goma zuwa sha ɗaya,sam
kamanninta ya sauya,babu wata cikakkiyar nutsuwa atare da ita,ga rashin kunya,duk wani ilimi
da take dashi yanzu babu ya gudu,takoma kamar jaka, bata da mutunci sam,ga ƙarfi kamar ba
mutum ba,ba wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa ko ya ɗagawa innarta,duk mutanen gidan yanzu
shakkar ta ake, ƙaramar yarinya amma ta addabi kowa,musamman umma da ƴarta Ikilima
wanda suke nuna sam basuda alaƙa da ita,mama de dama ba shiga shirgin kande take ba,tun
bayan da ɗanta Abdullahi yakoma sashen ta shikenan burinta ya cika,dama ba dan Allah ya
barshi a gurin inna ba, barazanar da mlm Musa mijinta yamata ne yasanya ta kyaleshi
acen,amma yanzu tunda ya dawo gurinta ba abinda ya shalleta dasu.
Abdullahi ya gudu shashen uwarsa mama ne tun ranar da kande ta tayarda aljanu, yaji tsoro
sosai ya kwashi kayansa yakoma sashen uwarsa wanda har yau wata na biyu da faruwar abin
be dawo ba,tun Inna na magana da mlm har suka hakura,mlm Musa ma be ce ya koma ba
hakan ya yi wa Mama daɗi kuwa, ɗan ta ya dawo gare ta.
Tun daga lokacin kuma Abdullahi ya fita harkar kande ya dena kulata,itama bata damu ba ta fita
iskar sa.
Dama acikin unguwar mace ɗaya ce ƙawarta layuza maƙota ne dasu inna,layuza tanada haƙuri
sosai bata cika yin fushi ba,duk masifa da bala'in kande tana shanye wa, Allah ya ɗora mata
ƙaunar kande,hakan yasa suke ƙawance,.
Tunda ɗabi'un kande suka sauya iyayen layuza suka hanata hulɗa da kande anna ta kafe ta
ƙiji,kusan kullum tana hanyar zuwa gidansu kande,.
Layuza tana tallar dafaffen dankali, kasancewar basu kai su kande hali ba,hakan ke burge
kande sosai,ita tallah mugun birgeta yake,a ƙa'idar gidansu mlm habu yaro baya tallah,saboda
sunada rufin asirin su,amma rana tsaka kande ta tayarda bala'i ita tallah zata fara,tun mlm da
inna suna ganin abu wasa har ta fara kuka tana tirje tirje ita se an yimata sana'a ta fita tallah.
Haka mlm badan yaso ba ya goya mata baya,seda ta zaɓi abinda zata dinga tallar ma,awara ita
kadai take so,haka mlm yabata kuɗi taje tasiyo rabin mudu,inna tayi mata awara,ranar da ta
fara ɗauka taci wankanta jikinta sanye da wasu riga da wando ƴan dai dai na maza tasha cover
shoe dinta babban size wanda yafi ƙarfin ƙafarta,ta ɗauki bokitin ta fito tana ƙwambo tana buɗa
kafaɗa dede umma na baiwa Ikilima sako a ƙofar shashensu da alama aikene ake bata,wata irin
dariya suka kece da ita kamar zararru,yi suke sosai suna nuna kande wacce ta tsaya sororo
tana kallonsu fuskarta a murtuƙe,dake sashen umma dana inna suna kallon juna,sashen mama
ne ke cen kusada na Amo suma suna kallon juna.
Cikin hura hanci kande ta dubesu tace "da uwar uban wa kuke ne?"
Dariyace ta sake kama su ganin yadda ta karkace baki kamar wata ƴar daba,umma wnn sauyi
na kande ba ƙaramin daɗi yake mata ba,tana rokon Allah ya dawwamar da ita haka har ƙarshen
rayuwarta,ko dama yadda ake ji da kande agidan ba ƙaramin ci mata tuwo a kwarya yake
ba,kowa agidan idan ka cire umma da mama son kande yake,har ƴaƴansu mata da sukayi aure
sunason kande, har mijin umma Mudassir idan ana zancen Ikilima batada ƙoƙari a makaranta
seyace tadinga zuwa gurin kande tana koya mata,hakan na baiwa umma haushi,amma yanzu a
kalli kanden ita kanta batasan komi ba balle ta koyawa wani.
Cikin fusata ta ajiye awararta agefe ta fisgo Ikilima ta buga kanta da ƙofar shiga sashen
nasu,ihu umma ta ƙwallah ganin take kan Ikilima ya fashe jini ya fara fita,juyowa kan umma tayi
bayan ta sake Ikilima ta faɗi kasa dafe da kanta tana ihun itama,ai umma na ganin yadda idon
kande ya juye tana mata wani kallo kamar zaki yaga nama ai aguje ta koma cikin shashen nata
ta afka ɗaki ta rufo ƙofar se zagi take aunawa kande amma ta rufe kofar.
Daukar bokitin awarar ta tayi takara gaba,awaje ta haɗu da layuza ɗauke da tiren dankalinta,
murmushi tasakarwa kande cikin murna ta matso tana faɗin "laa ashe dagaske kike,kai aikuwa
ji yadda awarar tayi kyau dagani zatayi daɗi" fuska amurtuke kande tayi gaba se banka sauri
take,ko saurarar layuza batayi,itako baiwar Allah se sauri take tanaso ta cimma kande amma
takasa.
Haka sukaje gurin da layuza take zama da tallar ta bakin wata secondary school suka
zauna,adede lokacin ne aka tayar dasu break,haka ɗalibai suka fito kamar kiranye sukayo kan
bokitin awarar kande suka yanyane kowa nason ya siya,duk da kuwa ba ita kaɗai bace me
awarar.
Seda tagama shan kanshinta sannan ta taso tabuɗe bokitin awarar ta ta tafara basu suna bata
kuɗi,tun daga ranar aka dena siyan awarar kowa seta ta,seta siyar sannan seta koma kan tiren
dankalin layuza ta zauna,nan ma a yanyame ayita siya,tas suke siyarda komi,har inna ta kara
hannun yimata awarar.
Daga gurin tallar yau gungun wasu yara maza wanda suma tallar suke kaiwa amma ba'a taba
kallonsu har se idan ta kande ta ƙare,kullum abun na basu haushi,yau suka haɗa plan akan su
tare su kande su musu shegen duka ta yadda gobe bazasu kara kai tallah gurin ba.
Tofa suwaye waɗannan masu rabon shan wahalar???
Muhadu a next pg.
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:05
Bismillahirrah manirrahim.
Sun ɗanyi nisa da tafiya kawai Sega matasan yara maza kusan su biyar,ko wanne da ƙatuwar
bulalar darbejiya a hannunsa,sun tari gabansu kande gadan gadan,aƙalla yaran zasuyi shekaru
sha biyar biyar,ba wata wata wanda yafi Kowane tsayi acikin su ya laftawa layuza bulalar
hannun sa,yana zare mata ido.
Hannu yasa ya ture kande wacce ke tsaye ƙiƙam tana masa wani kallo,sauran yaran mutum
biyu suke rirriƙe mata hannuwa suna faɗin ita hukunci ta na daban ne,su zata nunawa shigar
maza to sune maza na ainahi, sbd duk da shigar maza da kande keyi hakan be hana agane
cewa ita mace bace da kallon farko.
Dauda shine sunan yaron daya fara dukan layuza kuma ya ture kande,wanda suka riƙeta kuma
da zakariyya,da Buhari,gefe kuma wani yaro ne kamar wawa hancinsa duk majina,ya sake
baki,cikin sakalta se kallonsu yake, ɗauke da tiren dafaffiyar gyaɗarsa,ko inda ake rigimar be
matso ba yana gefe yana kallo sake da baki.
Dauda ya ɗaga bulalarsa ze sake dukan layuza wacce harta fara kuka, kamar wata jarumin
namiji haka ta fizge hannuwanta da suka rirriƙe,kamar kaji haka suka biyo hannun kamar an
januosu suka haɗe,gib goshinsu ya daki na juna,ihu sukayi suna faduwa ƙasa kowa ba laluba
kansa dan sun bugu sosai.
Juyowa Dauda ya yi aiko sejin saukar bulala ya yi ajikinsa, dukansa kande take kamar Allah ya
aikota, sekace uwarsa gashi ya fita tsayi ta haɗa da su zakariyya da Buhari se jibga take,tuni
sukayi buɗu2 da jikinsu agurin, se susar jiki suke suna kuka,seda tayi musu duka sosai kafin ta
yarda bulalar wacce duk ta karye ajikinsu.
Bello ko harararsa batayiba amma yamaƙale ajikin bishiya yanata rusa kuka,fuskarsa tayi
dameji da hawaye, ga majina yarara tanabin hancinsa har zuwa cikin bakinsa,se kuka yake
jikinsa na makyarkyata.
Juyowa kande tayi ta kallesa ai tuni ya ƙara ɓare baki Yana kuka,fadi yake tayi hakuri karta
dakesa, dan Allah karta dakesa,wata irin dariya ta kwashe da ita tana kallonsa tace "kai sagalo
na dakeka ne kake wannan kukan?" Saurin girgiza Kai yayi kamar ze tsinke wuyansa yace "a'a
baki dake niba,amma kar ki dakeni dan innarki fa baffanki yuuu wayyo Allah na" dariya take
sosai ganin yadda yake kuka sosai yana suɗe majinarsa,sak dolo.
Daka masa tsawa tayi tace "ya suna ka?"
Seda ya shanye majinarsa yace "Bello",zuwa tayi inda yake tariƙe kunnensa tace "daga yau
sunanka Bello sagalo kaji" tafaɗa tana zare masa manyan fararen idonta, dasauri ya jijjiga kai
yace "eh naji na yadda dan Allah karki dakeni".
Juyowa tayi kansu Dauda daketa kuka tace "duk kufaɗa min sunanku", da sauri zakariyya yace
"sunana Zakaria" , "nikuma sunana Buhari",nide sunana Dauda "
Seda ta sake dingure masa kai tace "daga yau sunanka Dauda duna, kaikuma zakariyya
zakarius,kai kuma Buhari boris,kunajina ko" tazare musu ido.
Kamar puppet nata haka suka dinga gyaɗa kai,tace "oya zaa goo,maza2 kutashi kubar nan
arnaye kawai"tafaɗa tana cije baki.
Aguje suka bar gurin tare da kayan tallar su, Bello wanda tasaka wa sagalo kuwa ko tiren
dafaffiyar gyaɗarsa be dauka ba ya ruga aguje.
Allah ya yiwa kande wani irin kwarjini,ko babban mutum baze iya kallon ƙwayar idonta kai tsaye
ba balle yara ƴan uwanta.
Dariya take itada layuza sunata nishadi suna mayar da yadda abin ya kasance har suka kai
ƙofar gidansu kande,dake gidansu ne farkon isa,ta shige layuza tayi gaba tana murna ta siyarda
dankalinta,ga yadda kande ta tare musu faɗa.
Wasa2 seda aka jera kwana biyar inde kande taje gurin tallah tofa su zakariyya zakarius sede
suyi cimbi,bame kallon sashe da suke balle asiya, sede sunaji suna gani kande tasiyar da
tallarta,takoma kan tallar kowa na gurin seta siyar masa bandasu, nan da nan tayi suna agurin
kande me Sa'a,kowa kande ɗalibai kande masu tallah kande,malaman makarantar ma harsun
san labarin kANDE me Sa'a.
Ana haka yauma kamar kullum sun biyo hanya kawai Sega su zakarius da uban tallarsu
akai,Dauda awara yake da yaji, zakarius kuma shinkafa da mai Buhari kuma doya da ƙuli me
mai da albasa, Bello sagalo kuma dafaffiyar gyaɗa.
Ja tayi tana kallonsu da niyyar duk wanda ya matso inda take seta zubar masa haƙura.
Amma kawai seganin tayi sun zube aƙasa suna bata haƙuri,dan Allah tayi hakuri tayafe musu ta
temaka ta cire ƙofin da tayi musu aka dena siyan Kayan sana'ar su,kuka suke wiwi suna
roƙonta,nan danan zuciyarta ta karye tauasayinsu ya kamata,mace koya takaiga taurin zuciya
mace ce kuma me rauni,balle yarinya kamar kande.
Amma ta dake tace "dalla arnaye ku tashi kun wani riƙen kafa,oya ku ajiye kayan tallar acen", ta
nuna musu gaban itacen durumi kusada wani masallaci, dassauri suka kai kayan sana'ar suka
ajiye,ana idar da sallar azahar kamar anyiwa mutane kiranye suka fara tsaya wa suna siyan
abinda su Dauda duna suka ajiye,kan awa daya ansiyarda kaf abincin da suka ajiye,aikuwa
banda ihu ba abinda suke,suna kiran se kande me Sa'a,bata rai tayi tace ita sede su dinga ce
mata zaa kand ko kuma zaa soja da turancin literature kenan.,aikuwa suka dinga fasa mata kai
suna kambabata se wani hura hanci take ita adole boss.
Tundaga wannan ranar tare suke tafiya tallar su,duk shiriritar kande basa tafiya se tazo,sedaga
baya suka san ashe duk a unguwa ɗaya suke,kawai layine kowa da nasu,kullum seta siyar da
awararta sannan take siyar musu da tasu,agidan iyayen kowannen su an san labarin zaa kAND
zaa SOJA zaa ƙanwar maza me Sa'a.
Daga baya sauransu suka dena tallar kowa ya koma makaranta,dama ana cikin hutun yajin
aikine a makarantun gwaunati,a lokacin kuma aka ɗauki Bello sagalo jikan me unguwa,aka
kaishi cen garin bauci gurin ƴan uwan babansa almajiranci.
Kande kuma atafau taki komawa school,har school authority dinsu sunzo dubata,Kuma sun aiko
da letter akan ana buƙatar ta a school dan zasuje wani debate na state kuma sunada cikakken
yaƙini da hope me yawa akan kande cewa idan akaje debate din nan da ita to ba makawa zasu
lashe,sbd turancinta ma is totally different,kamar ba a Nigeria take karatuba.
Amma wat shock dem the most shine zuwan wasu malaman makarantar da aka wakilta domin
zuwa duba kanden shine ganin yadda takoma, sam dafarko basu yadda cewa itace takoma
total tomboy ba,abin ya basu tsoro matuƙa,sannan yadda sukaga tayi biris dasu kamar batasan
inda suka fitoba ya ƙara basu mamaki,dan se wani cijewa take tana shamusu ƙamshi,ga wani
kafurin turanci da take suburbuɗo wa kamar bata taɓa sanin hanyar ajin school ba.
Wani ƙarin abin mamakin ma seda sukaga Ikilima ta shigo tanata rusa kuka,fuskarta kamar
tumatir sbd jaa dan itama farace,kuka take tana faɗuwa tana tashi,yauma de tsautsayi yasake
haɗata fada da kande.
A hanya taga kande da bokitin awarar ta ta dawo tallah,se tafiya take tana buɗa kafaɗa tana
shan ƙamshi sak de irin yara marasa ji din nan, buɗar bakin Ikilima se cewa tayi,"a'a ƴar daudu
an dawo daga aikin banzan? Allah yasa ba ƙwaƙwuleki akeyi agun tallar ba yasa kika nace
kullum se kinje,duk gidanmu bame tallah seke,mtwss aikin banza", tafaɗa tana yin gaba kamar
wata babbar mace,Ikilima a lokacin bata wuce shekara 7 ba,amma sbd tsabar rashin kunya da
manyance idan tayi magana seta baka tsoro,kuma hakan ya samo asali ne daga yadda umma
take,duk nauyin zance bata jin kunyar fadarsa agaban Ikilima,kuma abakin ta Ikilima taji cewa
wai kande ƙwaƙwuleta ake agurin tallah.
Cikin wani irin fusata kande ta fizgo Ikilima wacce tayi hanyar gida, jikinta sanye da uniform din
sabuwar private school din da mlm yasaka su itada Abdullahi, kamar jaka haka kande ke
fizgarta har zuwa gaban wani kanti, ba tsoro tare da ita tacewa me kantin "bani razor blade
yanzun nan", miƙo mata ya yi tabashi kuɗi yana cemata tayiwa yarinyar ahankali kartaji mata
ciwo,danshi ya dauka rikon wasa ne tayi wa Ikilima bawai rigima suke ba.
Da karfi ta janyo Ikilima har wani ɗan lungu daba mutane sosai,fizge hular kan ta tayi tasanyata
atsakanin cinyoyinta da karfin bala'i ta askewa Ikilima kai tas,se kyalli yake kamar silba, kuma ta
kwashi gashin ta zuba mata a jaka,Ikilima zuwa lokacin kamar zata shiɗe sbd kuka,se mulmula
take akasa tana ihu, fuskarta gwanin ban dariya,kallonta kande tayi tace "now we luk zee
same,duka mun koma maza dagani harke, nonsenseus kawai arniya" tasa kai ta wuce tabar
Ikilima agurin.
Riƙe haɓa sukayi dukansu daga mlm har teachers din bayan sungama jin jawabin komi abakin
Ikilima wacce tasha aski kamar namiji,se kuka take sherɓawa,haƙuri mlm yabata yace tashiga
ciki zaizo yasamesu itada kanden yaji meya haɗasu,dan Ikilima bata faɗi gskyr me tacewa
kande ba,cewa tayi haka kurum kande ta kamata tamata aski. Gogar kuwa tana gefe tana hura
hanci taƙi cewa komi.
Anyi anyi da ita har malam seda yasa baki amma ta turancesa tsaf da haukarta,kuma tace wlh
idan aka matsa mata seta koma sede anemeta arasa,gatade yarinya sosai amma kalaman
bakinta abin tsoro ne,sanin matsalar ta yasa Malam ya basu haƙuri da cewa suje kawai daga
baya ze lallaɓata ta dawo.
Ya faɗa musu haka ne kawai dan su tafi,amma yasan tunda ta kafe to no way out,Kuma ajikinsa
yakeji yafara nadamar hukuncin da ya yanke a kanta.
Aranar ko anyi bala'i sosai agidan dan umma wando ta sanyo tazo sashen inna wai yau ko
abata kande tamata aski ko kuma su daku da inna,mama na side dinta tanaji amma ko leqe
balle tabada hakuri,haka aka dinga bala'i harda Amo,se daga murya take tana faɗin idn umma
ta taɓa mata takwara seta saka itace ta sheme ta🤣da kyar mlm ya kashe wutar nan,dan
alokacin baban Ikilima baya gari yayi tafiya
Haka kande ta cigaba da rayuwa ba boko ba islamiyya,tunda ƙananun shekarunta ta sami
wannan nakasun, yayyenta wani lokaci har kuka suke wa mlm akan araba ta da duk wani aljani
da yake tare da ita ko an samu sauƙin wani abun,dan su acewarsu duk abinda yasameta to
haka Allah ya ƙaddara mata,babu tsumi babu dubara,amma be dace abarta da wannan aljanin
da yake iƙirarin kare ta yake ba yana lalata mata rayuwa da future nata ba.
Duk wannan sauyin marar daɗi daya samu kande hakan be hana an cigaba da jifan rayuwarta
da mummunar nufi ba,ga hassada da ƙeta kala kala,sam rayuwarta ce ba a so yanzu.
Duk da cewa ansan babu hanyar ratsa jikinta da wani sihiri hakan besa an saduda ba,dama jaki
de akoda yaushe sunansa jaki, kuma duk yadda akayi dashi seyaci kara.
Haka kande ta cigaba da gudanar da rayuwarta har kawo yanzu data girma tazama cikakkiyar
budurwa,babu abinda ya sauya sema gaba da yake kara yi,gashi bata ƙaunar sabon kaya,sede
taje gwanjo ta zaɓo abinta,gata da tsafta da ibada,amma kayanta kamar an ƙwato abakin
kura,sam bata ƙaunar guga, takalma kuwa idan ta ƙadan masa to in Sha Allahu seya dagargaje
yadena ɗinkuwa sbd wahala sannan zata dena sakawa,kuma har yau bata dena tallar awararta
ba.
Ga awarar tasu da farin jini,amma duk yadda kuka kai da kwaɗayi idan bata tashi fita tallah ba
to sede ka mutu, bata siyarwa acikin gidan,dole sede ajirata har sanda ta fito tallarta,kuma ba
kowa take siyarwa ba,taga dama ma idan ta fita tayi gun almajirai ta basu bokitin awarar tace su
raba,duk maitar me siya kuwa sede ya hkra.
Idan kuma awarar ta kwana seta faɗawa me siya,tace ta jiyace inzaka siya ka siya in bazaka
siyaba ka bari ehe.
Kamar de yau da ta kai chamber su ta samari seda ta faɗa musu ta shekaran jiyace idan zasu
siya to idan kuma bazasu siyaba su suka sani,lols.
*_cigaban labari*_
"Mama me kikeso kicemin ne?, kina nufin wai har yanzu taurarinta sunfi na duka ƴaƴana haske?
haba mama kefa babbar bokanya ce wacce ba abinda ya gagareki, atemaka asan yadda akayi
aka dusasar da hasken nata,dan Allah yasani idan ina ganinta jinake kamar na haɗiyi zuciya,na
tsani wannan yarinyar daga ita har uwarta,uwarta ita tamini katanga da auren mlm na ƙare a
auren ɗan uwansa,gashi nan har yau banida tsuntsu bare tarko, mama kitemaka min bazan iya
ƙara jurar faɗuwa ba,baze yuwu uwarta tayi galaba akaina kuma ƴarta taƴi akan ƴaƴana ba,ko
ma jini nawa ne zan bayar,wannan karon a shirye nake mama,Ajuji ya ja kwananki mama me
tukunyar sharri,".
Ta cikin madubin wata mata ce zaune da baƙaƙen kaya, ba'a ganin fuskarta sbd doguwar rigace
ajikinta baƙa me hula hoodie,ya rufe mata fuska ba'a iya gane ainahin kalarta baƙace ko
fara,sbd ba wata gaba ta jikinta dake waje.
Magana tafara kamar haka muryarta na amsawa bibbiyu..........
______________?????
Shin wacece wnn matar ta gaban madubi?,
Akan suwa take magana?
Tauraron wacece ta dusashe nata dana ƴaƴanta?
Wacece wnn matar tacikin madubi?
Muhadu a next pg.
#
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:06
Bismillahirrah manirrahim.
Wacce aka kira da Mama ta cikin madubin ce ta fara magana muryarta na amsawa bibbiyu da
sauti me firgitarwa "dolene zaki bada cikin jikin yaranki kamar yadda aka saba,sannan a yau
base gobe ba kije ki nemo mahaifar baƙar karya tare da ɗan da karyar ta haifa ki binne su da
ransu,ki tabbatar kowa be ganki ba,muddin wani ya ganki to kome yafaru dake ke kika janyo wa
kanki,kisani wannan aikin bama buƙatar kowa ya ganki ko da kuskure,in ba haka ba komi ze
lalace duka abinda kika yi ze komo kanki".
Batareda ta sake samun damar sake magana ba madubin ya yi duhu cen kuma ya washe
yakoma normal mirror,miƙewa tayi ta cire doguwar rigar da ta sanya baƙa me hula,fuska wacce
ya bayyana seda wayar ɗakko rahoto ta kusa faɗuwa,guess whoo,mama😱
_*Nigerian elite special force*_
General Asim,"munsamu wani hint gameda wadannan ƴan mata tara da aka sace,majiya me
ƙarfi ta sanar mana anfita dasu ne da sunan za'a basu aiki a Saudiyya,amma a zahiri ba haka
bane,ƴan mata uku kawai aka kai saudiyya suma da niyyar karuwanci aka kaisu bayan an
yaudari iyayensu,sauran kuma Uganda aka kai su,wasu kuma south Africa for prostitutional
purpose*
Sannan ba iya ƴan mata suke safara ba,harda yara ƙanana suke safara suna kaisu ƙasashen
waje,wasu kasuwancin sassan jikinsu ake, wasu kuma ana training dinsu ne dan su zama high
assassin's, hacker's,gays etc".
Numfashi wanda aka kira da G.Asim ya sauke,har yanzu fuskarsa tana kallon wajene be juyo
ya kalli me basa jawabin ba,ingarman namijine me ƙirar sadaukan maza,girmansa ma kawai ya
isa ya firgita me kallonsa,yanada faɗi jikinsa ko ina amurɗe,ya goya hsnnuwansa abaya,jikinsa
sanyeda kakinsu na special elite force,yanada yalwar suma me tsayi baƙi siɗik,dan har ɗaurers
ya yi ta baya, hannunsa daya goya wasu irin jijiyoyine kwance akansu muscles ta ko ina,hannun
kawai zaka kalla kasan ba baƙin mutum bane haka kuma ba fari bane,fatarsa chocolate color
ce,sak Ethiopian.
Wani ne yasake shigowa office din yasara musu kafin lieutenant general Habib yace masa "ya
akayine Captain Abdul?" Wata takarda wanda aka kira da Captain Abdul ya miƙa masa yace
wannan saƙon general ne"amsar envelope ɗin L.G Habib ya yi yace "tnk u captain" seda
yasake Sara musu kafin ya fita,har lokacin G.Asim be juyoba.
Tabbas abinda L.G Habib yake faɗa ya ɗauki hankalinsa amma babban abinda yafi damunsa a
yanzu shine be wuce yacce yakama matarsa ta aure tana zuba masa poison a abinci
ba,matarda sukayi auren soyayya amatsayinta na ƴar uwarsa,duk da cewa da farko be wani
damu da ita ba,amma daga baya haka kurum yaji duk duniya ba wacce yake so da ƙauna irin
Meerah.
Shiko wace irin rashin Sa'a ce dashi har haka,ace aure har biyu amma babu matar arziki a
cikin,shi yasani ba duka aka taru aka zama ɗaya ba dole acikin dubu akwai ɗaya zakka amma a
ina? wani guri? "Hmmmmmm" ya sauke gauron numfashi yana juyowa tare da sanya
hannuwansa acikin aljihun wandon kakin jikinsa.
Subhanallahi wa bihamdihii,fatabarakallahu ashanil khaliqiin,wani irin halitta ne me wata irin
fuska wacce kai tsaye bazakace ga daga jinsin daga yakasance ba, wani irin sassanyan kyau
ne dashi me sanyaya zuciyar me kallonsa,kyakkawa ne ainun,shi ba fari ba shiba baƙi
ba,haɗaɗɗene wanda ya amsa sunan sa me kyau,kai tsaye zaka iya kiransa da giant rocky
hanmson.
Fuskarsa meɗan tsawo da faɗi,laɓɓansa jajaye ne pure red,manyan piercy silver eyes,darked
brows,pointed nose,he's just damn hamson,_General Asim Al-Amin Muhammad_ the general
commander na elite special force,bangare na musamman wato (ALPHAH).
Kallonsa L.G Habib ya yi yace "abokina kana lfy kuwa?anya kana bacci acikin kwanankin
nan?kalli yadda idonka ya sauya,nd u look so pale,tun shekaran jiya kake cikin damuwa amma
ka ƙi kafaɗa min,pls tell me my friend ko Meera ce?"
"Hmmm, exactly Habib meerahhhh" sekuma ya yi shiru,ya sunkuyarda kai don wani irin zafi
zuciyarsa keyi,jiyake kamar yanzu ne yaganta tana zubawa.
"Ehen tell me ok?" Cikin lallashi Habib yake tmbyr sa, kuma ga dukkan alamu damuwar babba
ce tunda har yakasa faɗa kai tsaye, "calm down bro,kasan barin kashi aciki baya maganin
yunwa,pls tell me friend,kasan koda yaushe problems told is half solved always umm,so kafaɗa
mini menene ya faru da meerah".
Cike da jin ƙwarin gwiwa yace "L.G i caught meerah red handed poisoning my food, she's trying
to get rid of me,5 wat bloody reason huh? I loved nd care 5 her,cherish her,na bata full asset to
do wat ever she want with her lyf nd my wealth, or giving her freedom is a crime? Habib pls tell
me am i not worth to be loved huh?*
Habib nakasa ganewa kaina gaba ɗaya ya kulle, menene atare da ni dayasa mata basa sona?
Aure biyu duka ba dan Allah suka aure niba,duka kowa da tashi matsalar da ta sanya suke
tarayya dani,kowacce she's after my lyf for wat reason for goodness sake?"
Jikinsa har rawa yake idanunsa nan take suka kaɗa sukayi jajir,dasauri Habib ya tashi ya ɗakko
ruwa me sanyi acikin deep freezer din dake office din yazuba a glass cup y miƙowa Asim,ba
musu ga amsa ya kafa kai seda ya shanye,kara zuba masa Habib ya yi har sau uku har ruwan
ya ƙare kafin Habib ya daga kafaɗar sa yana matsawa a hankali,jan ajiyar zuciya kawai Asim
yake kafin Habib ya fara magana cikin taushin murya.
"Haƙiƙa Sameerah ta aikata babban kuskure,kuma dole fa fuskanci hukunci,yanzu abinda
nakeson sani shine tasan ka ganta ne a lokacin da take zuba maganin?" Girgiza Kai Asim ya yi
idonsa a lumshe, yace "kwana na biyu anan ba koma gida ba,tun ranar da naganta banyi
making any sound ba na baro gidan,kuma na kashe wayata,kasan baze yiwu naje gidan hjy
kwana ba dole zata gane akwai matsala,das y I decided to stay here at d office,tunda i have
everything her just lyk home,hjy ma kiranta kawai nayi nafaɗa mata aiki ya riƙe ni bazan samu
zuwa gurinta ba".
"gud,yanzu abinda za muyi shine ka kunna wayarka", ba musu Asim ya ɗakko wayarsa ya
kunna,tana gama loading saƙonnin barkatai suka fara tseren shigowa,kafin kiran meerah ya
biyo baya,alamar ya ɗauka Habib ya masa ba musu ga ɗauka yasa a handsfree "oh tank
goodness u on ur phone honey,Ina ka shiga ne haka,kabarni da tunani duk ka tsorata ni, are u
ok babe,pls talk to me,I was so worried dabaka nan,U scared me love"
Sauke numfashi ya yi bayan ya kalli Habib alamar kaji makira ko,ido Habib ya masa alamar yy
magana, seda yaja numfashi kafin yace "hey meerah am alive ok,ban mutuba kamar yadda
kikaso" cikin daburcewa tace "am eh na'am baby wat do mean?wat are you saying?" Gabanta
na mugun faɗuwa, murmushi taji ya yi tacikin wayar yace "relax bay am just kidding u" wata
wawuyar ajiyar zuciya ta sauke har seda Asim da Habib suka kalli juna,cigaba da magana ya yi
"wani aiki ne ya tsareni kwana 2,it's urgent shiyasa nayi zamana har komi yazama steady amma
don't worry ok,Ina lfy ina nan dawowa soon prepare something delicious for me nd my kiddo,see
you soon I have a big surprise for you".
Thumb Habib ya nuna masa kafin yace raɗawa Asim wata magana a kunne,kallonsa Asim ya yi
yace "baka ganin ya yi sauƙi yin hakan,da wlh niyyata na azabtar d ita Sosai,amma bakomi
wannan shawarar ma tayi,tank u so much friend,barinje zuwa gobe zamuyi magana akan ƴan
matan nan".
Sallamar juna sukayi Asim ya nufi hanyar gidansa tare da convoy na mototinsa da security
ɗinsa.
Wani irin gidan naga an nufa a unguwar Nassarawa GRA,gaban wani gida me kamar na
president suka nufa,tun kafin su karasa wasu sojojin ne suka buɗe masu tangamemen gate din,
danna hancin motocin sukayi zuwa cikin ƙaton mansion ɗin,sojoji ne birjik acidan na
security,seda suka wuce gate biyu bayan na farkon,duk gate din da suka wuce wasu daga cikin
motocin zasu tsaya,har suka dangana dana ƙarshe kafin motarsa ta shige ita kaɗai,aguje wata
farar siririyar mace ta rugo jikinta daga ita se wata half lassy gown shoulderless brown wacce
tasake fito da ainahin kalar farinta, Dede sanda ya fito daga cikin motar tana zuwa ta ɗane
ajikinsa rana ihu kamar ƙaramar yarinya,kanta ta tufƙesa amma sbd yadda ta ɗanesa aguje