mama take ciki tunda ita mijin nata yaƙi
ɗaukar zuga.
Kasancewar inna a asibiti ta haihu wnn karon daga ita se mijinta, dan ƴan uwanta ma seda aka
sallamota sukaji haihuwar, ba wanda yasani har uwar mijinta Amo hakan yasa seda suka dawo
snn ƴan gidan sukasan ma haihuwa tayi kuma mace,ƴan uwan A'isha ƴan bala'i ne basuda
mutunci haka suka dinga kiɗe kiɗe suna shewa da guɗa an haifi kANDE,ranar suna yarinya taci
suna Amina,anyiwa Amo takwara ba zaman lfy lols,seya kasance kamar ba suna biyu akeyi
ba,ƴan uwan Aisha sun cika gida an kashe kuɗi anyi ɓarna sosai da kuɗi da abinci da nama,
sam bazakace wai ana wani suna a sashen Zabba'u ba,dan da gayya ƴan uwan Aisha suke
wani abun dan niyyar su ana tankasu se sun ci uwar mutum.
Wannan yaƙara girmama baƙin cikin Hadiza kuma taci alwashi sosai akan seta lalata rayuwar
ahalin A'isha,inda mama Zabba'u ko ajikinta tunda de ta haifi namiji to ai angama komi,yaro yaci
suna Abdullahi.
Tare kande da Abdullahi suka taso se suka tashi kamar twins, sam basaji ko kadan tare suke
zuwa makaranta Arabic da boko kullum se ankawo kararsu ko sun daki yaran mutane ko sunyi
wani abun,gasu da ƙoƙari amma sam basaji,kullum mlm habu na hanyar makarantar
su,shekararsu biyar amma sam basaji,a lokacin umma takara haihuwa ta haifi Ikilima,daga
lokacin se haihuwa ta tsaya musu duka matan gidan.
Kande irin yaran nan ne da ake kira gifted, duk abinda aka karanta mata sau ɗaya yashige
kanta kenan ba maimaici,nan take take ɗauke abu a kanta,tanada zuciya sosai batason
reni,gata yarinya amma ƙoƙarin ta har tsoro yake baiwa inna da mlm, shekararta biyar amma
tana iya karanta duk ayar da aka janyo acikin Kur'ani,sbd idan mlm habu na koyarwa a zaure
itada Abdullahi suna gurinsa,hakan yasa duk yadda wasa ze dauke mata hankali baya hanata
ɗauke abinda taji an karanta koda ba ita ake gayawa ba.
Kande ta tashi cikin tsananin soyayyar uwa da uba,ga yayye maza kowa kande, sunan da
kakarta tasaka mata kenan Amo,itace take kiranta da kande ko kuma tace takwara,A'isha (inna)
kuma tace uwar masu gida,wnn suna yana ƙonawa umma da mama rai,gabaki ɗaya sun tsani
yarinyar ganin duka ƴan gidan kowa yana son kande, hatta ƴaƴansu ba wanda ya dakko baƙin
halin uwarsa.
A cikin yaran Zabba'u siddiqa ita tafi kowa sanyi,yarinyar batada hayaniya sam,ga ilimin addini,
baruwanta.
Yaran umma kuwa kusan dukkan su basu da hayaniya bakamar itaba,Ikilima ce kawai tayo
halin uwarta.
Matan kusan duk sunyi aure, Hafsatu, Maryam,yaran Zabba'u duka sunyi aure, siddika ce kawai
ta rage se Abdullahi autan mama.
Yaran umma ma Hulera da Asiya duk sunyi aure suma.
Kaf unguwar ansan gidansu kande gidane na ƴan izala masu ruko da addini,dan su Hamza
daga malamin islamiyya se alaramma,se wanda ke kasuwa gurin kasuwanci,suka sunada aikin
yinsu,bame zaman banza, twins kuwa suna jami'a.
Ko daga waje duk wanda ze shigo gidan to ina kande shine abinda ze furta,duk ta dusashe
tauraron sauran yaran gidan,tun mama na damuwa harta gaji ta saki,umma ce kullum cikin
wahala, batada aiki se jifan kande da inna da mugayen alkaba'i,inde akan inna ne bata furta
alheri.
Haka baba Musa komi ya samu kande,ko yace wnn na uwar masu gidane, Abdullahi ko kamar
bashi ta haifeshiba ganin tasa tazo ɗaya da kande hakan yasa yaron ya tattare kayansa ya
koma ɗakin inna.
Ankai ruwa rana sosai da mama, dan ta kafe akan ɗanta baze zauna agurin innaba, duk ƴaƴa
maza da Allah yabata amma se ɗan gudalenta za a ɗauka awani baiwa inna,hakan yajanyo
baba Musa yace idan takara tayarda zancen abakin aurenta,dan shi yana ƙaunar ɗan uwansa
mlm habu,kuma sam baya ɗaukar wargi, hakan yasa baya iya hanasa ɗan uwansa duk abinda
ya nema,duk da cewa bashi ya nuna yanason ya rike Abdullahi ba amma ganin yaron nason
zama agurin inna yasa yake jin nauyin amsarsa,dan gani yake kamar idan Abdullahi yabar gurin
inna mlm habu zeji ba daɗi.
Mama tanaji gana gani aka rabaga da ɗanta,bata wani damu sosai ba dan tasan inna ba
maƙetaciyar mutum bace,dan kular da ze samu agunta ko ita wacce ta haifeshi se haka.
Kwatsam wata rana aka baiwa kande scholarship daga makarantarsu zuwa babbar makarantar
nan ta m.m. Haruna English academy, alokacin shekararta goma,tagama primary zataje
secondary,dan jumping aka dinga yimata, ga haddar izu talatin akanta na Kur'ani.
Haka akayi ta murna agidan ana tayata farin ciki,inna kuwa har sadaka seda tayi.
Yayyenta maza kuwa kowa seda yabata kyauta.
Ranar ta ta farko a school.......
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:03
Bismillahirrah manirrahim.
Tun ranarta ta farko a makarantar tayi kawaye yaran masu kuɗi,tasaje da yaran masu kuɗi
itama saboda irin kalarsu gareta,farace sosai,tanada tsayi ba lefi,gata da hanci da manyan
ido,idan tana magana bakinta kamar bashi ke motsi ba,siraran lips ne da ita,fuskarta oval
shape,sumar hanta tana da tsayi sosai,ga saje daya biyo ta gaban kunnen ta,tanda 1 side
dimple, kyakkawar gaske ce,yarinyace amma jikinta a murje yake sosai,fatarta tanada matuqar
kyau,snn gashin ta ba baƙi bane wuluk,akwai ruwan golden brown aciki hade da baƙi suffarta
daban take kamar ba ɗiyar hausawa ba.
Ga ƙoƙari kamar alhuda-huda,komi aka fada mata sau daya ya zauna akanta kenan koda ba a
ajinsu bane,hakan yasa satinta uku aka fara shirin yimata promotion zuwa j.s.s. 3,ranarda
takoma gida tana murna tare da takaddar gayyata izuwa ha mlm habu,koda su umma sukaji
labari nanfa bala'i ya tashi akan sede asaka Ikilima da saddiqa da Abdullahi a m.m. Haruna,duk
da cewa siddika tana shekarar ƙarashe ne amma haka umma ta dinga bala'i,mama de uffan
bata cewa,tagaji da yiwa inna hassada tunda kullum Sa'a a gefen inna da iyalanta yake.
Kwatsam rana tsaka aka dawo da kande dg school tafaɗi,sunkaita clinic na makaranta an
dubata har drip ansaka mata amma sam taƙi ta farfaɗo,hankali tashe inna ta shinfiɗe ta,anata
shafa mata ruwa taki farfaɗo wa, Amo kuwa banda ihun kuka ba abinda take,murya a sama
irinta bebaye take faɗin,duk wanda yake son ganin bayan jikarta karya bari ta ganosa dan seta
yi masa rashin mutunci,haka taketa zabga bala'i tana ihu irin ta kurame.
Haka mlm habu yadawo ya samu autarsa unconscious,addu'a kawai yake tofa mata,haka ya
karanta wasu manyan surori aruwa yace inna ta shafe mata jiki,yin hakan ko keda wuya ta
farka,kamar robot haka ta miƙe tsaye batareda jikinta ya lanƙwashe ba,a tsorace inna ta matsa
tana zare ido cike da faɗuwar gaba,duk yayyenta dake ɗakin ba wanda be tsorata ba ganin
yanayin da ta farka aciki.
Fuskarta tayi kore sosai,jikinta ma haka,idonta yakoma ɓaki duka ko ƙwayar fari babu,cikin
buɗaɗɗiyar murya kamar ta maza tace "lahuhu irmati gidigam gam,abukanwatur fadurma gim
gam" kamar wata bokanya haka take furta wasu irin dalamisai,jikinta banda jijjiga ba abinda
yake,bakinta har wani hayaƙi yake fitarwa, nan take dakin ya fara jijjiga kamar ze ruguje,cikin
ɗaga murya mlm habu ya fara karatun suratul baƙara,yi yake da karfi, nan take su Hamza suka
ɗauka,da karfi suke karatun, Amo na gefe se tsandara ihu take kamar ana yankata, ta tsula
fitsari yakai sau biyar,sun rungume itada inna se kuka suke, Amo se ihu take tana gwalanci wai
nan addu'a take.
Ihu kande tafara yi tana jijjiga kamar ba mutum ba,cen tayi wata irin gigitacciyar ƙara wacce duk
maƙotansu seda sukaji,gashi marece ne anata kiraye-kirayen sallar magrib, ihu take tana susar
jikinta kafin takara yanka wani ihu me karfin da yafi na baya tazube aƙasa ta zauna kamar ƴar
bori, still su mlm habu basu dena karatunba sema wasu manyan ayoyi da suke sake janyo
wa,kamar a mafarki tafara rera karatun tare dasu,idan suka cenza aya itama tacenza har suka
yi shiru,amma ita seda takai ƙarshen aya.
Zuciyar mlm habu akarye cike da firgicin wannan sabon al'amari daya riskesu yau,amma Cikin
dakiya ya buɗa muryarsa babu wasa yace "wanene kai? Me kake yi ajikin ƙanƙanuwar yarinya
irin wnn? Ko ta yimaka wani laifin ne da ka zaɓi shiga cikin jikinta,kuma ga dukka alamu sun
nuna cewa kai ɗin musulmi ne".
Cikin wata babbar murya marar hayaniya akace "Assalamu alaika ya Imam Abubakar bin
Hamza,Tabbas ni muslumi ne kamar yadda kaji,kuma sunana Muhammad Arun ɗan Sarkin
aljanun baihak,ni musulmi ne,kuma ni ɗin na kasance ajikinta tun tana cikin cikin
mahaifiyarta,sannan ni ne wanda nake bata kariya bisa umarnin kakana muzgar".
Jikin inna da Amo banda rawa ba abinda yake,yayyenta ma dauriya kawai suke,domin abin
babu daɗin gani kwata kwata halittar jikinta ya sauya kamar wani ƙaton gardi, ga wasu jijiyoyi
sun ratsa mata a damtsen hannunta,gashi daga ita se vest da leggins.
Jinjina kai Malam habu ya yi yace "tabbas nagani kuma naji kai ɗin musulmi ne,amma shin me
wannan yarinya ta aika maka,ko ta cutar da kai ne dayasa ka bayyana akanta ko kuwa?".
"Babu ɗaya daga cikin biyun tambayoyin ka,wato zancen gsky naso nayi zamana shiru
batareda na nuna wata alamar cewa ina tare da itaba,amma hakan baze taɓa yiyuwa ba,anyiwa
goɗiya wani mummunar sihiri wanda akaso bayan tagama wulaqanta tayi mummunar mutuwa.
An sadaukar da jini ga baƙaƙen aljanu an tura su jikinta da mummunar niyya,kuwa hakan
yakusa yin tasiri sakamakon bama tare da ita a lokacin ,munyi wata doguwar tafiya zuwa ƙasar
misra domin gabatar da wani yaƙi acen tsibirin asgarul mundal, sannan mun nasaka fararen
rauhanai a domin bata kariya da kuma gadinta kafin mu dawo,amma se akayi rashin Sa'a
baƙaƙen aljanun da aka turawa goɗiya sunfi ƙarfinsu,hakan yasa sukayi nasara akansu har
suka raunatasu,duk da cewa mun bar wani kariya ajikinta hakan yasa sukayi kwanaki bakwai
suna fama kafin su sami nasarar shiga jikinta ta hanyar wacce tayi mata turensu,tabata ɗan
wake taci,acikin ɗanwaken akwai wani magani wanda ya karya garkuwar da muka bari atareda
ita,a jiya ne muka sami nasara akan baƙaƙen aljanun da suka addabi tsibirin da mukaje
yaƙi,cike da azama muka dawo gareta kwatsam se mukayi arba da shugaban baƙaƙen aljanun
da muka nema muka rasa a fagen yaƙi, yana shirin ɗaukar rayuwar goɗiyarmu,wanda da hakan
ta kasance to tabbas da sede mu mutu atare da ita, domin rayuwar mu gaba ɗaya sadaukarwa
ce ga ahalin goɗiya.
Kakan goɗiya ya taba temakon kakana alokacin da yayi ɓadda kama amatsayin ɗan Adam
kuma almajiri, lokacin kakana ba musulmi bane,amma karamcin da kakanta yayi masa yataɓa
zuciyarsa,har ya amshi musulunci,a dalilin haka yasa yake bibiyar ahalinsu.
kakanta ya temaki kakanmu, yana saurayi a lokacin batareda ma yasan cewa aljani yatemaka
wa ba,a hannun kakanta Abu Rayyan kakana ya amshi musulunci,hakan yasa kakana ya tara
iyayenmu yabasu labari kuma ya umurce su da amsar musulunci tare da faɗa musu lalle su
kasance masu baiwa ahalin Abu Rayyan kariya har ƙarshen rayuwarsu.
Mun kasance tare da mahaifin goɗiya kafin faruwar wani babban al'amari, daga baya kuma
muka koma gareta tun acikin cikin mahaifiyarta,.
Tabbas makashinku na tare daku, tabbas anaso a salwantar da rayuwar goɗiyarmu hakan yasa
muka riƙe baƙin aljani Gandamul arzu bawai dan bazamu iya galaba akansa ba, a'a sedan
munaso ya bayyana ajikinta akan idon ku,yaso tserewa tun da sa'ar da mukayi arba da juna
aɗazu,amma na riƙesa sakamakon munaso kufara hukunta sa da kanku da ayoyin Allah,ya yi
iya yinsa dan ganin be iso nan ba,sbd yasan karonsa da mlm ba zeyi masa kyau ba amma sam
bamu basa damar yin hakan ba.
Niyyarsa ya aiwatar da abinda aka aikosa yakama gabansa batareda ya iso gidan nan ba
amma bamu basa damar guduwa ba.
Shine wanda ya fara bayyana ajikinta sakamakon ruwan addu'a da aka shafa mata, seda muka
tabbatar kun ƙonasa da ayoyin Allah ta yadda baze ƙara moruwa ba kafin muka barsa ya
fita,fita ta har abada bakuma ze ƙara gigin shafarta ba".
Se yanzu ta sauke numfashi idanunta arufe,cikin sanyin jiki malam yace in Sha Allah babu
abinda wani mahaluki ya isa ya yi agaremu face abinda Allah ya tsara mana.
Tabbas munji daɗi kuma muna gdy bisa kariyar da ka kasance kana baiwa ƴarmu,amma kasani
mudin bil adama ne babu wani haɗi tsakanin mu daku, muna godiya matuqa amma dole zaka
bar jikin wnn yarinya,idan kayi duba da ƙarancin shekarunta sbd haka ina gamaka da Allah
akan kayi haƙuri ka barta".
Ido rufe kuma cikin wata murya wacce ta fi ta farko ƙarfi da firgitarwa tace "wannan ne kuma
bazamu iya yi muku alqawarin aikatawa ba,zamu tafi yanzu,bazamu kuma bayyana ba,kuma
zamu ɗauki mataki dede gwargwadon abinda aka aikata wa goɗiyar mu,sannan zamu aikata
wani al'amari atareda goɗiya wanda muka tabbatar shine kariya agareta kuma zaman lafiyar
kowa aciki harda ku,duk abinda zata aikata kar wanda ya ƙalubalanceta akai,tabbas komi
yanada lokacinsa, kuma idan lokacin da muka dibarwa hukuncin da zamu yanke ya kai to
tabbas komi ze bayyana.
Mlm Abubakar bin Hamza tabbas kaiɗin mutumin kirki ne,ka kasance me aikata alheri akoda
yaushe,kuma me saka sharri da alheri,saboda haka karka ce zaka ɗauki wani mataki akan
hukuncin mu,zamu tafiiii amma kusani muna tare da goɗiya akoda yaushe,domin nauyin kare ta
yana rataye a wuyan ahalinmu,wannan alƙawarine.
NATAFIIIIIIII...., KUMA ZAN DAWOOO...."
Wata babbar hamma kande tayi kafin ta tafi yaraf ta kwanta kamar ta mutu, wani nannauyan
bacci ne ya yi awon gaba da ita.
A lokacin sallar isha'i ake kira,jikin malam habu amatuqar sanyaye yatashi tasake tofe kande ta
addu'o'i,wacce banda gumi ba abinda take,dukama wanda yake ɗakin ya haɗa uwar zufa.
Se a sannan inna da Amo wanda idonsu yajiƙe sharkaf da hawaye ya kumbura suka saki
junansu,kaka Amo kamar abin tsafi duk abinda ya wakana taji raɗau kamar ba bebiya ba.
Zuciyoyin duka wanda suke cikin ɗakin ɗauke da tambayoyi masu yawa amma kowa ya bari har
lokacin daya dace kafin ya furta.
Haka mazan suka fito daga ɗakin jiki a sanyaye,akan idon mlm habu yaga gittawar mutum da
gudu ya yi hanyar waje.
Girgiza Kai kawai mlm habu ya yi dan sarai ya gane ko wanene,kawai shiri ya yi,kuma yasawa
ransa koma menene da yaddar Allah baza ayi nasara akansu ba.
Haka kande ta share kwana biyu batasan inda kanta yake ba,kullum se malam yamata tofi
aruwa ashafe mata jiki.
Yau kamar a mafarki inna tana sallar azahar taga wani abu kamar inuwar mutum ya tsaya
adede kan kande.
🌹kANDE🌹
(_The tomboy_)
Paid book.
Na.*SADIKA IBRAHIM.*
*MOMSANI*
*Marubuciyar*:
# saurayin yayata free
# sirikara free
And now
# kANDE paid.
Free page:04
Bismillahirrah manirrahim.
Kafin inna ta karasa setaga kamar wannan inuwar ta faɗa ajikin kanden.
Saurin miƙewa tayi bakinta ɗauke da addu'o'i ta nufo inda kanden take akwance,tana zuwa
dede lokacin kande ta buɗe idonta wanda sukayi jajir jini ya kwanta acikinsu kamar an zuba
mata,baka ganin farin cikin idon ko kaɗan,tana gani tar amma idon yayi mata nauyi.
"Alhamdulillah" shine abinda inna ta furta tana kama hannun kanden datake miƙa mata.
Jikinta yayi mata nauyi sosai bata iya motsa ko ɗan yatsan ta,kuka inna keyi ƙasa ƙasa,ta janyo
wayarta keypad tana dannanwa mlm habu kira, alokacin shi kuma ya shigo cikin gidan
hannunsa ɗauke da wata gora ta ruwan addu'a, Kasancewar an idar da sallar ya sallami
ɗalibansa masu ɗaukar karatu,tare suka shigo da twins wanda suka dawo sbd ciwon kanden.
Dasauri mlm habu yakarasa shiga ɗakin yana tofa mata addu'o'i,ahankali yace "mamana",
bakinta yamata nauyi sosai amma ta ɗaga idon ta wanda yake nan gwanin tsoro sbd yadda ya
koma ta kallesa,hakan yabashi tabbacin ta dawo cikin hankalinta,
Sake tausasa murya ya yi bayan ya janyota daga kwance ya mayar jikinsa ta jingine dashi ya
sake cewa "kingane wacece wnn?" Yafada yana nuna inna dake durƙushe kusada gadon tana
hawaye,ganin yadda fuskar ƴar ta ta ya kumbura sosai bakinta abushe idonta babu daɗin kallo.
Jinjina kai tayi a hankali alamar ta ganeta, "waɗannan fa?" Ya nuna su twins wanda suma
hawayen suke,dan akwai shaƙuwa me tsanani tsakaninta dasu kamar ba saƙonnin ta ba,duk
ma yayyen ta maza suna matuƙar ƙaunarta,sake jinjina kai taji a hankali,amma ba magana.
Hamdala mlm da inna sukayi,gorar ruwan addu'a mlm ya ɗakko ya yi bismillah ya kafa mata
gorar abaki,ba musu ta amsa ta fara sha da sauri, sefa tayi rabi kafin ya cire mata ta
huta,sannan ya sake miko mata ta amsa seda ta shanye tas,kaɗan ta bari ya zubaa hannu ya
shafa mata afuska sannan ya ajiye gorar.
Lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta fara yinƙurin amai,da sauri inna ta miƙo mata
wani ƙaramin baho aikuwa tafara sheqa wani irin amai baƙiƙirin dashi,harda wasu abubuwa
kamar kwalba, aman babu kyan gani,ga wasu abubuwa kamar tsutsa se motsi suke,seda
takusa yin rabin bahon kafin aman ya tsaya mata,takoma jikin mlm tana sauke wani wahalallen
numfashi,ba jimawa wani baccin ya sake kwasheta.
Shimfiɗeta mlm yayi yasake tofeta da addu'a kafin suka sake fita.
Seda takai la'asar tana bacci kafin ta farka,cikin ikon Allah koda ta farka idonta ya fara washewa
kuma harta iya tashi da kanta ta zauna, Amo na gefe se zare ido take,dazarar taga kande zata
kallo ta setayi maza ta ƙara damƙe carbin ta,murya asama take istigfari,dan wlh tsoron bala'i
kanden ke bata,ganin take har yanzu al janun na nan basu tafi ba.
Inna ce tashigo ta kamata suka shiga toilet takai mata ruwan zafi wanda mlm ya yi mata tofi
aciki,inna tayi mata wanka dan har lokacin jikinta babu ƙarfi.
Tea me kauri inna ta haɗa mata da ruwan addu'a wanda mlm ya yi mata shi dayawa komi nata
inde naci ne ko nasha to da wnn ruwan za'ayi mata amfani,har wanka.
Duk wannan abin da ake yi umma bata leƙo sashen ba ko sau ɗaya,mama de ta shigo sau ɗaya
ta tsaya daga bakin ƙofa tace Allah y kafa afuwa tayi gaba,ko takalma bata cireba balle tashi
ɗakin.
Duk da inna taji zafin abinda suka mata amma taji daɗin yadda mama tazo ta duba jikin
ƴarta,koba komi de tazo,tafi umma wacce ko bakin ƙofar sashen bata leƙo ba.
Seda kande ta shafe sati ɗaya kafin ta fara magana, maganar ma me ban mamaki dan kamar
wata namiji haka take magana tana wani karkace baki gefe,da farko abin dariya ya baiwa inna
hartana cewa "haba uwar masu gida,daga buɗe baki kuma se shegan taka,meye haka kamar
namiji?" Tafaɗa tana murmushi.
Cikin cijewa kande tace "yo inna da mecece ni ɗin,ai ni namijice kawai totally,kallifa duka
yayyena maza ne" tafaɗa tana nuna su Hamza da su Hamis da twins dasuka kalli juna., saboda
haka nima namiji ne kuma soja zan zama in Sha Allah.
Ya Musa yace "haba auta ke mace ce,kuma kyakkawar yarinya,ƴar autar inna da malam,jikar
Amo kallifa ji sumarki me kyau da ita ga tsayi".
Kallonsa tayi tace "Allah ko ya Musa,wannan gashin shiya sake saka wa nake kama da mata
ko? To yau base gobe ba zan askesa,Sena je an aske mini shi".
Kamar wasa tafara acting kamar namiji,duk kayan da inna ta ɗakko mata ta sanya setace sam
bata sonshi, ita sede anemo mata riga da wando su zata saka.
Tun Inna na kallon abun a matsayin wasa har tafara jin haushi,cikin fusata tace "zanci ubanki
fa,ki tashi ki saka kayanki,tun ɗazu kin sauna da ɗaurin zani,karki bari raina ya ɓaci", se mafifa
inna take.
Nan take idon kande ya cenza tayi tsaye ƙiƙam taki motsi ta sunkuyar da kanta gashinta ya
zubo ya rufe mata fuska,inna tayi magana har ta gaji amma shiru babu amsa,ganin hakan yasa
ta sakko ta fara lallashi da ban baki,amma shiru kamar tanayi da dutse.
Matsowa inna tayi ta dafa kande tana yimata waƙa kamar yadda take mata idan tayi fushi,
amma ko alamar zata motsa babu,janyota inna tayi da niyyar rungumeta amma taƙi janyu
wa,sema ji tayi kamar ba mutum take jaba, kamar gini haka ta maƙale agurin, cikin tsoro inna ta
saketa taja da baya,aguje ta ruga zuwa zauren gidan tana ƙwalawa mlm kira, jikinta banda rawa
ba abinda yake.
Arikice ta fada zauren inda mlm ke tsakiyar karatu da ɗalibansa,da sauri ya tashi yana
tarota,cikin sauri kuma ya janye ta sukayi cikin gidan yana tambayar ta meya sameta harya
firgita ta haka,inna banda rawa ba abinda jikinta yake se nuna masa hanyar ɗakinta take,ta
kasa magana hawaye se zuriya yake akan fuskarta.
Hanyar ɗakin ya nufa da ita,amma ta cije a waje taki shiga,baiwar Allah Inna banda rawa ba
abinda jikinta yake.
Sakinta mlm ya yi yashiga ɗakin yaga kande a halin da take,bakinsa ɗauke da addu'a yake
nufarta,haka mlm ya shafe tsawon lokaci aɗakin kafin ya fito yana sharce gumi.
Yana fitowa Sega kande abayansa tana faɗin "inna yunwa nake ji wallahi,dan Allah kiyi mana
ɗan wake", jikin inna be dena rawa ba ta kalli malam,jinjina mata kai ya yi alamar bamatsala.
Cikin ɗari2 inna tace "to auta in Sha Allah,zoki amso mana fulawar", inna ta fada tana miƙo
mata naira dubun da mlm ya bayar,cikin murna ta yi hanyar waje daga ita se ɗaurin zani a ƙirji
ko ɗan kwali babu akanta,ga dogon two color hair dinta dakenan har kusada mazaunanta
yanata tashi iska na kaɗa mata shi,kamar ba ƴar hausawa ba,da sauri mlm yace "a'a uwata
kawo na bayar a amso muku", haka tundaga wannan ranar kande ta koma me siffar maza.
Bawai jikinta bane ya koma siffar mazan, a'a,tana nan a yadda take,kawai de gabaki ɗaya
yadda take gudanar da al'amaran rayuwarta ne ya koma na maza,inna batasan ya akayi ba se
ganin kan kande tayi an aske mata rabin sumarta, normally sumarta ta kai har ɗuwawu amma
kawai se wayar gari akayi an yanke Mata fiye da rabi yakoma kamar na namijin ba indiye.
Shigarta da komi nata sak namiji, school ma ta dena zuwa,ɗan karatun ta da ake taƙama dashi
aka nemeshi aka rasa,bayan fatiha babu abinda kande ke karanta wa daidai,a fannin boko
kuwa ɗum,kai ya koma kamar na kifi bata gane komi,tunrancin da yazamewa bakinta kamar
yaren ta na usuli shima aka nemesa aka rasa,komi nata kamar an juya mata shi,tamkar yadda
ake juya riga daga Dede takoma baibai.
Ada ta kasance me yawan son turanci,har bayan samun matsalar ma bata dena son yin turanci
ba,amma fa kafurin broken english take kwaɓawa,baƙaramin ciwa turanci zarafi take ba,idan ta
kwaɓa wani turancin se dariya ta kusa kashe mutum,amma ita ko ajikinta,ta fuske,ita adole
turancin gaske take.
Ga baki daya rayuwarta tayi juyin waina acikin tanda,yayyenta maza abun ya yi musu ciwo
sosai,gashi sun kasa samun wata gamsashshiyar amsa daga iyayen nasu,sude sun san tun
sa'adda tasamu matsalar jinnu din nan bata kuma samun kanta ba,kullum da abinda zata fitar
sabo arayuwarta.
Tun ranarda sukayi ƙungiya sukayiwa inna ƴar tsure tare da jefa mata wata nannauyar tmby
wanda yakusa zautar da jin ta,har girgizar da tayi sanadiyar tambayar su ya bayyana afili,nan
take ta fatattakesu sbd rashin gamsashshiyar amsar da zata baiwa ƴaƴan nata.
Hakan yasa suka juya tmbyr izuwa kan mlm,tabbas shima ba ƙaramin jijjigashi tambayar tayi
ba,amma dayake namijin gaske ne shi be nuna ya firgita da tmbyr ba.
Cikin dakiya mlm yace "Hamza me kace?,me kuke son sani gameda lalurar ƴar uwarku
ne?bayan komi akan idon ku ya faru,kuma duk abinda aljanin yafada kunji da kunnenku".
Maimaita tambayar Hamis ya yi cikin kwantar da murya yace "am mlm dama cewa
mukayi,menene gaskiya akan abinda muka ji aljanin kan auta ya faɗi?shin wanene Abu
Rayyan,menene dalilin da ya sanya gabaki ɗaya rayuwar auta ya cenza,kuma munga baka
ɗauki kowanne mataki ba,kamar ma abinda take yi yanzu baya damunka,gashi mutanen
unguwa harsun fara gutsira zantuttuka akan sabon tsarin rayuwar da ta ɗakko a yanzu,sam
sekace ba ƴarka ba,komi nata ya sauya,mlm dubi yadda takoma sak namiji,kuma ma dakanka
ne kabata kuɗi tasai irin tufafin da maza suke sakawa,wanda kaine ka koyar damu cewa duk
namijin da yake kamanceceniya da mata to yanada babban zunubi agurin Allah (s.w.a),haka ma
ga macen ta take kamanceceniya da maza,harfa yanke gashin kanta tayi,wanda yin hakan a
addini shima haram ne,gashi yanzu bata tsoron kowa,shekaran jiya nan naga ta kama Ikilima
tamata shegen duka seda ta yimata targaɗe a hannu,mlm dan Allah kafaɗa mana menene
asalin abinda yake faruwa wanda mu bamu sanshi ba,kuma wanene ABU RAYYAN* a iya sanin
mu kune iyayenmu,kuma aduk cikin kakanni mu bamusan wani me suna abu Rayyan ba,mlm
kai masani ne wanda Allah yabashi baiwar ilimummuka me tarin yawa,kuma abinda take yi Sam
ko a addini be dace ba,idan ma sbd aljanun kanta ne ai Allah ya baka sani ta yadda zaka
magance komi batareda an bar wani aljani ya sauya mata rayuwarta hakaba,ka gafarcemi mlm
idan na faɗi abinda ya sosa maka rai,bada nufi bane ".
Dogon numfashi mlm yaja kafin yace "duk naji abubuwan da ka faɗa kuma tabbas maganganun
ka gaskiya ne,amma abunda nakeson ka sani,duk wata cuta Allah be halicce ta ba har seda ya
fara saukar da maganinta, sannan idan ka lura gaba ɗaya rayuwar auta maƙiya ne a kewaye da
ita wanda nasani kuma kun sani,tun kafin bayyanar wannan aljanin atare da ita ansha neman
nakasta rayuwarta wanda ku ƙila a yau kuka san wannan,akwai aljanun da zaman su atareda
mu bil adama babu alheri wanda hakan kesa muke yin duk yadda zamuyi araba wanda suka
shafa dasu,akwai kuma nau'in aljanun da zaman su atareda mu wata kariya ce daga Ubangiji*
Tabbas rayuwar auta ta sauya kuma babu wani wanda hakan kewa daɗi daga Ni har
mahaifiyarku,kuma duk yadda zakuji ciwon sauyawarta baku kai mu ba tunda mune muka
kawota duniya,kuyi hakuri kubata lokaci,idan kun lura harda kuruciya a lamarin uwata,in Sha
Allah komi ze dedeta da izinin Allah*
Ni nasan abunda baku saniba,wanda in Sha Allah idan lokacin kusani ya yi tabbas ba makawa
se kun sanshi,rayuwar auta akwai wasu manyan sirrika wanda lokaci ze bayyana su,kuyi hakuri
ku bata lokaci,kuma ina roƙon ku kar wanda ya hanata abinda take ko ta nema,inde befi ƙarfin
ku ba ina neman alfarma abata,sannan Abu Rayyan bakowa bane kawai zancen aljanin
ne,nagama magana kutashi kuje Allah ya yi muku albarka".
Sam mlm be basu damar yin wata magana ba,kuma tabbas sunajin cewa akwai abinda mlm be
faɗa musu ba,amma kamar yadda yace komi lokacine suna fatar lokacin nan ba anesa yake
ba,dan duk wanda yasan auta ada yarinya me hankali ga ƙoƙari ga son karatu,to ba ze yadda
itace ta koma yadda take a yanzu ba,yarinya ƙarama me shekaru