Share this page
5 / 9
ita dai Aira bataji me Dayan bangaren aka ceba saiji tayi Aysha ta ce " Okay Baby ka shigo zaka ganmu da marun Abaya"bata katse wayarba suka hangoshi yana nufo su aysha murmushi ya kasa barin fuskarta harya karaso ya zauna chair din kusa da ita. "Aira dai na kallonsu kawai take Shima ba laifin yana da kyau gashi Daga gani kamar akwai Naira Aysha cikin farinciki tace" Nayi missing naka my baby Tunfa sanda ka kawomun ziyara rabon da muga juna kusan 5months ta fad'a tana shagwaba "Shima cikin so da k'auna ya Ce " Miss you too my prince's kinsan yau ba cikin k'aramun farinciki nake ba na ganinki sannan ya kalli Aira da take kallonsu ya ce . "Dear ko ita ce k'anwar tamu da ake ji da ita " Aysha tace "Eh baby itace " Aira ko "yafada yana kallon Aira murmushi tayi ta ce " Eh ina yini "Lafiya qalau kanwarmu y school gsky yayarki Naji dake fa kusan kullum saitayimun maganarki" murmushi Aira tayi ta ce "Ai nima ina ji da ita sosai " Aira najin Aysha da Saurayinta na zuba love ita dai cikin ranta mamaki take daga karshema barin wajen sukayi suka koma Dan nesa da ita tana nan zaune rik'e da wayar Aysha taji wani yayi mata sallama ba tare da ta d'ago ba ta amsa . "zan iya zama Hajiya" Ba matsala ta fad'a ta na kauda kai"y'an mata bazaki kalleni ba "yafada yana murmushi kamar bazata d'ago ba sai kuma ta d'ago ta ganshi wani dogo mai matsakaicin jiki ya sha shaddarshi me kyau. kauda kai tayi yana b'ata rai Dan bata son takura " ina yini Hajiya Sannu da hutawa"Lafiya "ta fad'a ta na kauda kai" Kamar bazai magana ba saikuma ya ce "Tun d'azu na hangoki ina son nayi maki magana kikamun kwarjini na kasa Sai yanzu dak'yal nayi shahada na taho Dan na fad'a maki abunda ke cikin zuciyata Gaskiya tunda nake bantab'a ganin macen da ta burgeni ba sama dake nayi yawo wurare da dama Amma bantab'a cin karo da macen da sace zuciyata kai tsaye ba idan ba ke ba fatan baza a watsamun ruwa a k'asa ba za a amshi tayi na hannu bibbiyu" . Aira ji tayi kamar ta shakeshi Dan Haushi tace "d'an naci a zuciyarta amma a fili cewa ta yi" Kayi hakuri ni bana soyayya a gida an hanani"Saiki fara a kaina na tabbatar zan sanyaki farinciki "tsaki taja cikin ranta ta ce " maye "Nan yayi ta mata magana da magiya tayi banza ta Kyaleshi Suna Haka Aysha ta dawo ita kad'ai ga Alamun saurayin nata ya tafi Tana ganinta Aira ta mik'e ta ce " Aunty Aysha mu tafii". Kallon Aysha saurayin yayi ya ce "Auntynmu ina yini" murmushi Aysha tayi ta ce "lafiya qlau brk da hutawa" yawwa Aunty gwarama da Allah ya kawomun ke nasan zaki taimakamun ki shawomun kanta tun d'azu nake nan amma ank'i bani dama gimbiyar tawa dai ga alama akwai mulki "Dariya Aysha tayi ta ce " karka damu Insha Allahu zanmata magana haka take "kai amma nagode Wlh Aunty kinyi taimako amma ya sunan gimbiyar tawa" Hajara Amma ana ce mata Aira"wow so sweet name "nikuma suna na ABUBAKAR YUSUF MADUGU”ni D’an sokoto ne nazo bikin aboki na ne ni bakone a garin nan. Ah Babban suna sunan Abbanmu"cewar Aysha " kice ina da manyan y'ay'a to yanzu Aunty yaza ayi naga kamar Sauri kuke zaku wuce ko zaki taimakamun da number ta"wlh bata da waya yanzu kam"to Dan Allah kozaki taimakamun da taki saimuyi magana"ba matsala Aysha ta fad'a tare da karantomai number ta. rafar y'an 500 ya Aje musu Aysha taki amsa dak'yal ya samu ta amsa tare da mashi Godiya ya wuce "Aira ko duk Haushi ya isheta saitajima mutumin duk ya bata Haushi ga haushin Aunty Aysha da ta biye mai. A mota Aira ta kalli Aysha ta ce " Aunty wannan Wanda yazo wajenki d'azu waye"baby Abdulkarim kenan Boy friend d'ina ne kuma mijina insha Allah tafada tana murmushi wara idanu Aira tayi cike da mamaki ta ce "To Aunty yaushe har kuka hadu keda kika tafi karatu kuma nasan kafin ki tafi Abba baya barin kowa zance " Dariya Aysha tayi ta ce "Aira kenan kede kawai ayi sha ani amma ni tun ina s. S three nake soyayya ta a b'oye kawai dai ina nunawa Abba ne amma soyayya ta nake ke yanzu fa kai ya waye akanme ace Y'an mata gand'ama gand'ama damu ace ba samari yaushe garin zai waye my Abdul a Airport muka had'u dashi tun lokacin tafiyata karatu ta farko tun daga lokacin muke soyayya ina sonshi sosai Shima haka yana ziyarta ta chan akai akai munshaku sosai Dan tun bayanzu ba yakeson muyi aure na ce yayi hakuri ya jira lokacin da Na gama karatu gashi yanzu kuma alhmdllh yanzunma maganar ce mukayi nace ya samu Abba yanzu ba wannan maganar ba Wannan Sadiq din yana da hankali wlh sosai ga nutsuwa ki nutsu Kuyi soyayyarku saina dinga had'aku kinji kanwata baki da matsala dani ba meji". Turo baki Aira tayi ta ce "Ni Gaskiya Aunty kibar zancenshi ni baimun ba bama wannan ba kinsan Abba ya hanamu nikuma bazanyi Abunda ya hanaba Gaskiya gwara Na hakura nayi karatuna kawai yanda yakeso din"galala Aysha tayi tana kallonta tana tuki ta ce "Amma wlh Aira baki da wayo to maza kiyi sakakka irin na Aunty Maryam ta biye Dokar Abba harta gama Karatu bata da saurayi Abba ya had'ata da d'an Abokinshi dukda ba wani sonshi sosai take ba ta hakura danma yanzu suna son juna Amma ai Kinga batayi mata dad'i ba b'ata auri Wanda takeso ba To wlh kika biye kema haka zakuyi nidai ba ruwana tunda na kama My Abdul Dina" . Tab'e baki Aira tayi ta ce "Uhm Aunty yaya Arman fa Yama hanani kula samari fa kuma nayi mashi alkawari bazan kula kowa ba " galala aysha tayi ta na kallonta ta ce "Ke amma sakaraice ma Hajara har wani Arman ne zai hanaki kula samari to idan baki kula samari ba ubanwa zai Aure ki ko Shi Arman d'inne zai Aureki iyeeeeee kujimun ikon Allah " Aira daram Gabanta yayi irin mummunan fad'uwa jin Kalmar Aunty Aysha ta k'arshe "Ko shi Arman d'inne zai Aure ki?????!!!!!..............✍🏿 *Ni da Yaya Arman Book1 ne Free Book2 Ba free book ba ne Na kud’ine Book one zai k’are ne daga Page 30 daga nan za mu shiga Book two kai tsaye Ba tare da Gargada ba zaku iya fara biya tun kafin a k’are Book one zaku turo katin MTN #200 ta wannan number 07026166536 tare da shaidar biyanku ta 07026166536 y’an niger kuma ku bini pc ta number nan dana d’ora +2347026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain a ciki* _Normal group = #200_ _PC = # 300_ _V t u # 300_ *Sainajiku masoyan asali na tabbata bazaku tab’a nadamar sayan littafin nan ba darajarshi tafi ta #200 kachal na barshi ne hakan kawai saboda kauna da soyayya ga masu buk’atar a tallata musu hajarsu su tuntub’eni kai tsaye a number wayata kamar haka 07026166536 zamuyi ciniki cikin sauk’i insha Allahu sainajiku Masoyan asali na tabbata bazakuso ayi zazzafar doguwar tafiyar nan babu ku ba*👯‍♀️🙇🏽‍♀️🙇🏽‍♀️🙇🏽‍♀️ *Share fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [6/2, 09:31] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏 Hot love story♥️🔐 ```MALLAKAR``` *Hajara L Sadeq* 📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚 بسم الله الر حمن الر حين *BOOK ONE*📔 🅿️...............21&22 Sosai gabanta ya fad'i sai yanzu ma ta tuna da Dan ayi Aure ake soyayya Shiru tayi ta na ta sak'e sak'en a ranta Tanajin Aysha nayi mata fad'a tayi mata banza ta kyaleta Har suka isa gida Suna isa Aira kai tsaye Part din Inna ta nufa Dan lokacin har Angama kiran magriba. "Bayan tayi salla a palourn zaune tayi tana lazumi kafin ta tashi innace ta shigo ta na fad'a tana cewa " Haba nidai wlh ana wahalshe dani ace Dan kinibibi Kamar Rahama god'ai god'ai da ita Bata iya wankan jariri ba koma ta iya Dan iskanci batayiwa d'anta wanka ba saini to zanga Ranar da babuni ubanda zai dinga musu ai duk gani na ne ya kawo hakan malalata kawai tun daga zamaninmu aka dena haifo mutanen kwarai Wai kamar Rahama da in Auren k'auye ake y'arta ma saita Aurar da Y'a Amma tsabar iskanci sai an wahalshe dani ". Aira na jinta tayi mata banza Dan ba kowani fad'an inna take tankawa ba " Tsaki Inna taja ta kalli Aira Dan ta tsani tana fad'a a mata banza in ba a bata hakuri ba gwara ko tankawa kayi ta ce "Ke kuma y'ar gidan malalaciya Daga gidan ubanwa Kike Rabonki da nan tun azahar ina kikaje " Tsaki Aira taja tare da tashi tayi bedroom d'inta ta na jin Inna na cewa "Uwarki da ubanki kikayiwa tsaki ba niba fitsararriya mai ido a tsakar ka " Murmushi kawai tayi dan yau ba y'an fad'an take ba shiyasa bazata biyewa inna ba ta na shiga d'akin ta kulle Dan yau batajin ko dinner zata iyayi sbd ciye ciyen da sukayi a waje. Ta na zuwa Sauri tayi ta cire kaya ta fad'a toilet ta yi wanka tana fitowa tasa kayan bacci ana kiran isha I nan ta tada salla saida ta gama ta tashi ta ninke hijab ta d'auko k'aramar wayarta da babba ta baje kan Gado wara idanu tayi ganin missed call d'in Arman rututu a k'aramar wayarta cikin Sauri ta Danna mashi kira saida ta katse tukwana ya kira cikin Sauri ta d'aga ta ce "Hello my Yaya ina yini" Ajiyar zuciya taji ya sauke daga bangarenshi ya ce "Nayi ta kira Baki d'auka ba ina kika shige" Sorry yaya wlh Aunty Aysha ce tazo shine na rakata unguwa"Yaushe tazo?Dazu "da ina da ina kikaje" gidan kawarta muka fara zuwa daga Chan muka wuce wajajen shakatawa amma waje biyu kawai mukaje muka dawo"Ita Aysharce daga dawowarta zata d'aukanmunke ku tafi yawo me yasa da zaku tafi baki fad'amun ba kafin nan ma wasu kaya kika fita da su? "sorry yaya na manta ban fad'a maka ba Bansa matsatsun kaya ba wlh doguwar Riga ce a ma baje take Aunty Aysha ta sayo mana Nida ita idan kana soma saina turo maka hoton ka gani"ba sai kituroman ba na yarda Amma fad'amun Gaskiya akwai saurayin da yace ya na sonki?gabanta ne ya fad'i sai sannan ta tuna da Sadiq cikin y'ar in ina ta ce "ya ya ba kowa" Aira kenan a tunaninki Idan kikayimun k'arya bazan gane ba baki saba karya ba Dan haka duk sanda kikayi ganewa nake oya fad'amun Gaskiya"Kamar zatayi kuka ta ce "To yaya bazakayi fad'a ba " Eh bazanyi ba gsky kawai nakeson ki fad'amun" Ajiyar zuciya ta sauke nan ta bashi labarin had'uwarsu da maganarsu da Aunty Aysha bata b'oye mashi komai ba "Sosai ranshi yayi mugun b'aci cikin fad'a da masifa ya ce " Ita Aysharce daga zuwanta har zata fara koya miki biye-Biyen Samari," "yaya Dan Allah kayi hakuri "Tafada kamar zatayi kuka " Cutie bakiyimun komai ba Amma Aysha tayi mugun bani mamaki Yazama dole gobe na shigo garin na kad'e mata warning Sannan duk sanda ya kirata ta baki ko kika bashi number ki kukayi mu'amula ko soyayya Allah ya isa ban yafe miki ba kinsan dai Mahimmancin Allah ya isa sarai(😆😂oh ni Arman hada Allah ya isa sai kace ubanta). Sosai Aira tayi mamakin kalaman Arman wai Allah ya isa Amma dayake tasan idan ranshi ya b'aci saida lallab'o tafi kowa iya zama dashi shiyasa ta ce "To Yaya Bazanyiba Goben da gaske zaka zo" ta fad'a ta na son sauya maganar "Eh cutie zanzo Amma kwana biyu zanyi na juya" Cikin murna Aira ta ce "Amma Naji dad'i my yaya Allah ya kawomun kai lafiya" Ameeen my Cutie ya fad'a tare da cewa Good night kiyi bacci yanzu nasan kingaji"murmushi tayi mai cike da so da k'auna ta ce "Have a nice dream yaya saida Safe". Tana kwanciya bacci yayi awon gaba da ita washegari Suna Yaro yaci suna Abdullahi za ana cemai Ameer sosai gidan ya cika ranar da mutanen Arziki Kanwar Abbansu Aira ma dake Aure a Kaduna Mama Halima tazo tare da y'arta Hafsat sa'ar Aira ce kuma kawarta ce sosai Ranar Aira jinta take cikin Farinciki duk inda tayi Hafsat na biye da Ita Da misalin k'arfe biyar na yamma sosai Aira tayi kyau cikin Wani tsadaddan lace black and blue sai ratsin pink sosai ya amshi farar fatarta batayi wata make up kamar koda yaushe hoda da kwalli kawai ta shafa Sosai tayi kyau kamar ka saceta ka Ruga a lokacin ta na bedroom d'inta dake d'akin inna Bayan ta gama shiryawa ta feshe jikinta da turarruka masu k'amshi drawer gefen gadon ta ta bud'e cike yake choculate kala kala kamar kaje Kanti duk Wanda yaya Arman yake saya mata ne manya biyu kawai ta d'auko ta fara sha Dan yunwa takeji sosai tunda safe rabonta da abinci Dan ita daman haka take batacin abincin sabga Nan Tasha hotunan ta sosai tana gamawa tayi status a what's app tana ganin amfara comment akan hoton ta maza ta kashe datar ta sauka wayarta ce k'arama tayi ringing ganin Yaya Arman ne ya sanyata picking cikin Sauri ta ce "Yaya Badai har kazo ba " Daga bangarenshi ya ce "Yanzu haka ina bakin gate d'in gidan Inna " Tsalle ta daka ta safko daga Gado ta ce "Wow Sannu da zuwa yaya ka shigo mana" bazan shigo ba cutie Naga akwai mutane a wajen kinfi kowa sanin ban fiya son taron mutane ba Kidai fito Kawai " "to yaya ga ni nan "ta fad'a ta na saurin Saukowa daga gadon cikin Sauri ta boye babbar wayarta a locker ta rik'e k'aramar takalmi da gyale ta zira tayi Sauri ta fito a palour ta tarar da mutane gaishesu tayi ta fita A farfajiyar gidan ta gamu da Hafsat Hafsat ta ce " Aira ina zuwa naga kina shirin fita"Taho ki rakani wajen YAya Arman zani" Dariya hafsa tayi ta ce "Ah koda nace wannan show d'in kice love za a sha wannan k'auna keda Yaya Arman har yanzu akwaita kenan" Murmushi Aira tayi tanajin dadi har cikin ranta ta kama hannun Hafsa ta ce "Ai kauna ta na nan Hafsa *NI DA YAYA ARMAN* Mutu ka raba Dariya Hafsa tayi ta ce " Allah yarda ni daman najima da sanin soyayya kuke wlh"wara idanu Aira tayi ta ce "Rufamun Asiri waya fad'a maki soyayya muke kawai dai k'auna ce muke " Uhm idan tayi tsami dai maji cewar Hafsa suna fita suka tarar dashi a cikin mota back seat driver na gaba Zage glass din motar yayi ya tsaya kallonta sosai ta tafi dashi ba k'aramun masifar kyau tayi mashi ba baisan lokacin da ya sakar mata murmushi ba Itama mayar mashi tayi Dan sosai yayi mata kyau cikin Dakakkiyar shaddarshi da Tasha aiki fara Hafsa ce ta ce "Ina yini Yaya" Lafiya qlau Hafsa yau a gari"murmushi tayi ta ce "Wlhko Yaya Suna mukazo tare ma muke da Mama " Aira ce ta shagwabe ta ce "Yaya bazaka fito ba wai ka hakimce a cikin mota" Dan murmushi yayi ya ce "So kike na fito a gama kalle maki ni wannan wankan nakine ke kad'ai" Dariya tayi ta ce "Wayau dai kawai cikin shagwaba ta ce " ni fa yunwa nakeji ba abunda naci tun dazu"wara idanu yayi ya ce "Subhanallahi garinya aka barmunke da yuwa" Yaya ban iyacin abincin Taro shiyasa"ai zama bai ganmu ba maza-maza shigo muje restaurant yanzunnan" ya fad'a yana bud'e mata Kofar da yake ciki Kallon Hafsa tayi ta ce "Sis taho muje" Girgiza kai Hafsa tayi ta ce "A a kije kawai Sis Mama ta ce Zan rakata gidan Daddy su gaisa Dan muna sa ran gobe zamu koma " To shknan saimun dawo Aira ta fad'a tana shigewa batare da shakkar komai ba Restaurant mafi kusa ya kaita saida ta tabbatar da ta koshi tukwana suka fito Suna shiga mota Yaji kiran daddy yana d'agawa nan Daddy ke shaidamai akwai Wani metting da za ayi karfe Tara a Zaria kome yake ya maza ya tafi Zaria yanzu yaje ya wakilceshi da to Arman ya amsa mashi Kallon Aira yayi da take latsa Wayarshi ya ce. "Cutie zamuje mu saukeki a gida yanzu Tafiya ta kamani zanje zaria zan wakilci Daddy wani metting " Yaya Dan Allah ka tafi dani Daman bantab'a zuwa Zaria ba Saidai mu wuce ta cikinta in zamu wuce Dan Allah kaje dani"tafada ta na marairaicewa "Rik'e hannunta tayi ya ce " Kiyi Hakuri my cutie Amma bazaiyu na tafi dake Zaria da Daren nan ba Kuma idan munje dinma bamusan tsawon lokacin da za a d'auka ba kiyi hakuri next time idan nazo zan daukeki da kaina na kaiki kiga ko ina da rana " "nidai Allah yaya ban yarda ba katafi dani kawai " Dafe kanshi yayi ya ce "Aira case Ce " to so kike na tafi dake na ja maki fad'a a gida Kin manta dare ne Zaiyi"Yaya wlh har muje mu dawo ba maiji ni daman b'angaren Inna nake kuma bamai sanin ma Inda naje"Ba yanda Arman baiyi ba Dan kar ya tafi da ita amma ta nace daga karshe ma kuka tasa mai hakan yasa ba yanda ya iya dole suka tafi tare tana ganin an tafi ta sauke ajiyar zuciya sai murna take daman ita tanason tafiyar mota a rayuwarta karfe takwas da wani Abu tayi musu a Zaria Rasa Inda ma zaikaita yayi hakan yasa ya yanke shawarar kaita gidansu Wani abokinshi kafin su gama metting d'in Abokin nashi ma bai gari mamanshi ta amshesu hannu bibbiyu Daga nan Arman ya wuce wajen metting d'inshi Hankali kwance nan Aira taci abinci sai nan nan y'an gidan suke da ita Dan Arman ya ce Musu kanwar sa ce Aira ganin Har 10Arman baizoba tana ta jiranshi Har bacci yayi awon gaba da ita. Arman ko metting d'in saida ya jasu Har 11:30 hankalinshi duk ya rabu gida biyu ga tunanin Aira daya baro. Koda ya koma maman su abokinshi hanashi daukarta yayi ta ce su barwa safiya ba irin yanda bai yiba amma ta hana tace bazasu tunkari hanya da Daren nan ba ga kidnappers da sukayi yawa suyi hakuri su barwa safiya ba yanda Arman ya iya sai hakura yayi yaje ya kama hotel ya kwana Aira ko tana baccinta bata San wainar da ake toyawa ba saida ta farka da asuba Ta ganta a wannan gidan Kan Gado Sosai gabanta ya fad'i ta ce. "Na shiga ukku ba dai a gidan nan na kwana ba " Sai sannan ta tuno da gida ba Wanda yasan Inda take Cikin firgice ta tashin hankali ta tashi Kanwar Abokinshice ta shigo Dan tada ta tayi salla Tazo ta isketa harta tashi Wanka Aira taje tayi ta mayar da kayan jikinta ta fito suka bata break fast mai rai da lafiya taci tana gamawa Arman yazo Godiya sosai Arman yayi musu tare da alheri Aira ma Godiya tayi musu dukda firgicin da take ciki. B'angaren gidan su Aira basu lura da Aira bata gida ba sai wajen 11pm Inna ta rikice ta nufi part din su Mamy ta fad'a musu Aira da bata gida Nan aka shiga nemanta lungu da sak'o ba a ganta ba Sosai suka shiga tashin hankali musamman Mamy hada kukanta Har 1 ana neman Aira ba a ganta ba ranar kwanan zaune sukayi Bcci saidai barawo. Hafsat ce da tasha baccin ta wajen Asuba ta farka Taji kamar ana neman Aira lokacin duk suna palourn Inna sunyi jugum Hankali tashe har Abba daya kasa zaune ya kasa tsaye inna ko inbanda kuka ba abunda take Hafsa dake bacci jikin mamanta ta ce "Mama Wai Aira ce bata dawo ba kowa" Duk kallonta mutanen dake palourn sukayi a tare sukace "ko kinsan Inda take ne Hafsa" Tashi tayi ta ce "Eh jiya dai da Yamma wajen magriba Yaya Arman yazo Nina rakata wajenshi tace yunwa takeji zaikaita joint taci abinci da tare zamuje saina ce Zan raka mama gidan Daddy shiyasa lokacin da muka dawo ni nazaci ma harta dawo" "Salati dukansu sukasa musamman Mamy kuka ta fashe ta ce " Na shiga ukku Airance tabi Arman suka kwana waje"Abba ko Shi kadai yasan yanda yaji a cikin ranshi safa da marwa kawai yake yama rasa wani irin hukunci zai yanke mata "Inna ko Salati ta rafka ta ce " ku bari sudawo muji dalili Dan nasan Tarbiyar Mujahed da Hajara sarai bazasuyi wani abunda bai kamata ba ni har hankali na ma ya kwanta tunda tare take da d'an uwanta"duk kallon mamaki suka bi inna dashi saikuma suka Jinjina kai Abba ko ya kasa magana sai safa da marwa da yake "Mama Halima ce ta ce " Dan Allah yaya ka kwantar da hankalinka Tunda dai anji Inda take sai a jirari dawowarta"Cikinsu ba Wanda Abba ya tankawa shi kadai yasan Zafin da yakeji cikin ranshi. Aira ko tun a mota take yiwa Arman kuka tasan yau Abba yasan bata kwana gida ba ta shiga ukku kasheta zaiyi tun yana Lallashinta har ya rabu da ita 7:20 tayi musu a Kano Kai tsaye gidan Inna suka isa Ba yanda Arman baiyi da ita ta fita ba amma taki sai kuka ta ke "tausasa murya yayi ya ce " "Kinga irin haka nake guje miki shiyasa Banso kika Bini ba Amma kika dage yanzu ki kwantar da hankalinki ki shiga nasan ma bazasu Gane ba Tunda Bangaren inna kike kuma inna ba d'akinki take shiga ba shiru Aira tayi ta na tunanin kuma hakane k'ilama Allah ya rufa mata asiri basu sani ba Kallonshi tayi cikin sigar shagwaba ta ce. "To bazaka rakani ba yaya" Idan na rakaki wani zai iya ganinmu Amma idan kikashiga ke kad'ai ba mai ganewa zaisu zaci ma kinfita ne sayan wani Abu Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Hakane Yaya to sai Anjima " Murmushi yayi mata ya ce "kije ki k'ara hutawa saimunyi waya Ko na shigo" gyad'a mai kai tayi bata samu damar ma mayar mai da murmushinba ta nufi bakin gate a hankali ta kwankwasa mai gadi ya fito ya bud'e yana mata kallon mamaki. Ajiyar zuciya Aira ta sauke ganin farfajiyar gidan ba kowa Arman ko yana ganin shigarta ya sauke ajiyar zuciya driver ya jashi suka tafi Aira ko gabanta na fad'uwa haka ta tinkari k'ofar d'akin. saida ta tofa addu'oi tukwana ta yi bismillah ta tura kofar a hankali kamar Munafuka tana bud'ewa tayi turus ganin Duka mutanen Gidansu a palour zata iya cewa a rayuwarta bata tab'a shiga tashin hankali irin na ranar ba baya tayi da Sauri tare da Niyyar Rugawa Kafin tayi taku d'aya Abba ya chafkota cikin zafin nama da b'acin rai yayi mata wani irin Mahaukacin ruk'o tare da d'auketa da wani gigitaccen mari..............✍🏿 *Kamar yanda na fad’a a page 30 In-Sha-Allah zamu gama book one ma ana free page kenan ku hanzarta biya tun kafin a kammala book one if you want to subscribe pay #200 katin MTN to 07026166536 hoton katin ko transfer masu Vtu suma zasu tura ta number tare da shaidar turowan amma su #300 wanda basu da buk’atar group ma ana ta pc za a tura musu suma #300 zasu biya ta number da na d’ora zasu tura y’an Niger kuma kumin magana ta wannan number +234-7026166536 zan turo muku number da zaku tura katin zain na 200 sai a saka ku Group karku manta book d’innan garab’asa ce babba da na sakeshi a 200 kachal Darajarshi tafi ta 1k Ni da Yaya Arman ba a fara komai ba bama a shiga wasan ba wannan duk somin tab’i ne hmmmmm wasan na nan gaba wannan shi ake kira koda kud’inka saida rabonka wannan salon na musamman ne masoyan asali ku harzarta ku biya nasan babu wanda zaizo ayi doguwar tafiyar nan batare da shiba saina jiku*💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾💃🏾 *Share fisabilillah* _*Miss Hajo ce*_🤙🏿 [6/4, 22:40] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏 Hot love story♥️🔐 ```MALLAKAR``` *Hajara

Chapter 5 of 9