dinga hira cikin nishad'i da Annashuwa har lokacin tashinsu yayi ganin anfara fiffitowa yasanya Aira Kallonshi ta ce " My yaya antashi Kar malamin mu ya ganni"To my cutie sai gobe Ai zamu had'u ko "murmushi tayi ta ce " Insha Allahu "wasu manyan ledoji ya mik'o mata guda biyu d'aya kayan makuleshene su choculate, biscuit'juice kala kala d'ayar kuma Kaza ce gashin oven guda biyu " .
Kallonshi tayi a hankali ta ce "Thnks Yaya " Harararta yayi ya ce "ban hanaki yimun Godiya ba" Cikin shagwaba ta ce "Yaya aidole na maka Godiya ko Allah idan muka gode masa dad'i yakeji ya k'ara mana fiye da Wanda ya bamu a baya" Murmushi yayi ya ce "na manta fa mutuniyar tawa ustaziya ce " Dariya tayi tare da rufe fuska Rafar y'an dubu d'aid'ai ya mik'o mata cike da tsoro ta ce.
"Dan Allah yaya kayi hakuri amma Bazan karba ba inma na karba Allah bansan Abunda zanyi dashi ba" Lokaci guda taga ya murtuke ya ce "Na k'ara magana baki amsa ba ranki zaiyi mugun b'aci kinsan dai banason gardama kuma bana kyauta a maidomun ko a k'i Amsa" Badan Aira ta so ba ta amsa ta ce "Nagode Yaya " lokacin da Arman ya tafi amma ta Iso Suka jera Suka tafi gida a k'asa Nan Aira ta nunawa Amma abunda Arman ga bata sosai Amma tayi mamaki ta ce.
"Chab Kedai Kibi A hankali wlh kuma karki k'ara Amsar kudinshi ko ran nashi zai b'aci karki amsa ai dole ya huce " To Sister Aira ta ce "Sannan ta mik'awa Amma dubu Ashirin ta ce " ga naki sis"kin Amsa amma tayi Aira tayi ta mata magiya ta ce "Dan Allah ki amsa wlh ni Banmasan ta yanda zan kashesu ba " Amsa Amma tayi ta ce "Nima d'in bansan tayanda zan kashesu ba bari dai kawai na amsa" Suna isa gida Aira tayiwa kudinta mugun boyo kayan da ya kawo mata kuma ta ba Inna wasu Inna sai sa mata albarka take taci Wanda ta iyaci sauran ta kaiwa su Amma.
Washegari da Yamma Aira ta shirya cikin hijab d'inta ta gida blue kasancewar Alhamis basa Tahfex a d'aki ta samu Mamy na linki Bayan ta gaisheta ta ce "Mamy Dan Allah gidan su Khady nake son naje idan kin barni zan duba ta bata da lafiya"
"Ke ya akayi kikasan bata da lafiya"jiya da naje islamiya k'anwarta take fadawa Malam kinsan Tahfex d'inmu d'aya "To shikenan kije amma karki jima Dan Allah sannan ta mik'a mata dubu d'aya ta ce " Kiyi kudin transport A a Mamy ki barshi ina da kud'in da Abba ya bani jiya da zani Tahfex "Maida kudinta Mamy tayi batare da ta ce komai ba.
Aira ko tasan wannan karyarce kadai zatayi mamy ta barta ta fita Aira tana zuwa gidansu Khady sun dan taba hira ba ajima sosai ba Arman ya kira ta ba Khady tayima Arman kwatancen gidan ba ayi minti sha ba sai gashi Nan Aira tayiwa Khady bankwana " Khady ta ce "haba kwt daga zuwanki daman Nasan zuwan nan naki ba banza ba " Dariya Aira tayi ta ce "Karki damu Besty zandawo nayi maki yini akwai labari" Har bakin get Khady ta rakata ganin ta shiga motar Arman ya sanyata Juyawa Aira ko da Arman yawo sukasha waje waje cikin nishad'i da Annashuwa Ganin magriba ta gabato ya sanya Aira cewa .
"Yaya ka maidani gida Mamy ta ce kar nayi dare " Okay nima gobe zanwuce ki kulamun da kanki kinji kyakyawata"B'ata fuska tayi cikin shagwaba ta ce "Yaya jiya kazo ka ce kuma gobe zaka wuce" Kinsan yanayin Aikin namune bamuda Hutu sosai Amma ai kinsan bazan jima ba zanzo na k'ara ganinki"Cikin shagwaba ta ce "Yaya daman fa waccen tafiyar saida kayi wata kusan biyu bakazoba"
" yanzu bazan sake dadewaba tunda my prince's bataso kamar karsu rabu da juna Arman ya tsaida mata napep ya bashi 10k mai napep sai Godiya yake saida yaga tafiyarta tukwana ya juya cike da kewarta a duniya shidai ya kasa gane wani irin sone Allah ya jarabceshi dashi na Aira Kwata_Kwata Ko wajen Aiki yaje Allah_Allah yake yazo ya ganta daidai da second d'aya da zai samu dama bazaiso yayi batare da Airanshi ba cike da so da kewarta ya koma gida washegari ya koma Abuja.
Aira sosai take fachaka da kudi Dan ko Abincin gidan ta daina ci saidai ta aiki mai gadi ya sayo mata abunda take so Ummy da Aysha sunyi da ita ta fad'a musu Inda Take samun kud'i amma taki fadamusu .
Yau Aira ta shigo d'akin Mamy kenan ta tarar da Haidar yana yiwa Amer wasa "K'arasa shigowa tayi ta ce " yau kuma Kaine d'an rainon kuma fa kayi kyau da rainon"Hararta yayi ya ce "Mamy ce tace na rik'e mata shi nayi maki kama da d'an Reno matsala ta dake wulakanci wlh ya Aira"Dariya tayi ta ce " Kardai kamun Rashin kunya kayiwa Arziki kulli Yaro "Naji ya fad'a tare da mika mata Amer amsarshi tayi ta ce .
" Ina mamyn take"Tana Part d'in Abba "yawwa nasan ba yanzu zata dawo ba Aikenka zanyi yi Sauri kaje ka sayo mana Kaza da ice cream da shawarma ta fad'a tana fiddo kudi cikin siket d'inta" wara idanu Haidar yayi ya ce "Kam ya Aira ina kika samu kudi dubu goma ce fa kika bani ''ya fad'a yana juya kudin da ta bashi" Hararshi tayi ta ce "Dan kaci sa a zanci dakai shine Zakawa kanka inbazaka sayoba ban kudina" washe baki Haidar yayi ya ce "Chab wa yaga banza ya bari" Dariya Aira tayi ta ce "Uban son banza".
Tana nan zaune tanayiwa Amer wasa sai Dariya yake Ba ayi minti sha biyar ba Haidar ya dawo da leda hannunshi plate suka d'auko suka baje kazar suka fara ci Haidar sai sawa Aira albarka yake tana Dariya ta ce " shegena banza ta samu"Dariya yayi ya ce "Aiko banza ta samu Allah karo na banzar muci mu nare.
basu ida cinye kazarba kowa ya d'auki robar ice cream suka fara sha basusan ba Mamy ta shigo saida sukaji ta ce " Ubanme Kuke ci "cikin rud'u Aira ta tashi tare da ja baya Shima Haidar tashi yayi Kallon kayayyakin dake gadon tayi ta kalli Haidar ta ce " wa ya baku"Nuna Aira Haidar yayi cikin tsoro ya ce "ita ta bani na sayo mana" Kallon Aira Mamy tayi cikin b'acin rai Ta ce "Waya baki kud'i Dan ubanki harkika bada akayo wannan uwar sayayyar" .
yarfe hannu Aira ta fara tare da mik'ewa kan gadon ta fara hawaye ta ce "Dan Allah Mamy Kiyi Hakuri bazan sakeba" Ubanki keda hakurin tambayarki nayi ko hakuri nace ki bani Munafuka sai anyi magana ta dinga yarfewa mutane hannu tana bada hakurin munafurci cewa nayi wa ya baki kud'i"Haidar yayi saurin cewa "Mamy saurayin Aunty Aysha ya bata ".
Kallonta Mamy tayi ta ce "Na tambayi Aishar gyada mata kai tayi ta ce " Eh"Dannawa Aisha kira Mamy tayi tana zuwa ta Kalleta ta ce "Wai saurayinki Aysha ya ba Aira kud'i" Kallon mamaki Aisha tayiwa Aira ta ido Aira ta dinga nuna mata ta rufa mata asiri ta ce Eh "Eh Mamy shi ya bata " jin Abunda Aisha ta fad'a ya sanya Aira sauke ajiyar zuciya Gaskiya Haidar ya taimaketa har ya fita tunanin wannan mafutar Dukda baisan wa ya bani ba .
"Itama Mamyn Ajiyar zuciya ta sauke ta ce " To angode sannan ta kalli Aira ta ce "Shine ko ki fadamun" nazata fad'a zakiyi shiyasa banfad'a maki ba "kede kika sani cewar Mamy Aira da Aisha suna fita suna Shiga Dakinsu Aisha ta tsare Aira da Tambayoyi akan saita fad'a mata Inda ta samu kudi badan Aira taso ba ta fad'awa Aisha Arman ne ya bata har wayar da ya bata saida ta fad'a mata " cike da mamaki aysha ta ce "Chabd'i amma Aira wlh kunfini rawar kai har ki rik'e har iPhone 13 ba tare da sanin kowaba''turo baki Aira tayi ta ce.
" to Karki fad'awa kowa"Ba Wanda zaisani sister Amma ki fad'amun soyayya kuke da Arman koko ki fad'amun Gaskiya insha Allahu zan taimaka maki da shawarwari"k'asa da kanta Aira tayi wasu zafaffan hawaye na zubo mata ta ce "Aunty ina sonshi sosai nima bansan tun yaushe na fara sonshi ba amma dai na sani ina matuk'ar sonshi son da bazan iya rabuwa dashi ba " Cike da tausayin y'ar uwar tata Aysha ta ce "Nasan Hakan zata faru Aira banyi mamaki ba najima da zargin kuna son junanku keda Arman Amma shi ya tab'a fad'a maki yana sonki".
Girgiza mata kai Tayi ta ce "A a a a" Karki damu sis komai zaizo da sauki insha Allahu nima zanbada gudummawata d'ari bisa d'ari Dan Gaskiya Arman dake ya dace haka kema dashi kika dace Allah dai ya sa iyayenmu su yarda Ku auri juna"Sosai Aira taji dad'in yanda Aysha ta nuna tanason tarenta da Arman Ranar sun jima suna Hirarraki.
Haka Rayuwa taci gaba Aira sosai ita da Arman suke shan wayarsu Idan yazo kuma tasan dabarar da zatayi ta fita ba Wanda cikin iyayensu ya k'ara gane tare take da Arman sosai hankalinsu ya kwanta musamman Abba yana murnar Aira ta rabu da Arman baisaniba saima gaba da yayi.
Komai aka sakawa Rana sai yazo ya rage saura sati Ukku biki Aysha Da Ummy suka tafi Umrah sai ana jibi za a fara event d'in suka dawo sosai suka k'ara kyau dan sunsha gyara a Chan baki na nesa da na kurkusa duk sunzo Har Yayarsu Aunty Maryam da ke Aure a Lagos tazo tare da yaranta Zainab(Yasmeen) Ahmad,Sadiq Aunty Halima ma da Hafsa duk sunzo.
Haka aka fara hidimar biki sosai amaren sukeyin kyau ranar farko akai Friend evening rana da biyu walima rana ta Ukku Aka d'aura Auren Bayan kowacce an kaita gidan mijinta sosai Aira suka sha kuka musamman ita da Aysha Da dare aka shirya Dinner sosai amaren da angwayen sukayi kyau Wajen da ake dinner ma an kawatashi Aira ma ba abarta a baya ba Sosai Tasha kyau cikin wani tsadadden lace d'inta purple Anko anyi mata Riga da siket rigar mai dagewar nan sosai kayan suka amsheta ga make up d'inta da tayi bala'in mata kyau ko gyale bata yafe ba.
haka aka fara gudanar da programs d'in cikin tsari Bayan anyi hotuna aka fara rawa sosai Aira ta saki jiki take rawa saboda ansa wak'ar da take mugun so kuma daman tace a bikin yayyin nata saita chashe Sosai ta burge mutanen dake wajen sai lik'i maza ke mata ganin haka ya sanyata saurin Zamewa ta fita daga filin rawar Taje ta zauna a kan chair
tana zama wani ya biyoto ya zauna kusa ta isa Tare da cewa "Y'an mata yakike Gaskiya kin hadu ba k'arya kin burgeni sosai Dan Allah zan iya samun number wayarki" D'agowa Aira tayi ta Kalleshi daga k'asa har sama sannan taja tsoki,.
wayarta babbar ta fiddo zaro ido tayi ganin missed call d'in Arman rututu cikin Sauri ta Danna mai kira Abun mamaki sai taji ringing d'in daga bayanta juyawar da zatayi idanunsu suka sartse cikin na juna Fuskarnan tashi a murtuke Kamar bai tab'a Dariya ba ya sanya hannuwanshi cikin Aljihu sosai Aira tayi mamakin ganinshi ko dai gizau ne yake mata amma ai da Yamma ma sunyi waya yake ce mata yana Abuja Bata gama wannan tunanin ba Taji ya........โ๐ฟ
*Kamar yanda na fad'a a page 30 zamu gama book one ma ana free page to na k'ara muku page biyu wannan shine page din biyun karshe da zamu gama freee Wanda suka sayane kad'ai suke da damar cigaba da karanta wannan littafin ga mai buk'atar saya ya tuntub'eni ta wannan number 07026166536 haka zalika masu buk'atar a tallata musu hajarsu suma su tuntub'eni kan number wayata*
*NORMAL GROUP #200*
*V T U #300*
*PC #300*
_*Miss Hajo ce*_๐ค๐ฟ
[6/9, 12:56] Hajo: ๐ *NI DA YAYA ARMAN* ๐
Hot love storyโฅ๏ธ๐
```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*
๐ *JARUMAI WRITERโS ASSOCIATION * ๐
ุจุณู
ุงููู ุงูุฑ ุญู
ู ุงูุฑ ุญูู
_Last Free Page_
*BOOK ONE*๐
๐
ฟ๏ธ...............33&34
........Ya Janyo hannunta janta ya fara yi tun tana tirjewa harta hakura Dan sosai ta tsorata suna fita farfajiyar wajen Hall din Ya wullata Ta fad'i dafe kanta tayi Wanda da kyal ya hana ya buge kuka ta fashe dashi ta ce.
"Yaya Airanka ce fa da kajimun ciwo fa" Cike da b'acin rai Arman ya nunata da yatsa ya ce "Daman irin abunda kike bana nan,ki shiga filin rawa kina karkada jikinki ko wani k'are da doki yana karewa halittarki kallo kega mahaukaciya,ko gyale babu ga wannan tsinannun kayan da suka matseki ya mukayi dake kwanaki ban hanaki rawa ba sannan ban hanaki saka matsatsun kaya ba ,ban hanaki mu'amula da maza ba ,Duka abubuwan da na hanaki yau na kamaki da kaifinsu daman irin abunda kike bana nan" ya k'arasa fad'a cikin d'aga murya .
Aira sosai tashiga tashin hankali tasan Idan ran Arman ya b'aci bai iya fushi ba Batasan lokacin da ta tashi ba ta fad'a jikinshi tare da sakin kuka ta ce "I'm so sorry yaya Bazan sakeba forgive me please kayi hakuri " Ajiyar zuciya Arman ya sauke sai yaji zuciyarshi tayi sanyi yana daga cikin abunda yake k'ara mishi k'aunar Aira da idan tayi laifi zata bashi hakuri koda kuwa itace mai Gaskiya bata da girman kan bada hakuri.
daddab'a bayanta ya fara cikin kwantar da murya ya ce "yi shiru daina kukan is okay na hakura Amma karki sake kinji my cutie idan ba so kike zuciyata ta buga ba " Sosai Aira taji dad'i k'ara Rungumeshi tayi tare da Murmushi ta ce "Thnks yaya shiyasa nake sonka kana da saurin yafiya" Sai kuma ta rufe bakinta sai yanzu ta tuna b'aram b'aramar da tayi murmushi Kad'an Arman yayi sannan ya janyeta daga jikinshi
kama hannunta yayi ya bud'e mata mota suka shiga ta na Front sit shi kuma yana mazaunar driver A hanya Aira ta ce "Amma Yaya ya akayi kazo wajennan Bayan nasan baka gari kuma bakasan Wajenba" Cutie kenan Kin manta yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba"Cike da mamaki Aira ta ce "Yaya kiwon mutum kuma me kake nufi" Ina nufin kome mutum yake a idon mutane yanda akai nazo wajennan a isha'i ma ina Abuja Wajen 9:45 haka Wani Abokina Dake nan kano ya kirani yake Cemun yaga kanwata wajen wata dinner.
Sosai nayi mamaki nace wace kanwartau sai yake Cemun nahau what's app zai turomun videon ta na gani idan ita ce "Ina hawa ya turomun videon ki kina rawa wasu tsinannun y'an iska na miki lik'i karkiga yanda hankalina ya tashi ban k'arasa Kalla ba na tashi na tafi Airport na yanki ticket na taho Ina zuwa na kirashi yayimun kwatancen wajen shi kanshi saida yayi mamakin cewa Na shigo garin"
Cike da mamaki Aira ta ce "Chab Amma abokin nan naka anyi Dan sa ido to shi a ina ya sanni" A Hoto"Hoto kuma yaya a ina kenan Nida ba post din hotona nake social media ba "Hararta yayi ya ce " kima fara mana ki gani"
Dariya tayi ganin yanda yayi maganar ta ce "wace ni wa ya haifeni a garin nan " Dariya yayi Kad'an sosai Komai Aira tayi take burgeshi ya ce "a d'akina da ya tab'a shiga Yaga hotunanki a lokacin ya nuna mun yana sonki na cemai kanwata ce kuma anyi mata miji Sai ya hakura " murmushi Aira tayi ta ce "Me ma zanyi da d'an sa ido gwara da kace mashi haka dukda dai ba ayimun mijinba".
Harar wasa yayi mata yace "wa ya fad'a maki ba ayi miki miji ba Ai nariga da zab'a miki mijin da ya dace dake ko bazaki amince da zab'in yayanki ba" Murmushi tayi tare da Kauda kai ta kalli gefen titi Dan batason maganar"Baikara cewa komai ba harsuka isa gida lokacin 12pm danma Allah yasa a gida Ansan Dinner sukaje kuma a motar gida sukaje A ita za a maidosu saitaje ita gaba tayo,
Bye bye tayiwa Arman Ta ce "Sai gobe yaya daan Allah gobe ka shigo Inna fa na nemanka" karki damu cutie zanshigo goben "Thnks my yaya bye bye ta fad'a tana daga mai hannu saida yaga shigarta tukwana ya wuce guest house d'inshi Dan yanzu yaje government house Mummy cewa zatayi ba Lafiya ba gwara ya bari sai gobe yaje ba .
Washegari Aira da Amma sukaje suka gygyarawa yayun nasu gida saida yamma suka nufo gida kamar karsu rabu A Hanya Aira ta ce " Amma bakiga Aunty Aysha iyayin nan yau duk tayi lakwas ko bata lafiya dai bakiga ba a sanyaye take ba Yau shikuma Yaya Abdul sai wani lillike mata yake ba ko kunya a gabanmufa dazu yayi mata kiss".
Dariya Amma tayi ta ce "Kikak'i tambayarta kafin mu taho kema da kukafi kusa baki saniba bareni y'ar karoro ko mu koma ki tambaya" Waro idanu Aira tayi ta ce "Rufamun Asirin Har ya koro mu" Dariya Amma tayi sosai ta ce
"Nikuma ya Ummy ce ta ban Mamaki ji fa yau hada cewa Dan Allah karmu tafi mu bari sai Bayan Isha'i Yaya Usman ya maidamu yau ko jarabar babu "Dariya Aira tayi ta ce " Ba dole taso muk'i tafiya ba Barin gida ai saidole Ni ko tausayi bata banba yanzu dai shikenan mune manya a gida Aira ta fad'a tana murna Dariya Amma tayi ta ce "Wlhko muci karanmu ba babbaka Har suka isa gida Suna gulmar yayyin nasu.
Bayan kwana biyu Arman ya koma Wanda dak'yal Ya shawo kan Aira saida ya shaida mata nan da two weeks zaidawo yayi hutun One months sosai Aira tayi farinciki haka ko akayi baiyi sati biyu ba ya dawo Aira jinta take cikin Farinciki Marar musaltuwa Tunda yazo Aira ta tarki k'aryar fita Wanda Aysha ce ta d'aure mata gindi saita kira Mamy ta ce " Dan Allah Aira tazo ta tayata Aiki haka Mamy zata barta batare da kokontoba Dan yanzu Hankalinta ya kwanta a tunaninta Aira harta mance da ARMAN.
A palourn Aysha suke zauniya su sha Hirarsu Saisu shafe awa Hud'u suna Hira Yauma yazo Aysha ta sa Aira ta kawo mashi snacks Kad'an yaci Shima Dan Aisha ta nuna bazataji dadi ba Sosai Aira da Arman suke shan hira Sai wajen magriba Arman ya tashi yace zasu wuce "
"tashi Aira tayi ta ce " bari naje nayi mata bankwana saimu tafi "ta fad'a ta na Zuwa Palourn Chan ciki Inda Aysha take da mijinta " Abdul ya ce su Aira manya Angama Shan Love din"Dariya tayi tare da rufe fuska ta ce "Kai yaya kaima haka zakace Nasan Aunty zata fad'a maka " Aysha dake jikin mijinta kallon Aira tayi ta ce "Ai yanzu ba wani rufe rufe y'an matan Abba yanzu kuma sai ina".
Uhm gida zamu wuce"Okay to ki gaishe da mutanen gidan"To Aunty zasuji "Saikuma yaushe " Sai idan kuma an barni kinsan dazu dak'yal Mamy ta bari cewa tayi nafiya miki zarya"Dariya Aysha tayi ta ce "Lallaima Mamy Danma batasan ba ba saboda ni ake zuwaba Duka zuwan na Arman"
Dariya tayi ta ce "Kai Aunty Nifa saboda ke nake zuwa Yanzu dai munwuce kar ya gaji da jira" Okay to Allah kiyaye Aira harta juya zata fita Aysha ta kira sunanta Juyowa tayi tashi Aysha ta kama hannunta ta ce "Sis karki bari wata matsala ta afku kidinga bi a hankali kinsan Abba yasan kuna had'uwa da Arman a gida na ni kaina na shiga ukku sannan ku daina yawo barkatai a gari Dan Allah saboda gudun zargi "
k'asa tayi da kanta ta ce "Insha Allahu Aunty zan kiyaye " Hug din juna sukayi tukwana Aira ta tafi Bayan Aira ta tafi Mijin Aysha ya ce "My love abunda kike kina kyautawa kuwa?Cike da mamaki Aysha ta ce " Me Dia"Na barin Aira da Arman suna kebewa anan mana Bayan iyayenku a yanda kika fad'amun sun rabasu me zaisa ki basu shawarar su hakura da juna Ita kuma ki bata shawarar ta tunkari karatunta Amma wannan hanyar da kika bud'e musu ba mai bullewa bace
yanda Abba keda burin y'ay'anshi suyi karatu banga Alamun ko Kad'an a idon Aira akwai wani karatu a ranta ba bakiga Duka Rayuwarta a soyayyar ARMAN take tafiya ki bata shawarar Ko bazata rabu da shi ba ki nuna mata karatu zatayi kafin inma auran ne ya biyo baya bakiganin yarinyace marar wayau"ya k'arasa fad'a yana Jan numfashi
"Shiru Aysha tayi Tabbas hakane cike da damuwa ta ce " Baby bazaka gane bane Aira da Arman suna matuk'ar son junansu Wanda ni kaina bazan iya kwatanta maka kalarsa ba ta Riga ta mutu a kanshi tun kafin tasan kanta Shima kuma haka sauya musu ra'ayi Abu ne mai wahala dalilin da yasa kuma nake barinsu zuwa nan dole ne fa saisun had'u a koma ina ne gudun kaucewa hanya kasan ance duk Inda mace da namiji suka had'u na ukkunsu shaid'an ne dukda nasan ba halinsu bane amma kiyayewa na da kyau hakan yasa nace su dinga zuwa nan yafi kwanciyar hankali akan suje wani wajen daban
Ina son y'ar uwata Abdul sosai bantaba Jin a raina ba wai ba ciki d'aya muka fito da Aira ba sonda nake mata yafi son da nake yiwa wanda muke uwa d'aya uba d'aya Dan haka bazanyi Abunda zai chutar da ita ba "hakane kuma baby da wata ya wannan Allah dai ya kawo musu mafita cikin Sauk'i " Ameen Aysha ta fad'a .
Aira ko Arman har gida ya maida ita kullum saisun had'u idan basu hadu ba idan zata tahfex to sun hadu idan ta dawo Innace ta fito Cikin masifa Kallon Aira tayi tare da mik'a mata wayar ta ce " kiramun Mujahid laifin me nayi mishi da ya daina zuwa wajena "Aira ta kira mata Mujahid yana ganin kiran Inna murmushi yayi ya kira cikin Masifa Inna ta ce "
Mujahid ko d'an fari na kashe maka ai sai haka watanka nawa rabonka da gidana "Hakuri Arman ya dinga bawa Inna tare da cewa gashinan zuwa yanzu Lokacin da yazo Aira na zaune akan sopa tana kallon wani series a Bollywood Hankalinta na wajen ya shigo tana ganinshi itama ita yake kallo kashe mata ido yayi girgiza kai tayi ta na murmushi inna ko washe baki tayi ta ce ""
" Ko kaifa mai gidan Har hankali na ya kwanta ashe ma kana garin shine Ko kazo ka gaishe ni ko"To yanzu ba nazo ba y'ar tsohuwa sai a rufe chapter ya fad'a yana zama kan sopa K'asa Inna ta zauna Suka shiga gaisawa da Arman sai zolayanta yake dayake tana son ganinshi yau ko fad'an Babu Kallon Aira tayi da take kallo ta ce .
"Hajara bakiga Mujahid ba ne Kika wani kauda kai" Juyowa Aira tayi ta ce "Na ganshi Inna ta fad'a tana kauda kai" Hakan da tayi duk cikin shirinsune "Salati Inna ta farka ta kalli Arman ta kalli Aira ta ce " Nashiga Ukku ni Halima ba dai Iyayenku sunyi nasarar raba ku ba.
Kallon Inna Aira tayi ta kalli Arman dake satar kallonta tashi Inna tayi Ta kamo hannun Aira ta janyota ta had'a da na Arman ta fashe da kuka ta ce "Karku sake Iyayenku su zama sanadiyar lalacewar daddaddiyar Tarayyarku mai cike da Albarka Na tabbata Allah da abunda ya gani ya had'aku Karku sake ko dad'i ko wuya suyi nasarar rabaku koda bana numfashi Duk sanda alak'arku ta lalace to ina da tabbacin komai ya Riga da ya lalace Iyayenku bazasu tab'a Shiryuwa ba muddin bakwa tare da junanku Kune nake fatan ku zama silar Daidaituwar Iyayenku kuyimun Alkawari Dan Allah bazaku rabu ba kodan ni ko da bana raye" .
Aira tunda Inna ta fara jawabin nan take kuka Rungume Inna tayi Cikin kuka Ta ce "Insha Allahu Inna munmuki Alkawari sannan ma kina raye insha Allahu" Arman ma Rungume Inna yayi cikin k'arfin hali ya ce "da yardar Allah Inna zamu sanyaki Farincikin da kike buk'ata da ranki insha Allahu" Allah yayi muku albarka Ya nunamun Ranar da nake ta tsumayen jira da raina da lafiya"Kallon juna Arman da Aira sukayi sai