aka koma na Hausa duk de bata canza zani ba,dg baya tafara wasu ƙuraje ajikinta kamar ƴan zufa, daga baya aka gane ashe baƙon dauro ne yakamata, duk da cewa bashida alaƙa da ciwon kanta,amma tunda aka gano baƙon dauro ne aka tashi tsaye da magani,daga wnn ciwon seya zamto batajin magana sosai,bakinta ma dakyar idan tayi magana ake gane abinda take faɗa,tun ana zuwa asibiti abu yaƙi sauki har daga baya idonta ma ya fara wani fari2,seya zamto bataji,bata gani,bata magana,hakan yasa tabar wasiyyar riƙon Abubakar a hannun Hafsatu,dan ta sakawa ranta ciwon bana tashi bane,iyayen Amina sunso su ɗauketa amma nlm Hamza da Hafsatu suka hana,Hafsatu na iya bakin ƙoƙarinta da Amina,mlm Hamza yana kan neman magani baya gajiya,cikin hukuncin Ubangiji aka kwatanta musu wani me maganin gargajiya hardana iska acen kura,datemakon Allah aka fara samun sauki,idonta ya washe haka tafara magana amma da ƙarfi,kunnenta yafara budewa ta yadda sekayi magana da karfi sannan zataji. Wannan shine dalilin zamowar Amina bebiya,daga baƙon dauro takoma bebiya,bayan tasamu sauki sukaci gaba da zamansu da Hafsatu lafiya har lokacin kuma Abubakar na hannun Hafsatu ta haɗa da ƴaƴanta ta rike. Kwatsam aka wayi gari Hafsatu ta rasu ba ciwo ba komi,daga baccin dare bata farka ba, Amina da mlm Hamza sunyi matukar yin baƙin cikin rashin Hafsatu daga baya suka dangana,se rikon yaran duka yakoma hannun Amina wacce suke kira da Amo. Musa, Abubakar, Mudassir sun kasance ƴan uwa masu son junansu,sunada hadin kai sosai,sam bazakace suɗin ƴan uba bane,saboda suna da haɗin kai,manoma ne kamar mahaifinsu, suna noma da kiwo sosai hakan yasa sukeda rufin asiri sosai. Sunyi karatu boko zuwa matakin secondary,daganan Abubakar yakoma cikin kasuwar ƴan kaba yana sana'ar hatsi da kayan lambu da kayan koli,Allah yasanya masa albarka aciki,Abubakar wanda akasuwa ake kiransa da mlm habu me kayan koli yanada tarin ilimin addini,ɗan izalane na gaske,hakan yasa da dare yake koyarda magidanta harma da samari agida,da karancin shekarunsa aka basa limami. Shida ƴan uwansa suka sake gyare gidansu suka mayar dashi sashe huɗu inda kowansu yayi aure,aka barwa Amo da mlm Hamza shashe ɗaya,mlm habu duk yafi ƴan uwansa hali,hakan yasa yake temaka musu sosai,duk rabin ɗawainiyar gidan shine,sbd mahaifinsu yanzu baya aikin komi, zaune yake agida sbd jikin girma,sun bude masa shagon hatsi anan cikin unguwa,baya zuwa ko ina kullum yana shago kusada gida. Matar mlm habu me suna A'isha mace ce me kirki da faram2,amma masifaffiyace sosai ta gaske inde aka shiga harkarta to ba mutunci,tanada kyauta sam bata da munafunci da shiga abinda be shafeta ba, itace ta fara haihuwa acikin gidan ta haifi namiji aka sanya masa sunan mlm Hamza,akwai kishin sauri sosai tsakaninta da matan su Hamza da Mudassir,sam basa sonta sun haɗe mata kai,kullum cikin zuga mazansu suke akan sun zauna basuda ƙwaƙƙaran aiki se noma,gashinan habu ya amshe girma da ragamar komi,sugasu su biyu shikuma shikaɗai amma yafisu arziki,akan haka Musa yataɓa sakin matarsa Zabba'u, wacce takasance sumumu kasau, batada hayaniya sam amma muguwa ce,ko alama bazata nuna fushi ko ɓacin rai afuskarta ba amma seta bada mamaki ta hanyar abinda zata aikata,batada mutunci,amma sam ba a ganewa,tunda aka mata saki ɗaya sbd iyalan mlm habu dashi kansa daga nan seta cenza takunta, ganin faɗan zahiri ba riba seta koma yi ta bayan fage. Seta zuga matar Mudassir Hadiza,dake ita Allah yamata bakin tsiya,batada kunya ko kaɗan,idan faɗa yahado ku duk abinda ya fito abakinta faɗa take yi kanta tsaye,sam bata ganin girman A'isha,ta tsani A'isha ga jan faɗan tsiya duk yadda ka kaiga hkr seta ƙureka ka tanka ta. Hakan yabaiwa Zabba'u damar aiwatar da yaƙinta ta hanyar Hadiza. Abangaren Mudassir tun baya ɗaukar zigar matarsa Hadiza hartaci galaba akansa ya fara adawa da ɗan uwansa,sam baya ganin ƙoƙarin mlm habu akansu. Gashi su har lokacin Allah be basu ƴaƴa ba,seda A'isha ta haifi maza shida ajere, sannan haihuwa ta tsaya mata,Hamza,Hamis, Ibrahim, Musa, Mudassir,dan sefa yayiwa ƴan uwansa takwara sannan Aminu,bayan Hadiza matar Mudassir tasaka an riƙe bakin mahaifar A'isha ta hanyar asiri acewarta dan ita komi nata ba sirri,idan ranta yaɓaci seta furta mugun alkaba'i tare da cewa mutum seya gani,hakance ta kasance tacewa A'isha seta gani akan sunyi faɗa ranar sunan Aminu. Alokacin ne kuma matar Musa ta haifi mace aka samata sunan Hafsatu,wata shida tsakani Hadiza ta haifi mace itama,Musa yayi2 da Mudassir yasaka sunan Amina amma ƴaki,sbd Hadiza tace muddin ya yarda aka sakawa ƴarta sunan amo to sede ya saketa kuma ba inda zata da ƴar sede ya kaiwa Amo bebiya da akayiwa takwara ta shayar da ita,shikuwa ba wacce yake ƙauna aduniya bayan Hadiza da ƴarsa,haka aka sanya wa yarinyar suna Hulera sunan uwar Hadiza kenan. Alokacin ne mlm habu yarasu yayi ciwon kwana biyu yarasu. Kwatsam Sega A'isha da ciki,hakan ya firgita Hadiza matuƙa dan tayi tunanin A'isha tagama haihuwa,a tunaninta A'isha bazata kuma haihuwa ba har ta mutu,hakan yasa ta sakankance kawai sede suka farga da tsohon ciki ajikin A'isha,haka tasake haihuwar ƴan biyu maza, alokacin ne akayi tashin hankali dan kiri kiri su Hadiza suka nuna baƙin cikinsu afili wai da gangan take haihuwar maza sbd ta cinye dukiyar gidan, alokacin ne suka raba gari tadena mu'amala dasu kwata2 bayan ta sauke musu kwandon hauka da shika-shikan rashin mutunci,dan ƴan uwanta masifaffu ne suma haka akayi baram baram,sam malam habu bayajin daɗin wnn rashin jituwar ta matansu,daga lokacin A'isha bata shiga harkar kowa acikin su,sbd akan fuskarta suka fada mata basa ƙaunarta itada mijinta da ƴaƴanta kuma in Allah ya yarda seta gani,hakan yasa ta tayarda bala'i sede mlm habu ya cenza mata gida sbd abinda facalolinta sukace, shikuma yace bame rabashi da ƴan uwansa, duk abinda yasamesa ko ƴaransa daga Allah ne bawanda ya isa ya cutar dasu se abinda Allah ya tsara masa. Dama shine yake taka mata birki take rage wani abun,amma dan ta ita kullum se anyi bala'i agidan,ƙiri ƙiri se a dokar mata yara amma mlm habu yahata magana,ranar da ƴan biyu suka rarrafa sukaje sashin mama suka zubar mata da gasara kashesu ne kawai Hadiza batayiba, dake tana sashen itama, A'isha na sallah sede ta dinga jin ihunsu ga ƙarar duka alamar dukansu ake,tana zuwa mama dake bakin ƙofar shashen tashige toilet da sauri, Hadiza ko bataga zuwan A'isha ba tayi nisa se zabga musu tsintsiyar kwakwa take a hannu,aikuwa kamar walƙiya A'isha tayi wani irin tafiyar yaji da Hadiza, duk kibarta seda A'isha ta kaita kasa tanata jibga, daƙyar aka raba wnn faɗan lokacin Hadiza tayi laushi se kuka take an fasa mata baki da hanci, se bayan anrabasu sannan mama tafito daga toilet tana sallallami, ko kallonta A'isha batayiba ta kwashi yaranta wanda suke ta ajiyar zuciya. Aikuwa aranar Hadiza bata kwana agidan ba dan wani ƙaton macijine yashige ɗakinta kan gado ya fasa kai se huci yake. Daga kan twins inna bata kuma haihuwa ba, kullum addu'ar ta Allah ya bata mace,tanason ƴa mace arayuwarta, gashi ba halin ta ɗauki yaran facalolinta yanzu se suce tanason ta kashe musu ƴaƴa. Ahaka Zabba'u takara haihuwar mace aka sanya mata siddiqa se Maryam, Hadiza kuwa bayan Hulera ta kara haihuwar Asiya, se Ikilima. Mama kuwa daga baya Allah yabata namiji,kusan tare suka kara haihuwa da A'isha wacce batasan tanada cikiba har seda yayi girma ajikinta,bata faɗawa kowa ba segashi sun haihu tare da Zabba'u wacce yaran gidan suke kira da Mama,aranar Hadiza har suma takusa yi saboda baƙin ciki. Zabba'u bata wani damuba ganin ta haifi namiji itama,amma sam aƙasan zuciyarta bataso A'isha wacce yara ke kira da inna tasake haihuwa ba,amma bakomi zasu gani,Hadiza de ita nata baƙin cikin afili yake amma bawanda yasan me

Chapter 1 of 7